Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

su a jiki ,
ihu Rayyanat ta saki ta tashi a firgice tana lalubar bayanta inda taji saukar ruwan zafi.
Mari pretty takai mata tace"er iska ai yau sae kin bar gidan nn wlh tunda bana ubanki bane!
Taja Rayyanat kamar wata kayan banza ta ingizata waje da qarfi sae kawai Rayyanat taji ta fad'a jikin mutum hkn yasa taji saukar wani irin gigitaccen marinda ya soma fitar da ita hayyacinta.

Billy giro😊
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
🔮```BAZAN BARSHI BA!```🔮

```Na Billy giro😊```

17/12/2016

🔮```8```🔮
La'ilaha ilallahu Muhammadu rasulillahi sallallahu Alaihi wa sallam!
Cewar inna wacce ta fito daga gurin wanka tace"Muhammad me rayyanah ta muku ne da zaku mata taron dangi tun ina bayi naji ihunta Fatima na faman sirfa mata masifa yanzu gashi na samu ka tafka mata uban mari haka!inna ta qarasa magana cikin muryar kuka irin na tsafi d'in nan.
Nan take man damuwar sa ta bayyana ya shiga bawa inna haquri bata kula shi ba sae kuka take taja Rayyanat suka koma cikin d'aki.
Pretty ta kalli man dake qoqarin bin su inna tace"to wai meye abun damuwa kabar su mana tunda kasan halin inna dama saurin kuka ne da ita in ba don shi ba meye abin kuka wa wannan er qauyen,harara ya dalla mata yace ai duk ta dalilin kine banga uban me ya kawo ki gidan nn ba....kamar ya yaya...zan mare ki wlh idan baki 6ace min da gani ba!
Turo baki tayi tana faman gunguni har ta fita gidan.
Man kuwa shiga d'akin yayi amma a iya falo ya tsaya inna ta fito tana shar6ar hawaye zata d'auki wayarta dake kan TV stand yace"inna yi haquri Allah sam na d'auka rashin hnklinta ne yasa ta fad'o min a jiki ban san cewa pretty ce ta ingixo ta ba,amma Muhammadu ai ka saurara mata ko! yanzu gashi bayan fasa mata baki da kayi duk bayanta ya kwaye... Kamar ya inna nifa marinta kawai nayi... Yo kai ba kasan ruwan zafi pretty ta watsa mata a baya ba,shiga ka duba ta kaga ai nasan dole sae an yanke wnn ftr ,ta qarasa maganar cikin kuka snn tace"ka shiga mana ka duba min yarinyar mutane kazo kayi tsaye se kallona kake!
Ba musu ya shiga ya sami Rayyanat ruf da ciki se kuka take abin tausayi zip d'in rigar ta a bud'e fatar bayanta har yyi ja, kauda fuskar sa yayi tare da sauke ajiyar zuciya snn ya kalli inna dake tsaye kusa dashi tana matsar kwalla yace "inna ina ganin ta sosa bayanta ne a lokacin da aka watsa mata ruwan, kuma wnn da gani ma ba wani ruwa me xafi bne, Rayyanat da bata ji shigowarsa dakin ba sae maganar sa taji tayi saurin tashi xata rufe zip d'in rgrta, inna ta karaso da sauri
tace "A'a Rayyanah kar ki rufe ai shi likita ne zai duba miki bayanki in kuma baxae iya ba sae ya kira mana ubansa ya xo ya kai mu asibiti," Rayyanat ta girgiza kai ba tare da ta kallesu ba alamar bata so, inna tace "A'a ki yi haquri ya duba ki kinji jikata"
Man da takaici ya ishe shi yace "inna bari kawai zan turo a duba ta" yana kai wa nn ya fice daga dakin kmr xae tashi sama.

Sae da ya kira wani abokinsa likita snn ya bar gidan ya nufi gidan kanwarsa pretty.
Yana isa gidan Nasir ya samu kan dining sama sama suka gaisa yace masa "ina pretty" kafin ya basa amsa sae ga prettyn ta sauko, bata damu da ganin fuskar yayanta ba annuri ba ta daure fuska ssae tace "gani yaya lafiya dai ko"
Yyi mata wani mugun kallo yace "me wnn yarinyar ta miki da zaki xuba mata ruwan xafi a jiki," shiru pretty tayi tana kallon shi kamar bata san me ya faru ba har lkcn fuskarta a tamke, ya daka mata tsawa yace "ya kika min shiru kina kallona ina maki mgna?" Ta tabe baki tace
"To nifa yaya ban gane zancen da kake ba bare na iya ce maka wani abu," nn ya fahimci ta fita ne bada ixinin nasir ba shine take wani nuna kamar bata san da zancen ba.
mari ya kai mata don bata da nisa daga inda yake yace "yanzu kin fahimci zancen nawa!ko kuma sae na qara miki wani," da sauri taja baya tana kuka don ganin da gaske yake, tace "to shine zaka wani mareni wlh sae na gaya ma umma!
daga haka ta tafi da gudu tana kuka ta haura sama.
Duk da Man ya fahimci Nasir yana buqatar jin bayani bai tsaya yi masa ba ya tafiyar sa hakan yasa nasir ya tafi ya haura sama gun matarsa da shima ya fahimci gidan inna taje bai sani ba.

Da shigarsa ta taso ta rungume shi tana kuka tace "ka gani dai ko honey ban masa komai ba yazo ya mareni," mugun kallo yyi mata yace "bana son qarya pretty nasan halin Man ba zai zo haka kawai ya mareki ba ,ba makawa gidan inna kika je gun Rayyanat kika aiwatar da nufinki ko?" shiru tayi alamar can taje d'in, nn ya shiga yi mata fad'a sosai daga qarshe yace duk ta qara fita bada izinin sa ba sae ya sanar da Abbanta, fushi ta shiga yi dashi bai kula ta ba ya tafiyarsa yaci abinci ya fice daga gidan.

Gidan inna ya nufa yaje yaga aikin da pretty tayiwa Rayyanat lokacin ma har likita ya xo ya dubata, bata wani kone ba sae dae fatar jikinta da yyi ja ssae.
Sosai ya bata haquri daga ita har inna da abun yabi ya dama har tana cewa a kira mata kabiru, Nasir dae ya dinga bata haquri yace shi zai yi maganin abun amma fafau inna tace ita fa sae taje shima zai kaita gidan da kanshi.

Haka ko akayi dmn tare suka fita shida inna suka bar Rayyanat ita da hurera.

Wani makeken gida suka nufa kyace gidan shugaban qasa ne kan tsari da kyawo irin nashi, kuma ba wani gida bane face gidan su Nasir d'in da kuma su pretty wato qanwar man sbd gabad'ayan su family's ne en wa da qani ne,
Baban su Man shine babba snn mahaifin Nasir bayan shi kuma akwai wani Alhj sa'eed wato qanin mahaifin Nasir inda shi kuma yana da qanwa mai aure a garin kd dukkan su 'yayan inna ne shine maxan suka had'e kansu suna zama gida d'aya sae dai kowa da nasa 6angare.
Suna shiga gidan
inna ta nufi 6angaren su pretty sae ga wata yarinya tazo da murna ta tarbe ta tana fad'in "he inna nida nake batun zuwa gurinki shine kika zo, inna ta washe baki tace "tukuna saukar yaushe Ameera? Yau yau d'in nan aka bamu hutu inna ,to ina er uwar taki saliha? "Tana 6angaren su tare ma ne zamu tafi gurin ki nasan yanzu haka ta shirya tana can tana jirana wlh, inna tace "ayyo to ai yanzu komawa zanyi sae mu tafi tare je kira min Abbanku kabiru yazo ina da magana dashi, tace "to inna zauna na kira miki shi"inna ta zauna ita kuma ta haura sama.

Nasir kuwa wani 6angaren ya nufa da alama shine na iyayensa dmn matar da ya samu zaune a falo sak suke kama dashi, cike da ladabi yaje ya durqusa ya gaisheta yana qoqarin tashi yaji an rungume shi ana fad'in "oyoyo yaya" cike da murmushi yake kallon wacce ta rungume shi yace "A'a saliha shin yau ne hutun ku ko to wa ya d'auko ku?
turo baki tayi snn tace "Abba ne yaje da kanshi tunda kai kaqi zuwa "oh no saliha yi haquri sam na manta da yau ne hutunku amma umma ya akayi ba a sanar dani ba sae Abba ne yaje da kanshi? Mamar tace "Abban ne yace akwai aikinda yasa ka shine ya tafi dakanshi ya d'auko su, Nasir yace "eh gaskiya ya bani aiki tun jiya ban samu na qarasa ba amma inshaAllah yanzu zanje office na kammala kafin ya tambaye ni, nn ya kalli saliha yace "ina zuwa haka naga kinci kwalliya? Tace "Gidan inna zamuje nida Ameera," eyyah ai tare muka zo nida inna tana ma 6angaren su Ameera, Saliha ta 6ata fuska tace "ita ko dai inna...ai ba jimawa zatayi ba dn inaga sae na maida ita gida ne ko zan tafi office ,yauwa bara naje na ganta, cewar saliha wacce ta tashi cikin murna ta fita.
Nasir ya kalli mahaifiyar sa da kulawa yace"umma ina yarinyar da na gaya miki cewa nakaita gidan inna? Hajiyar tace "eh na ji" "wlh pretty yau taje ta mata lahani a baya ta xuba mata ruwan zafi, inda Allah ya taimaka ma ba wani xafi ga ruwan ba" Hajiya ta gwalo ido tace "ni kuwa yaushe pretty zata yi hankali ne tukuna me ma ta mata da tayi mata wnn d'anyen aikin? Nasir yace "Kawai don tana jin haushin an hanata tuqin mota a dalilinta kuma kinsan halin pretty ta tsani talaka ba kad'an ba, cikin damuwa mamar tace "to kai nasir baza ka sallami yarinyar mutane bane ka huta, shawarar da nazo yi dake kenan umma don gsky bana son wani abu ya sake faruwa da ita duk da nayi ma pretty kashedi amma hankalina zai fi kwanciya idan ta koma ga en uwanta sae dai inna ce matsala don yanda Rayyanat ta kwanta mata a rai ba lalle bane ta yarda da hakan zata iya cewa a kaita gun en uwan Rayyanat d'in in yaso ta nemi alfarmar su bar mata ita ta riqa yi mata en wasu aikace aikace in yaso duk wata ta riqa biyanta kinga kuwa duk dai ba'a rabu ba dmn gsky nafi son Rayyanat ta komawarta gun en uwanta.
umma ta nisa tace"to ya kake ganin za'ayi haka? Ya dan yi shiru snn yace "Eh to ina ganin kawai zan maida Rayyanat ba tare da sanin inna ba sae bayan na dawo na snr da ita kinga dole zata haqura.

Billy giro😊

🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
🔮```BAZAN BARSHI BA!```🔮

```Na Billy giro😊```

19/12/2016

🔮```9```🔮. And. 10
To shikenan Nasir amma ina son kafin Ku tafi kazo min da yarinyar na samu abinda na bata don yarinyar ta bani tausayi wlh har dai in na tuna ko wane hali en uwanta suke ciki na rashinta oho Allah kad'ai ya sani.
Wlh umma nima tunanina kenan kullum gashi taqi fad'a bare naji ko akwai lambar wayar su a kira a snr dasu halin da take ciki amma yanzu Alhmdlh tunda taji sauqi zan lalla6ata ta gaya min sae na maida ta.
Nasir Yayi mgnr ne yayinda ya tashi yace "to umma ni zan tafi "
Umma tace "To ka gaida innar" yace "to" snn ya fita.

Nasir na fita ya nufi 6angaren su pretty ya d'auki inna dasu saliha suka wuce.

Hajiyarsu pretty na fitowa daga bathroom sae ga mai gidanta ya shigo ransa a 6ace ta kalle sa da kulawa tace "lafiya Alhj me yake faruwa ne?" da taikaci ya kalle ta snn yace" ni nasara wace irin tarbiya ce kika bawa 'ya'yanki? kaf dangin nn ba wanda yakai su rashin mutunci idan suka tashi, musamman ma Fatima" nn cikin fad'an duk ya kwashe abinda inna tazo ta gaya mai har da yaron da pretty ta kad'e kwanaki don duk shi bai sani ba.
A fusace ya d'ora da cewa "kiramin ita yanzun nn tazo ina son ganinta, kwata kwata daga yau ma ta daina jan mota na hanata"
Umma ta dan tabe baki tace "ni dae kayi haquri Alhj, ai ba laifinta bane tsautsayi ne da kuma qaddara...." Rae bace Alhj yace "idan wnn tsautsayi ne me yakaita gidan inna har taje ta watsa ma er mutane ruwan zafi a jiki ko shima tsauyayin ne! Ku fa kiyaye ni ke da 'ya yan ki" ganin ynda ransa ya bace yasa tace "Ayi haquri Alhj bata kyauta ba dae, amma zancen tuqa mota tuni yayanta ma ya kar6e motar," Alhj yace "yayi dai dai don in kece baza Ki kar6e ba duk kinbi 'ya'ya kin lalata da baqin so sae kace kanki aka fara haifuwa.

Nasir na sauke su inna gida ya wuce office bayan sun shiga gidan, saliha da Ameera suka shiga kallon Rayyanat da ke zaune ta lanqwashe qafafu tana shan fura a falon, kallo d'aya Ameera tayi mata ta kauda kai sbd ta gano ita ce yarinyar da inna taje tana faman masifa akai don a gabanta akayi komai ita da saliha.
Saliha kuwa kallon Rayyanat take da d'an murmushi a fuskarta ta kalli inna tace "inna wnn itace Rayyanah?" Inna ta washe baki tace "eh ita ce er albarka babu ruwanta wlh" Saliha tace "eyyah sannu Rayyanat ya jiki?" D'an guntun murmushi tayi snn tace "Alhmdlh" a takaice.
Ameera ta ta6e baki taja hannun saliha tace "ke ni tashi mu tafi gidan inna hajjo mu gaidata" (wata makociyar inna dake nn kusa bbu nisa)
Inna ta washe baki tace "to in kunje ku kar6o min nono na samu na dama furar anjima" nn ta kwance ha6ar zanen ta ta basu nera d'ari tace "ku siyo na duka," Ameera ce ta kar6i kud'in tana walwale su tana dariya ganin yanda suka tamure tace "kai inna wai har yanzu baki daina dunqule kud'i a ha6ar zani ba" bata jira cewar Inna ba ta ja Saliha suka fice daga falon, sae a snn Rayyanat ta gaida inna da ladabi, inna ta amsa da fara'a tace "sae ynxu kike shan hurar, ya bayan in ga ni?" Rayyanat ta dan xuge zip din rigar jikinta inna ta duka da sauri tana kallon bayan, kmr xata yi kuka tace "Allah ya Isar maki, da bayan nn ya tashi yau da anga xube xuben ruwan xafi a jiki don duk sae na tafasa ruwa na bi ta har gidan mijinta na kona ta ni ma" Hurera dake kitchen ta fito tana dariya tace "A'a ba ayi hka ba Inna, Allah dae ya tsare" inna tace "ae ynxu ma daga gidan ubansu nake, kuma yace anjima da daddare xae xo ya gane ma idonsa" Bude kofar falon aka yi, duk suka juya don ganin wnda xae shigo, inna na ganinsa ta tsuke fuska, ya karaso falon fuskarsa a tamke, Rayyanat tayi saurin gyara rigarta, a fusace yana kallon inna ya soma magana "don me xa ki je ki hada ni da Baffana kan wata bnxa can yar kauye Hajiya," inna ta tabe baki tace "sae dae kae ne bakauye ko uwar ka amma ba yar nn ba," xaro ido yyi yana kallonta, ita ma ta yo waje da ido tace "kwarae kuwa!" Rayyanat da tun shigowarsa falon ta sunkuyar da kanta hawaye ya shiga bin kuncinta, ya huzar da iska ya cije lebe lkci daya idonsa ya kada, ya juya fuuu ya fice daga falon, inna tace "Wawa kawae." Baaba hurera ta sauke ajiyar xuciya tace "Ayi hkuri dae inna" mikewa Rayyanat tayi har lkcn hawaye na bin kuncinta, Inna na ganin hka ta rude ta shiga tambayarta lfya, Rayyanat ta kasa bata amsa, hkn yasa inna ta fashe da kuka tace "yo baki ji nace shine dan kauyen ko uwarsa ba, ni dae na shiga uku da 'ya yan kabiru" lkci daya Rayyanat ta hadiye kukan da take tace "kiyi hkuri inna, ni ba shi yasa nake kuka ba, naga ina ta hada ki da jikokin ki ne" cikin kuka ta karashe mgnr, inna ta hade rae tace "suke dae hadani da ke, kuma Allah ya fi su" Baaba hurera tayi murmushi, Rayyanat ta duka ta dauki sauran furan da take sha ta nufi kitchen.
Da rana nasir ya shigo gidansa, ya nufi dakin pretty ganin bbu kowa falon ga ko ina kaca kaca, xaune ya sameta sae fushi take, yaje kusa da ita ya zauna ya shafi gefen fuskarta yace "nasha gaya miki ki daina fushi baya miki kyau," hararar sa tayi snn taja tsaki tace baka son nayi fushi shine zaka kaini qara gun daddy," Nasir ya xaro ido yace "au kin dauka nine, to inna ce taje da kanta ta gaya mai aikin da kikayi don haka ko yanzu kika sake gigin aikata wani abu akan Rayyanat zata je ta snr dashi ne," cike da bacin rae ta tashi tana masa mugun kallo tace"ni yanzu banda lokacin wnn er qauyen bare na qara kulata" ta ja dogon tsaki daga haka ta wuce fuuu! ta barshi nn zaune" girgiza kansa kawai yayi ya tashi yaje ya bud'e fridge ya tsiyaya ruwa a cup yasha.

Washe gari ya gama shirin sa tsaf yaje d'akin pretty wacce yanzu ne tashinta zata shiga Bathroom dmn yin wanka.
Bai qarasa inda take ba a iya gun dressing mirror ya tsaya ya ajiye mata kud'i yace "zanyi tafiya ne ban kuma san yau ko gobe zan dawo ba" ta hade rae tace "ina zaka tafi?" Ya daga kafada yace "Kina da sako ne?" daga haka yyi ficewarsa, ta6e baki tayi gami da jan tsaki tace "aikin banxa, kadda Allah yasa ka dawo ma"

Nasir bai zarce ko ina ba sae gidan inna cike da niyyar ya d'auki Rayyanat ya maida ta gun en uwanta. Bbu kowa falon Inna, hkn yasa ya nemi gu ya xauna yana tunanin ynda xae fita da Rayyanat ba tare da sanin Inna ba, Baaba hurera ce ta shigo falon daga kitchen, da mamaki tace "A'a Nasiru yaushe kuma ka shigo" yyi murmushi ya gaisheta ta amsa da fara'a tana tambayarsa ya kwanan pretty, ya amsa da Alhmdllh snn yace "Baaba Rayyanat xa ki kira min amma fa kar ki bari inna tasan da ina gidan nn" tace "to bari in kirata" ba a dau lkci ba ta dawo falon Rayyanat na biye da ita a baya, hijab ne har kasa jikinta yasan inna ce ta sa aka dinko mata, ya kafa mata ido har ta karaso ta xauna kasa kanta a sunkuye ta gaishesa, ya amsa yana murmushi ya tambayeta ta tashi lfya, kai kawae ta gyada masa, bae kuma cewa komae ba har na kusan minti biyar hkn yasa ta dago kai tana kallonsa da manyan idanuwanta, murmushi ya sakar mata ta dukar da kanta da sauri, ya kira sunanta a nutse ta amsa ba tare da ta kallesa ba, yace "nasan yan uwanki na cikin tashin hnkli Rayyanat, kiyi hkuri ki gaya min ina ne garin ku" Rayyanat tayi kkrin ganin hawaye bae sakko idonta ba a karo na farko ta gaya masa sunan garin a hnkli, ya gyada kai da gamsuwa yace "to ina xa ki pretty ta kade ki da mota?" Ta girgixa masa kae da kyar tace "garinmu xan ko ma" yyi shiru snn yace "to da me ya shigo da ke kano? Shiru tayi taki cewa komae hkn yasa yace"kin shirya komawa garin naku gun yan uwanki ynxu?" Gyada masa kai tayi kawae, yyi shiru na wani lkci snn yace "to tashi ki dauko ledan kayan ki, amma kar ki Bari Inna ta ganki" tace "to" snn ta nufi dakin da Inna ta bata tana murmushi a ranta tace "don xan tafi ba yana nufin na bar shi bane, har abada baxan bar shi ba, nemo sa baxae min wahala ba tun da na ga gari."

Billy giro😊
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
🔮```BAZANBAR SHI BA!```🔮

```Na Billy giro😊```

22/12/2016

🔮```10```🔮

A sanyaye Rayyanat ta dawo falon rike da ledan kayanta ta samu har nasir ya fita xuwa gun motarsa, ita kad'ai yake jira taje ta bud'e gambun motar a hnkli xata shiga ta tsaya cak jin murya inna a bayanta tana fad'in "Rayyanah me zan gani hka ina kuma zakije har da leda a hannunki?"
Sake gambun motar tayi ta juya tare da sadda kanta qasa ta ki barin su had'a ido da inna, ba shiri Nasir ya fito daga cikin mota ya tsaya yana d'an kame kame sbd yanda inna ta tsare shi da ido baki bude.
Kmr xata yi kuka tace " kaddai mayadda rayyanah zaka yi baka ko snr dani ba Nasiru"
Ya dan sosa keya yace "Aa inna, dama wae da.." sae kuma yayi shiru. inna ta fashe da kuka tace "dama me nasiru! mayadda ita zakayi d'in knn, na rasa dalilin da yasa aka rainani hka, ynxu da bn fito ba sae dae in nemi yar nn in rasa" ta fashe da wani matsanancin kuka har da dukawa, Nasir yyi murmushi yace "kiyi hkuri Inna, kuskure ne" inna ta dago ta tsuke fuska tana kallonsa tace "rufe min baki munafuki kawae" dariya yyi yana shafa kansa yace "na yarda, amma inna baki tunanin halin da yan uwanta da iyayenta ke ciki ynxu? Ynxu misali lkci daya a nemi pretty a rasa wani hali kike tunanin xa mu shiga gaba daya" lkci daya inba ta marairaice tace "ni fa ban ce kadda a mayar da ita gun iyayenta ba, kawae rashin sanar dani da ba ayi bne ya bata min rae" Nasir yace "to ayi haquri inna," ta galla masa harara tace "yo da ban hkura ba da ban tara maka mutan anguwar nn ynxu ba," dariya yyi yana kallonta, tace "ynxu dae dani ya kamata muje gun en uwan nata su ganni nima na gansu na samu ko zasu bar min Rayyanah in rike, ni dae yarinyar ta kwanta min in sonta" ta karashe mgnr cikin kuka, tana matsar kwalla tace "ka ga idan Allah ya kawo mata miji na gari sae tayi auranta,"

Ba yanda nasir ya iya yace "to shiknn inna jeki d'auko mayafinki mu tafi"
Inna ta washe baki ta ja hannun Rayyanah tace "zo ki rakani er albarka bazan barki a nn ba don tunda yayi niyya zan iya dawowa na samu ya tafi dake ne kawae,
ko meye dalilin hkn da yyi ne oho," nn dai inna ta jata suka tafi ciki don dauko mayafinta.
Har yaja mota inna bata bar mitan da take ba, hkn yasa nasir sam ya manta da zancen kaiwa umman shi Rayyanat kamar yanda ta buqata.
Tafiya sukayi ba mai wani nisa sosai ba dmn da kano zuwa qauyensu awa biyu ne sae dai tun lokacin da suka kama hanya Rayyanat keta zubda qwalla a boye har suka isa.
A bakin shiga garin tace da Nasir ya tsaya a nn, ya juya ya kalleta yace "garin naku ba'a shiga da mota ne?" Rayyanat ta daure tace "Ana shiga da ita amma ku sauke ni kawai nagode, zan iya qarasawa da kaina," inna ta yo waje da ido tace "yo Rayyanah ai ni en uwan naki nake son gani ko zan samu sumin alfarmar bar min ke"
Shiru Rayyanat tayi hawaye suka shiga silalowa a hnkli kan kumatunta ta, inna ta saki baki tana kallonta, can tace "Rayyanah ko ba kya son komawa gu nane?" da sauri ta girgixa kanta muryarta na rawa tace "inna ni bani da kowa duk sun rasu"
Inna ta rafka salati da karfi ta fashe da kuka tana cewa "wayyo ni Hajara, wayyo ni" Nasir dae yyi shiru yana kallon Rayyanat amma ya kasa yrda da abinda tace, inna ta ci kukanta ta koshi Rayyanat na taya ta kmr a lkcn aka yi mutuwar, daga karshe tana fyace majina cikin kuka tace "Allah ya rahama masu, wayyo ni rayuwa" Da kyar Nasir ya iya bude baki yace "Allah ya ji Kansu" ba don ya yrda ba gani yake kmr karya tayi masu.
Cikin muryar kuka Inna yace "to nasiru muje muga mai garin nasu dmn haqqi ne akansa yasan Rayyanat zata zauna gun mu ko?" Nasir ya gyada mata kai kawae ya tada motar ya shiga tafiya a hnkli Rayyanah na nuna mai hanya har suka isa qofar mai gari.
Cikin girmawa aka tarbe su mai garin yyi mamakin ganin Rayyanah ya shiga tambayarta daga ina take, nn Nasir ya dan ji dama dama gnin mai garin ya santa, bayan an gama gaggaisawa Nasir ya zayyano abinda ke tafe dasu yana kallon Rayyanah, mai gari bai musa musu ba ya amince da

Please Login or Register in order to submit comment