Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abinda take iya yi.
Umman saliha ta nisa snn tace da nasir"ni ina mamakin wane irin abune Rynt tayiwa mohd da har ya iya mata wnn dukan"
Nasir yace"ni nasan ba abinda Rynt ta masa da yakai ga duka kawae dae rashin imanin sa ne ya motsa,kuma umma dama fa Rynt zaman haquri kawae takeyi a gidan shiyasa nake son inna tasani ko hkn zai sa man ya daina quntata mata sbd idan inna taji tamkar Abbansa yaji ne , Abba kuwa kai tsaye zai gyara masa zamansa ne don bazai ta6a barin sa ya ci gaba da cutar da Rynt ba.
Umma tace"lallai kam ba makawa zai gyara masa xamansa"

Daga haka basu sake cewa komai ba sae Nasir da ya ciro wyrsa a aljihu ya kira abokinsa yana gama waya dashi se juya alkalar motar sa yayi zuwa canza hanya ummar shi ta tambaye shi lafiya
yace"Fa'iz ne yace mu had'u can gidan inna sbd ya rigada ya baro asibiti.
Tace" haka yafi sauqi amma hlnda inna zata ga Rynt nake tunani"
Nasir bae ce komai ba don shima nazarin da yake yi kenan don yaso ace koda zata ga Rynt an ciyo kan matsalar sae dae kawae taji lbrn abinda ya faru.

Suna isa shima abokin nashi na isowa.

Dukkan su suka shiga gidan har shi fa'iz d'in wanda ga dukkan alama ya saba shiga gidan dan shine gaba sai sauri yake ya bud'ewa nasir qyallen qofa.
Nasir dake d'auke da Rynt ya ajiye ta kan 3 seater abokin nasa ya shiga dubata sbd sunyi sallama har sun gaji ba amsa.

Bayan abokin yayi en gwaje gwajen sa akan Rynt ya nemi akaita kan bed sbd yana son zai mata qarin ruwa .
D'akin inna aka kaita snn aka d'aura mata ruwan sae a snn ne inna ta shigo gidan wacce ga dukkan alama maqota ta fito dan riqe take da qullin nono da fura a hannu,ai kuwa tana shiga d'akinta ta saki furar da nono tana taslima inda a rud'e ta shiga tambayar abinda ke faruwa da Rynt.
Sae da nasir ya kwantar mata da hnkli snn ya snr da ita abinda ya faru.

Kukan su na tsafi ta shiga yi tana sirfawa mohd zagi ciki da waje snn ta d'auko waya a cewar zata kira Abban mohd yazo yaga d'ayen aikin da yayi wa Rynt.....bata kae ga kiran sa ba taji abokin nasir na cewa da nasir
"Haqiqa anyi babbar nasara dan duk irin dukan nn da tasha juna biyun da ke jikinta yana nn lfyrsa qalau"
Da kmr mamaki Nasir yace"juna biyu ne da ita? Yace"tabbas kuwa tana d'auke da juna biyu don hk sae a kiyaye a riqa bata kulawar da ta dace"
"InshaAllah"
Shine abinda nasir yace kafin abokin sa ke rubuta masa magunguna ya bashi.
Nn Nasir ya maida dubansa gun ummar sa da inna wad'anda kallo d'aya zakayi musu kasan sunyi farin ciki matuqa da jin zancen Dr musamman inna da kukanta ya koma dariya.
Yace musu"zanje siyo magani na dawo"
Inna tace"to d'an albarka sae ka dawo ,kai kuma Hafizu Allah sa ka gama da iyayenka lafiya don wnn lbr da na ji a bakinka ya kore min duk wani baqin ciki.
Da shi har nasir sae da sukayi murmushi suka fita sbd fa'iz yasha fhmtar da ita sunan shi amma sae tayi ta kiran shi da hafizu tun yana gyara mata har ya daina sae dae kawai yayi murmushi idan ta kirashi da Hafizu.
Suna fita inna taje kusa da Rynt dake ta sharar bacci tace "um! um! baiwar Allah, Allah iskar miki ga shashan yaron nn muhammadu ai zai zo ya sameni ne zai kuma had'u da ubansa kabiru dan sae na snr dashi komai kaf ba abinda zan rage shashan yaro kawai marar tausayi da baisan daraja mace ba.
Nn ta d'auki fura da nonon da tayar a kan fridge wad'anda umman saliha ce ta d'auke ta d'aura akai.
Ta d'auki furar tana mae fad'in"bari naje na dama ma er albarkar nn Rynh ita kafin ta tashi tayi sanyi sae tasha"
Tana gama fad'ar hk ta kama hnyr fita d'akin umman saliha ta tashi da sauri tana qoqarin cewa da inna ta kawo furar ta dama sae ga man ya shigo d'akin shaye da toka riqe da mami a hannun shi wacce taje da gudu kan jikin mamarta.
Mohd kuwa yana had'a idô da inna ya wani qara d'aure fuska dan karma inna taga damar shi .
Amma hkn bai hana inna ta shiga sirfa mae masifa tana"fad'in shashan yaro me kuma ya kawoka ko kazo ka qarasata ne iye!
Komai mohd bai ce da ita ba sae zuwa yayi kan gadon da Rynt ke kwance ya ajiye wata farar takarda ya fita .

Billy giro😊
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
[2/8/2017]
Billy giro😊:
```🔮BAZAN BARSHI BA!🔮```

🔮🔮🔮🔮
*page* *```47```*
Inna tace yau naga shahan yaro me kuma ka ajiye mata kan gadon da har ina ma magana zaka wani wuce ni.
Nn umman saliha ta tashi taje ta d'auki takardar ta karanta wacce tana gama krntawà ta saki takardar ta zauna sakwaf kan gado tana taslima had'e da fad'in innalillahi wa inna ilaihi raji'un!
A rud'e inna ta d'auki takardar tace"lafiya me ya rubuta mata a takardar ne?
Umman saliha tace"saki ne inna!
Da qarfi inna ta dafe qirjinta tare da fiddo ido waje tace"saki!
Sae kawai ta fashe da kuka tana"fad'in innalillahi wa inna ilahi raji'una anya kuwa muhammadu yana son ya gama lfy, me wnn er albarkar ta masa da zai had'a mata zafi biyu a lokaci d'aya nn ta koma fashewa da wani kuka inda cikin kukan ne ta kira Abban mohd ta snr dashi komai.

Kafin yazo sae ga nasir ya dawo da siyen magani ya qaraso jiki sanyaye ganin yanda inna keta fmn shar6ar kuka har da su fyace majina, a hnkli ya ajiye ledar maganin hannunsa kan bed yaje ga inna yana tmbyr me kuma ya faru?
Takardar hannunta ta miqa mae tace"gane ma idonka abinda d'an banzan yaron nn ya rubutawa Rynh ,yana kar6ar takardar ya hango saki 6aro 6aro nn ya cire hular kanshi tare da kallon Rynt dake kwance still tana bacci yace"ya saketa!
Daga nn shima ya zauna gefen gadon dafe da kai yana tunanin me Rynh ta ma mohd ne wae.
Yana cikin hkne yaji sallamar Abban mohd.

A hnkli ya d'go tare da zamewa kan gadon ya durqusa yana gaida shi ya amsa ba yabo ba fallasa yayinda ita ma umman saliha ta gaida shi ya amsa snn suka fito d'akin suka barshi shida inna.

Cikin damuwa Abban mohd yaje gun Rynt yana mae kallon yanayinda take ciki can ya nisa yace da inna"shi mohd d'in bai ce ga abinda ya had'a su bane?
Inna tace"meko yace sae shigowa kawai da yayi yaje ya ajiye mata takarda ya fita wanda har ma magana nake masa amma yaqi ko kulani.
Abba ya jinjina kansa snn yakai hannu ya ciro wyrsa a aljihu ya kira mohd
Yana d'agawa yace"duk abinda kake ka ajiye shi kazo ka sameni a gidan inna.
Daga hk Abba ya katse wyr.
Mohd dake zaune a asibiti gurin malika wacce tasa shi gaba tana ta kuka wae ita kukan baqin cikin zubewar cikinta take yayinda shi kuma duk ya wani sukui kuice yana fmn lallashinta.
Shine ya samu da qyar ya lalla6ata tabar shi ya fita.
Fa'iza wacce daman tana cikin d'akin.
Tana ganin mohd ya fita taje ta ba malika hannu suka lale ,malika tace"Abbansa ne ya kira shi nsn kan sakin nn ne da yayiwa wnn abar "
Faiza tace"hln bai ji dalilin sakin bane?
Ta6e baki malika tayi snn tace"oho masa nidai tunda buqata ta riga ta biya komai yayi"
Faiza tace"wae dae tukuna saki nawa ne ya rubuta mata"
Malika tace"har kya tambaya ai kinsan uku ne ba tantama,shiyasa kika ji nace buqata ta ta gama biya don ba zancen ace ya maida ta kuma sun rabu knn har abada yayinda ni kuma zan zame masa mutu ka raba takalmin kaza.
Nan suka koma lalewa suna kyakkewa.

6angaren mohd kuwa da isar shi gidan inna kai tsaye ya tafi sae d'akinta ya samu guri a qasa ya zauna yayinda inna ke zaune kan bed Abbansa kuwa yana kan sofa.
Abba ya kalle sa da kyau snn yace"Ashe baka da hnkli ban sani ba mene ne ya had'aka da Rynt da har ka iya dukanta ka kuma had'a ta da takardar saki?
Shiru mohd yayi .
A fusace Abba yace"shin bada kai nake magana bane!
Kallon mahaifin nasa yayi ya koma duqar da kanshi qasa snn yace"Abba da ka bari idan ta farka sae kaji a bakinta"
Abba yace"don uwarka ni sa'an ka ne da zan tambaye ka kace min na bari har Rynt ta farka ,kai dai zaka gaya min d'an iskan yaro kawai shashasha wanda baisan darajar mace ba,wae karasa inda zakayi zalunci sae akan mace.
Ran mohd ne ya soma 6aci da jin irin zagin da Abba ke mae ya daure yace"Abba ka daina ganin laifina akan abinda baka ji ba, yrnyr nn fa kwata kwata bata da gsky haka kuma hkncin da na d'auka akanta shine dai dai "
Abba yace" wane laifi ne Rynt zata maka da zata ci wnn banzan hukuncin naka na masara imani da rashin tausayi"

Mohd Yace"Abba cikina ta 6arar min dake jikin malika ta hnyar sanya mata magani a abinci"
Cikin d'aga murya Abba yace" sam! wnn qarya ne kwata kwata Rynt bazata aikata hk ba idan har zarginta kake to kayi gaggawa cirewa"
Abba ba zarginta nakeyi ba ta aikata ne don a gaban idona komai ya faru.....Qarya kake munafukin Allah Rynt bazata ta6a aikata hk ba kawae dama can ba son auren nata kake ba shine ka 6ullo da wnn hnyr na ganin ka yakice aurenta dake smn kanka to kasani wlh daga yau kar na koma ganin qafar ka a gidana tunda ni ban isa da kaiba koma nace baka d'auke ni a uba ba,don hk sae ka nemi wani uban bani ba!
Cikin fad'a ita kuma inna ta kama da cewa"marar kunyan yaro da baka santa meyasa to ka mata ciki!
Da sauri mohd ya d'ago ya kalli inna yace"ciki"
Inna tace"eh ko kuma cewa zakayi bakai kayi cikin bane iye!
Sadda kansa kawae yayi qasa ba tare da yace komai ba.
Abban sa ya daka mae tsawa yace"ka bata amsa mana bada kai take magana bane!
Yace"nawane"
Shi ne kad'ai abinda yace
Yayinda Abba yace"oya maza tashi ka bamu guri shasha!
kuma wlh kasani har nn gidan d'in ma ban yarda ka sake tako qafar ka ba kaji na gaya ma!
Daga hk Abba ya fita fuu yana mae gyara babbar rgr shi wanda yana kai falo yace da nasir"ina son gobe da safe kaje gidan nashi ka kwaso kaf kyn Rynt kazo dasu nn gidan"
Da ladabi nasir yace"to"
Snn Abba ya fita haka shima man ya fita yabar gidan cike da tunanin cikin da ke jikin Rynt.

9:00pm
Rynt ce ta shiga motsi a hnkli inna dake gefenta tayi hanzarin matsawa kusa da ita tace"Rynh kin tashi?
Komai Rynt bata ce ba sae yunqurin tashi zaune take nn inna ta taimaka mata ta tashi zaune.
Snn inna taje da hnzri ta bud'e fridge ta d'auko damammar fura a cikin kwanan shan ruwa wacce umman saliha ce ta dama ta kafin ta tafi.
Ta di'bar wa Rynt a kofi taje ta kai mata ,Rynt takai hannu ta kar6i kofin furar tana mae kallon inna'
Inna tace"Sha kinji Rynh"
ba musu takai kofin fura a bakinta tasha kad'an tace"inna bana son furar idan da kunu zan sha amma nafi son mai d'an tsami da sanyi"
Inna tace"Rynh za'a sami kunu mai sanyi amma baya da tsami sbd d'azu da rana Baaba hurare ta daman min shi sae dai idan kina so na sa maki ruwan tsamiyà a ciki"
Tace"Eh inna ina so"
Nn inna ta kar6i kofin furar ta saka shi a fridge snn ta fita zuwa kitchen ba jimawa sae gata ta dawo d'auke da kofin kunu ta ba Rynt wacce ta kar6a ta shiga sha"
Inna kuwa ta d'auko magunguna tana 6alla mata kmr yanda nasir ya gaya mata kafin ya tafi.
Tana gama 6allewa ta ba Rynt ta kar6a tasha snn ta tashi ta nufi bathroom tayo arwala tazo tayi sllr dake kanta .

Washe gari Nasir ne ya shigo gidan shida abokin sa fa'iz .
Da shigar su suka had'u da inna ta fito kitchen d'auke da ruwan zafi a cup zata had'awa Rynt shayi,sun gaidata had'e da tmbyrta mai jiki.
Tace "Alhmdlh mu shiga tana daga ciki"
Nn suka shiga suka sami Rynt kan gado ta had'e kai da guiwa.
Sallamar su yasa ta d'ago ta d'an saki fuska ta musu ina kwana suka amsa tare da fad'in ya jikin naki?
Tace"Alhmdlh"
Faiz yace"da akwai abinda ke maki ciwo ko kuwa"
Tace"Aa ba inda ke min ciwo kawai...sae tayi shiru.
Yace"zafin duka ko?
Kai ta gyad'a mishi tare da qoqarin mayarda hawayen da ke son zubo mata"
Fa'iz yace"kici gaba da shan magunguna kafin gobe inshaAllah zaki ji jikin ki dai dai kinji"
Tace"to"
Snn nasir yace"jiya kinsha magunguna?
Tace"eh inna taban"
Yace"to yau fa"
Tace"tukuna ban sha ba"
Inna dake zuba madara a ruwan tea tace"ai yanzu nake shirin d'auko mata magungunan idan ta gama shan shayi sae tasha"
Nasir yace"To inna mu zamu d'an fita mu dawo"
Tace"to d'an Albarka sae kun dawo"
Nan suka fita inna ta bawa Rynt shayin da ta gama had'a mata snn ta d'auko mata magunguna had'e da kofin kunu ta ajiye mata,taje ta bud'e fridge ta d'ibi fura ta zauna zata sha knn sae taji sallamar Abban nasir.
Washe da baki ta fita ta same shi a falo yayinda shi kuma yana ganin ta ya durqusa har qasa yana gaida mahaifiyar tashi.
Bayan sun gama gaisawa ya koma kan cushion ya zauna itama inna ta nemi guri ta zauna.
Yace"inna ya jikin Rynt?
Tace"taji sauqi don yanzu haka ma karyawa take,ko na kira ma ita ku gaisa ne?
Eh inna don akwai mgnr da ma nake son nayi da ita.
Nn inna ta qwalawa Rynt kira wacce sae da ta amsa kiran snn taxo falon ta durqusa cike da ladabi ta gaida Abban nasir.
Byn ya amsa yake cewa"Rynh ina so zan tambaye ki ne,shin meye ainihin abinda ya had'a ki da mohd?
A sanyaye tace"Abba ni ban san na masa komai ba kawai ina cikin bacci naji yana dukana amma banda shi ba abinda na sani"
Abban nasir ya nisa yace"amma kuma mohd yace abu kika sawa mtrsa a abinci taci cikinta ya zube"
Da sauri Rynt ta kalli Abban nasir cikin muryar kuka tace"wlh Abba ba haka bane ni ba abinda nasa mata a abinci"
Shiru Abban nasir yayi can yace"shikenan tashi tafiyarki"
Rynt ta tashi tana mae share qwalla ta koma daga ciki.
Bayan ta shiga ciki ne taji Abban nasir na cewa da inna"ni na rasa gane kan wnn al'amarin shi mohd da na kirashi na tambayesa har rantsuwa yamin kan cewa a gabon idonsa malika taci abincin da Rynt ta dafa ta kawo mata wacce ko spoon uku bata samu tayi ba cikin ta ya shiga 6ird'a daga hk ne ta soma zuvar da jini ya kwashe ta zuwa asibiti wanda koda suka isa cikin ya riga da ya zube bai iya ceto rayuwar abinda ke cikin ba"
Inna tace"yo kae ka yarda da zancen nasa knn ni nsn ba wani ciki da mtrsa keda makirci ne kawae suka qulla shida mtr tashi na ganin sun fitar da Rynh a gidan.
Abban nasir yace"kodai mtr tasa ce ta qulla makircin don bana tunanin mohd zai biye wa shirmen mata har a had'a irin wnn makirci dashi......yo tunda ba son auren yake ba ai zai biye mata ne.
Yace"to inna abar wnn zancen ni yanzu abinda nake so shine a sasanta tsakanin su, Rynt ta koma d'akin mijinta tunda saki d'aya ne ya mata.....yo so kake ta koma ya idata knn in yaso na rasa abinda zan cewa mai garinsu da ya damqa min amanar ta, to ba'ayi hk dani ba, fatana Allah ya sauke ta lafiya ya bata wani mijin mae sonta tsakani da Allah wanda kuma zai riqe ta da gsky,ba irin shashashan yaron nn da ba abinda ya iya sae cutar da ita ba.

Abban nasir yace"inna ki daina wnn zancen dmn ba abinda yafi dacewa irin a maida Rynt d'akin mijinta ko don qaruwar da suka samu a tsakanin su.
inna tace"kaga Bello idan wnn zancen kad'ai ya kawo ka gidan nn gwara ka tashi ka tafi don Rynh kam bazata koma gidan wnn marar imanin yaron ba,idan kuwa ka koma zowa ka matsa min da zancen wlh zan d'auki Rynh ne mu koma can qauyen nasu da zama kuma ba wanda yà isa ya sani na dawo.
Haquri kawae Abban nasir ya bata ya fita ya bar gidan cike da damuwa.

Inna kuwa rae 6ace ta koma d'aki ta sami Rynt sae kuka take kmr ranta zai fita wacce ba komai take yiwa kukan ba sae jin cewa tana d'auke da ciki.
Inna kuwa ba abinda ya fad'o ranta sae tunanin ko qazafin da mohd ya mata ne take yiwa kuka.
Nan taje gun Rynt sae dae kafin tace komai Rynt ta kalleta cikin kuka sosai tace"dan Allah inna kisa a cire min cikin nn wlh nayi qanqanta,dmn nasan mutuwa kawae zanyi gurin haifuwa"
Inna tayi er dariya tace "Rynt bazaki mutu ba zaki haifu lafiya kinji"
Tace"amma inna karatu na fa?
Tace"zaki ci gaba da karatun ki a nn kinji"
Inna to ta yaya zanyi karatu da ciki wlh kinsan da kmr wuya dan Allah kisa a cire min inna "
Inna tayi shiru tana kallon Rynh sae can tace"bazan 6oye miki ba Rynh kinzo dani gaa6ar da bazan iya ba don har gwara ma kice min kina son komawa gidan muhammadu da kice min a cire wnn cikin.
Daga hk inna ta tashi tabar d'akin.
Rynt kuwa ta qara fashewa da wani sabon kuka dan ganin take shike nn man ya 6ata mata tsarin rayuwar ta,ya kuma lalata mata duk wani lissafin karatun ta.
Lallai idan ba'a cire mata cikin nn ba,ba abinda yafi cancanta a gareta yanzu shine ta d'auki fansar ta kawae ta qara gaba.

Duk a cikin kukanta ne take wnn tunanin .
Yayinda inna ta dawo d'akin tana ta bata baki amma Rynt bata iya daina kukan ba don ma yini zungur ta kwashe tana abu d'aya.
Ai kuwa duk inna tabi ta damu sosai sbd ko abinci Rynt taqi ci wacce ko karin kumallon da ta fara da safe bata qarasa ba.

Cikin hkne nasir ya fad'o gidan inna ta tarbe shi da cewa"yauwa Nasiru dama kai nake shirin kira yanzu.
Yarinyar nn Rayyanah tun d'azu sae kuka take tayi ita sae an cire cikin da ke jikinta, ko abinci taqi taci tun safe har yanzu.

Nan nasir ya tambayi inna ko meye dalili ,
Inna ta gaya mae duk yanda sukayi da Rynt.
Yayi shiru snn yace "bari naje gurin ita Rynt d'in"
Bai jira me inna zata ce ba ya shiga inner room ya sami Rynt zaune kan sallaya ta had'e kai da guiwa tana ta kuka.
A hnkli nasir yaje ya durqusa kusa da ita tare da kiran sunanta

Nn ta d'ago a hnkli tana kallon shi da jajayen idanuwanta da duk suka kumbura yace"kukan ya isa haka indae ciki ne zan sa a cire maki kinji"
Cikin dasasshiyar muryar ta da tasha kuka tace"nagode"
Yace"to share hawayenki"
Ba musu takai hannu ta share hawayenta Yace"kici abinci kuma kisha magani idan na dawo gobe sae naje dake a cire cikin ko"
Nan ta gyad'a mae kai shi kuma ya tashi ya fita,
yaje ya sami inna yace "inna shikenan ta daina kukan yanzu kije ki bata abinci taci"
Inna ta washe baki tace"yo kai Nasiru me kace da ita ne da har tayi shiru kai tsaye?
Murmushi yayi yace"inna ina sauri yanzu amma gobe idan na dawo mayi magana"
Tace"to d'an albarka Allah kaimu goben"
Nn ya fita inna kuma ta shiga d'aki washe da baki".

```🔮BAZAN BARSHI BA!🔮```

🔮🔮🔮🔮
*page* *```48```* and. 49

Ta sami Rynt ta tashi tana linke carpet d'in sallah.
Inna ta kar6i carpet d'in ta koma shimfid'a mata a nn kusa da gefen gado tace da ita "zauna bari naje na kawo maki abinci kici ko"
Rynt ta gyad'a mata kai snn ta zauna,
inna ta kai hannu nn kusa da bedside drawer ta d'auki abincin rnr da Rynt bata ci ba taje dashi kitchen ta kawo mata tuyon shinkafa da miyar ganye wacce taji qassan nmn rago .
Ta kai kusa da Rynt ta ajiye snn ta kawo mata ruwa da kunu da magunguna a cewar idan ta gama cin abinci sae tasha.
Sae da Rynt ta yiwa inna godiya snn ta kai hannu had'e da bisimillah ta fara cin abinci.
Da ta kammala ne takai kwanika a kitchen ta dawo ta fad'a bathroom tayi wanka koda ta fito ta sami inna na waya cike da murna tana gama wyr ne take ce ma Rynt"Ashe saurin da na Nasiru keyi fatima ce a asibiti shine yanzu aka kirani aka snr dani ta sauka lfy ta sami d'a"
Rynt ta d'an saki fuska snn tace"to Allah ya raya masa shi akan sunna"
Inna ta washe haqora tace"Amin amin ai ba dan dare ba da naje naga sabon mae gidana"
Murmushi kawae Rynt tayi taje ta nemo kyn bacci ta saka ta kwanta.

Washe gari Rynt taji sauqi sosai don ita ma ta gyare gidan tsaf ta kuma je kitchen tana ragewa Baaba hurera aiki wacce tana zowa bata fara aiki ba suka tafi gidan su mohd gun barkar pretty ita da inna.

Tana cikin aikin ne suka dawo Baaba hurera ta shigo tana mata sannu da aiki snn tace taje inna na kiranta a falo.
Koda taje falon ta sami inna da Abban mohd taje ta durqusa cike da ladabi tana gaida shi ya amsa mata cikin sakin fuska snn yace"ya jikin naki?
Tace"Alhmdlh"snn yace"dama zançen karatun ki ne tunda kinji sauqi gobe
zan turo driver wanda zai riqa kai ki makaranta yana maida ki,snn kmr yanda ake maki lesson a can gidan nn ma zan nemo maki wanda zai riqa zowa yana maki lesson d'in,snn kuma duk wani abu da kk buqata ki snr da inna sae ta snr dani"
Tace"to Abba nagode"
Yace"shikenan tashi ki tafi"
Bayan ta wuce ne ya ciro kud'i a aljihun sa bandir d'in 1k guda biyu yaba inna yace"d'aya naki ne d'aya kuma ki riqa bawa Rynt d'ari biyar biyar duk safiya ta na samun na cin abinci idan taje mkrnta dn naga mkrntar tasu yini ake"
Ina ta kar6i kud'in had'e da sa mishi albarka yace"nagode inna ni zan tafi"
Tace"to d'an albarka Allah kai ka lfy"
Yace"amin"
snn ya fita.
Ita kuma taje d'aki ta adana kud'in.

*****
Kwance yake kan bed sanye da farar singlet da farin boxer malika ta shigo d'akin ta kalli yanda ya d'ora qafa kan qafa yana mai kallon silin.
Taje ta zauna kusa dashi tana mai kallon fuskar shi snn tace"my man ya kamata ka haqura ka daina tunani akan rashin da mukayi,ai Allah zai sake bamu wani ne komai baqin cikin wnn abar kuwa.
Lumshe idonsa kawae yayi ba tare da yace komai ba tace"ya

Please Login or Register in order to submit comment