Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zancen zuwa gidan naku ?
Yace"ki tafi kawai"
Tace"baza kaje ganin jariri ba knn ?
Kallonta kawae yayi bai ce mata komai ba sae kwanciyar sa da ya gyra.
Tasan ba amsar zata samu ba shiyasa kawae ta tashi tabar d'akin taje ta shirya ta fita.

Gidan su man d'in ta nufa wacce da shigar ta 6angaren su man kai tsaye ta haura sama zuwa d'akin mhfyr man ta bud'e qofar d'akin ta shiga ba ko sallama,pretty dake zaune kan bed tana shayarwa ta saki murmushi tace"sae yanzun"
Sae da malika ta zauna snn tace"hm nida nake ganin ma nayi sammako"
Pretty ta bata jariri tare da fad'in"yaya fa?
Tace"wlh yana can cikin damuwar rashin babyn mu har magana ma bai cika son yi ba"
Pretty ta cije le6e tace"wlh Allah matsiyar yarnr nn taci uban rainin wayo! ni kuna me wae ma har tayi nasarar 6arar miki da ciki?
Malika ta ta6e baki had'e da murmushi snn ta duba koina idan ba mai ganin su ta kai bakinta a kunnen pretty ta rad'a mata magana ,pretty ta fiddo ido had'e da washe baki snn tace"kai haba!
malika tace"Allah kuwa
snn tace"amma fa bakin ki qanin idonki wlh kar ki bari kowa yaji zancen nn don ina gudun ya koma kunnen yayanki"
Tace"haba dan Allah sae kace ban san me nakeyi ba ai ko umma bazata ji wnn zancen ba,,kuma kin san Allah da har kin ban haushi da naga na koma kai miki magani amma naji shiru ashe kinsan abinda kk shirin yiwa matsiyaciyar.
Malika tace"ai ke ajiye maganin gefe nayi nace sae na gwada plan d'ina tukun.
Pretty tace"shiyasa da muka je dubaki lkcn da umma keta masifa tana fad'in duk laifinki ne dan da kinsa mata maganin a abinci taci ta haukace da duk hkn bata faru ba sae naga kin kalle ta kawae kinyi shiru .
Malika tayi dariya tace"wae ina umma take ne ma?
Pretty tace"Wlh tana kitchen da fitar ta mane ba jimawa se kika shigo.

8:30pm
Inna ce zaune a falo ita da Rynt suna cin abinci bayan sun gama Rynt tace"inna nifa gobe bana da kayan sawa idan zanje makaranta duk suna gidan can"
Inna tace"ayyo ai tuni an kwaso maki kayanki suna a d'akin ki nasa nasiru yakai ,
ai a cikin kayan ne ma na d'ebo wasu en kyn sawa nakai miki a d'akina"
Tace"inna kayan mami fa?
Tace"yo ai kaji fa amma bari na kira nasiru naji da yaje kwaso maki kaya har da kayan mami ya kwaso ya had'o ko kuwa"
Nan ta d'auki wayarta ta kira nasir bayan sun gama wyr ne tace ma Rynt yace duka har kyn mami d'in ya had'o ya kwaso wanda tun d'azun yaso yazo ya d'auki kayn nata yakai gida sae bae sami lokaci ba amma yace yanzu zai zo ya d'auki kayan"
Rynt tace"to bari naje na had'a masa kayan kafin ya iso"
Inna tace"to"
Snn Rynt ta tashi ta nufi d'akinta da take zama a daa.
Kan gado ta sami kayan nasu komai har akwatinan lefenta wad'anda kallo d'aya ta musu ta kauda idonta ta d'auki akwatin mami ta bud'e taga komai nata na ciki ta rufe akwatin ta ajiye ta gefe kusa da qofar d'akin snn taje ta bud'e akwatin ta wacce inna ta saya mata ta samu itama komai nata na ciki zata rufe kenan akwatin ta sa6ule ta fad'i sae duk kayan suka fita nn ta hango tsofuwar ajiyar ta ,ta kai hannu a hnkli ta d'auki viva ledar ta bud'e .
Kayan da marigayi anwar ya bata ne a ciki nn ta shiga ciro kayan d'ai d'ai tana kallo.
Hawayenda suka cika mata ido ne suka shiga gangarowa a hankali yayinda ta ciro bandir d'in 1k guda biyu masu d'auke da jini a jikin su nn taji inna ta qwala mata kira tayi saurin mayarda kud'in har kynda anwar ya bata snn ta amsa kiran da inna ke mata had'e da share hawaye ta kama hanya zata fita sae ga nasir ya shigo d'akin yace"har kin gama had'a kayan?
tace"na samu kayan a had'e suke"
Yace "eh hkne ni na had'a kyn tun can sbd a wardrobe d'inta na sami akwatin ta shine na saka mata duk kayan da ke cikin wardrobe d'in haka kema"
Tace"mungode"
Snn yace"zancen da mukayi jiya dake ban manta ba ina son sae na sami lokaci ne sae nazo muje a cire cikin ko?
Tace"to"
Yace"yauwa sae ki maida hnkli ki ci gaba da zuwa mkrnta kinji"
Nn ta gyad'a mishi kae shi kuma yaja akwatin mami ya fita.
Ita kuma taje ta gyra kayan akwatinta da suka zube ta rufe sae dae kafin ta rufe akwatin sae da ta cire kynta na zuwa school ta d'auke su ta tafi dasu d'akin inna.

12:00 na dare
Man ne ya fito d'akin shi wanda bai zarce koina ba sae d'akin Rynt .
A nn bakin qofa yayi tsaye yana qarewa d'akin kallo sae can ya qarasa shiga d'akin yaje gun wardrobes ya bud'e yaga ba komai kaf an kwashe ya maida wardrobes d'in ya rufe .
Har zai fita sae ya hango farar suit jacket d'inshi kan sofa yaje ya d'auki jacket d'in a hnkli yana kallo,
Se kuma yayi saurin kauda idonsa kan jacket d'in ya kuma jefar da ita kan sofa ya fita.

Washe gari da safe Rynt ce ta kammala shirinta tsaf na school inna ta ciro d'ari biyar ta bata Rynt ta kar6i kud'in tace"ba canji ne inna?
Inna tace"canjin me kud'in ki ne fa da zaki tafi dasu makaranta na cin abinci ko basa isar ki?
Rynt ta bud'e ido tace"inna ai kud'in sunyi yawa ai d'ari biyu ma sun isa kuma ina ma da kud'i a hannu na da kin barshi kawae inna"
Inna tace"yo Rynh kud'in hannunki ai naki ne,wad'an nn kuma na cin abincin mkrntr ki ne kabiru ya bayar a riqa baki"
Tace"to inna nagode amma dae zan dawo da sauran canji dan sun min yawa"
Inna tace"to er albarka a dawo lafiya Allah tsare min ke ya kuma bada sa'ar karatu"
Tace"amin inna"snn ta fita ta samu driver na jiranta a qofar gida taje ta shiga motar yaja suka tafi.

Billy giro😊
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
```🔮BAZAN BARSHI BA!🔮```

🔮🔮🔮🔮
*page* *```49```*
Ana sauke Rynt a school sae kawai taji ihun mami tazo aguje ta rungumeta.
cike da murmushi Rynt ke kallonta tace"mami kece waya ya kawo ki?
Washe da baki tace"Abbana ne yanzu ya wuce"
Sae kuma tasha toka tare da fad'in"Anti wae meyasa kika koma gidan inna da zama?
Rynt tayi shiru tana kallonta can tace"to ai dama can gidan inna nake zama ko kin manta"
Tace"Aa ni nafi son ki koma gidan yaya sbd na fi son a riqa kawo mu school tare"
Rynt tace"ai ko ba'a kawo mu tare ba, ba gashi muna had'uwa ba"
Turo baki tayi tace"um um anti hk ba dad'i"
Rynt tace"kinga jeki 6angaren ku za'a fara assembly kar kiyi letti kinji"
Mami tace"to Anti gsky ni sae kin gaya min yaushe zamu koma gidan yaya"
Rynt tace"to kisa ido duk rnr da kika ga raqumi ya shiga akurki kizo da gudu ki gaya min sae mu koma ko"
Da murna mami tace"dgske anti!
Rynt tace"eh"
Mami tace"meye ma raqumi wnn abun mae girma kmr doki ko"
Rynt tace"eh"
Mami ta daka tsalle tace"Allah kuwa da jimawa na ta6a ganin shi hnyar kasuwa,gobe ma zan cewa umma muje kasuwa da na ganshi zanyi ta kallon shi har sae naga ya shiga akurki sae nazo har gidan inna na gaya miki,sae mu koma abin mu gobe gidan yaya ko.
Rynt tayi murmushi had'e da girgiza kanta ta tafi tana fad'in"to naji zan neme ki a break"
Tace"ok anti bye"

5:00pm
Rynt ce ta dawo daga mkrnta ta sami inna a falo duk ta raja'a gun kallo har sallama tayi kusan sau biyu amma bata ji ba, tayi tsaye d'auke da murmushi tana kallon inna snn taje a hnkli kan jikin inna ta rungumeta,
a tsorace inna ta juyo ganin Rynt ce ta sauke numfashi tace"yo Rynh kece aini har kinsa na tashi guduwa ,
Rynt tace"haba dae inna da tsufanki kk shirin guduwa?inna tace"yo ai shi tsoro ba ruwan shi da tsufa "
Dariya Rynt tayi tace"hln ma meya tsorota ki ne inna?
Tace"yo Rynh ina zaune qalau kawae naji an hau kan jikina bayan nsn ni kad'ai ce a falon ban kuma ji shigowarki ba
Tace"to inna ai nayi sallama har sau biyu kece dae bakiji ba sae kallo kike tayi abinki"
Inna tace"ayyo inafa zanji na maida hnkli gun shiriritar banzar nn da ba zata fisshe ni ba"
Murmushi kawae Rynt tayi ta tashi tare da fad'in "inna ni zanje na d'an watsa ruwa"
Tace"to er Albarka sae kin fito"
Nan Rynt ta wuce inna kuwa taci gaba da kallo.

Tana gama wanka ta shirya ta ciro wata baqar leda a cikin jakarta ta mkrnta ta fito ta tafi kitchen sae gata ta dawo d'auke da agwalima cikin bowl.
Taje ta zauna qasa kusa da kujerar da inna ke zaune akai ta d'auki d'aya zata fara sha tare da fad'in" inna ga agwalima"
Inna tace"yo Rnynh ni na d'auka ko abinci ne kika d'ebo"
Tace"Uhm agwalima ce na wanko na d'an sha ko d'aya ce sae naci abinci "
Inna tace"lallai kam ki hanzarta kici abinci kafin mai miki dasarin yazo"
Tace"inna ni idan ma da fura ita kawae zansha ba sae naci abinci ba dan bana jin yunwa"
Tace"to tashi kije ki d'ebo furar tana can a cikin firijin tayi sanyi kuwa.
Ba musu Rynt ta tashi ta d'ebo furar tazo tayi zaune ta shanye agwalimar hannunta snn tasha fura tana gamawa taje ta had'o komai nata na lesson ta fito ta samu inna na kar6a sallama inna na ganinta tace yauwa je d'auko tabarma don inaga mae miki dasarin ne yazo,nn Rynt ta koma d'aki ta d'auko tabarma ta fita.

6angaren mohd kuwa kwance yake a falo shi kad'ai kan 3 seater ya lumshe ido kmr mae bacci.
Da damuwa ya bud'e idonsa had'e da guntun tsaki sbd door bell d'inda yaji ana fmn dannawa kan dole ya tashi yaje ya bud'e qofa, ganin wanda ke tsaye yasa ya d'an saki fuskar shi ya bashi hannu suka gaisa har yana masa ya hanya.
Wanda ba kowa bane face lesson teacher d'in su Rynt wanda tun lokacinda yayi tafiya sae yau ne ya dawo.
Man bai iya bashi hanya ba sae nazarin abinda zai ce masa yake can ya kallesa yace"kayi hqr fa yaran basa nn sunyi tafiya"
Lesson teacher yace"to shikenn amma yaushe ne zasu dawo?
Shiru man yayi can yace"ka tafi kawae dae"
Ba musu lesson teacher d'in yayi sallama dashi ya wuce.
Man ya rufe qofar ya juya ya sami malika a tsaye tace"my man waye ne?
Yace" Lesson teacher ne
Tace"au shi baisan matsiyaciyar tayiwa kanta tsiya ba"
Komai bai ce da ita ba sae zama yayi ya jingina bayansa tare da lumshe idonsa .
Nn taje ta zauna kusa dashi tare da kwanciya kan qirjinsa yace "pls malika im nt in mood n i just wnt me alone ki tafi d'akin ki kinji "
Zata ce wani abu knn yace"pls just go"
Jiki sanyaye ta tashi ta tafi zuwa d'akinta,haka shima ya tashi ya bar falon ya tafi d'akin shi.

2 dayz later
haka mohd ya cigaba da rashin son damuwa komai qanqantar ta kuwa shiyasa ko yaushe yafi son ya kasance shi kad'ai wanda ko asibiti yaje baya wani jimawa yake dawowa.

Rynt kuwa sae karatun ta tasa ma gaba wacce ko yanzu zaune take a d'akinta ta tasa agwalima gaba tana sha yayinda take duba littafan mkrntar ta na boko dana islamiyya ,
kasancewar yanzu ta gyara d'akinta ta dawo ciki da zama sae bacci ke kaita d'akin inna.
Tana cikin duba littanfanta ne taji inna na qwala mata kira taje ta sami inna a falo inna taba ta waya tace"nasiru ne wae ki gaya mae abubuwanda aka ce ku siyo a makrnta.
Nan ta kar6i wyr ta snr dashi snn taba inna wayarta ta koma d'aki taci gaba da duba littafanta.
Ba ita ta tattara littafan ta ajiye ba sae da ta soma jin bacci duk da cewa dare bai wani yi sosai ba don qarfe tara ne a lokacin.
Bathroom ta shiga tayi wanka ta fito tayi shirin bacci cikin riga da wando ta zuba qaton hijabinta ta fito riqe da agwalimar ta guda biyu a hannu.
Nan ta had'u da Nasir ya fito d'akin inna zaije d'akinta hannun sa riqe da farar leda mai hoton littafai da kuma al'amin bookshop a rubuce ta gaida shi ya amsa tare da miqa mata ledar yace "duba kiga littafan ne "
Ta duba tace "eh sune nagode"
Har ya juya zai fita sae kuma ya juyo ya kalleta tayi saurin sadda kanta qasa yace"ki qara hqr kwana biyu kinji ni shiru har yanzu ban sami kaina bane"
Tace"ba komai yaya ai ka barshi kawae sae ka sami lokaci"
Yace"to sae da safe"
Snn ya fita ita kuma taje ta ajiye littafan a d'akinta taje d'akin inna.
Da shigarta ta bud'e fridge ta saka agwalimar ta a ciki.

Washe gari an sauke Rynt a makaranta sae dube dube take ta inda zata hango mami sbd kwana biyun nn duk suna had'uwa da safe idan an sauke su.
Tana cikin dube dube ne sae ga mami ta shigo gate d'in mkrntar da gudu Rynt ta saki murmushi taje ta tarbota tana mae fad'in"wnn gudu haka mami ba kya tsoron kije ki fad'i"
Tace"Anti sauri nake kar baki ganni ba ki tafi don na hango lokacinda aka sauke ki mu kuma muna baya da nisa har ma nayi ta kiranki baki ji ba,
to kince da nisa ya zan jiki mami,
Mami bata ce komai ba sae lunch box d'inta ta ajiye qasa snn ta ciro school bag d'inta dake bayanta ta bud'e ta ciro er wata container rubber mai marfi taba Rynt tace"umma tace na kawo maki"
Rynt ta kar6a takai hannu a hnkli ta bud'e.
Wacce tana bud'ewa qamshi mai dad'i ya daki hancinta nn taga
awara ce wacce taji cabbage da albasa bayan sauce d'in hantar rago da aka zuba akai mai had'e da kayan lambunda aka yanka su slice by slice ta yanda kallo d'aya zakayiwa awarar ka sami kanka da tsinkewar yawu.
Cikin nuna jin dad'i ta rufe snn ta kalli mami tace "kice ma mama nagode sosai kinji"
Mami tace"yauwa anti nifa har yanzu bamu je kasuwa ba bare naga raqumi ya shiga akurki,idan ma nayiwa umma magana se dariya kawae take min,ta qarashe mgnr ne shaye da toka.
Rynt tayi murmushi tace"umma da kanta take miki dariya"
Tace"eh mana"
To yi hqr jeki kar a fara maku assembly"
Daga hk kuwa sukayi wa juna bye bye suka wuce.

10:00pm
Man ne zaune kan bed ya rufe laptop d'inshi ya d'aura kan bedside drawer ya kwanta sae ga malika ta shigo d'akin taje ta kwanta kusa dashi had'e da kai hannu tana shafa sajen fuskar shi har izuwa qirjin shi,
kallonta yayi tare da janye hannunta daga kan jikinshi ya kashe wuta had'e da juya bayan shi,nn yaji ta matso gab dashi ta rungume shi ta baya
yace"pls malika bana son damuwa kin sani,ki matsa kusa dani bana son jinki a bayana.
Kmr kazar da qwai ya fashewa ta jaye jikinta daga nashi.

🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
```🔮BAZAN BARSHI BA!🔮```

🔮🔮🔮🔮
*page* *```50```*
Washe gari guraren qarfe goma na safe mohd ne ya fito daga bathroom sanye da white bathrobe wanda kai tsaye gun wardrobe ya nufa ya ciro black suit ya ajiye kan bed yayinda malika ke kwance akan bed d'in tana ta sharar bacci.
Bayan ya gama shirin sa tsaf ya d'auki makullin motar sa ya fita,ya bud'e motar sa zai shiga knn sae ga driver yazo byn sun gama gaisawa ne yake cewa "yalla6ai lafiya kwana biyu naga mami da yayarta basa fitowa zuwa mkrnta ko anyi hutu ne banida labari?
Ba tare da yako kalle sa ba yace"sunyi tafiya ne"
Daga hk kuma ya shigewar sa mota yaja ya tafi.

Yana shiga office wayar sa ta shiga ruri ya ciro wyr a aljihu ya d'aga tare da fad'in"Aamil ya akayi ne"
Daga d'ayan 6angaren yace"man muna son zamu shigo 9ja ne but no actual time,bcs akwai wani aikin da Amir keson qarasawa da sae idan ya kammala shi ne snn ko zamu zo,but idan mun zo d'in wnn karon ba a gida zamu sauka ba a gidajen mu zamu sauka shine muke son kasa a fara gyara mana gidajen sbd may be gyaran zai d'an d'auki lokaci kan irin yanda aka jima ba'a shiga gidajen ba,if ma gidajen na buqatar canjin komai pls duk kasa canza a mana.
Man yace"ok naji ka gaida Amir bye"
Daga hk ya katse wayar yaje ya zauna kan kujerar sa mai shillo tare da kai hannu kan landline ya latsa lambobi ya kira, ba jimawa sae ga wata er kyakkyawar farar yarinya ta shigo da bazata wuce 22 yrs ba d'auke da teacup n saucer a hannunta taje kan desk ta ajiye masa snn ta juya ta fita.
Mohd dake latse latse da laptop d'insa yakai hannu a hnkli kan teacup d'inda ke kan saucer ya d'auka had'e da kai bakinsa yana shan tean da ke ciki yayinda yake ci gaba da latse latse da d'ayan hannunsa.

Malika kuwa tunda ya barta ba ita ta farka ba sae 12 wacce da tashin ta ta fad'a bathroom tayi wanka ta fito taje d'akinta ta shirya kafin take sa cleaner ya gyrawa mohd d'akin shi.
Bayan ta gama shiri ne tazo downstairs tayi breakfast taje kan 3seater ta kwanta sae chat take.
Sae jin tayi an fizge wyr tayi saurin tashi zaune had'e da kallon wanda ya fizge wyr.
Qawar ta Fa'iza ce ta gani tana mata dariya itama dariyar ta mata snn tace"yau kuma bazata kika min"
Tace"wlh kedai kan hanya muke nida hubby zamu je gidan su shine nace ya d'an biyo dani nn mu gaisa mun kwana biyu bamu had'u ba tun asibiti"
Malika tace"aini fushi ma nake yi dake wae ace tun asibiti ba waya ba text ba chat"
Sae da Fa'iza ta nemi guri ta zauna kusa da ita snn tace"wlh banji dad'i bane kwanakin nn shiyasa banida lokacin waya don kashe ta ma nayi sae yau na kunna"

Malika tace"eyyah to ya jikin?
Allah naji sauqi sosai ya man da haqurin rashin babyn shi da yake fama?
Malika tayi er dariya snn tace"in gaya miki har yanzu ya kasa haqura ya cire abun a ranshi har ma baya son damuwa kwata kwata he is so lonely.
Fa'iza tace"lallai yana son baby sosai sae ki hanzarta ki samar mai wani "
Tace"Hm ba yanzu ba sae mun gama baje soyayyar mu tukun"
Fa'iza tace"ta bayan fa da akayi?
Aikin san wnn soma ta6i ne ga kuma wnn abar wacce duk da nasan ba kulata yake ba amma idan na tuna cewa wae mtr my man ce sae na nemi farin cikina kaf na rasa but now nsn cewa ni kad'ai ce nayi waje da matsiyaciyar banida wata damuwa sae hln damuwa da my man d'ina yake ciki a yanzu wanda ko shi na d'an kwanaki ne zai ajiye shi mu dawo normal.
Fa'iz tace"hkne kam kinga bari na tashi naje nabar hubby shi kad'ai a mota"
Nan malika ta tashi taje har mota ta rakata suka gaisa da mijin fa'iza snn ta dawo.

Rynt ce a class ita da qawar ta sae er fira suke yayinda Rynt ke d'anyi tana duba littafinta kasancewar free period suke malami ba zai shigo ba.
A cikin firar ne qawarta ta riqo hannun Rynt tace"ni kuwa Rynt kinga wani haske da kika soma yi harda er qiba da kuma wani irin laushi da jikin ki ya qara gaya min meye sirrin"
Ta qarashe mgnr tana murmushi haka ma Rynt murmushin tayi snn tace"hm yanayi ne kawae....da kuma hutawa ba,cewa da qawarta, Rynt wacce still murmushi nakan fuskarta ta girgiza kanta tace"Sarah knn ba kya rabo da wasa"
Sarah tace"Allah ki tambaya kiji duk wanda ya kalli ftr jikin ki yasan cewa ke er hutu ce"
Rynt tace"jikin ne kawae"
Sarah tace"ba wani nn kedai kawae ba kya son a fad'a ne"
Rynt dae bata sake cewa komai ba sae murmushi kawae da tayi yayinda Sarah ta d'aura da cewa keda yayanki skin nature d'inku d'aya sae dai ya fiki kyau da haske"
Da wasa Rynt ta bugo ta tace"is not gud mun sami time mu 6ata shi a banza karatu ya kamata muyi ba surutu ba"
Sarah tace"to qanwar biro da takarda ke kullum karatu dae karatu ba hutu"
Rynt tace"naji dae muyi karatun idan kuma kince srt sae na qara gaba"
Ta fad'i hkne had'e da yunqurin tashi Sarah tayi saurin cewa "no yi hqr muyi karatun to"
Da haka kuwa kowaccen su ta kama litfafinta suna dubawa yayinda wasu en class d'in keta fmn hayaniyar su har da su tsokane tsokane da guje guje"
Can Rynt tayi d'an guntun tsaki ta kàlli sarah tace"Sarah nifa surutun nn ya isheni muje library"
Nan kawae sarah ta bud'e tsakiyar littafinta ta 6alli paper tare da bud'e murya tace"noise maker!kuma d'iya ko dogon motsi kikayi wlh sae na rubuta sunanki na kuma had'aki da uncle ci ubaka"
Sae kaji take class d'in yayi tsit sbd kowa na tsoron malamin ga kuma Sarah no mercy ce kan shine ma yasa aka bata class monitor.
Kan desk Sarah ta hau ta zauna inda take fuskantar kowa ta kalli Rynt tare da d'aga mata gira snn tace"to reader master gareki sae kiyi ta krtn ai ko"
Rynt tayi nurmushi had'e da girgiza kanta ta jawo littafinta taci gaba da dubawa.

Bayan sati d'aya da faruwar haka.
Nasir ne shi da Rynt a office d'in abokin sa fa'iz yayinda fa'iz ke snr da nasir cewa "a gsky idan akace a cire mata cikin nn yanzu ba qarama wahala zata sha ba koma nace zata iya rasa ranta gabad'aya dmn watannin cikin sunyi qanqanta da a cire mata shi yanzu sae dae zuwa nn gaba idan ya qara wasu watanni tukun"
Nasir ya sauke numfashi had'e da kallon Rynt da kanta ke qasa yace"kinji abinda yace a cire maki ne ko kuwa?
Jiki sanyaye ta d'ago ta kalli nasir tace"Aa a barshi idan ya qara watanin sae a cire"
Nan Nasir ya kalli fa'iz wanda ya shiga rubuce rubuce akan takarda da ya gama ya bawa nasir yace"a siya mata wad'an nn magungunan ta riqa sha kafin lokaci yayi"
Nasir ya kar6a had'e da yi masa godiya snn suka fita.

Bayan sun iso gidan inna ne Rynt ta nufi d'akinta Nasir kuwa ya shiga d'akin inna wacce tana ganin shi ta tarbe shi da fad'in"inace anyi nasara?
Nasir yace"anyi nasara inna dmn sam bata fhmci wayo ne ake mata ba"
Inna ta washe baki tace"kai Rynh knn akwai quriciya shike nn ta yarda idan ya qara wasu watannin zuvarwa za'ayi"
Nasir yayi murmushi yace"to inna kinsan fa qaramar yarinyar ce sosai"
Wlh kuwa shiyasa na tausaya mata da cikin nn da ta samu da wuri haka da akayi auren na d'auka ko muhammadu zai yi mata en dibarun su ne har ta kammala karatun ta amma da yake shashashan yaro ne ya d'ura mata ciki ya kuma saki"
Nasir yace"ayi ta hqr kawae inna da sannu komai zai wuce"
Tace"hkne kam amma ya kake gani idan cikin nn ya tsufa haka zatayi ta zuwa mkrnta d'auke dashi kuwa?
Eh to nima

Please Login or Register in order to submit comment