Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya ciro takalman snn ya fita ya koma driver seat yaja musu motar.
A nn Rynt ta snr dashi inda zata.
Komai bai ce da ita ba sae kallonta kawae da yayi ta jikin mirror yaci gaba da tuqin sa har suka isa gidan nasu.

Tana fita yaja motar sa ya tafi ita kuma ta shiga gidan ta nufi 6angaren su mami .
Ta sami mami kwance a falo ita kad'ai wacce tana ganin Rynt ta tashi had'e da buga wani irin ihun murna tazo da gudu ta qanqame ta.

Umma dake kitchen ta fito a rud'e har tana had'awa da gudu se tayi tsaye turus tana kallon Rynt da ta d'auki mami sama zuwa jikinta.
Nn ta girgiza kanta d'auke da murmushi a fuskarta snn ta qarasa gurin su.
Rynt na ganinta ta saki murmushi had'e da gaida ta.
Cikin sakin fuska ta amsa mata har tana tambayarta inna tace"tana lfy"snn ta nemi guri ta zauna kmr yanda uman saliha ta buqata.
Umman saliha kuwa taje ta kawo ma Rynt abinsha da abinci ta ajiye tana mae kallon mami dake zaune gefen Rynt da ta fara cika Rynt da surutu tace"keh kam ko ba lfy bakin dae baya mutuwa ko"
Rynt tayi murmushi kawae tana kallon mami da ta tura baki tana kallon ummarta wacce takai hannu zata buge bakin tana mae fad'in"wae bana hanaki ba"
Mami kuwa tayi saurin 6oye fuskarta a jikin Rynt tana fad'in"yi hqr umma na daina.
Nan umma tayi dariya kawae tace da Rynt"kinga sauko kuci abinci tun d'azun ke kad'ai mami ke jira kixo kuci abincin nn har dae da taga lokacin tashi mkrnta yayi sae zuwa gate take tana dubowo idan kinzo .
Rynt ta kalli mami tace"ba kya jin jiki ne hln da kike faman yawo mami"
Umma tace"hm sauqi dae ta samu don jiya sae kuka take tamin har bata iya cin komai"
Rynt tace"Allah sarki Allah ya qara sauqi"
Umma tace"Amin sauko kuci abincin nn Rynh"
Ta fad'i hkne tare da bud'e kulolin abincin.
D'ayar kula alala ce d'ayar kuma sauce d'in qoda ne a ciki sae kunun aya dake gefe cikin jug yayi sanyi har ya gaji.
Ta zuba musu alalar a plate had'e da sauce d'in qoda gefe snn ta zuba musu kunun aya a cups tace"oya sae ku hanzarta kuci kar abincin ya sha iska.
Nan ta tafi ta barsu da suka gama ne umma ta dawo d'auke da ledar magunguna taba Rynt a cewar taba mami tasha kowanne spoon d'ad'ad'aya .
Rynt ta kar6a umman saliha kuwa taje da sauri ta d'auki wayarta da ke faman ruri kan dining wacce koda ta gama wayar har Rynt ta gama ba mami magungunan ,
nn ta kar6i ledar magungunan ta tafi dasu d'aki.
Sae ga Abban mami ya shigo ,
Rynt ta russuna har qasa tana gaida shi wanda cikin sakin fuska ya amsa mata snn ya shiga daga ciki.


Sae kusan qarfe hud'u Rynt tabar gidan koshi sbd tana da lesson ne amma taso ko zuwa yamai ne snn ko zata koma.

Da dare bayan sllr isha'i Rynt na zaune ita da inna,inna na cin abinci ita kuwa ta gama cin abincinta tana shan agwalima.

Sae ga Abban mohd ya shigo d'auke da sallama a bakinshi.
Inna ce ta amsa sallamar yayinda Rynt ta gaida shi cike da ladabi ,
ya amsa had'e da tambayarta ya karatu "tace"Alhmdlh"
Yace"baku fara Exams ba?
Tace"a'a mundae kusa"
Yace"To Allah taimaka tace"Amin"
Snn ta wuce.
Sae a snn suka gaisa shida inna bayan sun gama gaisawar ne yace"inna inshaAllah idan su Rynh sunyi hutu zamu je qauyen su mu kaiwa mae garin nasu gaisuwa sbd bae kamata ace tun lokacinda muka je neman aurenta ba bamu koma jewayarsu ba"
Inna tace"hkne kam nima na jima ina wnn tunanin sae naga Rynt makaranta take zuwa kuma kai kanka baka zauna ba sae tafiye tafiye kake shiyasa ban tuntun6e ka da maganar ba.
Yace"hakane gsky amma yanzu har izuwa lokacinda zasuyi hutu inshaAllah inada lokaci"
Inna tace"To Allah nuna mana lokaci ya kuma kaimu lafiya ya dawo damu lafiya"
Yace"Amin inna, bari na tashi dan ba daga gida na fito ba kan hanya nake"
Tace"ayyo to ko a kawo ma abinci kaci ne?
Yace"Aa inna ga dae wnn"
Ya fad'i hakane tare da ajiye mata leda a gefenta.
Inna tace"to Allah shiyi Albarka mungode"
Yace"Amin"had'e da fita.
Nan inna ta bud'e ledar ta sami gasasshen naman rago da ya gasu yayi kyau ga timatir da albasar da aka yanyanka akai da kuma qullin yaji gefe.
Rufe ledar tayi sae da ta kammala cin abincinta snn ta kira Rynt ta d'ibar mata nata sukayi zaune a nn falon suna kallo suna ci had'e da er firar da sukeyi jefi jefi.

Zuwa qarfe tara ne suka tashi Inna ta nufi d'akinta haka ma Rynt wacce da shigar ta ta cire kayan jikinta ta fad'a bathroom koda ta fito kawae ta sami mutum kwance kan gadon ta ya wani d'aura qafa kan qafa yana duba littafanta da ta bari kan gadon.
Mugun tsoro taji kafin ta fahimci waye .
Nan ta kama hanya rae 6ace zata fita d'akin had'e da kiran inna.
Man da ke kwance bai san lokacinda ya fizgota ta fad'o kan gadon ba ya kuma sa hannu ya rufe mata baki.
Sae kawae ya tsinkayo muryar inna tafe tana fad'in"Rynh gani ya akayi ne"
Nan yaja Rynt ya shiga da ita bathroom ya rufe wanda still hannunsa na kan bakinta ya rufe gam.
Nan yaji muryar inna tazo gab da bathroom d'in tana fad'in"Rynh me ya faru ne?
A nn Rynt ta shiga qoqarin magana ta qasan maqoshinta , man yayi hanzarin had'e bakinsa da nata yayinda inna ta d'auka ko gyaran murya ne Rynt tayi na alamar tana bayi hkn yasa ta fita.
Man kuwa sae da ya tabbatar inna tabar d'akin snn ya zare bakinsa suna kallon juna shida Rynt kmr wasu zakarun da sukayi fad'a.
Rynt ce ta fara kauda fuskarta had'e da sa hannu ta share lips d'in ta.
Ta juya rae 6ace zata bar bathroom d'in ya riqo towel d'inta tayi saurin kai hannu a qirjinta ta riqe towel d'in had'e da juyowa ta kalle shi nn kawae ya sami kansa da jin wani yanayi a jikin shi kan yanda ta damqe qirjinta had'e da towel sae duk rabin mammanta ya taso har yana ji kamar ya d'aura hannunsa akae.
Nan ya qara jan towel d'in had'e da jawota zuwa jikin shi yana kallon qirjin nata da yake tajin yakai hannun shi.
Bai d'aura hannun sa ba sae saurin kauda idonsa da yayi had'e da sauke numfashi a hnkli tare da sake mata towel d'inta da ya riqe.
Inda cikin kasalalliyar murya ya kalli Rynt da zata bar bathroom d'in yace"kar ki fita zo muyi wata magana kinji"
Rynt ta kallesa tace"to bari na sa kaya tukun"
Wacce ta fad'i hkne kawae amma niyar ta da ta fita rufe d'akin zatayi dashi snn kuma ta kira inna.
Mohd kuwa ba musu Yace"Ok je kisa kayan kizo amma kimin alqawarin baza ki kira inna ba"
Tace"nima kamin alqawarin idan na dawo na saurare ka ba zaka sake dawowa gidan nn ba haka kuma ko school kar ka sake zuwa ka sameni"
Yace"meyasa?
Tace"sbd bana so"
Nan ya kalle ta kawae had'e da sauke numfashi yace"naji na kuma yi alqawarin amma idan kika karya naki nima zan karya nawa"
Nan ta lumshe ido had'e da gyad'a mae kai snn ta fitav bathroom d'in ta sako kayan baccinta riga da wando ta dawo wacce tana shiga bathroom d'in man ke binta da kallo cike da sha'awa.
Rynt bata ankara ba sae jin tayi ya jata zuwa jikinsa yana mata abubuwa masu mugun rikitarwa wacce lokaci d'aya ta sukuikuice ta fara mai kuka tana qoqarin qwatar kanta amma bata da wnn qarfin sbd ya gama kashe mata jiki gabad'aya sae ma kayan jikinta da ya shiga yunqriñ rabata dasu.

Naso na d'an qara maku but wasunku na qorafi sosai akan daren da nakeyi.

``🔮BAZAN BARSHI BA!🔮```

🔮🔮🔮🔮
*```Page 58```* and 59

A nn Rynt ta shiga kuka sosai tana kai masa duka ta koina.
Amma aikin banza dan tuni ya rabata da kayan jikinta ya shiga wasa da albarkatattun kirjinta dake ci gaba rikitar dashi.
Wanda sae yana gab da cimma burin sa ne kukan Rynt ya soma dawo dashi hayyacin sa,nn ya samu da qyar ya saesaita kanshi had'e da rungume ta yana lallashinta.
Tayi saurin fizge kanta a rud'e zata bar bathroom d'in ,
Bata kai ga fitar ba sae jin tayi ya rungumeta ta baya had'e da kai hannun sa kan d'an cikin ta da ya soma tasowa yana shafa cikin sannu ahnkli kmr wani mae shafa qwae,yayinda lips d'insa ke kan wuyanta yana wasa da harsen sa akai.
Nan taji qafafuwanta sun kasa d'aukarta sae zubewa qasa da tayi ya bita yana qoqarin janye hannunwanta da ta rufe qirjinta.
Bai iya janye hannyen ba sae d'agowa yayi yana kallon yanda jikinta ke rawa sosai ga hawaye dake gangarowa a hnkli kan fuskarta.
Nan yakai hannu zai share mata hawayen tayi saurin matsawa had'e da d'aukar kayanta ta rufe jikinta tare da fashe masa da kuka.
Nan kawae ya kalleta ya tashi ya kimtsa kanshi ya fita bathroom d'in ya barta sae kuka take can ta tashi tasa kayan baccin ta ta fito batroom ta share fuskarta da tasha kuka snn ta fita a d'akin taje d'akin inna,
ta samu inna na shafa'i da wuturi taje tayi kwance kan bed kamar wata marar lafiya dan har wani kamewa guri d'aya tayi kamar mae jin sanyi.

Inna da ta gama sallah ta d'auka ko sanyi Rynt keji shiyasa da taje zata kwanta taja blanket ta rufa mata jikinta.
Rynt naji amma ta lafe kamar mae bacci sae ajiyar zuciya da ta fitar a hnkli.

Washe gari Rynt ta gama shirin ta tsaf na zuwa school zata fita inna ke ce mata na manta ban gaya miki ba Rynh jiya da kabiru yazo yace yana son idan kunyi hutu zamu je qauyen ku gurin mai gari mu kai masa ziyara".
Jikin Rynt ne yayi sanyi don inna na d'auko maganar qauyen su sae ta sami kanta da tuna baffanta ta kalli inna kawae tace"to"had'e da fita.

Yanda taje school jiki sanyaye haka ta kasance har aka tashi tazo bakin gate tana rarraba ido inda zata hango motar drivernta sae roqon Allah take idan ba mohd ne zai zo ba duk da cewa yayi mata alqawarin ba zai koma dawowa ba amma tasan ba lallai bane ya cika alqawarin.
Tana cikin hkne ta hango motar drivernta yazo nn ta sauke ajiyar zuciya taje ta shiga motar suka tafi.

Koda aka sauke ta ta shiga se ta had'u da Aamil zai fita gidan wacce tana ganin sa sae da gabanta ya fad'i don ta d'auka ko mohd ne har dae yanda ya bita da kallo sae kawae tasha toka bata ce dashi komai ba ta wuce.
Sae ga inna ta fito da sauri riqe da waya a hannunta tana kiran Aamil da ya manta wayar shi.
Aamil ya juyo yayinda inna taba Rynt waya tace takai mishi wyr.
Taje ta kai masa waya had'e da gaida shi wanda sae da ya kar6i wayar snn ya amsa gaisuwar yana mai kallonta har sae da ta juya ta tafi snn ya kauda idonsa akanta ya wuce.

Rynt kuwa da shigarta d'akinta taje ta rage kayan jikinta tayi wanka ta fito ta shirya ta fita ta sami inna zaune a falo tana kallo nn ta qarasa ta zauna qasa kusa da kujerar da inna ke zaune akai inna ta dafa kanta tace"wae Rynh me yake damunki ne na fhmci tun da safe kike cikin damuwa"
Rynt ta girgiza kanta had'e da cewa "ba komai inna"
Inna tace"ko kina jin jiki ne?
Tace"um um bacci ne kawae inna"
Inna tace"to tashi kije ki d'ebo abinci kici sae ki d'an kwanta kafin qarfe hud'u tayi mae miki darasi yazo"
Rynt tace to had'e da tashi ta nufi kitchen ta d'ebo abinci tazo nn falo ta zauna ta shiga cin abincin cikin natsuwa.
Bayan ta gama cin abincin ne tayi kwanciyarta akan 3 seater ba jimawa kuwa bacci ya kwashe ta inna ta kalleta kawae ta ci gaba da kallonta wacce tana cikin kallon ne ta jiyo sallamar Aamil ya dawo gidan ,
inna ta amsa sallamar yayinda ya shigo riqe da wata leda a hannun shi yayi tsaye kawae yana kallon Rynt dake bacci sae can ya sauke numfashi had'e da lumshe ido ya kauda fuskarsa ya kalli inna da tace"ya akayi ne Aamil?
Bai ce komai ba sae ledar hannun sa da yaje ya ajiye kusa da ita snn yace"wae fruit ne na siyo maku d'azun da zan shigo shine na manta su a mota har sai da na koma gida snn na tuna.
Inna tace"ayyo d'an albarka shine ka koma dawowa to Allah shiyi albarka mungode"
Yace "amin"had'e da zama kusa da kujerar da Rynt ke kwance .
Inna kuwa tashi tayi taje kitchen ta d'auko kayan gyaran fruits tazo tayi zaune a qasa ta miqe qafafu zata fara gyara fruit d'in Aamil yace"inna da kanki ina wnn Baabar take ne?
Inna tace"ayyo ai Baaba hurera bata sami shigowa ba yau sai dae ko gobe "
Yace"to inna bari na taya ki"
Ya fad'i hkne tare da tashi yaje gaban inna ya zauna had'e da lanqwashe qafafuwan sa yana mai kwashe hannuwan rgrsa.
Dariya kawae inna tayi ta bashi tray da wuqa don ba yau suka fara ba.
Nan ya fara gyara fruits d'in sae yi yake yana kallon Rynt dake baccinta.
wanda yana gab da kammala gyara fruits d'in ne yaga Rynt ta shigo motsi tana juyi kmr zata fad'o kan sitar yayi sauri zai tashi sae kawai yaga bata fad'in ba sae tashi zaune da tayi tana mustsuke ido.
Bayan ta gama mustsuke idonta ne ta shiga kallon Aamil da mamaki kan aikin da ta gani a gaban sa yana yi ta dae san ba mohd ba kam sae dai ko wanda ta gani d'azun ko d'ayan shi.
Inna ta katse ta da cewa"Rynt kin tashi?
Tace"eh inna"
tace"zaki sha 'ya'yan itacen nn ko sae sunyi sanyi tukun"
Tace "Aa sae sunyi sanyi inna"
Inna tace"wae naga kina son 'ya'yan itace sosai shiyasa na d'auka ko zaki d'an sha kafin suyi sanyi"
Uhm hakane inna amma yanzu so nake na fara shirin lesson don naji kmr an fara kiraye kirayen sllr la'asar.
inna tace"to shike nn jeki muma ai tashi zamuyi ynx.
Nan Rynt ta wuce Aamil da ya bita da kallo ya maida duban sa gun inna kmr wanda zai tamvaye ta wani abu sae kuma ya fasa.
Ya tashi ya d'auki kayan gyaran fruits d'in da ya gama aiki dasu yakai kitchen ya dawo yayi ma inna sallama a cewar daga masallaci zai wuce.
inna tayi masa Allah kai lafiya snn ta d'auki bowl d'in da fruits ke ciki taje d'aki ta saka a fridge ta nufi bathroom zuwa arwala.

Sorry 4 dis one.

Billy giro😊
[2/23/2017]
```🔮BAZAN BARSHI BA!🔮```

🔮🔮🔮🔮
*```Page 59```*
Koda 8:30 tayi na dare tuni Rynt ta kammala duk wani abu da tasan tanayi a d'akinta ta rufe d'akin taje d'akin inna.
Wacce don mohd kad'ai tayi hkn sbd ta fhmci guraren qarfe tara da wani abu ne yake zowa,ba wae don ta manta alqawarin da yayi ba sae dan ta tsorata sosai da abinda ya tashi faruwa jiya da ita haka kuma bata da tabbacin cewa zai cika alqawarin.

6angaren mohd kuwa kwance yake kan bed yana dubin silin daga shi sae farar singlet da farin boxer ya lumshe ido kmr wani mae bacci sae ga malika ta shigo d'akin riqe da cup a hannun ta ta ajiye cup d'in kan bedside drawer ta zauna gefen gado nn kusa da man tana mae kallon fuskar sa snn ta d'aura hannunta a hnkli kan sajen fuskar sa tace"my man ga ruwan Lipton d'in na had'a ma"
A hnkli ya tashi daga kwancen da yake ya zauna malika ta d'auki cup d'in zata kai bakin shi ya dakatar da ita ta hanyar kar6ar cup d'in ya maida kan bedside drawer ya ajiye ya kuma koma abinsa ya kwanta.
D'auke da mamaki malika tace"my man lafiya?
Yace"malika bana jin zan iya sha"
Cikin damuwa ta lumshe ido ta ware su akan shi snn ta riqo hannun sa tana mae kallon fuskar sa tace"my man na rasa me yake damunka tun daren jiya har izuwa yau kuma idan na tambayeka sae kace min wae ba komai shin banyi matsayin da zaka gaya min damuwar ka bane ko kuwa?
Man dake kallonta ya jawota tare da kwantar da ita kan qirjin sa yana shafa bayanta ba tare da yace da ita komai ba.
Malika dake lafe a qirjin nasa tace"my man baza ka gaya min damuwar ka ba"
Yace"malika na gaya miki ba komai"
Tashi tayi daga kan qirjinsa tana kallon sa tace"kawae dae baza ka gaya min ba amma wlh kana d'auke da damuwa"
Ta qarashe mgnr ne cikin 6acin rae mae had'e da muryar kuka snn ta d'aura da cewa" a duk duniya kaine mutum na farko da na fison naga na sharewa damuwar shi idañ na gañshi a ciki amma sae gashi kai sam baka son ma ka gaya min damuwar ka bare har nayi yunqurin ganin na kawar ma da ita.
Tana kaiwa nn ta fashe da kuka ta tashi ta bar d'akin .
Man ya bita da kallo kawae har ta fita snn ya gyara kwanciyar sa zuwa gefen hannunsa na dama yana mae kallon agogon bangon d'akin yaga 9:00pm nn ya lumshe idonsa a hnkli had'e da kai hannu ya kashe wutar d'akin.

Washe gari ya fito daga wanka sanye da white bathrobe a jikin shi ya sami malika zaune kan bed wacce tana ganin sa tayi saurin tasowa taje gab da shi tayi tsaye tana kallon sa d'auke da idanuwanta da sukayi jajir kan kuka,
nn kawae ta fashe da wani kukan ta fad'a jikinsa ta rungume shi tana fad'in"my man na fhmci ynz ka daina sona kwata kwata na rasa meyasa"
Dagà hk taci gaba da kukà man ya qara rungumeta yanà lallashinta yanà bàta màgaña har ya samu tayi shiru ta kuma manta komai nn take.
Wacçe d'auke da murmushi a fuskarta ya jata suka je kan bed zai shafa Vaseline, ta kar6i Vaseline d'in ta shiga shafa masa.
Tana gama shafa masa ne ya yunqura zai tashi zuwa saka tufafi ,
ta maida shi zaune tana kallon sa cike da sha'awa snn takai hannu ta shafo sajen fuskar sa cikin marairaicewa tace"my man u know i really missed u"
Shiru kawae man yayi yana kallonta ita kuwa sae ci gaba take da shàfa sajen fuskar shi yayinda takai fuskarta a hnkli kan tashi ta had'e bakinta da nashi tare dà kai hannu tana shàfa jikiñsà ta koiña bae hanata ba ya biye mata don baya son shiga haqqinta,duk da ba irin abinda yafi so irin ace Rynt ce ya samu ba ita ba.

******
Aamil ne fake cikin motar sa a nn bakin gate d'in gidan inna da shima kanshi bae san dalilin zuwan shi da sassafen nn ba.
Nan dae ya fito motar ya shiga gidan bai sami kowa a falon ba sae fruits salad da ya samu an had'a cikin d'an wani transparent rober bowl mae marfi an ajiye kan center table.
Ya kauda idonsa had'e da sallama inna ta amsa sallamar snn ta fito.
Wacce tana ganin Aamil ta washe baki zuwa murmushi tace"Aamil kaine da sassafen nn ina ce dae lafiya ko?
Yace"lafiya qalau inna na shigo ne kawae"
Inna zata yi magana knn idonta ya fad'a kan fruits salad d'in da ke ajiye kan center table taje ta d'auka had'e da fad'in"ayyo ashe Rynh haka ta tafi mkrnta ta manta 'ya'yan itacen nn nata"
Aamil da yaje xai zauna sae fasa zaman yayi yace" eyyah ina ne makarantar tasu sae na kaimata?
Inna tace"da kuwa ka kyauta min Aamil dan wlh Rynh na son 'ya'ya itace nsn yanzu haka tana can tana fama da zullumin mantasu da tayi.
Ta fad'i hkne yayinda Aamil ya kai hannu ya kar6i fruits salad d'in had'e da cewa"wace makaranta take ne?
Inna tace"yo ai kaji fa ni zaune kawae nake da ita ban ko san sunan makarantar tasu ba amma kira nasir a waya zai gaya ma"
Nan ya fita had'e da zaro wayar sa a aljihu ya kira nasir wanda sae da suka gaisa snn ya tambaye shi.
Bayan nasir ya gaya masa ne yaja motar sa ya tafi,
bai zarce koina ba kuwa sae makaratar su Rynt.

Rynt na zaune cikin class za'a fara teaching d'insu d'auke da damuwar mantuwar da tayi don ana sauketa gate ta tuna cewa tayi mantuwa.
Tana cikin hkne kuwa se ga security an aiko ana kiranta.
Yi tayi kmr bata ji ba dan ta d'auka ko mohd ne yazo kmr rnr da ya ta6a zowa shiyasa tayi zamanta har sae da teachern su ya mata magana snn ta tashi ta fita wacce tana ganin Aamil ta yarda cewa mohd d'in ne yazo taje shaye da toka tana kallon sa tace"me kuma ya kawo ka?

Da mamaki Aamil yace"Aamil ne fa"
Da sauri ta sadda kanta qasa tace"dan Allah yi hqr bana banbance ku ne"
Yace"no ba komai had'e da bata robar fruits salad d'inta da yasa abu yayi wrapping ba'a ganin meye a ciki kmr gift ,bata kar6a ba sae kallon sa da tayi, yace"fruits salad d'inki ne da kika manta"
Dad'i taji har ranta don d'auke da murmushi ma takai hannu ta kar6a had'e da yi masa godiya.
Murmushi kawae ya mata snn ya juya ya tafi ita kuma ta koma class.

Man kuwa bayan sun gama abinda sukeyi ne yayi wanka ya fito cikin shirin sa na zuwa asibiti wanda har zai shiga mota sae yaga motar Amir ta kunno kai a cikin gidan ,
nn ya fasa shiga motar tasa ya tsaya jiran Amir da ya faka motar sa ya fito ya same shi had'e da bashi hannu suka gaisa .
Snn yace" zaka je asibiti ne?
"Eh"
cewar mohd kafin yake cewa "ya akayi ne"
Amir yace" wae gidan inna fa zanje sae kawae nayi sha'awar nazo nn "
Mohd yayi murmushi yace"ai ka kyauta dan da Aamil ne bazai zo ba ,rabona dashi ma har na manta"
Amir yace"ksn shi Aamil kmr kaine gidan inna yafi zuwa akan koina"
Mohd yace"hkne amma yaushe zaku koma ne nikam?
Eh to tukuna bamu sa rana ba dan wlh ni har ji ma nake kmr mu dawo da zaman mu a nn har aikin mu"
Man yace"kan ku ake ji nidae idan kaje gun inna kace ina gaida ta"
Amir ya kalle sa yace"inna kuma dake fushi dakai"
Yace"to ai so nake ta

Please Login or Register in order to submit comment