Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daina fushin dani ko zan sami hanyar bawa Abba hqr dmn naga cewa na dawo da wnn yrnyr"
Yace"hkne ni na tafi"
Nan sukayi sallama da juna kowanen su ya shiga motar sa suka bar gidan.

3 dayz later
Aamil ne zaune a falon inna shida inna suna firar su yana yanka fruits wanda tunda yaji cewa Rynt na son fruits kullum sae ya siyo ya kawo kuma duk ya kawo shi keyin zaune da kanshi ya gyara.
Suna cikin hkne sae ga Rynt ta dawo daga school wacce tana shigowa idonta ya sauka akan Aamil dake gyaran fruits kanta qasa ta gaida shi d'auke da er alamar dariya a fuskarta.
Aamil dake kallon ta ya amsa had'e da kallon inna yace"inna Rynt fa da kmr dariya nake bata idan ta ganni ina aikin nn ko meyasa?
Inna ta washe baki ta kalli Rynt wacce tayi saurin barin gurin cikin jin kunya
Innà tace"ni kuwa ina zan sani wata qil bata saba ganin namiji na aikin nn ba"
Yace"inaga hakane inna don naga har kunya takeji idan ta samu ina aikin nn"
Inna tace"ai ita Rynh komai kunyar sa take ji"
Aamil yace"wlh inna shiyasa take matuqar bani sha'awa"
Inna tace"ai Rynh abin so ce ga kowa don yrnyr ba ruwanta wlh"
Aamil yayi murmushi zai yi magana wayar sa ta shiga ruri ya d'aga wayar had'e da fita wanda sae da ya jima kafin yake dawowa ya sami Rynt ta maye gurbinsa tana ci gaba da aikin da ya bari.
Yayi tsaye kawae yana ta kallon ta yayinda Rynt keta aikinta bata ko san yana yi ba sae inna ce ta lura dashi tace"yadai Aamil ko zata tashi ne ta bar ma aikin ka qarasa abinka?
Ya kalli inna kawae snn ya kalli Rynt yace"hln yau mai lesson d'in naki ba zai zo bane"
Ba tare da ta kalle sa ba tace"zai zo"
Yace"amma kuma shine kika zauna ma aikin nn da dawowarki school ko abinci ma baki ci ba"
Inna tace"kai fad'i ba yanda banyi da ita ba nace ta bari ni na qarasa ita taje taci abinci tace Aa"
Aamil dake kallon Rynt yaje ya durqusa a hnkli kusa da ita snn yakai hannu ya kar6i wuqar da ke hannunta yace"bani aikin tashi kije kici abinci kinji kafin mai lesson d'in naki yazo"
Sae da Rynt ta kàlle shi snn ta tashi ta tafi d'akin inna ta d'ebo fura a cup taje d'akinta tayi zaune tana sha.


A washe garin rnr mohd ne zaune a office d'in shi da kallo d'aya zakayi masa kasan cewa yana d'auke da damuwa a ransa wanda tun daga wnn rnr bai qara zuwa gidan inna ba haka kuma bai sake bibiyar Rynt a school ba kan alqawarin da ya d'aukar mata da ya soma jin ba zai iya ba.
D'auke da damuwar da yake ciki ne ya kalli Amir dake zaune suna fuskantar juna yace"wae Amir a wnn rnr da zakaje gidan inna har nace kace ina gaidata ka snr da ita kuwa?
Amir yace"eh na gaya mata mana sae dae yi tayi kmr bata ji ba"
Mohd yayi shiru can yace"Amir a gskiya ina cikin damuwar rashin wnn yarinyar a kusa dani bazan 6oye maka ba ina son ta dawo gareni ne sbd ina sonta ba wae dan babyna kad'ai ba.
Amir ya sauke numfashi snn ya kalle sa yace"to ai tunda hkne ka tashi muje kawae ka bawa Abba hqr "
Man ya girgiza kansa had'e da fad'in" no Amir ina gudun naje na qara tinzira Abba ne.......Kaga kawae kasa a ranka cewa idan munje ka bashi hqr zai haqura da haka kuwa sae kaga Allah ya taimake ka ya haqura.
Mohd yace"haka kake gani?
"InshaAllah"cewar Amir
Yayinda mohd ya kalle sa jiki sanyaye yace"shiken nn muje d'in".

Nan suka tashi suka d'unguma sae gida suka nufi 6angaren su kai tsaye suna shiga dae dae Abba na saukowa kan staircase suka had'u dashi ,
a nn mohd ya tsaya cak ko tako d'aya ya kasa qarawa sae kansa da ya sadda qasa sbd wani irin mugun kallo da Abba ya tsaya yana musu dashi har Amir.

``🔮BAZAN BARSHI BA!🔮```

🔮🔮🔮🔮
*```Page 60```* and 61

A fusace Abba ya qaraso gurin su wanda kai tsaye gun mohd ya nufa ya d'aga hannunsa cikin zafin nama ya kai masa mari had'e da nuna shi yace "Ba nace kar na qara ganin qafar ka a gidan nn ba ko kuwa rashin d'a'arka ce kazo ka qara nuna min ne, to bari kaji wlh idan har ka sake kuskure irin wnn sae na maka abinda baka taba tunani ba shashasha kawae, get out of this house!"
Juyawa mohd yayi idonsa ya kada yyi jazur yyi saurin fita daga gidan, yayin da Amir ya kalli Abba cikin yana yi na son bashi haquri Abba yayi saurin dakatar dashi ta hanyar d'aga masa hannu yace "Amir idan har ba so kake laifin mohd ya shafe ka ba to kaima kayi gaggawar fita a nn in daina ganin ka"
Amir ya girgixa kai da damuwa yace "Dan....." cikin d'aga murya Abba yace "ka fita nace!
Jiki a sanyaye Amir ya fita ya samu har mohd yaja motar sa ya bar gidan.
Nan yaje ya shiga tasa motar ya tafi sae gidan mohd.
A nn falo ya tarda Muhd kwance kan doguwar kujera idonsa lumshe sae girgixa kafa yake, Amir ya xauna kujerar dake kallon Wanda yake ya kirasa a nutse, da kyar mohd ya iya bude ido yana kallon dan uwan nasa.
Cikin muryar rarrashi Amir yace"pls am really sorry ban san cewa haka abin yake ba"
Mohd dake kallon sa yace"Inafa zaka sani ina ma bayani kaqi ka fhmta yanzu gashi meye riba in banda qara 6ata min tsari da kayi"
Yana gama fad'ar hk ya buga tsaki ya tashi ya bar masa falon Amir da ya bisa da ido ya girgiza kansa kawae snn ya tashi ya fita.

5:00pm
Rynt ce zaune a falo ta tasa littafanta gaba tana dubawa sae ga Aamil ya shigo had'e da sallama ta amsa sallamar yayin da ta d'ago ta kalle shi bata kawo kowà ba sae shi Aamil d'in don ta fhmci yanzu kusan ko yaushe shine ke zowa.
Nn ta gaida shi fuskarta ba yabo ba fallasa ya amsa mata cikin sakin fuska snn yace inna fa.
Tace"inna tana maqota amma tace bazata jima ba zata dawo"
Yace"OK"snn ya zauna yana mae kallon Rynt da ta maida hnklinta gun duba littafanta yace"kuna da test ne?
Tace"um um ina dubawa ne kawae"
Yace"gud haka nada kyau ,but yaushe zaku fara exam ne?
Rynt tace"wani sati mai zowa inshaAllah"
Yace"olryt next week knn ,inga littafin"
Ba musu ta bashi ya kar6a yana dubawa nn yaga rubutun nata mai kyau dashi.
Yace" zaki koya min rubutun nn naki mae kyau"
Ya fad'i hkne d'auke da murmushi a fuskar sa yana kallon ta"
Kallon sa tayi ta kauda kanta d'auke da d'an guntun murmushi ba tare da tace komai ba,shima d'in dae bai ce komai ba sae sauka yayi kan kujerar da yake, ya zauna nn qasa inda yake fuskantar ta ya lanqawshe qafafu kmr yanda take zaune itama snn ya d'aura littafi a nn tsakiyar su ya kalle ta yace "a ina kika tsaya da karatun naki?
Tace"topic d'in yau ne kawae kuma shima tun a school na fara dubashi kuma shine kazo ka tarar ina dubawa"
Yace"shikenan zan tambaye ki abinda kika fhmta akan kowanne topic dake ciki"
Ta gyad'a masa kai yayin da shi kuma yaje ga topic d'in farko ya fara mata tambayoyi tana bashi amsa shi kuwa ya kafe idon shi akanta se kallon d'an qaramin bakinta yake dake ta koro bayani filla filla kmr malami na koyar da d'alibi.
Sallamar inna ce ta katse su nn Aamil ya fitar da numfashi a hnkli ya kalli inna tare da amsa mata sallamar snn ya gaidata.
Washe da baki ta amsa had'e da tambayar sa mutan gida
Yace"duk suna lafiya kuma suna gaida ke"
Tace"madallah ina amsawa"
Kafin take kallon yanda suke zaune da kuma littafin da ke hannun Aamil tace"Au yau kaine ka maye gurbin mai darasin nata knn "
Nan Aamil yayi saurin duba agogon hannun sa yace"af inna ai na
manta cewa lokacin lesson d'in nata yayi wata qil ma har yazo yayita sallama ba muji ba"
Inna tace"Aa ai yau ba zai zo ba sbd rnr yau an ke6e mata ita ne dan ta samu ta huta"
Aamil ya kalli Rynt yace"to inna ai karatu kuma na samu tanayi ba hutun ba"
Inna tace "yo ai ita Rynh ko yaushe haka take kullum cikin karatu take uwa ta jika takardar ta shanye"
Aamil dake kallon inna ya maida duban sa gun Rynt yana murmushi yace "Rynt is gud kid'an riqa hutawa kinji ko"
Gyad'a masa kai tayi shi kuma ya bata littafin ta tare da fad'in"to jeki ajiye gobe idan na dawo ma qarasa ko"
Tace"tohm" had'e da kar6ar littafin ta had'a da sauran snn ta tashi ta nufi d'aki yayin da Aamil ya bita da ido har ta shige d'aki yace "inna wae ina kika samo yarinyar nn ne wlh se naji ta kwanta min a rai sosai, ga ta da hnkli"
Jin shiru yasa ya maida duban sa gun inda inna ke tsaye yaga ashe ta d'aga bata nn.
Mikewa yyi a hnkli ya dauki makullin motar ya fita daga falon. Bayan 'yan mintina inna ta dawo falon rike da kofin fura tana cewa "gashi nn sauran na Ryynt ne...." Bude ido tayi tace "Au har ya tafi ko me?" Kwala ma Ryynt kira tayi ta fito inna tace "ina wnn yaron ba dae ya tafi ba" Ryynt tace "ban sani ba inna ina ciki" inna ta tsuke fuska tace "to in gidan uwarsa yaje xae tafi bae mata sallama ba dan bnxan yaro kawae, inda Muhd ya fi su knn" Rayyanat dae murmushi kawae tayi bata ce komae ba ta juya ta koma daki.
Karfe takwas da kusan rabi Ryynt na xaune falo suna kallo da baaba hurera inna kuma na daki tana sallah aka bude kofar falon hade da sallama, Amir ne ya shigo ya karaso cikin falon murmushi dauke a fuskarsa, baaba Hurera ya gaidar snn ya xauna yana kallon Ryynt, ta dan sake fuska had'e da gaishesa dan ta d'auka ko Aamil ne da ta d'an fara sabawa dàshi ,ya amsà gaisuwar yana màe ci gàba dà kàllonta yayin da Baaba hurera tace "Yau kaine a gidan namu shugaba"
sae a snn ryynt ta gane Amir ne don sunan da baaba hurera ke kiransa knn, yyi murmushi yana shafa kai yace "nine baaba, innar fa"Baaba Hurera tace "tana ciki tana sallah" shiru yyi bae ce komae ba yana dan satan kallon ryynt da ta maida dubanta ga kallon da take, mikewa baabà hurera tayi tace "bari in kawo maka abinsha ko" kmr jira yake yace "to baaba" ta mike ta nufi kitchen, sakkowa kasa yyi da sauri yana kallon ryynt yace "Rayyanat ina son muyi wata magana da ke don Allah, ko idan xan tafi xa ki dan fito na jiraki" hade rai tayi tace "nifa sanyi nake ji" shiru yyi yana kallonta snn yace "ae ba wani ddewa xa muyi ba" fitowar inna daga daki ne ya sanya shi yin shiru ya maida dubansa ga tv kmr me kallo, inna tayi michi michi da ido tace "waye wnn nake gani kmr Muhd a falona" Amir yyi yar dariya yace "A'a nine inna" tace "ayyo wace gulmar ce to naga kamar kana yi" dariya yyi ya mike yana kallon ryynt yace "ni kinga tafiyata ma inna tun daxu na shigo gaishe ki" bae jira cewarta ba ya fice daga falon.
Yayin da inna tace"to Allah kiyaye"snn ta nufi kitchen.
Rynt kuwa ba dan ran ta ya so ba ta tashi da sauri tabi Amir ta samu har ya fita gate, dan tsaki ta ja ta bi bayansa, jingine ta samesa jikin motarsa ta karasa tace "gani" bata rufe baki ba aka bude motar, kamshin turarensa kawae ya bugi hancinta ta juya a tsorace xata bar gurin ya fizgota, kuka ta saki tana kallon Amir tace "amma ka cuceni wllh," Amir ya girgixa mata kai yace "ki tsaya ki sauraremu Ryynt, mgnr fahimta muka xo ayi"cikin kuka tace " bana bukata, ni ku rabu dani kawae kar in maku ihu ko ana dole ne"
Nn ta gatsara wa mohd cixo ya cikata ba shiri tayi cikin gida a guje, Amir ya fuzar da iska yace "sae da nace maka kadda ka fito man ban san me ya fito da kai ba mtsw c wat you've caused now" Muhd ya dafe kansa yace "I just can't control my self ne" Amir yyi tsaki ya shige mota, Muhd ma ya bude motar a sanyaye ya shiga Amir ya tada suka bar layin. Ryynt na shigowa falo ta had'u da inna ta fito daga kitchen tace "Aa ina kika fito ne Rynh? ryynt dake kkrin boye hawayen fuskarta tace "na d'an fita ne kawai" snn ta nufi daki da sauri don xuwa yin kukan dake cinta ko xata ji ddi, wani mugun tsanar Muhd na mata yawo a xuciya.
Washegari ya kasance lahadi Ryynt na kitchen tana soye soyen kajin da Abba ya aiko masu da shi safiyar ranan Baaba hurera na can bakin famfo tana wanki, inna kuma ta tafi anguwa awanni biyu da suka wuce, gajiya ryynt tayi da soye soyen don wani mugun bacci kawae take ji gashi bata dad'e da farawa ba, tana kwashe Wanda ya soyu ta xuba wani ta xauna kan yar kujerar dake kitchen din ta jingina jikin bango ko minti biyu bata kara ba bacci me shegen nauyi ya dauketa, kiranta taji ana yi a nutse cikin bacci ta farka a tsorace lkci daya ta mike tsaye shi ma ya mike, kallonsa take har lkcn a tsorace tana son gane waye, ya sakar mata murmushi da ya bayyana fararen hakoransa, juyawa tayi da sauri tana kallon gas ta ganshi a kashe ta karasa gun da sauri don ganin suyan da take ta ga saura kadan ya qone, karasawa yyi kusa da ita yace "don me baki bari kin tashi daga bacci ba kika yi aikin," bata basa amsa ba sae ma gaishesa da tayi ta soma kkrin kwashe naman dake cikin mai.

Dan Allah kuyi hqr da na bar ku kuna ta zuba ido wato kwata kwata sabo da posting d'in dare ya mantar dani yanda nayi daku.
Gashi kuma yau na d'an samu kaina busy but am really sorry pls n pls 🙏🏻
Luv u all❤

Billy giro😊
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮?🔮🔮🔮🔮🔮?```🔮BAZAN BARSHI BA!🔮```

🔮🔮🔮🔮
*```Page 61```*
Tsaye kawae yayi yana kallonta har ta gama kwashe naman ta zuba wani snn ta kalle shi tace"nifa kasan ba gane ku nakeyi ba waye kai?
Aamil da still kallonta yake ya lumshe idonsa a hknli ya kuma ware su akanta snn yace"Aamil ne"
Tace"oh yi hqr ai na d'auka ko wancan d'ayan ne"
Yayi murmushi snn yace"ba komai je ki qarasa baccin naki idan naman ya soyu se na kwashe maki ko"
Murmushi tayi had'e da girgiza kai snn tace"ai baccin ma ya tafi"
Yace"eyyah sorry ashe da ban tashe ki ba"
Tace"ai ba komai dama karatu nake da niya idan na kammala suyar"
Yace"wae ke kam ba kya hutu ne Rynt"
Ta kalle sa tace"uhm jarabawa fa zamu fara gobe"
Yace"hkne fa gobe ne monday ko?
Ta gyad'a masa kai had'e da fad'in eh"yayinda ta d'auki abun tsama tana juya suyar da naman ya soyu ta kwashe suka koma falo Aamil yace ta d'auko littafanta ya taya ta dubawa.
Ba musu taje d'aki ta dau'ko littafinta da za'ayi masu jarrabawar sa gobe.
Sukayi zaune a nn tsakiyar falon yana mata tambayoyi tana bashi amsa cikin natsuwa shi kuma sae kallonta yake tayi dan gabad'aya ta tafi da hnklinshi ganin komai ya tamvaye ta kai tsaye take bashi amsa da kuma bayani gamsasshe wanda har ya gama mata tambayoyi akan all topics d'in da ke cikin littafin en kurarra kad'an tayi ya gyra mata.
Ya bata littafinta d'auke da murmushi a fuskar sa yace"na yaba da qoqarin ki sosai Rynt ina roqon Allah yasa kifi haka "
Cikin nuna jin dad'i tace"Amin nagode"
Kafin Aamil ke cewa to d'auko wani littafin sae mu duba ko"
Kallon sa tayi cikin yanayi na shagwa6a da sam bata san tayi ba tace"Allah bacci nakeji sosai"
Sae dai ya d'an jima yana kallonta kan yanayin shagwa6ar da tayi snn yace"ok jeki kiyi baccin"
Tace"to"snn ta tashi ta tafi d'aki.
A nn Aamil ya furzadda iskan bakin sa a hnkli tare da jingina bayansa a jikin doguwar kujera yana mae bin qofar Rynt da kallo dan ko kad'an bai so ta tashi ba.
Inna da nasir ne suka shigo ya miqe had'e da amsa sallamarsu snn yaba nasir hannu suka gaisa ya kalli inna yace"wae inna dama ba kya nn ne?
Inna tace"yo naji shashasha da to a gurin wa kazo da har baka san bana nn ba"
Sae da yayi murmushi snn yace"inna gurin wa zan zo kuwa banda ke kawae dae da ban ganki ba na d'auka ko kina ciki kina bacci"
Tace"au ai ka tambayi Rynh kaji inda nake ko kuma baka ga Ryynh d'in bane itama"
yace"na ganta har ma mu kayi karatu yanzu ma ta shiga daga ciki zatayi bacci.
Inna tace"wato kama ga Rynh sae baka tambaye ta inda nake ba dan ba ina uwarka ba ko"
Er dariya Aamil da nasir su kayi snn Aamil yace"ko d'aya inna ba hk bane kin sani"
Tace"to ya kabaro mutan gida?
Yace"suna lfy ,ai ilham har so tayi nazo da ita sae gashi koda zan fito tayi bacci"
Inna tace"ayyo ai sae kazo min da ita gobe idan zaka zo ko"
Yace"to inna"kafin yake cewa ni zan tafi"
inna tace"au ko gaisawa ba muyi ba har zaka tafi"
Yace"inna akwai d'an wani aiki da nake son naje gida nayi ne amma inshaAllah zan dawo anjima"
Tace"to a dawo lafiya"
Nan suka fita shida nasir wanda shima sae da yayiwa inna sallama kafin suke fita.

Washe gari man ne da Amir a bakin mkrntar su Rynt fake cikin mota sae ga Rynt ta fito gate wacce kai tsaye ta nufi motar drivernta da yazo d'aukar ta yayin da Amir ya kalli man dake kallon Rynt har ta shiga motar suka tafi bae ce komai ba sae jan tashi motar yayi yabi bayan su har suka iso gidan inna,
Rynt da drivernta sam basu lura cewa ana bibiyar su a baya ba.
Wacce koda ta fito motar hnklinta na gun Aamil da ta hango shigar sa gidan riqe da hannun er sa ilham ta kwasa aguje ta shiga gidan tana kiran ilham.

Ba shiri man dake cikin mota ya bud'e gambu motar zai fito Amir ya riqe shi yace"ya kake hkne wae"
Cikin damuwa man ya kalle sa yace"kai baka ga yanda ta kwasa aguje bane bayan ba ita kad'ai bace ka sani"
Yace"its all ur fault da ka mata ciki bayan kasan qaramar yarinya ce"
Rai 6ace yace"abinda zaka ce knn"
Amir yayi er dariya yace"yanzu dae meyasa muka biyota tun daga school har nn nida na d'auka ko da ta fito d'in nn zaka je ka sameta ne kuyi magana amma sae naga kana kallo har wae taje ta shiga mota driver yaja suka tafi baka ce komai ba sae wani biyo su da mukayi"
Man yace"Amir dama fa ina so na ganta ne kawae"
Amir yace"to ya zancen mgnr da muke son muyi da ita ne?
Zan same ta anjima muyi maganar,
A ina knn ?a nn gidan mana ,ta yaya tunda dae kasan yanzu bazata qara yarda ta fito ba,hkne zan sameta ne a d'akinta ,kana nufin cikin gidan zaka shiga knn? Eh ai ba yau na saba ba,hm amma kasan dae idan inna ta ganka baza ku kwashe ta dae dae ba ko, inshaAllah ma bazata ganni ba.
Allah yasa cewar Amir man yace"Amin had'e da jan motar suka bar gurin.
Rynt kuwa tana qwalawa ilham kira suka jiyo da ita har Aamil nn ilham taje da gudu jikin Rynt ta rungume ta yayinda Aamil yayi tsaye d'auke da murmushi yana mamakin yaushe suka san juna ne da har suka saba haka.
Rynt d'auke da ilham ta qaraso gurin shi ta gaida shi ya amsa tare da fad'in ya exam?
Cikin sakin fuska tace"Alhmdlh"
Snn suka qarasa daga ciki yana mai fad'in "yaushe kuka san juna ke da ilham ne?
Tace"ranar ne fa kawae da suka kawo wa inna yini"
Aamil yayi murmushi had'e da jinjina kai don ya tuna rnr har wasa ya gansu sunayi.
A nn Rynt ta fice d'aki da ilham yayinda shi kuma ya nufi d'akin inna yana mai jiyo Rynt dake tambayar ilham Sadiq fa? (cewa da d'an Amir).

Da dare mohd ne ya shigo gidan wanda kai tsaye d'akin Rynt ya nufa koda ya mird'a handle yaji sa gam a rufe ya dafe kai cikin damuwa had'e da kallon qofar inna ya nufi qofar a hnkli cikin sand'a ya leqa.
Da sauri ya shiga d'akin ganin inna bata ciki sae Rynt dake kwance kan bed riqe da littafi a hannunta ta kare fuskarta.
Koda ya qarasa shiga d'akin yaji saukar ruwa a batroom alamar inna na ciki tana wanka yaje gab da Rynt had'e da d'auke littafin da ke kan fuskarta nn yaga ashe bacci take ,
ajiye littafin yayi gefe yana ta kallon fuskarta sae can ya maida duban sa a kan cikinta tare da d'aura hannun sa akai yana shafawa a hnkli Rynt ta motsa had'e da juya kwanciyar ta nn kawae yaji inna ta bud'e bathroom zata fito ya tashi da sauri zai bar d'akin sae kawae makullin motar sa ya fad'i a nn tsakiyar d'akin bae iya d'aukar makullin ba ya fita sbd a lokacin har inna ta fito tana fad'in"waye ne?
"Nine"cewar Amir wanda ya duqa tare da d'aukar makullin ,
inna tace"yau kuma zuwan dare aka min?
Cikin sakin fuska Amir yace" na shigo ne kawae mu gaisa na tafi dan kan hanya nake"
Inna ta washe baki tace"to sannu d'an albarka ai ka kyauta ya Maryam da sadiqu duk suna lfy dae ko.
Yace"lafiya qalau suke"
Tace"madallah" kafin yake cewa" to inna a kwana lafiya zan tafi sae gobe idan na shigo inshaAllah"
Tace"to a gaida gida Allah kai lafiya"
Yace"Amin kafin yake fita.

A wajen gate ya sami man jingine a jikin motar sa ya qarasa gab dashi yana kallon sa yace"u see yanzu da banzo ba fa ya knn kaida kace d'akinta zaka sameta shine ka wani je ka sameta har d'akin inna"
Man dake kallon Amir cikin damuwa yace"Amir ban same ta d'akin ta bane shiyasa"
Da baka same ta can d'in ba ai se ka haqura har gobe ba wae kaje d'akin inna ba,Amir wane irin haquri ka kuwa san irin yanayin da nake ciki ko kuwa don ba kai bane.
A natse Amir ya kai hannu ya dafa shi yace"man duk da bani bane na fhmci irin yanayin da kake ciki sosai amma zan fi so kabi komai a sannu har ka cimma yin nasarar shawo kanta.


Please Login or Register in order to submit comment