Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da niya bane asalima ban san cewa ya mutu ba"
Kaga bashi nake son ji ba ka gaya min ta yaya akayi har ka kashe mata mahaifi?
Ba musu Aamil ya gayawa Abba komai yanda abin ya faru ba tare da ya 6oye masa komai ba har magagin giyar da yake ciki kuwa duk sae da ya gaya mae.
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un shine abinda Abba ke ta furtawa, yayinda ya cire hular kanshi yana fifita ta a jikin sa sbd wani irin zafin bala'i da gumi dake tsastsafo mai ta koina a jikin sa had'e da wani irin ciwo da yake ji ta 6angaren zuciyarsa,
ya dafe gurin da sauri yaje zuwa fad'uwa Nasir da man sukayi hanzarin tarbarsa inda a rud'e suka tafi dashi kan doguwar kujera suka kwantar ,
inna ta tafi cikin rud'u da firgici ta bud'e fridge ta ciro ruwa ta kawo musu suka yayyafa masa.
Amma bai farfad'o ba sae d'aukar sa sukayi zuwa asibiti yayinda man da Amir ne ke kansa har suka samu ya farfad'o suka mai allurai ciki har da ta bacci.
Koda suka fito suka sami inna sae kuka take tana fmn sirfawa Aamil zagi yayinda Nasir ke gefen ta yana ta fmn lallashi wacce tana ganin su Amir sun fito ta nufe su tana tambayar halin da Abba ke ciki nn suka nuna mata ba wata matsala bace dan har ma ya farfad'o sun mai allurar bacci,
a nn ta nemi ta ganshi basu hanata ba suka barta ta shiga tare da Nasir yayinda su ma suka juya zasu bi bayansu sae ga hjyr su da man ya kira tazo cikin rud'u tana tambayar sa abinda ya faru da Abban su,
Man yayi shiru kawae yana kallonta ya kasa ce mata komai sae Amir ne ya bud'e baki yace"umma muje dae kiga Abba tukun"
Bata musa musu ba tabi bayan su suka shiga dan dama ta matsu taje ta ganshi.
Ta sami Nasir ya jawo wa inna kujera ta zauna nn gefen gadon da Abba ke kwance akai.
Ta qarasa ciki tare da gaida inna yayinda ita kuma nasir ya gaida ta ta amsa tana mai kallon Abba dake kwance yana bacci ,
ta sauke numfashi tana ci gaba da kallon sa snn ta kalli su man tace"na tambaye ku tun a waje me yake damun sa baku gaya min ba sae cewa kukayi na shigo na ganshi"
Amir ne ya sadda kansa qasa cikin jimamin baqin cikin abinda zae snr da ita ya d'ago had'e da share er qwallar baqin cikin da ta fito masa ta gefen ido snn ya shiga snr da ita lbrn komai abinda ya faru cikin nuna baqin ciki da damuwa"
Yana gama bata labarin ne kafin tace komai sae Aamil ta hango tsaye a bakin qofar d'akin yazo gab da ita ya durqusa a gabanta d'auke da idanuwan sa da sukayi jajur kan kuka,ita kuwa sae kallon sa take cikin mugun 6acin rae yace"umma ki yafe min,a yau nayi babbar nadamar qin daina abinda kika hana ni wato shan giya da ke kad'ai kika sani sae kuma Amir,kuma kunyi iya bakin qoqarin ku na ganin na daina amma sae na kasa har takai ga na aikata babbar 6arna,wacce tun daga rnr wlh ban sake yarda nasha giya ba umma duk da cewa ban san nayi kisa ba amma ko kad'an banji dad'in abinda ya faru ba a lokacinda hnkli na ya dawo gare ni wanda tun daga rnr nake fmn istigifari a gurin ubangiji na ina neman yafiya a gurin shi,dmn dama tun farko bada niya na fara ba sharrin frnds ne da kuma sharrin shaid'an da har ta kai ga na aikata abinda har mutuwa ta ba zae ta6a kankaruwa ba.
Ya qarasa maganar ne cikin muryar kuka mai qunshe da baqin ciki,
umma kuwa sae kuka ta fashe dashi tace"lallai Aamil ka riga ka cuci rayuwar ka tun farko sae da na gaya maka wnn banzar tabi'ar sam bata dace dakai ba ka daina ta amma kaqi yanzu gashi ka aikata abinda har mu mutuwar mu baza mu manta ba ,ka 6ata mana suna ka wulaqanta mutuncin gidan ku da kaf dangi ma baki d'aya,
shashasha kawae fita a nn in daina ganin ka!

Hawaye ne suka sailalo a hknli kan kumatun sa snn ya kama hanya ya fita d'akin jiki sanyaye.
Nan man ya kama hanya zai fita d'akin, umma ta takadar dashi ta hnyr cewa "ba dai bin Aamil d'in zakayi ba"
man ya girgiza kansa yana kallon ta sbd shi ba inda zae je ba knn gun Ryynt yake son ya tafi.
Bata ce dashi komai ba sae Abba ta kalla da ya soma tari wanda ya bud'e idonsa a hnkli had'e da tashi zaune ,
umma ta qarasa gurin sa tana mai sannu haka ma inna da su Amir duk suka mae sannu yayinda Man yaje ya kawo masa ruwa had'e da masa sannu Abba ya kar6i ruwan yasha.
Bayan ya gama shan ruwan ne ya kalli man yace"Ryynt fa?
A hnkli man ya sadda kansa qasa yace"tana gida"
Nan Abba ya maida duban sa gun nasir yace"je ka zo min da ita"
Nasir yace"to"snn ya fita d'akin wanda ya d'an jima kafin yake dawowa suka shigo d'akin shida Ryynt wacce kallo d'aya zakayi mata kasan taci kuka har na fita rai don duk idanunta sun kumbura sunyi jajur tayi tsaye kawae a bakin qofa kanta qasa ta kasa kallon kowa.
Abba dake kallonta yace"qaraso daga ciki Ryynt"
Cikin tako mai natsuwa ta qarasa gurin Abba wanda ya kalleta da kulawa yace"Ryynt ko kad'an banji dad'in abinda kikayi niyya ba amma kuma banga laifin ki ba dmn babban mai laifi shine Aamil da duk shine yayi silar haddasa faruwar komai ,
ya haddasa miki baqin ciki da quncin rayuwar da kika shiga a matsayin ki na er qaramar yarinya da har yasa kika yi tunanin abinda bai dace dake ba,da hk nake son kiyi haquri ki ajiye wnn tunanin ki bar komai a hannu na dmn nida kaina zan sa a kama Aamil a kuma yanke masa hukunci dae dai dashi ta yanda duk wani mai banzar tabi'a irin tasa bazai ta6a sha'awar aikata abinda ya aikata ba.
Girgiza kanta tayi had'e da share qwallar da suka zubo mata tace"Abba ka barshi,
dama duk a tunani da gayya yayi kisan shiyasa na d'auki wnn alqawarin wanda na d'auki
alqawarin ne cikin baqin ciki da jin zafin yanda aka kad'e Baffana da kuma sanin cewa ko na kai qara a hukuma ba lallai bane abi min haqqina a wnn lokacin kasancewar mu talakawa en qauye da ba'a d'auke mu a bakin komai ba shiyasa amma ni ynx na yafe masa Abba"
Abba ya girgiza kansa yace"ai ba ubanda ya ake sa shan giyar dn hk sae na nuna masa kuskuren sa ta yanda zaiyi babbar nadamar fara shan giya a rayuwar sa"
Ryynt ta sake share qwallar da suka zubo mata tana tunanin hallaci irin nasu tace"Abba dsgke na yafe masa kawai ka barshi"

Abba yace" ko d'aya Ryynt ke yarinya ce mai kirki da mutunci da ya zama dole abi maki haqqin ki kan zaluntar da ya miki,dmn ya zalunce ki mafi zalunta .
Inna ta kama masa sae masifa ita ma take kan lallai fa sae an hukunta shi tun da shi yajawa kansa ba wanda yaja masa.
Ryynt tayi shiru kawai tana sauraren su sae hawaye dake fmn sauka kan fuskarta yayinda taji har ranta mutanen sun qara shiga ranta wad'anda had'i da hallacin da suka mata ne yasa taji ta yafewa Aamil dmn sun cancanci fiye da haka a gurinta sae dai kunyar su da kuma tsanar Aamil da zata zauna a ranta bazata bar ta iya ci gaba da zama tare dasu ba shiyasa ta shiga tunanin suna komawa gida tafiyar ta kawae zatayi ba tare da kowa ya sani ba.

Bayan sun koma gida bayan sllr magrib Ryynt ce riqe da abun hannun man sae fmn juyashi take tana kallo wacce still bata ga sunan da ke jikin abun hannun ba sbd cikin wani salon qawa da ba kai tsaye ake ganewa ba akayi rubutun.
qwallah ne suka zubo zar kan fuskarta sbd ko kad'an bata ji dad'in zargin da ta d'aura akan wanda ba shi bane sai dai baqin hallinsa ne ya janyo tafi zargin cewa shine.
Inna dake tsaye a bakin qofa sae kallon ta take don ita ko kad'an bata ji haushin dalilin zamanda tayi a tare dasu ba sae d'inbin tausayin ta da taji nn ta girgiza kanta kawae ta juya zuwa d'akinta ,ba tare da Ryynt tasan da tsayuwar ta a bakin qofar ba har ficewarta.
Ryynt kuwa tana cikin hkne wayar ta ta shiga qara ta tashi a hnkli ta d'auko wayar taga umman saliha ce mai kiran ,ta d'aga wyr jiki sanyaye dan duk sae ta soma jin kewar su.
Koda ta gama wyr sae hawaye ta shiga sharewa sbd lbr ne yakai kunnen umman saliha na komai abinda ya faru.

Da dare guraren qarfe tara Ryynt ta fito gidan ba wanda ya sani riqe da er viva ledar ta wacce kayan ta da tazo dasu daga qauye ne kad'ai a ciki wato kayan da marigayi anwar ya bata haka ma na jikinta kala d'aya daga cikin su ne ta saka.
Tafe take tana waiwayen gidan cike da jin kewar inna har ta fito gate d'auke da hawayen da ke ta fmn zarya a kan fuskarta ba tare da ta damu da ta share hawayen ba.
koda ta fito gate d'in sae wani irin hasken mota ya sauka kan fuskarta har sae da tayi saurin sa hannu ta kare fuskar tata wacce bata ankara ba sae jin qamshin turaren man taji gab da ita.
Nan ta janye hannun ta da ta kare fuskarta had'e da kallon man dake tsaye a gabanta ta kauda fuskarta gefe snn taja baya a hnkli sbd bata son qamshin turaren sa yana shiga hancin ta sbd qamshin turaren kaita yake ya baro don sae tayi ta son jin kasancewa a jikin sa.

Man dake tsaye yana kallonta kanta qasa ta wani kai viva leda a bayanta ta 6oye yace"ina zaki tafi da daren nn?
Shiru tayi had'e da d'an qara matsawa baya dashi sbd ko magana yayi wani irin qamshin dad'i mai rikitarwa take jin yana fita a cikin bakin sa.
Man ya kalleta kawai yace"da ke nake magana kinyi shiru"
Still shiru ta mai tare da qara matsawa,
shi kuwa yakai hannu zae riqo ta tayi saurin cewa"kar ka ta6a ni bana so"
Wacce tayi mgnr ne cikin sanyin murya yayinda shi kuma ya sauke numfashi yace"to koma daga ciki idan ba so kike na d'auke ki na kaiki da kaina ba"
Cikin muryar kuka tace"ni ka bar ni na fita"
Yace"kiyi me wae idan kika fita"

Bata riga tace komai ba sae muryar inna suka tsinkayo tana fmn qwalawa Rynt kira,
Aamil dake can la6e a bayan su yayi saurin barin gurin wanda yazo ne dmn bawa Ryynt hqr amma kuma yana jin kunyar had'a ido da ita.
Man kuwa a lokacin da yaji muryar inna sae d'aga tasa muryar yayi a natse yace"inna zo gata a nn"
Rynt ta kalle sa rae 6ace don hannunta ya riqo ya kuma jata ya kaita sae gun inna wacce suna had'a ido tayi saurin sadda kanta qasa inna kuwa sae taslima ta shiga yi tana kallon viva ledar da ke hannun Ryynt.

🔮🔮```BAZAN BARSHI BA!```🔮

🔮🔮🔮🔮
*```Page 66```* and 67

Snn ta riqe baki tace"Ikon Allah ashe kuwa hasashe na ne ya tabbata dmn tun da muka dawo daga asibiti na fhmci wani yanayi da ynryr nn take ciki da ya bani cewa tafiya take so tayi,da to idan kin tafi ina zaki je ne iye!ko kuwa a tunanin ki idan kinje qauyen naku zan barki ne banje na dawo dake ba.
Cikin sanyin murya can ciki Ryyñt tace"inna yi haquri"
Inna ta kalle ta kawae taja hannun ta suka je daga ciki yayinda man ke biye dasu.
Falo suka zauna inna ta kalli Ryynt a natse cikin kulawa tace"Ryynh haqiqa na fhmci dalilin da yasa kk so ki tafi ,
a wani 6angaren naga laifin ki a wani 6angaren kuma banga laifinki ba,laifin ki da na gani shine ya muna zaune qalau cikin aminci da juna kice zaki tafi bayan duk irin shaquwar da mukayi Ryynh ,
idan har dan a dalilin zaman da kika yi damu ne ai ba laifin ki bane laifin wnn banzan yaron ne da ba abinda zance sae dai nace Allah isar miki ,
kuma hukunci ya zama dole a kanshi amma zancen tafiya ki bar mu sam bai taso ba ,
idan ba so kike nima na biki mu koma can qauyen naku da zama ba.
ko kuwa kin gaji da zama damu ne Ryynh.
Da sauri Ryynt ta girgiza kanta tace"Allah inna ba haka bane"
Inna tace"to Ryyñh idan ba haka bane ai sae kiyi zamanki muci gaba da zaman mu kinji er albarka"
Ryynt ta gyad'a mata kai inna ta washe baki tace"yauwa er albarka to je maida kayanki a d'aki kinji"
Nan Ryynt ta tashi a natse ta nufi d'akinta.
Yayinda inna ta bita da kallo tana fad'in"wlh yarinyar nn sosai ta kwanta min a rae tun rnr da na fara ganinta kuma har yau ban soma jin ta fita a ran nawa ba,sbd ko yaushe qara ganin hankalinta nake wlh.
Man da duk ynx tausayin Ryynt yake ji da kuma wani irin sonta da ya qara shigar sa ya sauke numfashi yace"shiyasa inna nake son kuyi haquri ku barni na maida ta wlh ina sonta har raina ba wae don abinda take d'auke dashi kad'ai ba"
Inna ta kallesa tace"Hm muhammadu knn ba inda Ryynt zata koma taci gaba da ganin wulaqanci kaji in gaya ma"
Mohd yace"wlh inna ni banada nufin sake wulaqantata"
Inna tace"yo ai kace haka tunda so kake ka maida ta"
Mohd yace" inna ko d'aya ba haka bane na rantse"
Inna tace
"Yo kai ka sani da wani rantse rantsen ka can ai ba yau na soma sanin halin yaran zamani irinku ba"
Kmr zai yi kuka yace"haba inna sae kace ban san muhummancin rantsuwa ba"
Inna dake kallonsa tace"kaga ni duk ka cika ni da surutu je ka sami ubanka kabiru ka gaya mai"
Man ya kalleta a sanyaye yace"shike nn inna zanje amma idan yaqi amincewa zaki sa bakinki dan Allah inna.
Inna tace"bari kaji bafa zanyi ba don ka sani dmn bazan ta6a yarda a had'a hannu dani a cuci marainiyar Allah ba.
Ta fad'i hakane tare da tashi ta bashi guri ba tare da ta tsaya jin me zai ce ba.
Shi kuwa har zai fita yaji yana son ganin Ryynt ya tafi sae d'akinta bai ganta ba tana bathroom ya fito jiki sanyaye yana tunanin ko Abba zai saurare shi idan yaje.
Haka dae ya bar gidan cike da tunani a ransa.

6angaren Aamil kuwa a lokacin da ya fice family house ya tafi da niyyar xuwa gun Abba amma kuma ya kasa shiga gate d'in gidan ko ma nace ko cikin motar sa ya kasa fitowa dan bai san ya zaiyi ya had'a ido da Abba ba sae zaman sa yayi a cikin motar yana ta kuka cike da nadamar fara shan giya a rayuwar sa inda ba kowa ne ya janyo masa haka ba sae frnds d'insa na waje wanda idan yaga suna sha kallon su kawai yake a asararru dan ya musu magana har ya gaji sunqi dainawa sae gashi bai san ya akayi ba daga kallon su har shima ya soma ra'ayi ya fara sha.
Wnn knn.
Bai iya shiga gidan ba dae sae jan motar sa yayi ya koma gidan sa ya sami matar sa wacce tun lokacinda taji labarin abinda ya faru sae kuka take tayi ya bata haquri har ya gaji taqi dainawa sae ma takadar saki da ta nema a gurinsa a cewar bata iya ci gaba da zama dashi a matsayin miji hkn ne ya qara masa damuwa sosai ya rasa ta inda zae sa kansa yaji sanyi.

Washe gari koda aka wayi gari ba Aamil yayi tafiyar sa sae saqon wasiqar sa Abba ya samu ya dawo daga sllr asuba wanda koda ya gama karanta wasiqar sae numfashi ya fitar cikin yananyin damuwa ya shiga gidan ya sami hjyr su man, ya bata wasiqar ta karanta sae kuka don kalamai ne na ban haquri masu karya zuciya kai tsaye.

Koda gari ya gama waye labari yakai gun kowa family don iyaye maza har meeting suka had'a a cewar Abba yayi haquri a nemo Aamil ya dawo gida tun da Ryynt dae ta yafe masa.
Abba ya nuna musu kawai su barshi kan dole kowa ya kama gabansa cikin damuwa dan sunyi sunyi dashi ya kafe kan A'a.
Bayan an watse meeting d'in ne Abba ya kira Amir da mohd a cewar suje gidan Aamil su dawo da matar sa Khadija gida don dama da ita har matar Amir duk en familyn ne wato 'ya'yan Alhj sa'eed qanin Abban Nasir.

Koda man da Amir suka je gidan suka same ta zaune a falo ta had'e kai da guiwa sai kuka take tayi riqe da takadar da ta samu Aamil ya bar mata ta ban hqr.
Lallashin ta suka shiga yi sosai don duk sai ta basu tausayi har dae ilham dake gefen ta itama tana tayata kukan.

Bayan sunzo dasu gida ne Abba ya zaunar da ita ya bata magana ya kuma rarrashe ta sosai har damuwar da ke ranta ta d'an soma rage mata.

6angaren su Ryynt kuwa suma duk sunji labarin tafiyar Aamil dan tun da asuba wani yayi wa inna sallama ya bata takarda a cewar Aamil ne ya bada a bawa Ryynt wanda koda Ryynt ta gama karanta wasiqar sae qwalla ta sami kanta dashi dan itama kalamai ne sosai na ban haquri masu karya zuciya da suka sa ta rage jin tsanar sa sae ma tausayin sa da ta soma ji kan irin hukuncin da yaje yiwa kansa a inda ya tafi ba tare da ya snr da kowa inda yaje d'in ba.

Malika kuwa bazan ce taji labarin ba don tayi tafiya zuwa dubai ita da mahaifiyar ta.

Washe garin rnr da dare mohd ne tafe cikin mota zai tafi family house gun Abba cike da fargaba yayinda yake ta fmn addu'a a ransa na Allah yasa Abba ya amince ya barshi ya maida Ryynt don tun rnr fargaba bata bar yaje ba duk da cewa yanzu kmr kar abubuwan nn su faru yaga Abba ya d'an fara sake mai.

Zaune ya sami Abba a falo shi kad'ai yana sauraren labarai ya sami guri a qasa ya zauna inda cikin ladabi ya gaida shi ,Abba ya amsa ba yabo ba fallasa.
Mohd yayi shiru ya kasa cewa komai sae kansa da ya sadda qasa.
Abba dake kallon sa yace"ya akayi ne?
Cikin inda inda Mohd yace"Abba dama nazo baka haquri ne akan dan Allah kayi haquri ka barni na maida Ryynt wlh bana da nufin sake cutar da ita"
Abba da still kallon sa yake ya numfasa snn yace"mohd sanin kanka ne Ryynt bata son komawa gidan ka kuma ni baxan ta6a tursasa ta akan abinda bata so ba don haka sae ka tashi ka bani guri"
Cikin marairaicewa mohd yace"Dan Allah Abba kayi haquri kasa bakin ka inshaa Allah zata yarda ta koma"
Abba yace"Da zaka saketa kayi shawara da ni ne da har kake tunanin xan saka bakina akan ta koma,to bari kaji ni bazan yi wnn ba dmn Ryynt ba jakar gidan ku bace da zaka daka ka kuma d'aura mata sharri had'i da saki ka kuma yi tunanin zan saka bakina akan ta koma gidan ka sam ba zai ta6a yiyuwa ba .
A nn mohd yayi shiru cikin damuwa sosai sae can yace"Abba dan Allah kayi haquri wlh inshaa Allah hkn baxai sake faruwa ba nayi alqawari.
Abba ya girgiza kansa yace"kaga tashi ka bani guri kuma kar na sake ganin qafar ka a nn gidan da sunan wnn mgnr"
A nn fa idanun mohd suka kad'a sukayi jajur ya kasa tashi ya kuma kasa cewa komai.
Abba ya tashi zai bar gurin mohd ya kalle sa inda cikin murya mai d'auke da tsananin damuwa yace" Abba dan Allah kayi haquri ka bani dama ta qarshe "
Abba ya tsaya ya kalle sa snn yace"naji kaje ka sameta kuyi magana idan ta amince to idan kuma bata amince ba wlh wnn kai ka sani"
Cikin jin dad'i sosai mohd ya d'ago yana kallon Abba ya masa godiya snn ya tashi da hanzarin sa ya fita.
Abba kuwa koda ya juya sae umma ya gani tsaye gun staircase wacce tun lokacinda mohd ya shigo take tsaye a gurin tana jin duk abinda suke fad'a.
Ta kalli Abba fuskar ta ba yabo ba fallasa sae dae kuma bata ce komai ba har ya ra6a ta gefen ta ya wucewar sa xuwa d'aki ita ma dae hkn ta koma d'aki abinta.

Mohd kuwa da fitar sa kai tsaye gidan inna ya nufa ya sami falon ba kowa ya qarasa d'akin inna had'e da sallama,ya sami inna na shaf'i da wuturi,
ya nemi guri kan sofa ya zauna yana mai kallon Ryynt dake kwance kan gado sae sharar bacci take abinta.

Bayan inna ta idar da salla ne suka gaisa snn mohd ya gaya mata yanda sukayi da Abba.
Inna tace"shike nn ai sae ka tuntu6i Ryynh d'in kaji sae dai kuma yanzu kaga bacci take"
Yace"haka ne sae gobe da safe idan na dawo"
Inna tace"da safe fa kasan makaranta take zuwa"
Yace"wae basuyi hutu bane har yanzu?
Inna tace"ai gobe ne hutun nasu don sun gama jarrbawa tun ba yau ba.
Yace"shike nn Allah taimaka inna tace"Amin"shi kuma ya tashi ya fita had'e da yi mata sae da safe"
Inna ta bisa da ido har ya fita snn ta kalli Ryynt dake kwance tana bacci ta kauda idonta takai dubanta gun ledar da Mohd ya ajiye mata da zai fita koda ta duba daqwalen kaji ne guda biyu gasasshi da hollandia yogurt wanda ya siye su ne kan hanya da zai zo.

Washe gari cikin farin ciki Ryynt da ta dawo daga school tana shigowa falo ta fad'a jikin inna tare da nuna mata result d'inta da tazo ta d'aya.
Washe da baki Inna ta kar6i result d'in tana ta murna tana sa albarka.

Mohd da shigowar sa knn ya kar6i result d'in yana kallo d'auke da murmushi a fuskar sa ya kalli Ryynh yace"sosai kinyi qoqari Allah qara miki basira"
Inna tace"Amin yayinda Ryynt ke gaida Nasir da kusan tare suka shigo shida mohd wanda shima ya kar6i result d'in cikin murna yace"MashaAllah kinyi qoqari sosai gaskiya Allah yasa ki d'ore da hakan"tace amin tare da sadda kanta qasa tana wasa da en yatsunta yayinda man keta kallonta sae son yake su had'a ido amma ita bata ma kallon gefen sa,
yana kallo ta ficewar ta d'aki shi kuma yayiwa inna sallama ya fita wanda dama akan ta kad'ai ya shigo gidan yaga idan ta dawo sbd yaje school d'in su d'aukart bai same ta ba.

Bayan awa d'aya da faruwar haka ne Ryynt ce ta fito daga kitchen ta wanko agwalimarta cikin bowl sae ga saliha ta shigo gidan ihun murna Ryynt ta

Please Login or Register in order to submit comment