Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ku d'aki ne?eh har ma da sarkin kd duk ni ke gyara musu d'aki,da sauri ya kalleta sbd su asalin en kd ne yasan agun inna taji, baqa ta masa kenan,yace"ke ina wasa dake ne? um um kaidai ka nemi na maka haka amma ni ba halina bane raina wanda ya kama girmansa,d'an fari da ido yayi sae kuma yayi murmushi yace"to naji a wuce gun ga wnn ladan gyara min 6angare na da kikayi,Rynt ta kalli kud'in da ya ajiye gabanta zasuyi 20k tace"nayi dan Allah ne ba don wani abu ba"
Eh na sani ai kyauta ce na baki.... Kyautar ce bana so ,ya d'ago da d'an mamakinsa sae kuma ya basar yace"to me kike so? Har tayi niyyar saka mai wata maganar sae kuma ta fasa ,tace"waya nake son nayi da inna"
Ga mamakinta sae ya ciro waya a aljihunsa ya kira mata inna ya bata, bata san lokacinda murmushi ya su6uce mata ba ta kar6i wyr ta kwasa da gudu zuwa d'aki, mohd kuwa binta yayi da shu'umin murushi yayinda a ransa yake mamakin raina sa da tayi.

Duk abin nn da suke Abba na kallon su sae ya musu wata fahimta ta daban wacce tasa yaji dad'i har ransa,
da saukowa zai yi amma ya fasa ya juya zuwa d'akin umma ,
ganin yanda yake murmushi yasa ita ma ta shiga murmushi tace"yadai Alhj?
Sai da ya zauna snn yace"zauna tukun"
nn kusa dashi ta xauna.
Yayi gyran murya snn ya fara da cewa" haqiqa tun zuwan Rynt a gidan nn na yaba da hnklnta da kuma natsuwarta har hakan yasa na kwad'aitu da son ace ta zamo cikin wnn family namu ma'ana ta kasance suruka a gidan nn mata ga mohd.

Billy giro๐Ÿ˜Š

๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ
๐Ÿ”ฎ```BAZAN BARSHI BA! ```๐Ÿ”ฎ

_1/06/2017_

๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ
_*page*_ ```20```

Zumbur umma ta miqe tace"haba Alhj! ni na d'auka ko zancen arziqi ne zanji ashe na tsiya ne.... Kina da hnkli shi zancen aure ne na tsiya...yo zancen tsiya man idan ba haka ba meye had'in mohd da wnn yrnyr er matsiyata er qauye ga 'ya'yan manya a gari,haba dan Allah! ,dan Allah Alhj ni ka ma daina wnn zancen.
Baxan daina sa ba kuma aure tsakanin mohd da Rynt kmr anyi an gama ne, ai bake keda iko dani ba haka shima ba ajiye ni yayi ba da ko yaushe na masa zancen aure se yace tukuna sbd ya maida mutane en iska shasha.... Amma alhj tsakani fa da wnn cutar dashi kake sonyi ai gwanda ya zauna ba aure da ace wnn yrnyr ce matar sa sae kace bakin uwa a rasa wacce za'a ce ya aura sae ita haba dan Allah!
Mtsw sae yau na fhmci rashin hnklinki ne kika yarfawa 'ya'yanki da kaf famlyn nn ba wanda yayi rashin mutuncin su ,na dai ji amma nikam sam bazan yarda da wnn zancen ba don wlh bazata sa6u ba wai bindiga a ruwa.

Fuuu!Abba ya fita yana mai fad'in"tsakanin ni da ke sae aga wanda keda iko akan wani .
Bai zarce koina ba sae downstairs ya samu still mohd na kan cin abinci
yace da mohd idan ka kammala cin abincin ka same ni a d'aki.

Nn take mohd ya kammala cin abincinsa yaje ga kiran Abba.
Abba ya kalli mohd da ya nemi guri ya zauna a qasa yace"mohd ina son ka saurare ni da kyau kaji,kuma bana son kazo min da wani shashanci, zancen auren ka shin har yanzu baka sami wacce ta maka bane ko yaya? Aa Abba dama malika nake jira ta kammala karatun ta kuma ta kammala yanzu ni a shirye nake inshaAllh, Abba yayi shiru na tsawon lokaci can yace"er gidan wacece ita malika? ba wani bane Abba sananen mutum ne wato Alhj ilyas na Allah..... Alhj ilyas na Allah ,yace"eh Abba da wata matsala ne? Abba da yayi shiru yana mai nazari yace"Aa ba komai jeka"
Cikin farin ciki mohd ya fito ya sami Rynt ta fito kenan tana neman shi.
Yayi tsaye daga inda yake har ta qaraso gurin shi ,ba yabo ba fallasa ta miqa masa wyr tare da fad'in"ngde" snn ta juyo tayi ficewarta.

Bayan kwana biyu da faruwar haka ne Abba ya sake kiran mohd.
Yace"mohd a gsky zancen aurenka da wnn yrnyr malika sae dai nace kayi haquri sbd ba er mutunci bace kwata kwata shiyasa tun lokacin da ka snr dani waye mahaifinta na shiga nazari dmn nasha jin cewa baya ganin kowa da mutunci,sae gashi kuwa da mukaje hakane ta faru damu,dmn wasu banzan sharudda ya shiga snr damu kan auren ka da er sa wad'anda sam hnkli ba zai d'auka ba,don haka tunda ersa ba er gwal bace ka haqura da ita.
Mohd da tun lokacin da Abba ya fara zancen sa yaji zufa na karyo masa.
cikin rawar muryar yace"Abba malika yarinya ce mai mutunci kayi haquri kabar ni na aureta tunda ba cewa yayi bazai bada aurenta ba"Abba ya kalle sa kafin yake cewa
"wae mohd ka koji irin maganganun da yake fad'a ne da kowanen mu sae da ya fito cikin 6acin rai wai ace hatta mahaifinku sa'eed da Allah yayi masa sanyin hali matuqa sae da yayi magana kan rashin mutuncin Alhj ilyas na Allah,
gaskiya da sake don nikam baza ka kwaso min er gidan Alhj Ilyas na Allah ba ,koda kuwร  ace ita kad'aice 'ya a duniya tofa sae dai ka hqr don baza ka aureta ba.
Komai mohd bai iya cewa da mahaifinsa ba sbd gabad'aya lissafi ya kunce masa .
Abba yace"gaka mohd ina wnn yrnyr Rynt er gidan inna? eh Abba ,to na yanke hukunci zan aura maka ita don wlh ta kwanta min arai kuma inaji a jikina ita alhairi ce a gare mu, cikin tsananin mamaki ya kalli Abbanshi yace"Abba wnn yrnyr fa kace"
eh wnn d'in nn itafa Rynt ba.....ina Abba wlh ni bazan iya aurenta ba kawai dai ka bani dama wlh zan saisaita tsakanin ku da Abban malika, hm mohd kenan kaje dai kayi nazari akan aurenka da Rynt amma malika kam sae dai ka haqura da ita.
Tashi ka bani guri!

Da qyar mohd ya iya tashi ya bar gurin don gabad'aya jikin sa ya mace.

Ya tafi 6angaren sa cike da tunani kala kala a ransa ya zauna kan sofa tare da dafe kansa ,can kmr wanda aka tsakura ya zari makullin motar sa ya fita.


Wani katafaren gida ya nufa yayinda anguwar ta kasance very cylent ,ya parkar a bakin gate d'in gidan snn ya d'auko waya ya kira malika ,yana gama wyr ya d'aura kansa kan sitari ba jimawa sae gata ta fito cikin wani banzan dressing awa arniya ,kyau kam ba laifi akwaishi haka ma qirar jiki Alhmdlh kamar ita tayo kanta.
Cikin isa da yanga ta shiga motar tare da fad'in "my man ya baka shiga ciki ba ka tsaya a nn kmr wani baqo?
Mohd ya d'ago yana kallonta da idanuwansa da suka rine zuwa ja,yace cikin harsh voice"malika meyasa mahaifinki zai mana haka!"ta kauda fuskar ta gefe inda cikin sanyin murya tace"kayi hqr my man wlh nima banji dad'in abinda Abbana yayi ba,kasan hlin Abba sae a hnkli ,ba kace ga wanda yake mutunci dashi ba kowa ciwa mutunci yake..... Gud! ai gashi yanxu ya jamana baza mu auri juna ba ....ta zaro ido tare da fad'in "haba my man me yayi zafi haka? Sae da ya watsa mata mugun kallo kafin yake cewa"hln su iyayena duwtsu ne ko kuma basada zcy a qirji da Abbanki zai gaggaya musu maganganu ransu bai 6aci ba!,calm down my man sharudda ne fa ya kafa musu ba maganganu ya gaggaya musu ba,wane sharudda ne wai?tayi shiru tana kallon shi ,yace cikin d'aga murya "ki gaya min mana!kukan shagwa6a ta fashe masa dashi tace"nidai kayi haquri ba sae kaji ba wlh ba dad'in ji kuma don Allah ka ajiye zancen ba aure tsakanin mu wlh i cnt be wit a u,
yace"malika ke da sauqi ma shin kinsan chakwakiyar da nake ciki ma ta had'ani aure da ake shirin yi da wata banza can er qauye !
A rikice tace"bangane ba"baza ki gane ba kam tunda mahafinki ya 6arar mana da lissafi.
Ta wani marairai ce fuska tace"don Allah kamin bayani wlh ban fhmta ba"yace"malika Abbana ya hana min aurenki sbd zafin abinda Abbanki ya musu shine har yake qoqarin had'ani aure da wata kucaka,Komai kasa ce masa tayi sae kallon sa take hawaye na fmn zarya kan kumatun ta yace"take it easy don ko mutuwa nake bazan auri wnn yrnyr ba,abu d'aya nake so dake yanzu shine kisan yanda zakiyi Abbanki ya bawa iyayena haquri ya kuma janye banzayen sharuddansa to idan kika yi haka inshaAllah Abbana zai haqura.
Share hawayenta tayi tare da fad'in"shikenan my man inshaAllah i will try my best"

Kusan kwana hud'u amma malika ta rasa ta yanda zatayi ta shayo kan mahaifinta don ta sanshi kaifi d'aya ne in ya fad'i abu tofa shikenan.

Mohd kuwa kullum bayada aiki sae na roqon Abbansa kan yayi haquri ya janye aurensa da Rynt amma sam yaqi .
Rynt kuwa kwata kwata bata ma san da zancen ba ga soyayyar ta da munir sae abinda ya qaru wanda yanzu munir jiran dawowar inna kawai yake dmn ya snr da ita abinda ke tsakanin sa da Rynt ya kuma snr da ita yana so zai aure ta.

Mohd ne durqushe a gaban iyayen shi kmr kullum yazo bada haquri a janye zancen aurensa da Rynt Abba yace"bafa zan janye ba idan har kaga na janye tofa lallai inna ce ta buqaci haka"haba Alhj gaskiyar magana kana son takura yaron nn ai kasan halin inna zama d'aya take amincewa da duk wani zancenka,kawai kar ma ka snr da ita zancen nn dan Allah ka bar yaron nn ya auri wacce yake so...na barshi ya auri wacce ya keso ai inace kinji abinda uban nata ya mana wae har mu yake cewa yaji ya amince zai bada er shi ga d'anmu amma fa mu sani shi er shi ba tunkiya bace ko akuya da zata je tana haifawa d'anmu 'ya'ya barkatai kmr yanda yake ganin a familyn mu ana haifo mana 'ya'ya hkn nn ba tsari,shi a tsarin sa bazai wuce ace ersa ta haifawa mohd 'ya'ya biyu ba idan ba haka ba tofa sae dai d'anmu ya haqura da ersa,wnn wace irin magana ce babu dad'in ji snn har kike tunanin zan amince na had'a surukuta dashi.
To Alhj sae akace don ya fad'i tsarin sa shi zai sa dole abi ,muradi kawai ersa ta shigo hannun mu ,mu kuwa sae yanda mukayi da ita tunda ta rigada ta dawo a qarqashin ikon mu..... Sam bazan yarda da auren da za'ayi ana dinga ci min mutunci ba, dmn nida shi ba wanda zai nunawa wani kud'i ba kuwa zai zo yana dinga nuna min iko ba don kawai d'ana yana auren ersa!
Cikin damuwa sosai mohd yace"don Allah Abba kayi haquri wlh a guna ba matsala ai yara biyun ma sun ishe mu jin dad'in rayuwa.....kul!na qara jin zancen nn ya fito a bakin ka!kuma maganata ta qarshe shine ba zan janye aurenka da Rynt ba wlh,sae idan ita Rynt d'ince ta furta da kanta cewa bata sonka, kuma ko bayan raina ban yafe maka ba idan ka auri malika!

Billy giro๐Ÿ˜Š

๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ
๐Ÿ”ฎ```BAZAN BARSHI BA! ```๐Ÿ”ฎ

๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ
_*page*_ ```21```

Amma Alhj Allah ya isa tsakanin mu dakai don wnn cutuwa ce wlh!
Cikin nuna fushi Abba ya nuna ta da yatsa yace"wlh Rabi'a ki kiyaye ni da banzan kalaman nn naki dake shirin janyo miki mutuwar aurenki!
Gama fad'ar haka ya tafi kmr wanda zai tashi sama.
Umma kuwร  ta bishi da kallo ta6e da baki tace"indai wnn kalmar ce ba yau na saba jinta a bakinka ba bare ta tayar min da hnkli,snn ta kalli mohd da ya shiga cikin tsaรฑanin tashin hnkli tace"kaga kwantar da hnklinka aurenka da malika kmr anyi an gama kuma baza ka auri wnn er qauyen ba indai ina numfashi a doron qasa,kmr wanda zai yi kuka yace"umma ta yaya kike ganin hkn zai yiyu bayan kinaji Abba rantsuwaa yayi kawai ma umma dan Allah ki daina sa bakin ki a zancen nn sbd ko kad'an banji dad'in yanda Abba ya sako rabuwar aure a zancen nn ba .... Yo ai ba yau ya fara ba kuma dan ya rantse sae me! Kaidai tashi ka tafi kawai ai er iskar yrnyr zata dawo daga islamiyya ta sameni.....Aa ki barni da ita kawai umma ni nasan yanda zanyi da ita....ai da ka barni da ita wlh...No umma bana son kwata kwata wani abu ya had'aki da ita ne bare ta raina ki.

6:00pm
Rynt ce tafe kan hnyr dawowa islamiyya ita da munir sae er fira suke mai cike da nishad'i yayinda Rynt ke d'an duba kan titi ko zata hango napep.

Kmr daga sama ta hango motar man tafe ya zo gab dasu ya tsaya kmr mai shirin taka musu qafafu don tsirif ya rage har sae da sukayi saurin ja da baya.
Dukkan su da mugun kallo ya fito yana binsu dashi,yace da Rynt shiga mota"kallon sa ta tsaya yayi ya daka mata tsawa yace"shiga mota nace!cikin 6acin rai taje ta shiga motar ya zagaya ya shiga yaja motar a tsiyace had'e da bazawa munir qura.

Tafiya yayi da ita mai nisa snn ya samu guri ya parker ya kalli Rynt da tun lokacinda yaja motar gabanta ke dukan tara tara kaddai ace ya gane ko ita wace ce,yace"oya cire wnn baqin abun dake kan fuskar ki magana nake son zanyi dake"
Ba musu ta yaye niqab d'inta ba tare da ta kalle sa ba.
Sae da yakai hannu ya d'ago fuskarta yana kallonta shaye da toka snn yace"abu zan nema agunki wanda ban ta6a nema agun kowa ba wato alfarma, alfarmar itace ina son dan Allah idan Abbana ya kiraki ya tambaye ki ko kina sona kice masa A'a shine kawai ni kuma idan kika min haka nayi miki alqawarin duk wani abu da kike so a rayuwa ki tambaye ni zan miki shi koma mene ne kuwa"amma wlh kar ganin na had'aki da Allah ki raina min da wayo dmn duk kika yi gigin amincewa buqatar Abbana sae dai a nemi wata bake ba!
Manyan idanuwanta farare tas take ci gaba da kallon shi dasu snn ta ta6e baki tace"ai sae ka fayyace min komai ta yanda zan fhmta"
Mugun kallo ya watsa mata yace"daqiqiyar inace ke da bazaki fhmta ba ,da Allah ni ftr min daga mota kuma wlh ki tabbatar kinyi abinda na saki!
Ba musu kuwa ta fita motar don yanda taga yanayinsa ko tura ta zai iya yi ta fad'i, sae dai da gani akwai mgnr da takeyi a ranta haka kuma akwai nazarin da takeyi shi kuma mohd har lokacin kallon takaici yake mata snn yaja motarsa a tsiyace ya bar gurin.

Da qyar Rynt taga ta sami napep sbd yanayin anguwar da ba kwaramniya bare abin hawa ya yawaita.
Nazari take yi kam har ta isa gida ko kuma nace har akayi sllr isha'i bata daina nazarin ba yayinda tuni zuciyarta ta ganar da ita abinda ke shirin faruwa sae dai taqi bawa kanta damar amincewa da hkn har sae Abba ya kirata tukun taji koma mene ne.

Tana gama cin abinci Abba ya aiko Ameera yana son ganin ta.
Taje ta same shi shi kadai zaune a falo.
Ta nemi guri a qasa ta zauna ta kuma gaida shi cikin ladabi kmr koyaushe.
Cikin sakin fuska ya amsa snn yayi gyran murya yace"Rynt haqiqa duk mutumin da ya zauna dake zai yi sha'awar kyawawan halayenki da kuma d'abiunki,a dalilin hakane ma yasa nayi sha'awar had'aki aure da mohd,amma kuma ba dole sae idan kina ra'ayi kuma dan Allah kar ki 6oye komai a ranki,dmn ita rayuwar aure wata sabuwar rayuwace da ta banbanta da kowace rayuwa wacce dad'inta ka auri wanda kake so yake sonka, shiyasa nake son ki snr dani gskyr abinda ke ranki ma'ana idan ba kya ra'ayin auren ki da mohd kar kiji shayin komai ki snr dani idan kuma kina ra'ayi sae dai nace Alhmdh dmn zanfi kowa farin ciki da haka.
Tun farkon fara zancen sa ba qaramin girgiza Rynt tayi da jin zancen ba amma sae ta dake bata yarda ya fhmci halinda take ciki ba.
Bata son mohd bata kuma jin zata soshi har abada!amma kuma ko don ta d'auki fansarta a sauqaqe zaisa ta amince da aurensa to kuma ya zata ce da yaya munir dake matuqar son ya aureta.
Duk a cikin ranta take wnn tunanin ,Abba ya katse ta da cewa ke nake saurare Rynt ,sae da ta qara sadda kanta qasa snn tace"na Amince Abba zan aure shi"Abba yace "kin tabbatar Rynt ba cutar kanki kikayi ba? eh wlh Abba har raina na amince.
Wani irin dad'i Abba yaji har ransa, yace"Allah yayi miki albarka Rynt, ya kuma sa ki gama lfy da duniya"da qyar ta iya cewa amin kan kukan da ke qoqarin zo mata sbd tuna baffanta da tayi da kusan kullum sae yayi mata irin addu'ar nn.

Koda ta koma d'aki ba kowa sae tayi kwance abinta tana ta kukan tuna Baffanta har sae da tayi mai isarta snn ta tashi tana tunanin me zai faru idan mohd yaji ta amince da buqatar abbanshi ko ita ma kasheta zai yi kmr yanda ya kashe mata Abbanta.

๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ
[ 1/8/2017]
๐Ÿ”ฎ```BAZAN BARSHI BA!```๐Ÿ”ฎ

๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ
_*page*_ *```22```*
Don tasan a rashin imaninsa zai iya aiwatar da abinda ma yafi haka in akwai, amma kuma bari taga shin me yake nufi da sae dai wata ba ita ba.
Abba kuwa da mohd har umma ba wanda ya kira cikin su bare ya snr dasu yanda sukayi shi da Rynt kawai ya yanke hukunci sae inna ta dawo su yanke shawara shi da ita asa rnr aure.

washe gari hnklinta a kwance tayi shirinta na islamiyya ta fita.

Ko minti 5 batayi da fita ba inna ta dawo daga qauye kuma a nn gidan ta sauka sae murna ake da dawowar ta yayinda ita kuma ta matsu taga Rynt nn Abba ke snr da ita ai ta tafi islamiyya.

Bayan inna taci abinci ta d'an huta Abba ya shiga snr da ita shawarar da ya yanke kan zancen had'a mohd aure da Rynt har yanda sukayi da Abban malika duk sae da ya snr da ita.
Sosai inna tayi murna ba kad'an ba haka kuma itama bata bada goyon bayan mohd ya auri malika ba wanda duk zancen nn da suke yana kunnen hjyrsu mohd wacce tana gama sauraren kaf abinda suka tsara ta koma d'aki cike da masifa ta kira mohd a waya ta snr dashi tace"ga irinta nn sae da nace kbr ni da yarinyar nn ni nasan yanda zanyi da ita wanda ko da kuskure baza ta yarda ta amince da zancen Abbanka ba wlh, amma kace a'a wae kar ta rainani ,raini duk ya wuce ace kmrta baqauya er matsiyata ta had'a surukuta dani,mohd yace"yanzu umma kina nufin duk yanda nayi da ita ta amince da buqatar Abba? Hm!na nawa kuma gashi har sun tsara anjima da dare iyayenka zasu tafi gidan inna asa ranar aurenku!ai wlh kayi wa kanka!don yanzu sae kasan yanda zakayi ka ftr da kanka ko kuma ka nemi wata uwar don muddin ka rasa mafita har takai ga an aura ma ita tofa bani ba kai tunda tun farko sae da nace kabarni da ita kaqi.
Daga haka ta katse wayar sae huci take
tace"in shi mai hnkli ne ko islamiyya baxata dawo ba sae dai wata ba ita ba amma bari nasa ido naga ko dabara ta tayi!in yaso ni kuma na tayasa da wani aikin ta yanda baza ace dasa hannun mu kan 6acewar ta ba.

Mohd kuwa hjyrsa na kashe waya ya rasa ta inda zai sa kansa kan baqin ciki da kuma tunanin hukuncin da zai yiwa Rynt.
Ya zama dole yaje ya jirata kan hnyrsu ta islamiya don yau sae ta fad'i wanda ya aiketa .

Yana fita da motar sa yayi kici6is da Malika ta parker motar ta ta fito, dole ya tsaida tasa motar ya fito yaje gab da ita ya tsaya yana mata wani irin kallo,ita kuwa ta wani langwa6ar da kanta snn tace"my man wai ya ake ciki ne tun jiya da mukayi waya naji shiru har yau "
yace"to shine zaki wani biyo ni har gida da kuma wnn banzan dressing d'inki salon Abbana ya ganki yace bakida kamun kai kuma,in yaso Komai ya qara cakud'e mana! Kayi haquri my man wlh banda wasu kaya sae ire iren su kuma ka sani,to me ya hana ki kirani a waya muyi magana? Ina mgnr zata yiyu a waya nida kwata kwata daren jiya ban samu nayi bacci ba,amma malika kinsan bana son damuwa koma mene ne ai zanje na sameki har gida,kayi haquri na damu ne sosai ,tayi mgnr cike da qwallah tap a idonta, yayi saurin cewa"shikenan kar kiyi kuka gaya min me kike so yanzu?so nake ka gaya min abinda ake ciki ,ajiyar zuciya ya sauke snn yace"wnn yrnyr ta lalata mana komai don ta amince da buqatar Abba snn kuma Abbana har yanzu dai yana kan bakarsa na bazan aureki ba,amma kar ki damu zan shawo kan matsalar komai inshaAllah ,matsalata d'aya yanzu shine anjima za'a sa rnr aurena da wnn yrnr shiyasa at all kaina ya kunce bansan ma wane hukunci zan yanke ba, ga umma ta sani cikin wata chakwakiyar wae bani ba ita idan ban nemo mafita ba har akayi aurena da wnn yrnyr.... Wae da kana nufin zaka yarda ayi auren ne to! Malika uba ba abin wasa bane idan kuma ya yanke hukunci ba yanda za'ayi kuma ya rantse cewa in ta amince tofa shikenan ba fashi aurena da ita, but my man be wise mana,idan ba yrnyr ai ba auren shike nn dole Abba ya haqura, aikin hnkli dai malika ina mai gaya miki 6atar wnn yrnyr tmkr tsinuwace na jawa kaina don dole Abba yasan nine, kawai dai zan aureta amma na d'an wani lokaci .....Wlh! my man bari kaji in gaya ma ba maccen da ta isa ta aure ka bayan ni don ka ma daina wnn sa6on!daga haka taja motar ta a tsiyace ta bar gurin.
Har zai shiga mota sae ga kiran Abba yana son ganin shi,dole ya juya ya tafi ga kiran Abba.

Yau Rynt ita kad'aice kan hnyr dawowa islamiya sbd da safe munir bai cika zowa ba sae da yamma.
Tana cikin tafiyar ta har takai titi zata tsaida napep sae ga wata tsaleliyar mota ta tsaya a gabanta.
Malika ce ta fito daga motar taje gab da Rynt tare da kai hannu ta yaye mata niqabi,nn malika ta yamutse fuska kmr wacce taga kashi tace"hm rainin wayo wai kece ke shirin shiga tsakani na da my man,ta nuna ta da yatsa snn taci gaba da cewa" lemmi tell u 1 thing ruwa ba sa'ar kwando bane haka kuma ramin kura ba gurin shigar akuya bane,a bisa yanda ma na fhmta kwata kwata tsabar talauci ne ke d'ibar ki da haka zan taimaka miki na baki check ki rubuta duk iya kud'in da kike so after that ki sani inda dare ya miki ma'ana kwata kwata ki 6acewa duniyar mu ki tafi can taku duniyar ta matsiyata wnn umarni ne dmn in kika sake kika dawo gare mu wlh sunanki gawa!
gama fad'ar haka ta zaro cheque da biro ta miqawa Rynt ,sae kuma tace "koda yake nasan duhun kai na tattare dake

Please Login or Register in order to submit comment