Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

*MASARAUTAR MAYU!*


*WRITING AND STORY*


*UMMUH HAIRAN*


*MARUBUCIYAR*
👇🏻
AMINIYA KO KISHIYA
HABIBULLAH
QUEEN FARHA
GIDAN UNCLE
ADANDI
WACECE NI
AURAN BAZAWARA
DHOOM ISHAQ
MATAR LAMEER
DUBAI
AND NOW👇🏻
MASARAUTAR MAYU!


*P 1-2*


Farfajiyar gdan sarautar cike yake maqil da mutane da aljanu harma da wasu halittu Dana kasa fahimtar menene, tambura ne algaitu da bushe bushe suke tashi a kowacce kusurwa ta masarautar.
Wani bangare da naga kowa ya mayar da hankalinsa nima nan na nufa na kurɗa na kutsa na shiga tsakiyar taron mutanen dake gurin, ai bankai ga qarasawa ba naji fitsari ya qwacemin saboda sabuwar masifar da idanuna suka ganemin.
Ba komai bane face wani gunki girke tsakiyar filin wanda girmansa ya kere misali, sake ja nayi da baya ba girmansa ne yake kadamin hantar ciki ba aa yanda wangamemen bakinsa yake budewa yana aman jini da wuta a lkc guda shine yafi girgiza imanin ruhina, ban gama shiga wannan tantamar tashin hankalin ba naga wani shirgegen tsuntsu me kama da hankala ya fado tsakiyar filin tik, tare da daga bakinsa sama ya fara wani irin kuka me tayar da tsigar jiki.





Gani nayi kowa dake gurin yana faduwa qasa sumamme kafin wani lkc gurin yayi fetal babu wata halitta me numfashi ciki kuwa har Dani,
Shudewar wani sa'o'i da bazasu wucce uku ba kowa ya fara farfadowa dukkanmu muka tashi tare da yiwa wannan gunki sujjadar girmamawa.
Wata murya ce me amo da hargowa ta fara mgn kamar haka “Sanhu Sanhu ya shugaban allolin duniya haqiqa mun fuskanci matsin rayuwa ta hanyar yunwa qishirwa da fari haɗi da mutuwar dabbobinmu wanda mun sani a duk lkcn da wannan abu ya faɗo cikin birnin Jawal, to shakka babu akwai wata mummunar qaddara da take tunkaromu wanda kake kangemu daga gareta ya shugaban allolin duniya shakka babu cikin qaddarorinmu akwai abinda ya fusata shugabanmu...."
Wata kururuwa gunki Harsan ya saki wacce ta sanya kowa zubewa muka rinqa juyi a qasa, ita kanta qasar girgiza takeyi tana darewa wasu bishiyun suna shigewa cikin qasa.




Dakatawar wannan hargowar yasa wata iska me qarfi tashi tayi sama da wata yar qaramar halitta ta nutse cikin gajimare, iskar ta shude kowa ya miqe ya tsaya cak tare da daga kansa sama,
An dauki kusan rabin saa kafin mu jiyo wani qugi ya fara tunkaro tsakiyar birnin kowa ya toshe kunnensa tare da runtse idanunsu abin ta'ajibi manya da yara maza da mata kowa sai kayan jikinsa ya fara sabulewa suka tsaya tsirara haihuwar uwarsu suka fara gabatar da rawar Jawaleey



BIKIN JAWALEEY wani bikine na al'ada da ake gudanarwa a masarautar jawal wanda ya samo asali tun farkon kafuwar masarautar shekaru dari tara da suka shude,
Wannan biki ba qaramin shagali ne a gurin al'ummar wannan birni ba dama maqotansu na kudancin Bahrain saboda saboda kasancewarsa bikin sheqe aya sannan bikin masoya Kuma bikin nuna bijintar kowanne mutum da irin baiwar maitarsu ta gado tun kakanni.
Sukanyi kwanaki bakwai suna gudanar da wannan shagalin biki ta hanyar kade kade da bushe bushe yammata da samari zasuyita rawa da juyi tsirara dasu, a wannan biki abinda yake bambamta tsakanin matar aure da budurwa guda dayan, matar aure zata sanya baqin qyalle ta rufe al'aurarta sannan zatayi zanen kudan zuma a saman nononta.



Ita Kuma budurwa zata sanya wani jan ganye a saman kan nononta sannan zata sanya jan qyalle ta rufe gabanta, wannan jan ganye da aka lika mata a kan nononta shine yake nuna ta isa aure saboda haka yammatan zasuyi ayari su rinqa zagawa a cikin garin suna raye raye da kade kade, fa'idar hakan shine a wannan zagayen ne idan yarinya taje gaban saurayin da Gunki Harsan ya zaba Mata a matsayin miji wannan ganye da suke Kira sutura zai fadi a gabansa koda ace sunkai su dari shi wannan saurayi shine zai fara ganin faduwar ganyen to yana ganin haka zai taso ya cire kamfen daya rufe gabansa dashi ya sanya Mata ya rufe mata qirjinta shikenan sai a daukesu akansu gaban gunki Harsan su fadi suyi sujjada wannan shine yake tabbatar da cewa Ubangiji Harsan ya sanya musu albarka, to daga wannan lkcn ta zama matarsa zata bisa gdansa shikenan anyi aure.




Idan kuwa wannan ganyen sutura ya fadi batare da kowanne namiji ya gani ba to wannan budurwa ta barranta da kanta zata tafi inda iyayenta suke tana kuka taje ta fadawa iyayenta abinda ya faru,
Sukuma iyayen da yan'uwanta zasu dauketa su tafi suna kuka su kaita gaban sarki Jamal su fada masa ganyan suturarta ya fadi batare da bayyanar miji ba saboda haka sun sadaukarwa da ubangiji Harsan jinin wannan budurwa.
A gaban danginta da yan uwanta zaa dauketa a jefata dakin ubangiji Harsan da yake cikin gdan sarautar tana kuka tana komai haka aljanun tsafi zasu tsotse jininta sannan a fito da gangar jikinta a gasa a rabar da namanta wa mutane amma banda danginta.
To wannan shekarar ma haka bikin yake kasancewa amma na wannan shekarar ya bambamta dana kowacce shekara saboda kasancewar fara bayyanar Yarimah Isham wato da daya tilo a gurin sarki Jamal wanda ya kasance shine shugaban jaruman masarautar, tsantsar rashin Imani da tausayinsa ta buwayi yankin Zamhar inda anan yankin ne masarautar jawal take,
Shekarun Yarima Isham Ashirin da bakwai da haihuwa amma bai taba fitowa wajen masarautar ba wannan umarni ne na gunki Harsan, Yarima Isham ya kasance sadaukin jarumi da buwayarsa a duniyar tsafi take neman danne buwayar ubansa sarki Jamal da a zamaninsa ya gagari sarakunan duniya face sarki daya tak a duniya wato sarki Lussar na yankin nahiyar Yamen daya gagareshi bugawa a duniya.




*A WANI* bangare na masarautar jawal kuwa a qarshen katangar gabas da garin akwai wani magidanci me suna Uddatu wanda ya kasance maharbi ne Kuma matalauci ne sosai saboda ya kasance bashida cin yau bashida na gobe amma kullum zai fita daji yayo farautar naman dawa ya kawowa matarsa me suna Uddura ita Kuma ta sarrafa musu suci ita da mijinta da yarsu qwaya daya tal a duniya wato
*NAJMAH* wadda itama tunda take a duniya bata taba fita sararin gdansu ba kasancewarta kyakkyawar da duk yankin Zamhar babu kamarta, wannan dalilin ya sanya mahaifinta Uddatu yake boyeta saboda tsoron bayyanarta ga wannan azzalumar masarauta tasu yasan komai zai iya faruwa.
Ya kasance Najmah tanada shekaru goma sha biyar a duniya mahaifinta ya yanke shawarar zai fara fita da ita daji saboda gwajin jarumtarta daya dauki shekaru yana bata horo akanta tare da bata kariya da surrukan tsafinsa wanda yakeda tabbacin matsawar tana tare dasu burin manyan aljanun duniya bazai taba cika akanta ba,
Ta kasance duk takunta tanayinsa ne cikin halwar tsafin mahaifinta sannan a duk lkcn da zai fita da ita zuwa daji yakan shafeta da wani baqin shuni ya nade dogon gashinta ya sanya mata hula ta yanda duk wanda zai ganta zanyi zaton tsohuwa ce kasantuwar yanda fatarta take yamushewa a duk lkcn data shafa wannan baqin shunin tsafin.



Yauma hakace ta kasance bayan dawowarsu daga bikin Jawaleey suna zaune a farfajiyar gdan nasu sunacin naman gada suna hira tayi wanka ta wanke wannan baqin shunin sunata hirarsu cikin nishadi da iyayenta maharbi Uddatu ne ya dago idanunsa da suke zubar da hawaye.
Hankalin Uddaru da yarta Najmah yayi mugun tashi suka dago suka kalleshi Najmah ta matsa kusa dashi tasa zara zaran yatsunta tana share masa hawayensa tace “haqiqa a iyakar tsayin rayuwata dakai ya mahaifina bantaba ganinka cikin irin wannan yanayin tashin hankalinba wanda har ya sanyaka kake zubar da hawaye"
Ajiyar zuciya yayi ya dago fuskar yar tasa yace “yake sarauniyar kyawawan yankin Zamhar! Haqiqa lkc yana gaf da qurewa lkc ya kusa da abubuwa da dama zasu faru a wannan bikin Jawaleeyn da akeyi Yarimah Isham zai fara fitowa sarari kowa ya ganshi, kuma kema ubangiji Rundatu ya umarceni da ki fara zuwa bikin Jawaleey na wannan shekarar"
Dagowa tayi cikin matsananciyar damuwa idanunta na kawo ruwa tace “Amma ya Abbana me hakan yake nufi nasani iyakar sanina baka barina zuwa bikin Jawaleey Kuma ma bayan hakama bazan iya yin irin shigar da sukeyi wajen bikin ba kasani wajibine a gurin duk wanda yaje bikin Jawaleey sai yasha jini sannan sai ya rinqa fita rawar maita da dare nikuma a qa'idar madubin tsafina bai bani damar fita da dare ba sannan ya haramtamin ta'ammali da jini kowanne iri ne idan har hakan ta faru tsarin jikina zai karye zan kasance kamar kabewa kowanne irin qaramin sihiri zai iyayin tasiri a jikina"
Miqewa Uddatu yayi batare da ya bawa yar tasa amsa ba ya nufi dakinsa itama miqewa tayi ta nufi nata dakin tana shiga ta zauna a gefen gadonta ta dauki wata kumfa ta watsa saman wani baqin madubi, wata iskace me qarfi ta taso daga cikin madubin ta kewaye dakin sannan tazo tayi tsiri a gabanta miqewa tayi ta shiga tsakiyar iskar kawai sai ta rikide ta koma wani qaton basamude ta kece da dariya ta sake rikida ta komo asalin kamanninta ta tsaya gaban mudubin tsafin tayi wasu surutanta sannan ta bude manyan lumsassun idanunta akai kawai saiga hoton Yarima Isham ya bayyana yana kaiwa da komawa a tsakiyar dakinsa ta zuba masa ido tana kallonsa kyakkyawan gaske me cikar zatin halitta qirar jarumta ta gama bayyana a jikinsa asalin rashin imaninsa ya bayyana a kwanjinsa, kallonsa kawai takeyi tana murmushi har ya qarasa gaban wata qwarya ya bude ya debi wani ruwa me kama da jini ya kurba ya furzar ya nuna wata katanga da yatsansa wani farin haske ya fito ya kewaye katangar sannan hasken ya rikida ya zama ita, murmushi tayi masa shima yayi Mata murmushi ta nunashi da yatsa tace “dama baka wahalar da kanka da zuciyarka wajen son sanin wacece ni ba nice zan mulkeku da sannu Kuma nice sirrin nasararka idan naga dama zan iya kwace duk wani qwanjinka da sirrikan tsafinka cikin abinda bai wucce qiftawar ido ba, am kada na cikaka da surutu yau zamu hadu dakai a bikin Jawaleey bisa sahalewar ubangijin da nake bautawa wanda yake kareni daka sharrinka da sharrin sauran matsafan duniya...."
Tana gama fadin haka ta daga hannunta ta shafe fuskarsa dagakan allonta ta yanda duk yanda zaiyi bazai iya ganinta ba kuma duk binkicensa bazai iya gano daga wanne yanki na duniya tayi masa mgn ba.


_Assalamu alaikum_

_Masoyana inayi muku fatan alkhairi, domin cigaba da karanta wannan lbr na *MASARAUTAR MAYU* ki turo kudinki/ka VIP 500 regular 200 ta asusuna 0255526235 Fauziyya Tasi'u Umar GTB ko katin waya MTN ta WhatsApp number na 09013718241 idan VTU zaka/kiyi Kuma Zaki turane ta wannan number 09031307566: kada ki tura VTU ta number farko domin bazan gani ba only evidence of payment zaki turo a ita._
_Mutanen Niger ma zaku iya turo katin orange wanda zaiyi daidai da kudin dana ambata a sama ta number farko, na gde sai najiku._

_Sannan akwai littafin *WANI QANGI* 200 ne VIP 400 idan kina buqata Zaki tura ta wadancen numbers dake sama ko ta account din dake sama_
# *UMMUH HAIRAN**MASARAUTAR MAYU!*


*WRITING AND STORY*


*UMMUH HAIRAN*


*MARUBUCIYAR*
👇🏻
AMINIYA KO KISHIYA
HABIBULLAH
QUEEN FARHA
GIDAN UNCLE
ADANDI
WACECE NI
AURAN BAZAWARA
DHOOM ISHAQ
MATAR LAMEER
DUBAI
AND NOW👇🏻
MASARAUTAR MAYU!


*P 3-4*


Tashi tayi ta fara shiryawa bayan ta gama ta dauki wannan baqin shunin ta shafa a jikinta tayi girgiza jikinta ya sauya zuwa na tsohuwa ta fito cikin shirinta tare da duban mahaifiyarta tace “yake mahaifiyata fatan nasara gareni" tana fadin haka ta dora hannunta bisa gwiwar mahaifiyar tata ita Kuma Uddaru ta dora hannunta akanta yartata tace.
“Kijima ki qarko yake yata ki kasance cikin ambaton sunan abin bauta Rundatu tabbas zai baki kariya daga fadawa halaka" jinjina kai tayi daidai lkcn da Uddatu ya fito ya matso gabanta ya kama damtsanta ya sanya mata wani guru ya dafa kanta yanaci gaba da karanta surkullensu na tsafi itama rufe idonta tayi har zuwa lkcn daya gama ya saketa daidai lkcn da wani jaki ya keto ta tsakiyar ginin garun gdan ta haye samansa ya shilla da ita batako waiwaye suna tafe tana kalle kalle,
Ajiyar numfashi tayi a ranta tace “yanayi me dadi gari me cikar ni'ima amma ko Ina kabi a cikin garin qasusuwa ne na dabbobi da mutane sakamakon annobar data sauko musu cikin shekarar data shude wadda mutane da dabbobi da tsurrai suka rinqa mutuwa saboda rashin abinci to har gara ma mutane idan anga suna sharafa akan gasasu a barbadesu da yaji a bawa yaran da qwanjin maitarsu baikai su faracin danye ba saboda sunyi qanqanta wajen fita rawar galji wacce a itane ake rabon maita.



Haka Najmah ta rinqa ratsa tsurrai da tsaunuka har takai ga Isa da'irar da aka ware domin gabatar da wannan taro, birki tajawa alfadarinta ya tsaya ta sauka ta shafa bayansa ya bace bat, tsayawa tayi tana qarewa al'ummar dake gurin kallo ga yammatanan birjir da samari sunata yawo soqai soqai dasu haska fitilar idonta takeyi domin ta hango wata halitta mai muninta a duk fadin gurin amma ta kasa gani bawai baqin fatarta ne yasata muni ba aa yamushewar da fatar tata tayi ne sannan ga rashin wani wadataccen gashi akanta asalin nata ta nadeshi ta boyeshi cikin hula tasa hular gashi gashinma cikuikuyayye.
Tananan tsaye tsayin lkc mutane sunata zuwa suna wucceta kowa yazo wuccewa saiya kalleta, a qa'idar wannan biki idan anayi babu meyiwa wani mgn amma fah mutanen da sukayi ido biyu da wannan halitta tata sun shiga mamaki da al'ajabi harma zukatansu sun fada tunanin daga wacce nahiyar ta hauro tasu domin ganin bikin Jawaleey, wanne tsautsayi ne ya kawota makasarta?
Tagaji da zaman kallon mutane kasancewar ita mutanen ma baqine a wajenta a rayuwarta batasan kowacce fuska ba face fuska uku fuskar mahaifinta mahaifiyarta saita Yarimah Isham da lkc zuwa lkc takeyi masa kutse cikin halwar tsafinsa batare daya sani ba, Ubangiji Rundatu shine ya bata wannan saa Kuma yanzu ma da sahalewar sa cikin tsaronsa ta fito, shiga tayi cikin taron tana kutsawa tana kurdawa har ta isa cikin tsakiyar taron tayiwa kanta guri ta zauna kusa da wasu matasan yan mata guda uku tana zana qasa.



Kallonta sukayi suka tabe baki sukaci gaba da hirarsu daya cikin yammatan tace “mahaifina ya sanar dani fitowar Yarimah Isham daidai dake da qara wanzuwar zalumci cikin wannan masarauta Mahaifina ya sanar dani cewa idan Yarimah Isham ya fito haskan fuskarsa zai dusashe hasken rana a lkcn daya fito anyi ittifaqin cewa mutum dayace a yankin Zamhar zata iya gogayya dashi ta fuskar qarfin sihiri da kyawun halitta itace Sarauniyar kyawawa NAJMAH bincike ya nuna ta wanzu a doron qasa tana rayuwa cikinmu amma har yanzu babu wanda yasan wacece ita shi kansa Yarimah Isham ya kasa sanin daga wanne yanki na duniya zata bayyana"
Numfashi daya cikin yammatan ta sauke tace “zata bayyana tabbas zata fara bayyana cikin wannan bikin Jawaleey din da ake gabatarwa ni da zan ganta zan kasheta ne na kwashe sirrikanta sannan na tsotsi jininta ta yanda nima zanyi haske zan buwayi duniya kamar yanda kurwarta ta gagari Sarkin Mayu Bargas ya kasa samun damar lasheta Kuma ya kasa samun damar bata maitar ta hadiya Wanda ta hakane kawai zata bayyana duniyarmu ta santa"




Murmushi dayar tayi tayi wani kaki saiga wani qoqo cike da jini ya fado daga bakinta Najmah tayi saurin miqewa daidai lkcn da kida da sautin sarewa da algaitun ya fara canzawa nandanan gurin ya yamutse da ihun matasa suna fadin “Barden duniya! Barden duniya!! Yariman mu!!! Yariman mu!!!" Haka suka rinqa ihu, bayan shudewar wani lkc gurin yayi tsit kamar ruwa ya cinye kowa.
Lkc me tsayi suna tsaye a haka kafin Yarimah Isham ya gama daidaita tsaiwarsa saman mumbarin ya tsaya sosai Najmah ta dago ta zuba masa ido cikin shigarsu ta sarautar qasaita sanye yake da alqabba wacce aka dinkata da fatar damusa anyi Mata ado da zaren jauhar da duwatsun lu'ulu'u hatta takalmin qafarsa na fatar damusar ne, kallonta takai wa murdadden damtsansa guraye ne kala hudu baqi fari ja da yalo.
Faffadan qirjinsa ta sauke idanunta akai da yake cike da suma murmushi tayi ta durqushe daidai lkcn da hadimai suka fara rabon tsumi tana qasa a durqushe har suka gama sannan ta dago ta sake kai dubanta kan Yarimah Isham idanunsa a rufe take yana addu'a har ya gama ya bude idonsa tana nesa sosai taga ya motsa hannunsa tuni taga baraden fada sun bazu da manyan dorinoni a hannunsu sun fara bin yammatan suna dago fuskar kowacce suna duba zanen jikin wani qyalle dake hannunsu ta gabanta sukazo suka wucce suka rinqa zagaya wajen sun kasa ganin abinda suke nema haka suka koma gurinsa suka zube gabansa suka fada masa sakamakon bincikensa a take ya tashi manzanni da takardu suka kaiwa sarakunan qofofin garin guda hudu.



Hakan baiyi masa ba saida ya sauko dakansa ya rinqa bi layi layi yana dubawa har zuwa lkcn da yazo layin da Najmah take ya tsaya a kusa da ita yana bude hancinsa tare da dube dube a daidai lkcn zobben yatsanta ya sabule ya fadi kan takalminsa ta sunkuya tasa hannunta ta dauka.
Hakan ba qaramin fusata zuciyarsa yayi ba aikuwa ya nunata da yatsa tayi saurin kaucewa wani haske ya daki qasa ta tsage take gurin yayi rami sake nunata yayi ta sake kaucewa da muguwar azamar data gigita kowa dake gurin wani tsalle tayi ta dira a bayan ya juya ya zuba mata ido tare da sake nunata da hannunsa tayi hanzarin sanya tafukan hannunta ta tare hasken ya sake tura mata wani ta watso masa abinsa ya kauce da azama tare da jefa mata wata sarqa ta daureta tamau yayi Mata murmushi yace “Haqiqa wannan tsohuwa salonki ya birgeni har yanzu zamani yana tafiya dake Urwat ka dauketa ka kaita kurkuku ka adana ta kullum da safe a rinqa gana Mata azaba kala ashirin har tsayin watanni uku"
Lumshe idonta tayi ta budeshi akansa ta bude bakinta tace “yanzu salon wasan zai fara kaje ka sake shiri" tana fadin haka tayi wata miqa sarqar ta tsittsinke yabi sarqar da kallo cike da firgici ya dauki zare daya na sarqar ya jinjina kai yana kallon tsohuwar tare da tunanin inda yasan wannan muryar, sakeyi masa murmushi tayi a karo na biyu tace “basai ka daureni ba idan ka daureni mutanenka zasuga kasawarka su koma gefe suna cewa ka gaza mace ma tafi qarfinka saida ka daureta sannan ka iya kamata duba kamar can kalli ma can"



Juyawa yayi da sauri da gaske kuwa mutane ne suketa gulmarsa nandanan zuciyarsa ta kumbura ya juya a fusace yace “tsaiwar me kakeyi da bazaka kamata ka tafi da ita ba...." Da sauri bafaden ya matso zai tabata ta janye da sauri tace “karka tabani hakan na nufin katsewar numfashinka daga ruhinka" dogarin ya firgita da lamarin tsohuwar me muryar yara shiyasa baiyi jayayya ba tayi gaba yabi bayanta ta waiwayo ta kalli Yarimah Isham tayi masa murmushi ta juya abin mamaki itace tayiwa dogarin jagora har magarqamar ya bude ya shigar da ita ya bude Mata wani daki ya hankadata ciki.
Bin dakin ta rinqayi da kallo tsoro ya mamaye dukkan ilahirin jikinta ta rinqajin gumi na karyo Mata tsugunnawa tayi ta dauki wani qashin haqarqari ta zuba masa ido cikin matsanancin tsoro tayi jifa dashi ta rintse idonta jikinta na karkarwa saboda tashin hankali, ba komai ne ya tashi hankalin Najmah ba face yanda taga qasusuwan bil'adama a qasa a birjik a dakin.
Daqyar ta samu tsoronta ya ragu ta bude idonta ta fara tattare qasusuwan tana tarawa waje guda aikuwa ta tarasu jibgi guda ta koma ta zauna tana haki tana bin kowacce kusurwa ta dakin da kallo, matsawa tayi inda taga wani rubutu tasa hannunta ta goge qurar data rufeshi, ja tayi da baya a tsorace tana maimata �? *BAITUL MAUT*"
Zamewa tayi ta zauna a qasa tare da fashewa da wani matsanancin kuka Saida tayi me isarta sannan ya miqe ta haska tafin hannunta da idanunta tana wasu surutai, hoton Fuskar mahaifinta ya bayyana a saman tafin hannunta ya kalleta da sauri yace “ya akayi kika bari kika shiga BAITUL MAUT?" Ajiyar numfashi tayi tace “bansan meye hakan yake nufi ba ya akayi kuka janye tallafin tsaro daga kaina har takai ga zoben kariyata ya fadi tabbas da banyi gaggawar daukeshi ba da tuni labarina ya shude a wannan duniyar" katseta mahaifinta yayi yace “wannan dakin da kike ciki ma shine qarshen daki me hatsari ki koma asalin Najmarki ki kiranyeshi yazo ya fitar dake idan ba hakaba tabbas iskarki da numfashinki a qidaye suke"
Yana fadin haka ya bace bat ta murza ta kirashi yaqi bayyana kawai saiji tayi an shaqeta ta baya, shaqa bata wasa ba aka dauki wani bututu me kama tsinken tsire zaa caka Mata, cikin yanayin fitar hayyacin da take ta hura wata iska ta tafida wannan bututun shaqar da akayi Mata taji an saki ta fadi qasa tim, da sauri ta murza zobenta daidai lkcn da Yarimah Isham yake shiga turakarsa yaga zoben hannunsa yayi baqi, da sauri ya dakatar da dukkan masu tsaron lafiyarsa ya shiga cikin turakar tasa shi kadai ya dage labulen madubin tsafinsa ya zubawa madubin ido cikin daqiqu hoton wannan tsohuwar ya bayyana cikin abinda bai wucce shudewar daqiqa hamsin ba yaga ta rikida ta zama wannan kyakkyawar budurwar da yake nema tsayin rayuwarsa kwance qirjinta kafe da wani qoqon tsafi jinin jikinta yanabin wani bututu yana feshi a dakin cikin halin rai kwakwai mutu kwakwai.



_Assalamu alaikum_

_Masoyana inayi muku fatan alkhairi, domin cigaba da karanta wannan lbr na *MASARAUTAR MAYU* ki turo kudinki/ka VIP 500 regular 200

Please Login or Register in order to submit comment