Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

so,dan yankakken kwan ya dauka daya tal yace gashi jeki malama,Salma cike da shagwaba tace wannan?Dan wannan? Ni..ni..ni bana sonsa,ya kara mata daya again ta tafi tana kukan shagwaba sai doka kafafu take a kasa,ta tafi da Imanin Na'im bata sani ba,cin danwakensa yakeyi kawai yana Shan ruwa,Salma tazo ta zabgawa nata yaji tana ci,Na'im yace wai kin san mene Aure? Salma ta girgiza kai tace yo ni ina na sani,yace to haifuwa fa?Malam yace baya Haifuwa mene na? Tace a haifi da kamar ni ko kai,yace to ya? Cikin shagwaba tace to wai kai ni sani nayi,ance a asibiti naji namiji ne yakewa mace ciki ta haifi da,Na'im yace Oh na gane shine ake aure kenan,to me ana yi kenan a haifi da? Salma tace wata a asibiti tace min wani yayi mata ciki wai ya dinga taba ta ya sa mata wani sanda,Na'im yace wlh to ina son wannan abin ana taba jikin mata,ko na tambayi malam? Salma tace kai ance Iskanci ne fa,Na'im yace kai kamar nasan word din nan Iskanci,Salma ta tabe baki tare da cewa yo ni ina zan sani,tunda Malam yana koya mana karatu watarana ai zamuji ne ko cewar Salma,Na'im yace uhm idan Malam yace Aure da kyau sai na nemo wata a kauyen nan ayi mana gaskiya ina jin son mashe(mace) Salma tace kai kamar nasan maganar nan taka au na tuna a asibiti naji,Salma tace Yan matan garin nan basu da kyau kuma baza su baka auren yarsu ba gwara ma ka hakura sarkin son iskanci da mata,Na'im yace ranar nan naga wata a hanyar mosque tana da dan kyau sai a bani ita kawai,Salma tace to me zakayi da mace wai kai? Na'im yace abinda akeyi, ko nace Malam ya bani ke ya mana aure kawai gashi nan muna ganin Malam da Umma me sukeyi girki,hira sai muyi muma ko,amma Idan zaki bani wannan katuna katuna na chest naki na gani ko? Salma ta kyalkyale da dariya tace to ayi mana mana na yarda baka ganin Umma daki daya suke kwana da Malam,Na'im yaji dadi a hankali yace Allah?tace sosai ma one Bed na taba gani da naje kai musu abinci,Na'im yace wlh sai mun koya muma ai,Salma tace hakkun a zaune take wannan ana ci da rabonmu ana yi bamu a gari,amma ka bari nayi wata kawa a kauyen nan tana da aure Rahina gobe zanje na tambayeta mene akeyi idan anyi aure Na'im yace to Allah ya kaimu kije,amma kar mu fadawa kowa mission dinmu sai mun gano abin.Salma tayi kamar me rada tace to Muhammad amma Umma tace na dinga ce maka Yaya Muhd,Na'im yace shima da rada a'a naji Umma tana cewa Malam me gida nima ki dinga ce mini me gidana hhhh sukayi dariya harda tafawa irin shegun nan sun hada tsiyarsu.

Sai bayan Sallar Isha Umma ta dawo ,Malam ma ya shigo Salma ta idar da Sallah kenan tana duba karatunta tayi musu sannu da zuwa,Umma tace ina Muhd? Salma tace yana masallaci yanzu zai shugo,Bayan minti kadan sai ga Na'im Shima sannu da zuwa ya musu Malam yana cin abincin da Salma tayi tuwon shinkafa miyar taushe Na'im ne shi zai iya ci shi yasa ta girka musu,Umma kuwa tace ragowar danwaken rana zata ci da safe taci tuwon.

Salma ce ta fito daga dakinta tace Sannu da dawowa me gidana kafin ace wani abu Na'im yace yawwa me dakina,Malam da Umma suka dinga dariyar abin wai su suka kwaikwaya tunaninsu wasa sukayi kawai sai suka ji washe gari ma Salma haka tace harda durkusawa me gidana barka da asuba,Na'im ya basar ya amsa kin tashi lfy ko? Tace lfy Alhmdllh yace ehem yawwa me dakina.

Umma tana kallonsu a ranta tace a lallai nan gaba idan kun warke kafin ku bar gidan nan sai Malam ya daura muku aure Insha'allah,Na'im yasha tea yasha Madara da kosan da Salma tayi musu sai bread,Salma da Umma sun gama aikin Gida kaf,tayi wanka tasa Lace riga da skert tayi kyau Salma kamar a Abuja,Na'im yasha farar Shadda me shegen kyau sai kamshi sukeyi sun dace da juna,Salma tace Umma mun tafi yawo,Umma tace to a dawo lfy kar a dade,Salma ta yafa dan gyalenta kalar kayanta suka fito gari a karon farko, Salma ta rada masa tunda su Umma basa gani mu rike hannunmu,Na'im yace to mu rike mana caraf suka rike hannun juna Kamar watan Ramadan haka ake kallon su Na'im kamar za a cinyesu turawan gidan Malam Magaji ne haka ake fada sai binsu akeyi yuuu yara suna cewa turawa ne turawane.

Gidan Rahina Salma ta shiga mijinta na ciki suka gaisa tace tare suke da me gidanta Da Sauri mijin Rahina Abubakar yace bari na shigo dashi ya zaki barshi a waje kaji mutan kauye da karramawa,Na'im ya shigo shima har palon Amarya Rahina harda kujeru dai dai talaka,Salmada surutu ga tambaya suka dinga hira sosai da Rahina da Abubakar, Na'im baya magana sosai sai da kyar.
Salma tace tashi muje ciki ina da tambaya,suka shige cikin bedroom na Rahina,Na'im da Abubakar suna zaune jefi jefi suke dan hira tunda Na'im shi ba sanin abubuwa yayi ba baya tunawa,Abubakar bai gane ba ya zata gayu ne na mutan birni kawai.
Salma da Rahina Salma tace ke wai aure fa za ayi mana da wannan kwanan me akeyi idan anyi aure?Rahina kanta ya daure,duk girman Salma gata gogaggiyar birni ace bata san ma me ake a aure ba ko girman dare daya tayi irin na yan birni,Rahina tace kamarki baki sani ba?Salma tace to na taba yi ne?ki fada min mana dan Allah,nan Rahina ta daure ta karantawa Salma tas,komai bata boye mata ba,ta dinga kwararo bayani abin kunya ya bawa Salma da taji ashe ba Sanda ba abin Maza ne,sai da ta gama ji tsab tace to gobe ko jibi zan dawo ki kara min haske.
Tana fitowa tace Na gama muje Muhd,suka musu sallama tare da fitowa suka shiga zaga gari suna yawo waje waje,har suka dan fita bayan garin kadan bishiyoyine na mangoro duk sun nuna jajir ga sanyi a wajen,gefe magariyace da kurna da Sauran bishiyoyi da dama inuwa ko ina,kan wani itace suka zauna ita da Na'im bayansu na Gugan juna Na'im yayi mukus yana jin dadin jikin Salma a jikinsa.

Salma tace sai ya dagata sama ta tsinko mango,ya dorata a wuyansa ta Ciro guda goma jajir dasu masu kyau,ta wanke da purewater da ta dakko guda biyu a gidan Rahina,ta bashi suka fara shan abarsu,Na'im yace me Matar ta fada miki?Salma tace babbar magana kenan Bazan iya fada ma ba akwai kunya sai daí gobe mu koma ka tambayi Abubakar shima ya fada maka kace kana da cutar mantuwa ya baka labari.bai takura mata ba yace Allah ya kaimu tare da jan tsaki yace ai sai kina fada min tun dazu a can na tambayeshi nima.
Salma tace uhm kai za a sha fama fa Amma Allah muma ayi mana mu gwada abinmu tsab zamu iya,Na'im yace ai dole ne ma karfa ki fadawa Umma da Malam na sanki da surutu Salma tace ai shuru zanyi ba a fadar irin wannan Magana nauyi gareta inji Rahina me gidana.
Nan suka shanye mangoes dinsu tas tare da wanke hannu da ragowar dayan ruwa,gayyen Magariya tace bari na ebowa Umma naga tana amfani dashi,ta samu ta ebo ganyen da yawa,yayan magariyarma sun nuna tare da yayan kurnan ta ebo su da yawa ta kwance dankwalinta ta zuba a ciki komai da yawa,har mangoes sun fi guda ishirin ta kara ebowa ta daure a dankwali Na'im ya dauka suka tafi gida lokacin an fara kiran Sallar Azahar,a masallaci ya tsaya akayi Sallah,ita kuma ta shiga gida tayi tata Sallar sannan ta nunawa Umma abinda suka samo.

Salma yanzu ta saba da addini sosai ta Dage tanayi bata da matsala,sabo da ko ta manta Umma zata sata dole har ta saba ma,karatun Addini ma haka ita da Muhd.
Yana idar da Sallah ya dawo gida shima,abinci Umma ta zuba musu shinkafa da miya da taliya da salat harda tumatir, Na'im yana ta faman kallon Salma kamar zai cinyeta,ita Salma suna hada ido zata masa murmushi,Umma a ranta tace uhm Allah dai ya baku lfy kunya suke bata wlh shi yasa bata son zama kusa dasu ma,su kuwa ko a jikinsu,Umma har Malam ta fadawa Malam yace baza ta yuwu suna haka a daura musu aure ba Sabo da bamu sani ba ko Salma tana da aure,dole sai sun warke,Umma tace gaskiya Salma da Alama bata taba aure ba amma zan tambayeta ko zata iya tunawa idan hakan ya gagara zan dubata na gani idan namiji ma yayi amfani da ita ai zan gane da dabarunmu na mata.Malam yace shi dai ba mahaukaci bane bazai daura aure ba babu ruwansa.Umma ita kuma tace gaskiya ayi musu shahada za a ayi.

nima nabi bayan Umma ko Ya kukace fans sai Umma.







Tnx alot fans dina.






AsmaBaffa
[1/14, 5:14 PM] Sis Asma: 🏉KAMARSU CE DAYA🏉








66-70








Official








By
AsmaBaffa






Ga page naku mutanena

Mrs Farouq,Mommyn Zahra,Asmau B Yusuf,Hafcycy,
Hapsy,Jannat
Hafsat khairan,
Naja'atu Aliyou,and Zulaihat.

BILLY TABACO godiya nake dubu dubu nagani,kimin Afwa bana kusa wlh abu sunyi yawa kuma lokacin ina zazzabi shi yasa.na gode da kulawa.








Ko da Malam Magaji yaga mangoes da suka samo yace waye ya hau sama?,ba tunanin komai Na'im yace ni na dagata sama ta tsinko,nan fa Malam ya dinga musu fada da nasiha cewar mace indai ba muharramarka ba to bai halatta ta taba namiji ko Ya taba ta ba,Na'im yace ko dan hannu? Malam yace kwarai nan yayi ta tunatar dasu,kawai suka ce to sunji,washe gari kuwa Na'im shi kadai yaje wajen Abubakar mijin Rahina ya warware masa zare da abawa aiko ya dinga murna kamar an masa bushara da Aljanna yace dama haka yake so.
Abubakar yasha mamaki kwarai shima shi kam Bai ganewa halin turawan gidan Malam Magaji ba Sam.
Nan Abubakar yace nan da kwana biyu za ayi wani shagali da ake kira Sallar Taushe ranar ko jaririne a kauyen sai an yanka masa kaza guda za aje kasuwa mata da maza ayi siyayyar kayan dadi,ranar kowa sabon kaya zai sa kamar sallah su a garin ma wannan sallar Taushe tafi Sallar gaske ta kowa da kowa sabo wasu ma basa dinkin Sallah ta eidi sai a wannan ta aladar kauyen akeyi,wasu basa yanka sai a wannan Sallar,nan Na'im yace suma dasu za ayi tare da me dakinsa,Abubakar yace za a kwana ana kida da wasanni iri iri,wasu ma da suke birni suna zuwa asha wannan Sallah dasu,yanzu ma sarkin kauyen ya maida Sallar kwana biyu za ayi ana cashewa,yan mata da maza za a cashe ko wacce da gwaninta.
Na'im yana dawowa ya tambayi Umma ta kara yi musu bayanin sallar da akeyi tace gobe ne ranar cefane idan zakuje kasuwa kai da kanwarka sai ku shirya Malam zai baku kudi sai ku yo cefane kuma.

Washe gari kuwa mutane sai hada hada ake a kauyen zuwa wata yar kasuwa wasu na zuwa wasu na dawowa,Salma da Na'im su basu San yan kauye ne ko yan Birni ba kawai suka shirya,Na'im yace sai dai tasa hijab sabo da ya fara Jin kishin ana kallonta,da dan hijab dinta suka tafi kasuwa,suka ga ana ta wucewa da kaji da zabi wasu dan akuya da kaji,wasu harda rago da masu sa,abin nayi ne cewar Salma,Na'im ya kalleta cike da shauki,sabo da basa fita basa komai sun kara fresh da kyau, yace ke me kyauce fa Salma I swear.
Kunya taji tare da rufe idonta tace ai ka fini,kin San ranar dana ganki saida gabana yace dam dam 3times,Salma tace kamar ka sani ji nake a raina ana ce min ga mijikinki nan gashi nan,murmushi sukayi suna ta hira suka je har kasuwar kauyen,Malam Magaji ma yana ciki yana ta cefane domin yace bazai basu ba basu San yanda akeyi ba amma ya basu kudi Salma ta kara da ragowar kudinta 4k na hospital,suka siyi kaji uku uku da kayan miya da sauran Abubuwa,Salma harda kwan zabi guda talatin, coconut,da Aya da sauran kayan ciye ciye,kajin masu rai sai tsiyau tsiyau sukeyi aka daure musu kowanne a cikinsu ya buga tsalle ya gudu suna tsoron kajin ana ta musu dariya,sai Malam Magaji ne yazo ya karba ya tafi dasu gaba daya da nasu gida,su kuma suka dauko kayan miya da tarkacen Salma,Salma tace muna zuwa yau zamu cinye ayar mu ko?yace nafi son coconut din ni,Suna zuwa gida Umma ta dinga tsokanarsu sun kasa dauko kaji,Zama sukayi suka wanke ayarsu da kwaka aka bawa Malam da Umma suka ce basa ci su Umma ce ta dauki Coconut yanka daya,su kuwa suka zauna sai da suka ga bayan tarkacen nan tas,musamman Salma,Umma tace Ku taso ayi gyaran kaji daku bazan iya ba sunyi yawa.

Allah yasa garin ana basu Wutar nefa ko ina kullum da haske,suka zauna cikin daren ake ta faman girke girke ko ina a kauyen kamshi ke tashi,wuta da haya ki na tashi gidan kowa,can kuma can bayan gari filin da ake shagalin masu Dj da kade kade iri iri tare da masu wasanni an kawo kayan komai da za ayi amfani dashi,Umma tace to ai ke Salma Saurayin naki Bai baki kudin kaji ba duk saurayi sai ya bawa budurwarsa kudin kaji, da can Dubu biyu amma wannan shekarar Dubu biyar idan Bai bada ba to baza a aureshi ba,ko an sa rana haka akeyi a kauye,tunda ka kasa biyan wannan kudin to ya nuna baza ka iya ciyar da matar ba, to wannan shekarar har kudin waya Dubu bakwai ake bawa mata,dan haka mikowa Salma kudinta idan ba haka ba kar ka kara ce mata me dakinka.

Na'im ya shiga ya fita ya koma bedroom ya fara bincika akwatinsa baiga komai ba ciki sai 100 usd doller a cikin wandon kayansa,suma mantawa yayi da ita tun yana Abuja,yace gashi ya mikawa Umma,Umma ba tausayi ta mikawa Malam wai ya bincika sun kai nawa,Malam yace wannan ai yanzu ta kai kusan Dubu talatin idan aka canja ta,
Suka hangame baki,Na'im anyi abin kirki harda sosa gashi tare da harde hannaye,Salma kunya ta kamata sai murmushi takeyi tana rufe ido,Malam shima ya mikawa Salma kudin ba ruwansa yace ta karba saurayinta ya bata.

Ta karbi kudi,Umma tace sai kice an gode Allah kara Budi,Salma ta fada kuwa tana tufe Ido,Na'im sai murna yake.
An soya kaji,anyi farfesu da wasu harda su zabbi,da safe kuma Umma sukayi Shinkafa da miya da nama ga hadin salat,ga kaji suna tokare murfi da da kafa,haka makwafta ma suka dinga kawo kalar nasu suma suna basu,ga kowa an raba an bashi nasa a kwano shi kadai dukkansu kowa kaji Uku da farfesu guda daya,biyu kuma soyayya,Naman rago kuma a miya,wai ranar ana bargaje dadi,Salma harda siyo musu lemon kwalba kowa biyu,nan fa kowa yaja gefe Kaci son ranka ka rufe anjima ka kara,Yamma tanayi kuma kowa ya dau wanka na gaske kai ba kace yan kauye bane,har matan aure kowa da sabon kaya yara da manya maza da mata samari da yan mata tare da tsofaffi gaba daya an fito ga kida da wasanni na tashi iri iri,kuma kidan wakokin hausa na zamani na wannan shekara,mata da maza cashewa akeyi harda yan jarida suna dauka.

Salma da Na'im wankansu kamar party zasu halarta a Birnin duniya,sun kure adaka da kayansu na karshe,Salma ansha doguwar rigar material cotton maroon and white,haka Na'im ma komai fari Kal,suka fito tare da jerowa,Umma da Malam suna gida sunce basa fita su,
Ana karasawa Salma taji kida jikinta har rawa yake karku manta dama ta saba da rawa abinta tun suna tare da Raheel ta iya.
Yan mata cashewa sukeyi samarinsu ana musu liki,Salma ta basu Doller dinta a Dubu ashirin suka bata sababbi yan Dari da yan hamsin ta bawa Na'im yan 100 ita kuma ta rike yan 50.

Yace shi bazai shiga ciki ba,Salma ta fara kukan shagwaba Saurayin kowa yana gwada bajinta amma yanda suka Sha kyau yaki yi mata Zata fasa auren ma,nan yace to zai je amma liki kawai zai yi mata,ana canja kida me tashi Salma ta shige yanda take rawar birgewa nan take waje ya dau ihu da tafi,kafin Na'im ya shiga maza sunyi yuuuuu suna zazzage lalitar kudinsu kan Salma,sun manta da yan matansu harda matan ma liki suke ta yiwa Salma,Na'im zuciyarsa kamar ta fito kawai sai ya jira su gama,aka canja kidan Yan Nija me dadi gaske da duka,Salma kamar yar rawa dama haka take canja salo,Ana Shan kallo,Na'im ya shiga duk ba wanda ya lika yan Dari sai shi ya zazzage kudin duka ya rage 3k ciki kawai ganin yanda ake kallon Salma ya fasa ya janye ta sukayi waje,suka koma yan kallo tuni labari ya cika gari turawa sunyi bajinta,sun hada Kansu da mutan kauye basu da girman kai,ai sai aka koma sonsu a kauyen,ana ai ba ruwansu basu da girman kai komai dasu akeyi suna shiga su Zama dai dai da yan kauye,shigarsu ce kawai ta ban banta.Anan nake tunatarwa ga duk wacce ko wanda Allah ya kaishi aiki kauye ko wani abu kar ya dinga nunawa cewar shi ya fisu yana wulakantasu,ana nunawa basu San komai ba etc ka Zama social to duk inda kaje ko aiki ne za ka samu yabo da shedar arziki,ba ana cewa kasan wance kaji ance Allah ya tsine mata,tsinanniya,ai wannan jaraba ce,Allah ya mata kaza etc ba dadi amma duk inda akaje aji ana yabon ka da shedar kirki ko mutuwa akace kayi addua za ayi maka sannan ka samu sheda me kyau,basai kauye ba ko ina Allah ya hadaka muamula da mutane a kiyaye a zauna da mutane lfy a fahimci juna,sai ka samu kyakyawan sheda.

Salma suna gefe suna kallon masu yi can suka koma wajen masu wasanni,wasu yan matan da maza gada akeyi ana wake waken dandali ,Salma taji ana In... nai... haka.. in.. nai. .haka na gano rufin dakina,wai gidan mijin da zasu aura,wata tace in nai haka na gano shi tsaye,Salma ta shige itama ta juya kai kamar yanda sukeyi tace in. Nai....haka...in...nai...haka na gano masoyiiiina....ta kalli Na'im yana sakin murmushi kamar yanda mazan sukeyi idan tasu ta fadesu,sunsha kallo iri iri so sweet sannan suka dawo gida wajen 12am na dare sai baccin gajiya.

Washe gari kuwa Umma tasha labari na kallon da sukayi har gwadawa sukeyi yanda akeyi,yauma da yamma basu shiga ba amma sunsha kallo,wani Dan birni yazo da kafceciyar waya ta birgewa Camera kamar ka dauko mutum,ya dinga yiwa su Na'im da Salma pics iri iri a ko ina tun jiya haka yau ma,har kajin su saida yaje gidan ya dauka,ya daukesu tare da Malam Magaji da Umma ya musu iri iri masu kyau, sannan Salma ta karbi yar karamar wayar Rahina tana da memory aka tura musu pics dinsu a ciki wai idan sun siyi tasu zasu tura abinsu.
Dan birni yayi deleting pics nasu daga wayarshi yayi musu Sallama ya tafi.

Mummy Allah Sarki ta rame hawan jini ya kamata me karfi kullum suna hanyar asibiti,gaba daya Family din ba a jin dadi a cikinsa Sabo da rashin Babban jigonsu Na'im da ace mutuwa yayi da hankalinsu zaifi kwanciya sunga gawarsa da ace bata yayi,Kullum Sa rai sukeyi za a ga Na'im Amma shuru.

Affa da Ummitu ana ta cin duniya ba ruwansu da kowa,kawai cin kudinsu sukeyi,wannan shekarar ma Affa ya saida wasu shanu nasa zai tafi kasa me tsarki domin sauke farali,ko Salma basa tunawa a rayuwarsu,sun manta ma da ita,Affa arziki ya karu yace yanzu ya daina zama da ka sai da bin malamai ana neman tsari Sabo da masu hassada,nan ya fada malamai a tsare masa dukiyarsa,tsafi da shirka iri iri yakeyi akan shanu,har makabarta yake binne binne Sabo da wai duk na tsarin kai ne da dukiya Sabo da harkar ta koma ta malamai,ana neman ran mutane ana neman lafiyar mutum shi yasa yanzu mutane mutum bashi da niyyar bin malamai Amma Sabo da mutanenmu sun koma shirka ana kashe juna,ana tsafi ana neman lfy mutum,ana shatile ma kafa,yan mata,kishiya,yan kasuwa,ma'aikatan Gomnati,yan siyasa,barayi,yan fashi,yan sane,samari matasa etc kowa kusan yanzu Malam,mijikinki zaiyi budurwa tana sanin cewar yana da mata tun kafin ta shigo za a fada malamai ganin an raba su,ta mallake miki miji tun tana waje,uwargida tana kunsar takaici,daga nan itama a bata shawara baza ta dinga addua da kanta ba sai a fada malamai,idan kuma an sawa mutum cuta dole sai da malamai za a warke daga nan idan an warke baza a hakura ba anga hanya shike nan sai aci gaba da kai bukatu.
Malam ya zauna ya nuna shi na Allah ne yana ta kawo aya da wa'azi ta yarda dashi malamin kirki ne baya shirka ashe a daki shi kadai yana can yana rafka Sabo yana bautar Aljani yana shirka wa Allah,gasu nan abinda akeyi kenan yanzu,ko yar karamar sana'a mutum ya fara sai ya fada malamai Sabo da yanzu masu hassada za fara masa binne binne a wajen na layoyi,dan a hanashi ci gaba,wani container zai siya kafin ya hada ta wai sai kaga har anje an masa binne binne ciki,abin haushi yanzu har gonaki na kauye akeyi,da anga gonar wane tayi kyau sai aje ayi maka kulunboto ta lalace kar a samu abin kirki,kar dai aci gaba.
Abin haushin kaga mace bata ci gaba wata ma ragwargwajajjiya Amma in kaji tana lissafin malamai abin sai ya Bada mamaki,kuma dai bata ci gaba ba tana nan yanda take sai baya ma da taci,a dinga hakuri da lamarin Allah mata,wasu ma su suke dauko HIV wajen bokaye su sawa mazan ace miji ne,wasu ayi amfani da ruwan ni'imarsu,aji tsoron Allah mata da Maza musulmi,shirka Babban laifine kar a mutu anayi wlh wuta har abada ba sassauci ba rangawame.
Idan ma kinayi ki roki Allah ya rabaki da shirka ki daina,duk rabonka bai wuce ka,abinda zaka samu shi zaka samu a duniya ba wanda ya Isa ya hana ko yasa.

Maimuna anyi kiba an kara haske anyi kyau sosai tana juya Hashim dinta domin magungunan mata take sha tana gyara jikinta,bata shirka iya maganin gyaranta take siya sai yanda take kunna Hashim dinta yana like mata,Zainura matar Ubale tana da kishiya anyi mata Amarya ta siyi me kwado dan mukulli,Zainura tasa Ubale baya sha'awar kowa sai ita,kishiyarta Asiya sam Ubale baya sha'awarta duk ranar kwananta,sannan ta siyi maganin sawa a tsohuwar rijiya na malkakar miji,itama Asiya taje takanas ta siyo me dan mukulli,duk ranar kwanan ko wacce sai ta kulle Ubale,ranar kwanan Zainura sai Asiya Tace Bismillahi na kulle Ubale,shike nan bazai sha'awar Zainura ba yanzu,Haka itama Ranar kwanan Asiya sai Zainura ta daga nata tace Bismillahi na kulle Ubale sai ta saki karfe fas shike nan,gaba daya sun hana Ubale sha'awar ko wacce cikinsu,ko wacce ta kulleshi,sunyiwa kansu sun cuceshi kuma.

Kwana Uku da gama shagalin kauyen,Salma yanzu ta iya girkin gargajiya da yawa komai ta iya,haka Umma tana koya mata dabarun mata idan sunyi aure,dole take sata tana amfani da ruwan zafi da gayyen magariya tana tsarki dasu,har wasu tsumin tana dan bata irin na yan mata Sabo da lafiyarta ta zauna daram tare da maganin infection na ciwon Sanyi da dawwamar da Ni'ima a jikin mace.
Na'im yana zaune yana duba wani littafin musulunci ya rufe fuskarsa da littafin Amma a zahiri ba karatu yake ba idonsa ya leko ta yar kafar littafin yana ta faman kallon Salma,ji yake kamar ma ya jawota jikinsa ya maidata cikinsa su zauna

1 Comments On KAMARSU CE DAYA
avatar
abdulkadir-lawan-yusuf

9 months ago

Reply

Littafi me ma'ana

Please Login or Register in order to submit comment