Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba kyau.

Irfan yace mu baka ganin abinda take mana sai ita kawai kace kana sonta zaka dinga raina mana hankali ba wanda ya isa yayiwa yarinya fada ko magana sai ka wani shige ciki kana fada,har Mummy baka kyalewa,ai sangarta ne da lalata mutum, na fada maka dai Allah karna kara ji kana mata gorin bata Sallah,tunda ba nasiha kake mata ba sai dai kawai ka fada mata bakar magana,ok baka ganin rashin kunyar da take mana nawa take Hunaif da Aisha sun girmeta,little kid ce sai kuyi hakuri har ta daina. Shuru Irfan Ya masa saida Na'im ya karaci fadansa sannan yayiwa guards nasa waya zai fita Hospital,kallon Salma yayi duk ta shiga damuwa akan zai fita,ita bata saba da kowa ba sai Na'im,ki shirya Driver zaizo ya dauko min ke ok?cikin farin ciki tace to bye Allah ya kaika lfy,Har Irfan saida ya kalli Salma domin shi baita jin tace Allah ba sai yau.

Kamar yanda yace da wuri ya dawo domin su fita da Salma bai turo Driver ba da kansa ya dawo, ta shirya tana Murna Mummy tace ba inda Na'im zai kaita wani yawo suna yawan kebewa,tsoron Mummy kar Salma a kuma ganinta da ciki ace Na'im ne yayi mata bare tace Kamarsu daya da Aljaninta.
Na'im yayi yayi ta fada masa dalilin hana shi fita da Salma amma Mummy tace kawai Bana son fitar ne sabo da tasan Na'im yanzu nan zaiki yarda da maganarta yace sai ya ganar da ita gaskiya,gaskiyar magana kuma Na'im tunda yake tare da Salma bai taba kawowa ransa cewar zai ko rike hannun Salma da niyyar yi mata wani abu dan yaji dadi ko har ta kai da ciki,duk kuwa da cewa Bai taba ganin me kyan sura irin Salma ba,kuma komai nata yayi masa amma Bai taba ma tunanin ko rike mata hannu da niyyar yin wani abu na Jin dadi ba,kamar kanwarsa blood sis yake ganinta.
Na'im Bai taba kai mace Hotel ko wani waje daban dan yayi romancing ba,a gidansu yake kirasu,baya zuwa ko ina yayi wani bad abu,Salma kuma tunda ta gano hakan shike nan ta Zama me gadi,kullum tana makale a corner na kusa da Room din Na'im,da mace tazo ko wace baza ta shiga dakin ba,sai ta koreta ko ta wanne haline,Mummy tana gani amma bata hanata ba dadi ma taji tunda ta fuskanci Na'im ya fara iskancewa shima nan gaba abin yawa zaiyi,Mummy ma turai tana taba ta,indai ba gani tayi da idonta ba kana wani abu marar kyau to baza ta zarge ka ba bare ta sa ma Ido har ya kai da ta ma fada,sai dai tayima addua,sai ma idan Salma ta fada mata tasan gaskiya ne Salma ke fadi shi yasa take musu fada,yanzu kuwa tunda taga Salma na kafawa ta tsare tasan da dalili.

Na'im yanzu haushinma Salma yake ji ta takura masa gaba daya ta hanashi sakewa,ko wacce duk ta rabashi dasu ko waya ya kira bata taba dauka duk wacce ya samo indai yace tazo gidansu tana zuwa sai ya nemeta ya rasa ta gudu kuma idan ya kira back baza ma tayi picking ba bare ta dawo,ya rasa me Salma ke musu kuma ko yaushe kamar aljana indai yace wata tazo sai yaga Salma a kusa da bedroom dinsa tana ko danna wayar Aisha ko computer ko tana Jin kida.
Amma yace sai ya gano me takewa matansa suna tserewa,Mummy kuma tace tunda ta gano Na'im ya koma neman mata gwara suje Kebbi ita da Dada kawai akwai wasu yan mata dama su biyu yan Uwanta, Na'im ya zabi daya ciki shima Irfan Ya dauka ayi musu auren zumunci a karfafa zumunci.

Dan haka Mummy tayi shiri ita da Dada suka tafi Kebbi wajen iyayen Rasheeda da Hamziyya a Nemo aurensu,kafin dangin uban Na'im suzo da Kansu.

Kafin Mummy taje Raheel ya rigata zuwa yayi suffar manyan kawayen wannan yara ya hure musu kunne kar su yarda ya basu dalili masu Zafi,iyayen yaran ma ya koma dattijo yaje a suffar abokan iyayen na kwarai ya zuga su tas ko ina saida ya dauresu da hujjoji sannan ya tafi,basu gane ba mutum bane.
Mummy suna zuwa Family house Aka kira mata Hamziyya da Rasheeda kyawawan yan mata tare da Iyayensu kaf maza da mata aka taru a babban Palo yasha alatu na alfarma,bayan gaisuwa da addua Mummy ta gabatar da Abinda ke tafe dasu,sai ko Yan matan suka tabe baki Hamziyya tace nidai wlh ina da wanda nake so,baya ga haka ma me zanyi da Bature wanda ya taso a turai wa yasan me suke aikatawa acan sai Allah,Rasheeda tace gane min hanya Mata ne yanzu sun lalace da son abin duniya da ance wane a turai yake da Zama ko ya taso ko acan yayi karatu ba ruwansu da halayensa sai ayi ta rubibi ana auresu,sai daga baya Ido ya raina fata agansu daga shaye shaye sai neman mata wasu ma abin yafi haka,duk da ba duk aka taru aka Zama daya ba ni dai wlh ba dani ba.

Uban Rasheeda ma ya goya mata baya,haka na Hamziyya ma,can kuma iyaye mata suka ce yo mu ai abinda mazaje suka ce bama ketarewa.
Halin Dan Adam kenan kaf danginsu Mummy ke taimaka musu ba abinda bata musu ba a rayuwa duk da cewa suna da Hali suma amma ta taimakesu da dama kan wasu abubuwa amma suka murza Ido sukace wlh baza su auri yan kasar waje ba Sam.Mummy tayi murmushin yake tace ba komai Allah tabbatar da abinda yake mafi alkhairi,Dada harda kuka anci mutuncin jikokinta,Mummy tace mene wannan ai ba komai bane suma suna da hujjarsu wlh banga laifinsu ba,washe gari Suka dawo gida ba nasara.

Dada ta tara Na'im,Irfan,Hunaif da Aisha tace ba wanda zata dagawa kafa tunda sun lalace ko wanne ya nemo matar aure za ayi masa musamman Na'im da shine Babba.
Na'im ganin watarana Salma tana harararsa tana fari da Ido tare da murguda baki shine Bai San mene a hausa ba kawai ya gallawa Dada Harara sannan ya murguda mata baki shima.
Dada ta rafka Salati tana tafa hannu tare da cewa ta tabbata Na'im ya lalace har rashin kunya ya koya ni kake murgudawa baki ko kunya baka ji ba jibgege dakai sai kace dan daudu?
Suka dinga dariya banda Na'im yace shi kam aure ba yanzu ba,Salma ce ta fito tasha wanka kamar yar Shugaban kasa yanda take shiga ta kece raini,taji ana zancen cewa Na'im sai yayi aure,kusa dashi taje ta zauna itama kamar an ce tazo,Dada ta gaisar da Mummy suka amsa da fara'a, Dada tace oh yar nan ko har ke za a hada ayiwa auren ne?Salma yau wai kunya take ji kuma har da jawo rigar Na'im ta rufe fuskarta,ya fisge abarsa yana dariya dungure mata kai yayi see this girl zakiyi mini yamutsatse da kaya(zaki yamutsa min kaya)

Irfan Ya tabe baki yace sai kace wata kunya ce da ita ma,kullum cikin rashin kunya take iri iri,ance hausa Fulani masu kunyane more especially na kauye amma wannan abinda takeyi ko wanda yaje kasar waje bazai yi ba,Harararsa tayi ta murguda baki tare da juya Ido,Na'im ya kalleta abin ya birgeshi yace dan kara yi mugani? Me? Salma ta tambaya,yace murgudede da nan ya nuna mata kumatu,tace sai idan zaka bani Dari biyar,aiko ya fyallo 1k yace gashi tayi masa guda tana murmushi tace to kalla,tayi masa da yawa,yace wannan ma yafi na dazu kyau,tace da zaka karo kudin sai na maka wanda yafi wannan,da wuri yace nawa nawa? Tace 2k me tsada ne wannan,ya bata kuwa ta kwalla tafi yanda yan kauye keyin tafi da hannu tare da murgudawa da yawa,Dada ce ta duma mata dundu a baya,yau nake jin yan iskan yara dama haka kukeyi,Amma ke kina gani Maman Na'im kike kyalesu lallai dole yara su lalace,ke Salamatu dake zan tafi ki zauna a gidana tunda kema duk daya kuke da yan turai zamuce ta tadda mujemu,Humm uhm wlh bazan je ba a nan zan zauna ko kin kaini sai na gudu nan gidan.

Mummy tace kyaleta Salma wannan me gadice a gidan nan ta dalilinta sun rage halayensu na banza,Dada tace ai shike nan tunda ke kike biye musu,Salma tace kuma ni ba sunana Salamatu ba Salma sunana inji Raheel,Na'im yace Raheel everything Raheel tsinanne Raheel Allah ya tsine masa da yawa da yawa,Salma ta cuno baki tace kana zagin kanka ne tunda kamarku daya ai,Allah yaye min nayi kama da Aljani dan iska cewar Na'im.

Dada ce ta katsesu tace to nidai na fada muku aure zaku nemo da wuri ko karuwace gwara a daura da ita Ku karata,Salma ta radawa Na'im alkawarina da kayi min a hospital wlh baza ka karya shi ba na fada ma ko zaka shekara Dubu ba aure sai ka cika min shi amma Sai idan Raheel Bai aureni ba kasan shi nake jira,sai yanzu Na'im ya tuna ma da maganar da sukayi a Hospital,y ace God....na zauna ina jiran shegen banza ko? Dada ta kallesu tare da tabe baki tace wannan kwai yan iska a gidan nan abinda sukeyi kenan,Irfan yace yafi haka ma,abinda wannan ita ko Sallah ba.....kafin ya karasa Na'im ya buga masa tsawa if u dear ehh.....shuru Irfan yayi tare da cewa na rufa mata asiri,Mummy ma saida ta Harare Irfan.

Salma tace nasan me zakace dai Bana Sallah to banayi din idan zan shiga Aljanna ka datse kofar mu gani,Na'im yace yama isa shi a wa yana can yana ta kansa, muje yau dole dole sai kinyi ta azahar ko? Ta makale kafada zatayi kuka wai baza tayi ba,yace to na daina kulaki nima,karki kara yi min magana,tace ae naji din,akan kawai kiyi sallar? Tace ae to sai dai idan jam'i zaka ja mu muyi tare zan bika,yace to za ayi,Irfan yace indai ji kunya(an dai ji kunya).
Dada tace na tafi gida ni wannan gidan naku na yahudawa ne bani iya yini daya ciki sai bakin ciki ya hallakani,tsohuwa driver dinta ya jata sai gida.

Yau Salma dai anbi Na'im sallah sunyi tare jam'i tayi azahar,magrib da isha duka Ukun yau sai gori take yiwa Irfan ta hanashi sakewa akan tayi Sallah har uku rana daya.
Mummy dariya ma take basu.
Washe gari da rigima Salma ta tashi ita kauyensu zata tafi taga lafiyar Ummitu da Affanta, kuma sai ta je can Borno state wajen su Malam Musa,tana Palo tana ta shure shure ita kadai,kowa yazo ya wuce ta ba wanda ya saurareta,Na'im yana fitowa cikin shirin Office yasha kyau yace schl zan mai dake naga abin naki harda naki iya shege shege.
Kauye sunce basu na Sonki,yar iska ke,yace ni na shinyeka na baka Baby fa(wai tuna mata yake su Ummitu sunce mata ita Karuwanci takeyi kuma sunce shine ya cinyeta ya mata ciki)

Salma tace kai ba acewa cinyewa iskanci ne fa,to fada min sunansa da Hausa ta rasa me zata ce tayi shuru tace amma ka canja word ko in English ne ka fada better akan da Hausa,Na'im yace shima turanci dan ba yare naka bane amma idan naka ne zaka ce yayi Bad da yawa word din.
To naji bani kudin mota zanje kauyen na dawo,muje Driver ya kaiki,so kake su kara ce min yar iska?,kawai ka bani kudi naje a taxi alright je ,je ki shirya,tana shiri ta fito tare da yiwa Mummy Sallama cewar zata dawo watarana ga kayanta nan baza ta dauki komai ba,suna fita Driver ya tsaida Taxi ya biya mata Drop ta shiga ta Wuce shi kuma ya tafi wajen aikinsa cike da tunanin Salma karfa ta bace,ko taki dawowa gidansu.

Maimuna matar Hashim har yanzu burinta ta kaiwa Malam Musa Karar Hashim ya takura mata,sai taje ta dinga Shan magungunan mata kuma idan ya makale mata tazo cikin gida tana terere dashi,harda kai kara wajen Malam,yau ma tun jiya Hashim yake abu daya har rana yaki hakura,har kuka tayi,aiko tanayin wanka ta fito sanye da hijab,taje har zaure wajen Malam Musa yana hutawa suka gaisa tace Malam ni dai bazan iya ba ta fashe da kuka dama tuni ya gano karar da ta kawo, da Masifa yace haba Maimuna Waiko baki da Ilmi ne ke?haka kikaga wasu matan nayi ko kunya bakya ji,yaro fa hakkinsa ne da hannuna na biya Sadaki,mene auren to?,ya kike so ayi miki ina ganinki me hankali,wancan lokacin na goya miko baya banda wannan kam,yaro ya wanke goma ya tsoma biyar ba abinda ya dameni,gonarsa ce abinda yaga dama shi zaiyi idan zaki iya zaman auren kiyi idan baki yi ga hanya tashi ki bani waje,da gudu Maimuna ta koma wajenta ta fada bed ta dinga kukan munafurci,Malam yace ja'irar yarinya ai gwara na nuna mata nima dan zamani ne, in banda iskanci wani wahala take Sha,munafukai suna so suna kaiwa kasuwa,yaron nan tunda na kaishi kaciya tun yana karami abarsa ba wata ta azo a gani bace amma ko Fall wire ce karewar tsayi ai ta saurara haka nan dai Malam ya dinga fada shi kadai a zaure.

Da yamma kuwa Maimuna ba a fito majalisar matan gidan da wuri ba saida ta gama komai ta fito tana cijewa,tana dingishi tare da nishi,matar shehu tace yau naga abinda ya isheni kamar daren farko ai tunda na ganki sai yanzu nasan mai afkuwa ta afku,ya maganin yayi miki?a hankali Muna ta zauna tana yarfe hannu tace uhm ba a cewa komai yau ai bajewa nayi na saki fanka tayi wa wajen fifita saida ta saisaita ya huce,nan mata sun kai goma suka saki shewa,Wata tace ni banga wani abin wahala anan ba,wannan Harka ta taimakon juna yaji dadi kiji ke kullum a korafi,wata ma tace Ni inama nice na samu me naci haka ai da kakata ta yanke saka,ai mu har jira muke magriba ta kawo jiki to mu ai Shar kuma cewar wata.nan ma aka sheke da dariya,
Suna cikin iskancin hirarsu sai fa Hashim ya shugo gidan zai wuce ta gabansu ko wacce ta zuba masa Ido ana kallon yanda yake nishadi na lallai fa yana jin dadin Harka da Munansa,yana shiga cikin gidan matan suka kalli Maimuna suna rafsa Shewa ga gwaninta ya shigo,Maimuna kuwa har yanga take wai ita ga wacce miji ke nacewa,Wata da batafi sa'ar Maimuna ba tace gafa Ogan naki sai washe baki akeyi kunne harda motsi,sai ki tashi kije,Maimuna tace kyaleshi can na gaji tana yarfe hannu,
Can kuwa saiga Hashim ya bude gidan kofarsu tare da kwalawa Maimuna kira Muna zo mana ya koma ciki,sai suka fara kus kus ana tofa Muna da rana da yamma ma ba a huta ba,yau kinga ta kanki,matar Malam musa surukar Muna wacce fitowarta kenan tace ai sai kije a bawa dana hakkinsa wlh a daina tauye masa hakki ehe,Maimuna harda yar kunya ta tashi da dan farin hijab dinta ta shige kamar walkiya.

Tana shiga Hashim ya harareta yace au ke idan na shigo ma sai na je nace kizo zaki zo? Munafukai aikinku kenan gulma a tsakar gida,na hanaki zuwa kinki ji,abinda ke burge Hashim da Maimunansa Tsafta ko ina na gidansa da kayansa da jikinta tsaf tsaf yana kamshi,bata son kazanta,bata fita hirar ta bar gidansu da dirty sai ta gyara komai tayi abinci,har wankin kayansa tana masa tayi masa guga bashi da matsala.
Abinci ta kawo masa jullof rice ta masu karamin karfi tayi dadi ta Sha curry me dadi,harda zobon da ta hada me sanyi.
Maimuna munafukar komawa tayi ta manne jikin Hashim tana shafa kirjinsa yana cin abinci,nan ta dinga masa abubuwa iri iri na tayar da sha'awa,dama kuma Kadan Hashim yake jira,nan take ya rikide ya fara murzar Maimuna har ya samu abinda yake so,Maimuna tana bada hadin kai sosai dan ba karamin dadi take ji ba,Hashim gwarzo ne Ashe Maimuna duk karya takewa mutan gida cewar Hashim ke damunta itace take tsokanoshi,dama tana so itama,banga laifin Maimuna nan ba tunda tana so sai tayi masa abinda kullum zai manne mata yayi mata ko yaushe.ta dinga kunnashi kawai yafi.

Salma an sauka Lafiya a kauye kamar irin ba matsala ta sallami Taxi ta shige gidan Affa tana kwala Sallama yamma lis,Affa yana saman tabarma shi da Ummitu sun zuge tsinken tsure ga yogourt a gabansu yau dadi ake sharba.suna jin Muryar Salma takaici ya kamasu nan Ummitu tace me bakin halice ta dawo goga mana talaucinta shi yasa Babanta ya rasu a wajen gadi.
Dauke ledar naman tayi tare da turawa a bayanta Affa ya Mike cike da masifa,Ummitu tana tayashi,Muzurun da suke kiwo na gidan Ashe yazo jikin Ummitu yayi arba da naman a bayanta haba ya fara dinner da shagali kafin kace me ya cinye naman tsiren tas yana lashe baki har kulin naman Bai bari ba ya lashe komai sannan yayi mika ya juya yayi tafiyarsa,Ummitu ana ta balbalawa Salma masifa ta bar musu gida wlh ko Zama baza tayi a gidansu ba,nan Affa ya gaji da hakurin da take bashi sandarsa ya sura ya kifaa Salma har wajen gari suna zuba gudu da tsere,Salma ga nacin tsiya bakinta baya shuru still tana gudu tana Affa kayi hakuri tana dariya kuma har sai da ya Rakata har gefen titi sannan ya dawo gida ya kyaleta yana ta zage zage,Tana ta maida numfashi da dan guntun hawayenta tana dariya, bugul sai ga Raheel yau da kansa yazo a dalleliyar uwar mota,tunanin Salma ko dai Na'im ne ko Raheel?ta rasa ganewa,murmushi ya sakar mata na birgewa tare da kallon so me ratsa zuciya nan ta gane Raheel ne,bude gaban motar tayi ta shige suka bace bat sai a Borno aka tsinto Salma kofar gidan Yan uwanta can nesa kadan.

Shehu ya ganeta suna hada Ido ya Galla mata harara,ita dariya ma ya bata yanda yayi mugun muni da yayi hararar saiko ta sheke da dariya,Shehu yace zaki ci ubanki zaki karaso ne,Salma tasan basu ma hakura ba kawai ta murgudawa Shehu baki,ta rike kugu ta Harareshi sannan tayi tafi da hannu,Haka Malam musa ma yana fitowa Shehu ya nuna masa abinda Salma keyi can nesa,Malam ma ya kalli Salma ya nunata da yatsa zaki ci ubanki ne akwai lokaci,Salma ta kara murguda baki da kugu tana rikewa tana murgudashi tace heeeee dama ba hakuri nazo baku ba tsokanarku kawai nazo yi wullu ta musu gwalo tayi tafiyarta,Raheel ya dauketa suka tafi ko ina kuma zasu je oho,amma dama Salma tun a gidan su Na'im ta tashi da son zuwa ta tsokani su Affa shi yasa tajashi suka dinga gudu a kauyen riiiiii,haka ma tayiwa su Shehu nasu kalar,takanas sabo da haka tasa Na'im yayi asarar kudin motarsa.









AsmaBaffa
[1/14, 5:14 PM] Sis Asma: 🏉KAMARSU CE DAYA🏉






56-60






Official






By
AsmaBaffa









Koda Raheel ya dauketa Bai ajiyeta ko ina ba sai wani daji ba a San ina bane yace danginsa ne a nan su gaisa,a zahiri kuwa babu wanda ke ganin Salma itama kuma cikin gida ta ganta na alfarma,tayi sati guda a cikin wannan gida da mutane daji suke gani,ba a kara ganin Salma ba sai a kasar Enugu can cikin wani kauyen Igbo,Ta dinga kalle kalle Duk kudin dake Hannunta wanda Na'im ya bata babu ko kwandala bata San ina suka shige ba,sabo da duk wani abu da wani zai bata to indai Raheel yazo sai an nemeshi an rasa,duk abinda Raheel ne ya bata kuwa baya bacewa,haka ya bata sabuwar waya Samsung latest ta kai Dubu Dari biyu,dubawa tayi taga fa lallai wayace sabuwa Raheel ya bata,nan take ta duba Balance taga kudi 10k,card din da Na'im ya bata a Hospital ta shiga dubawa dama Pakistan na India ne a jikinta me kyau da wando harda aljihu,a ciki ta zuba cards din,dubawa ta shiga yi Allah ya taimaketa Cards din suna ciki,nan take ta dannawa Na'im kira.

Na'im tunda Salma ta bar gidan Sam ya kasa yin komai,ya kasa samin nutsuwa,missing dinta yakeyi ga tunanin kar Raheel fa ya gudu da ita gaskiya idan ya dawo sai yayi mata magani ko zata warke,ko yaje aiki baya iya yin abin kirki sai tunanin Salma,gashi ba waya a hannunta,yanzu ko zaman Palo ya dainayi gaba daya,sai Bedroom,yan matan ma bashi da time nasu sai tunanin Ina Salma take yanzu?
Haka zai fito yayi ta faman kallon inda take Zama yana tuna acting dinta,haka dakinsa ma zai zauna yayi ta kallon inda take Zama,Abincin ma ya rage ci,Mummy tayi fadan har ta gaji,ya daina walwala Sam,kullum cikin kunci,har ya dan rame ya zabge,Dada ma da yaje mata sai data masa fada tace rashin mata ne da yayi aure da ya huta.
Sai dai yaje ya kwanta a room yayi shuru ko gefen Bed yana tagumi da tunanin Salma,ina ta shiga,sai yanzu ma yake ganin yayi gangancin barinta ta tafi tunda yasan da Aljanu tare da ita.

Salma ta cika 2wks Yau da kyar ya dawo daga wajen aiki zazzabi ya rufeshi sabo da rashin Salma,yana kwance yana rawar sanyi yau 2wks da tafiyar Salma amma bata dawo ba,yana hawaye yana rawar sanyi,Mummy ta kawo mishi magani yasha yana dai kwance kudundune cikin Blanket still,Kirrrrrrrrrrrrr wayar Salma ta shigo da bakuwar Number tsaki yaja tare dagawa da kyar tunaninsa ko Embassy ne ko Hospital nasa,muryar Salma yaji me shegen zaki da dandano, tace Hello Raheel,tana cewa Raheel ya tabbatar Salma ce,bai San sanda ya Mike zaune ba,yace Salma kina ina yanzu? Dariya tayi tace inye naji yau kayi hausa me kyau,stop kidding pls just tell me ina kike? Ta daga kai ta kalli wani gefen titi ansa Enugu tace ina Enugu yanzu Raheel ya kaini ya tafi kuma fa bani da kudin Mota ta furta da shagwaba,What? Ya furta da karfi,Nan take yace za Ana zo a daukeki just wait ki tsaya inda kike kin gane?,

Nan ya kashe wayar jiki na rawa ya kira wani manager dinsa na Company dake Enugu Eseme yace yayi sauri ga kanwarsa bata San gari ba yaje ya kaita airport yayi mata booking Flight back to Abuja,ba bata lokaci Eseme ya figo mota tare da kiran Salma tayi masa bayanin inda take abinka ga wayayya,yana zuwa ya hangota hadaddiya ta siyi Exotic da biscuit tana ta ci a gefen hanya gindin wata bishiya,taci ta koshi tasha ruwa, tana zuwa tace bani Dari biyar, ba musu ya mika mata ta biya masu lemo da biscuit tace su rike canji,Igbo da kudi sai mutunci da godiya kamar zasuyi mata sujjada.

Basu tsaya ko ina ba sai Airport yayi mata komai tazo Abuja lfy tana fitowa ta hango driver na Na'im yana jiranta,saida Suka gaisa yayi mata sannu da zuwa ta bishi sai gida,tun a mota driver yace Na'im bashi da lfy yana kwance,Salma a fara kuka tana a kara gudun motar tayi maza ta ganshi, fara bata hakuri yayi tare da cewa zazzabi ne kawai,ko kulashi bata yi ba.

Mota na parking a gidan ta fito da sauri Allah yasa ba kowa a Palo kawai ta wuce Bedroom dinsa da sauri ko knocking babu kawai ta fada ciki an samu dai tayi Sallama,tana shiga ta hangoshi saman Bed yana kwance amma zazzabin ya sauka,da sauri ta karasa tare da daura hannunta saman wuyansa taji ko yaji sauki,taji ba zazzabi ajiyar zuciya ta saki,tace Alhmdllh ta juya tare da

1 Comments On KAMARSU CE DAYA
avatar
abdulkadir-lawan-yusuf

9 months ago

Reply

Littafi me ma'ana

Please Login or Register in order to submit comment