Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

takeyi.

Affa da Ummitu suna can takaicin rashin ganin Salma ya ishesu ga talauci,can Affa ya kokawa yan uwansa matsalar da suke ciki tare da abinda Salma takeyi,nan take yan uwansa suka hadu suka zugashi, shi yasa watarana ma shawara da wasu matsala ce, cewar Salma idan ta dawo ya koreta kawai yayi mata korar kare Domin zata kasheshi tun kwanan sa Bai kare ba,ya dawo ya Sanarwa Ummitu,itama ta gano zancensu gaskiya ne tace Malam wannan gaskiya ne ka duba farar kafa irin ta yarinyar nan tunda aka bamu ita kullum talaucewa mukeyi bamu taba ci gaba ba,munfi kowa talauci a garin nan namu,yanzu akan nema mata magani duk abinda muka mallaka ya kare,saniya ko daya babu,kayan dakina,gonakinmu duk sun kare tas,a abinci har makwafta taimakon mu sukeyi kullum talauci yaki ci yaki cinyewa sai yawan Shan garin kwaki,duk ya tsotse mana jini da ruwa,Uban Salma mahaifi ya zalunce mu dama yasan yarsa haka take Ashe ya lika mana ya mutu ya barmu da wahala..shi yasa yan uwansa suka ki riketa.
Affa ya nunfasa yace yanzu na tsani yarinyar nan wlh Bana kauna na bude Ido na ganta a gidana,dama kaddara ce tasa na dauki jaraba,tunanina munyi yar kirki Ashe jaraba muka Raina da hannunmu,
Bamu karu da ita ko tsinke ba sai raguwa,Allah ya gani munyi iya yinmu munyi na Allah munyi na Annabi munyi na Binta dan haka taje can tayi yawon duniyarta,wannan rainin hankali ne yarinya gantalalliya cewar Ummitu.

Affa yace ko ta dawo idan kika barta ta shigo min gida to Allah ya isa ban yafe miki ba,na gaji da talauci,Ummitu tace oh Ashe gaskiyar bahaushe da yace tsintacciyar mage bata mage mun karbi Bala'i da hannunmu,Affa ya kara da ni dama Bana kaunar rike dan wani,dan wani ko jaraba Allah bai bamu ba mu hakura,dama dan kar nace ban so ne kice wani abu shi yasa nayi miki kara naga kina sonta.

Ummitu ta tafa hannu tare da cewa yo aini ta Dade da sire min dama kwadayin yara yasa na karba jaraba ai zamu yarda kwallon mangwaro mu huta da kuda,nan take shedan ya kara dasawa Affa da Ummitu kiyayyar Salma a zukatansu suka ji ba wacce suka tsana a duniya sama da Salma,suna ganin cutarsu ma takeyi tun farko.

Dan Adam kenan bashi da tabbas,yanzu da Salma bata samu matsala ba ko Allah yasa suna daukota kudi suka samu ta hanyarta ko wani abu da yanzu basu da sama Salma, baza suce komai ba, amma an musu kyautar ya guda tsakani da Allah sabo da kaddara ta sameta ta shafesu suna furta kalamai munana,dan Adam me manta alkhairi,inama Tall Man Baban Salma Bai rasu ba yaga cin Amana,butulci da manta alkhairi wajen Affa da Ummitu,farko sunyi bajinta amma at the end sun kasa jure kaddara wanda ita kanta ba ita ta dorawa kanta ba,
Yanzu da yarsu ce ta cikinsu baza suce komai ba ta Zama dolensu,dole su hakura su karbi komai,kuma baza su taba tsanarta ba,amma wannan sabo da basu San ciwonta ba basu San zafinta ba sun zobe ladansu wajen Allah,dama haka dan Adam yake bashi da tabbas kuma ba a iya masa musamman zamanin da muke ciki,daga naka sai naka,naka iya naka,kowa kansa ya sani baza ayiwa wani Uzuri ba.

Tun daga wannan rana Affa da Ummitu suka shiga bata Salma a cikin wannan kauyen,duk inda suka shiga sai sun zagi Salma cewar ko Sallah bata yi ga bin maza,bayan sun tabbatar aljanu gareta amma saboda kar aga laifinsu kar a zagesu idan sun kori Salma sai suka fadawa duniya cewar cikin shegenta yafi uku ma,sune suke rufa mata asiri suna kaita can Borno wajen danginta tana haihuwa sai ta dawo wasu kuma aka zubar.
Mutane Fulani na daji da jahilci sun yarda sabo da duk wasu shedu sun samu sabo da Salma duk wani sign na cikakkiyar yar bariki Aljani Raheel yasa ya fito fili an gani wanda a zahiri ba haka abin yake ba,kuma su Affa sun San gaskiyar magana.

Nan garin ya dauka duk majalisa zagin Salma akeyi haka mata ma ana tsine mata,mutanenmu hausawa basa yiwa mutum addua ko aji lafazi da kyakyawan zato idan ya aikata mugun abu kawai sai dai a fara tsinewa mutane ana aibatasu ana zaginsu,ba Uzuri kuma mutum baya hango nasa laifin sai na wani,abin haushi ma yawanci zargine kawai ba tabbas a kan abun.

Affa da Ummitu Rashin Imaninsu bai tsaya iya nan ba,Tall Man ya rasu hankali kwance tunaninsa ya tserar da yarsa daga wahalar duniya zata samu rayuwa me kyau ashe an bar baya da Kura ba a sani ba,shi yasa mutum bashi da wani Plan sai abinda Allah yayi.
Afda suka ce ta inda aka hau ta nan ake sauka muje Borno kawai mu wanke kanmu idan ta dawo idan zasu iya su rike yarsu can,haka sukaje Har Borno suka shiryawa dangin Salma karya da gaskiya su Malam Shehu da Malam Musa Baban Hashim harda Kuka ta bata musu suna da zuriya,suma dama kadan suke jira,zamanin haka yazo idan ka rasa iyaye to kafin a samu me rikeka tsakani da Allah ya tsaya maka sai an tona haka zakayi ta garari ana zaluntarka.
Malam Musa ya kalli Affa yace Allah ya saka muku da alkhairi,Allah ya biyaku da Aljanna,ko a gun Allah kun fita tas,Mu mun San rufawa wannan yarinya asiri kukayi amma ba komai zata zo ta samemu ace Zuriyarmu da cikin shege har yafi uku,nan muka tashi da safe sabo da ta Kware da bariki tace ya bace cikin daga jikinta makaryaciya,Ummitu tace ai zuwa tayi aka Markade jaririn yanzu ciki ko wata tara ne ana iya markadeshi a cire ai anci gaba,makaryaciya ce kar Ku yarda da zancenta,Shehu kanin Baban Salma yace to ai tayi kai,zata zo ne dama ubanta shine ya hada tunda kuwa haka take ai zumunci ba dole ba dole bane sai ka ajiye shi ina zaka iya rike irin wannan.
Ku duba tunda ta tafi ko leko mu batayi ba, nan Kuwa Shehu Murna yakeyi sabo da ya cinyewa Salma Gadonta kaf gonaki,fili, da wasu kadarori da Babanta Yayansa ya mutu ya bari.

haka bangaren mahaifiyar Salma su indai ba wani abu zaka basu ba to baka da mutunci a idonsu,komai a basu,idan kaga ana washe maka baki to sun San zaka basu wani abu,ita kanta Khairat Babar Salma ta bar sarkar Gold da rakuma biyar,tare da gona amma tuni suka je Nijar suka siyar dasu da komai suka handame kudin kaf tunaninsu sunci banza Salma ai yarinyace,duniya kenan Dangi a gyara Hali dan uwanka na jini ya mutu ya bar yara amma a rasa me rikesu,a cinye musu gado kuma still ana zaluntarsu.

Affa harda Hawayen karya,haka kowa ya tashi da tsanar Salma me tsanani dangi da kuma marikanta su Ummitu haka suka dawo Rigarsu Ransu fari Kal sun gama fita daga zagin dangin Salma dana mutanen gari.

Washe gari suna tashi da Safe Affa ya daga kasan pillow nasa yaga kudi sababbi yan Dubu Dubu har Naira Milliyan daya,daga sama yaji murya na masa magana cikin nutsuwa ance kudin shanunka ka siyo shanu Kaci gaba da kiwo,haka ma kuma arzikinka zai bunkasa tunda ka rabu da me kashin tsiya.
Affa ya rasa inda yaji maganar ji yayi kamar a kunne aka rada masa,amma yace yanda yaji haka zaiyi,nan ya tafi kasuwa sai ga Affa da shanu har bakwai maza da mata,ya siya musu kayan abinci da yawa,yayi musu dinkuna sababbi ya samu ya siyi gona har biyu na noma,daga nan yaci gaba da kiwonsa cikin nishadi da jin dadi arziki ya Karu,tun daga wannan rana Affa hanyoyin samu suke bude masa,mutane sai murna ake tayashi cewar gwara da ya rabu da Salma tsiya.
Readers tunaninku Affa da Ummitu Aljanu suka sasu aikata hakan rabuwa da Salma da zaginta?ba ruwan Aljanu a nan da gaske sukayi wannan abun,hali ne na Dan Adam dama yana faruwa.
Dama Raheel kuma yace bazai barsu suyi arzikin da zasu nemowa Salma magani ba,gashi sun ce baza su bar ma Salma ta shigo musu gida ba shi yasa ya basu kudin da ya lashe musu ya biya su arzikinsu ya dawo,sai suke ganin dama Salma ce me kashin talauci ita ta jawo musu.

Allah sarki Salma tana Hospital na Na'im hankalinta yanzu kuma yayi gida babu wanda take tunani sama da Ummitun ta da Affa tare da yan Uwanta na borno,yanzu kam tace ta gaji da ganin Raheel dole yasa a kaita kauyensu ta gano lafiyar su Ummitu domin bata da Kamarsu a duniya, su Mummy sun dawo daga ziyarar yan Uwa a Kebbi kullum sai sunzo duba Salma da kayan dubiya iri iri.
Irfan yana yawan zuwa susha Hira da Salma yana jin shirmenta.

10am Na'im ya shigo room din Salma cikin Hospital sanye yake cikin light blue shadda yasha kyau kayan hausawa suna masa kyau,sai kamshi ke tashi,mutane ana ta faman kallon bature da kayan hausawa,Salma sai da ta kalleshi ta kara kallonsa kamar ta cinyeshi haka take ji,harara ya watsa mata yau yan wulakancin da rashin mutunci ne a kansa fuskarsa ba rahma yace tashi mu tafi,zumbur ta dawo daga tunanin da ta Lula bata dauki ko tsinke a kayan da ya siya mata ba iya pant da bra ne kadai nasa a jikinta amma rigarta daya ganta da ita farko ita wata nurse ta wanke mata ta gogo mata ta bata tasa abarta sai bakin dankwali data dauka cikin kayansa ta yafa a kanta,duk da bata yi kwalliya ba amma tayi kyau ta kara fresh, dauko kayanki ne fa,ni Bana so ina dasu a gida wanda suka fi wannan kyau ma Raheel ya siya min,
Raheel din daya barki a wahala ga cikin ki ya fara girma kalli ana ganinsa a rigarki kadan amma ko zuwa bayayi yana dubaki,ai gwara ni Na'im da Raheel,Kwalla ta cika mata Ido tace wlh gwara Raheel dina ya fika,ok kin gane kenan yanzu ba Raheel bane ni? Raheel ne mana kai amma mugu ne wancan me kirki me sona sai ka dinga zuwa min a fuska biyu,awai wa zaka yiwa wayo yaro,Bai San sanda murmushi ya kwace masa ba,nine yaron?ae yaro mana danye ma da nawa ka girmeni?ta wani cuno baki tayi gaba yana Binta a baya,sai kallon hips nata yake suna ta rawa abin sha'awa.

Mota security nasa ya bude masa ya zauna a baya ta zauna gefensa Driver yaja,securities sukace Oga wannan kauyen ya kamata ace ayi escorting naka haka Mummy tace,no Need Ku je da sauran cars din gida I wl talk to her never mind,ok sir suka tafi,suma driver yajasu sai hanyar Abuja can rigar su Salma,sai murna takeyi zata ga Ummitu da Affanta har wakoki take rerawa.

Itace ke nuna hanyar kauyen nasu sai gasu a kofar gidan Affa,Na'im yasha kallon rugar fulani kauye daji sosai ana rayuwa a ciki,sai baza ido yake,Salma tace dan kauye kawai ba a saba da ganin hadadden gari ba sai yau ai sai ka tashi anzo,dariya yayi sosai wai nan ne hadadden gari,cike da murna ta bude mota harda wani dirowa kasa kamar Conductor tana mika da hammar gajiya,
Mutane nan take yan fulani suka baibaye motar ana kallo,nan aka gano cewar Salma Living things ce ta dawo daga yawon karuwanci,bariki tayi riba harda Bature tazo yanzu da turawa take harka cewar mutan gari,mata da Maza an cika kofar gidan Affa ba masaka tsinke,tuni Labari ya kai kunnen Affa dake wajen kiwon shanu,Ummitu ma haka nan ta bar girkin da takeyi ba mayafi ta fito,Salma ta kwalla kara tare da fadawa jikin Ummitu,Ummitu babu bata lokaci ta jefar da Salma tare da kwada mata Mari lafiyayye abinda bata taba yi ba,Na'im dake tsaye jikin mota ba shiri ya zaro ido waje,Ummitu tana kumfar baki ta damewa Salma riga tace Jama'a kowa ya matso yasha kallon Katon cikin dake jikin Salma,kowa ya sheda cewar karuwanci takeyi,Karuwace ta kara yin wani cikin bazai wuce wannan baturen ne yayi mata ba,
Na'im ya gane me suke nufi cikin gwarancinsa yace Mummy ina son Iskanci But me am...not....kafin ya karasa Ummitu ta kwalla da karfi tana Salati Kunji ko bayin Allah ko kunya babu wai yana son Iskanci,Sai mutane suka fara tsinewa Salma da Bature Na'im cewar yan iska kwarto da kwartuwa,ana musu ihu sosai an fara watsa musu kasa ana zagi,Na'im me halin turawa so yake lallai sai ya kare kansa kar a zargeshi,ya kara cewa a tsaya pls ni ina son Iskanci sosai da matane Amma....kafin yaci gaba waje ya kara daukan salati ana Allah ya tsine muku etc, da karfi yace ni ina son Mata ina son nayi iskanci,kuma ni ina son Iskanci Amma ni ba.....tas Affa da ya karaso wa wanke Na'im da mari nan take gefen Fuskarsa yayi jajir ya kumbura,(so yake ya fadi gaskiya wai yana son Iskanci da mata Amma shi bai taba Iskanci ba,ba dan iska bane,kuma bai Yiwa Salma ciki ba).

Salma abin yafi karfinta ta kasa gane kan su Affa,tunaninta kawai dan fushi sukayi da ita,taje wajen Affa ta fara bashi hakuri ya samu ya sa Sanda ya maketa ta fadi kasa sai da ta daina gani na wani lokaci,tana tashi Affa yace daga yau babu mu bake,ki kaddara baki taba saninmu ba,wlh na kara ganinki kofar gidana sai na miki gunduwa gunduwa,Ummitu ma ta Dora da yanzu kam bama sanki,jaraba me farar kafa,kin jawo mana talauci,karuwar banza Allah ya taimakemu mun farfado zaki kara dawowa ki jefa mu a Uku,Kije can kici gaba da duniyancinki,fuuuu Ummitu ta shiga gida kaf kayan Salma dama ta hada su har soson wanka duk akwatunanta sun kai goma sha biyu na zamani ta watso mata su waje,tace Maza ku bar mana gida kafin mutan gari da me gari su jefeku daga ke har bakin naki,Affa ya juya ya tafi wajen kiwon shanunsa cike da tausayin Salma Sabo da ba karya a zaman tare dole sai sun shaku da juna,amma yana tuna talauci da Halin da ya taba shiga sanadiyyar Salma kawai sai yaji farin ciki yaji ya tsaneta.
Ummitu kuwa tana shiga gida Salma ta bita a baya tana Kuka wiwi kamar me tana bata hakuri,har durkusawa takeyi kasa tana rike kafafunta tana kururuwar kuka tana gunji ta cika unguwar,ta dinga birgima a kasa tana tsala ihu tana su yafe mata baza ta kara ba,amma ina,bin Ummitu tayi cikin gidan tana roko Amma Ummitu ta rufe ido ta jawota kamar wani kayan wanki tun daga Cikin gida kirrrrr a kasa ta watso Salma waje,Salma zata Bita again Ummitu tasa kafa ta harbota baya,duk me Imani sai ya tausayawa Salma a wannan lokacin,a wajen ta tsuguna tare da dun kulewa waje daya,Na'im takaicin Sharrin da akayi masa ta dalilin Salma yasa Driver yace suyi tafiyarsu matsalarsu ce,
Mutane duk su. Watse sai Salma kadai a kofar gidan ta dunkule waje daya tana kuka.

Na'im har sunyi Nisa yaji hankalinsa bai kwanta ba yanda yaji tausayin Salma,Driver yasa ya juya su koma kauyen,shi kanshi Driver yaji dadi kaga Doctor Me Imani,suna komawa Salma ya hango ita daya a kofar gidan ta dunkule tana Kuka akwatunanta a gefe a watse,Driver ya fito ya kwashi akwatuna ya zuba a Boot,Na'im yaje gaban Salma ya riko hannunta sai lokacin ta dago fuskarta ta kalleshi Amma saída tayi Murmushi Sabo da kauna ganinsa take Raheel ne,nan take ta fada jikinsa tare da rungumeshi tana ta Kukanta ya lallasheta tare da cewa muje na kaiki Borno state wajen danginki ?karki sawa kanki damuwa abin zai kara rikice miki Ok,hawayenta ta share ta shiga motar kamar dazu suka juya motarsu tare da Barin kofar gidan Affa.

Ganin Salma da gaske ta tafi Saida Ummitu itama tayi hawaye da Kuka sosai na shakuwar zaman tare,amma dai ai sun huta a ganinsu.
Direct airport Driver ya kaisu cikin kayan Salma akwati daya suka dauka yayi musu booking Flight yacewa Driver ya koma gida ya kai masa dukkan akwatunan Salma Part dinsa kuma yacewa Mummy ya tafi business meeting Borno state zuwa can dare zai dawo.

Salma dama Raheel ya sa ta saba da shiga jirage n sama ya koya mata komai,tana kusa da Na'im a sit ta kwantar da kanta saman kafadarsa Bai hanata ba don turai ta ratsashi ita kuma gani take fa Raheel ne.
Suna sauka taxi lafiyayya ya daukar musu Drop har gidan Su Salma gaskiya talakawane dangin Salma cewar Na'im a ransa,Malam Musa da Shehu suka tarar a kofar gidan saman tabarma katuwa suna hirar zumunci dama dukansu cikin gida daya suke gidan yawa gaba daya Family kowa da wajensa.
Suna ganin Salma da Bature suka Mike tsaye,Malam Musa yace Salma....ina ganinki me hankali Ashe abinda Affanki suka fada mana gaskiya ne?to maza sanki kanin kafarki ki bar nan bamu ba ke,munafuka Sumi Sumi cewar Shehu,wanda ya hada zumunci ya raba tunda baya raye ai ba dole kije can ki nemi danginki bamu ba,au har wani cikin kika kara zuwa dashi?mu ga yan iska ko?sabo da kin raina mana hankali harda zuwa ma a gabanmu da Bature,Na'im zaiyi magana kenan Malam Musa yace ahir dinka me Jan kunne ka kiyaye mu wato ka koyo hausa kazo munafuki kuyi gaba to.

Hashim ne ya fito yaga abinda akeyi yace dan Allah Ku daina haka Baba kuyi mata Uzuri Ku saurareta,me yasa hausawa muke hakane gamu musulmai amma mune muke abinda ya kamata ace yahudu ne keyi?babban yatsa Na'im ya dagawa Hashim irin ya birgeshi,Hashim yasa hannu gefen kunne ya kame yayi wa Na'im irin wai Sara masa yanda sojoji keyi,
Salma na bada hakuri amma sai sauran dangi ma da matan gida suka fito tare da yowa caaaa kan Salma suna korarta,Hashim kadai ne yake bin bayan Salma,
Salma ta tafi kenan zata zube gwiwoyinta a kasa domin rokar gafararsu ta basu hakuri caraf Na'im ya riketa tare da janta cikin Taxi din da suka zo cike da fushi me tsanani, kawai yace a maidasu airport.

Mutanen dangi sukace Umma ta gaida ashsha dama nan akafi kauri a Karuwanci.







Sharhi readers fa

AsmaBaffa
[1/14, 5:14 PM] Sis Asma: 🏉KAMARSU CE DAYA🏉






46-50






Official








By
AsmaBaffa








Basu tsaya ko ina ba sai airport Salma kanta na a saman cinyar Na'im cikin jirgi tana ta faman rafsa kuka idonta ya kimbura,da kyar ma ya dan lallasheta ta dan rage Kukanta,har suka dawo cikin Abuja gidan su Na'im lokacin magrib tayi,yau ba yanga da wuri ya fita tana binsa a baya har palo,Momma sun idar da Sallah suna palo zasu fara Dinner Na'im ya shugo tare da Salma,
Mummy tace ya na ganka da Salma dama ba a kaita ba?relax Momma zani fada maku anjima,Aisha dauka nata ka bata room daya a gidan nan,ba wanda yace komai haka Salma tayiwa Mummy sannu da gida ta wuce,kanta a sama tana so tace ita Raheel zata bi room dinsa amma tana taunawa sunce ba shi bane.

Wanka tayi ta leko ta jikin kofarta daga ita sai towel duk suna palon,a hankali tace Aisha jeki dakin Bro naku kice ya baki kaya zan sa,ba a ganin Salma sai daí maganarta ta jikin kofa.

Aisha tunda Salma ta tona mata asiri take tsoronta da Sauri taje tayiwa Na'im knocking daga shi sai singlet da 3qtr yasha kyau yace lfy?Salmanka tace ka bata kayan da zata Sa wai,
Sai lokacin ya tuna kayanta suna part nasa maimakon ya bata akwatunanta sai ya bude ya dauko Inner bra da pant,da riga da skert na jar Atamfa Holand yar gaske,kayan kwalliya ma budewa yayi ya ebo wasu ya Bada ungo kai mata,ka bayar a kai mata kayanta mana gaba daya me zakayi dasu?
Ina ne ruwanki? ina da reason ki daina shiga cikin lamarina banza shashasha dan Iska.
Allah baka hakuri cewar Aisha,yace Ameen.

Tana bawa Salma itama bata ce a kawo mata kayanta ba kawai wanda ya bata da su tayi amfani,zama tayi ta tsara kwalliya kamar zataje Dinner.
Kamar a saceta,yayinda Na'im tuni yana palo ya gama bawa Mummy da yan uwansa labarin abinda ya faru kaf, kitchen Mummy ta shiga tace bari nazo, cikin gwarancinsa yace wa Irfan cikin Rada kar wani yaji ya furta suna so suna she min ina cinye mashe,Salma fa wai na shinye ta ni na bata kato kato Wannan Baby, shi kanshi Irfan ba wata hausar ce ta ratsashi ba amma yafi Na'im yace kyale su ba Ilmi jahilceni suke ma(wai Jahiltarka sukayi yake nufi Irfan) sunji tausayin Salma,Mummy tace ta zauna dasu kawai har aga me Allah zaiyi,Aisha kirawota aci abinci,kafin Aisha ta mike wani kamshi ya dakesu ba shiri kowannensu ya dago kai Salma ce kamar yar India atamfar tayi mata kyau Dinkin ma ko yayinsa ba a a fara ba,ba wanda ya taba ganin irinsa ya hadu karshe ya kamata cif cif.
Irfan yaja ajiyar zuciya,Hunaif yace ya salam irin wannan ake nema,Na'im ya Galla masa harara yana hade rai,Aisha tace wow kinyi kyau Salma,Mummy kuwa masha'allah tace Salma tayi murmushi tare da jan kujera daya a dining kamar gidansu ta zauna itama kamar me rayuwa a turai ba ruwanta da wani kara komai normal kamar yar gida.

Kowa yana zaune a dining yayi serving kansa yana ci banda Salma,Mummy tace ke kuma me kike jira?baki ta turo cike da shagwaba tace ni Raheel ne zai zuba min shi nake jira Raheel dina ya saba min kullum shi yake zuba min tun ina kauyenmu yanzu kuma ya shareni, Allah idan bai zuba min ba Bazan taba ci ba.

Kowannensu sakin baki yayi yanda take zuba shagwaba kamar zata narke,
Na'im wani zir zir zir yake ji a Cikin Jininsa,Mummy tace kana ji to Raheel,haushi yaji tare da cewa nifa ba Raheel bane Momma ki daina hadani da wani dan iska can,Salma ta kwalla tafi cike da tsiwa tace wlh ba dan iska bane ehe,kuma sai ka zuba min naci,me zakina iya ci? Na'im ya tambaya, Chips da kifi,shi ya zuba mata tare da tura mata,tana ci tana kallon Na'im sonsa yana kara ratsata,ji take sai yanzu ma take son Raheel,yanzu ta fara sonsa.
Irfan yana gamawa ya mike yace Momma Na fita cinema,Da Sauri Salma tace wlh ba can zai je ba sunyi da wata budurwarsa Hanifa wajenta zaije zasu sheke aya karki barshi Mummy.
Mummy tace Irfan shiga room dinka,nan take Mum tayi waya tace a tsare mata gida kar su bar yaranta su fita ko kofar gida sai gobe.
Irfan ya kalli Salma yace Munafuka ya wuce room dinsa cike da borin kunya,Aisha najin an fara tona musu asiri ta sulale ta bar palon,haka Hunaif ma,Mummy tace Gwara da Allah ya kawoki Salma mutum yana shuka tsiya ki fada min ta mike tare da musu sai da Safe ta haura side nata,daga Salma sai Na'im suka rage suna cin abinci,mikewa yayi ya koma bedroom nasa ba tare da yace komai ba, ya dauko Beer dinsa me tsada zai dan kwankwada a dakinsa Ya bude kenan sai ga Salma ta shugo da Sauri ta kwace kwalabar ta kai toilet ta zubar ta dawo ta jefa kwalba a

1 Comments On KAMARSU CE DAYA
avatar
abdulkadir-lawan-yusuf

9 months ago

Reply

Littafi me ma'ana

Please Login or Register in order to submit comment