Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta hakura mu shirya,Mummy harda jin son Zainura a ranta ita kuwa Zainura so take ta dinga cusawa Aisha takaici shi yasa tace sai sunyi zumunci dole hhh

6:30pm Na'im ya shigo a gajiye Salma tana part dinsa tana jiransa taci uban wanka tana ta kumbura kamar zata fashe,Da Sallama ya shigo ta Mike tsaye ya nuna shi Sam bai San tana fushi ba,ya rungumeta tare da dagata sama ya direta saman Sofa yana dariya tare da cewa kinyi kyau Wifey,wa ya taba min ke naga kamar fushi kike,fada min shi nayi maganinsa,Salma tace kaine,ya zaro Ido yace da me?kaki tafiya dani,idan naje dake wa zai gyara min part dina? Wa zai min abinci ko yan aiki kike so suyi min? Salma tace to ai ni nayi ma yau Zainura ce tace haka nake ma a kauye wai naci gaba,Yau dai sai mun kalli CD da wayarmu da album na kauye muga me akayi ciki.

Da kanta ta shirya Na'im yau da kyar tana kunya ta sa masa kaya yaci abinci ya dauko wayar Kauye Cd plate da Album,ya kira kowa na gidan suka taru a Palo ya kuna Cd yasa plate kowa ya nutsu za a fara kallon shagalin biki.

Salma da Na'im aka fara nuna hotonsu tare da adduar aure wani take na Larabawa yana tashi,Zainura tana kusa da Irfan,Mummy da Hunaif ga Aisha a gefe.
Kauyen su Zainura ya bayyana,sai aka nuno wajen Daurin aure,motoci guda 8,ga Malam,su Me gari,Zainura tana laaaaaaaa wlh ga Babana,Baffa gashi ya wuce yeeee Irfan yace yana ina ta nuna musu shi kamar an shigarta Aljanna,daya bayan daya take ga Baban Zainab,yayan Jamila,mijin wance haka take ta yi kowa sai da ta fadi,aka dawo sai ga Ango Na'im cikin shadda Ruwan toka yasha kyau,da frnds nasa duk inda yayi tare da Abubakar,zainura tana musu fashin baki,nan har aka gama daurin aure ana ta hada hada,sai ga cikin gidan Malam an nuno Mata ana saukewa ana dorawa,Umma da Anty Rukayya na hada hada cikin Murna,Na'im da abokai na shige da fice, Anty Rukayya sai kula take da Ango haka Umma da Malam,Na'im yaga yanda suke masa tuni ya fara Hawaye a zaune,Aka tafi gidan yan Matan Amarya Salma,Salma ansha kyau irin color na Na'im,ana ta hira ana cin abinci,sai ga Ango yanda yake manne da Amarya,Haka Amarya tana ta zuba shagwaba yana bata abinci a baki tana bashi,Zainura tana kara karanta abin da wanda ma ba a nuna ba,Har aka zo aka gaisar da su Umma ana ta pics,anzo wajen kida yanda aka rakashe,ana zuwa wajen me rawar Michael Jackson Na'im da Salma suna hawaye suna dariya,yan dakin ma sai dariya suke,ana ganin irin rawar da mutanen kauye sukeyi,ga yanda Amarya take ta faman ji da mijinta shima haka suna daukin juna,kamar su cinye juna, an sa wakar Ado gwanja ko anki ko anso nine gwanja sai ga Zainura ta shige fili tana ta takawa,kowa ya kalleta ana dariya a palon Salma da Na'im suna mata liki,Zainab ma ta shigo tana juyawa haukar Zainab harda girgiza Irfan Ya dinga dariya dasu Aisha,ba kamar Hunaif ma yanda yace sai an taro me rawar Michael Jackson sun kara gani,sai da aka haska komai,Dada tana cikin kallo da Mummy suma sai hawaye sabo da tausayi abin ya taba musu zuciya yanda Malam sukayi halacci da mutanen kauyen tare da frnds na Na'im da Salma,Aisha tace ina son wannan Anty Rukayyan she is wise enough.

Na'im ya kashe bayan an gama,Zainura tace akwai a wannan wayar har wanda ba na biki ba kunna a gani,nan ma aka fara danno na waya daya bayan daya.
Sai next page zaku ji mene a wayar tasu tare da Album.












AsmaBaffa[1/14, 5:14 PM] Sis Asma: 🏉KAMARSU CE DAYA🏉







131-135 136-140










Official





By
AsmaBaffa







Fans kun rage Sharhi gaskiya zan rage yawan typing.❤❤❤❤❤❤

ZEEMAMA wannan page naki ne.






Waya ya kunna tare da sa mata USB ya jona da Computer yanda kowa zai gani,video ta farko Salma da Na'im suke ta hira cike da so suna can bayan gari a kauyen wurin wasu bishiyu na mangoes,Sai wanda take wanke masa kaya da guga yana daukanta shima yana daukan kansa,Sai su Umma da Malam ma suna ciki dasu,wani suna girki a kitchen tare,suna cin abinci,har aka dawo kan na bikinsu,nan ma waje kala kala,sai ranar da aka kawo Salma dakin miji,tana Amarya a lullube ya daukesu tare suna yiwa juna kallon so,sai kuma wanda sukayi bayan bikin da gidan aurensu na kauye gaba daya ko ina,wasu ma kunya suke ji ana gani dasu Mummy suna rashin kunya,Har suka koma kan pics,Malam Umma dasu iri iri,sai nasa da Salma ba kalar da basu dauka ba,har na biki,bayan sun gama na waya suka koma Album aka Sha kallo,wasu abin tausayi wasu dariya haka dai aka gama.

Na'im da Salma sai tunani sukeyi ko zasu tuna amma sun kasa,Na'im yace Allah yasa na tuna ko ban tuna ba sai na koma kauyen nan gaskiya,Salma tace wlh kuwa,nan suka mayar da komai suka boye abinsu,Salma tabi bayan Na'im part dinsa,yana saman bed yana faman kokarin tuna su Malam,Salma ta zauna tare da cewa Dan Allah Honey ka bari naje wajen su Ummitu da dangina,ni yanzu su suka dameni, mutanen da basu damu dake ba shine zaki je suci miki mutunci ko?Salma tace ae naji amma ai iyaye na,kai kana cikin naka dangin ni kuma ina nawa?ya kamata ka tausaya min, kema kin San wahala zaki sha kawai baza su yarda dake ba muyi rayuwarmu idan sun gaji sai su nemeki, Fara sheshekar kuka tayi,Na'im yace akan haka kike wannan kukan?tace ni bazan taba samun kwanciyar hankali ba matukar bani da kowa nawa for God sake wlh bazan iya wani aure ba idan kace bazanje ba sai dai mu rabu gaskiya,ni da dangina kace bazan je ba,kuma Su Affa ko me suka min ai su suka raineni har na girma muka hadu.
Tunanina kai me daidaitani da dangina nane Ashe baka kaunata tunda kace bazan je ba,Na'im yace ikon Allah ni ba hanaki nayi ba Hajiya Salma ga Driver nan a dawo lfy,ni dai bazanje ba su kara wulakantani ba,kin San sau nawa naje nemanki wajensu lokacin da kika bace ba irin wulakancin da basu yi min ba amma na hakura still ina zuwa wajensu.

Amma ai sai ka barni naje haka idan basu yarda dani ba sai na dawo,ban hanaki bafa kije ga Driver nan idan ma da kanki zakiyi Driving sai kin dawo Allah kaiki lfy ya Mike tare da ficewarsa,Wani Bedroom din ya koma can daya part din ya kwanta saman bed yana tunanin halin Salma na yanzu,shi to ya zaiyi da ita ne wai bata Jin magana.
Salma kuma yanda yace taje tasan baya so ma taje kawai bata San manufarsa ba,amma zata ci gaba da rokonsa.
Na'im tunaninsa ma haushin da ta bashi da take wani ambatar wai sai dai su rabu,baza ta iya ba,tama raina masa hankali wlh amma zaiyi maganinta.

Wanka yayi ya shirya sosai yayi kyau tare da haurawa Part dinsa domin daukan Wayarsa ya hango Salma gefen Bed sai hawaye take,kallo daya kawai ya mata ya dauki wayarsa yayi waje abinsa,abin ya dameshi bai son Ganin Kukanta musamman da ya San bata da kowa yanzu na iyaye,Embassy yaje yayi abinda zaiyi ya dawo.
Salma ya hango tana bacci tayi dai dai saman Bed dinsa daga ita bm short da yar riga cikinta gaba daya a waje,nan take Hankalin Na'im ya fara tashi ya taimakawa kansa tare da shigewa Toilet ya fara wanka,yasan Koma ya nemi Salma ba yarda zatayi ba indai ba wajen danginta taje ba yaga ma hankalinta baya kan komai sai danginta.

Bayan ya shirya sai lokacin ta farka idonta yayi dan ja,gashinta ya rufe mata rabin Ido sai ya bada wani sexy look,Na'im ya kalleta nan take yaji wani farin ciki yana ratsashi Salma bata laifi a wajensa,bare da bata da abin Zafi barta idan shagwabar ta motsa to sai kallo,
Yanzu ma tana ganinsa ta rarrafo jikinsa zata hau ya goce ya matsa tare da cewa ki kwanta a bed dinki,kina taba ni dole zan miki dole abinda bakya so,ki kiyaye taba jikina,Salma ta wani Kebe zatayi kuka tace dan Allah ka barni naje wajen ko su Affa ne pls,Na'im yace na barki am serious kuje keda Zainura nasan ta fiki baki zata tare miki,nima idan komai yayi settling zanje na gaishesu,amma 1day na baki kacal,bari na miki booking flight sai kije har can Maiduguri suma 1day tal ki dawo,idan kika kara Allah kinji na rantse saina kwankwatsaki wlh,Salma dadi yasa ta rungumeshi tana shakar kamshinsa tare da cewa sai kace wata attaruhu kuma,Na'im yace uhm yanzu ai kin fara magana sabo da zaki tafi unguwa,

Salma da Murna ta sanarwa Zainura zata Rakata nan ta sanarwa Zainura tarihinta kaf,Zainura ta jinjina taji tausayinta tace lallai kinsha wahala Salma,bari na shirya yanzu har jirgi za a hau dani?Salma tana dariya tace ae Zainura tace yau sai nayi Sallar dare Nafeela Alquran.

Yau Salma tana murna gobe zata je wajen yan Uwa da wuri ta shirya cikin wata tsiyatacciyar Night Gown ta fito kamar Amarya tana zuba uban kamshi,harda shiga kitchen ta hadawa Na'im tea me kamshi da dadi ba madara ciki yanda taga yana Sha da dare.
Ta shigo sanye cikin Hijab dinta,tun kafin tazo kamshinta ya bigi hancin Na'im,Aiki yake a System,ya dago ya kalleta tayi wani irin kyau na mamaki,Tea din ta ajiye a kasa cike da nutsuwa ta zare Hijab dinta,Na'im ya kusa shakewa sabo da yanda yaga Salma kamar a Indian Film, gefensa ta zauna a kasa itama tare da wani kasa da murya barka da aiki,Na'im yace wato Salma sai na barki abu zakiyi abinda ya dace,tace me ka gani?yace yaushe ma rabon da kizo wajena haka sai na rokeki hakanma da kyar kike zowa sai kin ga dama,dan na barki kije Wajen Family naki shine zaki wani zo,to Bana so tunda badan Allah kikayi ba,ni dan Allah na barki zuwa can,tashi ki tafi room dinki kici gaba da kwana ke daya,

Salma taja ajiyar zuciya tace Wlh badan haka bane kawai yau nishadi naji ban san dalili ba kuma ma ai ina so dama na gyara halina,idan kace a'a taya zan gyara to,Allah yau ma Zainura tayi min fada sosai kuma naga ban kyauta ba shi yasa,amma tunda kace na tafi shike nan,ta Mike tana jira yace ta tsaya taji shuru har ta kai bakin kofa ta juyo da kanta tare da cewa zan tafi fa,yace ok,tace Sai da safe,yace Allah kaimu,tace Ameen tayi shuru kuma taki tafiya,ta kara cewa uhm ni dai zan tafi kuma,ta bashi dariya ya gimtse yace to a gaishesu.

Ta gaji da tsaiwa yana ta aikinsa,yace yawwa zo ki dauke tea dinki ma,ta taho kamar gaske zata dauka sai ta rufe system din,harara ya zuba mata,gabansa ta dawo kamar zata shige masa ciki,hannayensa ta riko da nata tare da waresu nan take ta shige kirjinsa ta hade kirjinsu waje daya,Na'im ya fara borin Iska irin baya so wanda a zahiri tuni ya tafi wata duniyar karfin Hali yake.
Salma kamar zata masa fyade haka ta hade bakinsu waje daya ta shiga tsotsa sosai tana masa wasu salon wanda Bai San ta sansu bama,nan Na'im yayi Surrender tare da rungumeta tsam a jikinsa kamar zai maidata cikinsa,dama kadan yake jira, saman Bed suka koma ba tare da sun sani ba,yasa hannu ya kashe light duf,
Nan take ya rabata da kayan jikinta shima haka Deep Romancing sukayi me dumama zuciya tare da tsumata,Salma taji dadi sosai shima haka,saida suka huta,ya rada mata fyade zaki min? Dukan wasa ta masa a kirji cike da shagwaba,a hankali yace da gani kin saba da wannan na yarda da Zainura munayi, yana shafa kirjinta yace ina fara wasa da wannan kika haukace,Salma ta boye fuska a kirjinsa tace nidai ka bata min jiki muje muyi wanka.
Tare sukayi wanka tare da kwanciya,tana manne jikinsa yace kyaleki nayi yau sabo da nan da 2wks zamu koma gidanmu da zamu zauna.
Salma tace hmmm Allah ya kaimu,yana shafa gashinta yace amma idan mun koma kema kin San ba mutunci,Salma tana murmushi tace ba komai nasan ma ka taba yi a kauye tunda kamin abubuwa da yawa yau banji Zafi ba a wajen kaga kuwa anyi ma.
Na'im kuwa wayo yayi mata cikin Romancing ya dubata ya San baiyi komai ba,zai wahala ace yayi Sex Virgin ce still,amma sai yace ai ba sau daya bama,domin da sau daya ne ina taba wajen sai kinyi kuka,Salma tace hakane shike nan Allah kaimu mu tare na daina tsoro tunda dama wahalar ta wuce tuni.

Washe gari Mummy tace ai bazai yuwu Salma da Zainura suje su kadai ba sabo da dole ayiwa dangin Salma bayanin aurenta maganar Aure bata yara bace kuma ba wasa bace,Haka Mummy da Dada suka shirya takanas suka bi flight suka fara Sauka a Borno state gidan su Shehu da Malam Musa,ganin masu kudi Salma tazo dasu ba wasa,Shehu duk da a wulakance suka karbesu amma sun sauraresu,Dada ta musu bayani Malam musa yace Allah sanya Alkhairi,Shehu yace na taba ganin iyaye mata da shiga sabgar Aure? Kuma za a rufe mu yar da take tamu shine za a mata auren bariki sai daga baya za a zo a sanar mana sabo da ba a daukemu da muhimmanci ba,ba a mai damu iyaye ba,to Allah ya bada zaman lfy me kuma zamu yi mu ai sai Ku tafi da abarku,Mummy da Dada suka dinga basu hakuri ana musu bayani amma sukace su fa basu ce komai ba kuma Salma dole dai tasu ce ba uban wani ya haifeta ba dan haka dole ta nemesu aure kuma Allah bada Lada suje kar a cika su da surutu.

Hashim ne kadai ya kai su Mummy bangarensa Maimuna ta musu sauka ta mutunci,kuma ya tsaya ya gane duk abinda su Mummy suka zo dashi ya rufawa Salma baya,haka dangin uwar Salma Ubale da Matarsa Iklima sunyi murna kuma sun fahimci komai tare da sa albarka.
Mummy tace su kwana wajen Hashim Salma da Zainura wajen Ubale da Iklima suka kwana cikin Jin dadi.

Washe gari sukayi shirin Tafiya Mummy ta bawa Hashim Dubu Dari wai idan Maimuna ta haihu ayi suna,ya dinga murna da godiya,haka Ubale ma ta bashi Dari,harda durkusawa dan Murna,ta bawa Malam Musa shima,haka Shehu uban yan son kudi nan take ya canja ya fara nunawa Salma so yana mata fara'a sabo da kudi,matan gidan kuma kaf Dubu Ashirin aka ba ko wacce ta ja jari sannan suka tafi.

Zainura tace Bala'i Wallahi Salma danginki son kudi garesu,jiba rashin mutuncin da suka mana,daga Hashim sai Ubale ne suka karbe mu amma sunji kudi sun rude Allah ya shirya gwara da basu suka raineki ba Alquran da tuni sun jona miki son kudi.

Abuja suka dawo basu koma gida ba Mummy tasa Driver ya wuce dasu kauyen su Affa,suna Sallma a gidan Affa yana gyarawa Akuyarsa igiya ya hango lallai Salma ce da iyayen barikinta,Ummitu ta fito da kwarya da gari ciki,Su Mummy suka mata Kwarjini da gani an San kudi ya zauna musu,shuru sukayi basu ce su shugo ba kuma basu ce ga wajen Zama ba,Zainura ne ta shiga tare da rafka Sallama ta hango tabarma a jikin bishiya kamar gidansu ta jawo ta shimfida tace Ku shugo Mana,Affa dai basu iya magana ba sunga Mummy kalar Naira ba wasa,Bayan sunwa Kansu masauki nan Mummy tace Ku zauna Malam za muyi magana akan hanya muke,da kyar Affa ya zauna can nesa tare da zaburowa da Masifa muna saurarenki.

Mummy ta fara da Nasiha haka Dada ma ta nuna musu hakkin Salma dake Kansu a Matsayinsu na marikanta sannan ta musu bayanin komai har auren Salma,tare da fahimtar dasu su Affa sun San gaskiya amma suka take sani wai dama to mene a ciki sai me kuma dan tayi aure Allah sanya Alkhairi,Mummy sunga rashin Imanin su Affa,Salma kuwa murna tayi tasan an samu ci gaba domin da ace dane basu isa ma sun shiga gidan Affa ba,amma yanzu har sauraransu sunyi ai abin farin ciki ne,Mummy taga harkar ta su Ummitu ba mutunci ciki tace to Salma zamu barki a nan gobe kya dawo ko?
Affa yace ina? Yanda kuka zo da abarku Ku tafi da ita,Dada tace oh Ku kuwa bayin Allah kamar baku San darajar Dan Adam ba?Ummitu tayi tsagal tace kija girmanki iya mun fiki Sanin wace Salma ba ruwanku,Salma tace ya isa a bar zancen nan take Salma ta rubuta address kamar yanda ta bawa su Malam Musa haka ta rubuta Address na inda take da Phone Number ta mikawa Ummitu tace a kyale zancen haka gashi nan duk ranar da kuka huce kuka gane gaskiya zaku nemeni,Mummy Ku taso mu tafi,Nan Mummy ta zaro makudan kudi ta mikawa Affa ya buga tsalle yace bada ni ba,baza a siyeni da kudi ba,na karbi Dubu Dari nazo ina asarar milliyan daya ina dalili kuje da tsiyarku.

Mummy tayi murmushi ta maida jaka abinta,Zainura tace Alquran baku da rabo,
Salma tace Zainura Bana so muje kawai ina ruwanki iyayena ne fa,Zainura tace Allah ya huci zuciyarku Affa sai dai ayi hakuri damu na daukar muku tabarma ba izni,Affa dan Fulani da mugunta masu taurin kai yace can da matsalarku zaki zo da kafa kamar ta sauro ke ga marar kunya ko ya fadawa Zainura,Zainura ta dinga kunshe dariya har sai da suka fito tayi abarta wai kafata kamar ta Sauro,Dada suna dariya suka ce ai gaskiya ya fada,Mummy tace Amma ko a yan Fulani wannan na daban ne wajen taurin kai,aya hadisi duk basuyi ba,Salma tayi dariya tace ai baku gani ba da muka zo da Na'im ba arziki,hhhh Dada tace shu'umi shi yasa yace bazai zo ba Ashe shi yaga abinda ya gani,Salma tace ai da kun gani da kunsha mamaki,Zainura tace Allah sa dai bai kwadeshi da sanda ba,Salma tace Saura kadan wlh hhhh sai dariya,Mummy tace ki rabu dasu duniya zata nuna musu gaskiya Allah zai ganar dasu addua kawai zakiyi ki kwantar da hankali har gida zasu sameki,muma ai iyayenki ne ba abinda baza muyi miki ba,Dan ma Memory dinku bai dawo ba sai kinfi kowa gatan iyaye,gasu Malam Magaji,ga danginki na Borno,gamu muma,ga su Affa idan Allah ya ganar dasu kinga ke iyaye ko ina,dadi Salma taji tana dariya sosai taji hankalinta ya kwanta.

Tunda suka dauko hanyar dawowa City Zainura take ta labarin jirgin da suka hau,yau ta hau jirgi har Borno itakam da sa'a take a duniya.
Dada tana ta dariya tace Wai jikata yaushe zaki zo min ne ko kwana Uku muyi tare a gidana,Mummy tace ai sai dai Irfan ko Hunaif ya kawo ta idan ta shirya,Zainura tace ko Aisha ta kaini ba,fada zakuyi a hanya cewar Salma,Kiran Na'im ne ya shigo wayarta,sai da ta kusa tsinkewa ta daga hello ta furta cikin nishadi,ya aiki? Alhmdllh dazu na kiraka baka dauka ba,Ina Office ne,ya sun huce?Salma tace kadan ba har yau dai basu huce ba amma dai ba irin da ba,yace ok Allah yasa to su huce gaba daya,tace Ameen ina su Mummy?,gasu muna hanyar gida mun kusa karasowa,yaji sanyi a ransa tare da cewa can't wait to see u Baby missed u Badly,Salma su Mummy na kusa tace zan maka text ya gane baza ta iya magana ba sabo dasu Mummy,kiss ya mata ta waya tare da cewa ina jiranki a part dina ba sai kinyi text din ba,need to see u Hearty am just wanna feel u,Murmushi Salma tayi me Sauti tare da furta me too a hankali ta kashe wayar ta wani basar irin fa ba wani abu akayi ba.

Zainura tana can tana kallon gari har suka shigo cikin gida ta hango Irfan ya fito da shirin fita yayi hanyar wajen Zalleliyar motarsa,da sauri ta danna glass yayi kasa ta leko da Kanta tare da kwalla masa kira Irfan dan gayu....da sauri ya juyo ya San dama sai ita,dariya yayi tare da dago mata hannu,zai shiga mota kenan tace ka tsaya labari zan baka,motar na parking ta fito a nutse ta karasa wajensa tare da cewa ko kace Sannu da zuwa ya hanya,ya kalleta kawai yace to sannu da hanya,tace yawwa dama fada maka zanyi ta kare maka gaba daya ka daina min iyayi da kuri dan jirgin da kake jin ka hau nima na shiga kuma me zaka nuna min,kai kenan ka dauki photo a jirgi to nima na shiga dai.

Murmushi yayi tare da cewa ai ke na kauye kika shiga na Nigeria ni fa?duk dai sunansu jirgi ko,ina zaka je da yamma haka? Yace masallaci,Masallacin sai anje a mota sabo da sangarta,Mota ya shiga tare da cewa sai na dawo kya bani Labarin naki sauri nake,yau Hunaif ne nawa shi zan bawa Labarina sai na kureshi yau naji a ina karyar wankan nasa ya tsaya,Irfan yace sai dai kiyiwa Aisha,Zainura tace ai nafi karfinta Yasin Hunaif kadai zan kure yau naga shi yafi kowa rainani,Irfan yace to shi dai kika masa Zaneki zaiyi ba ruwana,jeka kawai bari naje na huta,Irfan yaja motarsa ya tafi,Zainura tana shiga gidan,tana shiga Hunaif ya kalleta tare da cewa ai na dauka an maida ke kauye,Zainura tace ka fara kuka ko? Allah sarki ai baza a maida ni ba ka kwantar da hankalinka ba sai ka fada min ba nasan sona ya kamaka Ashe kana nan kana ta tunani na ko an maidani zaka shiga uku ko?Hunaif ya dinga dariya tare da girgiza kai domin shi Zainura tafi karfinsa a magana,tace yaushe rabon da ka hau jirgi?kamar abin kirki yace tun last yrs,ta sheke da dariya tace to ni ba ajinka bace domin jiya i yanzu ina ta shawagi a sararin samaniya kamar tsuntsu,kaifa har shekara guda idan kuri ne kafi kowa,ni kuwa jiya me tukin jirgin da kansa yazo har wajena yace yan mata kece Zainura ko? Nace ae ya kalleni yace Zeena Baby kin tafi dani daga yau idan kina so kullum kizo zamu dinga yawo cikin gajimare,yau ma Mummy ce ta hanani amma da a jirgi za a saukeni a cikin gidan nan,Hunaif yace
Shi kuma duk ina tukin jirgin?ya barshi kuna yawo a sama yazo wajenki?Zainura ta zaro Ido tare da cewa sabo da na isa, jeki ki huta kizo yau na cinyeki a game Idan Irfan yazo kije kici gaba da raina masa hankali shi zai dauki shirmenki.

Aisha da tsokana ta fito tace a'a ba sabanba an hau jirgi duk an damu mutane a gida,yar talakawan kauye,Zainura taji haushi yau a maganar Aisha amma sai ta kyaleta bata ce komai ba,sabo da ta fuskanci sam Aisha wulakanta talaka ne da ita ba irin su Hunaif ba za ayi wasa da dariya,ita Zainura bata saba shuru shuru ba tafi so ayi wasa da dariya ana nishadi ta tsani shuru shuru.

Salma bedroom dinta ta shiga tare da sheka wanka ta shirya tsab ta dau wanka cikin wata yar Gown mitsil da ita ta daura hijab tana kamshi ta fito da niyyar zuwa part din Na'im sai taga Dada da Mummy,sai ta Rabe a Bango wai kar a ganta zata je wajen Wani,sai ta leko ta koma,basu san ma me takeyi ba,sai da ta tsaya ta shirya dabara sannan ta fito zuwa wajen Mummy tace Mummy Na'im ya baki Sako ki bani yanzu? Mummy tace ai ni tunda yayi min sannu da zuwa ya koma part dinsa,Shagwaba ta fara tana

1 Comments On KAMARSU CE DAYA
avatar
abdulkadir-lawan-yusuf

9 months ago

Reply

Littafi me ma'ana

Please Login or Register in order to submit comment