Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

doka kafa ni...Haka fa yace zai baki yanzu maybe ma ya fita,Dada ta saki baki tare da cewa ke baki san inda yake ba kije ki karba mana zaki damemu wlh shi yasa bana son zuwa gidan nan duk fitsararru aka tara daga matan har Mazan,Salma tana dariya tace Bari na dawo Hajjaju muyi hira zaraf kamar walkiya ta haura samansa,Na'im kuwa yana sama ya leko ta wajen steps yana kallon abinda takeyi,komawa yayi tare da labewa jikin labilen Palonsa,tana shugowa yace tatttt ta Tsorata sosai sai da ya fito yana mata dariya,Hararar wasa ta masa tare da cewa ka tsoratani zan rama,murmushi ya mata wanda ke kashe mata jiki,yana kallonta ya zare mata hijab yayi arba da rashana,Daukanta yayi tare da dagata sama suna dariya,zamota yayi kirjinta saitin kansa,ya tura kansa tsakiyar kirjinta yana shakar kamshi,Salma ta lumshe ido tare da makale shi,a hankali yace kinci abinci?Salma tace a'a,me zaki ci?Salma tayi wani fari da ido tare da juyasu tace shawarma,nan take ya jawo waya tana jikinsa ya Kira Irfan,kana ina?yace yanzu ma ina hanyar gida yace Dan biya ka siyo min shawarma,Salma tace da hanta,yace da liver,ta kara rada masa da zuciyar Kaza,Na'im yace da Heart din kaza,Irfan yace wlh baku Isa ba kun raina min Hankali ina Jinta fa sai dai taci ta Rago ko ka bata taka ta cinye,
Suna dariya Salma ta kara Radawa Na'im da Icecream da Doya da kwai,da soyayyen dankalin Hausa me yaji,Irfan ya kashe wayarsa tare da masifa abinda naga dama zan siya sai dai kar taci,nan ya tuna da Zainura baiwar Allah,ya Kira Mummy yace ta bata wayar,Zainura tana kwance tana hutawarta ita daya Mummy ta bata waya ta bar dakin,Zainura tayi Sallama ya amsa yace me kike sha'awa zaki ci ko sha?Zainura ta rasa me zata ce ta shiga tunani,yace fadi tace koma mene zanci,Irfan yace ki fada ko mene zan siya miki,Zainura dadi ya kamata dama sha'awar shan abun takeyi Baffansu na siyo mata idan yaje kasuwa sai ko tace yashin Madina ko carbin Malam,idan babu kuma ka siyo min tsami Gaye,Irfan bai taba ma jin me kama da sunan ba,yace mene wannan abin mu babu anan ban sansu ba,Zainura tace ni Alquran su nake so idan babu shike nan ni,yace nawa ake siyarwa?tace yashin Madina Yanzu yayi tsada Uku Naira biyar,Carbin Malam guda biyu Naira biyar idan Katon carbi ne,tsami Gaye biyar Naira biyar ne,idan yayi tsada kuma na hakura ka kyaleshi kawai,Irfan saida ya dinga dariya kamar ta kasheshi yace kinga wani abu zaki fada ko nama,shawarma,burger,icecream etc,Zainura tace tab ni na sansu ne,Nama fa kullum sai munci a gidan nan yanzu ma gasu can a kitchen sai kalar da nake so dan ta'adin kudi da almubazzaranci nace ka kara siyo min,Irfan yace to zan siyo miki ko mene,Zainura tace ni Alquran bana so Bazan ci ba,haka kawai mene babu a gidan nan,Irfan yana ta dariya yace to kayan kwalliya fa?dana sawa?Zainura tace kai kayana yanzu har sunfi kala ashirin fa,a kauye kayana kala Bakwai ne gaba daya a haka kuma ni yar gata ce,amma dan rashin godiyar Allah nace sai ka sai min wasu ai sai na zama me handama,idan ka dawo lfy ma ai munji dadi,banda tukin ganganci Allah kawoka lfy idan ka samu Yashin Madina to ina so sai anjima kit ta kashe wayar ta bar Irfan da dariya.
Zainura haka ta dinga mita wai ana kashe kudi a banza.

Salma kafin Irfan ya dawo ta dami Na'im da shagwaba ita yunwa,shi kuma sai lallabata yake,Irfan har wasu tsofaffi ya tambaya a wani Super market mene yashin Madina,da kyar wata tsohuwa bahaushiya tace dan nan matarka ce me ciki take nema?Ai a kauye ake samunsa,ban san inda za a ganshi anan ba,wata yarinya tace ana siyarwa a Islamiyarmu wata tsohuwa muna siya,Irfan yace Dan Allah bani Address yarinya ta gwada masa yaci sa'a ba a tashi student ba,yamma lis ya shiga ana ta kallonsa ya tambaya aka nuna masa tsohuwar gaba daya kayan Yara take siyarwa iri iri kawai ya siye kwando gudan komai da Komai Amma yace a nuna Masa yashin Madina?Ya gani garin Kuka da sugar fari kal,ya dinga dariya ashe kayan Yara ne bai san su ba shi.

Na'im ya Kira a waya fito Malam ka karbi abinka,Na'im murya na rawa da gaji dai Iskancinsu suke da Salma😀
Irfan yace wai mene haka jiranka fa nake,ka kawo min palona mana ka tafi,Irfan yace ni ban iyan kallon wannan harkar taka ba wlh gwara kayi Sauri ka karasa gidanka ku tafi,Haka Irfan ya kai palo ya ajiye masa ya tafi zai kira Zainura ta karbi nata.

Tunda Zainura taga sakonta ta dinga Murna tana zuba godiya tana lasa tana lashe lips sai ta zazzagoshi a tafin hannu ta lashe,ko kula Irfan batayi,tace sai na sanwa Salma nasan itama tana sha,Allah ya biyaka ya kara arziki da budi har na tuno su Jamila,Sadisu ya dinga siya mana muna jin dadinmu,na sanmaka?Ya miko tafin hannunsa ta dan zazzaga masa kadan ya lashe yanda yaga tayi,suna ta zazzaga suna lashewa haka Hunaif ya samesu ga abu a leda a gabansu da yawa,yace shima a san masa,Zainura ta dan zuba masa shima ya lashe sai yasha tsami Gaye da carbin Malam kawai sai ya zauna shima suna ta lashe lashe har dare Salma ta fito da Na'im tana gani itama ta fara murna ta ebo wasu tana sha ta sanwa Na'im yaji tsami da zaki yace wannan sai yara,Salma ta kwasa da yawa Na'im yace muje ke wannan sunfi iya shirme, suka koma Bedroom yana manne da ita suna maganganu kasa kasa tare da gabatar da Sallah suka sake sabon lale

Zainura kwana biyu ta gaji da birni fa ko magana ta daina sosai duk surutunta wai sai an kaita gida ita ta gaji,ba irin wayon da ba a mata ba amma taki yarda,duk wasan da take musu da tsokana ta daina sai taki fitowa ma,yau ma da kyar Salma ta fito da ita amma cewa tayi baza ta sake fitowa ba sai dai ranar tafiya kauye tazo,ba komai ne ya damu Zainura ba face Aisha da take hanata sakewa a bedroom dinta yanzu idan dare yayi,Aisha da ta daina Lesbian amma ganin Zainura na kwana a dakinta sai abin ya fara dawo mata,Sai tace yanzu ta yarda Zainura ta dawo su dinga bacci gado daya,tana janta a jiki da mutunci,Saida ta saki jiki sai tana bacci taga Aisha tana shafata tare da kokarin cire mata kayan jikinta,idan tayi niyyar fada sai taji tsoro kar ace sharri ta mata ko yan Uwanta suga laifinta,shi yasa Zainura Sam bata da sukuni ita bata gane nufin Aisha ba,ita kuwa Aisha yanzu sha'awar Zainura take tana birgeta,shi yasa sai tayi ta mata kyauta abubuwa masu kyau da tsada.
Zainura duk sunfi mutunci da hira da Irfan sai su zauna suyi ta hira tana bashi shawara suna dariya abinsu,sabo da su ba ruwansu da wani wulakanta mutum ko dan kauye kowa yayi harkarsa ayi wasa da dariya,Aisha ce ma halinta ya dan banbanta kadan.
Yau Zainura ta sawa Ranta sai ta fadawa Irfan abinda Aisha take mata,samunsa tayi a Palo yana kallo tare da danna waya yana chat,batayi magana ba ta tsaya can nesa tayi shuru,Irfan ya ganta Sam bai son ganinta haka sun saba da abin dariyarta tana sasu nishadi amma yanzu ta canja lokaci guda ko mene dalili oho,yafitota yayi da hannu kamar wacce kwai ya fashewa a ciki tazo tare da Zama kusa dashi,ya kalleta yana mata murmushi tare da tsokanarta kinga ma kinji dadin birni har kyau kike,murmushi tayi kawai bata ce komai ba wanda da dane sai yasha surutu ya gaji a kan maganar nan,can ta bude baki tace magana zan fada ma amma baza ka fadawa kowa ba? Yace ae ai bazan fada ba kin sani muna sirrinmu,tace ka sa a canja min dakin kwana dan Allah ko kayiwa kanwarku fada kullum da dare sai ta dinga shafa min jiki tana kokarin ciremin kaya rannan ma a Palo na kwana,i dan ba haka ba a maidani gida,sai ta dinga lasheni kamar kare,tana min abinda su Salma keyi da Na'im.

Irfan ransa ya mugun baci wato Aisha bata daina halinta ba harda bakuwa zata lalata,nan take ya mike a fusace,Zainura ta rikeshi tace idan kaje zata ce sharri na mata fa,Mummy zata ji haushina,idan kana so kayi fadan da hujja ka bari na jawo ka kamata da hannunka,ka bari da dare kazo ka gani da idonka,ni wlh duk ta hanani sakewa haka kawai ni na taba ganin haka abu iri daya dan lalacewa ai wlh gwara hannun Audu me kifi ya taba ni da nata,haka rannan ina bacci na ta danneni da kyar na tureta na Arce Billahillazi in dai ba a dau mataki ba kaji na rantse Yasin sai na fasa mata kai,nan Zainura ta dinga mita yi take yi take kamar Irfan ne ya mata,saida ta Amayar da abinda ya dameta tas sannan tayi shuru ta zauna tare da zumburo baki tace kuma ka kaini yawon shakatawa kafin ka dawo kaci ubanta ko na dauki mataki da kaina haka kawai a dinga lashe min jiki,ana taba ni banyi da Namiiji ba sai mace,Irfan yayi dariya yace yanzu nasan Zeena ta farfado Amma da gidan nan ba dadi ashe Aisha ce,
Yo ai wannan wlh a daina kiranta da suna me daraja Aisha Albasa batayi halin ruwa ba,ku koma kiranta da Indo ko A'ilo Amma ba wata Aisha.

Irfan dai ya kwantarwa da Zainura hankali yace haka ma Maza ana samun masu mummunar dabi'a haka,Zainura tace ikon Allah katako da katako Allah ya masa mace shi gwara ya nemi gardi me jiki duk tauri kamar katako da wari,Irfan ya kunshe dariyarsa yace to mazane masu wari? Zainura tace ai ba irinku ba gasu nan da yawa a gari basa wanka ba Tsabta Amma har kaji suna zagin mata wai ba tsafta.

Irfan yau yasha hira har su Mummy sunji dadin ganin Zainura yau ta saki ranta,Irfan dare nayi ya je har Bedroom din Aisha ita kadai ya sameta ya dinga cin ubanta yace wlh ko hannu ta rikewa Zainura sai ya farfasa mata jiki,Aisha dama su basa karya tace to ai ba wani abu na mata ba kawai dan jin haushinta nayi,Irfan yace ubanki ya mata jikin?da zaki taba ta kije kiyi da yan uwanki yan Iska ba Zeena ba,yarinya ta gari zaki lalata ta kin hanata sakewa Nan Irfan ya kwashe kayan Zainura tas ya canja mata Bedroom,Amma duk da haka saida Zainura taje dakin Aisha daga jikin kofa tace sai dai ki lashe kanki in Allah ya yarda sai anyi girgizar kasa a dakinki a kaiki can kasar da aka kifar da wanda suka ki bin Annabi lut,kuma farko ana saki a kabari walakiri zai janyeki can kasa ta Bakwai ya miki guduma daya a goshi sannan ayi can dake wajen yan uwanki.
Aisha tayi murmushi tace koma me zakice kice Amma kina da kyan sura Zainura,Zainura tayi tafi tace da ace Irfan ne ya fada sai ya birgeni naji dadi Amma ke da karya daya kuke a wajena,kiji tsoron Allah A'ilo,A'ilo ina jiye miki fushin Allah tam,ta rufe kofar tayi waje tana jin dadi yau zata yi bacci domin ta dade bata bacci sai da asuba Sabo da tsoron Aisha,tana kwanciya ta baje saman Bed tace haba Amma kullum bacci sai da ido daya,Aisha kuwa tace wlh baza ta kyale Zainura ba sai ta cimma burinta,da ace ma Salma zata amince da har ita zata hada su dinga shanawa yan mata kyawawa a kusa.
Aisha da tayi niyyar Aure Amma yanzu ta fasa Maza basa birgeta sai su Zainura da Salma,A mma tana tsoron Na'im bashi da Imani akan Salma indai ya kamata wlh wajen Sarki Kanin Babansu zai kaita kasar larabawa a mata hukunci mai tsanani,Na'im baya daukan hauka, musamman da ya tsani masu wannan rayuwar,shi yasa baya shiri da Aisha.









AsmaBaffa
[1/14, 5:14 PM] Sis Asma: 🏉KAMARSU CE DAYA🏉








141-145 146-150







Official









By
AsmaBaffa










Wannan page nawa ne ni kadai ASMABAFFA😅😅😍saura naji yan bakin ciki.









Aisha ce kamar munafuka kullum tunani take ya zata samu Zainura ta mata wayo ko kuma Salma zata Yiwa wayo Sabo da Salma tafi saukin kai kuma yanzu bata da Aljanu shuru shuru ce.
Salma tana Bedroom dinta tana shirin Tafiya wajen oganta Na'im tasa kayan daukan magana domin duk wanda ya ganta cikin wannan kayan sai yaji kunya da kansa ya tafi,Aisha ta dade a tsaye tana kallon Salma wacce bata san tana yi ba,jikinta ya mutu sai lokacin ta shigo tare da Sallama,Salma ganin mace ce kuma kanwar mijinta da fara'a tace Aysha ina zuwa haka,Aisha tace Wow Anty Salma kinyi kyau nan ta rike hannun Salma,Salma ta dauka kawai yabo ne,ta shafa gashinta gaskiya kina da gashi,Salma tace tnx ai kin fini,nan Aisha ta wani rungume Salma tana fakewa wai murna take,Salma taga abin yana wuce hankali sai wani shafa mata wuya Aisha takeyi,Salma tace ke Aisha mene haka ?Ban gane ba anyi yamma da kare,kwartancin naki kaina ya dawo?ko kin manta nasan halinki da sanda na fara zama a gidan nan,a gabana ake miki fada fa ni wlh na dauka kin tuba ashe karya ne na muzuru ne,

Aisha tace kufa baku san abin arziki ba komai akayi a Iskanci ake mene wannan?har abada baza ku waye ba villagers,karaf a kunnen Na'im da dawowarsa kenan yana Sauri yaga masoyiyarsa direct dakin ya taho,bai shigo ba ya tsaya a kofa,sabo da zargin Aisha yake dama har yau bai yarda da tubanta ba,yana kallo Aisha zata shafa masa Salma,Wani kishi ya taso masa da bakin ciki kanwarsa ta rasa wacce zata bi sai matarsa,Salma tasan ya shigo tace wayyo Honey zata taba ma abinka Sabo da kisisina, basu san da zuwansa ba sai Mari da Aisha taji me azaba,duka ya rufeta dashi ta ko ina,nan ya fisgo wayar Tv ya fara jibgar Aisha ba ji ba gani,ba ruwansa da inda yake duka,Salma tazo tana rikeshi wai ya kyaleta sai ga Zainura jin ihu ta shigo tare da janye Salma ta karfi tayi waje da ita tare da Sa kafa ta banke kofar tace a fara mata dana duniya kafin na walakiri yazo,Salma tace so kike yayi Kisan kai gashi ba kowa a gidan bare a ceci Aisha, Zainura tace ke kinfi so tazo ta dinga tabaki kenan yayanta yazo itama tazo ko? Salma suna jin ihun Aisha a ciki tana neman agaji Amma Zainura dan kar yan aiki ma suji ta kure Volume na kida har waje kida ke tashi,Salma ta dinga dariya yanda Zainura take cashewa wai rawar Dukan Aisha take,Na'im kuwa yana can yana casa Aisha tun tana kuka da neman agaji har ta kasa,ko me ya dauka dukanta yake fuskarta ta kumbura kamanninta sun sauya gaba daya,
Zainura lokacin ta kashe kida ta nutsu,Salma tana ta tunani karfa ayi kisa a kanta ga Zainura ta riketa da ta mike da niyyar taimako sai Zainura ta jawota ta riketa kam.

Na'im ya fito ya hada uban Zufa,Zainura je ki kwara mata ruwa kar wanda ya bata ko paracetamol,Zainura tace an..an..angama tayi ciki kamar yar Sanda ta kwaso ruwa cikin wata roba tunda wai Na'im cewa yayi ta kwara ba ta yayyafa ba ta kwarawa Aisha ta farfado tana kuka,tana dan Allah kayi hakuri wlh Bazan kara ba,addua zakuyi min pls Bro,Zainura ta kyalkyale da dariya tare da cewa A'ilo yau Maita ta koma? Haka kawai in banda kankanba irin taki ai gwara ki tsaya a kaina nice zan iya rufa miki asiri in ci ubanki da kaina,amma yo ke da kin san yanda Salma da yayanki suke ai bakya fara ba wlh akanta zai iya kasheki,Salma idan kwakwalwarta ta buga billahillazi ko sirri kikayi da ita kinyi da banza soyayya tana kado mata Zata kwashe ta fadawa mijinta,ba a munafunci da Salma ko da bai kamaki ba tana zuwa wajensa taji tsotsa wlh sai ta fada masa kin taba mata ko hannu gwara ki rufawa kanki asiri tunda ke tuba babu ko?to ki koma wajen irinki,Aisha tace wlh ni fa kawai hannu da wuya na taba mata,Zainura ta sheke da dariya tace tab lallai yau abinda kika gani yafi girgizar kasa Alquran ai sai ace Traler ce ta makeki,yo haka kawai kema yayanki da abunsa kema kizo kice akwai rabonki ciki kice kema da ke a ciki,Aisha ta fashe da kuka,Zainura tace yi min shuru ko na murje miki hanci yanzu me zaki ce da su Irfan,Mummy,da sauran yan gida? Aisha tace uwarki zance yar Iska,Zainura ta kwandala mata robar ruwan a ka Aisha ta kwalla kara,tace yi shuru ko na karasaki,Zainura tace zan gasa miki jiki Amma wlh in kin san zan tabaki kiji dadi Bazan yi ba,

Da kyar Zainura ta hada mata ruwan zafi taje ta gasa jikinta,ta fito ta bata magani tasha tace to tafi dakinki kiyi bacci can,idan Mummy ta dawo kya san abinda zaki ce,haka Aisha ta rarrafa ta tafi dakinta,Zainura ta gyarawa Salma dakinta ta rufe ta dawo palo tana kallon Indian film,Salma kuwa tana can Na'im yana ta sauke mata masifa akan tayi sakaki Aisha zata bari ta rike ta,Salma tace kayi hakuri Amma Dukan da ka mata yayi yawa,Kema zan miki kalar naki ai Dukan soon tunda baki da wayo har yau.

Salma tayi dariya tare da rungumeshi ta baya wani lumshe ido yayi tare da janta Toilet ta masa wanka Amma taki yarda wai kunya,bashi kike daukarwa kanki Baby ina tarawa,Salma tace naji kayi Sauri bari na zabo ma kayan dai,koda ya fito ta tayashi ya shirya,ya zauna zai shigar da wasu Record system,yana gefen Bed a zaune Salma ta zagayo ta bayansa tare da sakalo hannayenta ta wuyansa ya daura nasa saman nata tare da jawo Hannayen tana a bayansa ya rike yatsunta yana danna keyboard dasu a haka yake shigarwarwa tana ta dariya,yana dannawa da yatsunta,Lips dinta saman kunnensa tana ta masa Salo iri iri yana jin dadi kida na tashi kadan a system din.
Haka suka gama aikin tare da zubewa saman Bed,Salma tasa Hijab dinta tare da cewa bari na kawo ma Abinci ka Sa na manta wlh,riketa yayi tare da jawota ta fado samansa ba yanzu ba sai anjima nayi Sallar Isha,Kwanciya tayi a jikinsa tana wasa da kirjinsa tana kara narkewa sai shagwaba take abinta haka kawai,shi kuma yana lallashi tare da Rada mata ya akayi uhm? Me kike so Baby,my Heart ya akayi?Salma ta kara wani Uhum...uhum....ni...dai...ka maidani schl naci gaba nima,dole idan da rai da lfy zaki koma,Irfan zai kaiku ke da Zainura ko? Salma taji dadi ta kara makale Na'im tare da cewa tnx Dear saura...uhm...massage zaka min yanzu na gaji,ba musu yace Ok Darlin Sabo da yasan me take so,Shi yasan in yana so ya kunna Salma yaji dadinsa hankali kwance, in daya san yana tabawa zata sandare nan ya fara mata salonsa sai ga Salma tana mika idonta ya canja,zafafan Salo takewa Na'im wanda badan ya kai zuciyarsa nesa ba to yau bazai kyale Salma ta kwana lfy ba,bai son yayi abu ne ba son daya a ciki,yafi so sai ta yarda tana so yana so shine ba cutuwa,shi Sex abinda yake bukata kenan dole sai ko wanne bangare yana so da yarda zai Bada ma'ana baya ga haka ma Salma tafi sabawa dashi sanda suna kauye kuma basu tuna lokacin ba,shi yasa ya bari yanzu ma ta saba da wannan sai suji dadinsu.

Salma idan suna Romancing din nan nasu bata sanin inda take tabbacin ta saba dama,wani abun ma bata san sanda take cewa yayi mata ba,itama haka ta gama da Na'im gaba daya da salonta,yanda take tsayawa tana tsatseshi tas,Susuta shi take sosai burinsa ya tsokano Salma yasan baida matsala wajen yanda take Bada hadin kai ya gamsu ba tare da sunyi Sex ba,amma yanzu kam ya gama kaiwa kaeshe,yanzu ya dawo yace ba sai sun koma gidansu ba,bazai jira ba har 14days ya fasa wlh.

Mummy ta dawo ita da Dada suka Iske Aisha cikin rauni,Mummy ta firgita tayi kan Aisha Aysha me ya sameki?Tana kuka a kwance tace Na'im ne ya dakeni saura kadan ya kasheni,Mummy tana ji tace Na'im tace af wlh Babban laifi kikayi Amma Haka kawai Na'im bazai saurareki ba bare ya dakeki dama Hunaif kika ce nasan yafi saurin fushi,Mummy tace ina Na'im nan ta nemo shi yana can suna bacci da Salma,Sannan ta kira Zainura ma tace me ya faru haka Aisha ta karbi wannan hukuncin?
Na'im yace gata nan ki tambayeta me tayi?Aisha tace Mummy Allah Salma ce ta fada masa wai ina taba mata jikinta,Na'im yace da idona na gani wlh tun kafin ta fada min dalilin da yasa Irfan ma ya canjawa Zainura room kenan ya fada min tana neman ta shi yasa rannan ta daina magana a gidan nan tace gida zata tafi.

Mummy ta fashe da kuka tare da kara rufe Aisha da duka Dada tace mene Amfaninki Aisha kinyi asara wlh,Aisha a zuciyarta bata hakura ba tana nan kan bakanta Amma wajen Zainura,a fili kuwa sai hakuri take bayarwa ta daina,sosai akayi mata nasiha tace taji wlh baza ta sake ba shaidan ne,sannan Mummy ta kaita asibiti aka dubata suka dawo.

Irfan sai da yayi Sallar Isha ya dawo gida a gurguje yayi wanka yaci abinci,8pm da dare sai ga budurwarsa Rayhanat taci uban wanka dama yar gayu ce ta gaske tayi kyau sosai,ta samu Mummy suka gaisa,Hunaif ne kadai zaune a palo yana kallon Ball,abin na Rayhanat zuwa gidan Saurayi har da dare dan lalacewa,ta zauna tare da mikawa Hunaif hannu suka gaisa wai ita baturiya,Zainura fitowarta kenan daga kitchen ta dauka ma budurwar Hunaif ce yanda ta manne kusa dashi harda gaisawa kamar Maza,Hunaif ya yace Zeena ga budurwar Irfan je ki kira mata shi,Zainura tayi murmushi tace dama itace Rahane take ko Rayhanat,Budurwar tayiwa Zainura kallon Banza tace yan kauye ku dama masu shara da wanke wanke idan kuka samu waje sai ku nemi raina masu gida mene wani Rahane?

Zainura tayi shuru ta tafi dakin Irfan tayi Sallama daga kofa tace budurwarka tazo tana palo kazo,Irfan yaja tsaki yace kash akan wai 2days ban daga wayarta ba,Zainura tace kace mata an maka mata balarabiya a kasarku tayi hakuri ba laifinka bane Kanin Babanka ne Sarki yace ya baka yarsa,Irfan yace kin kawo shawara,suka fito tare da Zainura a jere,Rayhanat taji haushi gashi taga Zainura ta fita kyau da komai baza ma a hada su ba ko kusa,Cup ne a hannun Zainura tana shan Holandia ta mikawa Irfan tana dariya tace shanyeta,Irfan ya kalleta yayi dariya sai da kika gama shanyewa zaki ce wani na sha suna saman Steps sunki karasa saukowa ga Rayhanat tana kallonsu Zainura tace Allah sai ka shanyeta tare da kafawa Irfan Cup din a baki ta toshe masa hanci da daya hannun wai dure take masa,Hunaif yana ta dariya yace wlh anyi girman banza wannan yarinyar ce zata dinga ma dure kai kuma ka tsaya wai ko kai Irfan Namiji ne? Cup din Zainura yana bakinsa ya ware hannu ya zagi Hunaif wai zagin hausawa da ake cewa dakuwa.

Rayhanat ta cika fam,Zainura tace au Rayhanat yan gayu tana jiranka fa masoyan Asali je ku sha Soyayyarku,Rayhanat tana jin Abinda Zainura take fada,Irfan ya karaso Zainura tana saman Steps tana kallo yayi murmushi tare da zama yace ya akayi Baby barka da zuwa,Hunaif ya mike ya bi ta wajen Zainura tare da ce mata kai baki da kirki wlh kiji tsoron Allah,Murmushi tayi tace me nayi daga hada alkhairi sai ya zamo tsiya,nuna min taka Babyn?Hunaif yana dariya yace Allah kiyaye ki rabamu a banza ai ni ko gidana Bazan bari kije ba kashe min aure zakiyi.

Salma da Na'im ne suka shigo da

1 Comments On KAMARSU CE DAYA
avatar
abdulkadir-lawan-yusuf

9 months ago

Reply

Littafi me ma'ana

Please Login or Register in order to submit comment