Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wlh Na'im yafi kowa jaraba Allah ne kadai ya kareshi bai taba kusantar mace ba sai da yayi aure,amma bashi da hakuri a harkar ko kadan,Irfan yayi dariya tare da cewa dan rainin Hankali ka ganshi dai kamar baiyi komai ba,yanzu zai ta yiwa mutane muzuran banza,Hunaif yace cewa zaiyi ma bata zo ba shi kadai ya kwana bari ya tashi kaji.
Na'im bayan yasha bacci ya tashi Hunaif yace Wai Anty Salman Mummy ta barta tazo wajenka kuwa jiya ai kace Mummy ta hanata da farko,Na'im ya basar yace bata zo ba fa ai Mummy ta bani matsala ta hanata haka na kwana ni kadai,da kyar ma nayi bacci jiya,Hunaif yayi dariya yace gaskiya kam ka kwana ba bacci Salma bata kusa,Na'im yace hmm kai dai bari waya nayi ta dannawa ina aiki ciki,Irfan yace ah lallai kasha aiki maimakon kazo ka tashemu mu koma Bed din,Na'im yana tabe baki yace mantawa nayi,
Irfan yace wlh karka raina mana hankali Bro naga sanda kuka bar Palon nan tare da ita da asuba har da kin tashin mu Sallar asuba,Na'im ya bata rai yace zanci Kutmar...bai karasa ba yayi kwafa tare da cewa yan sa idon banza yau baza ku kwana a nan ba Allah.Hunaif ya dinga dariya yace haba dan Allah mu ai yan zaman dakinku ne yanzu muna yara me muka sani,Zaman daki muke muku.
Salma da hijab dinta ta shigo ita da Anty Rukayya suka jere musu breakfast,Hunaif yace Anty ina kwana Salma tace lfy,yace nifa ba da ke nake gaisarwa ba babbar Anty Rukayya,Rukayya ta amsa tana dariya suka gaisa,yanda suke birgeta ba ruwansu da wani girman kai yan turai kenan,Salma cike da shagwaba ta kalli Na'im wai ni bazai gaisheni ba sabo da ya girmeni,Na'im yayi murmushi yace kyaleshi mu bama son gaisuwarsa.

Irfan yace ita waccen wai sai ta gudu gida taki fitowa,Zainura ai tazo gida ta manta kowa kuma ma ai yanzu safiya ce me zata fito tayi maka cewar Na'im.
Bayan sun karya kowa yayi shiri suka fito gaba daya za aje gidan su Zainura su gaisa da iyayenta,Irfan yafi kowa Zumudi.
Suna zuwa sunsha tarba da karramawa Mummy taji dadi Iyayen Zainura ba ruwansu wayayyu dasu,Umman Zainura itama akwai Surutu da hira sosai,Zainura bata gidan ma wai ta tafi gidan yan uwansu.
Sun Dade sannan suka dinga zuwa gida gidan da suke mutunci dasu Salma frnds harda me gari duk sunje, dangin Malam dana Umma duk sunje an gaisa sun musu godiya,ko wanne gida in dai sunje to zasu Sha kyautar kudade kuwa,har na gari idan aka gaisa in dai Na'im ya sanshi to sai an masa kyautar kudi,gari ya dau Murna da jin dadi.
Na'im yace Zai gina musu makaranta da hospital Gomnati zata dauki ma'aikata,zai musu titin kwalta,sannan kuma za ayi musu tuka tuka da yawa a garin,yan gari sai murna da jin dadi ana godiya,Yace kuma Malam da Umma su shirya dasu zasu tafi,Malam yace ba da ba jika zasu bisu zasu dinga zuwa ganin dangi ana gaisawa.
Zainura ba a ganinta gaba daya tunda sukaje a yawo take wajen yan Uwa da abokan arziki.
Abubakar da Rahina kuwa Na'im ya bawa Abubakar Manager na Company nasa a Kano tare da kyautar gida dallele da mota sabuwa,sannan yace ya koma Ya karasa Degree dinsa,Dangin Rahina da Abubakar sai godiya domin Salma Dubu Dari ta bawa Rahina Jari.
Anty Rukayya da dukkan frnds din Salma dana Na'im tare da iyayen. Zainura kujerar Makkah ko wanne za a tattarasu su tafi gaba daya,Zainura tace pls a hada da ita,Irfan yace a'a sai idan Zasu je a gidansu dasu Na'im zasu tafi har ita.

Basu bar garin ba saida akayiwa masu tafiya aikin Hajji passport a garin Katsina,aka bada kwangilarsu an biya kudaden da komai,sannan aikin da Na'im yace Zai gina musu a garin duk an kawo kayan da komai shima an fitar da kudi an bada kwangila me gari ne jagorana aikin har a gama,tafiya Saudiya harda me gari,Su Barira dasu Jamila kamar zasu haukace zasu je Makkah,Salma tace duk iya frnds dinta da sukayi Kamu tare kayan daki idan aure ya tashi ita zata musu kyauta gudun muwa, suka dinga ihu shewa da tafi,Na'im sai da yaje sukayi magana da chairman na local government din su Malam ana kammala aikin makaranta da Hospital a turo ma'aikata su dinga aiki gomnati na biya su albashi.
Chairman yazo garin anyi komai dashi anyi godiya tare da jinjinawa su Mummy masu taimakon aluma Basai lallai ace Gomnati ba.

Kwana biyar sukayi zasu tafi Malam yace zasu biyo bayansu amma tunda zasu je Saudiya da mutanen kauye zai zauna sai sunje sun dawo sai su taho Abuja shi da Umma,Salma tace suna dawowa ma zata musu booking Flight su dawo Abuja.

Salma takaicinta su Affa sunki gane gaskiya taso ace sune aka fara yiwa haka,suma suji dadi Sanadiyyar riketa da sukayi amma ina,sai tayi tunanin kara komawa sai ta fasa kawai sabo da tasan zai wahala ma su yarda da ita,h aka yan uwan mahaifinta ta rasa me ta musu da basa kaunarta ita,amma tana addua Allah ganar dasu.
Kwanan su Na'im biyar a kauyen nan sai da suka gama saita komai sannan suka nemo Zainura da kyar suka ce tazo su tafi Abuja,k afin su Mummy su fito saida ta tambayi Irfan a sirri ko yana son Zainura?yace Sam shi ba soyayya suke ba kawai frnds ne tasu ce tazo daya ba so bane,Mummy tace shike nan amma taso ace sonta yake da sai ayiwa iyayenta magana tun kafin su bar kauyen a tsayar da magana amma yace ba soyayya bace shi.

Jamila suna jikin motocinsu suna ban kwana,Zainura tace Sababbin kawayena na Abuja sunce na gaisheku,Zainab tace Allah?kice Wallahi?Zainura tace am serious,Jamila tace ai kece Amasiros din Dalla mu me muka sani,Zainura tace da gaske sunce na gaisheku,Zahrau tace dan Manzon Allah? Zainura tace kullum nayi ta basu labarinku,Barira tace kice Yasin,Zainura tace to karku yarda din aikin banza, ai baku ga tafiyarsu ba tab,Kamar baza su taka kasa ba,Jamila tayi dariya tare da cewa ko dai tausayin kasar suke ji ne? Zainura tace na sanma yan Iska,Zainab tace cab ai taketa nake duf duf har girgiza nake a kan kasa wlh to haka kawai ranar da aka binneni fa sai ta matseni ai gwara na moreta nima,Hunaif ya dinga dariya wai har girgiza take a kai,
Zainura ta shanye hannu ta sagaleshi kunga yanda sukeyi yan bantan uba ta fara yanga tana Shan kamshi tana taku dai dai,yan matan suka dinga shewa Zahra'u tace amma yan Birni anyi yan kwalabar uba wlh dan Iskanci kawai a kama yanga to ta uban mene,Zainura tace ke ai ita take tashe yanzu a can idan bakyayi babu namijin da zai kalleki,kici uban kwalliya Malam nima yanzu na fara koya so nake na Zama star,
Rahmatu tace ke Zainura ki rufawa kanki asiri karki koyi iskanci,Zainura tace na nawa kuma,ni ai komai ba a barina a baya in dai Harkar gayu ce,tsaya kuji Salma tazo a tambayeta.

Salma na zuwa zata shiga mota Zainura tace Salma da Allah ya batun iyayi da yanga a birni ai ke kin iya dama,Barira tace ai Salma ita dama girman Birni ce,Zainura tace inji ubanwa?to billahillazi ba Tonon silili ba Salma karki ji haushina na fada? Salma tace wlh in kika fada sai na fadawa Na'im,Zainura tayi dariya tace ke yakewa Kwarjini har zai miki fada kiji, to Alquran sai na fada Salma kauyensu bai fi gida takwas ba yasin gwara mu sau Dubu a birni muke,Salma bukkar yan fulanine duk ko katanga babu sai ta kara,idan kunga garin ko bacci baza ku iya ba,Jamila ta buga uban tsalle taja gefe tare da rike gefe wai ta firgita da labarin Zainura ta sheke da dariya suna an kureta wlh to a ina kika waye haka? Salma tayi dariya tare da cewa Wlh Zainura sai na miki rashin mutunci gida takwas fa kika ce,Zainura tace Sorry to gida Dubu na manta,Mummy tace wannan anyi yar ja'irar yarinya ba sirri,Zainura tace ai ita take ta mana wani iyayi bata fada mana ba tun farko,amma ai iyayenta a birni suke Maiduguri,amma asalinsu yan Nijar ne shi yasa suke suma kamar Arab,amma Allah Barira Ku daina ganin wani kimar Salma Ashe ma duk mun girmeta da wajen wata biyar ai naga takardar haihuwarta Yasin yarinyace muke wani daraja ta.

Salma tace Dan Allah mu tafi a bar banza a nan tayi ta tone tonenta,Sai lokacin Zainura sukayi Sallama ta shiga motar suka tafi Airport.
Yau a kusa da Irfan take,Na'im kusa da Salma,Hunaif yana gaba,Mummy motarsu daban,Malam da Umma har Airport suka rakasu a motar Malam.
Irfan suna hira Da Zainura yace ai gwara ma da za a koma tunda kika zo ko ganinki ba ayi,Zainura tace kai Ya siyi kawuna wlh busy ba time ina ta Zumunci,shi dariya ma take bashi kamar wata Babba idan tana magana.

Na'im ne yace Salma Hijab zata sa sabo da a mota ko jirgi zai dan dinga zura hannunsa yana wasa da dukiyar Fulaninta ba tare da kowa ya gani ba,Suna mota tayi mukus a jikinsa yana ta tabe tabensa a jikinta,Salma in taji dadi sai dai ta kudundune cikin hijab kamar tana Jin sanyi,sai ta dinga fakewa da shigewa jikin Na'im wai sanyi take ji,Irfan har ac yasa aka kashe amma taki daina ji
Zainura ta gane me sukeyi kunya ta kamata harda baccin karya wai Salma tana sata kunya ko uban wa ya San me sukeyi oho amma wai haka kawai dan taga Salma na lumewa cikin jikin Na'im sai taji kunya wai.

Zainura taji itama inama ace da Irfan suke haka suma da taji dadi wlh nan Zainura ta fada tunanin Iskanci itama jikinta ya mutu,firgit ta dawo normal sai ji sukayi tace Bana so ma,me zanci dashi tir Allah kiyaye,sun San Zainura uwar shirme sai suka shareta,taci gaba da tunaninta,Irfan ya leka fuskarta tare da cewa lfy? Zainura ta girgiza kai tare da cewa wani abu na tuna,Wayarta ta dauka tare da turawa Salma text cewar dan Uwarki kina tayar da hankalin marasa aure ni na gane me kike sa mijinki yana miki ,Salma tana gani ta karanta sai ta nutsu ta zame jikinta an ganota,su kuwa su Irfan hankalinsu bai kai nan ba Sam basu San ma me suke ba.
Ta kara turawa Salma text dolene wai sai kin kwanta a jikinsa ki tashi mana mu baza ki dinga samu tunani ba.










AsmaBaffa[1/14, 5:14 PM] Sis Asma: 🏉KAMARSU CE DAYA🏉







171-175 176-180






Official








By
AsmaBaffa






JANNAT wannan page din Naki ne.








Sun Sauka lfy a birnin Tarayya Abuja yayinda drivers da Securities suka zo daukansu har zuwa gida,kowa ya kule bedroom domin hutawa.
Aisha ita kadai a daki kamar mayya taji dadin dawowarsu koda Na'im ya shiga dubata zai mata Allura sai kuka takeyi dan Allah a bude ta haka,Na'im yace Sam sai an gama komai lokaci ya cika,taci kuka har ta gaji,Mummy har tausayin Aisha taji,
Bayan kwana biyu Zainura son Irfan ya shigeta sosai duk da cewa bata San so ba amma tace zata tambayi Salma taji ko cutar so ce ta kamata,kullum tasan lokacin da Irfan zai dawo ko zai fita sai ta san yanda tayi ta buya ta kalleshi a boye ba tare da ya sani ba,
Yauma da yamma ta cakare ansha wanka ta fito kamar kallo take amma Irfan take so ta gani taji sanyi a ranta,bata dade ba sai gashi ya shigo cikin shiga ta Alfarma,yasha light blue jean da farar riga,ba karamin kyau yayi ba dama suna kama da Na'im sosai kamar me,Zainura ta kalleshi a sace ba tare da ta bari ya gane ba ta dauke kai irin ko kallo Bai ishe taba,Ganin kwana biyu tunda suka dawo akan Mummy tace ko yana son Zainura shine ya rage kulata sai gaisuwa take hadasu,itama da taga haka shine take shareshi sai taga dama take gaisheshi ma,

Yanzu ma ko sannu da zuwa bata masa ba ta dauke kai,Irfan yayi mamaki yana jira ta kulashi yaga ko kallo Bai isheta ba to ko baiyi kyau bane yau?bedroom ya shiga ya kalli kansa ya kara fitowa ya wuce ta gaban Zainura sai ma ta kalli TV tana dariya irin bata San an halacci Irfan a wajenba,ya shiga kitchen ya fito dauke da Bowl karami me kyau da fruits ciki yana Sha da fork ya zauna kusa da Zainura.

Still Zainura saima ta koma danna waya tana dariya,kallonta yayi tare da cewa baki ganni bane? Zainura tace na ganka mana mene ne?ta fada tana kallon wayarta,to ki gaisheni,akan me zan gaisheka? Irfan yana kallon gefe can daban yace har tambaya kike,kofa Sannu da zuwa baki min ba,Hunaif ne ya shigo yace wow Zeena yau kinfi kullum kyau nan gaba za a ga zukekiya,rannan da mukaje gidan Dada frnd din nan nawa yace wlh yana Sonki zan hadaku idan ya miki baki gani ba komai da mace take so ya hada,

Zainura ita Irfan take so amma ta danne tace to Sai yazo na ganshi mun saba idan halinsa ya min shike nan, Hunaif ya haura side nasa.
Irfan ya gama kulewa shi taki kulashi tana Kula Hunaif har wani Saurayi zai mata,kallonta ya karayi amma ko ta tasa batayi,yace baza ki min sannu da zuwa ba,kawai
Zainura tasa headphone ma a kunnenta yaji haushi ya Mike tare da fisge Headphone din ya tsinkashi gutsi gutsi ya watsar tsawa ya buga mata ni sa'anki ne? Zainura ta firgita bata taba Jinsa haka ba yafi sauran hakuri ba shiri tace Sannu da zuwa an dawo lfy to Alhmdllh,ya hanya ya aiki tana sunkuyar da kai kamar wacce tayi karya,ba kunya yace lfy yayi gaba abinsa ya barta nan.

Salma ce ta fito ta zauna tare da cewa Zainura Irfan yace kin rainashi yanzu wai kina kallonsa kin daina masa magana gaba kikeyi dashi,Zainura tace gaba kuma?da dan masu gida ni na isa,kawai naga yana wani shareni ne shi yasa nima Naja mutuncina,ni kin San ban son raini zanyi wasa da dariya amma da naga za a rainani zan canja wlh haka nake ni,da ace tun farko ma naga irin masu wulakancin ne harkarsu bazan shiga ba,ni ban masa laifi ba naga yana wani daure fuska ni dama gidan aka zo domin ko wanne part na iya bugawa.

Salma tace to naji ai ba haka ake ba baza ki nuna ba mutunci ba gaba daya ke da mutuminki har sirri kukeyi Ku kashe Ku rufe amma sai kuma ku dinga haka,ki daina dai ko ba komai ya girmeki yayanki ne,Zainura tace uhm naji amma kin San ni bazan zauna yana Sha min kamshi ina kulashi ba,kefa banza ce Zainura anya kina da hankali,Zainura tace ya za ayi kiyi hankali nayi,Salma nafa girmeki ehe,to shine bazan fada miki gaskiya ba da wata nawa kika girmeni gaba daya zaki dameni,Salma wai dan Allah idan kana son ganin mutum kullum,kuma idan ka ganshi kaji dadi yana ratsaka yana birgeka,kana son kasancewa dashi,kana son jin ko muryarsa,idan ka ganshi gabanka na faduwa,baka da burin da ya wuce ka birgeshi mene wannan nakeji? Salma tayi murmushi tace so yayi miki mugun Kamu,kina bukatar serious treatment cikin gaggawa,ya miki babban Kamu ke wane wannan kike sonshi haka? Zainura tace wani dan makarantar mu ne ya shiga raina na rasa me nake ji,tab yaro ne ina zai aureki ki canja sharawa schl mate fa,Zainura tace ae naji ina son abuna ni haka,Salma tace Allah taimaka.

Zainura tace tofa so ya kamani kai wannan tafi so sai Kauna,ya Zama chronic disease,Bedroom ta koma bata yarda ba wai chemist ko asibiti a dubata,zata je amma me yasa ma zata tambayi Salma ga Na'im babban Doctor, taje ta Samu Salma har Bedroom muje ki rakani wajen mijinki likita tambayoyi zanyi masa ke ba Doctor ba me kika sani,Salma tayi dariya muje to amma kin San ba likitan Soyayya bane ko? Wai Salma me yasa kike min haka kamar ba kawarki ba,suka tafi har palon Na'im Zainura taga haduwa iya haduwa a part din Na'im,Na'im ta gaisar da fara'a ya amsa Zainura tace Salma fada masa ni dai ya min Kwarjini yau,Salma ta korawa Na'im bayani shi dariya abin ya bashi,amma sai yace to Zainura babbar cutace ta kamaki sai kin Sha Allurai da Karin Ruwa,Zainura taji Allura tace yanzu soyayya za ayiwa Allura?Ya akayi kika sani ke ba Doctor ba ai har operation sai anyi miki,gobe za a tafi dake asibiti a fede miki ciki sai a cire cutar,Zainura taga basa wasa da Na'im ta san ma da gaske yake fede ta za ayi,sai ta fara hawaye Kuka,Na'im yace Salma rakata wajen Mummy ki sanar mata ayi hadin kwanciya a Hospital zuciyar Zainura ta Kamu da cuta sai anyi aiki,Zainura taji da gaske ne fa ta kara fashewa da Kuka ita baza a fede ta ba,Salma sai dariyar haukar Zainura take,tun daga Ranar Zainura ta shiga damuwa za ayi mata aiki a fede ta,Mummy tace Zainura lfy kuwa kwana biyu kin hana kanki sakewa sai tunani kike,Zainura tace Ciwon Zuciya ne ya kamani wai Sai an Fede ni inji Na'im,Mummy jin ance Na'im ya fada itama sai ta yarda ta fara jimami,ganin haka ya karyawa Zainura zuciya ta dinga Kuka kamar me,Mummy ba hakurin da bata bawa Zainura ba amma taki yin shuru,daga karshe ma daki ta koma take ta Kuka,
Hunaif ya dawo Mummy ta sanar masa ga abinda Na'im yace sun dauka wani gwaje gwaje akayiwa Zainura shima ya firgita ya jajanta harda zuwa ya mata Nasiha,Zainura tace Ashe ni mutuwa Zanyi,Irfan bai San me ake ba Mummy harda cewa kar a fada masa zai fi kowa damuwa.

Zainura tasa abin a ranta tana kwanciya sai tayi Mafarki ance mata wani satin zaki mutu,shike nan tana farkawa ta kasa cin komai bata fadawa kowa ba,carbi ta dauka da Qur'ani ta kulle kanta take ta yi tana Istigifari, kwana daya shuru,biyu,shuru,ukushuru har sati ya cika ranar da taji ance zata mutu sai ta hau Saman gado ta kwanta tana ta salati tana jira taga Mala'iku daukan rai amma shuru,tace to ko sai wani satin ake nufi nan ma taci gaba addini ba ji ba gani,sati ya zo na biyu tace to watakil na sati Uku ake nufi ko wata daya,kafin sati Uku Zainura ta rame sosai an rasa gane mata komai kana magana sai Wa'azi zata fara irin ta saduda

Irfan yayi duk yanda zaiyi ta dinga shiga harkarsa amma Bai sani ba Zainura ita ta kanta take zata mutu,Mummy ta gaji da halin da Zainura take ciki ta kira Na'im tace lallai ya kawo takaddun gwajin Zainura,Na'im ya dinga mamaki yace wasa fa nake mata wlh bata da wata cuta kawai shirme tazo min dashi shine na tsokaneta amma ni bata da wani ciwo,Hunaif ya dinga dariya yace to wlh ka dau hakki gata can bata ko cin abinci ta rame sosai ko fitowa bata yi sai addini take ta Saduda da duniya.

Shi kanshi Na'im yayi dariyar wannan shirme na Zainura har Bedroom ya sameta yayi mamakin yanda ta Zabge,ya sanar mata baki da wata cuta wlh Kawai dai da alama Son wani ne ya kamaki,nan Na'im ya zauna ya ganar da ita,taji wani Sanyi a ranta amma har yau akwai tunanin mafarkinta na zata mutu fa.
Sai Lokacin Mummy ta fadawa Irfan,Irfan yace kuma Mummy kamar yara ai in da cutar Ku zai fadawa ba yarinyar ba,ita kuma shine take ta damuwa bari naje na fito da ita Allah sarki zai kashe mana ita.

Ya shiga ya hango Zainura Saman Sallaya ana ta Jan carbi,Irfan yace Zeena Har yau baza ki kwantar da hankalinki ba,ance miki mutuwa Sallama take,Haba yan matan mu,Zainura tace to duniyar nawa take ai kowa na can ne mu dai kuyi mana addua,ita duniya ba matabbata bace,Zainura ta fara wa'azin lahira,to naji tashi muje kici abinci,tace ta koshi,yace gobe akwai schl fa,tace bazanje ba me nake nema a duniya,tashi muje Bana son Surutu,a gaba ya sata Har dining ya dinga dura mata abinci sai da cikinta ya cika sannan yace muje kiyi wanka to,tace ai dazu nayi yace wani zaki karayi,Zainura taje ta sake sabon wanka ta shirya,wai amma baza tayi kwalliya ba,ya shigo wajenta yasata dole tayi,tasha kyau,muje to suka fito har wata dalleliyar motarsa ya bude mata ta shiga shima ya shiga ya ja suka bar gidan,suna tafiya bata ce komai ba yace Zeena akwai wani abu bayan cutar da Na'im yace? Zainura ta fara Kuka sosai, Irfan yaji tausayinta ya gangare gefe tare da gyara parking,Hawayen ya kai hannu zai goge mata,ta matsar da fuskarta irin an hakura da duniya kar ta aikata Sabo,Na'im ya sa hannunsa cikin nata Zainura ta fara kokarin fisge hannunta tana Istigifari,fada min me yake damunki? Zainura taga fa bata da kamar Irfan,tace tun rannan nayi Mafarki ance zan mutu wani satin,nayi ta jira shuru gashi har anyi 1mnth shuru.
Irfan ya danne dariyarsa ya shiga kwantarwa Da Zainura hankali har ta yarda ta daina damuwa sai lokacin ta fara dariya,yace wai zaki kashe kanki ki jawo min masifa,Zainura tayi shuru tare da cewa hmm Son Irfan ne yake azalzalarta amma shi bai ma San tanayi ba,

Wuraren shakatawa ya kaita hadaddu sunyi nishadi sosai sunji dadi tasha kallo tayi nishadi kasancewar Irfan yana kusa da ita masoyinta tuni ta daina tunanin wata mutuwa ma,
Mummy sunji dadi ganin Zainura ta dawo Normal kamar da,Doctor Aliyu ya turo Manyansa an kawo kudin auren Aisha tare da sa ranar biki nan da 3mnths,Mummy tacewa Irfan idan yana da wacce yake so ya kawo sai ayi bikinsu tare da Aisha,yace a'a a gaban kowa Mummy ta masa maganar,Zainura bakin ciki kamar ya kasheta wato ma baya sonta,cikin dare harda kuka Irfan baya sonta Ashe,tana tunanin Zai iya Sonta Ashe ba haka bane,abokin Hunaif da ya damu yana ta bugawa Zainura waya akan ta bashi dama ya dinga zuwa Zance kawai Zainura ta bawa Usman dama badan ta so ba, Saturday weekend tace yazo tayi kwalliya normal gaba daya yau Family suna Palo suna ta hira,Zainura ta fito da takalminta coge tana taku daya daya,ta karasa wajen Mummy ta sanar mata Mummy nayi Bako zanje,Mummy tace kice munyi suriki sai ki kaishi palon baki.
Irfan ya Mike da sauri yace Mummy bari na fita wurin frnds yanzu zan dawo yayi waje,yana fita ya bi ta daya hanyar ya riga Zainura zuwa ya kulle palon bakin,y aje ya tare Zainura a hanya,tayi banza dashi ya fisgota da karfi tare da cewa ki sallami wancen dan iskan ba a zance a nan gidan,Zainura tace to,ya zata taji maganar ya kyaleta kawai amma sai ya hangosu hirarsu ma suke yi a jikin motar suna dariya tana ta yiwa Usman Murmushi,Irfan kamar ya haukace ya koma ciki ya koma Bedroom ya kwanta ya dukunkune Zazzabi ya rufeshi.

Saida Zainura ta gama hirarta har dare sannan ta shigo gidan Mummy tace je kiwa Irfan Sannu yau bashi da lfy tun yamma yake fama da Zazzabi,Zainura tace to tana zuwa jikin kofar bata shiga ba ta Labe kawai a gefe tayi Jimm ta dawo tare da sanarwa Mummy ta dubashi tayi gaba abinta,kwana biyu Irfan yana fama da Zazzabi amma ko kafar Zainura bai gani tazo duba shi ba,yayi jiran har ya gaji,Mummy ya kira a waya wai tasa Zainura ta hada masa tea,Mummy kuwa ta sanar mata ba yanda ta iya haka ta hada komai ta nufi dakinsa,yana kwance cikin bargo ta

1 Comments On KAMARSU CE DAYA
avatar
abdulkadir-lawan-yusuf

9 months ago

Reply

Littafi me ma'ana

Please Login or Register in order to submit comment