Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai ya fara kuka sosai,wata tazo ta kawo dakan gero ta tafi,Affa yace wacce doguwar matace ta wuce min daki? Ummitu da mamaki ta kalleshi tace Hajiyayye ce fa makwaftanmu,kuma ba daki ta shiga ba fita waje tayi gidansu, wace Hajiyayye ban Santa ba? Affa ya tambaya.
Yace Ummitu ta fito dashi waje zai sha Iska ta fito dashi kuwa yana kwance,yake nuna ledoji yace sai an dauko masa suna bin iska,idan ta dakko yace a wankesu a ajiye idan na mutu sai ku zuba Wainar Sadaka a ciki,Ummitu ya bata tausayi ta fara kuka,ya dawo yace sai ta nemo masa me daukan photo dake kauyen,takanas taje har shagon Buba me hoto ta kirashi da camera,Affa yace ya daukeshi masu kyau sai da aka dauki kala biyu Buba ya tafi,Affa ya kalli Ummitu da kyar ciwo yana cinsa yace wannan Hoton ke na daukarwa shi idan na mutu sai ki kalla,wannan gidan nawa tunda Allah bai bamu haihuwa ba na bar miki shi halak malak,ragowar gonata guda daya duk nakine Ummitu na gode Allah ya miki Albarka kinyi kokari kina ta dawainiya dani,Ummitu kuka take kamar ranta zai fita gani take da gaske ne Affa rasuwa zaiyi sabo da ciwon an kwashi wurin 6mnths har yau yaki warkewa,ba kudin asibiti,shi kanshi Affa wannan lokacin sai da yayi kuka sosai na tausayin Kansu.

Yau asabar yaune sati hudu da kai su Salma Amare sabon gidansu wanda suke kwasar love,yaune kuma dangin Salma na Maiduguri sukayi waya tare da sanarwa Mummy gasu nan a hanya anjima zasu karaso Abuja,Sabo da dama Salma ta basu address da komai na su Mummy,Mummy tayi murna tare da duk Masoyin Salma,Salma tunda taji labarin tafi kowa murna ta gigice sabo da dadi,ga Na'im yau weekend yana gida amma taki saurararsa sabo da murnar da take ciki itama yanzu tana da yan Uwanta,sai shige da fice take ta rasa ma me zata shirya musu,Na'im ba abinda zaiyi sai na ya taya Sahibarsa murna,da yamma suka sauka gidan Mummy sun samu tarba ya gaske,su Kansu basu taba ganin gida irin na Mummy ba yanda ya hadu,mamaki suke wai Allah ne ya daukaka Salma take wannan daula ,ni kuwa nace ai gidan Mummy ba komai bane kallon duniya na gidan Amare,Malam da Umma sune gaba wurin saukar su Malam Musa dasu Shehu,sunci sun Sha sun nutsu sannan Malam,Umma,da Mummy suka kara basu labarin komai na Rayuwar Salma da tayi,duk da cewar suma sun sani amma sai yanzu suka kara fahimtar abin,sosai suka dinga yiwa Malam da Umma godiyar rike Salma tare da Mummy itama,anyi addua sannan Salma da Na'im suka karaso gidan Mummy cikin shiga ta alfarma,sun gaisa da juna sannan su Shehu suka dinga bawa Salma hakuri suka bawa Na'im ma kan abinda suka masa da yaje neman Salma wajensu sanda ta bace,Salma cike da murna tace ya wuce ita dama bata rike kowa ba,kuma komai ta yafe koma mene har Gadonta duk ta yafe,da Murna ta nemo su Zainura a waya suka zo dukkansu har Afrah suka ga yan Uwanta suka gaisa sosai har su Irfan,sannan driver ya kaisu gidan su Amare Salma,sunsha kallo sun gigice sabo da haduwa gidan, kwanan su Uku a Abuja Maimuna da Iklima sun samu kaya sosai wajen su Salma da Zainura har Afrah,kudi da abin arziki suka tafi dashi gida lfy,sai watarana kuma Salma zata je musu suma,Salma an shirya da family itama yanzu tana waya sosai da yan Uwanta musamman Shehu kanin Babanta yana yawan kiranta,Sai Hashim,Na'im kuma Bai son Hashim ya dinga kira masa mata tunda yaji Dan uwan Salma ne kuma ba muharrami ba akwai aure tsakaninsu shike nan ba dama suyi waya dashi sai yayi ta faman kishi yana fushi ana ji masa muryar mata.

Salma ta sani kawai sai ta shareshi har ya gaji da fushinsa ya hakura,yau ma Hashim ya kirata suna gaisawa yana hadata da dangi suna gaisawa,yace mata kuma Na'im yaje shekaran jiya,ya bada kwangila za a canja musu gidansu na Zamani ya bawa ko wanne namiji jari me karfi both dangin uwar Salma da na ubanta,Salma tayi mamaki yaje har can bata sani ba dama ranar yace mata zaije meeting Maiduguri dama ba meeting bane abinda yaje yi kenan,dadi da farin ciki ya kamata,son Na'im ya kara mamayeta ta ma rasa me zatace,suna waya da Hashim ya fito yana latsa waya duk ya bata rai,Sallama tayiwa Hashim tace sai watarana kuma in sunyi waya.
Ta kalleshi ya daure fuska kamar bai taba dariya ba,Hannunsa Salma ta rike tare da hade yatsunsu waje daya,Honey lfy naga ranka ya baci? Me ya faru dan Allah ka fada min,Na'im cike da shagwaba kamar yaro yace ni...Bana son kuna waya da wannan Hashim din,bana Zarginki don't misunderstand me kawai kishi nake ji tunda dan uwanki ne ba muharaminki bane,sanda naje nemanki ma duk ya damu da bacewar ki lokacin,komai naki baya ganin laifinki,da anje da zancenki shi zai tsaya ya wuce gaba ya saurari lamarinki haka kawai ni tsoro nake ji yaje ko Sonki yake ji a ransa yazo ya dinga ji min muryarki a banza,komai yace Salma aikin banza yaje yace wasu matan mana ko su Iklima ai suma yan uwansa ne matan yan Uwa kuma amma ni sai Salmata,gashi kuna kama dashi wlh kyakyawa dashi dan ma baiyi wani boko ba iyakarsa secondary Ashe amma yanzu na nemo masa admission a University na Maiduguri naga yana da brain,dariya Salma tayi tare da cewa kaima kana ganin kamarmu da Hashim Ashe?Wlh kowa haka yake cewa,ai cousin dina ne ,Da farko fa bama shiri dashi fada muke sosai amma yana da hankali ai,matsalarsa kawai yana dan yiwa matarsa ba dai dai ba amma Malam ya masa nasiha yanzu lfy suke zaune ya daina shirme.

Ni ki daina yabonsa wlh ba ruwana da hankalinsa ni dai ki rage waya dashi ki daina dadewa kuna gaisawa ki kashe ko kice aiki kike,Salma kawai tace to na daina ba matsala in dai akan Hashim ne ka shafawa kanka ruwa pls,naji Ashe gidanmu kaje ban sani ba,duk ya gaya min abin arzikin da kayi musu Na gode Allah ya kara arziki da Budi,Allah yasa kafi haka,Na'im ya Mike yana cewa ki daina min godiya na fada miki shi yasa Bana son na fada miki abinda zanyi zaki fara godiya,to addua fa nayi Honey,Ameen yace ya haura sama yana jin dadin adduar da Salma ke masa.

Zainura ma ba Irfan ne yaje ya gyarawa iyayenta gida ba Na'im ne bai yi shawara da kowa ba yaje ya aikata komai tare da kara musu jarin noma,sai labari Zainura taji,ta sanarwa Irfan yace ai mu haka muke family dinmu idan naga dama zanwa dangin Salma abu ba sai na fadawa kowa ba,Zainura har Na'im tayiwa godiya yace ai ta Zama family nasu duk Wanda ka aura to kun Zama daya shima ya Zama danginka,Irfan kuma ya biya musu aikin Hajji gaba dayansu Har Hunaif da matarsa,Salma da Na'im Saura 4mnths su tafi kasa me tsarki daga nan zasu je Lebanon wajen dangi da kuma Uk sai su dawo Nigeria

Hunaif takanas yaje wajen Zainura yace dan Allah idan Irfan baya nan ta dinga zuwa wajen Afrah duk abinda taga Afrah tayi ba dai dai ba ta tabbatar ta gyara mata Zama,Zainura ta dinga dariya bata kawo komai ba ta dauka wasa yake tace to insha'allah,yau kuwa ta sanarwa Irfan yana fita Office ta gama komai nata ta shirya ras ta dauki wani hadadden keken Irfan da yake fita exercise dashi kullum,irin kamar na yan tseren keke,dama ta iya kekenta tun a kauye ta fito dashi sanye take cikin doguwar riga baka hadaddiya me adon Golden da wando tight a jikinta golden,kamar Balarabiya haka ta fito ta hau keken Irfan fiiiiii ta kai kanta part din Hunaif,Afrah tana sama ta hango Zainura a Keke ta window ita kanta abin ya bata dariya da sha'awa Zainura kamar wacce take turai,tukin keken ma iri iri takeyi har tukin carrier takeyi har tazo gidan ta danna bell,tuni Afrah har ta bude mata kofa,ta shiga suna ta hira cikin harshen turanci, taga Afrah komai sai dai yan aiki suyi mata,girkin ma ba sosai takeyi ba sai taga dama,idan taga daman ma sai tayi wanda baza ka iya ci ba irin na Larabawa ko tace Wai tuwon Dabino da miyar Kubewa danya zatayi,kubewar ko yankawa baza ayi ba haka suke tsumbulasu guda guda wai anyi miya,ga kuma tuwon dabino hhhh,ko ta kawo ganye kawai da gurasa ana karyar wani green pepper,Zainura tace a bata abinci ai kuwa da murna tace yau tuwon Dabino miyar Kubewa za su ci yana cikin fridge,Hunaif duk da Rayuwar turai sukayi Mummy abincin Nigeria take yawan yi musu basa cin na turan sosai sai sama sama,
Zainura tace Dabino din Uwaki Afrah na taba Jin wani tuwon Dabino,Zainura ta zauna ta dinga ganar da Afrah abinda Hausawa suke so,Zainura bata San kadan ba ta dinga mita da masifa kamar uwar Afrah,tace kuma dole ta dinga gyarawa mijinta dakinsa da toilet da kanta,ta daina sa yan aiki,Zainura dan ta tsorata Afrah tace a Nigeria sex yan aiki sukeyi da mijin mace idan sun aiki,Ai ko Afrah da kishi tace zata kori yan aikin ma,Zainura tace mace daya dattijuwa za a bar mata kawai ta isa,nan aka mayar da sauran gidan Mummy da aiki,Kullum yanzu sai Zainura tace ta koyawa Afrah girki,kula da miji da sauran Abubuwa,idan tace tayi batayi ba ta shiga uku da Zainura yanzu zata ci zagi ba ruwanta,sati daya Afrah sai gashi ta gyaru,Hunaif yana jin dadinsa,yanzu tanayin kusan ayyuka da yawa,Zainura kuma tana ci gaba da koya mata girki har ta WhatsApp take tura mata irin wanda mutum zai iya ci,haka Salma ma ta dage tana dan lekawa watarana ta koya mata, sabo da anan nake so Naja hankalin mata masu yin girkin turawa da sauran girke girke,idan kika ce zaki dinga yin irinsu ke ga yar gayu mazanmu basu saba da irinsa ba,normal girki da mutum zai iya ci ya koshi zaki dinga yi sauran su snacks da abubuwan zamani ba a iya ci a koshi da marmari ake dan tsakurarsu a ci,sai ki samu kiyi irinsu kamar watarana idan yaci abinci abinci wurin 5pm ko wurin magrib to da dare sai kiyi na yan gayun duk tsiya kin San ba abinci yake nema me yawa ba sai aci wannan da marmari kadan ya isa,haka da safe ma ko da hantsi irin an gama breakfast kafin lunch to hantsi akwai yar yunwa zaki iya yin wannan ma,amma ba kawai kizo ki tafka su snacks da wasu girke girke da ba a iya ci kice ke abincin rana ko na dare bane ko dole shi za ayi breakfast dashi wrong Idea,very bad yaren Prof😅😅 naga yanzu da anyi auren mace wai irin kula da miji ta waye ita yar gayu sai taje tayi ta tafkawa me gida irin wannan girke girke marasa kan gado daga nan ma wani a tsure da Zawo.

Sai kuma girki dole matanmu mu kula mu koyi balance diet a dinga balancing abinci,karki zo ko mijinki yana da kwantancen ciwo kin ta dura masa abu daya kullum har ya tashi ciwon,ko yana risk na kamuwa da wata cuta baki sani ba Bai sani ba kizo ki ta bashi wasu abu ya tashi ciwon.
Har kullum ina fadawa mata cewar jikin mace da namiji ba daya bane,mata suna da kariya da yawa a jininsu,suna da wasu sinadarai da Allah ke hallitarsu kadai a jikin mace Immunoglobulins,garkuwace ta cikin jini masu yawa,mata duk suna dasu,namiji kwaya daya yake dashi shima wanda yake gado ne wajen uwarsa yake crossing placenter ya shiga jikinsa,shi kadai ne yake da ability na crossing placenter to the child,ga period tana tafiya da cutuka,gashi idan mace ta haihu jinin biki da wannan ruwa na haihuwa da suke zubarwa duk tafiya yake mata da cutuka,shi yasa cuta tafi saurin tasiri a jikin maza,da ta kama namiji zata nemi hallakashi ko magani bai cika yi masu tasiri ba kamar mace, mata a kiyaye,i internal organs suna da matukar hadari tunda ba a ganinsu, ba ganin kayan ciki ake ba bare kasan kaza ya Kamu da ciwo etc.

karki ga komai ya siyo miki na Jin dadi kice ke kullum dadi za aci,misali zan baku ace mijinki yana da ciwon hanta ta dan Kamu bai sani ba baki sani ba,sabo da kinga kullum akwai kwai a gidanki sai kice kullum ke sai da kwai zaku karya,kiyi ta sarrafa diff food da kwai zalla,kece soya wancan da kwai yi wannan da kwai,maiko,komai protein food to wlh ba zai dade ba zaki kashe mijin ki sabo da ke gani kike kun birge baki San cuta tana ta cin karfinsa ba,ko yana da ciwon sugar ko ya kusa kamashi baki sani ba kizo komai naki na kayan zaki zaki bashi,ko yana da ciwon kafa ba a so yaci Naman dabba kina ta abinci dashi,ya kamata mata mu dinga komai da Ilmi,musamman abinci,a nemi sani ayi ilmi a kansa sabo da lafiyar jikinmu data mazajenmu data yaranmu,a kiyaye yawan cin abu ba balancing,ko kina siririya maybe shi yanda kike siririya haka yake sonki bai son kiba kin samu dadi kika dinga narka sai ki canja ki dawo jibgegiya shi kuma siririya yake so kinga kinwa kanki hhh.
Kar Kuma ace abinci me lafiya a dinga kwabashi ta ko ina ace ai ba dadi ake so ba lafiya yake karawa da matsala tunda nasan akwai masu yin hakan😍😅,

sai addua mata a yawaita addua musamman ta lafiya,idan kina da wani ciwo ko danki ko mijinki,kiyi Bismillah ki daura hannun dama akan ciwon idan ma a ciki ne ki dora hannun kan cikin kullum ki karanta Fatiha kafa bakwai hannunki na saman kan inda yake ciwon to insha'allah ko baki warke ba Allah zai kawo miki maganin ko hanyar maganinsa da gaggawa cikin sauki kuma kina zaune katsam magani zaki ga hanyarsa tazo,ko da kansa ya warke,Allah sa mu dace.

Sati biyu Afrah ta gyaru ta gane komai,ita kanta yanzu tafi jin dadin jikinta bata kwanciya kullum ba exercise aikin gidanta shine exercise nata ana motsa jiki ana kara samu lafiya da karfin jiki,kullum cikin kazar kazar,Girki kuwa ta fara iyawa da yawa Salma ma tana koya mata wasu,Zainura tayi namijin kokari sabo da kullum sai taje a Keke,yauma ta dawo suuuuu a keken ta hango Irfan,Na'im,da Hunaif suna tsaye suna tattaunawa sai nishadi da zumunci sukeyi,su Kansu sunyi dariya ganin Zainura a keke tana ta tsere da keke a gidan nan,Shi kanshi Irfan Bai taba Sanin ta iya kekenta ba sai yau,sabo da bai San tana hawa ba,tunaninsa ma a kafa take zuwa har gidan Hunaif tunda tace masa itama exercise zata fara,ashe a kekensa take zuwa,dariya suka dingayi,Na'im yace matar nan taka bata Ji akwai kiriniya,Irfan ya daga mata hannu ta daga masa itama ta figi kekenta tayi part dinta ta koma ciki,ta huta sannan ta tayi sabon wanka ta dau wankan kananan kaya na daukan magana tare da fadawa kitchen tana shirya abinci.
Ta baya Zainura taji Irfan ya rungumeta yana sinsinar wuyanta tare da shakar kamshinta,ba tare da ta juyo ba tace sannu da Zuwa habibty muje ka huta,nooo... Muyi girkin a haka,hannunsa suna rungume da hips dinta ya kwanta a jikinta gaba daya a haka suke aikin,Zeena ta mika hannu zata dauki plate hannunsa a haka ya dauko mata yana jikinta,sai ya karbi spoon din yana juya abincin kuma still yana rungume da ita kwance a bayanta hannun kawai yake dagowa daga hips dinta yayi abinda zaiyi ya maida abinsa, tana soya naman kaza yana dauka a haka ya ci itama yana bata a baki.

Afrah kuwa yau tuwon danyar shinkafa tayi miyar egusi tayi dadi sosai,Hunaif yana son sa sosai ya dinga murna yana godewa Afrah,ita kuma sai dadi take ji tare da godewa Zeena,Afrah ko Dattijuwa me taimaka mata bata bari ta zauna a Palo idan Hunaif yana gida tsoro wai takeji Kar ta kwace mata mijinta abin alfaharinta.

Kwance take cikin Jin dadi amma abu daya ya hanata sukuni wato rashin su Affa a kusa,i dan ta tuna yanda suka riketa da Amana tun tana karama amma yanzu gashi lokacin da zasu ji dadin abin basa tare,tana tunani bata San Sanda hawaye ya fara sintiri a fuskar ta ba, tana wannan Na'im ya shigo yana Sallama amma bata San yanayi ba,ganin tana kuka ya karaso da sauri tare da mikar da ita zaune ya daurata a jikinsa yasan bazai wuce su Affa take tunani ba,tunda ita Salma dasu ta shaku sunfi kowa a wajenta,Na'im yace su Affane? Ta daga kai cike da shagwaba,its ok ko kidnapping dinsu wlh zanyi na kawo miki su,ko suna so ko basa so Salma na sai na kawo miki su very soon surprise zan miki ina sane dasu,sai lokacin Salma tayi murmushin jin dadi,yana lallashinta yana lashe mata hawaye da harshensa har ya samu tayi shuru sannan ya dauki abarsa suka shiga wanka.
















Ayi Sharhi fans,kar a gaji.




AsmaBaffa[1/14, 5:14 PM] Sis Asma: 🏉KAMARSU CE DAYA🏉





221-225 256-230









Official








By
AsmaBaffa









ASMABAFFA FANS CLUB INA MATUKAR GODIYA.











Bayan sunyi wanka zaune suke yana dan janta da surutu ko zata daina tunani amma bata wani magana sosai,kallonta yake a nutse kana yace wato sweetheart ban isa nace ki daina abu ko daina ba ko,su Affa nace Insha'allah zan kawo miki su mene abun damuwa,haba Babyna,why r u doing ths to me? Salma Hawaye taci gaba da yi abinta,yana kallon ikon Allah dazu fa ya lallasheta,tana shesheka tace na...dai...dai....na, baki yarda dani ba My love?nace miki zan kawo miki su kuma insha'allah zasu dawo dake kamar da,Salma a hankali tace Na yarda mana,amma kike kuka again? Cike da shagwaba tace ai na daina,kwantar da ita yayi saman Bed din rabinsa yana samanta,fuskarta yake shafawa a hankali ya hade fuskarsu tare da furta Smile Baby,murmushi tayi masa me shiga zuciya, nan take wani shauki ya kwashe shi ba bata lokaci ya mika lips dinsa tare da niyyar kissing dinta itama ta miko tare da lumshe ido sai ya fasa,sai ya kara haka,haka har ya hade lips dinsu yana kissing kadan yana janyewa har ya yi me gaba daya wato ya fara mata hot and deep kiss har hakoransu suna haduwa,tuni Salma ta karbi sakon hannu bibiyu.

Yau kimanin wata 3 kenan da auren su Zainura Soyayya suke zubawa kawai,sun kusa tafiya Saudiya,Zainura taje gidan Aisha tare da Afrah,Salma ce bata je ba tukun,Mummy kuwa suna sosai suna gaisheta,zaman lafiya suke ba a magana.
Aisha ma sunzo da Doctor Aliyunta sunyi zumunci,Kwana nan kuma Zainura ta fara Dan Zazzabi da tashin zuciya sama sama,Yau Saturday Irfan yana gida zaune saman Sofa dake palon,tun safe Zainura bata iya cin komai tashin zuciya take,Tana gefensa yana lallabata taci ko kadan ne,tace Sam idan ba yashin Madina ba babu abinda zata iya Sha,Da sauri ya fita har wajen Tsohuwar nan dake Islamiyyar yara ya siyowa Zainura Yashin Madina da yawa,ta zauna tana ta sha kamar ta samu Nama,tana gamawa tace yaje gidan Salma ya karbo mata Wainar flour da danwake,haka yaje duk ya damu,Na'im yana gida yana shagalinsa a jikin Salma,Irfan yaje ya dameta yayi sauri ta yiwa Zainura abinda tace,Na'im yace idan zaka kaita hospital ma ka kaita ba kazo ka damu mutane ba,Irfan bai ce komai ba ta lafiyar Zainura yake,ana gamawa ta bashi a flask ya tafi da sauri ya kai mata,tana ci tana murna,abin Zainura bai tsaya nan ba sai da yaga ta fita neman inda ake siyar da agwalima,yaje ya siyo mata yace ta shirya su tafi asibiti,asibitin Na'im suka je ya samu Doctor mace ta aunata tare da tabbatar musu cewar ciki ne da ita har na wata biyu da sati biyu,Zainura harda Rawa sabo da murna,Irfan kuwa kamar ya tsage da ihun murna haka yake ji,Suna parking a compound Zainura ta fito kamar wasa ta dage ta kwalla da karfi jama'aaaaaa.......I naaaaa...da.....cikiiii,kuuuuu.....fito....ciki...ne dani....Irfan yana dariya yazo shima ya tsaya kusa da ita ya dage da karfi nayiii....mataaa....ciki....sai....niiiii.....kyakyawan result har ya fito,Zainura tace sai....mijinaa...me....lafiya.....Wlh...good...job..suna ta dariya tare da Haki, duk yan gidan da ma'aikata sai da suka fito da sauri sun dauka wani abu ne tunda basa iya jin me akewa magana kawai suke ji da karfi,Sai da suka saurari abinda su Irfan suke cewa sannan suka gane, ai Salma da Afrah kamar sune da cikin,ikon Allah Salma ta riga aure da wajen shekara ma amma ga Zainura ita wata Uku kacal har ta samu ciki,
Na'im da Hunaif sai murna suke tayasu haka matan ma da ma'aikata,ba bata lokaci suka kira Mummy suka fada musu da abokan arziki,har na kauyen su Zainura frnds,iyaye da yan Uwa sunji labari ta waya.
Zo kuga kula da Zainura wajen Irfan Kamar wata kwai.

Wata daya tsakani suka bar kasar zuwa Saudiya,Na'im da Salma,Irfan,Zainura,Hunaif,Afrah,Aisha tare da mijinta Doctor Aliyu,suna gama aikin Hajji suka suka tafi Lebanon ansha riti,sai USA,daga nan suka dawo Nigeria,Zainura da Irfan sunje kauyen iyayenta kwanansu uku sunsha hira dasu Jamila suka dawo gida,Jamila ta samu miji a birni itama,Haka Zainab cikin Katsina,sai Zahrau Kd,Barira kano kusa da Rahina a nan ta samu miji,duk an sa ranar bikinsu,Rahmatu ma wani dan Uwansu aka bata dake Zaune a cikin dutse Jigawa state counselor ne a can dutse alhmdllh sun samu nutsatsu samari duk da cewa Zahrau ce kawai zata auri wani me mata me kudi dan 40yrs duk sauran masu rufin asiri ne amma samari kuma wayayyu yan Birni.

Bayan wata biyu da dawowar su Salma daga Saudiyya Afrah ma ta samu ciki wata daya,lokacin na Zainura har ya girma ana ganinsa,Itama sai murna kowa ta fara iya hausa yanzu,Salma har tausayin kanta taji,sai tunani take ko bata haihuwa ita Na'im zai iya karo aure wata ta haihu,hankalinta ne ya tashi duk da tana kokarin dannewa tana addua tare da turawa Allah Lamarinta,bata gama tsurewa ba sai da taji cewar Aisha ma ciki ne da ita na wata biyu,Allah sarki Salma ranar sai da tayi kuka a boye na tausayawa kanta.
Gashi sai taga Na'im normal harkar gabansa yake ko a jikinsa,tana so ta masa zancen ko zasu je asibiti amma tana tsoro.

Tana zaune a Palo ita kadai tana tunanin halin da take ciki ita har yau ko bari bata yi ba,katsam sai ga Na'im ya shugo bayansa Ummitu da Malam ne Shar dasu gaba daya babu alamar cewar Affa yayi wata cuta,haka Ummitu babu maganar wahala a jikinsu kamar ma sun Zama yan Birni haka suke,a rude Salma ta Mike harda kukan Dadi,Affa da Ummitu suka zube a kasa tare da fara bada hakuri,Salma da sauri ta katsesu haba Ummitu ashe ma zan bar iyayena na jini su bani hakuri,ai ni ya kamata na baku hakuri,ku zauna dan Allah Affa in ma nice na yafe muku kuma ku yafe min,Ummitu tana kuka tace baki mana komai ba yar nan mu ne da laifi sabo da son zuciya,yanzu mun gane gaskiya,Allah yayiwa mijinki Albarka,kinyi dace Salma,Salma tayi murmushi sannan Ummitu ta bata labarin halin da suka shiga da cutar Affa,Salma harda kukan tausayi,sannan Affa yace mijinki shine silar warkewa ta,muna zaune cikin kunci katsam sai gashi yazo da motoci,yana ganin halin da ya samemu yasa aka kwashe mu har birnin Abuja cikin asibinta sa shine yayi min magani ya kashe makudan kudi na warke,haka bayan na warke ya mai damu gidan kakarsu Dada a nan aka bamu bangare guda,da masu aiki bama komai sutura da komai sai dai mugani ya kawo ko ya aiko dasu,yanzu in kinga jin dadin da muke,kuma Mummy mahaifiyarsu da kowa nasa ya sanni ke kadai ce baki sani ba,har su Zainura da Afrah sun San damu,yace kar a

1 Comments On KAMARSU CE DAYA
avatar
abdulkadir-lawan-yusuf

9 months ago

Reply

Littafi me ma'ana

Please Login or Register in order to submit comment