Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

har abada,
Salma tana wankin kayansu da nata da nasa tana kallon abinda yakeyi idonsa har ya canja kala Sabo da jarabar Na'im, Salma ta kalleshi suka hada ido ta saki murmushi me tsada da birgewa,dimple nata ya loba,Umma na kallonsu ta tashi cike da kunya ta fada kitchen tana aikin abincinta,Salma ta dago masa hannu da kumfa a hannunta,dariya ya mata tare da yafito ta wai tazo,sanye take da English wears riga da skert sun mata kyau,cikin lafiyarta ta jan hankali da birge me kallo ta karaso wajensa ta tsuguna megidana gani,Na'im yaji wani sanyi,ya kalleta tare da mika mata tafin hannunsa yace mu danyi kadan kafin Malam ko Umma su gani,Salma tace me fa? Yace dan sabon mu danyi kadan Malam yace Sabo ne taba mace ba muharramarka ba ko?Salma tace eh,why not yau na taba kadan mu danyi kadan? Salma tace gaskiya hakane mu me mukeyi ma na Sabo ai mu salihai ne,to mutane da dama suna ganin basa aikata Sabo ko me sukeyi ai kadan ne,baka sani ba da kadan din sai yafi me yin babba a wajen Allah,Allah Sa mu dace.
Salma ta mika masa Hannun ta me santsi da laushi shima Na'im haka ya hade hannun waje daya gam yana murzawa Salma tana lumshe ido,yana kare mata kallo kamar me,da kyar ta kalleshi a kunyace yace me kike ji?da dadi?Salma ta rumtse idon kunya tace uhm...wani zir..zir...Kamar tafiyar tsutsa a jinina,A hankali Na'im yace nima haka,Malam ya mana auren ko?,Salma ta daga kai wai ae idan ya dawo ka fada masa tunda idan anyi aure ai zamu iya rike hannu da rungumewa ma Na'im yace hakane bari ya dawo je ki karasa aikin ya sake mata hannu ta koma wajen aikinta shi kuma yaci gaba da kallon abarsa,Salma tace au munyi Sabo to muyi istinghifari,sai ko kowannensu ya fara astaghafirillah wa atubu ilaih a hankali suna ta mus..mus..da baki.

Da dare Na'im yaje har dakin Malam suna tare da Umma ya sanar masa cewar ayi musu aure shi da Salma,Malam yace nafika son na hada wannan auren Amma ban san ko Salma ta taba aure ba taya zan hadaku azo a shiga matsala,Salma tana labe a jikin kofar harda goge hawaye anki yarda ayi musu auren,ta leka ta jikin labile tare da cewa Malam ni ban taba aure ba fa,Malam yace taya kika sani tunda bakwa tuna baya?Salma tace koma na taba auren ni wlh ko memory na ya dawo ni bana son wancan mijin nawa na farko wannan nake so Muhammad dashi zan zauna.
Malam yayi dariyar Manya sannan yace to ni dai Bazan daura ba sai Kwakwalwarku ta dawo dai dai.

Na'im kamar zaiyi kuka ya mike ya bar dakin,yana fitowa Salma ta tareshi harda janshi can wajen zauren kofar gida tace yanzu dai kayi hakuri tukunna muga abinda Allah zaiyi,ka daina fushi kar kasa damuwa ko ina da aure dole dai kai zan aura in dai muna raye,mene abin damuwa kuma? Na'im yayi shuru yana jin yanda take kwantar masa da hankali ba shiri ya jawota jikinsa cikin duhu ya rungumeta kam suna jin kamshin juna,bakinsa ya saka cikin nata suka fara kiss so deep Salma ta kara kankameshi a jikinta,sai kuwa suka ji motsin Malam zai fito daga daki zai je toilet,da sauri a tsorace suka saki juna Salma tayi waje kofar gida tunda 8pm na dare ba a dade da yin Sallar Isha ba,Na'im kuma yayi cikin gidan suka ci karo da Malam,yace ina kaje kuma Muhammad?yace wani...wani...uhm.....wani na duba ko zan ganshi akwai abinda yace zai fada min,Malam yace anya kuwa kana da gaskiya Muhd? Murmushin rashin gaskiya yayi yana sosa kai yace Ba komai fa,Ina Salma? Malam ya tambaya amma Na'im yace tana dakinta tace bacci zatayi yanzu.

Malam yace to to madalla ya shige bayi,Da Sauri Na'im ya leka cikin kasa da Murya yace shigo yana toilet, Salma ta shigo da gudu ta fada bedroom dinta tana dariya ta haye Gadonta ta fara baccin karya,Malam na fitowa Na'im yace Malam zo kaganta har tayi bacci ma Ashe,kuji rainin hankalin Na'im,Malam yace ai na yarda daku kyaleta Allah tashe mu lfy ya shige dakinsa.
Washe gari kuwa Umma ta tafi cikin birnin Katsina wajen kanwarta,Malam yana gona,Salma da Na'im kadai ne a gidan suna aikinsu tare kamar yanda sukeyi komai tare,Na'im ya kalli kirjin Salma yace ina son wannan abu naki,me?Salma ta tambaya,hannu ya kai saman boobs dinta da niyyar nuna mata,ta bige hannunsa tare da harararsa da wasa tace kai shiii dodo ne shishi ne,ba a tabawa,Na'im ya tintsire da dariya yace ni yaro ne zaki ce min wai dodo ne,Salma ma dariya tayi tace to kamashi dodo, indai wannan zai kamani to naji dadi cewar Na'im,Iskanci ne fa Salma ta furta,ashe Na'im ya haddace Kalmar zai fadawa Malam gaskiya watarana yana son Iskanci ayi masa aure.

Salma ce ta fara magana cike da nutsuwa serious muyi Sauri mu tuno baya ayi mana aure mu huta kaga idan bamu tuna ba Malam bazai mana auren ba,kullum ni ina kokarin tunawa da dare Amma har yau na kasa tunawa wlh,Cewar Na'im
Wasa wasa sai ga Salma da Na'im sun kwashe wajen wata tara a gidan Malam Magaji basu tuna komai ba.

Ranar Juma'a da dare Salma ta kara zuga Na'im ya koma ya fadawa Malam ayi musu aure,ta kara labewa a jikin labile tana ji,Na'im kalar tausayi yayi zaiyi kuka yace pls Malam ayi muna auren nan mana,Umma tace nima ina bayanku kawai ayi musu wlh nan gaba in sun tuna idan da matsala sai a warware,Malam yace sam basu da hankali bazai daura ba shi dai,kuma Bada yawunsa ba,Na'im yayi tunani ya samo reason dinsa budar bakinsa yace Malam ni dai ina son Iskanci tunaninsa sunan Breast ne hakan wai yana so,Malam ya hangame baki tare da ware hannu ya cillowa Na'im zagin manya dakuwa,ya kara masa ambola yace gidanku Muhd baka da hankali,Malam ya zauna yayi iya kokarinsa na ya fahimtar da Na'im me kalmar Iskanci ke nufi a Hausa Amma sai Na'im yace ai shi din yake so iskancin dai shi yake so,Umma ma tayi bayani kamar bakinta zai ciwo Amma Na'im yace ni dai ina so na zama dan iska tunda shi nake so,Malam sunga dai bazai gane ba kawai sai ma kunya da yake basu Suka ce ya tashi ya tafi,Kafin ya tafi ma saida ya kalli Malam yace ina son Iskancin Salma ni dai,Malam yace to dan ubanka wlh ka sake ka taba ta sai kaci gidanku Allah zai kona ka.shi dai Na'im yayi ficewarsa abinsa.

Malam yace naga ta kaina idan yaron nan yayiwa yarinyar wani abu,ni ya zanyi dasu yanzu idan tana da auren wani fa,kuma aure ba sanin iyayensu wlh Bazan iya ba.
Umma taji haushin Malam tace shike nan wlh alhaki a kanka su fa yanzu kwakwalwarsu a juye take komai zasu iya aikatawa bana son a samu matsala Malam mu zo muna danasani dan Allah ka daura musu auren nan,ni wlh ga raguna guda biyar a gidan Kanwata zan siyar na Bada sadakin,Malam yace ni ance miki bani da kudin ne?ko kyashi nake? Ranar dai sai da sukayi fada Da Umma da Malam tace sai an daura aure Malam yace a'a.

Na'im kuwa yana fitowa idonsa cike da kwalla saura kadan ta zubo shi kadai yasan me yake ji na Sha'awa kuma Salma kadai yake jin hakan a jikinsa.
Salma tana rakube a Bango taji ba nasara yau ma sai sharce Hawaye take ita dai Son Na'im kasheta zaiyi ma ta sani.
Na'im ya karasa kusa da ita yace nasan Solution ki bari sai gobe dole Malam yayi mana auren nan,7:30muke shigowa daga Sallar Isha to gobe kawai ki tsaya a zaure Bazan je masallaci ba a gida zanyi Sallah,Salma ta mike cike da kuri irin shegiyar nan an samo mafita tace za a gani ne wlh sai Malam ya san mune yan zamani mu muka san Zamani, we no dey carry last tayi kwafa. har kofar Bedroom nata Na'im ya rakata tare da riko hannunta yana wasa da yatsunta Salma jiki ya dauki Harama da niyya fa anyi shuru tayi lakato har ya sata a kirjinsa tare da rungumeta kamar suna Aljanna haka suka ji,da kyar ya saketa saida ta tuna masa da Umma ko Malam sannan ya mata kiss a goshi ta shige daki tare da yin juyi ta fada saman Bed dinta na jin dadi,Na'im kuwa yana haurawa saman Bed sai pillow ya jawo tare da rungumewa kam kamar shine Salma yana ta faman murmushi tare da Tafiya tunani Amma baya tuna komai sai rayuwarsa gidan Malam Magaji,haka ma Salma abin yake.






Sharhi fans






AsmaBaffa
[1/14, 5:14 PM] Sis Asma: 🏉KAMARSU CE DAYA🏉






71-75






Official





By
AsmaBaffa








Khadija A Hamza,Salisu Aisha,Fatima Abdullah,Naja'atu Aleeyou,Queen kk,Mom twins,Hadiza Hussaini and Agas wannan page naku ne Ku kadai Masoya.



Mrs.M.D.Argungun Ina godiya ina posting zanga comment naki tnx once again.


Mummy abin nata harda rashin tawakali ma domin yanzu har sambatu takeyi kala kala,yau tana kwance ta rame tayi baki kamar ba Mummy ba kowa ya ganta sai ya tausaya kamar Na'im ne kadai danta,Su Irfan har basa son ganinta Sabo da zuciyarsu karyewa takeyi,duk wanda ya shigo sai dai ta dinga Na'im kaine? Na'im dina ya dawo?Na'im zo na shafaka naji,abin gwanin tausayi surutu iri iri.
Dada ta dawo gidan da zama tana kula da yarta,haka dangi ana zuwa musu jaje da duba Mummy, yau Dada ta shigo dakin sai ko Mummy tana daga kwance Hawaye na sintiri a idonta ta fara Na'im kaine?ka dawo? Zo ga Mummy naka,Salma kake so?zan aura ma ita,duk inda ta shige za a nemota,Dada tayi tsalle gefe tare da cewa yau na shigesu da wannan yarinya ni yau me zan gani haka?kashe kanki zakiyi Sabo da rashin karbar kaddara,sabo da rashin tawakali,da mutuwa yayi fa sai kema ki bishi,yara nawa gareki baza ki godewa Allah ba sai shashanci,Mummy ita dai ba ruwanta tana ji ance ma da mutuwa yayi fa ta saka kuka wiwi harda gunji tana ni gwara na mutu na huta,gwara na shiga daji,Irfan duk sun tsaya can gefe ransu ya jagule,Aisha kuwa kuka itama take taya Mummy,tana tausayin Uwarsu,yanzu Aisha babu jin dadin rayuwar da za tafi shaye shaye,an daina lez ma gaba daya ta daina komai yanzu to gida ba lfy,dama komai jin dadi ke sawa ayi,Irfan kuwa shi ke komai duk business na Na'im shi yake rike komai bashi da time ko kadan,Hunaif ma ya zage a wani part din,kullum Irfan idan yaje Office companies na Na'im sai ya zubar da Hawaye,haka sauran ma,Hunaif kuwa Hospital din shike kula dashi na Na'im idan yaji ana neman Doctor Me Imani sai zuciyarsa ta karye ya zubar da Hawaye,ace sai dai kaninsa,nan ya tambayi me Na'im kewa patients ne suke damuwa dashi haka ana Jimamin rashinsa?Suka ce ai kaf patients indai shi ya dubaka to komai girman cuta kyauta za ayi maka aiki,nan Shima Hunaif duk Ranar da ya shiga asibitin shi ba Doctor ba amma Idan wasu Doctors sun duba zai zabi da yawa a musu komai kyauta yanda Na'im keyi yace idan ya mutu Allah haskaka kabarinsa,idan kuma yana raye anyi Sadaka Allah bayyana shi da gaggawa.

Aisha kuwa Watarana tana zuwa Embassy ta sanar musu duk halin da ake ciki fa ba a ganshi ba,wayoyin Na'im da System nasa duk Irfan ke Amfani dasu wajen Aikinsu.

Dada dai taga Mummy idan sunyi sake haukacewa zatayi kawai ta fara taimako da adduoi Amma abin kullum ci gaba yake,Irfan yace kawai a kaita asibiti ta zauna acan kar brain nata ya samu matsala.
Nan aka kai Mummy asibiti ana kula da ita ko yaushe,Dada na wajenta su Aisha suna hanya kullum har dare asibiti ya koma kamar gidansu ma.
Mummy tana dan jin sauki yau ma ta mike zatayi Sallah ta kalli kudu,Dada tace hauka kike ne?ga gabas nan,nan ma Mummy a kalli Arewa abinta zata fara Sallah da kyar aka samu ta daidaita abin ba dadi dai.

Salma da Na'im soyayya sai abinda yaci uban da,kullum Karuwa take a zukatansu kamar su hadiye juna, Malam Magaji ya siyawa Na'im waya me kyau yar dubu ashirin Tecno sabuwa dal,suka siyi sabon layi yasa,nan Salma ta karbo wayar Rahina suka tura hotunansu na Sallar taushe,Kullum sai sun dauki hotuna kamar hauka a wayar nan duk wanka sai sunyi selfie,Umma da Malam tun suna shiga har sun daina ana yin hoton dasu,har video suke daukan kansu idan sun fita yawo a garin,Yauma Umma ta aikesu a siyo mata Kubewa danya da dankalin Hausa,sun fita sai hira sukeyi suna tafka muhawara akan kalmar Soyayya da kauna,Salma tace na fika iya yaren nan fa So shine Love fa,Kauna kuma fa? Yace kauna...kauna ya tafi tunani ya kasa tunawa,Salma tace ahaf shine dai so,sanda kayi min kiss din nan jiya kasan sunansa?to soyayya mukayi fa,Na'im yace hakane soyayya?ke baki santa ba dalla,ai so shine soyayya ake soyawa,Salma ta langabe kai tace ohhh...na gane a kasko ko?yace kwarai ke baki ganewa ne har yau,tace to ai gwara da ka ganar dani kaga yanzu na gane,Ko dai mu tambayi Rahina? Na'im yace nop komai sai mun tambaya tunda muna ganewa mu daina tambayar kowa tace to.
Tunda Na'im yake bai taba zagi ba na ashar amma a kauyen nan ya iyata,daga shi har Salma basu san zagine ko ba zagi bane su Kalmar ma dariya take basu,sai suyi ta narkawa junansu ita suna video a waya,Salma ta daga waya sama yace Dan bura Uba shege suka kyalkyale da dariya,Salma ma ta fada masa,idan Umma ta aikesu har gajiya take da jira Sabo da hira da sukeyi da jarabar daukan hoto da video.
Suna dawowa Umma ta rufesu da fada tace daga yau na daina aikenku tare ba inda Dayanku zaibi daya,ya Isa na gama abinci Amma kuna can kuna daukan hoton Banza da wofi.
Saida suka bawa Umma hakuri ta daina musu masifa.

Tunda Na'im yace Salma zata jirashi a zaure yau kimanin 3days kenan basuyi komai ba akan Malam ya musu aure,waya ta dauke musu hankali sun manta da zancen nasu,Na'im garin danne danne ya gano yanda ake searching abu a Google nan ma Google yaga ta kansa shi da Salma duk kudin Malam suke karbewa suna Sa kati suyi ta searching Words na banza da wofi.
Malam Magaji ne yace ko su daina ko Ya kwace wayar shike nan aka samu salama basa dannawa sai jefi jefi,Malam yaga Sabo da waya ko addininsu yaja baya kawai ya kwace wayar ya kashe tare da boyeta yace su zauna haka tunda ba a musu abin arziki,Yanzu ba waya sai radio FM da Am da suke jarabar ji kowanne shiri ji sukeyi kullum radio sai za ayi bacci ake kashewa nan ma sun damu Malam ko wanne shiri sun san da zamansa musamman shirin soyayya ko karatun Novel har na yaki,Da sunji abin mamaki Salma zatace kai kaji dan Allah Me gidana,shima da yaji zaice kinji yi shuru,yauma ana shirin rai dangin goro sunaji ana karantawa ance Farouq ya mike ya zabga mata mari Salma ta dauki radion ta manna ta a bakinta tace ki rama kema mana Sadiya,ta kara fada da karfi,Na'im ya kwace yace baki iya ba basa Jinki muryarki tayi low,nan ya jijjiga Radion tare da cewa Farouq ka kara mata 1slap me cuta ce,Radio shuru sai karatu akeyi Salma ta doka radio da kasa tare da cewa aikin banza dan wulakanci sunki mana magana,Na'im yace gwara da kikayi haka kin birgeni,Saida Umma ta fito sannan ta musu bayanin mene Radio sukayi Zuru suna ji suna mamaki,Salma tace wai a duniya duk ake da wannan abin haka? oh duniya ina zaki damu cewar Na'im.

Sati daya tsakani Malam ya siyo sabuwar mota Gulf 2 zai dinga kai kayan nomansa kasuwa,dama ya iya mota Sabo da ya taba driving Taxi a Abuja.
Nan ya fara koyawa Na'im,Na'im sai yaji kamar ma ya iya tukin Amma ya kasa tunawa,sabo da tun da ya iya kawai sai gani akayi ya iya mota Amma ya kasa tunawa,kwana Uku ya koyi driving na kwararu,Tofa mutanen an samu abin yi,duk ranar da Malam baza su kai kaya kasuwa ba shi da Na'im to sai Na'im su shirya tare da Salma yasata a gaban mota su zaga kauyen da wasu kauyukan.
Yau kuwa Saturday Malam yana gona suka dauki Motar har cikin garin katsina city Salma ta hangame baki wai nan a ina muke haduwa wayyo,ta dinga nune nune kalii laaaa kalli kaga,Shima Na'im abinda yasa ya sani suna dan zuwa watarana da Malam,sukayi parking wani waje falau falau ya rike hannunta suka dinga zaga gari a kafa,suyi can suyi nan kamar yan tasha,Salma da yar doguwar rigarta da mayafi iska na kadata,Na'im kuwa Jallabiyace milk a jikinsa yayi kyau duk inda suka wuce kallon turawa akeyi,musamman Na'im da yake me farin Bature.
Tun Safe suke zaga garin unguwa unguwa wani a mota wani a kafa har wajen magrib,sannan suka fito zasu tafi gida Salma ta hango Bra a rataye suna Lilo tace laaaa kaga siya min wannan a Cikin kayana babu ita,ai kuwa kudin man mota da kudin Masara na Malam da ya bashi gobe za a sha mai dashi,S sauran kuma za ayi harkar Noma wajen Dubu dari,Na'im ya ebo bazai iya kasa siyawa budurwarsa abinda take so ba sai daí a fasa shan man da noma,Nan yace nawa wannan? Dari bakwai ya siya mata har kala Uku,me saida kaya yace ga panties ma suma ya siya mata har goma,aka kara cewa ga short Wando na mata da Maza ya siya musu kala Uku Uku,Salma taje layin masu glass tace kai a ina ake Sa wannan yace a ido harda gwada mata dan su siya,Na'im yace a siya miki?tace ae ta zabi wani baki wuluk kafcece na manyan Yara ya siya mata tun a wajen ta sa abinta yan kasuwa suka dinga zuki kai kai,Na'im ya hade rai harda masifa yace zasu fasa siya ma,Salma ta hango Atamfa yar 3k da wasu Yadi na Maza tace a siya,Na'im yace ke saura kudin Malam na masara da ya siyar,amma tunda kina so ba matsala nan ya dauko kudin a mota ya siya mata Atamfa har kala Uku tace a siyawa Umma daya,aka siya,tace kaima ga Yadi ka siya sai mu Bada dinki a Cikin birni tunda ance nan birni ne komai me kyau akeyi,Ana taba Yadi kala biyu dubu goma haka ya Cake kudin suka siya,harda siyawa Malam shadda light blue yar dubu tara,layin takalma suka je Na'im ya zabi kala biyu zalla zalla nasa dubu Bakwai bakwai,Salma kala biyu flat masu kyau 2k ko wanne harda na rubber na yawo a Cikin gida da kuma kofar gida,Sarka da dan kunne Silver ya siya mata masu kyau,harda Bangles,a wajen suka ce a ina ake dinki me kyau?Ai ko aka nuna musu shagon dinki dan gaske kusa da wajen,Suka shiga atampopin Salma guda uku harda zabar style aka gwadata tare da daukan size nata,nan take Na'im ya Cake kudin dinki. Umma sukace a kai mata tayi kalar na kauyen,Jikin wajen kuma wajen Maza ne na dinki,Na'im ya shiga ya kai nasa aka gwadashi yace wanda yake tashe ake yayi yanzu banda kato dai dai shi za ayi nan ma ya biya kudi cas aka ce Next wk su dawo su karba.

Kudin da suka kashewa Malam yau sun kusa dubu dari ko basu kai ba kadan ne,kuma amfanin nomansa ne na masara jiya ya siyar da ita tsautsayi yasa ya bawa Na'im wai ya ajiye a wajensa jibi zai karba to sun kashe kudin tas domin har abinci suka ci a resturant me tsadar gaske da 5k kadai suka dauko hanyar kauyensu.

suna Tafiya dare ya fara Motar ta samu matsala ya gangare gefen hanya kuma har sun kusa karasawa kauyen nasu ma abin haushin,Su basu san me zasu taba jiki ba,Salma tace dan bude murfin motar ka kare min Sabo da mutane zanyi fitsari, hakan ya mata ta tsula fitsarinta ya mika mata ruwa pure water tayi tsarki tace to yanzu ya za muyi ga sanyi wlh kuma dare yayi gashi da dan nisa tsakaninmu da kauyen.Na'im ya dan tura motar da kyar suka shiga can cikin wata hanya da ta nufi daji.
Su dai basu san wani tsoron dare ba,Na'im yace a nan zamu kwana kawai da Safe muje gida,Salma ta fara rawar Sanyi ta tsuguna tare da jingina jikin motar,kusa da ita ya dawo shima yayi yanda tayi,nan kowa ya fara jin shaukin dan uwansa sai tunane tunane sukeyi,kowa nason yaji jikin dan uwansa a jikinsa,Na'im ya matso kadan,itama ta kara matsowa,ya kara matsowa sadaf,itama haka har saida kafadarsu tana gugan juna,Salma ana dan rawar Sanyi shi kuwa karkarin sha'awa yake,hannu ya dan sadado itama ta miko masa da Sauri suka rike kam dama jiran kadan sukeyi.
Sai wasa da hannun juna suke kowa yayi shuru yana sake sake,can Salma ta jiyo zatayi magana shima tunaninsu yazo daya ya juyo,lips nasu saitin juna,a hankali suka dinga matsawa da fuskarsu lips dinsu yana gogan na juna suka hadeshi wuri daya suka fara tsotsar lips din juna da Zafi zafi, tuni Salma ta Fara Mutsu mutsu tare da zame hannunta ta daura su saman wuyan Na'im tare da sakalosu ta shige jikinsa tsam ta rungumeshi kam,shima hannayensa yasa tare da kara manneta a jikinsa,suna tayi ba ji ba gani,da kyar Salma ta tuna da fadan Malam Magaji ta zame jikinta,Na'im ya kasa magana domin ya kai kololuwa da kyar ya lashi lips nasa na kasa yana cije shi, yace Need more pls,Salma ta make kafada ka bari dai ayi mana aure kaji,Na'im ya mike muje gida a kafa mu fada masa wlh,sai yanzu aka tuno da auren? Salma ta furta,tsaki yaja kizo muje mana Ayi mana auren,Salma tayi dariya tace kalli nisa fa kafin muje Dodo ya kamamu,jin tace Dodo ya Tsorata domin Na'im mugun tsoron Dodo yake yace ni kin bani tsoro Allah,mu gudu cikin mota mu kulle sai muyi bacci ciki.
Bayan motar suka fada da gudu a tsorace nan suka danna lock ai sun tsira mota na cikin duhu kamar daki suke,Salma ta kwanta,yace to ni fa a ina zan kwanta kuma? Tace ga Dodo nan ta Window da Sauri ya fado kanta da kyar tana nishi tasa ya dagata tace to kai kwanta tun kafin Dodo yazo ba ruwana,ta dan mike a motar ya kwanta ya mike sosai kafafunsa ma sai kasa ya sauke tsayinsa motar tayi masa kadan,Salma tana tsugune kasan motar sai nishin wahala take,Na'im yace baza ki zauna ba sai wani abu ya cijeki a kasan motar ko kunama,da Sauri ta mike har tana bigewa tunda baki da nauyi to kwanta a samana,Salma tace tab naki,taki kwanciya har yayi baccin karya tunaninta bacci yayi tsoro ya kamata tace kai tashi mana banyi bacci ba zakayi tsoro nakeji fa,ya bude ido ta fara gyangyadi gefen kafarsa,ya bigeta da kafar tashi só kike Dodo yazo,ta bude ido da kyar bacci takeji sosai bata kulashi ba idonta rufe cikin mayenta na bacci tace muyi baccinmu tayi kwanciyarta a samansa tayi balance harda gyara kwanciya ma abinta,abinda Na'im ke jira dama kenan,sai ya rungumeta bacci ya tafi dasu me dadin gaske, jefi jefi mutane suna wucewa amma ganin mota suke tunanin ko mugayen mutanene kowa da gudu yake karasawa cikin kauyen ba wanda yayi tunanin zuwa jikin motar ko a tambaya lfy?

da asuba da wuri suka farka har gari ya danyi shaaaa,Salma taki

1 Comments On KAMARSU CE DAYA
avatar
abdulkadir-lawan-yusuf

9 months ago

Reply

Littafi me ma'ana

Please Login or Register in order to submit comment