Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta basu hakuri suka dainawa,Na'im shi dariya ce ma ta kamashi harda za a take masa wuya,yace sorry to ki daina zuwa wajensu jeki kiyi bacci,Salma ta saka kuka tace ni..Wlh sai ka bimin hakkina wlh bazan yarda ba bazan yafe ba,dama baka so na a zagi Uwata kace na tafi nayi bacci ni dama nasan baka so na,Na'im yace muje to dan Ubansu ya sa Salma a gaba har part din tasa kafa ita me miji ta harbo kofar baram,saida matan suka firgita,ta rike kugu,tace Honey gasu nan kuma shaye shaye sukeyi kalli kwalabe da kwayoyi wasu suna bedroom suna lez,anan ran Na'im ya baci sosai,suna zaune lfy ana so aure yayi albarka Ashe ana nan ana aikata masha'a salon auren ya lalace da wuri,

Aisha ta fara rantse rantse ba ita a ciki,yace wlh duk kuzo Ku tafi gidan ubanku,ke Aisha nasan na gama dake baki isa ki nemi wata ba yanzu sai dai ko nan gaba wuce muje ciki kuma saina hukuntaki,Nan take mata jikinsu ya dau rawa suka fara suturta jikinsu,Na'im ya kira security yace a fitar masa da wannan matan da suke part din nan kar a bar ko daya ta zauna,duk wace ta kawo musu raini suyi mata dukan tsiya su watsata waje,Nan kuwa Securities suka musu fata fata suka kori ko wacce a kofar gidan ma ba abar ko daya ta tsaya ba,Na'im yasa aka gyara part din tas ya kada kan Aisha har part dinsa saida tasha mari yafi Uku ranar sannan yace ta koma cikin su Zainura ayi komai da ita,part guda Mummy ta basu su zauna ciki kowacce ta sakata ta Wala,Aisha bata da kawa ranar ko daya,

Zainura ta dinga dariya tace Aisha me na fada miki wlh nafi Salma hankali nafi Salma rufin asiri,kinga ni da kuka min da kaina na dauki mataki kuma ban fadawa kowa ba,amma Salma ita gashi nan Mijinta ta fadawa na fada miki ki kiyayi Salma yar fari ce mijinta komai tayi ko akayi mata sai ta fada masa,baza ta fadawa kowa ba amma shi sai ya sani,Salma ta kece da dariya tace to ya iya bani dadi ne kun San gwarzo ne,na matsu wlh a kaini sabon gida sabon Bed mu hole,Zainura tayi dariya tace Wai da farko da Zafi ne?Aisha tace ke wlh ance da zafi bare ke da kike yarinya kuma Ya Irfan tab,Zainura tace ke manya na magana kina sa mana baki,kanwar mijina ai kanwata ce,me kika sani da zaki fada min bayan ke macece ta kwakwuleki da hannu,Aisha tace wlh Zainura zan fadawa Irfan Allah idan kina min haka,Zainura tace kinyi a banza mijin tace ne to ni zai bi bayana,Salma tace ai ta tuba ko?Aisha tace ae mana,Zainura tace to tunda kin tuba na daina tsokanarki amma ana kara kamaki ba ruwana Allah,Salma tace Zainura ba Zafi duk Wanda yace miki da zafi yayi karya,Dadi ake ji sosai Allah,da kanki zaki ce a kara miki,Zainura harda tafi da tsalle ta fada saman katifa ta dinga burburwa wai zata ji dadi,Aisha tace kinga Zainura wlh ba haka bane,Salma ta dan bigi Aisha,Aisha ma tace Salma ai ban so kika fada mata akwai dadi ba,so nake ta dauka akwai zafi taki yarda,mu kuwa muji dadinmu,Zainura tace muguwa yar bakin ciki Allah ya toni asirinki kuma watarana sai na fadawa Irfan gadar zaren da kika shirya min.

Salma tace ai ki saki jiki ki nuna masa love zaki ji dadi,Zainura ta rungume pillow tare da cewa wayyo Gardi da dandano,wayyo Irfan ni ayi a kaini,Jamila tace Wai Amare wanne kuskus kuke ne? Salma ta kafta musu Ido tace irin dadin da ake ji daren farko mana muke fada mata,Zainab tayi dariya a boye Rahina ma haka tana jijjiga yaronta tace matan aure ai suna sheka karyar zafi,Salma na zata Zafi akeji da gaske Ashe masifar dadi ne a ciki,sauran ma suka ce muma munji labari daga baya Ashe dadi ne,Zainura tace Amma Aishalle kwai yar kutmar....ta dinga mana kuka da safe da mukaje wai da zafi,Rahina tace Ashe karya take ai ta fada min rannan wai maganin da idonku tayi,Zainura ta fado kasa daga saman bed tace to muma Iskanci is somewhere around the corner wlh naga yar iskan da zata min karya nan gaba,oh na ciki baiga gari ba.






Page din nan ya min dadi wlh.


Ayi afwa da typing error pls.


AsmaBaffa
[1/14, 5:14 PM] Sis Asma: 🏉KAMARSU CE DAYA🏉







191-195 196-200







Official







By
AsmaBaffa








Wannan page nakine MARCYCOOL







ZAINAB ATIKU SALAMA,SAMEERAN GAYA,HAFSAT KHAIRAN and ASYCOOL godiya me tarin yawa kuna bada gudun muwa.

Gaisuwarki daban ce QUEENMERMU.








Zainura su Salma sai zugata sukeyi,ta daina Jin tsoron first night dama sabo da haka ma take Jin tsoron auren gaba daya shi yasa jikinta yayi Sanyi amma yanzu ba matsala,
Suna zuba hira Umma tazo tare da yan uwan Zainura suka fesa mata turaren Kamu ana guda,haka suka yiwa ma Aisha,Salma tace sai an kara yi mata itama da yake Umma ce sai ta fesa mata itama kamar Amarya,ana gamawa kowacce ta nemi wajen bacci,

Na'im ya kira Salma a waya,Aisha tace dan Allah Salma ki canja daki wannan wayar taki ta kaddara kullum sai kin kusa kwana,Zainura tace kuma fa Zancen Iskanci sukeyi a wayar in kin San haka ne ki koma wajensa mana ayi me gaba daya,kanku akeji cewar Salma,ta gyara kwanciya tare da daga wayar Na'im,can kasa take magana ba ka jin me take cewa,Hlo My Husband kamar kasan am just thinking abt u,really? Ya tambaya,of course 100% sured,can't do without u Dearna,Zainura ta tabe baki,Salma tace oya gist me Baby kaga na kasa bacci,bana iya bacci ba tare da ina Saman kirjinka ba,Aisha ta toshe kunne da hannayenta,Na'im yayi wani murmushin dadi har ana jiyo sautinsa sabo da kaunar Salma dake ransa sannan yace ba wani nan ba haka bane,da hakane me yasa zaki gujeni,kwana nawa ko ganinki banayi,cike da shagwaba Salma tace to ai ka kusa ganina kullum ma,kwana nawa dan Allah? Am doing ths for our own benefit Baby,u sure?yeah,am missing my lollypop,uhm na sani ai zan baka abinka sai yanda kaso nan da Sunday, shagwaba ya fara sauke mata shi ya gaji da jira tazo yanzu,biye masa ta dinga yi da kyar ta lallabashi ya hakura,Sun dauki lokaci me tsaho suna waya sannan sukayi Sallama.

Aisha kuwa Doctor Aliyu ne yake ta faman kiranta taki dagawa, har ta gaji ta mikawa Salma cewar daga kice nayi bacci pls zai damu mutum da naci, Salma kamar gaske ta daga Hello Doctor Aliyu gata nan kusa dani bari na bata ungo Aisha karbi Aliyu Hydar ne,Aisha ba yanda zata tayi tace baza ta dauka amma Salma anyi shu'uma.
Aisha ta karba ta dole tare da cewa hello tana turo baki,yana magana tana shareshi har dai ta dan sake kadan sukayi hira sama sama,Zainura kuwa tuni tayi bacci ta baje angonta Irfan ya kira shuru ta sa wayar a silent,Aisha ta daga tare da cewa hello ya Irfan,dalla bata wayarta,tayi bacci fa,tashe ta ki bata haka magana zamuyi,Aisha ta tashi Zainura ta mika mata waya,cikin magagin bacci ta fara magana Ango ne? Irfan yayi murmushi yace Amaryace,ke Amarya ya bakya kuka ne?ya kamata kiyi kuka,irfan yace akan me zanyi kuka ina son mijina,Zainura bacci ya kara tafiya da ita suuuuu ta farfado again hello waye wai? Irfan yace Amarya ce,nice Amarya zaka ce kaine ai na ganeka,tashi muyi magana pls,bacci a bari sai shekaran jiya sai ayi maganar,magagin bacci kikeyi da girmanki? Tace ae tun jiya ma inayi,jin Sam baya fahimtar me take nufi ya kashe wayarsa taci gaba da baccinta.
Rahina fa itama ta kara gogewa sabo da Zama da sukeyi a kano,ita da Abubakar dinta kamar bashi ba yana wajen su Na'im ana Harka dashi manager company kuma ya koma BUK zai karasa Degree nasa.

Washe gari Friday ranar daurin aure,ranar Sarkin Lebanon kanin Baban su Na'im ya sauka a Nigeria za a daura aure dashi,Su Na'im duk suna wajensa,an gabatar masa da matayensu dangin Mummy da kowa da kowa,yayi kyauta sosai ranar irin ta sarakai ta alfarma,har jinjinawa Malam da Umma yayi yanda suka rike musu Na'im har suka yi masa aure ba tare da matsalar komai ba yayi musu godiya tare da kyautar mota dalleliya me tsada ya bawa Malam, angwaye da Amare da sauran yan biki anci wanka,tsayawa fadar tsaruwa da haduwarsu bata lokaci ne,karfe 11am Central mosque Abuja aka daura auren Irfan da Zainura,Hunaif da Afra,Aliyu da Aisha,Sadaki Dubu Dari biyu ko wacce,Na'im ne ya biyawa ko wanne ango Sadaki.
Daga can Mazan suka wuce walima a wani tsararren waje,matan kuma Mummy ta shirya musu nasu a gidan anci ansha,sannan angwaye suka dawo aka dinga zuba pics an gama komai Sarki ya hau jirgi da wasu daga cikin fadawansa suka koma kasarsu,yana cewa da fatan nan gaba Su Na'im zasu kai masa Amare har kasarsu suga dangi kaf.
Ana gama komai tun 2pm Dj ya fara tashi a gidan nan,Kawayen Aisha wasu duk sun dawo da yawan gaske za asha rawa dasu,yan mata na gaske sunsha wanka na kece raini,suma na Zainura yan schl sun dau nasu,haka Su Jamila sun saje da yan Birni sabo da har kwalliya yi musu akayi komai na yan gayu baza kace daga kauye suka zo ba,cikin abokan Ango Barira tayi saurayi dan Kaduna,Zainab ma wani dan Adamawa ya makale mata,haka dukkan sauran ma sai da suka samu saurayi cikin samari a wasu state din suke,Zahrau ce kawai wani dan 40yrs yake sonta Dan cikin Katsina city ne me kudi da matarsa daya,Zahrau tace ai da irin su Sadisu ko Dan Isiya me Rake gwara me mata hadadde wlh aureshi zanyi ko a jikina.

Suna hutawa suka fito wajen kida gaba daya ba kidan hausa ciki kidan wakokin arna yan kudu ake sawa su Wizkid,Timaya,lilkesh,kiss daniel,Kawayen Aisha ne ciki suke ta bari da kudi suna taka rawar Shaku Shaku da wasu kalolin,Mazan abokan Angwaye suna wajen suma dasu akeyi suna liki,Zainab taje wajen Hunaif yana gefe yana waya tace yaje yace a sa musu na hausa su,Yace dole kuyi mana wannan rawar mu Sha kallo,Zainab ta dinga dariya tace Allah baza mu iya ba mu dai,Sabo da son kai Hunaif yace to ta Larabawa za asawa su Afrah suyi,aka sa musu Wakar Arab ta bellydance duk suka shiga danginsu jar fata suka dinga yi ba ji ba gani,Har Hunaif sai da yayi ta Larabawa,su Na'im suna ta dariya,Irfan Zainura tace yaje yayi shima ta masa liki ta garinsu,ya shiga aka basu fili kidan Arab na tashi amma da zai fara sai ya fara dariya ya fasa,Zainura kuwa tace in baka yi bani waje ta daga hannu sama yanda taga sunayi ba mistake kun San dama ta iya gwada komai na mutum idan yayi sai ta gwada,Zainura ta dinga yi kuwa aka dinga dariya da Ihu harda haukarta ma yi take wai ita balarabiya,ai kuwa Dukkan fararen da su Na'im suka dinga mata liki kamar me ana tafa mata,Na'im yace Salma taje itama ta gwada,Salma ta makale kafada tana dariya ni wlh bazan iya ba,na iya rawa dai amma banda ta Arab,Na'im yace to a koma kidan Nja songs Salma ta shige idan baku manta ba Salma gwana ce,sai da ta bawa kowa mamaki har bangaren su frnds na Aisha,haka su Mummy da Umma da sauran mutane suma sunyi liki,Ita kuma illar Salma idan ta fara rawa to bata san ta tsaya ba,Na'im yaga ana kalle masa abubuwa yace tazo su fita taki yarda,sai ya jawota ta makale,taki fitowa cashewa take abinta,kizo mu fita haka cewar Na'im,ni fa ban gaji ba,daya gaji sunkuyawa yayi sama da ita ya daukota kamar jaririya yayi waje da ita,Taji an canja kida ta kwace hannunta zata koma ciki Na'im yace zan bata miki Salma na gaji haka daga cewa kiyi kadan kina gani Maza sai kalle min abu sukeyi,me yasa bakya min ni na gani? Kace nayi maka ne? To shike nan zaki dinga min amma karki karayi anan.
Hunaif kuwa ba ruwansa cashewa yakeyi kamar ba gobe,Irfan kuwa ko ya shiga baya iyawa,Na'im yace Saura frnds din Zainura sun Zama yan kallo za ayi basu,yace Dj suma ya sa musu wacce suke so,
Aka samo masu shegen kida na Hausa na zamani,nan fa kallo ya koma wajensu suka dinga jijjiga hips a wajen nan suna bada show,kowa tunaninsa kalar na kauye zasuyi kuma kamar wanda sukayi training iri daya sukeyi,ko wanne kida aka sa to akwai rawar da sukeyi kuma duk iri daya sun iya har Zainura,Salma ta kwace zata fada ciki ayi da ita Na'im ya jawo rigarta kamar me Aljanu suka dinga kokawa wai sai shiga, Allah yasa Umma ta gani tazo tace ke baki da hankali ne?mene haka karki sake na ganki ciki duk mazan nan,Salma sai lokacin ta hakura wai ita an takura mata kowa da masu auren suna ta rawa amma ita an tsaneta an hanata,duk ga masu aure nan sai ita za a hana,tayi fushi tare da Zuciya ta bar wajen ma ta koma can bayan wani part building ta Zauna ta fara kuka.
Na'im ya dauka ta hakura ma tafiya tayi kawai zata huta bai San tana can tana kukanta ba,Irfan kuwa Kujera aka ajiye masa a tsakiyar fili ya zauna daram da kudinsa na liki Zainura ta shugo kamar shedaniya haka ta zage ta dinga casa Rawa yanda taga dama,yana mata liki,ana ta cin dariya ana ihu da tafi,ta tafi da Imanin kowa,Idan taga dama har mazaunanta zata juyawa Irfan baya ta murguda Masa Shi kanshi watarana kasa likin yakeyi sabo da dariya kamar ba itace Amaryar ba tayi rashin kunya yanda take so,Manya da yan mata Tare da Samari Zainura ta taka rawar birgewa tasha liki, Irfan ta mikawa Hannu ya Mike kuwa kamar wani abu sai aka ga ya cire hular da ya sa ya sawa Zainura ita ita kuma ta sa masa gogoronta,Na'im Ido ya rumtse sabo da rashin kunyar da su Irfan suke a filin nan yayi yawa,Hunaif kuma ya shigo da Afrah suka fara rawar turawa su biyu da slow music,
Doctor Aliyu shi gentle ne aikinsa liki kawai yake kowa,har Aisha in ta shiga zaije yayi mata liki ya gaji ya fita.

Hunaif yace to duk su Jamila kawayen Zainura su shigo ya shiga tsakiyarsu suka dinga cashewa dashi ana ta liki a nan shi kanshi Na'im yaje ya musu liki sosai,suka ce Irfan ma ya shigo shi tsayawa kawai yayi sukayi sosai suka Sha liki,gaskiya yau sun cashe kamar baza a mutu ba,anyi watsi da kudi,babu kamar Amarya Zainura a wajen nan yanda dama tace ta rantse idan bikinta yazo sai ta ajiye tarihi,ba wanda ya isa ace ta tsaya kawai sai ta cashe ta bar tarihi,aiko yau kowa ya sheda Zainura tana kaunar Irfan din nan nata.

Na'im ya nemi Salma ya rasa,ya kirata a waya taki dagawa ya duba ko ina bai ganta ba,har aka gama kidan wurin 9pm aka watse sai kuma gobe dinner.

Har 10pm ta wuce Salma tana can inda ta zauna a waje bayan Building wai a nan ma zata kwana tayi fushi,duk wanda Na'im ya tambaya sai yace Bai ga Salma ba,shi kuma yunwa yake ji ma so yake tazo ta bashi abinci,ya shiga nemanta,ba ita ba labarinta,hankalinsa yayi matukar tashi ya koma Compound yabi ta inda yaga tabi dazu har bayan Building din yabi wurin garden ya hangota Zaune ta kudundune a Zaune,da sauri ya karasa wajenta yana tambayarta lfy? tace ba komai tayi shuru,taso mu tafi me kikeyi a nan? Salma tace ni bazan je ba anan zan kwana,Me ya faru ne? Salma tace ka fini sani ai tana Hawaye,sai lokacin ya tuna me ya faru ma ya hanata shiga rawa shine tayi fushi,tsugunawa yayi tare da cewa oops na tuna kuma akan wannan kike fushi?ai dole nayi kowa gasu nan sunayi kuma da aurensu amma ni sabo da bani da gata bani da iyaye shine za a nuna min banbanci a hanani yi,to bazan kwana a gidan ba,dariya Abin ya bawa Na'im,Salma gani take kamar wani ne ya hana Danginta su kulata,sai tayi ta zargin cewar dan bata da gata shine ba a damu da ita ba,dama haka dan Adam yake ko mutum talaka ne aana yi masa abu zai ce dan anga mu talakawa ne bamu dashi,idan rashin lfy ne ma haka,idan rashin yan Uwa ne sai ace Allah sarki to bamu da gata,ba Uzuri Allah kyauta,komai ace dan kaza ne zargi kawai da hasashe.

Na'im ya kalleta kawai yasan to Dan Adam musamman ma mace me rauni,sai ya share tare da cewa eyya so Sorry ban san zakiyi fushi ba,bazan kara ba,yana tsugunne ya juya mata baya tare da cewa hau na goyaki mu tafi amma sai dai mu bi ta dayan part din sabo da main akwai mutane,ba kunya ta hau bayan tana mita ita dama bata da yanci har suka karasa part dinsa ba tare da kowa ya gansu ba.
Yunwa Honey baki bani abinci ba tun rana,bata ce komai ba ta Mike ta fita ta kawo masa wanda dama ta dafa masa da yamma,tashi tayi zata bar dakin muryarsa taji yana magana da alama ransa ya baci ki dawo bazan iya bacci ni daya bafa,Salma tace jibi fa za a kawo ni,dariya ma ta bawa Na'im kamar wata Amarya sabo da kuruciya wai sai an kawota,bai ce komai ba yace jeki to sai jibin,ba tunanin komai tace good night ta tafi abinta,kawai murmushi yayi domin kuruciyar Salma har mamaki take bashi.

Bedroom din Amare ta koma itama Salma,Zainab tace kai Jama'a Zainura ta fesa rashin kunya a wajen nan,Zahrau tace kamar ba itace Amaryarba yau Ango yasha kallom kugu,Zainura da fitowarta daga wanka kenan tace ai dama tun a kauye na Rantse da bikina sai na taka na girgije bazanyi kaffara ba ehe.
Aisha tana dariya tace zaki fadawa mutan garinku wlh mijinki Baida hakuri,Salma tace ai Zainura duk ranar da taji dadin Amarci Haukacewa zatayi,Zainura tace tun a first night dole mu murji duniya,suka dinga dariya Zainura zata fada nan gaba,Z ainura kuwa dadi take ji tace kai yau na cashe ban taba Sanin cewar haka nake ba sai yau e..e...e...e ta kara yin girgiza a gaban mirror tana kida da bakinta.
Kiran Irfan ne ya shigo wayarta ta sai da ta kusa tsinkewa wai ita Jan aji,hello! My life ya gajiya? Alhmdllh tana wani kashe murya,me kikeyi yanzu wanka nayi ma yanzu mai nake shafawa,Irfan ya gyara kwanciya tare da cewa mene a jikinki?Zainura ta kara kasa da murya,towel ne dan guntu,Irfan yaji yawunsa ya tsinke ya fara kissima Surar Zainuransa yanda zai more jibi,Allah ya kaimu Sunday Sweety,Zainura tayi shuru kawai tace uhm Ameen.

Washe gari Wedding dinner, ansha wanka anci kyau karfe 8:30 na dare suka fara dinner anci ansha anyi rawa Naira tayi Kuka 1am suka dawo gida,washe gari dukkan bakin nesa suka tafi gida har larabawa da sauran baki,frnds din Zainura ne kadai su Jamila suka rage basu tafi ba sai an kai Amarya da kwana biyu zasu tafi,an gyara gida kamar ba ayi wani biki ba normal.
5pm aka fara kai Salma part dinta kamar Amarya itama ansha addua,sannan aka dauki Aisha Aka kaita Maitama dankareren gidan Doctor Aliyu,sai kawayenta mutum biyu sai dangin Doctor aka barta dasu tana ta kuka,
Zainura tana daki ta dau wanka cikin wani material na India riga da skert,rigar me zare a baya kamar Amaryar India ta yafa mayafi,sai da tayi Nafeela da adduoi na zaman lfy,an sata a gaba ana ta yi mata nasiha harda kukan karya wai dan kar ace batayi ba,ta leka ta window sai kuwa ta hango motocin daukanta sun jere,Zainura da kukan karya ta juyo tare da cewa shike nan motocin sunzo ta fashe da kuka kamar gaske,ana ta lallashinta ai ya mace dama ta gaji haka,Zainura tace ni bazan iya ba a samu mutum a bawa namiji a kaika wajensa ba Uwa ba uba ba dangi ta kara sakin kukan karya,Mummy tace ke tashi mu tafi sai jiranki akeyi da kyar aka fito da Zainura wai baza ta je ba ta fasa auren,Haka tana ta sheshekar karya ta shiga mota daga ita Sai su Jamila a motar ai ko tana Zama ta sheke da dariya ta cikin mayafi tare da cewa dan uwarku ba kuka nake ba heeeee suka dinga shewa amma Zainura ke dai yar Iska ce,Zainura tace tab ina son mijina kukan me zanyi,Driver yana jin su sai dariya yakeyi,sai da suka je kofar gidan kowa mamakin tsantsaruwar gidan yake kamar baza a mutu ba,Jamila da sauran mutane kowa ya gigice da ganin gidan ko daga America kazo sai gidan ya tafi dakai sabo da haduwa.

Zainura data fito fuska a lullube kamar kuka takeyi haka tayi addua da sauran masu kawo Amarya manya da yan mata suka kaita har part dinta,Wai duniya a nan take ya tsaru,haka aka bar Zainura ita da frnds na schl dasu Jamila aka dauko Ma ta Hunaif Afra aka kaita nata part din duk gida daya amma wani ma bazai San Da wani ba yanda aka tsara ginin sai ka hau mota ko kayi tafiya me matukar nisa sannan ka isa part din daya haka sukayi duniya sabuwa.
Ba nisa kuma tsakaninsu da gidan Mummynsu abinsu daga gidan kana hango gidan Mummy.

Na'im yafi kowa Zumudi yau ana kai Salma dama an gama kawo komai nasu gidan har motocinsu kawai driver yasa ya kawoshi wajen Salmansa yau akwai budiri,Hunaif Matarsa ba kowa a wajenta shima yana yin Sallar Isha ya fesa uban wanka Driver kadai ya kawoshi shima ya wuce part dinsa direct.
Irfan angon Zainura har rafkannuwa yayi a sallar Isha sai da ya sake sallar Isha sau biyu bata dai daita sabo da zumudi,ya cancare amma wai ya bugawa Na'im waya yazo shi da Hunaif su rakashi wajen Amarya ayi addua da nasiha,Na'im ya hayayyako masa da masifa kamar zai cinyeshi kama raina mana hankali Irfan,mu ance ma bamu da mata,ka bushe a waje karka je wajen Amaryarka kit ya datse waya.

Irfan ya kira Mummy cewar fa sunce baza su je ba,Mummy ta kira Na'im ta dinga fada wai Zumuncin kenan to kowa sai an rakashi wajen matarsa a kira Hunaif,Nan ma ta kira Hunaif tace a fara Raka Na'im sai Irfan sai Hunaif.
Na'im yana fitowa yace ya kalli Irfan da ya dau wanka haka Hunaif ma yace yan Kutmar uba sai ku muje ai yan Iska kawai matan naku baza ku iya zuwa ba sai anyi wani zumunci munafukai,ya dinga masifa suna dariya,Suna zuwa Salma ita ba Amarya ba suka gaisa Na'im yace sai ku tashi mu tafi ai me kuma za kuyi,Hunaif yace ai ba muyi addua ba,kayi a sallah dan Allah ni sauri nake ina da aikin yi,kafin su Mike har ya bude part din sa yana jiransu,suka fito kuwa akaje wajen Irfan a mota,Irfan duk ya rude yace nima na gode kuje ka Raka Hunaif naje watarana,Na'im ya masa wani kallo ba shiri ya Mike suka Raka Hunaif,ganin Afrah ba bahaushiya bace sun tsaya sun mata nasiha sosai da addua sannan suka fito Hunaif ko kofa bai rako su ba,Na'im ya figi mota ya sauke Irfan sannan ya figi motar a 80 sai gidansa.

Salma tana gefen Bed a zaune tana jiran mijinta,ya shigo bai bata lokaci ba ya kashe komai na wuta ya shige bedroom,leda ya jawo kaji da Hanta me ruwa sai yogourt da sauran tarkace a ciki,tsokanarta yayi Amarya,dariya tayi tare da rufe ido,yana tsokanarta yana bata naman shima yana ci

1 Comments On KAMARSU CE DAYA
avatar
abdulkadir-lawan-yusuf

9 months ago

Reply

Littafi me ma'ana

Please Login or Register in order to submit comment