Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abin tashin hankali bane yanayin aikin ne haka basai na bata bakina ba ga oga nan ai shi yasan komai daddy ya yi murmushi ya ce ,toh zaid muna godiya sosai da wannan hidima gaskiya bamu da cikakkun kalmomi da zamuyi amfani wajen yi maka godiya sai dai muce Allaah ya saka maka da alkhairi mungode sai da safe Allaah ya kaika gida lafiya zaid ma cikin girmamawa ya ce Aameen dadi nima ina godiya sannan yabar asibitin....

Kasancewar Daddy likita ne ake barinshi yake dan dubani duk bayan awa daya saboda intensive Care ba'a barin kowa ya shiga.....

Karfe daya na dare nafara jin kamar ana yawo da ni a sararin samaniya ,sannan na farajin kamar lafiyar mutum sai kuma wannan hasken wukar da nagani yana walkiya,sai kawai na farka da wani irin firgita ina kiran sunayen Allaah,Dr da yake lura da yanayin numfashi na yaga na'rar da ke june da ni yana basu notification din na farka da gudu suka shigo dakin ganin karkarwa da fizge fizge da nake sukayi saurin rirrikeni sannan suka kira daddy suke sanar mashi cewa na farka amma mutum daya kawai suke bukata ya lura da ni kafin na dawo normal yanzu ina cikin gigin alluran da akayimun general anesthetic.....

Daddy sai da ya sanar da su mummy cewa nan da wasu lokaci zasu samu ganina amma yanzu shi zai zauna awajena.
Da hankali abubuwan da suka faru suka dinga zuwamun cikin kwakwalwata na fara turayosu daya bayan daya sai gashi komai ya dawo sabo a idanuna sai kawai na tsinci kaina da kiran sunan Arrauda shikenan ya kashemun kawata wayyo Allaah na Arrauda kitashi ki gudu kar ya kasheki.hawaye suna ta zuba daga idanuna babu kakkautawa daddy ya rike ni sosai yana tsoron kar na fizge na fado tun ina ganin daddy a nesa can sai gashi na fara ganinshi dishi dish,ganin na bude idon kuma ina ganinshi kamar yau na fara ganinshi ya ce zaratun ki bude idonki sosai nine daddy ki mai kaunarki sannu barka da dawowa cikinmu Allaah abin godiya.

Sai yanzu na Fara gani sosai kuma na gane daddy sai na ce daddy na nan ina ne ina Arrauda da su Mummy?

Ya ce nan asibiti ne baki da lafiya ne su mummy kuma bara na kira maki su duk suna jiran farkawanki ne....cikin jin dadi daddy ya kira su mummy har rige rige shiga dakin suke Humaira ce ta riga kowa shiga dakin da sauri zata fada jikina mummy tayi saurin riketa ta ba cewa yi a hankali kada ki fada jikinta aiko cikin sauri ta zauna a bakin gadon ta kamo hannayena duka biyu bamu ce komai ba sai kukan da muke yi na farin cikin ganin juna.dukkanmu a wannan lokaci muna kukan murnar.sai auntie Maryam ta mike da waya a hannunta ta shiga kiran Khalid da Dr zaid ta sanar musu na farka...
Niko sai tambayarsu nake ina Arrauda daddy ya yi sauri ya ce itama tana dayan dakin ana bata kulawa,sun boyemun mutuwarta saboda kar na shigo damuwa.......





_kuyi hakuri da typing errors saboda yau banyi editing ba_








*please share vote and comment*

⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐


*WACECE NI*




✍🏼by

*Fateema Muhammad Suleiman*
Email [email protected]
Wattad teemacool2020



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is ton entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*page* 4⃣0⃣&4⃣1⃣



*DAILY DAHWA*
[7, ROBIU THANI 1441]

```Allaah is sufficient for us, Truth are the words Allaah ﷻ`

*QURAN*
*If you obey and fear Allah, He will grant you Furqan [(a criterion to judge between right and wrong), or (Makhraj, i.e., a way for you to get out from every difficulty)], and will expiate for you your sins, and forgive you; and Allah is the Owner of the great bounty* (8:29)

*HADITH*
Narrated Abu Umamah (رضي الله عنه) said: I heard Messenger of Allah (صلى الله عليه وسلام) during the sermon of the Farewell Pilgrimage saying, *Be mindful of your duty to Allah; perform your five daily Salat, observe Saum during the month (of Ramadan) , pay the Zakat on your properties and obey your leaders; (if you do so) you will enter the Jannah of your Rubb*
[At-Tirmidhi].

*DUA*
Oh Allah (جل جلاله) *Protect us from known and unknown enemies*

*AAMIIN*


Duk da muryata bata fitowa sosai saboda nadewa da akayi da bandage,amma suna fahimtar duk abin da nake fada.koda da daddy ya nutsar da ni cewa Arrauda tana dayan dakin kawai nayi shiru ne amma bangasta maganar ba saboda da idona naga wannan mutumin ya caka mata wuka,kuma naji magagin fitan ranta.kukan zuci na Dinga yi, sai hawayen da suke zubomun masu dumi,muna cikin hakan sai ga Doctors kusan hudu da jami'an tsaro masu farin kaya,sai da suka kuma duddubani sannan suka shiga yima jami'an tsaron bayanin cewa zuwa nan da kwana uku zansamu damar yin magana sosai amma yanzu kada abarni tayi yawan magana saboda aikin da akayimun a wuya,dan ma Allaah ya taimaka yankewar bai shafi makogorona ba.dan yankewar da nasamu akan fatan wuyanne.


Jami'an tsoron suka matso kusa da daddy suka ce toh yallabai mu zamu tafi sai nan da kwana ukun zamu dawo saboda muna da tambayoyi da muke son zamu mata.
daddy ya gyada kai ya ce toh Allaah yakaimu lokacin.

Bayan tafiyarsu ne daddy ya umarci su mummy su fita suje su kwanta,ganin nima na koma baccin,kasancewar dakin ba mai jinyar da zai kwana tare da marar lafiya sai na 'ura da kuma nurses dinsu ke lura da marar lafiyar.haka suka bar dakin ba dan sun so ba,Humaira kam sai turjewa take wai ita za ta kwana da ni sai da daddy ya tsawata mata ta yarda ta bi su mum dakin da aka tadanar musamman saboda hutu.

Tunda Khalid yaji na farka yake Allaah Allaah y gari yawaye yataho asibitin,shima Dr zaid din haka ya sanar da sauran 'yan uwanshi na gidan cewa na farka kuma normal babu wata matsala,sun nuna murnarsu sosai.

Kashe gari da asubah bayan sun idarda sallah,daddy ya shigo dakin da nake ya iske na farka daga bacci ya yi sauri ya zo kusa da ni ya sunkuyo kanshi sosai ya ce daughter sunnu da jiki, bara na kira maki mum,ya yi sauri ya fito ya kira mum tare suka shigo dakin mum ta matso ta dafa hannayena,sannan ta dan zuba ruwa a saviet ta gogemun fuska.nidai sai ido bakin nawa ma yarufo tun bayan na farka daga bacci, duk maganar da sukeyimun da kai nake bada amsa a haka har ruwan dake hannuna ya kare,tun kafin daddy ya yi magana sai ga nurse ta shigo ta kuma chanjamun wani sabon ruwan sai da ta zuba metronizol da sauran magunguna sannan ta fita,bayan fitanta Mummy ta dinga shafamun gashin kaina dake kwance duk sun bazu ta ce wannan gashin naki kullum a tsefe bakyason kitso na kura mata idanu tsantsar sonta ne fal cikin zuciyata cikin kwana daya amma duk ta fada kamar mai jinya nida kaina nasan cewa tafi sona fiye da sauran 'ya'yanta bansani ba ko dan ita kadai ke gareni.

Karfe takwas dai dai sai ga Dr zaid bai samu wata damuwa ba kai tsaye ya shigo dakin da nake,mummy ce ta amsa mashi sallamarshi,sai da ya gaisheta sannan ya wuce kan gadon da nake ya yimun sannu da jiki ta kai nake amsawa sai yaduba bandaging wayana ya gyaggyarshi.ya juya ga mum ya ce munyi magana da Dr da yayi conducting aikin cewa idan kwana ukun yayi za'a fara bata abubuwa masu ruwa ruwa,da dimi, kafin zuwa lokacin, ko ta bukaci wani abu kada Ku bata.
Mummy ta ce toh zamu kiyaye sannu likita muna godiya sosai.
Sa Ai da takuma dawowa kusada ni yayimun sllama ya tafi.
Nabi bayanshi da kallo saboda bansan ko wayeshi ba sai da mummy take yimushi godiya ne nagane likitane.
Bayan fitanshi da kamar minti goma sai ga Khalid ma yau shigan larabawa yayi saboda juma'a ne,cikin girmamawa ya gaishe da mum ta amsa cikin Fara'a,niko tunda na ganshi hawaye suka fara fitomun babu kakkautawa domin ganinshi ya kuma tunamun da Yusuf Dina,cikin damuwa ya matso kusa da ni sosai sannan ya fara yimun magana a hankali sorry my dear ya isa haka ki daina kuka akwai abin da ke damunki ne na kira likita?

kai na girgiza mashi nuna alamun A'a.

Ya danyi murmushi ya fada kamar rada I love you,wish you quick recovery.Allaah ya tona asirin wannan azzalumi yakuma kara maki lafiya.

Sai da ya zo kusa da mummy ya ce ko akwai abin da kuke bukata ne?

Mummy ta ce Aa babu abin da muke bukata Wanda kakawo jiya ma suna nan Allaah yayi maka albarka mungode sosai da hidimarku.

Ya ce Aameen bara naje wurin daddy.mummy ta ce toh,ka kiramun Humaira,ya ce toh.
Sai bayan ya fita ta matso da kujeran kusa da ni,ta ce akwai abin da kike bukata ne?

Na gyada kaina nuna alamun eeh kafin takaramun wata tambayar sai ga Humaira ta shigo da sauri ta nufo gadon ganin mum da tayi ta bada dukkan hankalinta gareni,ya juya hankalina ga Humaira sannan na nuna alamun ina son takawomun wayata da sauri ta mukamun shi,sai mummy ta ce meye zakiyi da waya keda ba magana zakiyi ba?
Da ido nabita bance komai ba ganin na Fara daddanne wayata sai dukkan su ,suka matsa ajikin gadon.
Inbox dina na bude ganin yawan notification da na gani bisa saman wayar.
Duk kuma sakonnin yusuf ne sukafi yawa,sai kuma na 'yan makarantarmu da suke turomun jimaminsu sunzo dubani amma anhanasu shiga da dai sauransu.

Sakonnin da yusuf ya turomun nabi daya bayan daya.na karshen da na karanta,yana sanar da ni cewa yanzu za'a shiga da ni aiki my soulmate..
To daga wannan sako bai kuma turo wani sako ba,ina kyautata zato shima yana kwance kamar nine.....
Nima sai na shiga rubuta mashi sako kamar haka

_Abin sona,da badan hikimar ubangiji wannan sakon da na turo yanzu wadansune za su turo maka sakon mutuwata.amma Allah cikin ikonsa ya nufeni da rubuta maka da kaina,wani azzalumi ne yayi nufin rabani da duniya, sai dai adadin kwanakin ne basu kare ba. yanzu da nake wannan sakon ina kan gadon asibiti ne yin magana ma anyi restricting dina sai bayan kwana uku.ina yimaka fatan samun waraka daga mahaliccinmu nayi kyawarka sosai da sosai_

Sai da na turo sakon na ajiya wayar kusa da ni sannan na lumshe idona duk abin da nake kuma daga mum har Humaira hankalinsu na Kai na .
Sai ga nurses umarni aka basu akan a canja mun daki tunda yanzu nayi 48 hours a ICU din wani babban daki suka mayar da ni dakin ya tsaru sosai komai na bukata kuma akwai aciki,sai da suka ciremun kayan jikina suka gogemun jikin da towel sannan suka kwantar da ni bisa makeken gadon dake dakin kasan dakin Chinese carpet ne a shimfide,bayan nurses din sun fita sai ga surgeon da Dr zaid sun shigo, wajen da sukayi aikin ne suka duba ina jinsu suna cewa ina da jiki mai kyau kuma yana responding treatment.. Gaskiya naga so da kulawa ta mussamman daga iyayena da kawayena sun nunamun gata,Daddy kam babu abin da zance saboda tun asali son da yake nunamun baya yiwa Humaira ko yusuf su da kansu suka radamun daddy's girl.saboda shakuwaya da daddy din.
beep beep sako yashigomun waya ina dubawa kuwa number yusuf ne da Sauri na bude ga abin da nagani...

_Masoyiyata hakika jikina ya bani cewa akwai abin da ya faru da ke, nayi kuka sosai da na kasa jin muryarki nayi ta sake sake sai dag karshe na fauwala lamrin ga Allaah,bayan na rokeshi da ya tsaremun ke a duk halin da kuka shiga.lallai da na rasaki nima kuwa zan rayune cikin abu biyu imma mutuwar ko kuma rayuwata zata kasance cikin kunci da wahala ni Allaah yaji tausayi ya tsaremun ke nagode mashi bisa wannan taimako ina ji kamar nayi tsuntsu naje na kalleki amma hakan ba abu ne mai samuwa ba.nima kuma anyi conducting operation din,toh yadda Dr suka fada wannan na biyune,bayan wata uku ma za'a kuma yin wani operation din.to gashi anyi na biyu saura daya kenan amma yanzu Alhamdulillah ansamu improvement a aikin..ina maki fatan samun lafiya cikin sauri ina sonki so irin wanda bantaba yiwa wani mahaluki ba rokona dai kullum ki rikemun amanarmu_

Sai da nagama karanta sakon tausayin Yusuf yakamani sosai,sanin da nayi cewa ya kwallafa ranshi sosai akaina kuma ya yarda da ni .......




******************





Wasa wasa yau har kwana na bakwai a kwance a asibiti,cikin wannan kwanakin kuwa jami'an tsoro kuwa sai zirga zurga suke suna jiran umarnin likita ne domin yimun tambayoyi,tun a kwana ukun suke zuwa da Neman magana da ni sai dai Dr zaid ne ya hana ya ce sai ankunce stitch din sannan zasu samu daman magana da ni hakan kuwa akayi yau kam ankunce stitch din wajen ya warke sosai.sai da nayi wanka na shirya sannan jami'an tsoron aka basu umarnin shigowa.

Tambayar farko da suka jefomun shine sunana
Na fada musu sunan
Sannan suka ce toh mrs zaratun ko za ki iya bamu cikekken bayani game da wannan abin da yafaru?

Sai da na dan nisa na ja dogon numfashi,sannan na kwashe duk abin da yafaru da yadda akayi na samu na gudu na buya a gidansu Dr zaid,
Duk abin da nake fada suna rubutawa sai da nagama,sannan suka kara cewa ko za ki iya gane mutumin idan Kika kuma ganinshi?
Na ce kwarai zan ina ganeshi saboda kafin ya farga da ni a dakin na karemashi kallo.
Suka kuma jefomun tambaya toh mrs zaratun yanzu ace muka baki takarda da pencil zaki iya zana mana yanayin mutumin?
Na ce zan iya zana maku shi.....
Sai gashi sun mikamun farar takarda plain sheet da pencil,kowa a dakin yayi shiru an nutsu ana jin tambayoyi da bayanan da nake bayarwa.duk daga kai na da zanyi kuwa,sai munyi ido hudu da zaid din ya kuramun na mujiyarshi.a gefe daya shima khakid ba'a barshi a baya ba,shikam suna tare da daddy da yanzu suka zama kamar da da mahaifinshi.

Na zane mutumin dai dai kamar yadda na ganshi da kayan da yake sanye ranar black suit ne da hukar car boy sanye a kanshi,sai fuskarshi cike yake da kasumba .bayan nagama zanawa namika musu kowannensu sai da ya girgiza kai hasashensu ya fara zama gaskiya.sai da sukayimun godiya sannan sukabar dakin.


_ga wannan kuyi manage yau am kinda busy_













*vote share and comment*


⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐


*WACECE NI*




✍🏼by

*Fateema Muhammad Suleiman*
Email [email protected]
Wattad teemacool2020



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is ton entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*page* 4⃣2⃣&4⃣3⃣



*Dedicated this page to WACECE NI Fans lots of love*



*Today's Beautiful Hadith is about Dajjal*

Narrated Anas bin Malik (RA): The Prophet (peace be upon him) said, "There will be no town which Ad-Dajjal will not enter except Mecca and Medina, and there will be no entrance (road) (of both Mecca and Medina) but the angels will be standing in rows guarding it against him, and then Medina will shake with its inhabitants thrice (i.e. three earthquakes will take place) and Allah will expel all the non-believers and the hypocrites from it."

(Sahih al-Bukhari, Vol. 3, Book 29, Hadith 15)

_What an awesome reminder of how blessed Makkah and Madinah are! Full of serenity, worship and protected from the Dajjal. May Allah allow us all to visit there insha'Allah._





Musamman uncle Anas da uncle Mustapha suka zo daga Nigeria saboda yin dubiya,duk da mummy ta sanar musu cewa jikin nawa akwai sauki har video call take yi musu su ganni amma ran kakata Hajja Bintu bai kwanta ba sai da ta sanya yaranta suka zo dubiya.

Sai Vaishali da Muhammad Ameen da yaran duk sunzo sunyi dubiya,najmi ita ce 'yar Vaishali na biyu tunda sukazo tana tare da Humaira naga kamar jininsu ya hadu da ita,da suka tashi tafiya fafur taki binsu ta ce ita sai ta huta za ta koma haka suka barta duk da Vaishali ta ce ki bari idan ansallamosu kije gida taki saboda muma muna sa ran sallamar cikin kwanakin nan.

Suna zuwa office dinsu zanen da nayi sai da suka gama binciken da ya kamata suyi sannan suka sanyashi cikin system sukayi scanning dinshi sannan sukayi comparing dinshi da asalin hoton mutumin da suke zarginshi shekaru masu yawa amma basu da evidence da zasu kamashi sai gashi yau kuru kuru hoton da na zana da Wanda suke da shi ya zama abu daya mutumin da suke zargine yanzu yazama red handed......sai da suka tabbatar da zarginsu,gaba daya u.s a maganar akeyi antabatar da wanda ake zargi da kashe mutane sama hamsin. nan da nan kuma aka kamashi yana kokarin guduwa yabar kasar kenan.
Ni kuwa tun da FBI din suka fita na koma baccina,sai kusan sallar azahar na farka daga baccin mummy da Humaira naga sun idar da sallah suna kan rug na sallah suna lazimi.
Ganin na farkane Humaira ta yi sauri ta zo kusa dani,ta na tambayata ko da abin da nake bukata?

Kai na gurgiza mata nuna alamun Aa.duk da na fara magana amma jifi jifi naje nake yi saboda dama ni asalina ba mai yawan magana bane.tsawon sati biyu kenan ina asibiti,a wannan kwanakin kuma naga gata daga kowane bangare na friends dina na school,daga colleagues dina na department har da sauran dama bama department daya da su,sai uban gayya Khalid gaskiya shima babu abin da zance akanshi.uwa uba kuma ga Dr zaid da har kunya yake bani idan naga yadda yake azarbabi da nuna kulawa ta musamman,it seem to me,kamar neman shiga yake a wajena kuma kamar yana competition ne da khalid.saboda ko ba'a fada masa yasan akwai wani muhimmin abu tsakani na da khalid.nasha kamashi da wani irin harsh kallo da yake yiwa khalid alamun yana kishi da shi ne,idon yaga na kalleshi saurin dauke idanuwanshi yake daga Khalid din.cikin zuciyata kuwa tana mamakin halin maza,ni ina ta kaina ina naga wata soyayya..

cikin zuciyata kam dukkansu suna da darajar da bazan iya hada su da kowa ba especially Dr zaid kam da jininshi ke gudana ajikina, sai khalid da yadau nawin yimun aikin gyaran wuyan da za su yi kamar dai plastic surgery,saboda tabon da ke wuyana din za su gyara ya koma normal kamar dai yadda jikina yake da,toh gaskiya kudaden suna da yawa,har munfasa yin aikin bamusan wanda ya fada mashi ba sai kawai ya ce ayi aikin shi zai bada kudaden duka.

ranar dagani har su mummy mun rasa bakin yin godiya lallai a al'amarin khalid akwai abin mamaki wannan ta shi wane irin kudi yake da shi ne?kuma duk wani abu da akayimun shine duk ya biya kudadensu da daddy yaje biya ne management na asibitin ya ce khalid ya riga ya biya wancen ma dadi yayi ta mashi fada akan meyesa ya biya sannan yayi mashi godiya.

toh bamu gama yin godiyan wancen ma ba sai ga wani taimakon daga gareshi.gaskiya wadannan guys din bani da abin da zan saka musu dashi, sai dai addu'a.

Yusuf kam babu abin da yake dashi da zai taimakamun fa ce addu'o'in da yake ta yimun,kullum kuma maganarshi kenan abin sona hakika nayi bakin ciki da wannan abu da yasameki gashi bani da abin da zan taimaka maki da shi sai dai addu'a,wannan aikin da za'ayi maki Allaah yasa ayishi cikin nasara.sai dai hankalina ya tashi da kika ce wani ne daban ya dauki nawin wannan makuden kudaden nan.ina tsoron ya kwacemun ke wallahi this time around kam,na karaya sosai.duk lokacin da yusuf ya yi mun irin wannan magana tausayinshi ne ke kara ruruwa acikin zuciyata saboda sanin da nayi cewa yusuf jarumine tsayayye mai tausayi sannan nasanshi sosai rashin babu ne toh babu yadda ya iya shima kuma ya na fama da nashi darurar.nutsar da shi nake da kalamen masu karfafa gwiwa har ya hakura da maganar.saboda nima yanzu na karaya da wannan lamarin.

Idan zanyi maganar so na hakika Wanda zuciyata ta amince da shi ta zauna har karshen rayuwa ne toh yusuf ne,amma kuma Khalid da zaid,kam gaskiya sun Riga sun sace zuciyar mummy da daddy da dukkan makusantana.ni kam dukkansu suna da daraja a wajena amma maganar so kam yusuf dina nake so,saboda ni tun farko ba abin hanun wanda zai sace soyayya ta amma yanzu sai dai nayi musu kawaici.

Sanin da nayi cewa addu'ar Mara lafiya karbebbene toh addu'ar na gukufa da yi Allaah ya zabamun mafi alkhairi.

Tsakanin wannan lokaci kuma nidin na zama abin kwatance a duka ilahirin kasar saboda nayi abin bajinta wajen taimakon zanen wannan azzalumi da ya gagari kasar kusan shekara talatin kenan cases nayi death da aka tabbatar shi ne yayi a record mutane hamsin kuma da kanshi ya amsa cewa shine yayi duka wadannan kisan.
Da aka tambayeshi meyene dalilinshi na yin duk wadannan kisan sannan ana sanyashi ne yakeyi ko kuma wata gaba ne tsakaninshi da wadanda ya kashe?

Amsar da ya bayar ne kowa ya daure mashi kai.
Ya ce ko daya duk Wanda na kashe babu wanda yake sanyani kawai kashe mutum din ya zama,hobby nane.tun daga ranar da na kashe wani da mukayi musayar magana na kasheshi toh sai kisan ya zama addicted a gareni wallahi duk ranar da na sanya raina zanyi kisa toh idan bansamu nayi ba bazan iya yin bacci ba sai na kashe mutum sannan zan samu nayi bacci.saboda haka ne ma na zama mai farautar daukan ranta duk Wanda na kyalla ido akanshi idan har ranar yakasance ina da mode din kashe rai.musamman nake da Master keys dina na yin ammafani da shi lokacin da zanyi kisa.bayan nayi kisan sai na saje da mutane ta yanda ba'a gane ni ba.duk kisan da zanyi sai na tabbatar wanda zan kashe shi kadaine a gidan ko dakin da yake kwana saboda ina tsoron kar a ganeni.

Wannan bayani live ake nunowa a TV kowa yayi mamakin wannan lamari ace mutum yayi ta kashe mutane basu ci ba,basu sha ba.kamar wani kwaro duk tsawon lokacin nan sannan daga bisani aka kamashi ta dalilina wannan abu ya matukar farantawa gomnatin America sosai ko ta ina sunana ne ake ta yadawa mutane kowa sai zuwa sukeyi sukalleni daga.gomna da tawagarshi ma musamman suka zo suka dubani sannan ya jinjinamun namijin kokarin da nayi.abinka da turawa sai kyautukka suke ta kawomun na cewa ta sanadiyata sun samu kwanciyar hankali,saboda kullum suna cikin taraddine da zullumin yaushe za'a kuma yin wata kisa....yanzu kam wannan batu yakau tunda ankama boyeyyen mutumin da yake aikata laifin.gomnatin ta mayar da duk wani expenses da aka kashe zuwa account dina sannan ya kuma daukar nawin yin karatuna daga digree har zuwa gunda naga dama na tsaya a karatu,sannan da wani makeken gida na gani na fada da aka bani saboda wannan abin da nayi...

Farin cikin da muke ciki ba sai na tsaya na kashe ku da surutu ba,kuma kunsan recognition a bainar jama'a abin alfaharine balle abu ya hadu da har presidency sun san da maganar.

'Yan uwa da abokan arziki sai tayani murna suke...Khalid dad yakira ya ce mashi tunda gomnati ta mayar da kudaden da aka bata awajen jinyata toh ya karbi kudinshi.girgiza kai ya yi har idanuwanshi sun kada sunyi jajir sannan ya ce, haba daddy aiko duk dukiyata ne na kashe akan zaratun bazan iya karban wannan kudaden ba ni na batane duniya da lahira wannan da ta samu yanzu arzikintane Allaah ne ya arzurtata,saboda haka kabar zancen wadancen kudin.ni a tsarina bana kyauta kuma na sake karba.

Daddy ya jinjina maganganun Khalid sannan ya sanya mashi albarka sosai,sai gashi sunbar zancen sunkama wata hirarsu.
Shi ma Dr zaid sai da daddy ya sanar da shi cewa ko zai dan karbi wadansu kudade acikin kudaden da gomnati tabayar,shima kamar Khalid fafur yaki amsar ko da sisin kobo ne.shima ya ce matsayina awajenshi yafi kudi..
Toh haka dai daddy da Mummy sukayi ta jujjuya maganar Khalid da Dr zaid,sun kasa sanin yaya zasu bullowa wadannan jaruman samarin..mummy ta ce ni gaba daya kaina ya kulle bisa dukkan alamu shi ma zaid din son zaratun yake Khalid kam nadanji labarinshi a wajen Maryam cewa yana son zaratun din,duk da Maryam din take bani labarin duk da dawainiya da Khalid ke yi mata akwai wani da ita kuma take so,bansani ba ko zaid dinne,tunda mukam bamuga wani ya zo ba tun faruwar wannan al'amarin.

duk abinda suke fada inajinsu nayi lamo

Please Login or Register in order to submit comment