Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

maki ta sameki?bansan haka rabuwa da nasoyi yake sai da na 72 hours ban sanyaki ko jin muryarki ba nasan cewa lallai wani bangare na jikina babu.duk wannan maganar Yana yinsu ne cikin taushi murya duk yabi ya kashemun jikina,naji duk duniya babu wanda ya kaini shiga farin ciki.what a miracles.haka na sauko da fushin da nake da shi sannan na saki raina muka dinga hirarmu cikin nishadi nima nashiga fadamashi irin damuwa da missing dinshi da nayi ,har kusan karfe hudu muna waya sai ga wani Kira na shiga cikin wayanda muke babu tantama khalid ne dama ko yaushe idan karfe hudu tayi Yana tashina daga bacci.ban damu da kiran ba har ta daina shiga shima bai kuma Kira ba dan yasan cikin calling ne wayar ta shigo.sai da aka Kira asalatu sannan mukayi sallama ya katse wayar.
Bayan mun idarda sallar asubah na shiga kiran number Khalid har sau biyu amma bai daga ba abin da baitaba yimun ba kenan kodai yayi fushi ne da yaji number na is in another called....







*share vote and comment*

⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐


*WACECE NI*




✍🏼by

*Fateema Muhammad Suleiman*
Email [email protected]
Wattad teemacool2020



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is ton entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*page* 3⃣7⃣3⃣8⃣



*Today's Inspirational Hadith is about Punishment*

Narrated Ibn Mas`ud (RA): A man said, "O Allah's Messenger (peace be upon him)! Shall we be punished for what we did in the Pre-lslamic Period of ignorance?" The Prophet (peace be upon him) said, "Whoever does good in Islam will not be punished for what he did in the Pre-lslamic Period of ignorance and whoever does evil in Islam will be punished for his former and later (bad deeds).

(Sahih al-Bukhari, Vol. 9, Book 88, Hadith 4)

_Hold yourselves accountable before you are held to account. Know that repentance wipes sins and what you did when you didn't know the truth will insha'Allah be eradicated by what you do once you come to realize it._





~wannan page naku ne wacece ni fans ina ganin comment dinku sosai da sosai~



Yau asabar bamu da lecture,fixed lecture ne kuma ya ce bazaiyi holding ba saboda haka daga ni har Arrauda bamu runsa akan gadon ba itakam chat take yi abunta .

ni kuwa tunda na kira khalid bai daga ba sai na shiga kiran auntie maryam ringing na farko ta daga wayar,ta shiga bani labarin yadda suka karasa da project supervisor ta har yanzu kuma baigama da ita ba,nake tambayarta sai yaushe kenan zai barki baya ganin wahalar da kike sha ne? Ta ce ki bari kawai my angel Allah ma ya taimakeni Ina da wajen yin bakuqnta da expanses din sai ya yimun yawa.
kedai ki tayani add u'a nasamu mugama da shi cikin wannan week.
Na ce in sha Allaah,wish you best of luck.
Ta ce thank sai munyi waya,my regards to Arrauda.
Na ce toh za ta ji.

Laptop dina na kunna na shiga duba comment din da akayi akan sakon da na tura yawanci sunayimun fatan alkhairi ne da addu'ar samun asalin mahaifina a duk inda yake,sai kuma wadansu kuma kamar nidince suma suna neman real biological father su,gaskiya western part of the world ana abu sosai wani abun haushi wani ko tsantsar kafircine ke damunsu.ina cikin duba sakonnin naci karo da wani labari akan wata cleaner da me aiki a wani five star hatel sai taji labarin wani prince da ya kwana a hotel din sai tayi tracing dakin da ya kwana da safe tasamu condom da yayi using cikin wannan dare tayi inserting sperm dinshi zuwa jikinta,sai gashi after one month da tayi test pregnancy test is positive.aiko dama abin da take bukata kenan kawai tayi kararshi kotu akan cewa tana dauke da cikin wannan prince din.

aka nemeshi da yazo court ya yi musu akan cikin ba nashi bane domin shi baima taba ganinta ba,ta fada musu gaskiyar lamarin cewa condom din da ya yi amfani ya jefar ta dauka ta zuba maniyyinshi cikin al aurarta,toh da alkali yabada umarnin yin DNA test hakanne cikinshi ne,aka yanke mashi kusan dollar dubu dari biyar yabita na renon cikinshi.yanzu haka tabar hotel ta Kama business da kudaden.duk da shi ma prince din ya ce zai daukaka kararta akan shima baiyarda da daukar maniyyinshi da tayi ba.toh ga dai iri iren abubuwan da sukeyi.
Gashi nima mahaifiyata ta fada tarkonsu ta aikata abin da yanzu daga ni har ita muke cikin rudani.wannan zamani da kake da nasaba da komai ma idan bakaci sa'aba dangin miji sai su wulakantaka balle kana da abin fada.

duk tunanin ni daya nake abuna Arrauda kam da ta gaji da chatting ta koma baccinta.da hankali na taka matalan godon na sauko kasa da yake Ina kan up bed ne Arrauda kuma take kasa saboda ta ce ita bata iya kwanciya a sama.da yake gadon dakin irin na 'yan makaranta ne.dama unguwar da muke na students ne kuma ginin unguwar da komai anyishine bisa tsarin student.kitchen na nufa lokacin dai dai karfe takwas 'yan mintoci,kwai kawai nasoya sai tea sannan na hada fruit,sai da na gama jerawa a dinning na shiga,bayi nayi wanna na sanya riga da wanda masu kauri lokacin winter ne akwai sanyi sosai,Ina gaban dress mirrow sai ga Arrauda ta fitomun da wayata da na barta na fito daga bedroom,number yusuf ne da ya kirani jiya,saurin dagawa nayi saboda ta kusan ta tsinke.muryarshi a dashe kamar wanda yayi kuka yakemun magana cikin tsorata da jin muryarshi,nima kuma tawa muryar har taba m rawa na ce my soul lafiya naji muryarka haka?

Cikin sanyin murya ya ce nashiga damuwa ne sosai, saboda banason na rasaki ne mu soulmate,yanayin wannan aikin da za'ayimun between do or die ne kinga idan har ba'asamu nasara ba banida hope akanki.yanzu aka gama yimun counseling akan aikin 10% ne chances na warkewarshi.kinga ko dolene na shiga damuwa.

Tun kafin ya karasa maganarshi zuciyata ta karaya na fara yi mashi kuka tsawon lokaci yana jin yadda nake shishshikar kuka, bai hanani ba daga ji shima yana cikin matsanancin tashin hankali.da kaina ta tsayar da kukan da nake yi a take kuma na zama jaruma na danne damuwar da nake ciki saboda na karfafa mushi gwiwa cikin confidence nake maganada cewa my soul stop negative thoughts,in sha Allaah za 'ayi aikin nan cikin nasara ,kada ka cire tsammani daga ni'imar Allaah domin shi mai yawan gafarane mai jinkan bayinshi kuma kullum muna cikin rokonshi samun lafiyarka,sannan kasani cewa ni a haka naganka, kuma na soka ban taba ganinka ka taka kasa ba.asalima wannan yanayin da na ganka acikine sanadin da yasanya na soka,may be akwai wani abu da kayiwa Allaah na alkhairi ne ya kawoni cikin rayuwarka bandamu da kana tafiya ko kishiyar hakan, ba ni Kai dinne nake. so fatana Allaah yabaka lafiya but ka daina sanya kanka cikin damuwa sosai its can lead you to serious depression.sanya a ranka zaratun taka ce itama yusuf nata ne.انت مني انا منا.sai da yaga nayi shiru ya nisa yaja gogon numfashi,ya ce nagode sosai my wife and only soulmate,nagode sosai da karfafamun gwiwa da kikeyi a koda yaushe what a beautiful soul, wallahi you too much.

yadanyi shiru sannan ya ci gaba da cewa let me show my affirmation in sha Allaah ,zan warke,zamutyi aure zan nuna maki endless love dina. auren da zamuyi na zobe ne,for better for worst.ki kularmun da kanki,I love you with all my heart. misalin karfe biyu dai dai za'a shiga da ni aikin.

Na nisa sannan naji dadin kalamenshi sosai nima na ce I love you too wish you successful and quick recovery over the work dai dai lokacin zan karanta suratul yaseen zanyi ta wassali da shi akan Allaah ya sanya ayi aikin a sa'a.

Ya ce Aameen nagode sweetheart.

Na sako murmushi jin yadda ya koyikoyi muryata da zaiyimun sallama.tsawon lokaci ina rike da wayar inaji a raina wannan aikin za'a dace idan anyi.har lokacin Arrauda ta gama wanka ta shirya ta zo kusa da ni ta zauna tare da fadin toh laila majnun ko Romeo and Juliet zance ne irin wannan kalmomin soyayya haka, na rausayar da idanuna sannan na lumshesu na kuma budesu ido cikin ido nake kallon Arrauda sannan nace so kenan ashe shi baisan babbancin yanayi ko kudi ko sarauta kyau ko muni ba a zuciyar masoyar wadannan abubuwa duk basa tasiri,gaskiya ina son wannan guy madly...
Arrauda ta waro ido ta ce gaskiya zamu dage Yusuf dinki ya samu lafiya musha buki ko muma mu samu kunnuwanmu su huta da wannan suna Yusuf Yusuf,Allaah dai yasa shima haka yake sonki saboda maza yanzu basu da tabbas..

Yes but my Yusuf is different da sauran mazan.ta ce Allaah yasa haka,na ce Aameen sannan muka je kan dinning domin yin breakfast......

Tsawon yinin ranar munyishi ne cikin nishadi da hirarrakinmu har group called muka hada da kawayenmu muka sha hira Latifa ma taso tazo mana amma tana da abubuwan yi sosai shine bata samu zuwa ba amma itama ta danyi hira cikin group call din.
Tun bayan trying number khalid da na yi bai dagaba bankuma dawo ta kanshi ba saboda tun farko dama shine ya ce ya ji ya gani.sai ga kiranshi kamar na share amma sai nayi wani tunani na daga muryarshi babu yabo babu fallasa ya ce baby yakike yaya kin mutane?
na dan yatsana fuskata kamar ina gabanshi sannan na ce bangane yaya kin mutane ba ka kirani ina kan waya bansamu na dauka ba, sannan daga baya na yi calling you back kaki ka daga kenan munyi one one to meye na korafi?
Baice komai ba na dan ji shi yana murmushi kasa kasa bai kuma nunamun damuwarshi ba kawai ya basar da tambayar da na mishi ya ce idan zaki iya fitowa ina kofar gidanku maida wukar ina sauri ne sako zan baki.

Na yi mamakin Khalid da sonda yake nunamun kamar bashi da zuciya, kodai akwai wata manufa a wannan soyayyar da yakemun amma muje zuwa zanga iya gudun ruwarshi banso fitowa ba amma sai kawai na ce da Arrauda zan fito wajen Khalid ya na bakin get.

Batayi magana ba kawai ta gyadamun kai saboda ta yi nisa wajen kallon wani film, the reef a MBC 2.

Ina fitowa kufar gidan Khalid ya kuramun ido yana yimun kallon kurilla na je kusa da motor sai ya yi saurin fitowa daga motar muka kuma gaisawa sannan ya danyimun kalmominshi na love wanda nake jinsu kamar a dole ake fadamunsu bana kuma maida mashi duk wata kalma da ya furta na so,saboda gaskiya na gaji da yaudarar kaina tunda ni gaskiya ba sonshi nake ba gwara muyita ta kare tun abun yayi nisa.ya katsemun tunanin da nake kamar yasan zuciyata ya ce kiyi hakuri nasan ba'ason ranki kike saurarata ba amma kuma nagode da kulawar da kike bani.ga wannan ya mikamun vonch na dollars guda daya,naki karba kawai na waro idanu sosai sannan na ce gaskiya bazan karba ba,ka daina yimun irin wannan kyauta gaskiya bansan gunda zan kai wadannan kudaden ba, kaga wannan motor da ka bani bansan yadda zanyi na fada a gida ba ina dai jiran auntie Maryam ne idan ta dawo duk abin da ta ce shi zanyi,idan ta ce na mayar maka ma zan maido ta kasani am here to learn not to came and collect somebody properties,tun kafin na karasa magana ta ya ce
thanks you, ni kike kira da someone ko?
Hakan yana da kyau kiyi duk abinda zakiyi amma bazan daina sonki ba ki daina ganin laifina laifin zuciyata ce da ta fada tarkon wanda baya sonta,ya karasa maganarshi kamar zaiyi kuka.
Sannan ya yacusamun kudin cikin zumbulelen hijabin da na sanya ya ce wannan kuma naki ne,idan kina so kiyi amfani da shi ko ki bayar sadaka amma ni na rigada na cirashi daga dukiyata daga haka bai jira nayi magana ba ya shiga cikin motarshi yarufe niko nayi mutuwar tsaye sai da zai ja ya kama hanya ya zuke glasshin gaban motar ya ce am sorry my habibty ki shiga gida ni na barki lafiya sai da safe.
Bai jira yaji abin da zance ba ya yi saurin baiwa motarshi wuta yabar kofar gidan..

Sai da na kusan minti biyu sannan na shiga cikin gidan.....har kusan karfe tara sai ga kiran auntie Maryam take tambayata lafiyata da gida sannan ta ce in sha Allaah,itama zata dawo gobe idan Allaah ya kaimu.

Na ce Allah ya dawo da ke lafiya.
Ta ce Aameen.
Bayan munyi add u'o'inmu na bacci,muka kulle kofar dakin, nahau kan up bed dina na kwanta Arrauda kuma ta kwanta a kansan bed din kowa yana ta danne dannen wayoyinmu bamusanma lokacin da bacci yadaukemu ba.wutar dakin dim light ne,can cikin bacci naji kamar ana sanya keys don bude dakin da muke saboda ni bani da nawin bacci sosai aiko bangama tunanin hakan ba saiko aka bude kofar wallahi saboda tsorata kusan shudewa nayi,ina ganinshi ya nufo daidai kan gadon da muke hankalinshi duka a kasan gadon ne ni kuwa na kankame jikina sosai na kuma matsowa baya sosai amma na dan bude fuji kadan ta cikin bargon da na rufu,ina ji ina gani ya ciro wani waka acikin duhun ma sai walkiya yake ina ta makyartata jikina sai bari yake yi aiki sai ya caka wukar daidai kirjin Arrauda subhanallah readers a wannan lokacin da naji Arrauda da take makarin fitan rai, na sadaukar da komai na riga na yi over reacting,jikina da ruhina sun kasa resisting kawai sai wani irin kukan da yaci karfina ina kokarin ganin na toshe bakina saboda kada ya farga da ni,saboda shi a zatonshi mutum dayane a dakin duk kokarina na ganin na toshe bakin bai yiwu ba sai da nayi wani irin kuka duk da na toshe bakina da hannuna sai da kukan ta fito haba dagajin wannan kukan ya ce da wa Allaah yahadani,sai ya fincikoni daga kan gadon na fadi kasa cikin sauri ya sanya wukar a wuyana, yafara yankani da ikon Allaah da taimakonshi bansan lokacin da nayi kiciniyar kwatar kaina ba tureshin da nayi sai ya fadi kasa kafin ya mike ni kuma na samu hanyar barin dakin ban zame ko ina ba ina bude kofar gidan da gudu na dinga buga gidajen mutane kusan gida uku na buga amma duk a rufe kuma babu wanda ya jini,abinka da rayuwar turai kowa mind your own business ne.Allaah yabani sa'a a gida na hudun ina tura kofar sai na jita a bude da gudu na shiga cikin gidan wani dan karamin daki na gani abude ina shiga na Kama kofar na kulleta.shi kuwa wancen mutumin yana ta duba cikin gidan ne a zatonshi ina ciki kuma ganin ya yanke ni da yawa bazan iya gudu ba saboda haka bai wani nemeni ba yatafi, ni kuwa daga shiga wannan waje bankuma sanin inda kaina yake ba.










*share vote and comment*

⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐


*WACECE NI*




✍🏼by

*Fateema Muhammad Suleiman*
Email [email protected]
Wattad teemacool2020



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is ton entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*page* 3⃣9⃣&4⃣0⃣




*Today's Hadith is about Acting When Seeing Wrong*

Abu Bakr As-Siddiq (RA) said: "O you people! You recite this Ayah: Take care of yourselves! If you follow the guidance no harm shall come to you. I indeed heard the Messenger of Allah (s.a.w) saying: 'When the people see the wrongdoer and they do not take him by the hand, then soon Allah shall envelope you in a punishment from him.'"

(Jami`at-Tirmidhi, Book 33, Hadith 11)




Ina kwance cikin wannan dan karamin dakin bansan inda kaina yake ba, dukkan jinin jikina kuma ya gama zuba da kanshi bleeding din ya tsaya su ko 'yan gidan basu san ma nashigo gidan ba sai da gari ya yi haske,bayan sungama shiri zasu fita kenan suka fara karo da staining na jini da shatin kafar mutum suna bin kafar mutum, har zuwa gunda shatin kafar yakare daidai wannan dakin da nake ciki dukkansu sun tsorota da taba kofar dakin.wani a cikinsu mai suna zaid ya yi ta maza ya turo kofar sai ganina sukayi kwance cikin jini dagani babu rai.musayar kalmomi suka dinga yiwa junansu daga mai cewa mu kai report police station,zaid da tun da ya ga halin da nake ciki yashiga taba dukkan fannin da yasan za'a gwada agane mutum ya mutu ko yana raye,ya yi iyakan kokarinshi wajen gane ina numfashi daga karshe da ya duba pulse dina,ya gane ina numfashi amma ina cikin critical condition da yake dukkansu medical doctors suna kan yin internship na su ne,sun gane cewa ina da rai...
Duk da suna tsoron yanayin da nake ciki da wuya na rayu amma sunyi farin cikin jin ina da rai,cikin gaggawa suka kira jimi 'an FBI,saboda basu damar taimakona ba tare da sahannun hukuma ba kuma su kansu suna cikin fargaban meyene musabbabin faruwar hakan da zuwana wannan daki? Cikin minti goma sai ga Jami'an tsaro kusan mota uku,wadansu suna cikin mota sauran kuma suka shigo cikin gidan tun da kofar gidan kuma suka fara bin jinin dake kasa hakan yana nufin Wanda akayiwa kisan daga waje ya shigo gidan don buye kanshi.har suka gama binciken gidan gaba daya sannan zaid da tun da Jami'an suka shigo yake sanar da su cewa ina da rai ayi sauri a bani taimakon gaggawa amma basu kulashi ba sai da suka gama bunciken gidan sannan suka bada umarnin tafiya da ni asibiti.daga nan suka fara bin shatin kafar daga waje har zuwa cikin gidanmu to a lokacin ne suka kuma shiga tashin hankali mara misaltuwa ganin jinin da ke malale a kofar dakinmu suna cusa kai kuwa sukayi arba da gawan Arrauda akan godon duk jini ya bata farin zanin gadon.bayan sungama buncika gidan babu abin da suka samu na tuhuma itama asibitin aka wuce da ita.intensive care unit aka shigar da ni.taimakon gaggawa aka shiga yimun dan ganin numfashi na ya dawo normal,jini leda shida aka nema saboda dukkan jinin jikina ya kare.duk wannan abin da akeyimun zaid shi ne akan gaba,jinin ma ya ce a debi nashi saboda yana group 0 negative ne universal donor.da kanshi yaje lab aka gwada dukkan gwajin da sukeyi kafin daukar jini sannan aka debi leda daya,duk da yasan ba'a daukar jini leda biyu a lokaci guda ajikin mutum amma sai da ya ce akara dibar wani ledar, lab technician din ya yi murmushi ya ce haba Dr da kanka ai bama daukan jini leda biyu a lokaci da sai bayan wata uku za ka iya bayar da jini.Dr zaid ya yi murmushi sannan ya ce nasani kawai na tausayawa patient din da zan baiwa jinin ne tana bukatar taimako.lab technician din ya jinjina kai ya ce Allaah ya bata lafiya matar ka ce? Ya yi mashi tambayar ne saboda ganin irin damuwar da ya shiga gaba daya ya canja kamannishi.

Dr zaid ya juyo ya kuma kallon lab technician din,sannan ya shiga nazarina yadda ya ganni kwance santaleliyar budurwa mai kammala sai kawai maganar lab technician din nan ya burgeshi ya sanya a ranshi cewa gaskiya wannan baby Allaah yabaki lafiya kuma na kamawa kaina ke a matsayin mata.sai ya ce wadda zan aurane.lab technician din ya kuma yi mashi add u'ar Allaah yasa ayi aikin a cikin sa'a ya tashi kafadunta.
Ya ce Aameen .Sai da ya tabbatar ansamu dukkan jini leda shidan sannan ya komo dakin da nake kwance.angama shiryani domin shiga dani dakin operation.da aka nema sanya hannun taimakon gaggawa ma zaid din ne ya sanya hannunshi.
Wayoyinmu da suka dauko a gidane suka shiga neman iyayenmu.
Da farko iyayen Arrauda ne suka fara zuwa sannan sai ga su Mummy ma sun zo lokacin kusan awa hudu ne kuma duk wannan awowi ana kan yimun aikine domin yayankani sosai dayake ba'a yanka mutum ta gaba,makagoro baya yankuwa sai ta baya.fatan wuyana duk sun samu damage.
Bayan angama binciken irin wakar da yayi amfanin wajen kashemu aka gane nutumin da ya yi kisar da wannan mutane hamsin kenan ya kashe kuma ba'asan dalilinshi na yin wannan kisar ba,kuma babu wanda ya taba ganinshi tunda yake kisar sai dai a wayi gari aga anyi kisa amma ba'a gane wanda ya yi kisar da musabbabin yinshi kusan shekara talatin ake nemanshi amma har yau ba' a ganoshi ba.abu biyu yake amfani idan zaiyi kisar wuka ko silent pistol.haka iyayen Arrauda suka dauki gawar 'yarsu suka tafi da shi.idan ka kallesu dole idanunka su kawo kwalla duk rashin imanin mutum kuma dole yaji tausayinsu mahaifiyarta kuwa sumanta yafi a kirga.

Ta fannin mummy kam tashiga cikin kololuwar damuwa sai kuka da sumbatu takeyi daddy yana ta bata baki amma taki shiru duk da shima daurewa yakeyi irin ta maza amma kallo daya zakayi mashi kagane yana cikin matsanancin damuwa.

Sai ga khalid da Auntie Maryam ma sun samu labari sun zo,kowa yay I shiru suna jiran fitowata daga dakin operation da yanzu kusan awa biyar ana abu daya.Humaira da idanuwanta suka fada sun rine sunkoma jajir saboda kuka sai cewa take don Allah sis karki mutu ki barni idan ko hakan ta faru wallahi rayuwata tana gargada domin nima zan biki ne bani da kowa bani da kawa ko abokiyar shawara don Allaah kiyi hakuri kada ki mutu ya abar sona da tausayina.kukan da Humaira keyi da sumbatunta kowa sai da yayi kwalla auntie Maryam ce ke rarrashinta ta daura kanta bisa cinyarta tana share mata hawaye sannan ta ce kiyi hakuri sis in sha Allaah zaratun za ta samu lafiya .

Khalid ma sai kaiwa da kawowa yake,da ganinshi shima yana cikin damuwa.
Ana cikin haka sai gashi amfito da ni daga dakin ciyatar shame shame kwance kamar babu rai amma ansamu nadarar ceto rayuwata sun samu nasarar daidaita numfashina.duk suka mike sukayo kan gadon sannan aka wuce da ni intensive Care unit din.kowa sai hamdala yake yi ganin anyi aikin cikin nasara,zaid sai washe baki yake yana nuna farin cikinshi da kanshi ya zo wajensu mummy,yake sanar musu cewa Ku kwantar da hankalinku tana farkawa komai zai daidaita domin munyi nasara sosai awannan aiki.mummy sai kwarara mashi godiya take ganin yadda ya tsaya akaina aka gama komai.
Ta bangaren yusuf kuwa tunda aka suka sauka a Germany yake ta kiran number ta amma bana dagawa yayi mamaki sosai sai kawai ya turomun sako ko lafiya ina kiranki bakya dagawa?saboda shi bashida masaniyar abin da ke faruwa.karfe biyu za'ashigar da ni aiki saboda haka ina Neman addu'_arki..I missing you badly I love.

Dai dai lokacin magariba sannan Khalid yayi ma su mummy sallama ya tafi tareda jaddadawa auntie Maryam cewa duk lokacin da na farka ta sanar da shi.

Ta ce toh in sha Allaah za kaga feedback at any time.

ya ce toh mu kwana lafiya...

Bayan sunyi sallah daddy ma ya dawo daga masallacin asibitin sai ga zaid niki niki da ledoji abinci ne Kala Kala nasu mum daban da na daddy shima daban.mummy tayi ta koraro mashi addu'a gaskiya ta yaba da wannan zaid din ganin irin hidimar da yake tunda suka zo shine akan komai har ta kasa hakuri ta tambayi auntie Maryam akan wayeshi?

Auntie Maryam ta ce wallahi mummy nima sai yau na ganshi, da na tambayeshi yake sanarmun cewa gidansu zaratun din ta buya lokacin da abin yafaru, shima kuma student doctor ne ya na internship nashi ne Yanzu haka.mummy ta ce gaskiya na yaba da hidimarshi tun zuwanmu yana tsaye akan komai, yana da tausayi.

Auntie Maryam ta jinjina kai ta ce gaskiya ya kyauta sosai.Allaah ya biyashi,mummy ta ce Aameen.sai ga kanina yusuf da manya manyan ledoji a hannunshi,ya ce mun fita tare da uncle Khalid ne yabani wannan ya ce na kawo.mummy ta ce ayyah wannan kaya haka ai da bai wahalar da kanshi ba ga wannan ma bamusan gunda zamu sanya ba.....babu wanda ya ci da bisket ne acikinsu mummy ce ma take basu umarnin su ci wani abu amma duk duka ki ci saboda har yanzu suna cikin zullumin banfarka ba kusan awa hudu kenan da fitar da ni daga dakin ciyatar.
Sai ga Dr zaid ya zo ya yi musu sallama ya ce muna sa ran nan da awa daya ko biyu zata farka rashin farkawarta ba wani

Please Login or Register in order to submit comment