Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

container ta kawo fitsari.sannan suka koma office din Dr Thomas.

bayan Kamar minti ashirin da biyar sai aka aiko da results pt positive
Haka ya yi ma ta bayani da cewa ciki ya zauna ajikinki zaki reneshi har zuwa wata tara sannan ki haihoshi normal delivery ko cs Allaah kuma yaraba lafiya.

zuciyar ta ta dan tsinke da bayanan Dr cikin tsoro ta ce Dr yanzu kana ganin zan iya Haihuwa ba wata matsala?

cikin murmushi ya ce babu matsala *Aazeen* sarkin tsoro idan da akwai matsala tun farko ba za mu fara ba kedai ki kula da duk bayanan da muka yi maki kuma kici gaba da amfani da magungunanki sannan bayan wata daya zaki zo follow up.

ta mike ta mishi godiya da sallama ta fito daga office din.

Ta na fitowa daga office din ta ciro wayar ta ta kira number Vaishali,baifi ringing daya ba ta dauki wayar ta kara a kunnen ta cikin fadin abar so na ya dai daga wannan bangaren *Aazeen* ma ta ce masoyiya ina kan hanya na bugo ne kawai na ce everything going on successfully and I will became a mother in next 9 months and daughter to you.

Amma kinsan wani Abu wallahi kawai sai naji na tsorata tun da Dr ya ce mun cikin ya zauna Zuciyata ta fara bugawa kuma har yanzu ban koma normal ba.

daga wancen bangaren vaishali ta ke bata baki da cewa haba abar so na meye na tada hankalin ki bayan sanin da kikayi damuwa ba naki ba ne saboda darurar ki,kuma amfada maki ba'aso ki daga hankalin ki ko kadan

Please Kiyi sauri ki taho gida in sha Allaah za ki haihu normal kuma ki reni babin ki Allah dai ya baki lafiya ita ma ta ce Aameen ga ni na kusa isowa ma sannan ta katse wayar.

Haka suka ringa renon cikin vaishali ba ta barin ta ta yi komai.
David ma ya na iyakan kokarin shi wajen kyautata masu.

Yauma ya zo su na hira da vaishali a falo.kasancewar *Aazeen* cikin kwanakin nan sai barci....ya kamo hannayenta duka biyu yayinda ya ke murza zuben da ke tsakiyar hannunta.ya Kira sunan ta da whisky voice din shi.

Ta amsa cikin sanyi murya ba tare da ta dago Kai ta dubeshi ba ta na kokarin kwace hannunta da ya yi ma ta rukon bazan Sake ki ba,cikin kashe ma ta ido ya ce ki yi hakuri bazan wuce gona da iri ba na san addininku ya haramta maku yin musabaha da namiji amma ni sonki ne ke azabtar da ni kuma ki San cewa bani da nufin cutar da ku tun ranar da na sanya idanuna akanki naji ajikina na samu matar aure sai da na bincika aka ce ku ba 'yan kungiyancen ba ba ta kukayi sai kuma ku ka fada hannunsu toh tun daga ranar nayi alkawarin cire ku daga cikin su.

kuma yanzu haka muna iyakan kokarin ganin mun Sada ku ga kasar ku, ku yi ta addu'a in sha Allaah komai zai daidai ta may be embassy Australia da muka aika matsalar ku su nemeku..ba karamin dadi ta ji ba da bayanashi ya tallabo habanta.ita ma tana murmushi har dimples din ta sun lotsa ta rausayar da ido cikin dubara ta cire hannayenta daga nashi.

ya kura ma ta idanunshi masu matukar daukan idon Wanda ke kallonsu sannan ya ce I love you, and I will die for your love will you love me back as I did to you?

ta sadda kanta kasa nuna alamun Jin kunya, ya ce yes ki dube ni sosai kuma ki bani amsa ta.

ta ce zan fada amma ba yanzu ba.
ya ce no yanzu nake so idan ba haka ba zanyi fushi ya yi kicin kicin da ido nuna alamun kuka.

haka suka yi ta hirar su Kamar kar su rabu amma ana ta kiranshi awaya babu yanda ya iya,haka yakasance yi ma ta sallama ya ta fi bayan ya manna mata kiss a bayan hannunta.

Cikin *Aazeen* har ya shiga wata na takwas, kuma jikinta yana ci gaba da samun sauki har likitocin sunyi mamakin ganin yanda cancerous cells din ke komawa baya.dama sun daina yin radiation din tunda ta na dauke da ciki amma sai suka ga Kamar ya na konewa da kansa yana rayuwar da suke tsammanin nan da 'yan watanni zasu iya zama babu.

ba ta boys musu ba ta ce ni nama daina shan kowane irin magani sai nonon rakumi da fitsarinsa tun da naji annabin mu ya fada a hadisin sa shi ne na daina shan wadanda kuke bani...
Dr Thomas har tabarau shi ya cire ya kura ma ta idanu sannan ya ce kina nufin bakya shan magani sai camel milk girgiza mashi Kai ta yi.

shi ma ya jinjina Kai ya ce lallai za mu yi binciken akan wannan lamarin mu ma mugano wannan fa'ida...ya kuma bata shawarwari sannan ta koma gida cikin farin ciki.

ta na zuwa ta iske gidan da mutane bakon fuskoki sai David kawai da yake zaune bisa kujera ta shaida zuciyar ta, na dukan uku uku saboda tsoro.

su ma da suka lura da hakan cikin sauri David ya fara magana da cewa vaishali ki fito wannan babu wani surprise da za mu ma ta na ga daganin bakin fuska ta so ta rikice mana zo mu ba ta labarin farin cikin nan.

Ashe dama embassy na Australia su ka turo za'a mayar da su San Francisco garin da, da farko sukayi visa to za su tura su can daga can kuma su tura su zuwa ga embassy na kasashensu domin wanna case da dedden case ne da suka dade da nemansu har su ka hakura don babu abin da basuyi ba ba'a gano su ba....
Cikin kwana uku har anyi musu visa da komai haka su ka je asibiti aka basu dukkan file din ta da sauran magunguna ta Dr Thomas da Simon sun yi farin ciki sosai da faruwar wannan Al amari sun ba ta shawarwari masu muhimmanci sannan su ka yi musu sallama da 'yan kyaututtuka.....

farin ciki awajen wadannan bayin Allaah ba sai na bayyana maku ba sai dai na ce Alhamdulillah.

haka aka daga da su zuwa San Francisco....


shin *Aazeen* za ta warke gaba daya ne?
shin ya makonar cikin ta?
shin embassy za su maido su kashashensu?
To wai idan ta haiho dan ya ya sunan wannan Dan?







*share*
*comments*
⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐


*WACECE NI*

✍🏼 by

*fateema Muhammad Suleiman*
Email [email protected]
Wattpad teemacool2020


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```


https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation





*page* 1⃣3⃣&1⃣4⃣

Wannan page na ku ne *wacece ni* FANS1 ina ganin comments din ku sosai da sosai ana mugun tare.....


Suna landing a airport sai ga FBI da sauran securities masu dauke da tambarin sunayensu ajikin banner nuna alamun masu yi masu masauki ne daga gidan gommati.....

Motoci kusan uku ne masu daukan su zuwa masaukin da aka tanadar masu, haka suka shiga motar da ke na farko sannan sauran mutanen suka shiga sauran motocin su ka dunguma zuwa leisure office din su dake Georgia.

acikin babbar birninsu(Atlanta)
Bayan Kamar hour biyu da saukansu sai ga likitoci kusan uku suka shiga bincika lafiyar su *vaishali* dai normal babu abin da yake damunta sai *Aazeen* da tun farko da suke da medical records dinta sannan suka bukaci a Kai ta asibiti don yin ultra sound scanning.
Mintoci da ba su wuce goma ba sai ga su a,asibiti sun yi ma ta scanning EDD dinta zai Kama saura kwana goma sha takwas.

'yan jarida kuwa babu abin da suke sai daukan labaran su domin record na batansu na nan. kuma kullum cikin bincike su ke domin mutuwar high commissioner to United States of America ba karamin tada masu hankali ya yi ba.

ba'a gama binciko Wanda ya yi kisar ba sai kuma ga batan su yaran jakadan biyu kuma sun bata duk da cewa ba a kasar su abin yafaru ba amma visa su daga nan aka yi.
Kuma tun daga lokacin embassy na Australia suka kawo masu dukkan bayanan batan nasu.

Sun yi binciken su a lokacin har suka dan jinkirta binciken kasancewar kusan shakaru takwas kenan.toh sai gashi angano suna Italy tare da taimakonsu David ne da yake aiki a ma'aikatar bincike da harkokin waje.

Sai ga hotunansu a duka kafofin yada labarai da duk wani jarida
To a muhimman kanun labarai za ga ka sunayensu ne


AN SAMU YARAN JAKADAN NIGERIA DA PARKISTAN BAYAN DOGON BATA DA SUKAYI HAR NA TSAWON SHEKARU TAKWAS.



Nigeria

Hajja fanna da yaranta sai dukkanin dangi da abokan arziki fadin irin murna da farin cikin da suke ciki ma bata lokaci ne.Hajja fanna babu abin da yake fitowa daga bakin ta sai hamdala da hailala su na ta duba hutunan su da aka sanya a whatsApp abokanan su Anas din ne suke ta turo mu su dukkan abin da yake wakana. Suma duk sunyi visa domin tafiya can.

ta bangarensu Mr suhaib da matarshi da sauran family ma haka abin yake .Farin cikin da suke ba kadan ba.

Georgia

Haka aka cigaba da kula da su har tsawon kwanaki biyar sannan aka kuma tafiya da su zuwa San Francisco,( Florida )domin acan za su mika su ga iyayensu.

Yau kwanansu uku cib kenan yanzu babu abin da ke damunsa hatta *Aazeen* da aka kuma gwada level na cancer ta babu shi,sun kone kurmus ma'ana dai ta warke har ya sanya likitocin suka shiga binciken lamarin ta domin su gaskiya basu taba ganin Wanda ya warke daga cutar cancer ba kuma ta tabbatar musu cewa ta daina shan kowane irin magana, sai nonon rakumi da fitsarinsa.
Haka sukayi ta mamaki abin.

ya yin da ta bangaren su *Aazeen* murna da godewa Allaah suka dinga yi.

Ta kama hannun vaishali ta ce sister na gode da kulawarki gareni
ke ce irin mutanen da ake cewa a friend in need is a friends indeed.
Allaah ya biya ki ya kuma hada kawunanmu.


David da ke zaune bisa tree setter, ya jinjina masu Kai Shima yana matukar son ganinsu cikin farin ciki kuma ya yi alkawari cikin ranshi zai musulunta saboda yaga halaye da dabi'u masu kyau sabanin yadda ake musu bayanin cewa musulumai 'yan ta'addane kuma ya karya ta hakan.
Saboda ganin sun rabu da iyayensu kusan shekaru takwas hakan bai sanya sun bata tarbiyansa su ba.
Sabanin su da wuya kasamu Wanda ke karkashin kulawar iyayenshi amma za ka samu Sam ba tarbiya da kula da addinin christancin da su ma sai dai ka same su a club wai wayewa da sanin 'yancin Kai...

Yau anbukace su a can embassy duk yawancin 'yan Nigeria ne a wurin kowa kuma awajen nuno musu kulawa na musamman suke nuna musu.

Sannan aka hada su da family su, video call ne haba !)see happy a kowane bangare har tururowar yin magana da su ake daga kowane bangaren danginsu.

babu abin da ke fita daga bakin hajja fanna sai cewa ta ke habibty kin girma can't wait to see you soon my love.

Ita ma *Aazeen* hawaye ta ke ta kasa koda furta kalma daya saboda farin cikin da ta ke ciki bai yuwa ta baiyana shi.

sai ta tsinci kanta da fadin mummy na yi kewarki babu adadi na yi kewar cinyarki, bayanki, abincin ki Kai wadansu abubuwan ma abin dariya ta ke ta lissafowa wallahi mummy bantaba sanin cewa zamu kuma haduwa da ke ba kullum amma ina sanyawa a rai cewa ko ya kikeji da rashin ganina?

Mummy ta ce na yi rashin lafiya tun daga ranar da na samu labarin batanku zuwa yau zuciya ta bata taba Bari na na ko second daya ne ba akan tunanin halin da kike ciki.
Ban kuma gajiya da fadawa Allaah kukana ba akan ya kiyaye mun ku a duk inda kuke Ya kuma Kare ku daga sharrin aljanu da batattun mutane.
Domin ban taba cire tsammanin ku ba cikin raina.
mutane suna ganin Kamar na zautu a duk lokacin da na kawo zancen ku da bayyanawanku.
Gashi yau Allaah ya nuna mana shi isheshshene bisa ga dukkan komai.

Na gode Allaah da ya nunamun wannan ranar in sha Allaah munanan tahowa visa ne ma ya jinkirtar da zuwanmu Amman Muna sa rai daga gobe zuwa jibi za mu dau hanya.
haka kowa, daya bayan daya,suka dinga nuno fuskokinsu ana gaisawa. Kamar suna waje daya saboda a laptop ne suke call din dukkansu.


ta bangaren vaishali ma haka abin ya kasance da yake su hawaye babu wuya awurin su daga Mr suhaib, matar shi da yaran duk kukan murna suke su ma suna sa ran zuwa cikin kwana biyu.
Kamar kar su bar yin wayar haka su ka yi sallama da su,ba dan suna so ba.
sannan aka maido su gida.David ma aka wuce da shi wurin aiki domin karasa sauran abubuwan da bai kammala ba.

*Aazeen* da ke kwance rigingine ta na shafa cikin ta da yake Kamar ba yaron ciki,domin cikin na ta irin Wanda ake dauka a nono ne da hip da suka cicciko ta ce, ya salaam yau ina cikin matsanancin farin ciki Mara misaltuwa Allaah ya bani lafiya da na rasa.ya kuma bamu iyayenmu da muka rasa.

sannan ni kuma gashi na yi abin da yanzu nake da nasani.bansan ya zan bai yanawa mummy wannan lamari ba,
tana murnar samu na,sai kuma kwatsam da ciki abin da ba'a Saba gani,ko ji ba a kasar mu. Sai hawaye sirara da yafara fitowa daga manyan idanuwanta sexy eyes, masu daukan hankali.

Vaishali ta Mike ta zo kusa da ita ta kama hannayenta cikin rarrashi ta ke ma ta magana, haba soulmate meye na daga hankali wannan abin da mukayi ya rigada ya wuce, ai kuma kowane mutum da kaddarar shi. ke kuma haka naki kaddarar take.

kuma ba mu kasance masu sanin gaibu ba. Sannan report na komai naki yana wajen Doctors kuma na tabbatar za su yiwa su mummy bayanin dalilin da yasa kika yi wannan tunanin,ba dan rahmar ubangiji ba,to yanzu sai dai wani labari kawai mu godewa Allaah tunda ba zina kikayi aka samu cikin ba.

haka ta yi ta lallabata har ta samu nutsuwa ta kwantar da hankalinta.

Dan ya yi motsi Kamar yasan maganar shi suke
Haka ta shafa cikin ta ce ya Allaah kada ka kamamu bisa laifin da muka aikata cikin rashin sani Kai Mai gafara ne Mai jin Kai ka gafar ta mun zunubai na kasanya mutane su fahimce ni...
Hakika *LABARIN AAZEEN* akwai abubuwan rikitarwa da ban mamaki....

yau litinin rana ce da wadannan bayin Allaah da iyalansu suke farin ciki n haduwa da yaransu da suka fidda ran samunsu shekaru takwas cut. Tun daga airport murna da rungumar junansu har suka dawo masaukin su *AAZEEN* da *VAISHALI* manne da iyayensu mata sun rugume su gam Kamar za'a kwace musu su.
fadin irin murnar da suke ba abin a misalta bane....




*share*
*comments*

⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐


*WACECE NI*

✍🏼 by

*fateema Muhammad Suleiman*
Email [email protected]
Wattpad teemacool2020


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```


https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation





*page* 1⃣5⃣&1⃣6⃣

Haka su ke rungume da iyayensu har su ka iso gida su na kukan murya family guda biyun nan,su na cikin matsanancin
farin ciki Mara misaltuwa.

Sai tsumbatarsu su ke ta ko ina sai da su ka dauki Kamar awa uku kafin su ka ta kaita su ka shiga tambayar su abubuwan da su ka shiga lokacin batan su.
Haka su ka dinga labarta musu.har lokacin sallar la'asar ya yi.

Bayan sun idar da sallah sai da aka kawo musu abinci da abin sha. Sai kusan karfe biyar su ka kammala cin abincin.

Tun zuwansu *hajja fanna* ta yi noticing 'yar ta,ganin yanayin ta ya tabbatar akwai suspicious things.
ta jawo ta jikinta sosai,sannan ta shiga tambayar ta da cewa habibty na nayi farin cikin samunki a lokacin da na cire tsammanin samunki,sai dai kuma akwai abin da nake tuhuma daga gareki as a trained nurse.


*Aazeen* sai kuka ta ke har da shishshika tsawon lokaci ta yi mai isarta, kuma ta kasa baiwa mummy ta amsar duk da ta fahimci tambayar ta sai, ta tsakaita kukan da ta ke sannan cikin sanyin murya da idan baka kusa da ita ba za ka ji mai take fada ba ta ce,
mummy tunda muka bata ba mu taba yin tunanin sabawa umarnin ku ba ko kuma bata tarbiyan da kukayi mana wannan cikin kuma kaddara ce ta sanya na ke dauke da shi, ta dan yi shiru sannan ta ci gaba da magana da cewa mummy na yi rashin lafiyar da na cire tsammanin sake haduwa da ku saboda likitoci sun tabbatar mun cewa ina dauke da cancer of brain Wanda chances na zama na a duniya ba zai wuce shekaru biyu ba. Lokacin da su ka tabbatar mun babu Wanda Ya zo Kai na sai ke domin na tabbatar cewa baki cire ni daga ranki ba, na yi kuka na kuma shiga tsananin tashin Hankali mara misaltuwa a wancen lokacin na rasa abin da zanyi Inga na sameki ko da na second daya ne.

haka muka ci gaba da zama cikin rudani ga rashin lafiya ta ga rashin samunku,da taimakonsu *vaishali* da *David* ne na dan samu na kwantar da hankali na sai Dr Thomas shi ma ya taimakawa rayuwa ta sosai har na ci shekara daya da cutar bamu samu danginmu ba a wannan lokacin gaskiya na kuma sake shiga wani sabon damuwa saboda har yanzu babu labarin samun ahlinmu, kuma tunani na ya nuna mun cewa komai daren dadewa dole ne a samemu toh wannan lokaci ni zan iya kasancewa ma bana duniya jin labarin mutuwa ta zai kuma jefaki cikin wani damuwar kasancewar son da ki ke yimun ba kadan ba.

Ina cikin wannan tunanin sai na ci Karo da wani page na news paper the insider, sunyi dogon bayani akan inseminating, kuma na gamsu da bayanansu sosai sai kawai na yanke shawarar yin shi yaso ko babin aka Kai maki idan kin ganta za ki rage ciwon rashi na.

*vaishali* da farko ta ki bani goyon baya a lokacin da na tunkare ta da maganan sai daga baya da na kawo ma ta dalilai na ta amince da sharadin hakan ba zai kawo mun matsala ba.haka Shima Dr Thomas sai da ya yi mun gwaji sannan ya tabbatar mana hakan bazai kawo komai ga lafiya ta ba sannan aka yi mun.

to bayan anyimun insemination din kuma muka ci Karo da Deen TV program Wanda sheikh Asib Alhakim ke gabatarwa shi ne ya yi bayani akan cutar cancer da magninsa da kuma addu'o'i da mutum zaiyi ya samu lafiya kuma da muka bi duk abinda ya ce sai Allaah ya kawo mun sauki har na warke har su likitocin sun yi mamaki sosai da wannan lamari.sai a wannan lokacin ta yi shiru.


*Hajja fanna* ta nisa sannan ta kuma kwantar da *Aazeen* a jikin ta sosai har ta na jin yanda zuciyar ta ke harbawa akai akai,sannan ta ce, habibty ki nutsu ki cire damuwa daga ranki I am there for you hakika cikin lamarin ki akwai abubuwan dubawa kada ki samu damuwa wannan baby da za ki Haifa in sha Allaah zan yi iyakan kokari na Inga ta rayu cikin gata,zan nemi dukkan evidence din cikin saboda mutane su fahimci cewa ga dalilin da yasanya aka samu baby Allaah kuma ya saukeki lafiya diyata ta sunkuyo ta sumbaci goshin ta haka ta ci gaba shafa ma ta kai har bacci ya yi awungaba da ita.

Ta bangarensu Mr suhaib ma abin haka ya ke sun sanya *vaishali* a tsakiya sai labarin abubuwan da ya faru da su da wahalhalu da su ka shiga *David* ma ya na cikin su domin tunda ya ga Mr suhaib ya like mashi ya kuma nuna sha'awar zai musulunta sai Mr suhaib ya jeho mashi tambaya da cewa addininmu addini ne mai sauki kuma babu tilastawa acikin ta meye ka gani acikin addinin namu ya sanya za ka musulunta?

David ya ce, kyawawan halin da musulunci ke koyarwa sannan za ma nada su vaishali ya kuma fahimtar da addinin saboda duk da na lura su ma ba su fahimci addinin sosai ba amma su na bautawa Allaah.

akwai ranar da na iske vaishali ta na sallah sai da na jira ta kammala na ke tambayar ta cewa meyasa ta ke damun kanta da yin sallah tunda ba kwa tare da iyayenku.

amsa da ta bani shine ya sanya zuciyata binciken wannan addini har kuma na gane shi ne addinin gaskiya babu Wanda ya sanya zan karbi addinin nan fa ce Allaah da ya so ni da shiriya.

amsa da vaishali ta bani shi ne ni Allaah na ke bautawa ba iyaye na ba domin idan su basa gani na toh Wanda Ya kagi halitta ta, ya na gani na.

to a lokacin tunanin da ya fadomun lallai idan ko haka ne dole in bunciki wannan addini.

saboda abinda ake koyar da mu musulumi dan ta'addane, kar ku kuskura ku hada hanya da su domin za su kashe ku toh da na karanta qur'an sai naga sabanin abinda iyayenmu su ke fada mana sai gani ma nayi musulunci kiyaye rai yake ba kashewa ba.
wannan shi ne dalilina na son musulunta.

Mr suhaib ya ce Alhamdulillah da ma mu haka muke so mutum ya fahimci addini da kansa sannan ya karbi kalmar shahada.yanzu ka shirya ne za ka karbi kalmar shahada ko kuma za mu baka dama ka kuma fahimtar addinin sosai?

David ya ce na shirya ina bukatar a bani kalmar yanzu.
Mr suhaib ya sanar da jama'ar da ke wurin ga dan uwa yanason ya musulunta.

suka maso kusa da shi Mr suhaib ya na fada mashi kalmar shahada shi kuma ya na maimaitawa har ya kammala sai duk 'yan wajen su ka sanya kabbara tare da rungumar David su na cewa Alhamdulillah Barka da shiga addinin gaskiya Allaah ya kuma shirya da Kai ya kuma fahimtar da Kai addini.


dai dai lokacin magariba ne to aka nuna masa yanda ake alwala sannan su ka nufi masallaci.
Su na idar da sallah sai ga hawaye daga idanuwan David.

Da sauri Mr suhaib ya matso kusa da shi ya na tambayar meye yasanya shi kuka?

David cikin jinjina Kai ya goge hawayen sannan ya ce ,

Wallahi yau zuciya ta, ta shiga wani irin yanayi da bazan iya kwatanta ma ka ba. Sai godiya da zanyiwa Allaah da ya shiryayar da ni zuwa ga wannan tafarki madaidaici.

Sai ya kuma Kama hannunshi su ka rungumi juna har su ka bar masallacin da murmushin farin ciki a fuskarshi da ganin shi za ka tabbatar ya na cikin matsanancin farin ciki.




**********



Yau kwana goma kenan da zuwansu mummy da misalin karfe tara na dare, sun hadu dukkansu har da su Mr suhaib saboda su ma basu koma kasar su ba su na jiran *Aazeen* ta haihu sannan duk su koma kasashen su toh gashi a wannan dare *Aazeen* ta fara jin matsanancin ciwon mara da ma tun da yamma ta ke ji kadan kadan amma ba ta fadawa kowa ba sai yanzu da abin ya ke so yafi karfinta haka aka kaita asibiti.cikin gaggawa aka karbeta,saboda tun a gida *Hajja fanna* ta yi ma ta V.E ta na seven CM ne kuma su na zuwa ba su wani dauki lokaci ba ta haife yarinya Mai kamanta Kamar antsaga Kare sai dai farin da ta dauko na turawa hakan ya na nuna sperm donor din da aka yi ma ta inseminating din bature ne ana ba ta diyar ta ke wani irin so ya ziyartar ci zuciyar ta sai yanzu kuma ta tabbatar da haka soyayyar uwa ta ke ga danta take duk wani wahala da tasha ya kauce a jikin ta haka ta ringa kwararo addu'o'i ta na yiwa 'yarta Allaah Kai ne ubangiji na ina kan wa'adinka da alkawarin ka ina kaskanda da Kai kankantar da Kai na mai lafiya a gare ka ,ya Allaah na rokeka da sunayenka ka kyawawa da suffofinka

Please Login or Register in order to submit comment