Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce banji meye Kika ce ba Yusuf ko meye naji kin ambata?
Dago Kai nayi na kare Mata kallo sosai gaskiya na gaji da kunbiya kunbiya da boye boye yau dolene na zama jaruma na fito fili na fada Mata gaskiyar abin da ke raina koma dai meye zai faru ya faru,cikin sarkiwar murya kasa kasa na ce Yusuf dai daya shi nake nufi tun daga ranar da mukaje gidanshi bayan dawowarmu na Kira number sa don bashi hakuri akan abin da ya faru na so na dai dai taku amma da Kika ki ni na tausaya masa nake dan taimakonsa toh zuciya ta ta kamu sa sonshi kuma shima Yana so na.
Tunda nake magana tayi sakeke tana kallona maganganu na ma mamaki suka bata she is totally confused.
Sai da taga nayi shiru ta ce lallai zaratun kinyi babban kuskure ina hankalinki da tunaninki duk sukaje da har zakiyi garajen fadawa tarkon soyayyar musaki,a musakinma kuma talaka ta sake tabe baki ta ce wallahi am speechless amma zanyi maganinku daga shi har ke.
ke kam naki maisauki ne,yarinta ke dibarki.
Tunda ta ce haka zuciyata ke ta faman dukan uku uku,kuma Ina tsoron kartayiwa Yusuf rashin mutunci ni fushin da nayi da shima duk na zafin ciwone,amma ko kadan banrike abin da wani serious ba.tun muna asibiti yayi ta faman kirana amma bandauka ba saboda Khalid Yana wajen.toh yanzu idan auntie Maryam ta kirashi ta balbala mashi ruwan masifa ya zanyi zai dauka ma ni na sanyata,aiko bangama tunani ba ta fito sanye da hijabi.
Ta ce tashi muje gidan Yusuf din ashe shi Munafiki ban yarda kwallar mangoro ba kenan shinan yasamu karamar yarinya Yana fure mata kunne.
Na ce ni wallahi ba inda zani,kuma baya furemun kunne ni kawai tausayinshi nake yi,kuma gaskiya ba yadda za'ayi domin zuciyaya na sonshi,saurin fincikoni tayi ta mikar da ni tsaye sai da ta ingiza keyata waje sannan sa sanya kuka amma dole ta sanya muka kama tafiya da ma ta yi magana da cab bamufi minti biyu ba sai ga motar sai da Muna daidai layinsu Yusuf ta umarci driver da ya yi parking tun kafin motar ta daidaita parking ta kamo hannuna muka fito Muna m shiga cikin gidan,wayam dakin ba kowa ita ce ke duk duba ko ina na dakin amma ba kowa ,nayi mamaki shi kuma Yusuf ina ya shiga ne kodai tayi fushine da ni ya chanja apartment saboda kar bazo inda yake,amma kuma bazaiyimun haka ba ina cikin wannan tunanin auntie Maryam ta dakamun tsawa da cewa wato kin sanar mashi cewa zamu zo Kika sanya ya gudu to wai shi wannan gurgu ta ina ma ya samu ya fita ne tayi maganar cikin tabe baki nasan da biyu take kushe Yusuf don na ce ina son shi.
Bandamu da maganganunshi ni hankalinane ma ya tashi sosai kodai dama ba so na yake ba yaudara ce wata zuciya ta ce mun a'a akwai dai wata dalili munfi minti ishirin a gidan amma babu Yusuf babu dalilinshi abin mamakin ma kofar gidan da na dakin duk a bude.haka muka koma gida ta na ta yimun balbalin masifa sannan ta ce yanzu kam kin samu kanki idan kuma mutuwace zakiyi akan sonshi sai ki mutu, tunda ya gudu ya barki wallahi ya ci sa'a, da Yau yaga rashin mutunci ai.
Nidai bance komai ba Ina son kawai mu komo gida na Kira wayarshi inji Ina yajene munje gidanshi bayanan.
Bansanma mun iso gida ba sai jin motar ta tsayane ya ankarar da ni banjita ba nayi saurin sauka a motar na shiga cikin gida.daki na wuce direct bayan na rufe kofata har hannuna Yana karkarwa da nake dailing number yusuf bata shiga, is unavailable yake cewa
Haka nayi ta trying amma bata shiga zuciyata ta rayamun cewa kodai yusuf dama yaudarata yake baya sona.wata zuciyar ta ce a'a w akwai dalili koma dai ya ya zandiga trying time after time,ganin magriba ta gabato sai na dauro alwala na fito parlor,auntie Maryam tana zaune ta manna waya a kunnenta hira sosai take amma duk tsawon zamana banajin abinda me take fadi dagani hirar soyayya take.har na gaji na tashi yin sallah don lokaci ya yi banjirata munyi jim'i ba.bayan na idar na gane tana fashin sallah.na juwo na ce inajin yunwa muci abinci batare da ta dubani ba ta ce to ki fara ci I will join you later.
Har sai da na kusan gama cin abincin sannan ta fara cin nata.zan tashi sai ta kamo hannuna na kuma zama sai ta ce zaratun.
Na amsa da na'am

Ta kamo hannuna dake ciwo tana kallo sai ta ce my Angel kinsan cewa ina sonki bazan so na cutar da ba ko wani irin abu zai cutar da ke kuma zanyi iyakan kokarin ganin na kawar da shi,ke yarinya ce bakisan komai ba zuwa gidan namiji ba muharraminki ba haramun ne koda kowa saurayinkine ko mijin da zaki aure matukar ba'a daura maki aure da shi ba ballema na ki case is different coz yaushe zaki iya da default person.kinga komai da komai ke zaki mashi sai kin fara samun yara tukun za ki gane kuskurenki idan har kika biyewa zuciyarki Kika amince ya aureki wanda nasan da wuya hakan ya kasance ma.ki nutsu ki koma hankalinki sannan ki tattara wannan yusuf din ki cireshi daga ranki tun kafin sonshi ya kawo maki illa.
Idan ba abinki ba ga Khalid nan yana mutuwa akanki amma kinki tsayar da tunaninki waje daya wai ke tausayi da soyayya ko.toh yanzu Ina kike ganin zaki samu inda yusuf din ya tafi?
Ki duba fa dan butulci bayan ya konaki sannan yabar gidan ba tare da ya sanar maki inda za shi ba.
Tun da ta fara magana ban sanya mata baki ba ,sai da naga tayi shiru sannan na Fara magana da cewa,auntiena nasan kina sona nima kuma ina sonki,maganar yusuf kuma babu yadda na iya zuciyata ce tayimun laifi wajen sonshi kuma wallahi ya fadamun cewa he is not default,zaiyi regain health dinshi aikine akeson za 'ayimashi to kudaden ne suka kasa biya amma yanzu akwai wanda yadau nawin yin aikin,Ina ganinma can suka tafi wallahi ya yi ta kiran wayata dazu bandaga saboda muna tare da khalid ko maganar tawa bata bari na karasa ba.
Ta ce kinjiki dai ana maganar lafiyayya wa yake kawo abin da babu tabbas ko da anyi aikin Ina Kika taba ganin spinal cord injury ansamu waraka

Na ce kina musu da ikon Allaah ne kuma ai shi nashi mino injury ne in aha Allaah zai warke nidai abu daya nake bukata awajenki give me courage ni kuma zanji da sauran wallahi ba na nufin tozar taki ko kuma yi maki snatching naga nine tun farko kin nuna bakyayi da shi wallahi kuma taimakonshi nake so nayi bayan ya nemi taimakon nawa kinsan halin zuciya daga baya kuma muka koma soyayya Wanda bansan lokacin da tayimun dirar makiya ba.Ina wannan magana ido kuma duk akanta Ina nazirin yanda take sauraron maganganuna.

Ba ta kuma cewa komai ba kawai ta ce toh Allaah ya bada sa'a,amma nikam kada ki sanyani cikin shafgar yusuf dinnan.
Banyi magana ba naja bakina nayi shiru.da misalin karfe tara, na yi mata sallama na shiga bedroom shirin bacci nayi sannan na kira Humaira Muna Dan yo hirar school tana bani labarin yanayin makarantarsu,nima na dan bata namu makarantar sannan na kira dad naci sa'a suna kusa da mummy sai da suka Dan yimun nasiha irin na iyaye da in kula da kaina da karatu na ce yaushe zaku zo mana visiting dad ya ce very soon idan mun sanya lokaci za mu sanar da ke na ce I love you so much miss u.shima ya ce we love you too dear.
sannan na katse kiran.number Yusuf na kuma kira still is unavailable gaskiya nashiga damuwa sosai wannan wane irin abu ne haka amma koma meye ke fararuwa he should at least let me know,kamar in kuma komawa gidanshi nake ji amma babu hali.inacikin zancen zuci sai ga kiran Khalid din ta shigo kamar kar na dauka saboda Sam bani da mood din yin magana da kowa at this moments.
Muryata can kasa na amsa sallamarshi
Cikin damuwa ya ce ya hannun hope yayi sauki?
Na ce eeh Alhamdulillah
Sai ya ce ya muryarki somehow kodai hannun ne har yanzu na lumshe idanuna na ce a'a kawai na gajine kuma inajin bacci ya ce bari na barki ki samu Hutu ya ce I love take care .
Na ce loves you too thanks.
Daren ranar haka na kwana da mafarke mafarke barkatai babu Wanda na rike ko daya tun asubah na kuma kira number har yanzu dai bata shiga,komai cikin sauri na gabatar saboda kaguwan zuwa gidan yusuf .....ko tea na kasa sha auntie Maryam tana tambayata irin wannan sammako haka kamar wanda zaibar garin?

Na ce ehh ina da seven ne.
Ta daga Kai ta dubeni daga sama har kasa cikin kallon tuhuma amma Bata ce komai ba kawai ta ce yau zan je wurin supervisor na,na waro ido na ce kai! Auntie rancen ma da Kika je baki sameshi ba ance sai yamma lis yake zuwa?
Ta ce eeh to ya zanyi kinga samples din tun yaushe aka kawo kinsan idan har sun dade baigani ba karshenta yayi rejecting so ni kuma ban shirya yin asarar nakudan kudade ba.
Ki dauka wancen kawarki na hostel meemah Ku kwana tare da ita nikam idan ta kama kwanane ma zan kwana muhadu ya samun hannu.

Na ce to safe journey.

Ta ce thanks take care.

Na tare taxi nahau unguwarsu yusuf din na ce ya kaini tun daga kofar gidan na gane yadda muka barshi jiya haka yake ina cusa kaina sai wani mutum zai fito daga dakin yusuf shirin kulle kofar dakin yake nayi sauri na iske tare da tambayar mai dakin wato yusuf?

Sai da ya gama nazarina sosai sannan ya ce,ayyah yusuf an mayar da shi kauyensu tun jiya da yamma naji yana maganar ko sun samu mai maganine,ni makocinshi ne ya barmun gidan nan a hannuna ya ce akwai sako da yabarmun ya ce akwai wata da za ta zo gidan na taba sakon duk lokacin da ta zo please ya ya sunanki ya tambaya?

Na ce zaratun.

Eeh haka ya ce bara na dauko maki sakon,na tsaya jiranshi sai gashi da dan takarda ya mikamun sannan ya Kama hanya ya fita nima nabi bayanshi muka fita tare.

Ina shirin bude takardar sai kiran Khalid,ya na tambayata Ina nake?
Nayi mashi kwatancen gunda nake ko minti biyar ba'ayiba sai gashi nayi mamaki sosai da ganinshi Ina murmushi na ce sai kace dama kana wajen sometimes Ina ganinka kamar monitoring spirit kake na fada ina tabe baki sai ya ce ai dole nayi tattalin abata kafarki kafata,yanzu ma na zo ne muje ki zabi motor saboda gaskiya na gaji da ganinki kina hawa motar haya.
Na dafe kirji na ce nidin gaskiya I can't believe it,
Cikin farin ciki na shiga motar,bai zame ko Ina ba sai gunda ake sayar da motor,motocine Kala Kala new model burjik awajen ya ce ki zabi duk Wanda ranki ke so...

Kasa zaban motar na yi ina ta ruwan ido sai cen wata red color na zaba kawai mukullin Motar aka mikomun Wanda yake mikamun mukullin ya na murmushi ya ce favorite color na oga kenan kika zaba,bansan wani oga yake nufi ba saboda ga khalid din har ya nunamun naby blue na ce banason color shine nadau red colorn...bakina bai gajiya da yi mashi godiya ba shiko sai murmushi yake. auto ne motar, kuma a take na fara driving a hankali muka jira da khalid muka Kama hanyar gida.......duk da ina farin cikin samun motar to dayan bangaren zuciyata tana ayyana sakon yusuf da na boye acikin Jakata.......















*please comment share and vote*


⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐


*WACECE NI*




✍🏼by

*Fateema Muhammad Suleiman*
Email [email protected]
Wattad teemacool2020



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is ton entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*page* 3⃣5⃣&3⃣6⃣




*Tambaya* shin mace mai jinin biki zata zauna har kwana arba'in ne baza tayi sallah da azumi ba?ko kuma Abin Lura daga gareta zatayi tsarki ,tayi sallah kuma nawa ne mafi karancin kwanakin da zata tayi kafin tayi tsarki?

*Amsa*
Mace mai jinin biki bata da kaiyadadden lokaci sai dai duk lokacin da jinin ya zo Mata zata zauna baza tayi sallah ko azumi ba sannan mijinta bazai iya saduwa da ita ba.amma idan taga jinin ya dauke,wato ta tsarkaka ko da kafin ta cika kwana arba'in ne ko da jinin iyakacin kwana goma kawai yayi ko kwana biyar sai kawai ya dauke,to sai tayi wanka tayi sallah da azumi kuma mijinta zai iya saduwa da ita babu laifi cikin hakan.
Sai dai abin da yafi muhimmanci shi ne jinin biki al'amarine kebantacce kuma hukuncinsa Yana ratayuwa ne da shi ,wato idan jinin yazo hukuncinsa Yana nan baza tayi sallah da azumi ba kuma mijinta bazai iya saduwa da ita ba.duk lokacin da tayi tsarki to ta wofanta daga hukuncinsa.




Duk da na dade da koyar motar sai yau najita kamar sabon koyo koda yake hakan yadanganta da dadewa da nayi banyi tuki ba kowane abu idan dai practical aspects ne idan ka dade baka yi ba za ka manta,khalid har zolayata yake yi wai kawai na sanya L wato laner.na dan harareshi cikin wasa na ce anki din har da dan zunguro bakina duk wannan hirar munayine shima yana cikin motarshi amma muna kusa sosai.daidai kofar gidanmu mukayi parking tun kafin na shigo sai ga auntie Maryam ta fito da shirin tafiya turus taja ta tsaya ganin Ina nuna mata car keys din hannuna tare da pointing din motar nuna alamun na wane,shi kuma khalid ya fito a motarshi ya harde hannayenshi duka biyu a kirjinshi,Yana ta kallonmu cikin nuna sha'awar hadin kanmu sosai ta nuna farin cikinta sannan ta gaishe da khalid tayi mashi godiya ta ce my angel zan tafi sai na dawo zamuyi celebration da lunching na motar Muna rungumi juna tayimun kiss a goshi na ce miss you ta ce miss you too,har ta fara nisa sai khalid ya ce na dakatar da ita mukaita park....sai da na shigar da motar cikin gida na kulle kofa sannan dukkanmu muka kama hanyar park domin train zatabi.sai da muka jira tahau train din sannan muka kama hanyar komowa gida kawai na ce mashi ya saukeni a school saboda Ina da 2-4 human physiology lecture.Muna tafiya Yana ta jaddadamun soyayyar da yakeyimun ya ce please zatatun inason ki tsayar da hankalinki waje daya ki fadamun gaskiya akwai wanda kuke soyayya ne bayan ni?

Nayi shiru kuma na sadda kaina kasa saboda bani da amsar da zan bashi.
Ganin banida niyar magana ya kuma kiran sunana da wani irin husky voice dinshi mai tayar da hankalin wanda akayiwa,ya ce look at me what do you encounter in my eyes?
Da sauri na dauke idona daga lumsassun idanuwanshi da suka rine suka zama ja daganinsu tsansar sona ne aciki.

Gaskiya ni ba irin 'yan matan nanne masu yaudara ko ruwan ido da son abin hannun samari ba, once nace ina sonka I really mean it,saboda wannan dalilin ne ma na kasa sakin jiki da khalid ba,wanda shi kuma khalid ya kasa fahimta ta ..cikin sanyin murya sannan a hankali dama tun asali bani murya sosai na ce khalid gaskiya bazan boye maka ba akwai wani da muke soyayya kusan waya shida kafin haduwarmu da kai,amma kayi hakuri ban sanar da Kai ba tun farko please forgive me na nuna alamun roko da hannayena.

Tsawon lokaci ya kuramun idanuwa Yana naziri da maganganuna sai ya ce naji dadi da fadamun gaskiya,dama nasan bazai yiwu ace ni kadaine na kyalla ido akan wannan kyakkyawar fuskarki mai annuri da wannan ass da boob din da suke jawo hankalin mai kallonsu.
Duk kunya ta kamani da wannan maganarshi ta karshen.
Ashe shi ya sanya duk wucewar da zanyi agaban maza sai naga suna kananan maganganu Kai har lectures din suna kawomun hari amma duk babu wanda na bashi fuska,bana manta ranar da Muna practical a lab to ni Ina kusa da wani supervisor da yake duba ayyukan da muke na sargu da kallon kurilla da yake yiwa kirjina muna hada ido yayi saurin kawar da kanshi yabar wajen bayan kamar minti biyar sai gashi ya dawo da wata karamar takarda ya ajiye ya tafi Ina budewa naga ya rubuta number wayanshi sannan wai give me call and meet me at my office.
Dogon tsaki na ja,na yaga takaradar nayar. tunda daga ranar ya kullamun har yau kuma Ina carrying course din da yake daukarmu.sai yanzu da khalid ya kawo zancen ass da boob na gane Ashe abin da yasa duk wani namiji ya kalleni sai yayi attempting yimun magana hakan ya sanya bana kula kowa saboda na kasa gane manufarsu a kaina yusuf kam daban yake a cikinsu....

Kinyi shiru meye kike tunani haka?

Maganarshi ce ta dawo dani daga dogon tunanin da na fada firgigit na ce wallahi na tuna gida ne
Yadan sako murmushi sannan ya ce cikin masoyan naki ina neman alfarma da ki sanyani star saboda ba yadda zanyi na hanaki soyayya but sooner or later zan koyar da ke soyayyar da zaki manta sauran samarinki cox am always lucky musamman kan abinda nake so I will do what ever I can to have it..so wish me luck Yana duba cikin idona,gaskiya idanuwan khalid akwai wani abu kamar magnet da yake fizgar mutum sometimes yanayin kallonshi da maganganunshi suna yimun shige da na yusuf...sai dai yafi Yusuf tsaurin ido.
Nayi murmushi na ce wish you all the best of luck...

Ya ce thanks zan tafi idan kingama lecture give me a beep I will drop you back home.na girgiza kaina na ce haba gaskiya wahalar tayi yawa man sunan da nake kiranshi kenan,zan kira cab,amma karka wahalar da kanka nasan kaima kana da naka hidimomin nagode sosai da kulawarka gareni.

Stop it,nafada maki cewa zanyi iyakan kokarina wajen cinye gasar da nake ciki daga yau ne ma assignment dina zai fara aiki bear in your mine I am always at your service.kuma banason yawan godiya a duk lokacin da nayi maki abu bakisan yanda kike a zuciyata bane.

Na ce to nagode sosai idan kunyi waya da neelah my regards to her.

Ya ce to,sannan yayimun sallama tare da jaddadamun na kirashi idan mungama lecture.
Na ce toh....

Sai naje hall ba mutane sosai, saboda har yanzu da sauran lokaci,sai a wannan lokaci na samu daman dauko takardar da yusuf ya barmun ga abin da nagani...

*my soul mate*
Things were said in haste, things happened against fate, but if you do accept my apology, everything will be better again.wallahi I didn't mean to hot you.ya ciwon hope kinje asibiti sun dubaki? Tun ni anki a saurareni na kira likita,
Bada niya hakan ta faru ba kuskure ne,koda yake nasan ki sarai kina da sanyi hali da tausayi wadannan halayyarki su suke karamun kwarin gwiwar cewa nima fa cikkekken mutum ne, I reflected on the things I don't have in life but I remember I have you thats made me completed. so ki ci gaba da rikeni da amana da soyayyar da kikeyimun ni kuma na maki alkawari zan rikeki amana duk rintsi duk gaskiya.Na kira wayarki sau ba adadi amma baki daga ba.kamar yanda na fada maki wani bawan Allaah ya taimaka zuwa Germany akan aikinda za'ayimun.ranar Monday zamu tafi amma kafin nan Ina Michigan,zan kira ki idan nayi landing,ki kularmun da kanki sosai I love you take care.....

Sai da na gama karantawa na kuma nadewa na jefa a jaka sai yanzu kuma hankalina ya kwanta,amma toh meye yasa bai kirani ba har zuwa wannan lokacin?
nabarwa zuciyata,a haka har hall din ya fara cika dama kuma bamu wuce mu talatin ba a wannan course din elective ne...Muna gama lecture, ina hada littafaina sai ga latifa,ta tayani hada takardun ina tambayarta ina Arraudah? wata course mate dinmu ce kuma Muna zumunci sosai da ita. tana hostel
bata daukan wannan course,amma yanzu ki tabota a waya idan tana nan sai muje,wallahi ni gaba daya lecture4-6 din nan ya Fara fita akaina tana magana tana yatsuna fuska.
Na danyi dariya na ce ki rabu da prof paul lafiya dai kawai amma ba kina korafin time na lecture ba.
Na kara wayar a kunnena ringing na biyu sai ta daga da cewa yes ina nan ku tafomun da burger a web 10,na ce toh na kuma juya ganin web din Muna kusa da wurin sai da muka saye burger sannan najira Latifa ta dauko motar ta a parking lot muka wuce hostel.hira sosai mukeyi irin na kawaye kowa kuma yana kawo maganar samarinshi kunsan dai taron 'yan mata,munyi ciye ciye sosai saboda dukkan kawayenmu na hostel kowa abin da take dashi muka taba gonin ban sha'awa.sun tayani murnar sabuwar motar da nayi.na roki Arrauda da ta tayani kwana a gida saboda auntie maryam taje michigan wajen supervisor ta idan bata bata samu sun gama da wuri ba za ta jira shi.sai da muka idarda sallar la'asar muka dawo faculty, lecture will not hold today abin da class rep yarubuta a board kenan,saboda haka kowa yakama haryan fita daga hall din.Latifa taso ta saukemu a gida amma na ce zan Kira khalid.
Ta tabe baki ta ce Allaah sarki khalid ina yimaka fatan alkhairi ya dauraka akan wannan cheeks din girl din nan domin kana sonta diyawa.nayi murmushi nasan da biyu take wannan maganar.

Baifi minti goma da kiran khalid ba sai gashi,bakin wandon jens ne da long sleeve shirt sky blue sanye a jikinshi. Masha Allaah kayan sun karbeshi sosai cikin murmurshinshi mai ban sha'awa ya gaisa da Arrauda itama ta amsa,da kanshi ya budemun gaban motar duk muka shiga yaja muka tafi...
Yana fadamun abubuwan da yayi bayan rabuwarmu dazu,na waro ido na ce gaskiya Yau ka aikatu sosai kuma dama naji ance wannan level coordinator bashi da sauki,duk Wanda aka hadashi da shi to zaisha research a field but yana bada grade mai kyau.
Ya jinjina kai ya ce hakan yana da kyau.sai da muka tsaya a hajwan khalid ne ya shiga ciki,sai gashi da ledoji niki niki.

Daidai kofar gidanmu mukayi parking sai na mikawa Arrauda keys din kofar,ta sauka da ledojin. sai khalid ya juwo sosai yana fuskanta ta har inajiyo hucin numfashinshi nayi sauri na ja baya sosai.

Yadanyi murmushin abin da na yi ya ce matsorociya kawai, ganin naja baya ya ce stop it karki fadi sannan cikin dense voice dinshi yakira sunana zaratun please kibani dama asanda maganata agidanku mana wallahi na kasa controlling Kai na akan sonki ki tausayamun duk lokacin da muka hadu sai nayi mafarki da ke kuma kina sanyani yin wanka.na baki sati daya kiyi shawara akaina so zan jira feedback.ki shiga gida sai munyi waya.

Cikin sanyin murya na ce toh.sai da na jira ya tafi sannan na shiga cikin gidan.lokacin dai dai magriba ta gabato,na tarar har Arrauda ta dauro alwala nima ban zauna ba sai kawai na dauro alwala na fito,sai da muka gabatar da sallah muka jawo ledojin kalolin abinci ne sauran kuma fruits ne ga gashasshshun kaza guda biyu,munci sosai.
Sai da muka jira lokacin sallar isha tayi mukayi sallah. sannan muka wuce bedroom domin baiwa ido hakkinshi,saboda gajiya ko minti goma bamu kaiba bacci ya daukemu.

Can cikin bacci sama sama naji wayata na ringing cikin magagin bacci na Kara wayar ba tare da na duba ko waye ba jin muryar yusuf ne yasa na watsake na nude idanuna sosai karfe biyu da minti goma dai dai.

Tun kafin ya ce wani abu na shiga yimashi kuka har da shishshika.sai rarrashina yakeyi ta cikin wayar duk hankalinshi ya tashi,ya rasa inda zaisa kanshi saboda damuwa.shima cikin murya kamar kuka ya ce sorry its OK,kiyi shiru ki saurareni,ya ce meye ne baby na kada kiyimun kuka banaso meye ne yanzu toh.
Cikin kuka kamar yaron goye na ce ba kai bane sai nayi shiru...sai ya ce toh am sorry wallahi bansamu lokaci bane daga jiya har yau Muna kan abu daya sai dazu ne nasamu damar sayen Sim card amma kina cikin zuciya ta.
You are the one, who holds the key to my heart.daga kisani kin riga kin mallakeni.yanzu na Kira ne naji ya hannun naki? Ina fatan sakon da nabar

Please Login or Register in order to submit comment