Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne wato auntie Maryam sai da ta fadawa mummy maganar Khalid da yusuf amma ina ganin bata ce Yusuf din bashi da lafiya ba,ita kuma mummy da taga Dr zaid ta zata shine dayan da auntie Maryam ta ce nafi sonshi.

Dam zuciyata ta buga da naji daddy ya ce ai ita yanzu bata da zabi acikin su Khalid ne ya cancanta ya aureta,duk da shima zaid na yaba da halinshi to nayi la'akari da cewa Khalid ya riga da ya furtamun shifa son zaratun yake kuma da aure,duk da bance mashi komai ba na ce dai bari ta warke sannan muyi maganar toh kinga shi kuma zaid bai furta hakan ba.sai da na dinga ambatar sunayen Allaah nadan samu relief wato ni fa akwai gagarumin tashin hankali agaba saboda su basu ma san waye yusuf ba balle aje da zancen shi crippled,na dinga kullawa da kuncewa ta yaya zan fara kawo musu maganar Yusuf kwamachala kenan ni zaratun naga ta kaina ina zan tafi da son yusuf?

Har dare ina cikin jujjuya maganganunsu Mummy cikin raina.Allaah ya zarabceni da cuta gashi na warke sumul kamar bantaba yin jinya ba,watana daya cib a hospital sallama kawai muke jira,sai gashi yanzu nidin za'a iya kirgani a cikin young millionaire saboda kudaden da aka taramun a account.

Wayar yusuf ne ya dawo da ni daga dogon tunanin da nalula,sam cikin kwanakin nan jikina so weak idan muna waya da yusuf,cikin muryarshi da yake kashemun dukkan gabobin jikina ya faramun magana da cewa ala nguro,your excellency barkanki da hutawa wannan irin recognition haka yanzu na karanta labarinki a top of the insider news gaskiya your talented,ki godewa Allaah, kina da baiwa sosai,nima ina tayaki murna da tona asirin makashinki da dubban mutane da basu ji ba basu gani ba yayi sanadiyar turasu lahira,ki ji mutumin nan Ashe shi ne ya kashe wani ambassador da dadewa na Nigeria lokacin America tashiga tashin hankali saboda bilateral diplomacy dake tsakaninta da Nigeria.tun kafin ya gama zancenshi na ce dan Allaah ko zaka iya sanin sunan ambassador da kake magana akanshi?
Ya ce eeh ai ga sunan a jikin jaridar Alhaji modu,ai bangama jinshi ba saboda kadewa na katse wayar da sauri na sauko daga kan gadon na sanya takalmana na fito wajensu mummy da suke hirarsu a common room na asibitin.

Saboda sauri har kafata na sarkewa na iso da Sauri wajen Mummy sannan na ce mummy kinga wanda yayi attempting kasheni shi ya kashe daddy ki yanzu aka wallafa a jaridar the insider,kafin na gama maganata sai ga daddy da jaridar a hannunshi yana nunawa Mummy labarin sai ga hawaye daga idanuwanta shar gaskiya duk sai da mukayi ta kuka mutuwar tadawo sabuwa awajenmu.muna cikin wannan jimanin sai ga kira daga danginmu na Nigeria,
sai ga kiran Vaishali itama dai jajen tayi ta yi.
Kiran kam munshashi daga duk Wanda yasan kabarin wancen al'amarin.

Kiran yusuf dinne ya kuma shiga cikin damuwa yake tambayata lafiya na kashe waya bamu gama magana ba?

Sai da na nisa sannan na ce labarin da ka bani da sunan da na tambaya wato kana bani labarin mutuwar kakane fa alhaji modu tsohon ambassador.sanadiyar mutuwarshi kuma ya jefa mahaifiyata cikin mummunar al'amari mai rikitarwa.

Ya ce kai! Subhanallahi Ashe ki ce alhakin kakanki ne Allaah yasanya dubunshi ya cika gaskiya wannan azzalumin ya cutar da ku sosai, ga kakanki da aminiyarki da ya zama sanadin aikasu lahira,abin haushi kuma gashi kafiri.
Wane irin mummunar al'amari ne mahaifiyarki tashiga ya jefomun tambaya?
Na ce labari ne mai nisa in sha Allaah zan sanar da kai,yanzu gaba daya na gaji.

Ya ce toh ina expecting
Na bugo ne dama na sanar da ke cewa munyi landing yau,kuma na sauka a kauyenmu aiki Alhamdulillah ya yi kyau saura na uku da za'a gabatar wanda shine final daga shi idan Allaah ya taimakeni zan iya fara takawa da kafata.
Cikin murna na ce,well come on board my hubby gaskiya na tayaka murna abin sona Allaah yasa Wanda za'a kuma yi,ayi a sa'a.

Ya ce Ameen my wify bara na barki ki huta Good bye take care.na ce toh bye bye sannan muka katse wayar.......








_ignore any typing errors_





*vote comment and share*


⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐


*WACECE NI*




✍🏼by

*Fateema Muhammad Suleiman*
Email [email protected]
Wattad teemacool2020



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is ton entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*page* 4⃣4⃣&4⃣5⃣




*wannan page nakune masoyan wacece ni musamman masu yimun comment _zaratun_ tana godiya da kulawarku*



Best Line

“Keep in company of people of virtue; you will become one of them. Keep aloof from people of vice; you will remain safe from them.”
Remove your gaze from the splendor of the World. Do not let the love of this World enter your heart. Beware! The love of this World does not perhaps destroy you, just as it had destroyed previous nations.

(H) *Umar Bin Khatab* ( r.a )




Ina zaune a bakin gadon gaba daya asibitin gundireni, yau wata daya da sati daya kenan. tsananin mamaki da al'ajabi nake rayuwar duniyar kenan,Allaah kuma mai iko ne sannan shi mai yawan hikimane da jujjuya lamuransa yadda yaso waye zai kawo a ka cewa ni ce sanadin tona asirin wanda ya kashe kakana, tun kafin asan da zuwana duniyar? sai da na tiriyo dukkan abubuwan da suka wuce masu ban mamaki sannan na nisa na fada a fili cewa lallai Allaah mabuwayine gagara misali.sallamar da akayi ne ya dawo da ni daga tunanin da nake Dr zayd ne yashigo fuskarshi dauke da Fara'a.na amsa mashi sallamar cikin sakin fuska,ya shigo sai da ya zauna a kujerar da ke dab da gadon sannan ya ce your Excellency,ya dai duk tafiyar ce kike zaune a daburce haka?

Na rausayar da idanuna sannan na lumshesu na bude dama idanun nawa yanayinsu kamar mai jin baccine,na ce wallahi kuwa, duk na kagu ingani a gida gaba daya zaman asubitin ya gundireni,

Sai da ya gama karemun kallo sosai sannan ya yi murmushi ya ce mu kuma gashi bamu gaji da ke ba,saboda ke yanzu fitila ce ga wannan asibitin kin zama sarauniyarmu,saura kiris ki dane kujerar mulkinki ya karasa yana dariyarshi mai ban sha'awa Masha Allaah shima bashi da makusa kib kib da shi.

Na waro ido cikin mamaki, na ce nidince sarauniya? lallai ko da anga mulki.

Ya ce aiko kin tara kin samu domin mulki kam sanya a ranki kamar kinyi ne sai dai kiyi ta shan kamshinki,mu kuma muna tayaki.

Na ce toh Allaah ya bamu dukkaninmu
Ya ce Aameen.

kusan minti uku babu Wanda yakuma cewa komai sai can ya nisa sannan ya kira sunana da wata siga da bantaba jin ya yi irin ta ba.

Na dago idona sai kuma nayi saurin sadda kaina kasa ganin yanda ya kuramun manyan idanunshi masu matukar shiga rai gaskiya na kasa juriyar ganin idanun nashi.

Sai yayi saurin cewa ki dago idanunki ki kalleni maganar da zan maki mai mahimmanci ne inason ki fahimce sosai
Da hankali na juyo da fuska ina kuma fuskantarshi ido cikin ido.
Ya gyara zamanshi ya jingina bayanshi jikin kujerar sosai,fusjarshi kuma ba yabo babu fallasa cikin dakewa ya ce your excellent,

Tun kafin ya cigaba da maganarshi na katseshi da cewa haba Dr,wani irin nadi ne kukeson dangantani da shi?
ina fahimtarku tun jiya kuke dangantani da wani excellency,ina murmushin yadda yayi kasake yana kallon lebuna na,kamar yau ya fara ganinsu.
sai na ce zanfi jin dadi da kirana zaratun

Sai da ya sauke numfashi sannan ya ce haba wannan sarauta fa Allaah ne ya baki ba mu ba saboda haka dole kin amshi abin ki kawai,yanzu ma na zo da kokon barata ne bazan boye maki da gaskiya zuciya ta takamu da sonki wanda ina ganin idan bata sameki ba zata iya fadawa cikin wata matsalar duk da nasan akwai masu sonki ba sai kin fadamun ba amma nima inaso ki sanyani cikin masoyan naki tunda ance allura cikin ruwa mai rabo kan dauka.

Duk wannan magana yanayin sune cikin kuramun idanuwanshi.

sai da na nisa kamar bazanyi magana ba saboda na fada wata tunani wato su maza dama haka suke basu da kunyar furtawa mace so?dama nasan arina tunda na farfado daga gigin alluran anesthesia naga yadda yake zumudi da saurin at the end of day, abin da yake harin kenan.

zuciya ta kuma sai dukan uku uku take tunda ya furtamun yana so na toh ni meyema zance mashi gaba daya rasa amsar da zan bashi nayi.

Ganin da yayi bani niyar bashi amsa sai ya sauko har kasa yayi kneel down da gwiwowinshi cikin roko ya ce please answer me

Sai da nagama karemashi kallo, yana da qualities din da ko wacce mace za ta so ta mallakeshi a matsayin miji,amma ni nawa case dabanne,take jarumtakar yin magana tafadomun na runtse idanuna sannan na ce gaskiya Dr kafi karfin neman abu awajena Wanda zan iya hana makashi, sannan kai kana da duk wata qualities da namiji zaiyi gadara da shi,idan na ce zan tsaya yi maka godiyane bisa taimakona wallahi I don't have anything similar to upper you, compare to what you did to me....sannan bani da kalma da zanyi amfani da ita wajen gode maka.
Kai ne ka ceci rayuwa a lokacin da nake dab da stage na za ta kubucemun.,amma kamar yadda ka ce allura cikin ruwa mai rabo kan dauka yanzu ni bani da zabi sai wanda Allaah yayi coz you guy really throw me into something,with your beautiful heart and amazing care and loving...

Sai da yaga nayi shiru da maganar ya mike tsaye fuskarshi dauke da murmushin farin cikin magangaguna.

Sai ya ce toh nagode my sweetheart, Ku zauna cikin shirin yanzu Dr on duty zai bada sallamarku.
Haba tun kafin yakarasa maganarshi nashiga yin murna har da dan mikewata na fara hada kayan abincin da ke kan table.
Kasake ya ja ya tsaya, ya ce lallai kam wannan duk murnar tafiya gidane? toh can dinma zamu dinga binki ne yarinya,nayi murmushi da jin maganarshi.bayan ya fita na dauko wayata number Humaira na kira na sanar da ita shirin sallamarmu.
Sannan na rubuta sako na turawa yusuf da Khalid kalmomin da sakon yakunsa duk iri daya.
Ga abin da na ce

My hubby mun samu sallama yanzu Uncle Mustapha zai wuce da mu gida.idan na koma gida zamuyi waya.....

Kusan lokaci daya amsar sakonnin suka shigo.Tayani murna yusuf yayi sannan ya ce nayi kyawarki my wify ki kulamun da kanki sai kinji ni a waya....
Shina Khalid abin da ya ce kenan sai dai ya kara sa cewa shima zai zo har gidan gobe in sha Allaah.

Alhamdulillah na warke sumul Dr on duties ne ya yi discharge dinmu, bayan ya tabbatar da komai normal,munyi murna sosai Humaira ce ta tattara mana dukkan kayayyakinmu,uncle Mustapha ya yi dropping namu zuwa gida. bayan mun sanar da su daddy zuwanmu.sai gashi munzo gidan kamar yau ne naje makaranta,saboda lectures da muke having on and off, ya sanya bana samun zuwa gidan.
to gashi yau sanadiyar kaddarar da ta sameni, da badan ikon Allaah ba yanzu sai dai wani labarin.
na yi kuka har na gode Allaah da rasa Arrauda kawata ce na kut da kut bana boye mata komai saboda tamu tazo daya Allaah ya jikanki azizati.
na goge hawayen da suka fara zubomun,daga lumsassun idanuna.

Kanina yusuf ne ya shigo dakin,hannunshi dauke da flask na shayi da kofuna.sai da ya zauna, sannan ya ce, haba sister kidaina sanya damuwa cikin ranki mana komai yawuce ai, su mummy bazasu so ganinki cikin damuwa ba. please kiyi hakuri ga shayin kisha sannan ki fito parlor cikin mutane zaman kadai ke sanya mutum cikin tunani.

Gyada mashi kai nayi sannan na tsiyaya shayin cikin mug kamshin shayin ne yabugi hancina,nasha shi sosai kuwa don ni shayi yana daga cikin favorite dina.



***************





Yau juma'a kwana na shida kenan da sallama daga asibiti,shirin komawa makaranta nake saboda dab muke da mufara jarrabawa.Allaah ya taimakeni duk Assignment da ake badawa sauran colleague dina ke yimun shi,sai karatun ma suna turomun duk lecture da aka gabatar ina karantawa through waya.
Gidan yau full House ne,saboda dukkanmu muna gida Auntie Maryam ce ke bamu labarin wahalan da project supervisor ta ya bata,da yadda ta lallabashi har yagama tama duk abinda take bukata daga gareshi,sai ga su Latifa da tawagar friends dina sun kawomun ziyara haka muka yini cikin farin ciki da walwala duk dauniyar girki kuwa Humaira ce ke yi.saboda gaskiya daga ni har Humaira yin girki baya bamu wahala don mun saba tun muna yara tarbiyar mummy kenan.mun taso dashi ajikinmu girki kam babu irin wanda bamu iya ba.mun zama professional coolers..
Sai kusan magriba suka kama hanyar gidajensu saboda train sukabi sai da muka ga tashinsu sannan muka koma gida..

Cikin wadannan kwanakin kuma Khalid zuwanshi sau uku kenan kuma har cikin parlor yake shigowa ayi hira da shi kamar dan gida,sai zayd da yazo sau daya saboda shi bashi da ishashshan lokacin kansa kullum suna asibiti...soyayya santsa suke nunamun wadannan zaratan samarin Wanda har na kasa sanin waye acikinsu yafi kaunata?
Ga yusuf kuma a gefe da yake rikitamun zuciya da tsantsar sonshi da rurutashi I don't know why this love duk da bajintarsu da kulawarsu sun kasa cire yusuf a cikin zuciyata kullum gani nake kamar son yusuf din Kara karuwa take a zuciyata...idan na dubu kudaden da suke cikin account dina sai na ce meye amfaninsu kawai na dauka na bayar asake yiwa yusuf aiki cikin gaggawa,na fison ya warke sannan na gabatar da shi ga iyayena saboda yanzu su suna kallon cikin Khalid da zayd dole zan zabi dayansu.toh bani da kwarin gwiwar nuna yusuf a halin yanzu duk da zuciyata shi take so amma nasan su mummy ba za taba yarda da shi a halin yanzu ba.duk wata shawarar da na kulla sai ta warware na kasa yadda zan bullowa lamarin.kullum dare kuma sai munsha hirarmu na soyayya da Yusuf.duk wata hira da mutum zaiyimun idan ko ba Yusuf ba,
lami nake jinshi....

A daddafe na koma school badan ina so ba sai dai babu yadda na iya.Daddy da kanshi ne yakawo har gidansu latifa saboda fafur sukaki yarda na kuma zama a wancen gidan ,yahadu da kuma auntie Maryam ta kusan gama karatunta itama ta koma gidanmu da zama lokaci lokaci suke zuwa wajen supervisor su contact dinsu da makaranta ya ragu.Faruwar wannan lamarin ne muka gane mahaifin Latifa abokin daddy ne school mate nashi.yanzu kuma yake lecturing a makarantarmu.gidan dai dai ginin turawa komai yaji,dakin Latifan nayi parking kayana.bansamu wata matsala da gidan ba,saboda zamane da ake gudanar da shi cikin tsari.



Da misalin karfe goma duk muna parlor kowa ya baza takardunshi muna karatu nikam assignment dina nake sai kanin latifa guda biyu Abyan da Abyad twins ne shekarunsu kusan goma sha daya identical da su, kyakyawa masu ban sha'awa.sai latifa da ke kallonta.sai da na gama duk abin da zanyi sannan na mike na ce dear felling sleepy,ta dago kai ta dubeni sannan ta ce OK nikam sai nagama kallon wannan show before nayi joining naki,ga wannan ki shigomun da shi daki.bayan na karbi takardar da take mikamun.bacci ne yake so yaci karfina adaddafe nashigo dakin himar din dake saman rigar baccina na cire sannan na gabatar da addu'o'in bacci na kwanta.

Can cikin bacci na farajin karar wayata na dauko ta ko duba sunan wanda yakira banyi ba kawai na kara a kunnena.muryar Yusuf dinne kamar yadda nake zato,cikin muryar bacci nake amsa mashi maganganunda yakeyi.da kanshi yagane ina cikin magagin bacci ya danyi dariya har inajin muryarshi ya ce my wify wane irin baccine ke damunki yau?ki tashi ki wanke fuskarki ina son jin cikekken labarin da Kika ce zaki bani....
Na dan zunguro bakina kamar yana kallona na ce uhm uhm ni ka kyaleni bacci nake ji sai gobe.

Yusuf mutum ne Wanda yasan yadda zai tafiyantar mace har ya mantar da ita dukkanin tunaninta.

Shima sai yayi irin muryata cikin shagwaba ya ce naki wayon yanzu nakeson ji.

Da kaina na watstsake na shiga bashi labari tiryan tiryan kamar yadda mummy ta sanarda ni banboye mashi komai ba tsawon lokaci yana saurara na,sai dai naji yana jan numfashi.

sai da na zo dai dai yadda aka sameni har zuwa haihuwata sai kuka yaci karfina har da shishshika,shiga lallai shina yake,kamar karamar yarinya. shish shish,shikenan kiyi shiru ya isa haka.sorry my wify,gaskiya I felled your story is so touching.

Sai da yaga na yi shiru da kukan da nake yafara magana cikin tattausar muryarshi daga ji labarin da na bashi ya girgiza shi,ya ce,hakika my wify naji labarinki,amma wannan ba wani abin da zaisa ki tayar da hankalinki ba kada ki samu damuwa nidinnan zan zame maki garkuwa bazan taba guje maki ba duk rintsi duk wahala zan kasance tare da ke, amma kiyimun alkawari duk halin da Kika gani tattare da ni zaki dau hakuri domin akwai abubuwa masu matukar sarkakiyan da zaki fuskanta gareni, toh idan lokacin yayi, ki kasance mai juriya da kau da kai. toh na tabbatar maki cewa gaba kadan zaki samu farin cikin hakurinki.,saura kiris ya rage na baki cikekken tarihina,wannan labarin da zan baki shi sai naga nafara takawa da kafata ina tafiya,amma wani hanzari ba gudu ba idan aka kuma yin aikin ba'asamu nasara ba shikenan fa bani ba taka kasa toh idan hakan ta kasance zaki yarda ki aureni?

Gaskiya tambayar ta girgiza ni, idan ni na yarda to su mummy fa ga matsalar Khalid da zayd a gefe...wadannan abubuwan duk suna bukatar amsa.kuma bani da amsarsu .
Kinyi shiru fa ya jefomun tambaya?

kawai na tsinci kaina da cewa yusuf zan kasance tare da kai a duk halin da kake ciki amma daga ni har kai dole mukai zukantanmu nesa saboda akwai matsaloli da zamu fuskanta.....

Ya ce nasani my wify ,kina tsoron iyayenki ne akan bazasu yarda su aura maki masaki mara kafa ba....

Na nisa, bankuma cewa komai ba, gaba daya nashiga cikin tunanin yadda zamu bullowa Lamain......

Kusan minti biyar babu wanda ya yi magana na dauka ma ya katse wayar, sai da naji ya ja numfashi, na gane yana kan wayar. daga bisani ya yimun sallama tare da cewa my wify ki koma baccinki in sha Allaah,
Allaah zai kawo mana mafita good night..

Nima na mayar mashi martani da good night too bye.....




_masoyan yusuf next page zakusan waye yusuf😜_








*wayan comment yawan typing please kuyimun share,vote* _teemacool2020_ _wattpad_



⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐


*WACECE NI*




✍🏼by

*Fateema Muhammad Suleiman*
Email [email protected]
Wattad teemacool2020



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is ton entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*page* 4⃣6⃣&4⃣7⃣






*DAILY DAHWA*
[14, ROBIU THANI 1441]

```Allaah is sufficient for us, Truth are the words Allaah ﷻ`

*QURAN*
*Therefore remember Me, I will remember you. Give thanks to Me, and reject not Me* (2:152)

*HADITH*
Umar ibn. Khattab (رضي الله عنه) asked " Messenger of Allah what kind of wealth should we acquire?" The Prophet (ﷺ) replied: *Let one of you acquire a thankful heart.A tongue that remembers Allah.A believing wife who will help him with regard to the Hereafter*
-(Ibn Majah)

*DUA*
Oh Allah (جل جلاله) *You know my situations better than I do, please forgive me and grant me what is best for me*

*AAMIIN*



Ana kiraye kirayen asatu na farka da sauri na sauko daga kan gadon,saboda banason nayi latti ina da lecture 7am.komai cikin sauri nayishi cup daya ba tea na sha sannan na kama hanyar makaranta cikin sauri nake driving saboda na fara hawa motar da Khalid ya bani bayan samun umarni daga daddy.da farko bai yarda ba,sai bayan faruwar al'amarin da ya yaba da Khalid din,da yanzu suka zama kamar da da mahaifi saboda shakuwa.

Mun fito daga lecture kenan sai ga khalid,cikin murmushi yake gaba toni idonshi sanye da bakin space shigan kananan kaya yayi,sun mashi kyau sosai.

Tashi nayi daga wajen da nake na zo kusa da shi ganin bashi da niyar zuwa dai dai wajen da nake zaune cikin colleagues dina yawancinsu kuma maza ne yayi kicin kicin da ido wai shi yana kishin ganin muna zama acikin maza,yana kuma yimun kashedin hakan a koda yaushe cikin zuciyata kuwa cewa take kajimun mutum fa kai ba aure kake ba amma kana tsaramun yanda zan gudanar da rayuwata duk da nasan kaina ba kula wasu samari nake ba wadannan kam yawancinsu ma age mates dinane,sannan kuma abikanan karatuna ne so what is wrong da har zai dinga takuramun.

Kamar yasan abinda nake fada azuciyata,sai ya yi murmushi ya ce,yes gaskiya na ne dole nayi kishin ki,ni da son samune ma babu wanda zan yarda ko kallo ya yi maki ,bazaki sani bane,amma duk lokacin da na samu sa'ar aura Mani ke zaki ga real love nake maki.don Allah ji bani chance na turo maganata na wallahi ina cikin matsala fa yarinya ki tausayamun tun da su daddy kam nasan basu da wata matsala akai.

Sai da naga yayi shiru,sannan na dago kaina sosai na kuma kare mashi kallo shima kuma kallon nawa yake,sai ya ciro space din dake sanya akan idonshi ya ce ki dubi idanuna tsantsar sonki da son kasance tare da ke acikinsu.

Sai da na dube idanun nashi sun rine sunyi jajir,tsananin so na ne shimfide acikinsu,nifa gaba daya wadannan guys din sun jefani cikin tsaka mai wuya,wannan irin yanayi fa gaskiya ko a exams ne aka baka karubuta assay akanshi to ba karamin matsala bane zaka sha na fiddoda hakikanin amsar da zai gamsar da malaminka, to ni kuma gashi practically ina fuskantarshi.bangama wattsake daga maganar yusuf ba,sai ga na Khalid .a gefe daya kuma Dr zayd da shi ko sauraron maganata bayayi idan na ce ya yi hakuri ya bani lokaci sai fura wutar cewa cikin satinnan zai gabatar da magabatanshi,saboda yafara tsorota da ni kar yayi sanya akasashi.cikin zuciyata kuma duk ba ta su nake ba.ina son ganin yusuf dina yasamu lafiya naji dadin gabatar dashi da hujjar cewa,shine farkon wanda yafara furta yana sona kafinsu.
Sai da na sauke kallona daga kanshi sannan cikin sanyin murya na ce,
Khalid kamar kullum babu abin da zan iya cewa sai dai kayi hakuri,ka bani dan lokaci kadan kamar yadda kasani tun farko na fada maka akwai Wanda muke fita dashi to bashi da lafiya ne,ina tsoron kar ya zargeni da na yaudareshi idan yaji maganar ka agidanmu,dama inason na lallabashi ne har ya hakura da ni, sai na baka damar katuro nagabatan naka.tsawon lokaci yakuramun idanunshi,gani yake kamar ya daukeni ya hadiye..

Sai yadan nisa yaja dogon numfashi ya ce,
Gaskiya yarinya na fara tsorota da wannan man da kike magana akanshi wane irin so ne kike mashi haka?
A sanina fa duk wannan jinyar da kika sha banganshi ya zo wajenki ko sau daya ba,amma ki duba ni akanki wallahi da zan fada maki irin abubuwan da na fuskanta zaki daura hannu aka kiyi ta iho amma duk na share na mantasu saboda ina ganin wata kila zan iya samun wani gurbi daga zuciyarki .amma kuma abin da na fuskanta zuciyarki ko gizau batayi ba wajen sona.ki duba ki gani fa cewa kike bakyason ya zargeki da yaudara ni kuwa oho. kenan baki damu da halin da zan shiga ba...sai da ya girgiza kai ya fada a fili this love,u can't escape for fate....

Kasa bashi amsa nayi ganin yadda zuciyarshi ta baci banta ba ganin Khalid ya shiga cikin irin wannan hali ba gaba daya ya canjamun.sai kawai nayi shiru ina kallonshi har ya dan sauko daga fushin da yake.

Da kanshi yadan murmusa ganin yadda nayi kicin kicin da ni kamar mai son yin kuka,Allaah yayine mai jin tausayin mutum da karaya a duk lokacin da naga abin tausayi bana iyayin resisting hawayena,sanadin wannan tausayin ne ya jefani cikin wannan tsaka mai wuya,ko kadan bani da jarumtar fadawa duk Wanda ya ce,yana sona bana sonshi,sai dai nayi ta yi maka kame kame da hanya hanya,har mutum ya gane da kansa ya fita hanyata.shi kuma Khalid ya katse ya tsare har muka shaku da shi har zuwa wannan lokacin.

Nima na saki raina muka ci gabada hirarmu cikin kwanciyar hankali,sai da yaga lokacin lecture mu yagabato ya yimun sallama tare da jaddamun cewa sati biyu ya bani,idan suka cika to ba makawa cewa kawo iyayenshi wurin daddy su gama maganar aure har da cewa,na gaji da ciwon mara nan yarinya kisan yadda zakiyi da ni.....sai kawai

Please Login or Register in order to submit comment