Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsarkakku,ina rokonka roko irin na miskinai,kada ka kama ni da laifin da na yi cikin rashin sani, ga wannan kyauta da ka yi mun ka shiryar da ita zuwa ga tafarkinka madaidaici da bin sunnar annabinka Muhammad sallallahu alaihi wasallam,sannan ta yi ma ta huduba.

*Hajja fanna* ta karbi baby kowa da ya ke wurin sai da ya karbeta su ka dinga sanya ma ta albarkacin bakinsu .

haka gari ya waye aka sallame su, su ka dawo gida kowa ya na farin cikin *Aazeen* ta sauka lafiya. Sun bi sunnah a ranar Mr suhaib ya radawa yarinyar sunan sayyada Fatimatu zahra diyar ma'aiki sallallahu alaihi wasallam.
*vaishal* ta daga ta sama ta ce Allaah ka raya ma na *zaratun*
flash back asalin yanda labarin ya faro kenan......
idan kun tuna,tube number 489 da *zaratun* ta ke neman bearer din wato asalin babanta kenan muje zuwa dai, ga yusuf a gefe daya da auntie maryam......







*share*
*comments*

⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐


*WACECE NI*




✍🏼by

*Fateema Muhammad Suleiman*
Email [email protected]
Wattad teemacool2020



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is ton entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation



*Fans kuyi hakuri da rashin ganin rubuta na akan lokaci hakan ya samo asali ne bisa zazzabi da nasha fama cikin kwanakin nan nayi matukar farin cikin ganin add u'o'inku kuma nagode sosai da sosai Allah yabar zumunci*



*page* 1⃣7⃣&1⃣8⃣


Hmmm su Aazeen da baby haka ta rungumi diyarta a kirji tsananin so ne fal cikin ranta soyayyar 'ya da mahaifiya kenan satin su biyu da haihuwa jikin yanzu normal toh sun fara shirye shiryen barin kasar...

Yau sunje follow up wajen Dr Hamid mutumin Nigeria ne amma haifeffen garin Birmingham aiki ya kaishi san Francisco, kasancewarshi kwararren likitan mata gynecologist...shi ne kuma ya yi conducting ceaserian sectioning...tun kuma a lokacin ya ji son Aazeen din ta sirgo cikin zuciyarshi..ya yi ma zuciyar tashi alkawarin furta ma ta son ta idan ta zo next visit dinta kafin su bar kasar.
Sai ga shi yau da baby ta zaratun yarinya bum bul kyakkyawa Mai shiga rai.
Haka yagama musu duk abubuwanda suke bukata sannan ya karbeta ya sanyata bisa kafadarshi.Aazeen da tun farko ta sargo da kwallon kurilla da yake ma ta ,tadai sunkuyar da kanta kasa ta na wasa da 'yan yatsunta na hannun dama ya yinda ya Kira sunanta cikin wata siga da ba ta taba jin wani mahaluki ya kira sunanta ba.domin dukkan tsigan jikinta ya amsa da kiran.
A hankali ta amsa ba tare da ta dago kanta ba. gaskiya tana ganin girmanshi saboda a takaice zai kai shekaru arbain senior bachelor ne amma bai taba aure ba.

Ya ce,Aazeen so nake ki dago kai sosai ki dubani maganan da zan maki mai muhummanci a garemu.kinga ke yarinya ce naso nafara tunkarar iyayenki kafin in maki magana but na danyi tunanin hakan kamar tauyemaki hakkine,I just make my mind to express my feeling about you duk da ke yarinya ce ina sonki kuma da aure.kinga idan ki ka aure ni zaratun ba za ta tashi da bakin cikin rashin mahaifi ba...na baki lokaci daga yanzu zuwa gobe na ke son jin amsa don bana so yadauki dogon lokaci,nima ina son ganin mace kusa da ni kuma nima ina son zama baba tunda ga yaran cikina ma anzama mama yana referring ita kenan da kayataccen murmushi yakarasa magananshi....
Ya mike da zaratun a hannunshi ya ce, muje in sauke ku ba sai kin kira driver ba.

Ta mike biye da bayanshi har suka isa car park din dai dai gunda an rubuta Dr Hamid zaibaddeen shi da kanshi ya bude mata motor,kusan tare suka shiga ya yi wa motor key suka bar harabar hospital din.ya na dan taba ta da hira jifi jifi take maido mashi amsa har suka iso gida...

Ta yi mishi godeya sannan ta fito tallefe da zaratun,ya ce take care sai naji amsar ki..
Ta dan lumshe ido ta dubashi ido cikin ido bakinta dauke da murmushi har dimple dinta sun lutsa ciki ta ce toh thanks safe journey.

Ta shiga gida tana ta jujjuya maganganunshi cikin ranta.babu (owa gidan duk sunje shopping shiri suke sosai domin basu da isheshshen lokaci ta shimfida zaratun da har yanzu ke bacci acikin baby bed dinta sannan ta sauya kayan jikinta zuwa na zaman gida,ta kwanta akan tree sitter kiran vaishali ta shiga yi ringing na biyu sai ta daga sai ta ce habibty kina part dinku ne ko kema kintafi shopping din?
Ta ce yes ina nan ba inda naje kin dawone?
Ta ce eh kisameni yanzu.

Da sauri ta sanya takalminta sai r&s gyale da ta yafa ajikinta cikin sallama ta shigo falon tare da fadin barka da dawowa dear hope lafiya kira cikin gaggawa haka?
Ta ce ba lafiya ba habibty neman shawara ne kiji Dr Hamid fa he is madly in love with me kuma serious relationship that lead to marriage ya Kika ce Anya zan iya aure at this situation da nake ciki?

Tsawon lokaci vaishali tana juya zancen sannan ta yi dogon nazari vaishali yarinya ce amma akwai dogon tunani wat a shawarar idan ta yanta ba za ka tabacewa ita tayishi ba akwai tunani sosai shi yasanya Aazeen ba ta taba yanke hukunci ba tare da ta shawarce ta ba.

Ta nisa! ta ce shawarar da Zan bayar kawai ki amince ko dan wannan cheeks din ta nuna zaratun tana murmushi.
Kinga nima David oh! Na manta yanzu dai ya ce, na dinga kiranshi da Muhammad Al'ameen.
Ya dage shifa aure ya ke so kuma baya son daukan dogon lokaci kinga mu amince kawai mu aure su hakan zai bamu daman sake zama cikin gari daya ko kuma country daya ba za mudai yi nisa badai still we are together for good


Aazeen ta ja dogon numfashi ta ce to dear bari mummy ta dawo ko za ta amince kuma Ina fatan hakan Allah ya zabar mana mafi alkhairi.


Vaishali ta ce Ameen.


Haka suka ci gaba da tattaunawa har lokacin sallar azahar ta yi.sai da vaishali ta idarda sallah sannan ta jara musu abinci bisa dinning suna cikin ci sai ga su mummy sun dawo da niki Niki sayayya ne masu matukar yawa.
Ita ma riskesu zuwa dinning din vaishali ta yi saving dinta sauran kuma duk suka wuce yin harkokinsu bayan sun daga masu hannu su ma suka yi masu sannu da dawowa.

Mummy ta ce sannu diyata kindawo taya'yaruwarki ko? Kai Allah ya kuma Kara hada kawunanku..a tare suka hada bakin fadin Aameen.

Shiru kowa Yana cin abincinshi sai vaishali ta katse shirun da cewa mummy Dr Hamid ne ya maido Aazeen gida Ku ma ya bata assignment wai sonta ya ke yi da aure ya so ya tunkareku tun farko anan ta tsakaita da magananta.ta na kuma jin shakkar abinda mummy za ta ce!


Murmushi ta yi Mai kayatarwa sannan ta ce Ku dai kuce kawai daga ke har 'yar uwar taki so ku ke Ku sake samu yin kyawarku wanda har zaifi na da tunda wannan na zaman aure ne na din din din.to sai dai anyi shawara da iyayenta idan har sun amince anyi bincike akanshi toh mace dama ai ba ta da gari.

vaishali ta yi musu sallama ta ce sai dare za ta kuma dawowa.

Da daddare misalin karfe goma saiga Kira a wayarta bakon number ne tayi ringing har ta tsinke taki dagawa saboda dama ita ba maison damuwa bane sai kira aka kuma yi kusan za ta tsinke sannan ta daga amma sai tayi shiru a wancen bangaren.

Ya ce princess bakya daga layin da baki sani ba ko? To Hameed ne, how was your day?

Sai a sannan ne, ta gane muryarshi.cikin sanyin murya ta ce Alhamdulillah n urs?

Ya ce,boring duk cikin tunaninki na yini.na kasa jiran ki zuwa safe don Allah naji mai kyau can't wait to see you at my side I love you and I also do love you with all my heart please ki ce mun wani abu wanda Zan kwanta Ina jinshi cikin raina.

Ta yi shiru ita dai har ga Allah ta na sonshi amma kuma tana jin nawunshi sosai, saboda gaskiya wannan shi ne first love dinta duk sauran samari da suka dinga yi mata caa ba ta taba kula su ba,saboda bata yardada su ba,cewar ta duk bad boys ne.to ga Hameed kuma serious and responsible man cos he is man enough.ta ce gobe in aha Allah zan baka amsa.
Ya ce,nasani ina neman sweet ward ne for now.

Batasan maye za ta ce ba ita kam,ta yi shiru.

Ya ce,kinyi shiru koh sarkin kunya kada ki damu zan cire maki wannan kunya nan bada dadewa ba idan nayi sa'a ammallakamun ke.

Ya jita tana murmushi kasa kasa,sannan ta ce okay ahankali hakan ba karamin ji ya yi ajikinshi ba, saboda ta fadane with her soft and husky voice dinta.

Ya ce seriously zaki gane hakan soon yanzu dai ina baby na take? hope kin bata abinci kafin ta kwanta?

Cikin ranta ta ce jimun mutum sai da kagama shagalinka za ka tuno ta hmm! ta juyo ta duba baby bed din lub zaratun tana ta barci ta ce eeh gashi tana bacci lafiyanta.

Ya ce,gud haka ya yi kyau good night take care.

Itama ta maida mashi da good night too have a nice dream.

Ya ce,okay dream of you koh?

Ta ce,yes ita dai kawai so take ya rabu da ita tayi bacci don bata saba kaiwa har warhaka ba batayi bacci ba.

Sai ya ce, me too ina son ayi mafarkina gobe kuma zan tanbaya akai sai da safe sannan ya kashe wayar.

Ta ja dogon numfashi ta lumshe ido tana imagining dinshi cikin ranta a haka har bacci barawo ya yi awun gabada ita........







*please share and comment*

⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐


*WACECE NI*




✍🏼by

*Fateema Muhammad Suleiman*
Email [email protected]
Wattad teemacool2020



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is ton entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*page* 1⃣9⃣&2⃣0⃣


Komai ya yi farko dole ya yi karshe yau rana ce da su Aazeen za su yi bankwana da san Francisco zuwa kasar su na gado.Aazeen da vaishali kan kuka ba'a magana.sunyi kuka har sun gode Allaah,saboda rabuwa aminiya abokiyar shawara da tsananin shakuwa, har iyayen na su sai da suka sanya a kuka.rabuwa ne da basu da tabbacin sake haduwa idan ba ikon Allaah ba.dukkansu suna airport ko wannensu kuma yana jiran tashin jirgin kasarshi ne, David (Mohd Ameen) da Dr Hameed ma suna tare da su,shi dai muhd Ameen ya samu karbuwa Dari bisa dari daga wurin Mr suhaib kuma anyi alkawarin Sanya ranar aure da zarar sun je Pakistan.duk da shima Hameed din sunyi zai je Nigeria domin neman auren Aazeen din.haka suka yi kusan awa daya, kafin jirginsu ya daga bankwana da masoyi ba Abu ne mai sauki ba sai dai hakuri tunda ya za ma dole hakan za ta faru.Dr Hameed ne ya matso kusa Aazeen sannan ya sanya zobe a hannun ta.ya ce,
All my life I have searched but never found someone like you,who is so perfect for me. With you I do not need to worry about the future.I love you with all my heart I promise to give you my endless love,in sha Allaah ina nan tafe zuwa gare ki,ki rikemun soyayyata da zarar na je kasar ku,zan yi duk iyakan kokarina dan ganin na mallakeki in sha Allaah sai da igiyar aure zamu dawo zuwa wannan kasa.kada kusamu damuwa keda vaishali kam mutu karaba ne.....hawaye shar daga idanunta ta ce in sha Allaah na yi maka alkawarin duk rintsi duk wuya ina tare da kai,wannan alkawarine,take note.

Ya ce nagode meye za kiyimun Wanda zan dinga tunawa da ke kafin nazo Nigeria?

Ta ce bear in your mind I am yours and promise to be yours forever I love you so much..sannan ta Mika mashi zoben da ke hannunta na azurfa.

Ya ce nagode da wannan kyauta bazan ta ba manta shi ba. da yake yatsunta sirarane,sai ya sanya a dan karamin yatsanshi.ya yi kissing zoben sannan ya yi blowing iska zuwa gare ta nuna alamun ya gamsu da kyautar da ta mishi.

ita ma ta yi murmushi sannan ta jinjina kai ta furta ahankali I am gonna miss you for a while.....

Ya ce, its just for few days ne da zarar na kammala abubuwanda nakeyi za ki ganni....haka har ta hau matalar jirgin su na dagawa juna hannu har suka daina kallon junansu.
Ta bangaren vaishali ma hakanne ya kasance.

Sun yi landing a Nigeria misalin karfe biyu na yamma saboda sai da suka kwana a France sannan da safe suka kama hanyar Nigeria....daga abuja international airport sai Maiduguri international airport mutanen da suka zo tarbarsu ba abin magana bane daga familin mommy har daddy babu Wanda aka bari a baya..kowa kuma turuniyar son ganin Aazeen yake ya Anus da ta Almustapha su ne kan gaba.sai washe baki suke suna kuma mayar da gaisuwar da family friends dinsu suke musu.Aazeen kam sauran fuskokin ma ta kasa ganesu.har suka je gida zance dayan nan ne suke ta maimaitawa da ganinsu duk suna cikin farin cikin ganin gudar jininsu.kam dangi sun hallaru a wannan makeken gidan Alhaji modu,basu barsu sun huta ba sai kusan magriba kowa ya watse sai kannen Hajja Bintu da Alhaji modu da suka rage domin su kam zasu kwana a gidan domin za a gabatar da family meeting.
Gaba daya Aazeen ta zama kamar wata bakuwa a gidan nasu tun da ta shiga bedroom da zaratun bata fitoba duk kuma wadanda su ka zo yi mata maraba da zuwa sai dai su shiga su ga is he ta sannan su fito anyi anyi ta fito cikin dangi taki,sai su ka ce a bar ta yanzu tana bakuntane idan ankwan biyu za ta washe ta Saba da mutane...ya Anas ne iske ta tana ta danna wayarta,
Ya ce, sis ya dai you have to be feel free and be at home fa dan na lura baki son zama cikin mutane wanda duk wannan Jama'a saboda ke suka taru, gobe za'a gabatar da family meeting dole ki sake jikinki domin duk taruwar da za ayi saboda ke ne Ku ma ba za su ji dadi ba idan baki sake jikinki ba so be at home.

Ta ce in sha Allah zanyi yadda kake so nima gajiya ce sai kuma kasan yanzu na manta zama cikin mutane masu yawa saboda ai kaga irin environment da muka taso,so sai a hankali zan saba.

Washe gari da misalin karfe goma na safe mutane suka fara hallara, a babban dakin taron gidan Alhaji modu,Aazeen ta shirya cikin dakekkiyar sudin lace Mai duwatsu ajiki dinkin gawn har kasa sai farin takalmi flat da ta sanya a kafarta zaratun ma an shiryata cikin fararen kaya 'yar kanti kamar shigen wedding gawn gaskiya sunyi bala'in kyau kamar ka sacesu ka gudu.ta zama cikekkiyar madel lady,coz yanzu ne ta cika shekaru goma sha tara dai dai yau kuma ya dace da zagayowar ranar haihuwarta murna biyu za su gudanar kenan.

Alhaji Hamza shi ne kanin mahaifinta Wanda ke mashi kuma shi ne first in command na family din gaba daya.

Akan high table din farko Aazeen ce sai ya Almustapha da ya Anas mummy da kannenta,ta bangaren a hagu kuma Alhaji Hamza ne da kannenshi maza da mata,sauran kujeru kuma family ne manya da yara...

Barrister Mukhtar ne ya bude taro da add u'a sannan ya gabatar da makasudin wannan taro da dalilin taruwarsu.
shi ne da na farko awajen Alhaji Hamza din ya na da mata daya da yara biyu tagwaye fadil da fadila.tunda ya kella ido ya kalli Aazeen ya kudurta a ranshi ya samu second wife ko yanzu da ake wannan taro ya zuba mata idanunshi da wani irin mayetaccen kallo itama ta lurada shi sosai amma taki yarda suhada idanu da shi gaba daya a takure take da irin wannan kallon da ya dameta shi.
Muryar shi ne ya dawo da ita daga dogon tunanin da ta lula na Dr Hameed ta na tunano hirar da suka sha jiya da daddare murmushi ta fara yi kamar ya na gabanta haka take ji ajikinta.

Bayan ya yi gaisuwa sannan ya ce Ina mai farin cikin gabatar muku da baiyanar,' Yar mu kuma kanwarmu da ta bata shakaru takwas cib bata cikinmu nasan wasunku suna yara wadansunku kuma ba'ama haifesu ba, munyi bakin cikin wannan bata da tayi, ba sai na cika Ku da surutu ba kowa anan yasan irin jimami da gwagwarmayar da muka sha dan ganin an sameta amma abin yaci tura, gaskiya a wancen lokacin family mu sun shiga rudani sosai ga mutuwar jigon dangi ga batan gudar diyarshi sai abin ya za ma ba'asan da wanne za'ajiba...idan ba da taimakon Allah ba wannan baiwar Allaah nan ya nuna mummy Allah ne kadai yasan halin da za ta shi.amma tayi tawakkali ta fauwala lamuranta ga mahaliccinta sai gashi dukkan damuwarta ya za ma tarihi domin kudin shaida ne Aazeen ta dawo cikinmu cikin koshin lafiya muna godiya ga Allah bisa wannan taimakonshi da buwayarshi ya maido mana diyarmu mungode da halartar wannan taro Mai albarka.Zan so in kira daddy Hamza domin tofa albakarcin bakinshi.
Haka kowa sai ya zo ya tofa albarkacin bakinsa da taya juna farin ciki.sannan aka bukaci Aazeen da ta fito ta tofa na ta albarkacin bakinta da basu labarin gwagwarmayar da sika sha a tsawon batansu.

Ta mike cikin takunta daidai ta hau kan step din Barrister mukhtar din ne ya manna mata mic din jikin dan farin gyalen da ta yafa.sai da taga ta daidai da tsayuwarta sannan ta yi nazarin dukkan mutanen wajen,cikin korewa da salonta Mai burgewa ta fara jawabi kamar haka;

Ya 'yan uwa masu girma Ina mika dimbin gaisuwata a gareku baki daya bazan iya misalta maku irin farin cikin da nake ciki ba kasancewa tare da ku a wannan dakin taro mai albarka ba abune Mai sauki ba ace ka rasa danginka har na tsawon shekaru ba tare da ka sanya su cikin idanu ba kuma baka da tabbacin sake haduwa da su duk da shekarun kuruciyar da nake ciki nayi bakin cikin rasa mahaifi da nayi kuma ba'aje ko Ina ba sai na kina rasa dukkaninku
Fadowa hannun mutanen da muka fada wallahi nasan add u'o'inku ne Kadai ya kiyayemu ya kubutar da mu fadawa halaka.da taimakon David duk da kasancewarshi Christian amma yana da kirki sosai shi ne ya za mama jigo a rayuwa Wanda yanzu zancen da nake muku ya musulunta kuma shi ne zai auri vaishali 'Yar uwata da muka bata tare da ita.
Abubuwa sun yi mana sauki munfara tunanin samunku domin muhd Ameen Yana aiki ne a offishin harkikin waje kuma Yana kan yin bincike akanmu sai kosam cutar Cancer ta kamani Wanda farkon text da akayimun sunce chances na rayuwata shekaru biyu ne kacal.
Sanin da nayi cewa kuma ba za Ku taba cire tsammanin da ni ba kusan she Kara da wani abu ina fama da cutar kuma babu bayanin samunku ya sanya aka yimun artificial insemination ta zatona ko ni bana raye toh za Ku ga yaro ko yarinya wannan shi zai dan kwantar maku da hankali toh da taimakon Allah sai na warke daga cutar ma gaba daya ta na wannan jawabi hawaye ne ke jirara daga kuncinta sai dan tissue da take sanyawa tana gogewa da shi.
Ta dan taikaita sannan ta ci gaba da cewa yau ranar zagayowar haihuwata ce Ina mika godiya ta ga rabbi izza wal A'ala cikin hikimarshi ya kuma hada ni da Ku...
Sannan na godewa jigon dangi uncle Hamza da ya nuna namijin kokarin shi akaina gaskiya Ina alfahari da Ku sosai samun irin wannan dangi da za su tsaya maka a wannan zamani abu ne mai matukar wuya, sannan mahaifiya Ina sonki sosai da sosai Allan yaja mama ranki.nagode nagode sannan ta sauko ta zauna a ma zauninta

Sai da akayi ta rabon kyaututtuka na tsarabar da su ka so da shi.sannan
aka rufe taro kusan karfe daya da minti ishirin.
Da dare misalin karfe goma sai ga video call na Dr Hameed duk da gajiyar da take fama da shi sai da ta daga hira sosai na soyayya yake kashe ta da shi.
Shi fa ya yi missing dinta wallahi banki ace yanzu haka muna tare ba,Muna cuddling together duk gashi na gaji da kina nan za ki yi mun messaging jikina..
Ta yi murmushi sannan ta ce ni ma fa yau duk a gajiye nake, munyi family meeting bara na turo maka clip din yanzu.
Ta katse kiran ta tura mashi sannan ta kina kiranshi da ya dauka ya ce,bara nayi downloading sannan muyi magana coz na kosa da inga wannan meeting din sai da ya gama kallon clip din sannan ya kuma ki ranta ya ce lallai danginki suna sonki wannan taro haka kamar duk garinne sai dai wannan mc din banyarda da kallon da yake maki ba.wannan kallo kamar zai cinyeki toh koma meye nufinshi Ina rokon Allaah ya mana katangar karfe tsakaninmu .

Ta yi murmushi har yaji sautinshi ta ce laa cousin dina ne fa Barrister mukhtar ya na da mata ma har da yara.
Sai ya ce koma menene nikam banyar da da wannan kallon nashi ba zan kuma dauki mataki tun kafin kado yayimun kafa....

Ta ce to shikenan tunda baka yarda ba sai ka gaggauta zuwa asan abinyi haka suka yi ta hirar su na soyayya basu so su kashe wayar ba amma da yake dukkansu a gajiye suke sukayi sallama bayan ya dangara mata hot kiss sannan ya ce gudnyt sleep of me.
Ita ma,ta ce good night too sleep tied.sannan ta katse wayar saboda ta na jin bacci sosai,adduoin bacci ta yi sannan ta kwanta a hannunta na dama bata fi minti biyar da kwanciya ba bacci ya yi awon gaba da ita.......




*ga wannan comment kawai nake bukata*

⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐


*WACECE NI*




✍🏼by

*Fateema Muhammad Suleiman*
Email [email protected]
Wattad teemacool2020



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is ton entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*page* 2⃣1⃣&2⃣2⃣


*Dedicated to labarin Aazeen fans*



*Today, nurses nationwide (basic,post basic and undergraduate)begin their final qualifying examination.I wish them all,good luck and success in their chosen career......*







Da asuba bayan ta idar da sallah sai ta dauko Qur'anin ta,tafara bitar karatunta cikin suratun-nisa'i,har gari ya fara haske lokacin shuruk kenan sai da ta yi raka'a biyu na shuruk din sannan ta fito falo ta iske mummy Wanda itama ta idar da sallar kenan.
ta ce good morning mum?
Itama ta mayar mata da cewa morning dear how was your night?
ta ce Alhamdulillah sai dai zaratun ba ta barni na yi bacci sosai ba, duk tabi ta dameni da kuka har Ina son kawo maki ita, sai kuma na tuna kina cikin gajiya sosai.
Mummy ta yi murmushi ta ce bakunta takeyi canjin yanayin waje kuma itama ta gaji da daukanta ai,yanzu ta na bacci kenan?
ta ce eh.
Sannan ta zauna akan tree sitter ta shiga danna wayarta.number vaishali ta kira bugu na farko ta daga cikin fadin habibty na yakike ya yau duk na yi missing dinki fa?

A wancen bangaren ta amsa da cewa ya Azizati wallahi baki kaini missing dinku ba duk na yi missing na Ku da zaratun gabadaya na kasa sukuni duk a takure nake wallahi bansan haka sabo yake ba sai da muka rabu duk da na koma cikin dangi na, amma Sam rashinki daban ne ya mutuminki ko danginki sun amshi maganarshi?

Aazeen ta dan nisa sannan ta ce,A'a tukunna jiya dai munyi family meeting amma duk zancen akan murnar samummu ne toh next week meeting za mu kawo maganar shi sannan shima muna expecting nashi within that time.
to ya naki da David oh! Na manta muhd Ameen?
ta danyi murmushi har sai da ta ji sautin a cikin wayar ta ce komai normal,muna jiran zuwan danginshi ne kuma sun yi alkawarin cikin wannan satin za su dau hanya.
Aazeen ta ce toh Allaah ya kaisu lafiya ya tabbatar mana mafi alkhairi.
Vaishali ta ce Aameen.
sannan ta Katse wayar.
Sannan ta koma bedroom ta shiga bathroom domin yin wanka har zuwa wannan lokacin kuma zaratun ta na ta sharar bacci.




******************



A gurguje

Please Login or Register in order to submit comment