Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

biyu kafin mu katse wayar sosai munyi missing din juna.







********************


Months later



Mun zama cikakkun 'yan jami'a amma sai muka samu ma banbancin university ni da Humaira
Ni na samu admission ne a Edward Bio medical laboratory scientist (BMLS)
ita kuma Humaira da ke Harvard ta samu admission za ta karanci law.
Tare da Auntie maryam aka kammala mana dukkan shirye shirye kasancewar muna makaranta daya da ita dole sai hostel aka kama mana badan Daddy yana so ba saboda ba acikin garin da muke makarantar yake ba Humaira ce dai tayi sa'a batayi nisa da su ba da kanta take driving zuwa makaranta.
Nikam sai rufe motor akayi saboda bazaiyimun amfani ba a yanzu.
Inajin dadin zama da Auntie maryam domin she is social simple but difficult to understand person to be frank gaskiya akwai girman Kai da raina mutum.Ina bata girmanta shi ya sanya muke zaman lafiya ita Ina kuma karuwa da ita sosai ta fannin karatu.
Sun hadu da Yusuf ne a fb chat tun bata kulashi har yaja ra'ayinta suka shaku da ita daga karshe sukayi exchanged na number waya,har soyayya ta kullu a tsakaninsu cikin kankanin lokaci.
Soyayya sosai suke gudanarwa har takai ga Bata iya bacci ba tare da sunyi waya ba nasha fada mata tabi komai a hankali since the guy she is dying of basu taba setting eyes din juna ba most of the fb user are hackers,da yake tayi nisa da soyayya ruwan balain da ta zubamun kadai na ranar ya zamemun kashedin sanya mata idanu naja bakina idan ta ce as sai na ce cas tun daga wannan lokaci bata sanyani shabgar ta da Yusuf sai wancen ranar da ta umarceni da in rakata gidan Yusuf din.bayan ta zuba mishi ruwan bala'i da rashin mutunci akan ganinshi da tayi kan wheelchair
Ita kam bata taba kawo aka cewa Yusuf gurgune kuma talaka sai a wannan rana duk wata kofar da zai samu ganawa da ita ta tosheshi,ni da yake kamun kafa don ganin na dai dai ta su abin yaci tura kashedi sosai tayimun na fitan hankali gaskiya idan ko ban cire hannuna ba bazanji da dadi ba a wurinta domin ko sunan Yusuf din bata so na ambata matashi.
Gashi shi kuma Yusuf din yana so ya takuramun akanta tun Ina yi mashi karya har takaiga na fito na fada mashi gaskiyar lamarin da cewa kawai ya hakura da ita.ya yi ta marairaicemun amma babu yadda na iya da ita,a haife ta girmeni nisa ba kusa ba kuma dama tun farko ita ta ce taji ta gani yanzu kuma ta janye babu yadda zanyi.
Nima kashedin nayi mashi da ya daina kirana amma duk da haka bai hakura ba yadaice mukasance abokai tunda Auntie na ta kishi,ya ce bai tabayin soyayya ba sai akanta ta koyarda shi zama da hira da mace kuma farat daya ta juya mashi baya,inyi hakuri Ina debe mashi kewa.
Bansan abinda yasa ba inajin tausayinshi,hakanne yasanya nake saurarar wayarshi duk lokacin da ya nemeni amma ni bana garajen kiranshi sai dai shi ya Kira ni.

Yau bani da lecture da safe sai 11-12 nake da shi Ina zauna da mug din shayi a hannuna Auntie Maryam kuma tana ta danna laptop dinta sako take turawa supervisor ta.sai gai Kira a wayana dam zuciyata ta bugaganin sunan dake kan screen din da na sanya mashi unknown kowai dan kar tagane saboda yanzu ta sanya mani ido a duk motsina ko ganin idan ankirani bana daga waya agabanta idan ba 'yan gida daga nace kawata wace sai wance to gashi yanzumma Yusuf din ne ke Kira kuma na kasa dagawa duk da na Lura hankalinta na kan laptop din ta ne...
A wayance na dau wayar nayi bedroom da shi sai da na bari muka gama gaisawa nake rokonshi da ya daina Kira na gaskiya kanason takurawa rayuwata ne,murmushi naji yayi mai dauke da fassarori sannan cikin murya kamar marar lafiya ya ce zaratun kiyi hakuri da ni kuma yanzu ma na kiraki ne bisa Neman taimakon gaggawa yanzu nakeson ganinki bani da lafiya ne kizo ki taimakamun.
Har ga Allah naji tausayin yanayin jin muryarshi amma sai na ce kayi hakuri yusuf bazan iya zuwa inda kake ba idan maganar wayane to da Zan taimaka maka.
Yasake marairaimun har sai da na ce to zanzo amma wannan ya zama first and the last promise.
Ya ce promise kuma nagode wannan dinma.
Sai da nagama wayar nashigo wanka na shirya cikin overall ne wanda zai rike sanyi domin yau Ana muku mukun Sanyi ga Snow ta ko ina.
Auntie Maryam ta yi matukar mamakin ganin fitan da zanyi saboda na ce mata sai 11 gashi yanzu ko 10 bai cika sai na ce yanzu ake sanarda ni course lecturer din ne yayi fixed zuwa 10. Jinjinamun Kai tayi tare da cewa take care of yourself..
Na amsa da toh.

Ban zame ko ina ba sai unguwar Yusuf,akasirin ginin unguwar zai tabbatar maka na masu karfin hali ne wanda gidan da Yusuf ke zaune kuma zan iya cewa shine less bisa sauran gidajan ma domin tsohon gini ne yana bukatar gyara sosai.
Haka na cusa kaina cikin gidan fili ne babba da daki daya da tsohon kofar katako wallahi gidan ba za ka dauka wannan gida daga abroad yake ba am feel kamar a nija irin unguwar talakawannan.koda yake ko wani gari da yana da high,middle and low class mutane.
Ina shiga dakin na iske kwance bisa gado ga wheelchair shi kusa gadon.

Yana ganin shigowana yayi sauri zai tashi amma sai ya kasa tashi.
Sai da na tallafa mashi ya jingina kanshi bisa filo sannan na zauna kujerar mutum daya dake kusa da gadon.
Sai da na gaisheshi nayi mashi ya jiki.
Ya amsa cikin sanyin muryar marar lafiya sannan ya dubeni ido cikin ido ya ce thanks for ur concern and considering my invitation.
Na gyada kai nuna alamun na gamsu da bayananshi,sannan na ce Yusuf wallahi Ina matukar tausaya maka amma kasani nima Ina shiga takura aduk lokacin da ka kira wayata saboda auntie fa tafara tuhuma ta ni kuma banason zargi ya shigo tsakaninmu da ita..

Sai yadan yi murmushin karfin hali ya ce
nasani zaratun amma ai yanzu babu wani bayanin zargi tunda ita ne ta gujeni don wannan larura da ta sameni da shi kuma ke munyi alkawarine abota kuma aboki na kwarai can stand for his friend in any situation Kika ga abokinki ke ciki abu daya da zan maki shi ne zan daina kiranki idan har kina gida sai kintafi school muke gaisawa..
Na gyada kaina sannan na ce toh nayarda Ina murmushi a gaskiya yanayin Yusuf da haduwarshi domin gaskiya handsome guy ne idan yana zaune ba za ka taba dauka shi gurgune ba.

Katsemun tunanin da nake yayi cikin fadin zaratun dama na kiraki ne ki taimaka ki dafamun abinci wallahi rabona da cin abinci tun jiya da safe.

Na ce toh amma ina da lecture by 11 kuma yanzu almost10:30 Ina nuna mashi agogo dake manne bisa bangon dakin.
Shima agogon ya mayarda kallonshi sai ya jinjina kai.sai na ce bara na dafa maka tea sai ka hada da bread idan mungama lecture zan kuma dawowa na girka maka abincin.

Ya ce to nagode cikin sauri na jona cattle da ruwa sannan na hada kayan shayi sosai komai yaji sai kamshi ke tashi bayan na juya a flask.na duba bread din babu sai na ce ba ka da bread ne acikin gidan?

Ya daga Kai alamun babu sai na ce to bari naduba ko zan samu nan kusa.

Sai ya ce to kuma ba kudin sayan bread din ne fa zaratun,na duba jakata naga kundin za su isheni zawa da dawowa daga makaranta duk da cewa bana daukan kudin da yafi na motar yawa.
Haka na fito waje bansan kuma gunda zansamo wajen da ake saida bread din ba sai waige waige nake sai ga wani saurari dan matsakaici a cikin wani hadedden sports car.
Ganina kamar ina neman taimako ya tsaya dai dai gunda nake tsaye sauke gilashin motor a hankali sannan ya leko cikin fadin hello lady you need a help?

Sai da na kare mashi kallo sosai dan hutune na karshe kuma shima ba laifi ya hadu.

duk da bana taba kula samari,amma tunda yanzu ina Neman taimakon yasanyani cewa yes am looking for a shop.

Ya ce shop sake tambaya?na ce eeh.
Ya ce gaskiya akwai dan nisa sai dai nashigo motor ya kaini na ce Aa na gode kawai ya kwatantamun naje da Kai na.
Ko ganin ban yarda da shiga motor ne ya mikamun compliment card dinshi hadanden Cati ne sai walkiya yake kamar diamond ajikin catin har da dan karamin hotonshi da bayanan sunanshi,royal family ne wato dan gidan sarauta na qatar yanayin sunanshi ne ya tabbatar mun da shi balarabe ne am ma idan ka ganshi a zahiri kamar bature...

Babu yanda na iya domin kusan nayi latti ma sai da na shiga yaja motor a wani shop muka tsaya da gudu na fito a motor saboda sauri dama ya lura duk tsawon tafiyar da mukayi Ina dubu agogon dake daure a hannuna.har na dawo yana na iske yana jirana.
Nayi mamaki daga yimun taimako har da jira cikin mamaki nake tambayar kodai akwai abinda yake jira?
Ya ce aa ke dince nake jira bakyason na maidaki ne yayimun tambayar cikin kulawa.
Na ce nagode sosai Allaah yabiya ka.

ya ce Amen.

A hankali yake tukunshi kamar yadda maganashi da yake yi cikin nutsuwa sai ta jefomun tambaya da cewa gunda na daukoki shi ne unguwarku?
Na ce Aa nazo yin ziyara ne asalima makaranta ne ya kawoni garin ni 'yar San Francisco ne.
Ya jinjina kai sannan ya ce shima haka karatunne kawoshi masters kuma adward din yake.haka muke ta tattauna yanayin karatun har muka iso layin gidan Yusuf sai na umarci da ya tsaya a anan zan sauka ya rage gudun motor yayi parking na sauka ina ta yi mashi godiya.

Sai ya ce zan iya jiranki ne saboda nima makarantar zan wuce.
Na ce toh da sauri na shiga cikin dakin Yusuf ya kifa kanshi akan filo cikin damuwa na taba kafarshi sai ya juyo muka fuskanci juna yadan yi murmushi ya ce sannu my zaratun Allaa ya saka maki da alkhairi yi sauri kije school kada kiyi missing lecture.
Na ce to sai da na hada mashi komai da yake bukata sannan na fito.
Har na iso wurin motor ina mamakin wannan bawan Allaah da ya Kira kanshi da Khalid....










*comment share and vote please*

⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐


*WACECE NI*




✍🏼by

*Fateema Muhammad Suleiman*
Email [email protected]
Wattad teemacool2020



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is ton entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation



*page* 3⃣1⃣&3⃣2⃣




*Today's Beautiful Hadith is about Embracing Islam*

Narrated Abu Sa'id Al Khudri (RA): Allah's Messenger (peace be upon him) said, "If a person embraces Islam sincerely, then Allah shall forgive all his past sins, and after that starts the settlement of accounts, the reward of his good deeds will be ten times to seven hundred times for each good deed and one evil deed will be recorded as it is unless Allah forgives it."

(Sahih al-Bukhari, Vol. 1, Book 2, Hadith 34)

_SubhanAllah! What a beautiful reminder! It's never too late to embrace Islam sincerely! Reflect, read, learn and grow, come closer to Islam. If you're a revert then Alhamdulillah, if you're born into the deen and have come closer to it, then Alhamdulillah!_


Tun kafin na karaso yabudemun kofar motar,yaja muka kama hanyar school Ina Allaah Allaah kar Prof yafara holding lecture domin baya bari ashiga idan har ya shigo hall.cikin sa'a kuwa bai shigo ba.amma ya sanar da class rep cewa ya samu emergency calling ne daga bursary.ya yi fixing lecture zuwa 12-1.
Duk mun zauna domin jiranshi kawata latifa ce ta dafa bayana da sauri najuyo da alamu yanzu shigowarta nake tambayarta dama kinsan yayi shifting lec 12?
Ta ce muna nan class rep yayi mana informing sai naje gida,ko 20 minutes banyiba kinga har na dawo saboda tsoron prof abu kadan ya hanaka attending lec.na ce ni Allah ya so ya daga time coz nayi late sosai.

Ta ce to ke Ina kika tsaya ne?

Na ce gidan yusuf bashi da lafiya.
Ta tabe baki ta ce amma lallai zaratun bakijin magana duk kashedin da auntie ki ta yi baki saduda ba,abin ya tashi a waya har biyoshi gida kike, anya ba son Yusuf dinnan kike ba kuwa?

Na harareta sannan na ce to 'yan sa idonawa masu bacci ido daya taimakona ya nema kuma na taimaka mashi ko taimako laifina a wajenki?

Ta ce wallahi Ina dai duba maki auntie Maryam ne gaskiya she is strict person.
Bankuma cewa komai ba sai ga lecturer mu da sauri muka shiga hall din
Yana shiga abinda ya Fara fitowa daga bakinshi move in your seat type your ID number and wait for the password.dukkanmu students kallon kallo muka tsaya yi wato shi kuma Mr Paul tanan ya bullo test without informing.duka course lecturer's din haka suke mana.bayan ya fada mana password kowa ya yi login Allaah yasa test din bai wani cire abubuwa masu wuya ba base on previous lecture nashi ya cire.
Ni na fara fitowa sai ga Latifa ma ta fito.
Muka fara tafiya sai ga khalid shima ya fito daga faculty bansan gunwa yaje ba.na yi mamaki da ganinshi.
Sai yadanyi murmushi ya ce kina mamakin ganina ko?
Na ce gaskiya dole na nayi mamaki mana kuma na ganka ka fito a faculty mu?

Ya ce eeh nazo wurin level coordinator Ku ne shine supervisor na project dina.so naga fitanku a hall that's why i followed you back.

Na ce ya yi kyau,sannan na juya fa Latifa da tun farko Bata sanya bakinta a maganarmu na ce dear meet my new friend Khalid.

Sai a sannan ta fuskanceshi tana murmushi ta ce good afternoon sir.

Shima ya sako murmushi ya ce afternoon dear my pleasure to meet you.

Itama ta ce my pleasure too.

A haka har muka iso car park direct gunda Latifa tayi parking motor ta muka nufa,shima Khalid ya nufi wajen motarshi bayan munyi sallama....

Wasa wasa shakuwa mai tsanani yashiga tsakanina da khalid domin shifa soyayya sosai yake nunamun yayinda ni kuma gaba daya zuciya ta ta allaka akan yusuf wallahi abin kamar asiri,tunda ya furta yana sona na amince mashi,amma ban fadawa kowa ba.ko Latifa da take tight friend dina na boye Mata saboda ko kadan batason na kama mata sunan Yusuf,duk ranar da na fada Mata cewa daga gidan Yusuf na tashi nayi mashi girki ne,cewa take yarinya ki ringa yiwa kanki fada fa idan ma son Yusuf kike to iyayenki bazasu amince ba saboda banbanci yanayi da kuke da shi Ina ke Ina gurgu.wannan statement dinta ya konamun rai sosai dan haka na daina kawo maganar Yusuf ko da ko wane irin hira muke da ita.ita batasan cewa larurar da yake da shi ne musabbabin sonshi da tausayinshi yadarsu cikin raina ba.
bana iya bacci sai naji muryarshi.da safe sai na biya gidansa na yi mashi dukkan abinda yake bukata sannan na wuce school.duk wannan abin da ke faruwa auntie Maryam bata da masaniya akai domin soyayyar Sirri muke amma mai tsafta.


Yau Khalid tunda muka fita daga lecture muna tare yana jaddadamun soyayyarshi,ya ce zaratun Ina sonki so na hakika amma ke kuma bakya ko tausayamun ki amshi soyayya ta tun ranar da na kyalla idanuna akan sonki yayimun mummunan kamu.please ki agaza ki amshi soyayya ta.har da yin knell down nuna alamun optimum roko.sannan yaci gaba cewa
Each time I look at your gorgeous face, I feel my heart melt in your love baby girl. I just cannot stop thinking about you.please love me back...


Sai da na daidaita zamana sannan na ce wallahi Khalid ba haka bane ina sonka and I do love you always amma yanzu kayimun uziri saboda yanayin karatuna yana bukatar lura da mayar da hankali sosai idan na ce zan hada soyayya gaskiya zan takuru.amma believe me inasonka.

Sai yadan nisa ya ce hakane bawai inason shiga cikin rayuwarki ko na karatunki ba what I wanted from you is your true love.ya tsuramun lumsassun idanuwanshi Khalid handsome guy ne da duk wata mace zatayi mafarkin samunshi a matsayin mijinta ga kudi ga kyau.amma ni kuma duk wannan baya gabana soyayyar Yusuf ne fal cikin raina,gudun kar yaga na wulakantashi ya sanya na yarda muke soyayya da shi.yanzun ma da ya ritsani da idanuwanshi bansan lokacin da na ce,
You complete my life and make it so worth living. you are nothing but an angel to me. I love you.kar ka damu ina tare da Kai a koda yaushe...

Ya sako murmushi da nuna alamun ya gumsu da maganganuna sannan ya ce thanks so much gaskiya yau zanyi bacci cikin farin ciki.

Har gida ya kawoni sannan mukayi sallama ya tafi.

na yi sallama auntie Maryam ta amsamun,Ina zama take tambayata Khalid ne yakawoki?
Na ce eeh ya ce na gaisheki.bayan munyi sallah mukaci abinci sai da muka kammala nadauko assignment dina na farayi auntie Maryam dince take guiding dina saboda akwaita da ilmi daidai gwargwado.itama wani lecturer su ne suke soyayya kuma da alama tana sonshi don har ta gabatar da shi ga ya Anas through phone call.
Yanzu ta cire maganar Yusuf ko sunanshi bata ambata ba.ni kuma bana nuna mata muna alaka da shi balle har soyayyar da muke.


Tsawon dare muna waya da Yusuf.hirar soyayya muke Yana kuma kasheni da kalamenshi masu rikitar da kwakalwata gaskiya Yusuf karshene wajen nuna soyayya da kalmomi masu sace dukkan wanda ake yiwa sunana kawai idan ya ambata sai dukkan tsigar jikina ya amsa.

Na amsa da na'am

Ya ce Allaah yayi maki albarka na gode da nunamun soyayyarki gareni,duk da halin da nake ciki kina taimakona both financially da taimakon kuma karfinki duk da na kasance ni ba kowa ba.amma dan Allaah meye dalilinki na kula da ni haka bayan nasan kedin mutane dayawa suna rubibin sonki?

Ina iya jin sautin kukanshi kasa kasa.
Nima na karaya da jin muryarshi na shiga tsoro sosai kodai Yusuf mutuwa zaiyi yanayimun irin wannan godiyar duk dadewar da mukayi bai taba yimun haka ba.sai da naji na dan daidaita da yanayin da na shiga sannan na ce,Yusuf zuciyata ce ta amince da Kai kuma ta yardemun da insoka kuma darurarka Allaah ne ya daura maka kuma kowa baifi karfin a jarabceshi ba.kuma in aha Allaah za ka samu lafiya.

Ya ce na gode Allaah ya saka maki da mafi alkhairi,Ina sonki sosai kamar yadda na ce maki wani bawan Allaah yadau nawi na zamu fita zuwa Germany ko za'a dace kinga mukam duk karfinmu ya kare wajen magani saboda yanayin rayuwa iyayena,sun koma kauye dama ni ke taimaka musu.

Na ce haka ne Allaah yasa aje a sa'a ya ce Amen.
Daren gaba daya mun karasashi cikin jimami sai kusan karfe biyu yayimun sallama bayan na mashi alkawarin zuwa da safe.....

Saboda ina fashin sallah sai kusan karfe bakwai na tashi na shigo wanka bayan na fito na shirya cikin dogon riga English wear ne pink color das kayan ya matukar karbata...

Na tarar da auntie Maryam har ta gaba hada kayan break ta jira bisa dining mug ne a hannunta dagani coffee ne take sha domin tanason coffee...Good morning Ina shirin zama nake gaisheta,ta amsa morning how was your night?
Na ce Alhamdulillah me fa?
Ta ce nima haka.

Cikin sauri na hada tea da bread kadan naci.tana korafin banacin abinci na damu kaina da karatu.na ce zanci ne yanzu am almost late ne cikin shagoba nayi maganar,banjira me ta ce ba nayi mata sallama na fito waje.banzame ko Ina ba sai gidan Yusuf.ko kofarshi bai budeba sai da nayi knocking ya zo akan kekenshi na guragu ya budemun.

Yana ganina ya sakarmun murmushi nima na mayar mashi da martani sannan yaban hanya na shiga dakin.
Komai a wargaje dan kwana biyun da banzo ba.sai da na share ko ina na kimtsa na daura mashi abinci,sannan na zauna...Ina dan duba agogo lokacin lecture na ya kusa.na zuba abinci cikin food flask,sannan na kawo kusa da shi na ajiye.na ce meye za ka Fara ci ko in zuba maka tea first?

Duk abinda nake ya zubamun idanu ko kiftawa bayayi sai da na fura mashi iskan bakina sannan ya dubeni ya ce ba laifi na bane yanuna zuciyarshi da hannu ya ce kinsan tanason mai kyautata Mata.

Na danyi murmushi sannan na ce kaci abinci ga shayinma na zuba bansan ya akayi ba saboda tsaban zafin da naji na kunar wuta gaba daya hannuna na hagu shayin ya zuba kuma yusuf dinne ya zubamun garin zai dauki shayin bansan lokacin da hawaye masu zafi suka dinga fitowa daga idanuna ba shima ya rikice sosai abinka da farin jiki duk sun tashi da rudo rudo,sai sannu yakeyimun ya yinda ni kuma nake mashi kallon kamar da biyu yayimun hakan......
Sai tambayata yake ko zai kira abokinshi likitane ya dubamun na girgiza kaina sannan nadau jakata nayi hanyar fita da sauri ya tare ni da cewa kiyi hakuri wallhai bangani ba subutar hannune ki tsaya abokina ya dubaki kaina na girgiza na ce zanje clinic na makarantarmu zasu dubanun.babu yanda ya iya haka yabarni na tafi school amma cikin zuciyata Ina ganin da gangan yayimun hakan...

Waya ta,na ciro na Kira Khalid akan muhadu a makaranta na dan samu kunar wuta ne.
Reaction dinshi acikin wayar koda bangashi wallahi yafi shiga damuwa fiye da Yusuf din da shine sanadin kunar nawa, ko minti goma bankai a school ba sai ga Khalid cikin shiganshi da yake burgeni Yana duba hannun cikin tsananin kulawa sannan ya umarceni muje asibiti aduba.

Na ce to domin hannun har yafara yimun zugi...







*Please share vote and comment*
⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐


*WACECE NI*





✍🏼by

*Fateema Muhammad Suleiman*
Email [email protected]
Wattad teemacool2020



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is ton entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*page* 3⃣3⃣&3⃣4⃣



*wannan page naku ne masoya Aazeen amma wadanda suke comment*



*Today's Beautiful Hadith is about Charity*

It was narrated from 'Umar, meaning, from his father, his grandfather 'Umar, that: He gave a horse in charity at the time of the Messenger of Allah (peace be upon him), then he saw its owner selling it for a low price. He went to the Prophet (peace be upon him) and asked him about that, and he said: “Do not buy what you gave in charity.”

(Sunan Ibn Majah, Vol. 3, Book 15, Hadith 2392)

_When you give in charity with that intention, let it go. Do not worry about the materialistic value of things and know that the reward of your intentions lies with Allah alone. What a great Hadith to remind us to reflect and work on ourselves to attain a higher status where everything is fisabilillah!_






Ba mu zame ko ina ba sai wani asibiti A&E muka wuce suka dubamun hannun sai da suka daye wajen sannan suka wanke da normal saline,iodine da gencial violet suka zubamun sai magunguna da suka rubuta khalid ya sayamun su daga pharmacy sai sannu yake yimun duk tambayar da yayimun ta ya ya hakan ta faru?na dai ce mashi mistake ne kawai.da yaga bani da niyar fada mashi ya ja bakinshi ya yi shiru.sai da ya sauke ni a kofar gida ya yimun sai da safe nima nayi mashi godiya na shiga gida.bansamu kowa a falo ba kawai sai na zauna na kunna TV banfi minti biyar da zama ba sai ga auntie Maryam ta fito dagani wanka tayi bata lura da hannuna ba sai ta zauna sannan cikin tsorata da hannun nawa duk ta tayar da hankalinta cikin damuwa ta ce subhanallah zaratun meye ya samu hannunki yayimun tambayar tare da rike hannun dake ciwo?

Kasa bata amsa nayi sai hawaye shar a idanuna,ta ce please kifadamun meye yasamu hannun cikin rarrashi take tambayata? This time kam bazan boye mata ba dole na fada Mata gaskiya.

Na ce ruwan shayi ne ya zubomun shi ne na samu kuna yanzu Khalid ya sauke zuwanmu kenan daga asibiti.
Cikin mamaki ta ce shayi kuma?
Waye kuma ya fara zuwa muku da shayi zuwa school?
Na ce ba'a school bane a gidan Yusuf ne ya kirani na taimaka mashi shi ne ya zubamun shayin a hannuna.
Wani kallo da harara da ta sakarmun wallahi sai da hanjin cikina suka kada,na shiga da na sanin fada mata gaskiya.
Cikin karaji har muryata baya fita dan masifa.
Ta

Please Login or Register in order to submit comment