Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta kowane bangare komai ya tafi dai dai ba asamu wata mishkila ba.duk da kasancewar barrister mukhtar ya nuna maitarshi akan Aazeen amma dangi sun bashi hakuri da nuna mashi cewa lallai Dr Hameed ne ya cancanci auren Aazeen din, saboda taka muhimmiyar rawa da ya taka wajen inganta rayuwarta da tsayin dakan da ya yi wajen ganin ta samu danginta.kuma da suka tashi zuwa har da mahaifinshi suka zo, dattijon da kusan shekaru ishirin bai taka Nigeria ba amma saboda dalilin maganar auren Aazeen din sai gashi ya tako Nigeria yar.

Dr Ahmad zaibaddeen dan Nigeria ne, iyayenshi 'yan asalin yola ,amma duk yaranshi a can aka haifesu kasancewar tun da ya je karatun likitanci da ya kammala suka rike shi ya zama cikekken likitansu toh da yana yawan zuwa Nigeria akai akai amma saboda halin girma ya daina zuwa Nigeria yar sai yaranshi da suke zuwa ziyara toh yanzu da Dr Hameed din ya zo mashi da maganar Aazeen din kuma ya ce ita 'Yar asalin Nigerian ne,to sai ya ji dadi sosai kuma shi da kanshi ya matsa su kawo maganar auren.Dr Hameed shi ne na biyu acikin yaran da ya Haifa guda biyar,kuma shi yagaji Sana'arshi wato likitanci......sisin gwal guda ishirin da hadu aka bayar na sadaki,sannan aka sanya sati hudu dan daurin aure.soyayya mai tsafta suke gudanarwa cikin wannan kwanakin.
Yauma suna zaune a cikin garden din gidansu wurin shiru sai kukan tsuntsayen da ke shawagi a tsananin wajen.ya tsura mata idanunshi na tsawon lokaci har ta gaza jure wannan kayataccen kallon nashi da yake kashe mata dukkan gabobinta ta sadda kanta kasa tana murza zoben da yasanya mata tun a san Francisco.
Cikin muryarshi da yake dimauta ta a duk lokacin da ya kira sunanta.
Ya ce Aazeen"
Ta ce na'am ba tare da ta dago kanta ba.
Ya ce ki dago ki dubeni sosai da sosai nifa bani son wannan kunyar taki tayi yawa Ina son mace Mai kunya amma taki gaskiya tayi waya idan banyi da gaske ba zaki cuceni.
Ta danyi murmushi ta dubeshi idanunshi da suka fi komai burgeta ta tsura musu idanu sai ya ce kalleni da kyau I am your nan da 'yan kwanaki zamu rikide my zama abu daya Ina son ki fadamun abubuwanda da kike so awajen Nada da Wanda bakya so feel free to ask me before then nima na tambayeki.infect what do u do?

Ta yi shiru na mintoci kamar ba za ta yi magana ba sai kuma ta nisa ta ce,bansan ta Ina zan fara ba amma zan iya cewa ni Aazeen tarihi na daga shekaru goma sha biyu da haihuwata zuwa kasa na ta so cikin gata da walwala ban taba sanin wani abu wai shi kunci ba a takaicedai ni daddy's girl ce,iyakacin karatuna kuma na tsaya daga jss 3 saboda iftila'in da muka fada basai na fada maka ba kaine shaidan hakan,abubuwanda da nake bukata awajen maza kuma shi ne Ina son mijina yakasance Mai gaskiya,tausayi da nuna soyayya a gareni idan nasamu haka to ni kuma zan zame mashi kamar baiwa ta karasa maganarta cikin yin kaya taccen murmushi.tun da take magana yatsura mata idanu ya na kuma duba dan karamin bakinta da take zaro maganar ta cikin hikima da fasaha ga duk Mai sauraronta,zai dimauce ko shidin baiso ta tsaya da maganar ba saboda har cikin bargon shi maganar ke shi ganshi.
Ya na cikin tunanin maganganunta yana kuma jujjuya zancenta cikin zuciyarshi.

Sai ta katse tunaninshi cikin sansanyar muryarta ta ce and you tana nufin itama ta na son sanin nashi bayanan?

Ya ja dogon numfashi sannan ya nisa ya fara bayananshi cikin kasaitarshi da muryanshi da yake rawarshi kamar bayason ya yi maganar,dama shi haka yake yawancin mutane suna daukarshi kamar ya na da girman kai ne but idan ka zauna da shi za ka gane sabanin hakan,kawai dai zamu iya kiranshi miskili ne amma ya na da saukin kai da taushin hali,bashi da kwaramniya ne kawai.
Ya ce ni Hameed Ahmad zaibaddeen,half cast ne haifeffen garin Birmingham aiki ne yakawo ni san Francisco,cikekken likita ne akan gynecologist,abubuwanda nake so mata ta ta kasance suna da yawa sai dai nasan duk kin mallake so,ya danyi murmushi sannan ya dan ja numfashi ya ci gaba da cewa,abu na farko da nake son mace ta kasance ta na da shi,wato shi ne tsafta,kula da ni sosai saboda ni mai yawan bukata ne saboda haka sai kisan yadda za ki yi da bukatuna idan na samu wannan ni kuma zan kasance mai tattalinki da baki kulawa ta mussamman ya yi shi sai ya juya ga tattabaru guda biyu da suke tsumbatar juna sai ya ce ki duba wadannan tsuntsayen mata da miji ne a ko yaushe kinga namiji yana tattalin matarshi ne toh zan kasance maki kamar dai wannan tsuntsun....
ta sadda kanta bata ce komai sai dai ta kasa dauki idanunta daga kan tsuntsayen ta na kuma jujjuya maganganunshi cikin zuciyarta.nima mai yawan bukata ne me hakan ke nufi?ta dai barwa zuciyarta amsar kawai saboda bata fahimta ba.

Kamar yasan zuciyarta ya ce na sanyaki cikin tunani ko yes ni jarumi ba akan aikina Kawai ba har wajen nuna kauna da soyayya.haka suka kasance kusan awa biyu suna wajen sai da suka dan ci snacks da kanun aya da kayan marmarin sannan ta koma cikin gida shi kuma ya wace wajensu dad kusa da su ya Anas ya samu waje ya zauna.



***************



A kwana a tashi babu waya a wurin Allah yau saura kwana uku a daura auren Aazeen da Dr Hameed,yau alkamis shi ne ya dace da ranar lalle cikin al'adun kanuri kenan gidan angwaye za su kawo lalle babban buhu da kayan al'adu daban-daban,domin lallen ma akwai babba,akwai karami.sai da yamma kamar karfe hudu aka ta taru a barwee suite hotel inda aka gabatar da kanuri night,sai washe gari kuma aka gabatar da wushe-wushe.

ranar asabar da misalin karfe goma na safe aka daure auren a babban masallacin juma'a wato Maiduguri juma'a mosque limamin masllacin imam Asil shi ne ya jagoranti daurin auren, kamar yadda addinin musulunci ya tadanar,waliyin ango ya karba daga wurin waliyin amarya wato kanin mahaifinta.

Amarya ta yi shar da ita duk jikinta yasha gyara da halawa da dilke sai walkiya take yi saboda haske da kyau musamman Ahayye ce ta gyarata gyara ta kuma irin nasu na ndjemaina (chad) tun da aka sanya rana wata daya bata fita ko bakin get domin a al a darsu suna Hana amarya yin kwalliya da fita waje,sai ranar aure.ko free wedding picture da kyar suka bar ta ta fita sukaje studio24 su ka yi kuma sunyi matukar yin kyau Masha Allah.
Da dare aka gudanar da 'yar kwarya kwaryar liyafa ango da amarya cikin shiga na alfarma sai walkiya suke saboda dukkaninsu 'yan hutu ne.

Sheikh Muhammad Mustapha Albarnawi ne ya gabatar da nasiha akan zamantakewar aure ...bayan anci ansha mutane suka fara watsewa.ango kam sai nan nan yake da amaryarshi yaki barinta ta sake Yana manne da ita sai washe baki yake da ganinshi yana cikin farin ciki Mara misaltuwa.musamma motor da aka tanada na ango da amarya suka shiga driver ya na su suka kama hanyar gida.dukkansu abayan motor suka zauna,kanta a duke ta sadda da shi kasa sai ya tallafo habartaya dago fuskar sai ta runtse idanunta nuna alamun jin kunya.


Ya ce aiko baki isa ba bude idanunki in kalli wannan fuskar ki mai yalwar haske da annuri gaskiya yau Ina cikin farin ciki mara misaltuwa na mallaki wannan kyakkyawar model lady...
Ita sai ta yi shiru ta na sauraronshi kawai,kuma batasan me yasa ba zuciyarta na bugu kadan kadan kamar da tsoro ne yakeson ziyartar zuciyarta.
A haka kuma har suka iso gida dai dai karfe goma kenan.

suna sauka babu kowa a harabar gidan sauran mutane har sun gama dawowa domin ga nan motoci burjik a wurin cikin sauri ta sauko a motar tana saurin yin part dinsu mum sai ya yi saurin riko hannunta,ya ce saurin me kikeyi ne haka ba za ki tsaya ki yi sallama mai kyau da mijinki ba?
baki ga yanzu duk sun mallakamun ke ba gaba daya tun awajen dinner kowa ya gudu ya barmun ke ba yana wani Shu'umin murmushi ya ke wannan maganar.


Ta dan sako murmushi ta ce nasani kawai dai gajiya ce kuma kayan sunyimun nawi inason ciresu ne.
Ya jinjina kai ya ce to na ji yanzu me Kika shiryamun ne kafin gobe
Ta yi shiru ta kasa bashi amsa.
Sai ya ce ya baki ce komai ba?
Ta ce to ai ni bansan meye zance ba.
Ya ce ya na da kyau kisan abin da da za ki ce.

Gaba daya ta kagu yabarta ta shiga amma sai da ya yi kicin kicin din da ya hada bakinsu wuri daya tsawon lokaci ya na tsosan sai da ya gaji da karan kanshi ya sake ta kuma ta ci sa'a babu wanda yafito sai da ta dan setu da yanayin da ta shiga sannan ta yi mashi good night shima ya mayar mata da sallamar ta sannan,ya ce bear in your mind flight dinmu fa by nine ne so ki samu shiri da wuri da wanda zaku tafi tare sannan ya kuma yi mata peak kiss a hannunta ya yi part din da aka basu tun zuwansu.

Ta na shi duk yawanci mutane suna ta hayaniya wadansu kuma suna harkokin gabansu ba su ma Lura da shigarta ba sai da ta shiga bedroom ta iske Fatima da Aisha wanda sune sa 'anninta yaran goggoninta ne cha sukayi mata da cewa kai wannan angon naki dan love ne tun yaushe muke zaman jiranki amma sai yanzu zai barki Ku dawo mu fa har mun dauka fa a can zaki kwana suka fada cikin zaulaya da dariya.

Ta harare su itama ma ta ce sai kuyi ai amma kuma rashin kunyar tawa ba ta yi yawan da zai sa inbi miji makwancinshi kuma na gidanmu.
Su ka tabe baki suka ce ka ji mun mata yadai daga maki Kafa ne ai to hakkinshi ne dole kuma zai kwata komai daren dadewa.
Ta ce kwaji da shi ni bara inyi wanka wannan kaya duk ya ta kurani Ku kuma parot kun cikani da surutu.ba ta tsaya jin amsarsu ba ta shige bathroom ta sakarwa kanta shower......










*share and comment*

⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐


*WACECE NI*




✍🏼by

*Fateema Muhammad Suleiman*
Email [email protected]
Wattad teemacool2020



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is ton entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*page* 2⃣3⃣&2⃣4⃣


*wannan page naku ne masoya Aazeen amma wadanda suke comment kuyi yadda kuke so da shi*



Sai da ta gama kimtsawa ta sanya kayan baccinta sannan ta fito falo duk yawanci mutane sunyi bacci sai fatima ce da ke gaban TV tana kallon series film Hayati Azab.
Ta dago ta dube ta ta ce amarya agidan Dr Hameed yadai akwai wani abu ne?
Aazeen ta ce eh ki nemomun abinci felling hungry,
Da sauri ta mike ta dauko mata flask sai slace bread da kamoniya acikin plate ta ce ga wannan ki yi manage.
Ta yi murmushi ta ce thanks wannan ma ya yi.
Ta na ci jefi jefi suke hira domin Aazeen din ba mai yawan magana ba ce.sai dai ita fatiman ce ta ke dan jan ta da hira.suna cikin zancen yanda dinner din ya kayatar sai ga Akhayya,kanwar mahaifiyarta ce,tare aka yi masu aure da Hajja fanna amma ita mutumin Ndjanmaina (chad) ta aura ta haifi yara uku maza biyu da yarinya daya toh tunda mijinta ya rasu, ta dawo zama a Nigeria.sai kuma bayan batan Aazeen da rasuwar Alhaji modu ta dawo gidan yayar ta ta wato Hajja fanna domin ta taya ta zama.ita ce kuma duk wani gyara da za'ayiwa amare sai da tayiwa Aazeen sirrika Kala kala wanda har ita Aazeen din sai da yafita akanta,yanzu ma zuwa ta yi da wani irin hadinsu na shuwa ta umarci Aazeen din da ta sha, ta karba cikin langabe kai a shagobe ta ce ni fa ammi abubuwanda kike duramun din nan,ya ishe ni.dubi jikina fa,duk sun ciko nifa banason kiba shi ya sanya ko madara banason sha sosai amma sai da kuka sa nasha peak da kwai har na tsowon wata daya ga sauran abubuwan da bansan Kansu ba da kike ta bani gaskiya ni haka ya isa ta karasa zancenta kamar za ta yi kuka.

Akhayye ammi sunanda suke ki ranta da shi kenan,ta ce rakrak hanaki ,ke me ma kika gani dan ma bakya chad ne da zan sanya har circumcision(kaciya) ammaki saboda yana cikin al'adummu amma nan duk kunyi watsi da shi.wannan abubuwa da nake maki 'yancin kanki nake nema maki kin manta kin haihu ne duk da cs ne duk service ya dan budu sannan mijinki saurayi ne.yanzu abin da nake bukata ki ta shi muje ki kuma tsugunawa akan wancen kaskon ki sanya lubban da gafgaf sai wannan ta mika mata wani kalan turaren wuta da bansan sunanshi ba,sai da ta jira ta tabbatar ta yi abubuwan da ta sanyata ta yi sannan sukayi sallama ta koma part din da take.

Aazeen ba ta samu ta sanya zaratun a idanunta ba kuma ta na son ganin 'yar ta ta amma sam sunki kawo mata ita batasamma a gunwa take ba Kiri kiri suka sanya ta hana mata nono,ba ta so hakan ba duk watan yarinyar shida amma anhana mata nono,duk dama exclusive breast feeding ta yi mata yanzu sai dai SMA suke bata Masha Allah kuma ya karbeta ba za ka dauka batashan nono ba,bulbul da ita tabarakallah.

Sai ga kiran angon na ta ya shigo sai da tayi ringing sau biyu sannan ta dauka a kasale domin duk gabobin jikinta ciwo ke yi saboda gajiya duk kwanakin nan bata samun hutu.shidin ma hakanne.
Cikin sanyin murya ta amsa mashi sallamar da ya yi sannan ya ce,baby girl gaba daya yau kinsa na kasa bacci yanzu kisan abin da za ki yi mun Wanda zai sanyani bacci.

Cikin lankwasawar murya mai taushi ta ce ni kuma na hanaka bacci sai dai ka ce gajiya ya Hana ka bacci dai kamar yanda na ke ji yanzu haka duk jikina ciwo kamar anyimun duka ta na maganan cikin shagoba kamar ta na gabanshi.

ya ce kada ki samu damuwa wannan gajiyar duk zan cire maki shi daga gobe ma.yanzu ki na ina ne ya jeho ma ta tambaya?
ta ce Ina kan gado inason yin bacci amma yaki zuwa.
Ya ce ko dai za ki zo ne kimun ko da massaging ne (tausa)?
Cikin ware ido kamar ya na kallonta ta ce chab ta Ina zan fara dazu ma dakyar na kwace Kai na a wurinka na lura sosai kana son sanyani jin kunya.
ya ce kunyar me? ai dama da suka mallakamun ke sun san abinda zai wakana kenan,dadin abin duk abinda za mu yi lada za ki samu.ke din ce idan ki na kusa da mutum sai ya kasa controlling kanshi dazun ma ba karamin hakuri na yi ba.
Ta yi shiru tsawon dakikai sai ya katse shirun da cewa.
Ya kinyi shiru ne?
Ta ce to ni meye zan ce?
Ya ce amaryata ki cire kunya ni fa ba na son mai kunya feel free I am ur husby kuma ina son ayi treating dina like a baby,so kunya bashi da muhallin zama a gidanmu.

Ta nisa har sai da ya ji hucin numfashinta a cikin wayar ta ce don Allaah ka barni na yi bacci yanzu kusan karfe daya fa nasan bazan yi bacci na two hours ba Ammi za ta ta sheni...
Kin gundura da ni kenan?
Ta ce ni bance ba kawai ina son na yi bacci ne before four o clock saboda gobe.
Ya nisa ya ce toh ya na iya gimbiya ta bani umarni am at your service always,to adan yimun kiss ko zan dan samu relief.
Ta yi raurau da ido kamar ta na ganinshi ta ce nidai a'a kunya nake ji.
Ya ce no zanyi fushi fa
Cikin jin kunya ta tsumbaci wayar kuma ya ji ajikinshi sosai har idanunshi sun dan rikide,
Ya ce mayar mata da shi cikin kwarewa sannan ya ce I love you good night.
Itama ta ce good night too,sannan ya katse wayar.

Sai da ya shiga bathroom ya yi wanka sannan ya sanya boxes kawai domin garin akwai zafi sai sanyin AC din da ke ratsa jikinshi.ya na ta tunanin Aazeen din cikin ranshi har bacci ya yi awon gabada shi.
Itama Aazeen din haka batafi minti biyu ba baccin yadauketa saboda dama shi ke damunta.

Karfe hudu daidai wayar Dr Hameed ya tayar da ita daga bacci, sai da ta yi wanka sannan ta dauro alwala ta gabatar da ra'atanil fajiri sannan ta gabatar da sallar asubah,ba ta tashi a wurinba sai da ta yi sallar shuruk.
Ta bangaren Dr Hameed shiri sosai ya ke yi duk ya bi aminanshi ya yi musu sallama.sai ga kayan karin kumollo abinci kala kala babban tare ne suka jera dukkan variety na abincin,haka akeyi a chad wannan kuma shirin Ammi ne.itama Aazeen an yi mata shiga irin na al'ada wato dan firirit din riga iya gwiwa sai farin laffaya da duwatsu sai walkiya suke Masha Allaah abin ba magana sai Wanda ya gani.ga skin dinta sai sulbi da walkiya saboda gyara.zaratun ma an shiryata cikin overall fari Sol,tana hannun Ammi ita ce kawai kuma za ta raka amarya dakinta sai Fatima acikin kawaye.

Dai dai karfe takwas kowa ya shirya domin raka amarya airport ,uncles dinta da aunties dinta daga bangaren uwa da uba sun sanyata a tsakiya nasiha sosai suka yi mata sai Alhaji Ahmad ne na karshe ya fara da cewa,
To diyata ina mai yi maki nasiha da kiji tsoron Allaah a gidan auren ki,ki rike amanarku ki kyautatawa iyayenshi da 'yan uwanshi da dukkan danginshi,shi aure 'Yar hakuri ce,ki kauda idanunki da kunnuwanki da jin ko ganin aibin da za a kawo maki na mijinki,ki sani cewa mun aurar da ke ne ba dan mungaji da ke ba sai dan bin umarin annabinmu da yake cewa,
Idan wani bawa da ya zo Neman auran'ya 'yanku mata idan kun gamsu da addininsu to Ku aura musu wannan shi ne yafi alkhairi.sannan kuma mutumcin'ya mace dakin mijinta to iyakancin gatan da za mu yi maki kenan saboda haka ki bi mijinki sau da kafa ,Allaah ya yi maki Albarka ya Albarkaci aurenku.duk suka amsa da Aameen.
Aazeen dai sai kuka ta ke kasa kasa sai Hakka fanna ma ta yi na ta nasiha a matsayinta na uwa ita ma kuma hawyen take sosai.
Ya Anas ne ya shigo ya bada umarnin a fito da amarya jin wannan faruci Aazeen da sauri ta Dada jikin mummy ta sai kuka wiwi da kyat dai aka banbare ta aka fito da ita har wurin motor..
Motor da aka ta nada mussamman dan amarya da ango aka sanya ta ,motoci kusan bakwai ne kuma suka yi musu rakiya zuwa airport duk tsowon tafiyar kuma sai fesa turare su ke yiwa jama'a duk cikin motor kamshin turaruka Kala Kala ke ta shi.a haka har aka iso airport manya mata sai guda sukeyi.angonma ba laifi ya yi shiga na al'ada babbar riga dau ngashau da fula yaudi mai matukar kyau duk cikan wajen ya fito daban acikinsu.bayan angama yin screening din kayayyakinsu sannan duk suka shiga musabahar hannu da juna na bankwana.
Sai da suka jira jirgin ya daga sannan suka koma gida.

Ango da amarya kujeransu a jere da juna sai Ammi da Fatima suma suna can gefe kusa da juna.sai dad dinshi da kaninshi suma suna kusa da juna.tun da suka shigo jirgin Aazeen kuka take babu sausautawa sosai yashiga cikin damuwa ganin kukan da take,ya kwantar da kanta bisa kafadarshi yana lallashinta da hankali yake mata magana cikin taushin murya,shhhhhi kiyi hakuri I am there for you,nasan kinyi missing gida amma kuma ni bazan ji dadi ba wannan kukan zai iya sanyaki ciwon kai so take heart na yi maki alkawari,ba za mu dau lokaci mai tsayi ba za mu koma ziyara.

Awa goma sha biyu suka yi a wannan jirgi sannan suka sauka a France,sai suka kwana da safe suka kuma daukan hanyar USA.sai kusan karfe goma sha biyu suka landing a babban birninsu wato Florida,anan suka yada Zango gidan da suka sauka babban gida ne mai part uku ginin ya tsaru dai kamar ko wane gini dake America akwai tsari.daidaikun mutane ne suka tarbesu saboda yanayin rayuwarsu basa shiga rayuwar kowa,mind the own business.part na farko su dad ne suka zauna,sai na biyu su Amma na uku kuma ango da amarya.

Sai da su dan nutsu sannan aka kawo order abinci da abinsha Kala
Kala,sai da ya lallashata ta danci abincin kadan.
sai kusan karfe biyar ammi ta hafa wuta a irin gawayin China da ake kunnawa sai ya Kama da wuta acikin karamin kasko ta hurashi,kabbasa n da suka so da shi mai naduwa ta warware ta kifa kayan Aazeen akai,sannan ta umarceta da ta yi wanka,bayan ta fito jikinta danye haka ta mika mata kaskon wutar da ta zuba turarukan wuta Kala daban daban,
Sai da ta tabbatar turaren ya ratsa dukkan jikinta sannan ta mika mata kulaccam da jannaniye da musuk ta shafa dukkan jikinta,duk wannan shiri kuma a part din su Ammin sukeyi domin sai dare za su kawo ta shashinta.
Shima uban gayyar shiri sosai ya yi duk yabi ya yi decorating dakin sai wani creative da ya yi a kasan dakin ya rubuta I love you forever.duk suna tsaye ba za ka gane meye a rubuce ba sai ya yi sign da tap me.
Sai akan gado ma duk ya zuba jajayen flowers masu shape na heart abin gonin ban sha'awa.

Sai kusan karfe takwas suka kawota lokacin Dr Hameed ya tafi masallaci sallah,yana zuwa kuwa abin da yayi tozali da shi kenan Aazeen laulube da laffaya baya ganin komai nata sai gyalen cikin zuciyarshi ya ce what a surprise,nadauka ba za Ku kawomun ita ba ai, ya ayyana a zuciyarshi.cikin girmamawa ya gaishe da ammi,sannan ya juyo ga Fatima,ya ce sannu da kokari Fatima ya gajiya ?
Ta amsa da alhamdulillah.gaba daya sai nan nan yake ya kasa sukuni har Ammi ta gane yanayinshi sai ta ce da Fatima tashi mu koma sai da safenku sannan su ka bar part din.
Su na fita ya yi sauri ya matso kusa da ita sosai har ya na jin hucin numfashin ta.
Kanta a kasa kuma a rufe sai ya ja luffayan ya bude kan nata ya ce,ki dago fuskarki ki duba angonki please.
Ta dan dago ta dubeshi ido cikin ido ya yi mata kyau sosai sai ya ce ki ta shi ki dauro alwala mu gabatar da sallah.
Ta,ce ina da alwala sai da na idarda sallar isha'I muka zo.
Ya ce fine bismilaah za mu gabatar da sallah raka'a biyu domin Mika godiya ga mahaliccinmu.
Sai da suka idarda da sallah sannan ya Kama kanta ya yi addu'o'I,sannan ya yi mata tambayoyi akan addininita.
Duk a takure take da yanayin da yake shige mata sai yadan ja luffayar ya ce wannan lullubi haka ki bude kisha iska mana,ya na warwarewa sai,gashi riga rub fitil da shi da babu duk dayane aiko baisan sanda ya ce Tabarakallahu Ahsalkhalikin ba, ganin yanayin surarta.a take kuma ya dimauce ba shiri ya shiga sarrafata tun tana jan jikinta ta na kuma bashi hakuri saboda gaskiya ta tsorata da shi sosai. a cikin wannan dare dai ya mallake ta ta zama nashi na har abada sai Albarka yake samboda mata 100% ta yi sai sumbatu ya ke sirrika ne tsananin miji da matarshi gaba daya ta galabaita domin ya murza ta son ranshi.yanayin da take ciki batada bambamci da budurwa saboda gaskiya sirrikan Ammi ya yi dari bisa dari.






*comment and share*

⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐


*WACECE NI*




✍🏼by

*Fateema Muhammad Suleiman*
Email [email protected]
Wattad teemacool2020



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is ton entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*page* 2⃣5⃣&2⃣6⃣


*wannan page naku ne masoya Aazeen amma wadanda suke comment*


Sai kusan asubah ya saurara mata, bakinta baigajiya da rokonshi da magiya amma duk da haka sai da ya yi ta ribatanta kusan sau hudu sai da ya dawo haiyacinshi sannan ya gane aika aikan da ya yi.
Idanuwanta luhu luhu duk sun kumbura saboda kukan

Please Login or Register in order to submit comment