Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jirgin wato sailor.


Mr *suhaib* sai matar sa *Arub*,sai *Afsheen*,da karamin dansu , *Aasif* suma jirgin su daya....tafiya ne mai dogon zango sukeyi acikin ruwa .

kowa kuma da hanyar da yadauka yayin da su *vaishali* suka dauki hanyar da sailor din ya ce suje ganin wani sabon species na halittar ruwa da ya baiyana ,
Wanda su kansu turawan basu San da shi ba ana dai yin bincike akai yawancin mutane da suke makota da wannan wuri suna ziyartar wajen domin ganewa idanunsu labari.


tafiya sukeyi kusan na awa daya amma basu iso wajen ba ga yamma yagabato sai kai ji sukayi wani ruwa da yayi bori sai ko jirgin na su tuni yafara tangal tangal,sailor ya kasa controlling jirgin sai tajuyo tare fadin kowa yayi addu'a according to your faith coz Allaah ne kadai zai fiddamu cikin wannabe bala'in da yakeson samunmu a rikice yake musu bayani
*vaishali* da *Aazeen* kam sun rungumi juna babu abin da sukeyi sai kuka,babu Mai basu hakuri haka ruwan yayi ta tafiya da su.cikin ikon Allaah sai ga wani babban dutse jirgin yayi Karo da shi to a sannan ne ya daidaita Ya tsaya tashin hankali kenan Wake ne abin ban tsoro ga gari yafara duhu duk suka fito daga cikin jirgin
*Aazeen* da tun abin nan ke faruwa ta kakkame jakkarta domin dukkan bayananta suna cikin jakan.

yadda sukaga dare haka sukaga rana acikin wannan dokan dajin ga uban sanyin da akeyi babu kakkautawa da taimakon wannan sailor mai suna *Aamil* ya dauko musu babban bargo acikin jirgin cikin su babu Wanda Ya runtsa idon shi har gari yafara haske....


*vaishali* da *Aazeen* suka nemi taimakon *Aamil* yadebo musu ruwa sukayi alwala kasancewar shi bayahude ne yawanke fuskar shi ya zauna agefe yana kallonsu suna sallah abin ya matukar burge shi, ganin su yara amma duk da halin da suka shiga ciki baisa sun manta mahalicci su ba...

dan guntun biscuits ne da yasaura suka sanya abakinsu zaune suke cikin jimami
daga can nesa suka hango tutar jirgi ke gabato su.


habawa sai duk suka Mike tare da daga rigunan na jacket don agane suna neman taimako. hakan kuma suma 'yan cikin wancen jirgin suna hango Kamar ana neman taimako saboda haka suka rage gudunsu har suka iso wurin sai ga yara da dan madaidaicin saurayi.

Batare da neman bayani ba domin ganin yanayin su da jirgin da ke kusa da su zai tabbatar maka da ba karamin Abu ne yakawo nan ba .

saboda wannan karamin jirgin baya zuwa irin wuraren nan saboda hatsarin haduwa da manyan kifaye Kamar su shark......

haka sukayi ta tafiya
sudai basu San ina aka dosa ba sun dai san sun kubuta a wannan dokan dajin....sai dai wani masifa da suka fara fuskanta acikin wannan jirgin to ganin mata tsirara haihuwar uwarsu ga mazaje ko wannensu dauke da mace tsirara a cinyarsu....

ga wani mutum da tun shigarsu *Aazeen* yake ta kallonsu mikewa yayi yazo kusa ita yace beauty hey can I sit here ya nuna mata kujerar kusa da ita?

bata ce uffan ba sai dai watso mishi kallon tsoro ta kankame jikinta sosai.

shi ko yakamo hannunta yayi mata kiss cikin fadin wow gorgeous I like your skin.

Ta hankade shi da duka kafin ta sannan da gudu ta bar wajen ta koma wajen *vaishali* ta kankame ta Allaah sarki idan ka gansu abin tausayi......


gefensu Mr *suhaib* kuwa sun shiga tashin hankali sosai *Arub* kam sau biyu take suma ana zuba mata ruwa tun yamma har dare, ma aikata suna binciken inda wannan karamin jirgin su yayi toh da aka gano jirgin, kuma annemesu kaf jejin babu su babu dalilinsu.

toh da aka kawo musu wannan labari ne, take ta suma.gaskiya suna cikin tashin hankali marar misaltuwa ,yara har biyu ga yarinyar amana da basu San ta ina zasu fara fadawa iyayenta ba....

haka rayuwa ta kasance musu su acikin wannan jirgin da babu abin da akeyi sai holewa zakiga mace ta kwanta agaban kowa na miji na zina da ita...
*Aamil* ma da yake Dan taimakonsu to yasamu bayahudiya 'yar uwarshi, yaje can suna shake ayarsu....
haka rayuwar *vaishali* da *Aazeen* takasance cikin wannan jirgin wannan mutumin da yake damun *Aazeen* yake taimaka musu babu yadda suka iya domin suna neman taimakon....
har tsowan sati suna cikin wannan Jirgi, daga wannan country sai wannan idan sun tambaya nan Australia ne ace musu A'a daga baya ma da suka dame su da tambaya cewa sukayi wannan jirgi bazai bi ta Australia ba.

duk gunda muka sauka nan ne gunda zaku sauka asali ma bama bin cikin gari saboda mu kammu bamu yarda da kammu ba idan kuma zaku bi mune toh,

Muna da ayyuka sosai da zaku iya yi da ganinku zaku kawo mana kudi cikin wannan harka...

daga wannan bayani ba Wanda yasake kulasu......
kuka sukeyi ba kakkautawa tunanin gida da iyayensu fal cikin ransu da gatansu da komai gashi kaddara ta jehosu cikin wannan kazamemmen rayuwa.....

please share and comment
the contents is the copyright of the writter

⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐


*WACECE NI*



✍🏼 by

*fateema Muhammad Suleiman*

Email [email protected]
Wattpad teemacool2020


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```


https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*Readers nayi matukar farin ciki da comments*
*Wannan shi yasanya ni* *kwarin gwiwar cigaba da rubutun Ana tare*


*page* 7⃣&8⃣



Rayuwar bar, rayuwa ce ta fitsara da tsabawa Allaah karara ga marasa addini, basu san ma sabo sukeyi ba.
toh waye ma yasan akwai addini awajen balle akai ga aikata shi.

haka suka tsinci kansu acikin wannan rayuwa yau kwana goma kenan suke shawagi,acikin wannan jirgin.
sun yada zango ne a gidansu dake kusa babban kogi.wato bar kenan, mata da maza ne sanye da kayan swimming,
wadansu suna cikin ruwa wadansu ko suna hutu bisa kujerun hutawa.

*Aazeen* da *Vaishali* ma sun fito amma su dogayen riguna ne sanye ajikinsu Wanda Mr *Paul* ya kawo musu kala uku uku don yalura basu da kaya...
Domin suma sun fara sakewa ganin sun cire tsammanin samun gida.

Kowa kuma harkar gabansa yakeyi matan kam gwara maza akansu dan tunda suka shigo jirgin babu mace daya da ta taba tanka musu.

sabani da mazan, suma kuma maganan da zasuyi maki bai wuce na batsa da zuwa su rungume ka ko su manna maka kiss din dole ba.

haka rayuwa tayi ta gudana ahankali Ibadan da suka,yafara fita,suka saje acikin su domin yanzu sun fara sabawa da yanayin wurin.

Yau shakaransu uku awannan waje ,'yan gida kam sun cire tsammani da su dan sun dauka ruwa yatafi da su ko kuma shark...

haka suka je Nigeria suka labarta musu aiko *hajja fanna* suma ba adadi daga baya kuma suka rungumi kaddara da fatan Allaah ya bayyana su rokon Allaah kam suna kanyi ga sadaka duk jumuah suna cirewa malaman tsangaya tsangaya...

Tsowon zaman da sukayi amma babu Wanda Ya taba yin sex da su.

domin dokan kungiyar ce ba'a sex da macen da take musu aiki..
Aikin kuwa shi ne exchange ne tsakanin su da manyan smugglers na cocaine and heroin

To duk lokacin da bukatar hakan ta tashi su ake turawa wajen ansan kudin......

Samari kuwa sunyi cha akansu ganin su 'yan mata sabon jini, acike suke dub da su boobs da hips kam ba magana Masha Allah....

*Aazeen* ce sanye da dogon wando da dan karamin riga hannunta rike da mug coffee ne neman *Vaishali* yafito da ita.

Sai ko ta hangenta daga can nesa tare da saurayinta *David* da sauri ta iso wurin, tare fadin cewa haba soulmate shi ne kika barni tun dazu nake ta kewarki cikin shagoba take maganan..

itama cikin kulawa ta mike ta rungumeta tare da bubbuga bayanta ahankali tace Kiyi hakuri habibty kina barci ne and I don't wanna disturb to wake you up but am so sorry...

*David* kam gaskiya 'yan matan na burge shi akwai nutsuwa tattare da su zaman wannan waje sam bai kamace su ba haka kawai yake jin zai taimaka musu....

duk yadda za'ayi sai yadauke su duk da hatsarin yin hakan agare shi, domin mutanen da suke karkashin su kungiya ce na , *kill man no case*.

*Aazeen* ce kwance bisa gado wando short nicker da half vest ajikinta kasancewar *Vaishali* tabi *David* sunje yin shopping.

hankalin ta duk akan waya tana daddannawa bataji shigowan kowa ba sai ganin mutum tayi, yafado gadon gadangadan zatayi ihu ya toshe mata baki da hannun shi..

Cafkota yayi zuwa jikinsa tare da finciko dan karamin rigan sai gashi tantsa tantsan boobs a tsattsaye sun baiyana.

habawa, ai bai San lokacin da yakai bakinsa kan nipples din ba arikice ya ce beautiful ganin nonon das da su..

Ita ko ture shi take da dukkan karfinta da yagushi sai winsil winsil ta ke.
Cikin zafin nama ya damke hannayenta duka biyu tare da fadin stop it don't text my anger,dole ne fa yau indauki rabona,
koda zai kasance wannan karshen zamana cikin wannan kungiyar...

dubi kayan more rayuwa ya tallabo breast na ta amma akafa wani dokan banza.ganin da tayi yana kokarin cire dan guntun wandonsa,
batasan lokacin da karfi yazo jikinta ba aiko ta takarkare ta bugi gabansa.

cikin tsananin jin zafi ya damke wajen yafadi kasa yana murkususun zafi,
Tana ganin haka ta wafce bed sheet,ta yafa ajikinta da gudu tayi waje.

daidai *Vaishali* da *David* kuma sun danno Kai zasu shigo apartment din sukayi Karo da ita.

*Aazeen* cikin kidima ta rungumeta ta fara kuka tare da nuna dakin da hannu.

ta fara tambayar ta habibty ya dai what is happening?
*David* kam bai jira yaji me zata ce ba yayi cikin dakin da gudu.

Turus yaja ya tsaya ganin *Sam* kwance a tsakar dakin hannun shi duka biyu a kasan shi.


*Aazeen* da *Vaishali* sun tsaya daga can nesa ,cikumo shi yayi ya tsayar da shi tare da cewa you mother pucker
how dare you ya kasa karasa maganan saboda tsaban bakin ciki sai naushi da yakai ma bakinsa aiko tuni jini yafara fitowa dagadaga yayi mashi sannan ya jehoshi waje da yi mashi kashedin na karshe...

Ya zama dole kubar nan wajen cikin satin nan zan Nemo muku mufita.
yazo kusa da *Aazeen* ya dafa bayanta cikin lallashi yace beauty Kiyi hakuri komai yazo kusan karshe
sannan ya sumbaci *Vaishali* yayi musu sallama ya tafi..

cikin sauke numfashi *Aazeen* ta shigo dakin ta sanya dogon riga Marar nawi,
Sun zauna tana duba shopping da suka zo da shi, yayin da take labarta mata abin da yafaru...

*Aazeen* ta ce gaskiya dole mu dage da neman ahlinmu kar mugaji muyi ta watsa labarin mu da hotunan mu through net ko Allaah ya taimakemu agano ibda muke duk da cewa hakan da Kamar wuya amma bazamu gaji ba nan wajen Kuma zamu barshi sooner than later...

cikin gyada Kai *Vaishali* ta ce by the grace of God we will try our utmost best...
cikin wayo da dubara *David* ya nemi izinin
Abokin shi suka Nemo musu dan karamin apartment kusa da su.

To ba laifi wajen yayi kuma da wuya a gano su
yanzu kam ba su da fargaban 'yan iskan nan sun sake suna kuma yin sallah duk da ba daidai sukeyi ba....

*Aazeen* ce ta sanya ta kardunta da hutunan iyayenta da yayyenta agaban hawaye fal sun cika mata idanu cike da shuki da kyawarku

ta ce nayi missing dinku ko yaushe Allaah zai Sada mu da ku? *Vaishali* da ke gefenta itama kukan takeyi ta ce ai gwara ke kina samun ganinsu koda a picture ne nifa tunda da muka rabu da su sai dai inyi imagining nasu ko hoton mutum daya bani da shi wayyo Allaah ka kawo mana mufita...

wunin yau haka suka yi shi cikin jimami...sunyi dai kudirin nemowa kansu mafita....





********





karfe daya da minti takwas na dare *Aazeen* ta tashi da mummunan ciwon Kai,nishin ta ne ya tayar da *Vaishali* daga bacci cikin rudewa ta matso kusa da ita,tare da tambayar ta me ke damunta ?kanta adafe ta ce sister ki taimakemu ni wallahi mutuwa zanyi, kaina kamar ana bugamun da dutse nakeji

dukkansu kuka sukeyi gashi cikin dare, kyalle ta samu suka daure kan, amma babu sauki .
Allaah Allaah suke asubah tayi suje asibiti.....








*share*
*comments*

⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐

*WACECE NI*





✍🏼 by

*fateema Muhammad Suleiman*

Email [email protected]
Wattpad teemacool2020


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```


https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*Readers nayi matukar farin ciki da comments*
*Wannan shi yasanya ni* *kwarin gwiwar cigaba da rubutun Ana tare*


*page* 9⃣&🔟


Daga *Aazeen* har *vaishali* babu Wanda Ya runtsa har Asubah.
A daddafe suka idar da sallah sai ga *David* ya na mu su knocking da sauri *vaishali* ta bude kofar idanunta fal da hawaye sosai shi ma hankalin shi ya tashi da taimakonshi su ka sanya ta a motor sannan su ka wuce asibiti....

Su na isa taimakon gaggawa ta samu saboda tun kafin su iso ya sanar da su da zuwansu.

An debi sample na jini da fitsara abin da Dr ya yi requesting urgent pcv, random blood sugar, sai test na widal and mp.

Cikin sauri aka yi urgent pcv din kuma ya nuna normal sai random blood sugar shi ma normal sannan suka sanya ma ta dextrose saline, bayan Kamar awa daya jikin ya danyi sauki.sai ga sauran results din ma ankawo kuma komai normal....

Dr Thomas Ya Kore a fannin malignancy wato cancerous cells kasancewar cikin kwanakin nan suna samun case din sosai duk patient da su ka kawo complain irin na *Aazeen* to idan aka yi test results ya na nuna akwai cutar ba tare da bata lokaci ba ya ba ma David shawarar yin test din Alpa protein.
Hakan kuwa aka yi kuma ya nuna ta na dauke da cutar cancer na kokolwa (canccer of brain )

Ba karamin kidima su ka shiga ba da jin wannan labari an gwada, kuma ta na stage one cikin gaggawa aka fara yin chemotherapy treatments kafin daura ta akan radiation treatment cikin kwana uku duk ta fita haiyacinta saboda chemotherapy ya na matukar wuya gashin kanta duk ya zube kan ya zama Kamar maku tal ba gashi gaskiya duk wani mai imani dole ne ya tausayawa wannan baiwar Allaah.

Da taimakon Dr Thomas da David ne ake samun ta ke dan sausauta kukan ta da kuma cin abinci ko da kadan ne vaishali ma duk ta fada saboda jinyar 'yar uwar ta da ta ke.

Ahaka suka share wata uku a asibiti amma yanzu kam Alhamdulillah jikin yana sauki sosai yana responding treatment.

sai da ta yi wata uku da sati daya sannan aka sallomo ta.su ka koma gida sai dai sati biyu biyu za ta dinga zuwa follow up.

Yauma su na zaune da vaishali ta na kwantar mata da hankali , *Aazeen* ta ce sister ina tausayin Kai na sannan ina tausayin mu gaba daya yanzu idan na mutu shi kenan labari na ya wuce ahlina baza su taba sanin gwagwarmayar da na sha ba har na koma ga mahalicci na.

Vaishali ma cikin tausaya ma ta ta ce in sha Allaah sis ba za ki mutu ba Za mu ga ahlinmu..

Haka kullum suke cikin juyayi har ya za na yanzu ta cire dukkan damuwa a ran ta shawarwarin da Dr Thomas ke yi ma ta kuma duk ta na bi.

Yau Sun fito bakin kogin dake gefen unguwar su su na dan hutawa sai *Aazeen* ta dago Kai ta na furkan ta vaishali da ke wanka a cikin ruwan ita ma ta ba ta full attention na ta sosai.
ta ce sis ina da shawara akan wannan abin da ya sa me ni jiya ina karanta wata jaridar insider na ga abin da ya ja ra 'ayina sosai, kuma mafita ne ga abin da na ke ciki kin ga Doctors sun tabbatar mun da cewa chances na rayuwa ta ba zai wuce shekara daya watanni ba kin ga bani da tabbacin za mu hadu da family mu may be ma a lokacin na bar duniya shi kenan tarihi na ya za ma babu duk wannan abubuwan da nayi encountering ba za su taba sani ba tun da har yau babu mu babu labarinmu duk iya kokarin da muke har yanzu shiru tabbacin ba su farga da sakonnin da mu ke ta turowa net ba duk da power dake kan net Allaah baisa sun gano mu ba kawai ina ganin akwai abin da Allah ke so da mu ta kasashe zancen ta cikin share hawayen da ta kasa controlling dinsu.

ita ma vaishali da tun ta Fara magana ta zo kusa da ita ta zauna ta rike duka hannayenta biyu to ita ma hawayen ta ke duk da ba ta ji shawarar da ta son yankewar ba. ta dai barta taci gaba da yin hawayen don tasan wannan kadai zai sanyaya zukatan su.

sai da ta dan samu relieve sannan ta ce I have an idea of doing artificial insemination.

Vaishali cikin tashin hankali marar misaltuwa ta ce sis kinsan abin da kike fada kuwa?
Cikin jinjina Kai ta ce na sani sosai kuma ina cikin hayyaci na nake maki wannan maganan.

sannan ta ci gaba da cewa kinsan da angano gunda da muke komai daren dadewa toh lokacin ni fa na bar duniyar ma saboda ba ni da tabbacin cikakkun shekaru biyu masu kyau toh kin ga samunki zai sanya mahaifiya ta cikin tsananin damuwa karshe ma ta rasa ranta saboda dalilin rashin samuna na kin san ni daya Allaah ya arzurta su da samu sai maza biyu na san kuma iyayenmu baza su taba cire tsammani da mu ba.
Saboda haka na yanke shawarar yin shi, kin ga bamu taba yin zina ba Allaah ya kiyaye mu toh jiya sai na yi Karo da lab din da su sayar da sperm donor duk Wanda ya ke da sha'awar samun yaro zai biyu kudade sai ahada da Kwan mace sannan za ta Haifi cikekken yaro ko yarinya. Kin ga idan har na samu na yi haka koda bani nan a duniya,ina da Kwan da uwa ta za ta gani ran ta ya dan kwanta.
Daga wannan ba ta kuma cewa komai ba,ta na son jin abin da vaishali za ta mayar ma ta ...

lallai sis baki kawo shawarar da zan iya dauka babu. ince Ki yi wannan gurbatacciyar shawarar da zuciyar ki gindaya maki ina kika ga gun da iyaye za su yi farin cikin samun yaro ba tare da uba ba duk da na ki shawarar za sayi sperm ne a ki kenkeshe da kwanki wannan ma ba mafita ba ne gwara ki ce aure to da dan dama.

waye ki ke ga zai aure ni a wadannan kwanakin da suka ragemun mutanen da basu ma da addini balle sanin kaddara ko tausayi.

Allah ya sani bazan yi zina ba amma insemination kam dole zan yi before then zan nemi shawarar Dr Thomas idan har ya ce zan iya rainon cikin a wannan yanayin to ni kuma na shirya.

ke abin da nake so daga gareki zaki rike mun abin da zan Haifa duk lokacin da aka samu labarin mu sai ki hada dukkan takarduna da yaron ki kaina mahaifiya ta.

Vaishali ta sake rike hannayen na ta da karfi ta ce sis toh gobe za mu ga Dr Thomas idan ya ce babu matsala shikenan kuma in sha Allaah zaki samu sauki har ki warke gaba daya har agano inda muke, ta sanya hannu ta na goge ma ta hawayen ta.
*Aazeen* ta jinjina Kai ta ce nagode sis I love you.
ita ma ta mayar mata da I love you too abar kaunata.

hakan kuwa aka yi yau tun da su ka yi sallar asubah ba su kuma kwanciya ba,su na lazimi har gari ya yi haske suka shirya dukkansu jacket su ka sanya ,su ka Kama cab ya kai su asibiti.
Duk da sammako da su ka yi sun iske Dr Thomas a office, cikin fara'a da sakin fuska ya tarbesu.

Bayan ya dudduba ta kuma yaji dadin yanayin da ya ganta gaskiya jikinki ya na responding treatment na ji dadin hakan ki cire damuwa a ranki a hankali komai zai zama normal.

ta ce nagode Dr. Cikin sanyin murya ta ke maganan sannan ta gaya mashi shawarar da ta yanke.

ya tsura ma ta ido na seconni sannan ya ce shawarar ki ma abin dubawa ne, amma sai mun tabbatar bazai kawo bara zana da lafiyar ki ba.

Da yake su wannan abin is normal thing ne bai dauke shi da wata matsala ba toh su mace lafiyayya ma sai ta ce bazatayi aure ba kawai zata je lab ta sayi sperm din kuma ta haihu yaro ta girmar balle wannan da yazo ma ta da darura ai shikenan nan fadawa ce ta zo daidai da zama.

Bayan gwaje gwaje da suka yi ma ta da taimakon Dr Thomas aka nuna mu su tube kusan number dubu daya.
aciki Dr Simon ya ce su zabi tube number 489, suka biya kudaden da ake bukata sannan aka yi komai,sannan su ka ba ta sati biyu ta komo su duba ta.....
magunguna ya Kara rubuta ma ta Wanda za ta sha na sati biyu din.

sannan su ka dawo gida.





*share*
*comments*

⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐


*WACECE NI*

✍🏼 by

*fateema Muhammad Suleiman*

Email [email protected]
Wattpad teemacool2020


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```


https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation



*page* 1⃣1⃣&1⃣2⃣






Su na dawowa gida *Aazeen* bathroom ta wuce ta sake shower akan ta sai da ta ji sanyin ruwan ya ratsa ko ina na jikinta sannan ta fito,ta iske *vaishali* bisa dinning table gaban ta duk kayan ciyeciye ne da ta girka tun kafin su je asibiti.

Ta na zama ta ce nifa coffee kadai zan sha coz ba na son cin komai a yanzu.

Vaishali dai ta dan ci kadan sannan dukkan su su ka mike da cup dauke a hannunsu falo suka zauna,ta kunna musu Deen TV taji dadi program din ta kuwa ake yi Wanda sheikh Asim Alhakim ke gabatarwa yau topic din su akan Al'ayn (kambin baka)evil eyes da turance.
sheikh ya yi dogon bayani akai inda ya ce
Hakika Annabi saw acikin hadisi ya na cewa Al'ayn hakk kambin baka gaske ce, hakika Al'ummata bayan kaddarar ubangiji to toh kambin baka ce ke kashe su.saboda haka duk lokacin da ku ka ga Abu ya burgeku toh ku sanya albarka a wannan abin domin sanya albarka zai kawar da cutar da 'yan uwanku ka ce, tabarakallah Masha Allah.

sannan ya yi bayani yawancin cutuka yanzu ya na faruwa ne bisa dalilin kambin baka.
Musamman wannan cuta ta cancer.

Ga addu'a da sheikh ya bada vaishali ta na rubutawa Kamar haka,
Bismillahi, A'uzubillahi min kudratihi min sharri ma ajidu wa uhazir .

Marar lafiya zai rike wajen ciwon,sai ya karanta wannan addu'ar sau bakwai

Sannan cutar cancer marar lafiyar ya kasance ya na shan nonon rakumi da fitsarinsa tsawon watanni shida. Yadda zai sha kuma gorar robar ruwa na nonon sai fitsari kuma daidai murfin robar sai ya hada ya sha in Allaah za'a samu waraka.

Gaskiya sun ji dadin shirin kuma sun karu musamman *Aazeen* da ta tattara dukkanin hankalin ta bisa ga shirin ta kudurce a ran ta duk za ta bi abin da sheikh ya yi bayani akai.

David su ka sanarwa cewa su na neman nonon rakumi da kyar ya samu irin Wanda ake shigo da shi daga yankin saudia saboda su ba su da rakumi a yankinsu.

Kuma ta dage shi ta ke ta sha kuma ta na jin dadin yanda jikinta ke samun sauki.

yau sati biyu kenan kwanakin da likitocin ta su ka bata,tun da safe ta shirya ta je asibiti sai da ta fara zuwa wajen Dr Thomas ya duddubata ya kuma rubuta ma ta magunguna.sannan su wuce wajen Dr Simon test su ka rubuta serum and urine pt, bayan sun dau sample na jini suka ba ta Universal

Please Login or Register in order to submit comment