Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

iya dagulewa.

      ****
Tun bayan dawowarsu,Umma daga jinyar, Alh hammayo, duk lokacin da ta zauna tunanin Shkurah yake damunta, har ta rasa inda zata cusa kanta, dan ko barci take, abu ɗaya, take gani.

Haka kawai ta fara, wasi-wasi, a ranta dan har addu'a tayi, sosai amma bata fasa jin shkurah, a ranta ba, duk abin duniya ya dameta, tun mutane gida basu gane halin da take, ciki ba, har sai   da ranar ta, yanki jiki ta faɗi,

          A guje akayi asibiti,da ita, cikin tashin hankali dan babu wanda yasan me ya kawo haka.

                 Likitar mace ce, akanta, bayan ta gama, saka mata ruwa ta fita, gurinsu Abubarka da bilal, dan sune suka kawota sai Ummi, kallonsu matar tayi, cikin fara tace.
"Alhamdulillah, jikinta da sauki jinintane ya hau, amma insha Allah, zuwa anjima zata farka amma don Allah a kiyayye abinda zai ɗaga mata, hankali."

   Miqa masu, takardan magani tai, sannan tayi tafiyarta,


         kwanakin Umma biyar aka sallameta, jiki da sauki ba laifi sai dai bata fiya son magana bane, sai da shkurah karama, ita kaɗai ce ke tayata hira.

      ****
A hankali take, buɗe idanunta da suka mata dishi-dishi, yunkurin mikewa tayi, amma tajita gam a jikin abu sake rufe idanunta tayi, da karfi zuciyarta na bugawa, wanda ba kome ya kawo, haka ba, sai jin numfashinsa da kamshin turaren da bazata iya mantawa dashi ba, a rayuwarta juyawa tayi daidai inda yake, ta kalle fuskarsa, zuba masa idanun tayi, a hankali ranta yake ɓaci wanda bata san dalilin haka ba, kokarin mikewa take, ayya yana barcinsa cikin nutsuwa haɗa karfinta tayi waje guda, ta hankaɗeshi.

Abinda yasa ya farka kenan, cikin firgici tare da zaro idanunsa waje yana.

     Cikin farin ciki, ya isa gareta, yace,
"My dear har kin farka, sannun bari na nima miki brush ki wanke bakinki Alhamdulillah."

     Watsa masa, wani malalacin kallon tayi me ciki da tsantsan kiyayya, tace.
"Kaga malam ina ne nan, ka kawoni wato ku abin kunya a jininku yake, shi yacutar dani, kai kuma ka, ɗaukoni nan ka maidani gurin iyayena kafin na tara maka mutane, na tsani ganinka bana kaunar ganinka, kafita min, a ɗaki idan kuma dan jikina kake bibiyata zo gashi, ai ba wani abin kunya bane a gurinku."

Lumshe idanunsa yayi, ba karya,magaggunta sun masa zafi, ji yake kaman ta fashashen ruwan dalma ake, watsa masa murmushi ya sake mata, sannan yace.
"Eh baki san, nima abinda nafara bakenan, ai daga zuwanmu nan, ai na ɗanaki yafi sau goma, gaskiya, kina da garɗi tashinki nan ma, da kika ganni amakale dake nagama, danakine gaskiya ina jin kunyarki fa,"

        rufe fuskarsa ya shiga yi, bakin ciki da ɓacin raine ya baiyana, karara a face ɗinta, hawayen da take dannewa suka, kuwa ɓalle daga idanunta, bata san lokacinda ta fashe da kuka ba, me ɗaga hankali take ya ruɗe, yazo gurinta ya rike hanunta yana bata hakuri tare da rantse mata wasa yake, kuma ba zai kuma ba, tayi hakuri tureshi tayi, cikin masifa, tace.
"Ka maidani gidanmu, nace bana son, ganinka inba haka ba, wallahi zan gudu,"

     ɗago kai yayi, yana kallonta mamaki ya rufe shi, yace.
"Ok, bari nakira dr ɗin su dubaki  Insha Allah, gobe zamu bar nan zuwa gida kinji."

        Ko kallon inda yake batayi ba, tace.
"Better"

          mamaki fal, ranshi yafita, sai gashi tare da likitotin da suka mata, aiki nan aka shiga dubata, bayan sun gamane, sukace.
"Babu, wani matsala zasu same sallama amma sai next wee.."

       Ai baikai karshen maganarsa ba, tajefa masa wata uwar harara, wanda ya hana shi karasa harafin karshe, takalleshi ta kalle sunanshi da yake jikin rigarsa tace.
"Yau!!!! zan bar asibitin nan, idan kuwa kuka, ki zan gudu kuma idan nafita nace, satone kayi akawoni nan dan ka"

         tass ya ɗauketa da mari, ciken zafin rai yace.
"Duk abinda zakiyi, ya kare akaina banda kowa, badan nasan wacce tabaki tarbiya ba danace baki dashi, na lura ke zuma ce sai an shaki da wuta,kuma sallama sai next wk kiyi abinda zakiyi."

      Aikuwa ɓare baki, tayi ta hau kurma musu ihu, abinda ya ruɗar da drs ɗin kenan take suka, sallamesu hotel ɗin da suka, sauka ya maidasu ɗaki ɗayane, ya kama a madadin biyu,

   Tun asibiti take kuka, har suka iso hotel ɗin banza yayi da ita, sannan ya shiga ban ɗaki yayi wanka da alola yafito ɗaure da towel, ɗagowa tayi suka, haɗa idanun runtsa idanunta tayi, ta soka kanta tsakiyar cinyarta tana kuka, kayansa ya ɗauka ya koma banɗakin yasaka sannan yafita, inda yabada oda akawo mata abinci.

Kuyi hkr, da wannan kusan typing ba sauki......💋
3/4/21, 9:47 AM - Ummi Tandama: *🙆QADDARAN RAYUWATA🙆
MAI DAMBU CE*






Afuwa.......👏
*Page 19*

Yanda aka, kawo abinci haka ya dawo yasamu, har ita ɗin, mamakine, ya turnike shi taɓe baki yayi sannan ya shiga bandaki yayo alola, sannan yafito yayi sallah,

                ya jima,akan abin sallar kafin ya tashi inda take yaje ya zauna yana kare mata kallo, lumshe idanunsa yayi, sabida kukan da take yana taɓa zuciyarsa a hankali yakira sunanta, amma ko taɗago kanta asalima sake cusa kanta tayi, ta cigaba da kukanta.

      Shiru yayi yacigaba da kallonta, dan ya rasa me zai ce mata, tunda ya lura tana bukatar kukane shi yasa takeyi,

            Janyota yayi, a hankali ya rungumeta, sosai tureshi take tana kara kukanta, bakinsa yakai kunnenta yana mata ynda akewa kananun yara idan suna, kuka "seeeeee......"
         A hankali yake bubuga bayanta, har tayi shiru cikin nutsuwa, yace mata.
"Kinyi sallah kuwa,"

     shirun da yaji tayi yasa, ya leka fuskarta idanunta yagani, a rufe taɓata, yayi yace.
"Kinyi sallah kuwa? idan bakiyi ba tashi kiyi kar lokaci yatafi."

         Mikewa tayi, daga jikinshi ta shiga banɗaki, kafin ta fito ya shimfiɗa mata, abin sallah tana fitowa salla ta gabata, tana idarwa ta kwanta a gurin ko minti biyar batayi ba barci yayi, gaba da ita.

       Zama yayi, yasata a gaba yana kallonta cikin nutsuwa, shi kaɗai yasan yanda sonta yake ɗawainiya da shi,

......
             Karfe uku, saura kwata na dare ya tasheta dan hudu da rabi zasu bar chicago, har yagama haɗa musu kayansu, mika mata brush yayi taje tawanke bakinta mika masa tayi, karɓa yayi sake mika mata wata doguwar riga yayi, da gyalenta,

         A gurguje tasaka, dan taga sai, kallon agogon hanunsa yake, yana kallonta yana son mata magana, amma yasan ba lallai bane ta amsa masa,

            jakarsu yafito musu, sannan ya juya, yace.
"Bamu da lokaci, in dan ne ki shirya a nutse, zan iya jiranki har iya karshen rayuwata, ba xan gaji ba, kuma bazan damu ba, kuma zanji daɗin haka pls ba dan ni ba, ko dan sonki da kowa gida, ki hanzarta."

               Fitowa tayi, bayan t ɗaura gyalenta ɗaukar handbag ɗinta tayi, tafito dan tabashi haushi tashiga tafiya kaman me jin tausayin k'asa, tafiya yayi wajen lifter ya buɗe ganin da gaske tafiya, zaiyi yabarta yasa ta haɗa da gudunta,

       tana zuwa, dab dashi yashi itama tabi bayanshi, tunda kofar ta rufekanta, ta koma gefe, ta takure kanta, haɗi da kame jikinta, waje guda ganin haka, yasa yayi banza da ita har suka sauko kasa,

        fita sukayi daga, otel ɗin suna waje me taxi tana jiransu, har airport ya kawosu.


          Sun jima kafin jirginsu, ya tashi, sai da suka biya ta Ethopoeia, hutun awa biyu sukayi sannan suka sake ɗauko hanya,


           ****
Karfe goma, nasafe suka sauka a garin kano, wani jirgin ya biya musu, zuwa bauchi, sun iso sha biyu, saura kwata.

        Suna isowa, ya kira yaronshi yazo ya ɗaukesu, kallon yaro yayi yace.
" Ka kaimu,gwallaga"

        tunda suka, iso take share kwalla dake taruwa, a idanunta gashi jikinta yayi mugun sanyi, a haka suka iso unguwarsu har kofar gidansu tunda motar ta tsaya, ta rike hanunsa, cikin kuka tace.
"Toh ynz me zance musu, idan nashiga ciki, ina jin tsoron Baba kar yasake korata, don Allah ka kaini wani waje, ina jin tsoro."

         Zuba mata idanun yayi, cikin damuwa, dan sai yanzun yayi danasanin tafiya da ita har na tsawon wata uku, batare da sanin iyayensa da matarsa ba, toh idan ya kaita, ciki me zai cewa umma idan ta gansu tare,kar tayi tunanin daman yasan inda take, ya ɓoye mata hura iskar bakinsa yayi, sannan ya cire hanunta, daga rikon da tayi masa,

            share mata, kwallar dake fuskarta yayi sannan yace.
"Ki nutsu, mu shiga babu abinda zasu miki, kinji ko asalima kullum dake suke kwana dake suke tashi. Idan zan iya faɗa miki kiyarda shine basu san kina, raye ba amma muje kiji da kunnenki."

             Tare suka, fito daga motar a hankali ya zagayo, wajenta a hankali ya riko hanunta suka haɗa, hanunwarsu suka sarkafe da juna, kusan atare suka kalli juna.

          Shi yake, gaba ita kuma tana baya da sallama suka isa, cikin gidan duk suna tsakar gidan, zare hanunta tayi daga nashi ta koma bayanshi tare da rike rigarsa, shiga cikin gidan yayi,su Ummi da Mama, da Fauziyya, matar Abubakar sai leka bayanshi suke dan cike suke da mamaki kaman, shkurah suka, gani a tare da shi.

        Basu tabbatar ba, sai da ya gaishe dasu ummi, inda ya durkusa, nan duk suka mike a tare,
         suna salati,  fauziya kuwa, ta cikawa bujenta isa, dan ta gama razana,

        Umma ce tayi karfin halin cewa,
"Shkurah, kece ? ko watace me kama, dake ?"

        jijjiga kanta tayi, cikin kuka, matsawa tayi, gurin Ummi rike hanunta mama tayi suka shiga da ita, har falon Alhaji Hammayo, dan umma tana gurinshi.

              Har gaban Alhaji hammayo ta kaita,
 
      mikewa umma tayi, cikin tashin hankali, durkusawa shkurah tayi jikinta har yana rawa,
        cikin kuka, tace.
"Babana kayi, hakuri karka sake korana, idan na tafi, bansan inda zan sake faɗawa, ba ku yafe min wallahi ba laifina bane, kaddarace ta faɗo min don Allah kayi hakuri"

          A hankali umma ta zuba, gwaiwarta a kasa tayi, sujidar godiya kirari takewa, ubangiji kafin tasake kuka, me sauti inda ta tashi tarungume, shkurah Alhaji Hammayo, kuwa shima kuka yake,

         ganin haka, mashkur ya juya yayi tafiyarsa zuciyarsa cike take da farin ciki.

       Ko da ya isa, gida yasame gidan a hargitse wuccewa ciki yayi, ya rage kanyan jikinshi sannan ya faɗa banɗaki yayo wanka, sannan ya sake kaya marasa, nauyi kwanciya yayi, dan ya gaji sosai.

       Hmm, Zubaida nacan ɗaki tana, barcin asara duk ta rame tafita hayacinta,

        tun karfe goma take, barci har ynx da yunwan cikinta yasa ta juya, sannun a hankali ta farka, wanke bakinta tayi a banɗaki.

       Fita tayi, daga ɗakin kicin tashiga taje nimawa kanta abinda zataci.

              Taliya, da manja da yaji, tayi, taci sannan tafito kallon falon tayi, duk yayi kura tsaki tayi, dan tasan laifintane, saunawa ana kawo mata yan aiki,amma suna guduwa, ga aiki amma babu abinci dan dole suke guduwa, bandan ransu nakin aikinba,

ga kishin jaraba, dan yar aiki bata isa ganin mashkur ba koda yazo fita koranta ɗaki ake dan karta ganshi😜

         Shi yasa yaran basu zama ga tsangwama da hantara.

           Sai karfe biyu mashkur ya farka,

      dogowar riga, yasaka sanan yatafi masalaci.

         Aikan yaronshi, yayi yaje ya sayo masa, abincin dan yasan ba samu zayi ba.


       ****
A can gwallaga kuwa, kafin wani lokaci, gidan yacika da yan uwan da abokan arziki ana barka da dawowanta,

              Abinci ma umma ce ta bata a baki, tsakaninta da mutane sai kuka, dan bata taɓa kawowa a ranta iyayenta zasu neminta haka, ba gashi kowa bata labarin abinda ya faru bayan tafiyarta ake,

......

      Bayan kwana, biyu mutane sunyi sauki nan, umma take tambayarta, yanda suka haɗu da mashkur iya abinda tasani ta faɗa mata, suna zaune sai ga kiran Na'im ya shigo nan,

    yake mata mita kashe wayar da tayi, na tsawon lokaci, dariya tayi sannan ta faɗa masa ai wayar ce ta ɓata, idan ba haka ba sai suta rigima sun jima sosai faɗa masa, tayi tana bauchi nan, murna ya rufeshi yace mata.
"Ina nan zuwa, kuma idan nazo zan nime izinin niman aurenki."

        Zuciyarta fess, ta tace.
"Haba, dai ai ba yanzun ba sai na kwana biyu dan nayi. kewar gida sosai,"

      dariya, yayi sannan yace.
"Allah baki isa ba, nida nake so nan da wata gudu, muna tare Wallahi ina zuwa, zan gabatar da kaina"

       Sun jima, suna musayar yawun kafin sukayi sallama,
   Murmushi Umma tayi, tace.
"
Auta mashkurne, naji kuna musayan kalamai dashi."

Kallon umma dan ta manta da shi, a shafinsa ma girgiza kai tayi, tace.
"Wani ne, a kaduna, Na'im sunanshi, shine zaizo niman izinin a wajenku."

"Me kike nufi, Auta mashkur ɗin fa, "
"Umma ni bana, sonshi wallahi kuma ai taimako yayi, dane naso shi, amma yanzun ina son na'im yayi hakuri kawai ya nemi wata, da mata da yawa a garin bauchi bani ɗaya bace mace..."


         "Shkurah, anya kinsan me ake nufi da hallaci kuwa, kinsan abinda kike shirin aikatawa, kuwa, wannan shine Batulci, baki san me ake kira da adalci ba."

    Allah sarki duk wannan maganar dasuke yana kofar shiga falon duk abinda suke faɗa akan kunnenshi be taɓa jin ciwon ace ba'a sonshi ba, sai yau kalmar bana sonshi da take yayi, masa zafi jin sabom tsanar Maina yayi a ranshi juyawa yayi, ya bar gidan.

Ran umma ba karamin ɓaci yayi,ba dan haka shiru tayi, tana kallon shkurah, cikin sigar lallashi tace.
"Uwata, kinga mashkur ɗan yar uwatace, don Allah karki min haka ki amince ki aureshi zaki so shi sosai kinji, ki tayani rufa min asirinki ki amince da soyayyarsa."

           Kallon umma tayi, cikin nutsuwa tace.
"Umma kigane mana, nifa bana sonsh...."





       Ayi hakuri Dearie's💋
3/4/21, 9:47 AM - Ummi Tandama: *🙆QADDARAN RAYUWATA🙆*






_Husna Kamshi, ga wannan shafin kyautane nabawa yan grp ɗinki, bana bukatar godiyarsu Soyayyar dasukewa buk ɗin ma ya wadatar dani ina musu fatan alkhairi_💕💝

*Phatima zahra, na grp ɗin farida sweery ina jin daɗin comments ɗinki keda sauran yan grp gsky jiya naji daɗin comments ɗinku nagode sosai*💋

*page 20*

Bata kai ayar maganarta ba, umma ta kafceta da mari, irin fayau ɗin nan(😹)
      tana kan kujera yaseen sai da ta dunguro, sabida karfin mari.
          Batayi ihu ba, kuma babu alaman kuka daga idanunta hanunta ɗaya yana rike, da kumatunta,

        Idanun umma, sun kaɗa girgiza kafatan take cikin kunar rai, tace.
"Amma wallahi kin cika butulu, mara imani, har kina da bakin cewa baki son mashkur toh bari na faɗa miki abinda baki sani, mashkur shine kaɗai wanda zai aureki batare da, ya miki gori ko wani kallo ba, shine kaɗai zai rikeki ba tare yaji ko ɗar akanki ba, wallahi na rantse miki da Allah bazaki taɓa auran nagartaccen mutum irin mashkur ba, Allah yabaki sa'a. shine abinda zance miki."

      Tana gama faɗin haka tabar falon baki ɗaya ranta na mata, zafi da abinda shkurah tafaɗa mata,

       batayi kuka ba sai da umma tabar falon sannan ta fashe da kuka, zuciyarta cike da haushin mashkur da alkawarin karta masa rashin mutunci idan ya kuskura yazo gidan,

        ****
A gefe guda, kuwa har ankai sadakin Bilal, saura yan kwanaki a tabbatar da aure.

           Tunda mashkur yaji abinda shkurah tace akanshi bai sake zuwa gidan ba, karshe tura drvnsa yayi ya ɗauko masa shkurah, ta musu kwana biyu tana gama kwanakinta, yasa aka maida ita.

       Aiyuka suka sha kanshi, haka ya rage masa zafin da yake ji, gefe ɗaya ga zuby itama tana nata rashin hankali, har addu'a yake Allah yasa a turashi wani waje ko zai huta, da damuwar da take addabarsa.

.....
Kaman yanda,na'im yace aka kuwa ya kasance yazo tun daga kaduna, kuma yasame Alhaji hammayo da maganar niman auren shkurah, shiru yayi kafin yace.
"Kasan bata jima da dawowa garemu ba, kayi hakuri idan an kwana biyu zan nimeka,"
godiya yayi sannan yayi musu sallama tare, da alkhairi

       sun karɓane, da kar yayi wani tunani,

       Kwanansa ɗaya, a bauchi ya koma kaduna.
Bayan tafiyarsa Alhaji hammayo ya tara yaransa baki shiru yayi yana kallon shkurah sauke nauyayyar numfashi yayi a hankali, yayinda yasa hanunsa na dama yana sosa goshinsa yace.
"Zainab, kece kika turo wannan yaron da yazo wajenki ?."

         Jefa mata tambaya, yayi cikinson jin me zatace, duk yan falon suka mai da idanunsu kanta, suna son suje me zatace.
     Sunkuyar da kanta tayi, tace.
"Eh baba,"

         "Toh gashi ni, har na bada aurenki ga Mashkur kice baki sani, yakenan."

          Bakinta narawa, tace.
"Baba kayi, hakuri don Allah ni bana sonshi kawai kubani wanda nakeso."
Rufe bakinta tayi, dan tana gudun kar wani ya muje mata shi,

           A fusace umma tayo kanta zata rufeta da duka,

"Habiba!!! karki taɓata, lokacin yanzun na gyara kuskurene ba na yanke hukunci cikin gaggawa ba, Allah yaga zuciyata mashkur naso ya aureki amma tunda kince a'a ba damuwa ubangiji ya tabbatar da alkhairi.

      Cikin hasala umma tace,
"Nagode da abinda kika min, Shkurah, ni kika kalli idanuna kikace baki son mashkur ko, yayi miki kyau Allah ya baku zaman lafiya, amma ga gargaɗina karki kuma tako inda nake karki kuma kirana da mahaifiyarki, da ina da wata yar wallahi da na bashi amma ba damuwa,"

         tana gama faɗan haka, tafi tabar musu falon kuka take babu wanda ya kulata karshe ma barin falon sukayi, daga ita sai Alhaji hammayo, murmushi yayi sannan yace.
"Tashi kishiga, kiyi kokarin ganin kin bata hakuri, yaron yana da kirkine shi yasa ta ɗauki fushi, bakiga har yarsa ya sawa sunanki, sannan ya ɗauki yarsa yabata, duk sabida ke, shin irin wannan mutumin me yadace asaka masa da shi ?"

         ɗago jajayen idanunta tayi, a hankali tana zubda kwalla masu zafi tace.
"Baba yayi kokari, amma kayi hakuri bana sonshine yaushe zan faɗawa Na'im kana nimansa."

          Kallon mamaki yake wato, tafiyarta nan amadadin tayi hankali da nutsuwa a,a sai ma wani kafirin taurin kai da tazo da shi hararanta yayi, tun kafin ya daka mata, tsawa tabar falon da gudu,


****
Weekend....
Zaune yake kasa ya ɗaura kanshi, akan cinyar mommah, yayi limo kaman bashi ba, duk ya rame sai uwar hanci da yakara fitowa,

        Shafa kanshi take, a hankali tace.
"Mashkur meke faruwa ne ? na ganka haka, hmmm gwara da kazo ina kaje wata uku da suka wucce, matarka hankalinta ya tashi kaman mahauciya haka ta koma, kuma ance ba kai kaɗai kayi tafiyar ba har da mace kuka tafi, meye ma'anar haka Son yaushe kasoma niman mata abinda bakayi ba tuntuni sai yanzun da ka fara tara iyali idan aure kake bukata wallahi zan tsaya maka kayi, amma da niman mata kanajina ko."

         Gyaɗa mata, kai yayi cikin damuwa yana son faɗa mata, amma yasan mommah da iya  bugan cikin mutum,  shiru yayi, ya cigaba da lumshe idanunsa.

        Da zai tafine suka keɓe da Ubaida sun jima sosai suna bawa juna shawara kafin ya bar azare.

       ****
Bayan sati biyu, Iyayen na'im sun zo daga kaduna har an tsayar da ranar wanda yazo dai dai danasu bilal,

      A wannan lokacin saura kiris ya rage mashkur yayi hatsari, karshe dakatar dashi akayi daga aiki.
       Dawowa gida yayi ya zauna, sam yanzun be wani damu da cigaba, ba dan beki a koreshi aikinshi ba, tunda yarasa shkurah sam baya jin zafin duk wani abinda zai rasa dan kallon abun yake mara muhimmaci.

              A bangaren umma kuwa, taki faɗawa kowa a danginta, shiru tayi gefe guda ruwan wulakancin da takewa shkurah ita da yan uwan shkurah, sai da Alhaji hammayo yayi musu, magana akan fita harkan shkurah dasukayi dan dole suka, shiga hidimarta.

        Abokan Na'im da Y'anuwansa suka, sakashi a gaba da suyi pre-wedding pic  haka ya tsallake ayukarshi yazo sukayi an wanke wasu, yayinda aka tura masa wasu a waya, gida ya dawo da ita washe gari ya koma kaduna,


        *Fitana wutar dajice*
Tunda ya isa kaduna, yan uwansa suka shiga tura ahotuna a wayarsu suna ɗaurawa a Whtsp da Face buk, tare da ranar bikin,
Wata kanwar Na'im haɗa hoton tayi, ta saka musu wanka da akayi, musu ta ɗaura a you tube.

         Kafin wani lokaci, har amfara mata, comments da fatan alkhairi.

      Cikin awa ɗaya zuwa biyu, har kusan mutane sama da dubu goma, sun kalli vidio,

        .......
Maina....
Fitowarsa kenan, daga ban ɗaki, yayi yar kiba kaman bashi ba, dan ya tafi har india inda aka sake duba masa, bayanshi wata ɗaya da yawucce kuma anyi dace sun bashi magani sosai yake, buga iskancinsa son ranshi.

             Daga shi, sai gajeran wando, ipad ɗinsa ya ɗauka yashiga duba median da you tube ya fara dan yaga sakonnin dan har channels yake dasu na batsa,
         Ganin vidion su shkurah yayi, ya buɗe jefar da ipad ɗin yayi, cike da tsoro can kuma ya ɗauko kare mata kallo yayi da sauri ya sauko ya fara haɗa kayanshi, sake maida vidion yayi daga farko, nan yaga inda za'ayi kamu da waleema,

          Murmushi yayi yace.
"Masoyiyata ganinan zuwa gareki."

Fashewa yayi da dariya.

       ****
Ranar laraba, sukayi lalle ita da kawayenta cike da jin daɗi.
    Ranar alhamis kuwa kamu aka tafi, dan kusan motartace ta karshe, har sun isa cikin inda za'a fara ga abokan ango zasu shiga gurin, kawai sukaji amfara harbin iska cak tsaya, duk mutane gurin kowa ya gudu.

       Fitowa yayi daga motarsa sannan ya kalle yaran da ya ɗauko haya wasu karti dasu yace.
"Muje ku ɗauketa, kusa min ita  A mota."


          Ashe tun fitowarsa tasuma a tsaye, basu lura da haka ba, sai da suka ɗauketa suka sannan suka lura.

         Gurin na'im yaje, dafa na'im yayi a kafaɗa, yace.
"Kayi rawan kai,fa amma ka manta da ita tunda kaga agabanka na ɗauketa, ka koma garinku, dan baka isa kwaceta ba, haka ma wanda ya bar maka ita be isa ba,inda kuma yana da zuciya, kace maina yace yazo tsallaken ruwan gubi dam, kace yazo ina jiranshi."

       Komawa motar yayi suka, ɗauki hanya kaman mahaukata.
         Bayan tafiyarsune mutane suka fara, dawowa nan aka tambayi na'im ina take faɗa musu abinda Maina yace yayi sannan ya kalle fatima, yace.
"Auntymu daman akwai wanda yake niman Shkurah ne bayan ni."

"Eh Cousin brodan mune, Mashkur,"

             Tace masa,

       "Toh kuwa wannan sakon nashine, ina yake."

            Kafin minti talatin Yan uwan da abokan arziki, suka zo nan aka cikin tashin hankali, umma tazo gurin Allah sarki faɗan irin tashin hankali da take ciki ɓata bakine.

......
Tunda bilal ya bashi Iv ɗaurin aure, ya ajiye a gabashi tunda baya zuwa ko ina, yau baki ɗaya yake jinshi dabam, ga faɗuwar gaba,

So yake ya tafi, azare, ɗaurin auren Ubaida da Bilal amma yakasa tashi karan wayarshi ce ta dame shi, ɗauka yayi yaga umma.

Ya kara a kunensa, cikin kuka tace.
"Mashkur, yazo ya ɗauke min Shkurah,"

            Be karasa, ji ba ya suri wayarshi sai gidansu shkurah, nan ake faɗa masa

Please Login or Register in order to submit comment