Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

malam"

dake yasaba da hidimar mata ganin kowacce ma haka take aikuwa kaman an aikeshi yakai hanunshi kugunta,
a razane ta ɗago ta kifeshi da mari wanda sai da yaga wasu stars

dai dai isowar Mashkur kenan tun daga nesa yake hango dramarsu ai kuwa fashewa yayi da mugun dariya ya fashe har yana dukan sitiyeri fita yayi fuskanshi ɗauke da murmushi ya isa wajen mika mata rigar ruwa yayi sannan ya kalle maina a yake rike da kunci yace,
"Bro ya dae karike fuska"

kallon mamaki shukrah tayi masa tace,
"daman kasanshi ne, rashin hankali ya nime yi min ni kuwa na kwaɗa mashi mari muje kakaini gida hankalin Ummana yana tashe."

Ko takan maina be biba, ya juya suka tafi, a mota ya kalleta yace,
"Don Allah karki sake fita haka idan ana ruwa kinji ko"

ɗaga mashi kaitayi, har gida ya kawo ta, sannan ya mata sallama fuskansu ɗauke da murmushi,

Tunawa yayi da maina da sauri yaje inda yabashi aikuwa yana wajen rike da fuska, da sauri ya fita daga mota yaje gurinshi yace.
"Maina me yasa, ka tsaya a ruwa idan mura ya kamaka fa,"

"Kana ganin, ta cimun mutunci, ta keta min duk wani jinkaina, kace na tafi ita wacece a gurinka meye haɗinka da ita, a iya sanina baka niman mata meye ke tsakaninku"

duk wannan maganar,a faɗa yake tambayar Mashkur, shima tsawa ya daka mashi wanda be taɓawa wani ba yace,
"Tambaya kake, toh ita nake so, kuma da ita zan rayuwa wallahi lokacin da kakai hanunka da niyar taɓata da ina kusa da kai sai na harbaka, don Matata ce, Ina sonta da duk xuciyata, da kuma ta iya kare kanta tabiyani, Wallahi tallahi maina koda wasa ka sake yunkurin kai idanunka kanta, sai na nak'asaka, ido kawai ina kuma ka kai hanunka hmmmm zaka sha mamaki wallahi."

yana faɗan haka yabar wajen zuciyarshi tana tafasa.

Sabida bakin ciki da maina yake ciki naushin glass din motarshi yayi idanunshi yayi jajur yaɗa murya yayi yace.

"Wallahi sai na sata kuka sai na wulakantata sai naketa alfarmanta, sai na jefata wata duniyar bakin cikin da damuwa, sai tarasa tundun dafawa, Mashkur idan na barka da ita cikin farin ciki, ba jinin sarauta nake ba,

yana gama faɗan haka yashiga motarshi yabar gurin.

Shima mashkur haka,


*Hmmm kusan six read more, nayi muku, ga ciwon idanun da nake fama da shi be hanani nayi muku typing ba, kuyiwa Marubuta adalci dan suma suna iya bakin kokarisu wajen nishaɗarta daku, amma abin haushi dakyar zamu sami sanun ko madalla, Allah yaga zuciyata idan kasaka min tnx bana bukata ko Hrt rike kayanka dan idansume nima zan iya jinjinawa kaina,kuyi hkr iya gskyna na faɗa*


_Toh fa me maina yake shirin aikatawane sai naji daga bakinku, Yawan comments ɗinku yawan read more ɗinki_




*Ina yinku_💋

#Mashkra💘
3/4/21, 9:44 AM - Ummi Tandama: *🙆QADDARAN RAYUWATA🙆*
_SHUKRAH_
Mai_Dambu

Al-Musawwiru Al-Gaffar Al-Wahaab Al-Qahhar👏

     '''Allah sarki Maina ashe haka kayi bakin jinin, H'ello makaranta, Sunan Buk ɗin zaku duba Qaadaran Rayuwartace zaizo mata a kai-kaice dan haka, ku biyoni a sannun muji wani irin kaddara ce haka Fatan Alkhairi nake muku'''🌹💋💕

*Page 7*
Ko bin takanshi bayi ba shiga motarshi  suka bar wajen, Maina yana komawa gida ɗakinshi  ya shige, ya ɗauki kwalbar giya yanda ya buɗe bakin haka ya ɗaura, akan bakinshi sai da yashanye shi tasss, sannan yasake buɗe wani kwalbar yasake ɗaukowa, wasa-wasa sai da yasha kwalba kusan shida a gurin aikuwa yana, gamawa yashiga jifa da duk wani abinda yake, ɗakinki kaman, mahaukaci haka ya koma, duk ya birkita kome, jin karan wayarshi ne yasa ya, nutsu sannan ya ɗauka a buge, cikin masifa ya dakawa me kiran tsawa yace,
"waye ?"
    "sorry Maina, ma'amurah ce dama zanje gida jos ne shine nace bari nakiraka mugaisa bansan zan dameka bane am sowiee"
       "Ok ki karasa, ina jiranki," sannan yayi mata kwantace, barrack ɗin,

         Daga tashar mass, mashin ta hawu, ya kawota har bakin gater ɗin barrack ɗin, masu tsaron gater bayani tayi musu, dake sunsan halinsa babu wanda yayi yunkurin hanata shiga unguwar,

             Tashi yayi ya gyara kayan ɗakin dukda a buge yake, be hanashin tuna abindasu Mashkur suka, masa ba ji yake kaman zuciyarshi zata faɗo daga kirjinshi,

          Buga kofar gidan da akeyi ne yasa zai fito rashin dace kafarshi tataka kwalbar da ya fasa, kuwa tayi masa mugun yanka, ga hanunshin da ta farfashe
        dukda zafin da yake ratsa koina najikinshi, be hana shi jin zafinsu Shkurah ba ji yake zafin yankar da yayi bekai zafin marin da Shkurah tayi masa, ba ɗaga kafar yayi ya cire kwalbar yafita, buɗe mata kofa tashigo, jin yana warin giya yasa ta sake murmushi, dan ita yar hanunce wuccewa yayi tabi bayanshi idanuntane ya kaikan kafarshi a tsoroce tace.
"Sir maina, kalli kafarka jini yana ɓata ko ina,"

         "Eh nasani yanzun, zanyi dress ɗin kafar, muje ki huta,
        ɗakin da Mashkur ya zauna nan ya kaita dan ya gyara ɗakin koda Ubaidatu zatazo masa hutu, bashi da matsala,

     Nan ya kaita, sannan ya koma ɗakinshi, tattara ɗakin yayi sannan ya share ko ina, ya zuba a kwandon shara, first aid box ya ɗauko ya ajiye sannan ya shiga wanka ya jima a cikin ruwan zafi, yana ratsashi ta koina rufe idanunshi yayi yana tuno, abinda ya faru da marin har da rashin mutuncin da mashkur yayi mashi, hmm wannan abin ya tsaya a ran maina, buɗe idanunshi yayi, sakamakon jin ana shafa masa kirji, Ma'amurah ce zaune daga ita sai towel, murmushi tayi masa sannan ta mike ta sake towel ɗin tashiga abin wanka,

kwanciya a jikinshi tayi, na wani lokaci sannan ta ɗauko sabulu tashiga goga masa, lumshe idanunshi yayi, yana me nazarin wasu abubuwa kanta,

             Karo nafarko da mace tasa maina hawan ruwa,

              Duk abinda ma'amurah tasani zatayi tayi amma maina be santana yi, ba haka sukq fito wankar ita tayi masa dress hanun da kafarshi, a nan kuma ya nuna mata m, daman kallonki nake, abinda suka fi jan hankalinshi, boons ɗinta dan haka dasu ya fara, cikin k'warewa yake sucking ɗinsu yar banza sai tura masa take tana riko kanshi, duk  ilahirin jikinshi rawa yake dan salon Ma'amura karshe ne, ta iya tafiya da zuciyar yan maza,
        Maina hooo.

           ***
Lokacin da shkurah ta shigo gida rank'washinta Ya sadeeq yayi dan baki ɗaya hankalin Umma baki ɗaya ya tashi, zuciyarta cike da fargaba da tsoro tana gudun karwani ya cutar mata da auta sai gashi ta dawo, ajiyar zuciya umma tayi sannan ta gallah mata hararanta tayi bayan tamata dakuwa, itakuws rike kanta tayi tana zubda kwalla sabida zafin rank'washinta da sadeeq yayi, cikin shashekar kuka tace.
"Meye laifina ince mashin ne ban samu ba, shine ake ganin laifina, idan da wani abu yasame ni me zaku ce" tana faɗan haka, tayi shige ɗakinsu.

      Tun daga ranar, ake zuwa ɗaukosu haka ya rage, haɗuwar Mashkur duk da bata fito ta nuna ba, but haka yana damunta, a islamiyya saura sati biyu, sugama har da hadda,

       kusan hidimar karatunta yasa kanta, amma duk ranar da kewar Mashkur ya addabeta, toh Umma sai ta koreta dan hiranshi tayi, da yanda take bashi ciwonkai, da yanda take masa shirme,

                    ...
  Ɓayan sallar magarib, yanda a kofar gidan yayi sallah, dake akwai masalaci a cikin gidan, yana idar da sallah, ya nemi iso a xuwa wajen Alhaji hammayo,  dake suna tare da Sadeeq ne ba a ɗauki lokaci ba ya shigar dashi har falon yana shiga da, ita ya fara tozali, sanye yake da wani yadin material amma na maza kalar cream wandon kaftani ne ajikinshi yayi kyau baisa hula ba dan daman dress ɗin bana hula bace,

             Umma tana kan kujera ita daman suna tattaunawane akan harkan kasuwancinsa, ita shkurah tana kwance akan cinyar  tana cin pop corn, a duniya abu abinda shkurah ta bashi amanna kaman kayan zaki, idan da tana kallon a reserve taga tallar wani chocolat toh dan masifa sai ta ɗagawa Babansu hankali yasa anemo mata, takan  faɗawa kowa, ita shazumamiya ce,
        Yanzun haka pop corn ɗin A sky crown aka sayo mata take, ci jin sallamar mutane yasa ta miqe zaune, tare da amsawa Ya sadeeq ne a gaba, Mashkur yana baya leka bayan Sadeeq tayi maahkur ya sakar mata murmushi zillowa tayi daga kujeran tana raraba idanun zillon da tayi yayi sanadin da hularkanta ya zame gashin da tayi gamonshi suka zubo bayanta,

           Mamakine ya rufeshi, suna zuwa cikin falon suka zube akan kafet gaida Baba yayi a kunyace sannan , ya juya ya gaida Umma, sannan ya saci kallon inda shkura take tunda taganshi ta bar cikin pop ɗinta, so take ya kalleta ta galla masa harara dan kusan kwananshi goma babu shi babu a lamarshi, shi yasa take kulle da shi.

         Sadeeq ne ya kalle Babansu yace,
"Baba yazo wajenkane,"
        mikewa Umma tayi ta riko hanun shkurah, dan su bar musu falon dansu zanta, da gayya ta sake robon pop ɗin ya zube a gaban mashkur, durkusawa tayi hankali ɗauki robon, ɗago idanunta tayi ta zuba cikin nashi tace,
"U luk nice."
          mikewa tayi tabar falon duk abinda suke akan idanu Alhaj hammayo, farin cikine ya cika zuciyarshi daman addu'a yake Allah yaba shkurah miji nagari wanda zayi alfahari da ita nagartace, Alhamdulillah ubangiji ya amshi addu'arshi.

       Tana fita ya alhaji ya maida hankalinshi kansa yace,
"Mashkur ko? meke tafe da kai,"

            gyaɗa masa kai yayi cikin nutsuwa da ladabi,
  duk kunyata rufeshi, (kai mashkur sai kace mace wanga kunya haka😹)lolz
             gyara zama yayi sannan yace,
"Daman naso niman izinkane,"
   shiru yayi kanshi a sunkuye, matsanacin kunyar Babane ya kamashi, murmushi Baba cike dattako sannan yace,
"Mashkur, kenan hmm toh wannan kunyartaka, ai zata k'wareka, amma kana nufin kazo niman wani abune a gidan nan?"
       gyaɗa masa kai,
   "toh me kake niman izinin?"

        Again gyaɗa kai yayi sannan, yace,
"Ɗaman shkurah?"
         dariyane ne yake cin Baba da Sadeeq, suna mamakinsa,
     "toh shkurah ko."
     Shiru Baba yayi, ya ɗauke wuta na wani lokacin ajiyar zuciya yayi sannan yace,
"Gaskiya bazan ɓoye maka ba, nayiwa shkura miji, kayi hakuri."
     Yana faɗan haka ya tsuke fuska,
          dukda karfin ac dake falon be hana mashkur jin zafi, zufa ke karyo masa tako ina a jikinshi, runtsa idanun yayi ya danke hanunshi cikin tashin hankali ya kalli Baba yace.,
"Don Allah Abba, karufa min asiri wallahi ina sonta, itace rayuwata, na haɗaka da Allah,"

          Shiru yayi sabida, bacika dogon magana ba, idanun kaɗa jajur hankali ya mike zai bar gidan.
        "Shin kai waye? daga ina kake,"Inji Baban shkura,
            juyawa yayi a hankali sannan ya durkusa, yace.
"Sunana Muh'd Hassan Muh'd katagum, sannan nafitone daga cikin gidan sarkin katagum, ni sojan samane, ina da matsayin captain ne,  Abba nayi maka alkawarin rike shkurah tsakani da Allah, zan tayata hidiman kuruciyarta bazan tauyeta ba, bazan takurata ba, zan bata matsayi na musaman a zuciyata, zanwa sonta hidima ba son wani abu ya cutar da ita ba, zan kare mutuncinta da kimarta."

           Sunkuyar dakai yayi yana sauke ajiyar zuciya, kallonshi Baban shkurah yayi nawani lokaci, sannan yace.
" kaman sati uku zuwa huɗu, akayi bikinku kaida yaron Sarki hussain kuma naje, ɗaurin auren kana ganin babu wata damuwa, da aurenta da zakayi."

         "Ubangiji ya bamu daman yin bibiyu uku huɗu, kuma ina da abinyi, kobana aikin gwanati, ni ɗan kasuwane ina da manyan shaguna anan bauchi da azare, ina da kampani haɗin gwiwa a japan muna kafet, Abba zan maida Shkurah sarauniya, Bazakayi da nasanin aura min y'arka ba, zanyi kuka lokacin da take kuka, zanyi dariya alokacin da take dariya, Abba koda ya ya shkurah tayi kunci nine zanji ciwon abun, zanyi amfani da shekaruna na maidasu dai-dai da nata, Idan ni shugabane a waje, zan maida kaina bawanta Abba bayan Mahaifiyata shkurah itace tabiyu a zuciyata, ko mahaifiyata tasan darajar Shkurah Abba wallahi zan iya sadaukar da komena da narasa shkurah gwara narasa kome, hmmm abba zakace ina maka daɗin bakine, Ina sonta zan bata rayuwata dan nata ya inganta."

       Zuba masa idanun sukayi daga Alhaj hammayo da Sadeeq,
cike da mamaki,

        Duk jikin Baban shkura yayi sanyi gyara murya yayi sannan yace,
"Muh'd mashkur kaje na yarje maka kanemi Zainab, kuma ina son nan da wata gudu, katuro Wakilanka suzo min aurenta, amma biki sai ta fara karatu kafin nan tasake nutsuwa, dan ak'wai yaranta a tattare da ita, sannan bana son yawan zuwa idan zakazo ma banda zuwan dare kazo da maraici, sannan bana son kasake mata kuɗi dan haka ma wani matsalane nan gaba, ina son kaso tane dan Allah ba dan abin hanunka ba ka gane ko, Allah yayi muku albarka,"

          Sadeeq ne ya amsa da Amin. Sallama yayi masa tare da godiya sannan suka fita, sadeeq ya kalle shi, taɓe baki yayi sannan yace,
" Yanzun kai don Allah zaka iya zama da mace yar karama irin shkurah, hmm yarinyar da taɓaci da ɗan banzan rashin kunya, karshefa rainaka zatayi dan ba kunya ce da itaba,"

"Tunanin kane haka amma ni ai ba damuwa, idan tarainani daman wanda yafi dacewa mace taraina ai mijintane dan ita tafi kowa sanin sirrinsa, kaga kenan ba laifi bane haka sai ma kara sabom dausayin soyayya,"

        "Ok bari na shiga nakira maka ita kugaisa."
       

         Shiga cikin gida yayi har falon Umma, gallawa shkurah harara yayi sannan yace,.
" Saura kije kita mashi hauka da rashin kai, da kika ganshi nan daga babban gida yafito kuma sojane idan kika mashi iskanci harbe kanki zayi."

Kallon sadeeq take baki buɗe ta marasa nacewa, can da yabata haushi turo baki tayi sannan tace.
"Babu inda zanje  yayi tafiyarshi tunda bani nice na kawoshi, ba da za'a min kashedi akanshi."
        Haushine ya turnike  Sadeeq tashi yayi da niyyar kwaɗa mata mari zillewa tayi ɗakin umma wacce take jin duk abinda suke faɗa,

       fitowa tayi sannan ta kalle Sadeeq, tace.
     " Wato kai, baka da hakuri ina ruwanka da ita, nasan ko me giyar wake aka bata bazata masa rashin.kunya ba balle ma baza tafara, ba kekuma maza ki ɗauki drinks da cup kije kugaisa sannan kice masa Babanku ya hana hiran dare."

"Baba ma yafaɗa mashi," inji sadeeq.

          Gyale ta ɗaura akan doguwar rigarta sannan ta fita hanunta ɗauke da tiren da drinks, ɗakinsu salmah taje ta kirata suka fita, tare.

        Yana jingine da motarshi, ya zubawa kofar gater ɗin idanu yana jiran fitowarta, yana ganinta ya sauke ajiyar zuciya sannan ya mike daga jiki motar yasaka hanunshi ɗaya a cikim aljuhun wandonshi,  hanunsa ɗaya yana shafa yan sumar kanshi da sukayi lufluf,

         lumshe idanunshi yayi ya sauke akanta, take ta diririce hanuntane ya shiga rawa tana niman zubar da abin hanunta, murmushi yayi sannan ya amshi tiren daga hanunta yana kallon fuskanta da tarufenta da gyale sunkuyawa yayi yana leken idanun, saka hanunayenta tayi tarufe fuskanta, dashi.

        Maida idanunshi yayi wajen salmah yace,
" kibata hakuri, na rashin ganina haka ya farune sakamakon wani aikin gaggawa da muka jeyi a jos, ne shi yasa ban zoba, tuba nake."

             Dariya salma tayi cike da kunya tace.
" Laa bakome an maka uziri, kuma nasan sister ta huce ai dan bata riko."
       "Eh toh ga alamun sun nuna ana fushi dani, tunda taki min magana ayi min hakuri dai idan kina son nayi tsalle kwaɗoto ni zanyi."

        Dariyar da bata shirya yins shi ne ya kwace mata, kallom shi tayi sannan ta sunkuyar da kan tace.
" Me yasa da zakayi tafiyar baka faɗa min ba, ka tafi abinka haka ake abotar nidai daga yau karka sake tafiya baka fada min ba"

               "Ok my queen magana ya kare ba za'a sake ba, Sister ki shaida, idan haka yasake faru, na fuskanci horo daga Madam,"

      tura mashi baki tayi cike da jin haushin kiranta da madam da yayi, kaman zatayi kuka tace,
" Madam sai kace inyamura, dai bana son sunan,"
      kallonta yayi yana yar dariya, kallon salmah yayi sannan yace.
"Kinjita ko, ai inyamurai ma mutane ne, dan ance miki magana natuba bazan sake ba, yayi miki Hajiyata"

         Haka sukaita hiransu cike da ban dariya da nishaɗartawa, har yayi musu sallama zai tafi buɗw motar yayi ya ciro mata tsarabanta, sannan yace.

"Ina ganin ba zan same halin zuwa ba dan zanje kano wajen Auntyki, sai nan da kwana biyar zan dawo, kinji"

    gyaɗa mashi kai tayi sannan tajefa masa tambaya da cewa,
"Ban gane Auntyna ba daman kana da mata ne? shine ko kafaɗa min sai yanzun zaka faɗa min, hmm halinku kenan thanks Allah da ba soyayya muke ba, dan nasan ba karamin haushinka zanji ba, hmm nagode kuma Umma tace na faɗa maka karkana zuwa kullum, sai anjima,"

      "Toh nima nagode" suna shiga cikin gida cikin gida ta kalle  Salmah tace,
" Don Allah kiji fa wai ashe mata yake da shi, nikam zan daina kulashi ma baki ɗaya dan ya bani haushi taya zai ɓoye min yana da aure da nafaɗa sonshi ya zanyi nifa bana ra'ayin me mata wallahi nayi rayuwata a cikin sansani na niɗaya ta."

            Kallon mamaki salmah take mata can tace,
" Toh me yasa kika ji haushi dan ya faɗa miki yana da mata, kin taɓa jin haushinsa kafin yau, ko sai yaune zaki daina kullashi,hmm abune me mugun wahala kidaina kulashi dan kowa a gidan nan yasan kuna son juna, malama kina kishinsane baki sani ba tuntuni kika faɗa (2-3-3-4) love idan kuma kina ganin karya ne jeki tambayi Adda Aisha zata faɗa miki, yarinyar kin kama big Fishi."

  Shiru tayi bata sake magana ba indai haka shine So lallai ta jima da tsunduma tsaki tayi da tatuna yana da mata,

       ***
Rayuwarsu gwananin ban sha'awa haka suke gudanarwa kowa yasansu har yan unguwar, gashi Allah yayiwa mashkur jama'a, akwai wani lokaci yazo wajenta yasamu ana rikici tsakanin yan unguwar da hukumar Nepa zuwa yayi yasaka baki sannan ya biya kusan dubƴ ɗari uku da ake bin yan unguwar amma banda gidansu shkurah, dan Alhj Hammayo yana kokarin biyan kome akan lokaci, haka da yayi ya sake samun mutunci a idanun yan unguwae.

     ***
Maina tunda ma'amurah ta tafi jos yake yawan tafiye tayi bayi da lokacin kanshi sai na aiki ga abinda Shkurah tayi yana tsaye a ranshi, da yasame lokaci zuwa kano yayi wajen Ubaidatu ya sauke mata haushin shkurah da Mashkur dan yaso mantawa da abin inda yayita bin mata, amma baya samun nutsuwa,ya koma shan giya shima bata sake zani,ba shine ya tattara yaje ya barjeta son ranshi sai da yaga tana kuka da rokonshi sannan ya kyaleta yashiga wanka,

        Bayan fitowarshi ne itama ta shiga abin tausayi dakyar take jan kafarta ruwan zafi ta haɗa me zafi tashiga shine taji dai dai,

           Tana mamakin fitinar maina shi yasa tunda suka dawo makaranta take kula da gyaran jiki da haɗa magguna, dilke akai akai bata wasa da jikinta baka mar Zubaida ba dan tana wasa da jikinta sosai.

            Kwanan shi biyu ya dawo, kiran mashkur yayi a waya ya bashi hakuri, kuma yace yaba shkurah hakuri, nan kuwa suka shirya har da hira,  a cikin kwanakin har gidansu shkurah yaje yabata hakuri itama tabashi hakuri.

             Saukarsu ce tasakosu a gaba, dan haka kullum tana gidan idan aka tashi a skul bata zama dawowa ake a cikin kwanaki da yarage kullum shigar da hadda duk takaɗe sai uwar hanci dan bata yawan cin abinci sai kayan zak'inta.

        Binta mashkur yake tafaɗa mashi me takeso yayi mata tak'i ita har yanzun fushi take da shi ya boye mata yana da mata shine idan yaxo take ɗauke mashi wuta, duk yadamu Sadeeq yasamu da maganar abin takaici da na haushi, zuwa yayi ya sameta a ɗaki tana duba wani buk ɗinta,

        roko kunnenta yayi ya murɗa, sannan cike da zafin rai yace.
"Uban me yayi maki kike  azabta dashi haka, me yayi miki da yayi  wulakantashi kinsa ma tukun waye shi, yau idan sarkin Katagum yayi murabus shine magajin wannan kujeran kinsan Matsayinshi kuwa a cikin sojoji Captain ne ba kurtu ba, banza wawiya har mutum kaman Mashkur yazo wajenki kina wulakantashi toh ashe nima zaki iya wulakantani,maza kije kisame shi kafin ma karyaki,"

     Umma da Aisha da Bilal ne suke tsaye suna jinshi umma ce tashiga ɗakin cikin rarrashi tace.
"Laifin me yayi kike mashi haka, hmm Uwata kina wulakanta me sonki babu kyau karki sake kinji ko Mamana."
         Cikin muryan kuka tace.
"Toh bashi bane ys ɓoye min yana da mata ba, sai ranar yake faɗa min shine nace daga ranar zan daina kulashi."😨
Zarro idanun Umma sukayi mamaki ya addabesu,  Aisha ce ta kasa ɓoye dariyar tayita kyal kyalewa har da rike ciki tace,

" Umma Autarki tana jealous lallai autar Umma hmmm"
    fita tayi daga ɗakin tace,

"hankali yarinya kina ynz kenan idan ya aureki kiga gane, me ye aure, ina ganin, haukacewa zakiyi da kishin mijin, ita ɗaya take maganar,

      rike hanunta Umma tayi sannan ta ɗago tace.
" Shkurahta babu kyau haka ai ya kyauta da ya faɗa miki, idanun wani ne ba zai faɗa miki ba,  idan kina haka ba zai sake, zuwa ba sabida kina masa rashin kirki, da wulakanci, kuma koda ya aureki ba zai damu dake ba ki tashi yanzun kitafi ku gaisa ko"

                 Mikewa tayi tana share hawaye tafita, tana ajiyar zuciya da jan majina dan Shkurah bakaramar sangartaciyya bace, tana zuwa ta tura mashi baki, tace.
" gani nan"

        murmushi yayi sannan yace.
"Kiyi hakuri, ga sunan  daman nayi mana, iri daya ne Am so sorry "

       Kallonshi take har cikin idanunshi sannan ta saukar da idanunta kasa tace.
" kayi hakuri, ba zan sake ba idan nashiga da kayan Umma da Baba zasu min faɗa"

       Gyara tsayuwanshi yaƴi sannan yace.
" ki koma ciki, kicewa Sadeeq ina nimanshi."

     gyaɗa mashi kai tayi sannan ta juya, bin yake da ido har tashiga ciki, tana shiga ta faɗawa sadeeq yaje yana kiranshi, ɗaki tashige ta fashe da kuka, tausayin, kanta take ji wanda batasan me ya haifar da haka ba,

          *Bak'ar Rana daga cikin Qaddaran Rayuwata*😭
          Yau ake saukarsu kuma an tashi garin anata ruwa dan ma a cikin masalacin Izala ne akwai babbar hall a ciki ake gudanar da saukar,

       Hankali ake gudanar da saukar mata sun saka Himar fari, da lace peach maza kuma shadda cream colour, sunyi  kyau amma shkurah ita shadda tasaka Brown ita da mashkur sukayi sunyi kyau, a ɓangaren mata itace ta ɗaya a ɓangaren maza kuma wani yarone sun same kyaututuka,

          Koda aka tashi makarqnta sun rikesu dan haka mashkur ya gaji da jiranta dan shi d maina ne,

A gidansu kuwa na ɗaga walimarta sai gobe sabida ruwa ba'a sallamesu ba sai.kunsan shida.

   fitowa tayi taga mashkur ya tafi dan haka tabi ta wani ɗan yanke da zai kainta gidansu amma akwai nisa dan sai da tayi tafiya mai nisa,

      Mashkur yaje makrantar akace ay taho gidan hanyar da zai sadashi da unguwarsu maina ya hangota tashiga wani lungu ga lokacin garin ya fara duhu, cewa mashkur yayi ya tsaya yashiga can

Please Login or Register in order to submit comment