Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a india da nafarka daga doguwar suma, Shkurah dake nafarka, mun dawo daga can nazo nasame mugun labari wai kinyi hatsari kin rasu, Shkurah kowa yana tunanin kin mutu, amma zuciyata taki karɓan mutuwarki, nasha gwagwarmaya, kafin Allah yasake haɗamu, shine zan gujeki, duk irin faɗi tashin da nayi a rayuwata, Sai na juya miki baya hmmm, ni ba butulu bane, koya kika zo min ina sonki ba virgin ɗinki nakeso ba, ke nakeso dan haka kirufe min idanunki muyi barci dan kin gajiyar dani."😇

    
     Murmushi tayi, sannan tagyara kwanciyarta, sosai a jikinshi tana sauke ajiyar zuciya a hankali tace.
"Ilvu my only,"

   kifa kanta tayi, akan kirjinshi tana ɓoye fuskarta, dariya yayi yace.
"Sake faɗa, naji."

           Cikin sigar shagwaɓa tace.
"My only barci nake ji, fa duk nagaji"

"Kin gaji wani aiki kikayi, ban sani ba faɗa min ko namiki tausane," ya faɗa mata yana dariya,
"Haba ina nagode bar haka, ynz ma ai kaki barina nayi barci ma,"

        murmushi yayi, cikin farin ciki rufe idanunshi yayi, sabida itama tayi barcin hanunshi yana kan nashanunta sai wasa dasu yake, a haka barci yayi gaba dashi basu farka ba sai karfe ɗaya na rana,ita fara farkawa kallonshi take yanda yake barci cikin nutsuwa, kallon kyakyawan fuskarshi take, me cike da kyau,

      duk wannan kallon da takw masa batasan ya farka ba, sai da yace.
"Kina kallon, kyakyawan mijinkine haka karki damu daga ke Insha Allah babu, kari."

       Rufe fuskarta cike da kunya ta mike zata shiga ban ɗaki, rikota yayi yana dariya yace.
"Karki min, asaran ajiyar danayi fa, dan ni jarumin namijine, tsaya miki wanka da kaina"

          murmushi tayi, sai da tabari ya mike dai dai yasake hanunta, turashi gadon tayi ta shige banɗaki tasa key ita dakanta tayi wanka, sosai sannan tafito ɗaure da towel tana goge kanta da ɗayan towel dariya yayi, sannan yace baida kinyi wanki ke ɗaya ba,toh bari nayi abinda zaisa musake wanka, tare.

    Zaro ido tayi cike da mamaki tace.
"Baka gaji bane, don Allah karufa min asiri bazan iya maka ba, dan kafi karfina..."

       Sungumarta yayi ya haɗe bakinsu waje guda, nan yashiga sumbatarta cikin wani salo me taɓa zuciya rike take da towel ɓata san lokacin da suka suɓuce ba, rike kanshi tayi sosai yanda shima yasamu damar haɗata da jikin wall ɗin ɗakin dakyar ta kwace kanta tana masa dariya, tace.
"Wallahi karaba kanka da, fitina ina zan iya maka mutum sai kace yasame tuwo abu ɗaya tun ɗazu."

            Kuma babu kaya ajikinshi take masa wannan gangancin girgiz kai yayi, zai shiga bandaki cikin zafin nama ya cafketa yana murmushi boss yace.
"Bakince kaman nasame tuwo ba, bari nanuna miki yanda ake ladba da irinki tunda bakinki baida linzami, kinga idan kika ji wuya gobe bazaki sake ba,"

      dirzanta yayi son ranshi, tare da kashe arna da kai ji yayi ashe ɗazun ba kome yayi ba, wasan gona yayi da ita, kuka kan yasha har da nashagwaɓa, tare da fushe ɗaga kafaɗa yayi yace.
"Ko a jikina yarinya Allah kika sake tsokanata, zan durzaki son raina," yana dariya.

Wanka sukayi tare sannan suka, fito sallah azahar yajasu, sannan suka shirya cikin kananun kaya ta ɗaura after dress akan kayanta, sannan suka fita wajen cikin abinci.

         Daga nan suka shiga gari, yawon buɗa ido. Kwanansu goma suka isa Manchester  ns birnin london, da akwai wasan da za'ayi tsakanin Real Madrid da Manchester din, sunyi kallo sai karfe goma sha ɗaya, suka isa hotel ɗinsu.

        Satinsu biyu, a can dan ya kaita Chelsea Sunday market siyayya sukayi nafitan hankali, sannan suka dawo,daga london,

       Suka nufi, zurich dan za'ayi wasan Olympic sunyi wayo sosai inda suka dire saudiya, dan suyi umrah,  satinsu biyu, acan suka mike dubai, kwanasu ɗaya Zubaida takira mashkur tans kuka don Allah yazo maina yana son, ganinsu shida shkurah.

           Washe gari.....
Suka bar dubai bai faɗa mata dalilin dawowarsu ba, dan ya lura kwana biyu nan, wani masifa take ji, ga mura da yasata a gaba, ko raɓanta bata kaunar yayi, kuka take saka mishi dan dole yake danne bukatarshi,(😂 Honemood da tsarabar)

           Sun iso abuja, cikin dare ahotel suka kwana, da safe suka bar garin zuwa bauchi.

      Suna isowa, yace.
"Baby girl, zan kaiki wajen umma ni zanje wani waje pls karki wahalar da kanki kinga kina mura ya kamata kisha magani amma k'inki idan nadawo zanzo sai muje asibiti me kikeso nakawo miki."

      ɗaga kai tayi, tana tunanin me takeso can tasake murmushi tace.
"Soya amma na yaɗi, wanda aka soya da manja, nake bukata sai kosan goro, kai har da ɗan malele, idan nashiga ciki zance umma tayi min dambu yaji kayan daɗi"

         zaro idanun yayi waje, cikin karamin tashin senses yace.

"Baby girl banda abinki, idan ki kaci abinda kika lisafo, cikinki zaiyi ciwo kawai zan sayo miki kaza ko balangu"   

      fuuuu tabuɗe motar tafita tace.
"Banaso"

      tashige cikin gida cike da jin haushinsa, bin bayanta yayi a tsakar gida yasameta tana kuka, mamakine ya rufe shi dake duk yan gidan suna tsakar gida har da umma tasa an shimfiɗa mata taburma, dan shan iska, tana shigowa tasaka hanun akai tana, shashekar kuka, duk hankalinsu ya tashi dan har sun mike, ganin mashkur ɗine yasa suke tambayarshi lafiya.
Gaishesu yayi, cikin nutsuwa amma hankalinshi yana kan baby yace.
"Umma wallahi bawani abu bane wai tana son wasu kayan ɓata cikine, shine nace mata, a'a shikenan fa."

          Kallonta umma tayi, tana kare mata kallo cikin nutsuwa tace.
"Shkurah har yanzun baki, girma ba ko, meye abin kuka a cikin maganarshi"

   "shikenan naji amma wallahi idan kuka hanani. an zalumceni dan bana son kome sai yaɗi da kosan rogo, ɗan malele da dambu, shine zaku hanani ba kome"  takarshe maganarta tana kuka,

rike baki, umma tayi tana kallon mashkur dan taɗago aika aikar a mashkur ya ɗirkawa autarta, dariyar da yake shirin kwace mata danne, tace.
"Su kike bukata zaki ci"

   gyaɗa kanta.
" Toh kira min Abdullah yana ɗakinsu, yaje yasayo miki,"

   tana mikewa, umma ta maida hankalinta wajen mashkur tace.
"Tana amai ne,"

girgiza mata kai yayi alamun a'a,

"sai mura da yake damunta, ina ganin ko dan sanyi da muka shigane, amma anjima zamu asibiti."

        "Yana da kyau, kasan wasu matan yanayinsu yakan sauyane da zaran ta ɗauki ciki, abinda bata ci da shi zata koma ci, abinda batayi shi zata tsirfo dayi, abubuwa zaka dunga gani masu daɗi da marasa daɗi, sai an jure stage ɗin farko, sai Allah ya taimaka ashiga stage na biyu daga shi sai stage na uku, san anyi hakuri dasu Allah yabaka hakuri zama dasu."

       Kunyar umma ne yarufeshi, cikin jin daɗi wato asashen shi ya taɓa cikinshi shkurah take ɗauke dashi. Godiya yayi mata yace zuwa dare zaizo ɗaukarta.
  Dan yau suka dawo,

     *........*

Asibiti ya nufa, kafin ya shiga yakira abokinshi Y Tilde bayansu gaisa, yace.
"Batun yarinyar nan, ka gama kome akai dan gobe nake son akawo min ita,"

     shiru yayi, cikin jin daɗi yace.
"Alhamdulillah, nagode sai ka iso naji daɗu sosai"

      sannan ya isa cikin ward ɗin da Maina yake, nan ya same zubaida har da Ubaida ga Mommah, itama tazo sai kuka suke a cikin ɗakin dai dai inda maina yace.
"Sabida zalumunci yarinyar nan, tana rokona da Allah banji ba haka narufe idanuna naketa mata haddinta, ban taɓa ganin ɓacin ran Mashkur ba, sai a ranar tunda muka taso be taɓa saka, hanun a jikina ba, sai akan shkurah, haka nashiga tsakaninsu na raba masoyan gaskiya, taya zan gama da duniya lafiya, taya zanyi kyakyawar karshe, Don Allah ku nemo minsu na roki yafiyarsu."

      Karshe maganar yayi, cikin kuka shiga ɗakin mashkur yayi, ya gaida yan ɗakin sannan ya isa gurin maina yace.
"Ya jikinka my broda, "

        Hanunshi ya mika yana niman mashkur cikin kuka, yace.
"Ɗan uwana, har ynz kana fushi danine, da kayi hakuri ita kanta duniyar nawa take kana kallon ko tafin hanuna bana gani balle nasan waye a kusada ni, amma kai naji a jikina kaine, Nasan katara iyalai yaranka nawa, Allah sarki ni bani da wanda idan na mutu zasu min addu'a anyi min auren na wulakantar, gashi ubangiji ya nuna min ezina, ɗan uwa kayafe min kace Shkurah ta yafe min, "

      "Wa ya faɗa maka, baka da me maka addu'a kana da ita, kuma gobe za'a kawota, Yarka da Shkurah ita kanta batasan yar tana nan ba, sakamakon abubuwan da suka faru yasa tasame matsala har aka cire baby a jikinta bata sani ba, lokacin da muka sake haɗuwa ɗa ita, tana cikin wani irin rayuwa dan ta manta da kowa har, dani cikin ikon Allah narabata da inda take, anan nasame files ɗinta ɗaya na ciwonta, ɗaya na yarinyar ankaita gidan marayu, naje gidan marayu suka tabbatar min an ɗauki yarinyar a hankali nabu diddigin, wanda ya ɗauketa ba muslumin bane, kiristane, nan muka shiga niman karɓanta yace baisan zance ba, shi ya haife yarsa ni kuma, nace nine mahaifinta, abiin har yaje ga hukuma, inda nanuna musu nima jami'n tsaron kasane, nan yan sanda suka tura case ɗin zuwa kotu muna zuwa, aka tura mu asibiti, duk da lokacin na rasa shkurah dan saura kwanaki a ɗaurq mata aure da na'im,

     Gashi nayi furinci nine mahaifinta, kuma ance muyi gwajin jini duk na karaya, da haka, koda muka je aka ɗibi jinina da nata aka gwada yazo ɗaya, da nawanca bayi dai dai ba, sau uku akayi sannan aka bamu sakamako muka dawo kotu, nan alkali ya amshi yarinya ya bani, mutumin nan ya tada rigima sai an biyashi kuɗinshi da ya kashe Banyi kasa agwiwa ba, na ce nawa ya kashe, abin haushi wai dubu arba'in da biya, dan nanuna masa y'ata tafi kuɗinshi daraja na bashi miliyan biu sannan natawo da ita, naso na kawota gidansu shkurah sai nayi tunanin karna lalata mata aurenta sai nakaita gurin Abokina, tabbas Maina kazalumunci shkurah, tarasa abubuwa da yawa, amma Ubangiji ya yafe mana, baki daya.,"

        Kukan da zubaida take yafi nakow, kallon mashkur tace.
"Me yasa baka, faɗa min abinda ya faru ba, har nake iya mata gori, Yaya me yasa ka boye min shkurah bata chanchanci abinda nayi mata ba, shi yasa aduk lokacin da nayi mata gori take kuka, kaman ran zaifita, ashe ita tasan ciwon da take ji, ashe ɗan uwanane silar lalacewarta, Amma ko bakome ta nuna min, kuskurena,"

             Kuka suke, dukkansu a ɗakin banda mashkur da yafiso jin ciwon kome, ɗago kai maina yayi, yace.
"Na bar maka Yarinyar dukkan sannan akwai dukiyata a rabawa marayu da marasa karfi, akwai wasu takarduna na mallakawa Yarinyata, akwai abubuwa da yawa karaba musu ita da mahaifiyarta, sai kuma wasu kuɗaɗe a banki da akwati kabawa Abba da Nana, mashkur kaine Ubanta bani ba, domin nasan bazan sake kwana ba,  don Allah kataya ni neman yafiyar shkurah."

"Insha Allah zan kawota anjima,"

            Kwanciya maina yayi tare da rufe idanunshi kaman me shirin barci.

          Ajiyar zuciya yasauke, sau uku, sannan yayi shiru, hanunshi na sarkafe da juna, zuba masa idanun mashkur yayi hawaye na zuba daga idanunshi cikin sanyi murya yace.
"Ubangiji ya jikanka, Muh'd Allah ya yafe maka kurakuranka," kukane ya kwace masa, me cin rai.

Duk wannan abinda yake, faruwa Sarki hussain yana tsaye abakin kofa, kuka yake shima tabbas da laifinsu na sakawa maina ido har yalalace."

   Lulluɓe gawar sukayi nan aka ɗaukeshi sai Masalaci gwallaga acan akayi masa wanka da sallah, inda aka kaishi gidanshi nagaskiya,

      

        Shkurah na tsaka da cin abincinta mashkur ya shigo, sun taɓa hira da umm nan yake faɗa mata rasuwarda akayi musu, zasu tafi da shukrah ne, nan tayi masa ta'aziya tare da musu fatan a dawo lafiya, haɗa mata abincinta umma tayi, sannan suka fito sai azare.

Karfe biyu suka, sauka banda barci babu abinda take ji, gurin mommah ya kaita shima yashige, ɗakinshi na gidan.

     *........*
Washi gari.....
Da safe Mommah take faɗa mata, rasuwar duk da bata wani damu ba, amma jikinta yayi sanyi ita kam fama take da, kanta shi yasa bata wani damu ba, sai wajen azahar Y.tilde ya iso da wata kyakyawan yarinya, wacce ta haɗa kala biyu kalar uwarta da kalar ubanta, idanunta da sufar jikinta na Shukrah ne, Fuska da magana cikin gadara dason iko na maina ne, kafin wani lokacu cikin gida ya ɗauka, kowa son yarinyar yake, shkurah tana zaune a ɗakin nana da mommah aka shigo da yarinyar ganinta sai da, zuciyarta ya yanke, nan mashkur yace ma yarinyar " ga Mommyki ce a zaune."

Tana shiga, ɗakin taje jikin shkurah takwanta,




        Sai da akayi addu'ar uku, sannan Iyayen maina suka nima masa yafiyar shkurah, cikin kuka tace ta yafe kodan Albarkaci Yarinyar,

Kaman yanda yace ayi da dukiyarshi haka akayi, inda shkurah taku karban wanda aka bata fir, ga zubaida ta nane mata kome shkurah musaman da suka san cikine da ita.


     Ranar da akayi bakwai aranar sarki yayu murabus inda aka bawa Mashkur, sarautar katagum,   baya son amma haka ya amsa, sakamakon saka baki da madan shkurah tayi.


     Sati biyu tsakani, yaje ya ajiye aikin gwonati, daga nan akayi bikin sarauta, Sarki na biyar Muh'd Hassan Mashkur.

   Anyi hidima sosai dan naga har da (Yan grp ɗina sunzo😂)



        Bayan wata biyar shkurah nagani zaune da cikinta da yafara fitowa tana cikin ayaba, zubaida ke ɓare mata, cikin jin dadu suna hira,  shigowa yayi a gajiye, niman gurin zama yayi, da gudu shkurah da Nana karama, wato yar maina😂

       Suka danne cinyar  Mashkur, Shkurah cikin jin haushe tace.
"Nana kawai"

itama nana tace.
"Cukula kawai be kukan kitso"

        Faɗa ya kaure a tsakaninsu daga Shkurah har Mashkur sunyi sunyi suhana rigiman abin ya faskara sai da zubaida tace.
"Kaiiiiiiii" duk suka shiga hankalinsu dan suna matukar tsoronta, tunda suka fasa mata show glass tazanesu shikenan suke tsoronta, a gidan Mashkur ana zaune lafiya, cikin aminci da girmama juna, hakuri da juriya, shine jigon gidan.


    *.........*
Bayan wata hudu Alhamdulillah shkurah tasauka lafiya, inda tasame yaranta yan biyu mace da namiji, Mace maryam sunan Mommah, ana kiranta da sajida namijij Sa'id ana kirashi da Sajid.


      Bayan suna ta suka tafi maiduguri da yola inda taje taga dangin Umma  kwanakinsu ashirin,  dan tare da mommah suka, tafi kuma da gayya take jawa mashkur rai, suna cika 22 suka dawo gida cike da ɗauki.


        Ranar da tadawo, sai data gane bata da wayyo dan mashkur sai da yayi mata dalla dalla sabida tasha gyara ya kashe arna har ya gaji, dan dole ya barta badan yaso ba,


Watan yaranta shida, tafara sabon laulayi, Zubaida ce ta yayesu, inda uwarsu take fama da wasu a cikinta.


*..........*
Bayan shekara bakwai, Duk yaran gidan sun zagaye mommah tana musu tatsuniya tana gamawa Mashkur da Shkurah da Zubaida suna shigowa gidan gaisheta sukyu, sannan suka dan taɓa hira,


         Bayam sun gama, suka kwashi yaran sai gida, Dukka yaran Na Shkurah ne, su takwas, maza uku mata biyar sai Shkurah karama yar zubaida dan tundaga kan Shkurah bata sake haihuwa ba, sai dai kulawa da yaran shkurah dan tana matukar ganin girman shkurah,

Raka zubaida ɗaki yayi, inda ya rungumeta, yana kallon fuskarta yace.
"Ina matukar sonki sosai da fatan zaki kula min da kanki"

gyaɗa masa kai tayi, cike da jin dadi dan kusan ɗabi'arshi kenan matukar ba ita vace da girki idan ya shigo ɗakinta sai yayi mata haka, sun jima kafin yayi mata sai da safe yafita.

       A ɗakin shkurah kuwa, har tayi wanka ta gyara jikinta, tana zaune rike da kwai da lipton tana ganinshi ta shanye sannan tafita da, kofin banɗaki tashi tayi brush sannan tafito, suka kwanta, sun jima sosai suna tuna rayuwarsu na baya, kafin aka rufe babin da farantawa juna rai.



.............
*Alhamdulillah, duknasa wasu bazasu ji daɗin lasting page ba amma ni anawa nazarin babu amfanin jan labari yayi tsayi matukar sako zai isa toh Masha Allah kome yayi kuyi hakuri da yanda yazo muku,*


Ubangiji yasake haɗamu a cikin wani buk ɗin Mai Suna *Sadauki*🌹🌈

Fatan alkhairi gareku baki ɗaya👇
Real Mai dambu Novel room
Musha Karatu 2
Mamuh gee Novella
Kundin Qaddara fans
Sidiya And Fans
Husna Kamshi novel grp
Brilliant fans 1
Brilliant fans2
Leema novel grp
Aisha novel grp
Maman Hanan Novel grp
Zauren A.U ADNAN

*Bazan manta daku ba*
musanman Jameela Musa tawa.
Mamuh Gee
Mom Ahmad
Mom Zahra
Naja'atu ta annabi
Aunty Raliya
A-smeen
Asma'u
Mom Haidar
My Bestie
My Jelata.
My Zinnas jelatty
Aunty Aisha
Aunty Kyauta
Maman Ansar
Adda Bestiena
Maman Almus
Maman Hidaya
Duk wanda baiji sunansa ba kuyi hkr

My Watpad fans ina muku fatan alkhairi

Ubangiji yasake haɗamu da Alkhairi.

Sai mun hadu a *🌹SADAUKI🌈* Ayi min hakuri💋

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment