Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

girma, dukda gogewarta tsakaninta da yan iska shafe shafe idan suka matsa toh karshe barci sukeyi, Hajiya Umaima tayi kuɗi a jikin shkurah dan manyan mutane suke fita da ita, amma tsakaninsu😹😹😹

        ****
Sannun a hankali lokaci yaja sosai cikin shekara hudu kome ya faru, Mashkur ne zaune a ofis ɗinshi yana ta aiki, a computer, ya jima sannan ya mike ya haɗa kayanshi sai gida fuskan nan ba yabo ba fallasa.

   Gidanshi ya koma, tundaga bakin kofa yake jin zazzakar muryanta tana ihu da kiran Daddy Daddy, da sauri ya shiga ya sameta tayi kuka idanunta sunyi jajur yar mashkur yarinya me kimanin shekara uku, ɗaukarta  yayi yace.
"Shkurah me ya faru kike haka ke dawaye"

    turo baki tayi, gaba tace.
"Nida Mahne ta hanani shan bobo, wai batason wanca aunty me sunana" tayi point ɗin babban Hoton shkurah wanda aka ɗauketa ranar saukarsu,

     murmushi, yayi sannan yace.
"Manta da ita, mukan muna sonta ko," sauke ta yayi ya taka har wajen  yana kallon hoton fuskasa ɗauke da murmushi kaman yanda take murmushi yace.
"Kina ina, ne nasan kina raye, yaushe zaki dawo gareni, oo, okni nazo kenan"

   tsaki Zubaida tayi, tace.
"Romeo sai muje kacire kaya, kazo wajen gunkinka ne, karka damu ta jima a kasa dan tsutsa sun gama wantadarta"

Shiru yayi, yana kallonta.

****
U.S.A
Kanal muh'd Hussain Muh'd a gaban ogansu, yace.
"Muh'd zamu turaku siriya, kuma muna son aiki me kyau, bamu son wasa, katabbatar ankai harin wuta tasama da takasa zaka iya tafiya."

      sarawa oganshi yayi, yafita wani murmushi, ogan yayi, sannan yace.
"Nasan yanzun, kakusan mutuwa, saura kaɗan zan gama da kai very soon"

        Fita yayi zuciyarshi ba daɗi, kusan sati biyu kenan, yake fama da wani mugun mafarki, gashi yana ganin iyayensu suna gudunshi sai, watsar da mafarki yayi ya shiga mota.

****
Zaune suke, a wani gurin cin abinci, kana ganinsu kasan wayayyune, suna gama cin abinci suka tashi ita tabiya kuɗin, zasu fita kanta a sunkuye tana, saka wallet ɗinta, A cikin jaka, sukayi karo da juna, zata faɗi yayi maza ya tareta,

          Kallonshi tayi sannan ta mike tafita, shima binta yayi da idanun tayi masa bakarya,

 
         Tun daga ranar ya shiga bin shkurah tuɓ bata kulashi har suka zama abokai.

 

        Agajiye ta zube a falo tana maida numfashi kallon hajiya umaima tayi, sannan tace.
"Hajiya, na gaji don Allah yau karki haɗani da kowa ina son zanyi barcine"

      "Toh preety ba damuwa" inji hajiya umaima,


   ****
Zaune take akan sallaya bayan tayi, mafarkin shkurah tana ihu, ga wasu mugayen halittu suna kawo mata sura, gudu take sosai a cikin Dawa, wani bakin kurane yazo ya kai mata mangari ta zuɓe kasa yaje zai kai mata cafka, Mashkur ya tureshi, rike hanunta yayi suka fara gudu sai da suka same wani dutse suka hawa, nan kuma shkurah da mashkur suka rabu yana kuka.

   A firgice ta tashi tayi addu'a san ta shige ban ɗaki ta ɗauro alola ra fara sallar nafiya.

      Wannan mafarkin ya tsayawa Umma a zuciya duk da shkurah, tasan shkurah, Addu'ar niman tsari tayi indan tana raye, Allah ya kareta, daga fitinar zamani idan ta mutu Allah ya jikanta.

   ****
Tagume yayi,cike da takaici, kuma bawani abu bane yaja haka, sai turashi kaduna da akayi ranshi ya gama ɓaci, mikewa yayi, yana nazarin yaushe zai sake farin ciki, tunda Shkurah ta tafi har ynz be sake samun farin ciki ba,

    komawa, gida yayi yana shiga ya zuɓe a kujeran falon, yana rike dan kanshi da yake masa barazar fashewa.

Cikin gidan ya koma, ya ɗakinshi sukayi kiciɓe da Zubaida, tana haɗa masa ruwan wanka dan taji shigowar taimaka masa tayi ya cire kaya ya ɗaura towel zuba masa idanun tayi tace,
"Bansan meke damunka ba, amma kayi, hakuri"

       tausayi tabashi, iya kokarin tanayi, amma sai ya shafe sama da wata uku, basu kwantawa waje guda ba, ba zai manta, ba rabon shkurah yasa ya fara, kula al'amarinta dan sai da suka shekara da rasuwan shkura, ranar yana cikin wani hali, yaje mata, dukda ya sameta full, amma be hana shi kiran shkurag ba dan itace a ranshi.

*Ina yinku*💋
Gaskiya comments da Voting ya yayi😥
3/4/21, 9:46 AM - Ummi Tandama: 🙆🏻‍♀ *QADDARAR RAYUWATA* 🙆🏻‍♀


mai dambu





*KISHIYATA JIHADI NA*
*YARO MA NAMIJI NE*
*NI DA YAYA MOH'D*
*WANI JINKIRI.*


'''Kuyi hakuri jiyan abubuwa da abebeɗe suka sha kaina, kuma akwai matsalar idanun shi yasa na ɗaga kafa😎

kar wata ta juya min maganata dan nima ya bani dariya oll de best👎'''😹😹😹😂

*Page 15*

Tunda yashiga ɗakin da yasauka, hankalinsa ya karkata, akan preety amma abubuwan da yake gabanshi ya hana shi yasake bin takanta, zuciyarsa ce take azalzalarsa da tunaninta, shidai kansa ya gama kullewa,ana mutuwa a dawone.

Ya jima yana tunani, sannan yacigaba da harkansa dan abinda yasa, a ransa matukar suka sake haɗuwa, toh sai ya tambayeta.

****
Zaune take, tana nazarin wani buk ɗin wale soyinka hankalinta yayi, nisa sosai a labarin dake, cikin buk ɗin, wayarta ceke tsiwa, ɗauka tayi tana dariya, tace.
"Aslm, bros bilal ya kake ya aiki."
Daga can, ya sake murmushi yace.
"Ubaidatu, Alhamdulillah, Ya zawarawanki,"

Dariya tayi, sosai sannan tace.
"Suna nan sai karuwa, suke."
"Hmmm, toh kenan akwai masu karfi kenan, har ina shirin faso kai ashe akwai masu, kurmusani." ya faɗi haka yana murmushi cikin nutsuwa."

Zarro idanun tayi, da mamaki rufe bakinta tayi tace.
"Kasan abinda kake, faɗa kuwa rufa min asiri."
Dariya yayi, sosai cikin nutsuwa, yace.
"Karki, ɗaga hankalinki ba wasa nake miki, ba ina sonki tsakanina da Allah, don Allah ki amsa bukata, karki ce min a'a kinji Ubaidatu."

Datse kiran tayi, jikinta narawa, ta fashe da kuka, tun bayan rabuwanta da Maina bata saka maganar aure a gabanta, ba duk wanda yazo bata kula shi, asalima tsoron maza take,
(Anya haka zayu kuwa)

****
Headquarter NATO dake siriya, shirin tafiya suke, gefe guda ya takure ba kome ke damun, ba wani abu ke damunshi ba sai yarinyar jiya da yayiwa raping kukanta yake ji a cikin tsakiyar kanshi, baki ɗaya jiya ya kasa runtsawa, yana rufe idanunsa ita yake, gani cikin mawuyacin.
muryanta yayi masa kama, da, muryan da bazai taɓa mantawa, ashekara huɗu bai manta da sautin muryarta ba,


Ɗauko, yar karaman kwalɓar giyansa yayi ya, kwankwaɗa, ji yayi full. mingirewa yayi a cikin a ofis ɗinsa, sai barci.

Hmm maina kenan ya manta da Allah, baya sallah ballantana salati kullum bashi da wani aikin niman manta. Dan ma yanzun ya soma jan baya sabida k'ugunsa da take masa mugun ciwo shi yasa ya ɗan rage, da matan titi sai na gurin yak'i irin matan da suka taimaka, toh ware masu yan kananun yan mata suke duk su lalatasu.
*(Wallahi ba karya, nayi muku ba siriya da sauran guraren da ake, yak'i Allah abinda sojojjin yak'in U.s.A suke, kuma duniya tana ganinsu, babu wanda ya isa ya dakarta dasu, kuma daga matan musulmai da na kiristoti sukewa, Kwanaki A kin tv Frence24 aka nuna wata matashiya tana bada labarin yanda tasha izaya a hanun yan ta'adda da sojojjin nato,😭😭😭😭 Allah kakare mana y'ay'anmu)*

Tafiya yake, cikin zafin sahara ga k'ishirwa, xafin saharan da guguwar haɗi da kasa sukayi sama da shi, sai da iska yayi watan gaririya da shi sannan aka makashi da kasa.

Mikewa yayi dakyar, yana tangaɗi, juyawa yayi gabar da yamma kudu da arewa, bega kowa ba, tafiya tacigaba da yi ga bakinsa, ya mushe daga can ya hango, wasu mutane da bakaken kaya, da sarsafa ya isa, gurinsu duk sauran babu fuskansu a buɗe yake, sai guda ɗaya da take durkushe, fuskanta da nik'af kuka, take.

Juyawa yayi, wajen manta suna rike da kofunan ruwa, sai tsiyayawa kasa suke zuwa yayi, ya sa hanun zai tara,
wani irin, magana yaji, me kama da faɗuwar aradu, a razane ya ɗago kai yana kallon wacce tayi, maganar.
Sake kai hanunsa, jefar da kofunan sukayi, mikewa yayi murya na rawa yace.
"Baku da hankaline, da zaku zubda ruwan babu ga halin da nake ciki bane"


Juyawa yayi zai bar gurin karan kaman wuka yaji yaaake, juyawa, aikuwa binsa sukayi, da gudu yana gudun yashin sahara na, rufe masa, idanun sai da suka kure saharan sannan suka shiga, wani mugun daji me ciki da sark'ak'iyan, gudu yake har sai da ya iso bakin wani wawakeken, rami sannan ya juya yayi, yana basu hakuri.

Ratsa cikinsu tayi, suka bata hanya, tana isa gabansa ta zaro wukarta ta kare masa kallo sannan ta suka masa, ɗaga nik'af ɗinta tayi, zaro ido yayi zai magana, turashi cikin ramin tayi me cike da ababen tsoro.

"Innalillahi...." da ita ya farka zuciyarsa tana bugawa, Ogansa yagani a gabansa fuskansa ɗauke da murmushi, mika masa cup yayi, na ruwa,
(rashin sani yafi dare duhu, da yansa abinda aka bashi da be amsa ba arne ne, fa koda yake babu bambanci, dan duk wanda yabar sallah har na kwana3 da saninsa babu lalura toh a ingantattun hadisai an tabbatar da shi ɗin kafirine, dan sallah itace ke banbanta kafiri da musulmi, toh maina baya sallah.)

Karba yayi yasha, sannan ogan yafita daga, ofis ɗin maina.


****
A cikin kwanakin da yayi, cikin nasara yagama kome, saura komawa gida, abinda ya tsayida, shi, tun ranar da suka haɗu basu, kara haɗuwa ba ga bakon al'amarin da yake ji game da ita, zuciyarsa tana tabbatar masa ita ɗin ce.

A gajiye yashigo, cikin hotel ɗin yay nemi guri yayi faking, sannan ya, fita ya kashe motar.
Ganin yanda matasa ke shiga wani garden a cikin hotel ɗine shima ya bisu yayi ko Allah zaisa adace ya ganta, abin haushi ana shi, shiga akayi suka ce yasake kaya, zuwa englishi wear, komawa yayi ɗakinsa ya sauya kayanshi, zuwa wani rigar army colour, wandon 3qrt itama, kalar rigar,face cap yasaka, sannan ya ciro wani takalminsa itama army, colour,,,,Yayi bakarya.

Da sauri yafito, duk inda ya wucce binsa ake da idanun, har wajen taro yaje yana ta raba idanun hangota yayi Manoor yana saka mata zube, zuba hanunsa yayi aljuhu, ransa na masa, zafi.


****
"Wallahi ba zamu yarda ba, akan wani hujja, Alhaji A.malik, ka taɓa kusantar preety,"

Alhaji ɗalha ya jefa masa, tambaya.
Girgiza kai yayi, yace.
"Ina fa, duk hajiya Umaima ta haɗamu da wannan fitinar duk lokacin dana ɗauketa, barci nake gashi har maganin kuzari nake, kasan nawa nakashe kuwa, kusan miliyan ɗaya da rabi nakashe mata, abin haushi ko murjeta ban taɓa ba, sai aikin barci."


Hararansa Alhaji tanimu, yayi cikin jin haushi wani tsaki yayi sannan yace,
"Dube shi, miliyar 1½ har wani kuɗine, toh bari kaji nabata kusan miliyan biyar, ga motar miliyan bakwai ko matata ban sayawa ba, balle y'ay'ana, yarinya sai faran dabara."

Dariya darackta yayi sannan yace,
"Ni banga laifinta ba, Wancar ita munafukar, maza kifito mana da kuɗinmu,Dan har da kuɗin mutane na taɓa, maza kifito mana da kuɗinmu kafin mu shayar dake madaran rashin mutunci."

Dhaka mata tsawa yayi, jikinta na rawa, tace.
"Wallahi babu, kuma bansan baku taɓa hayeta ba shegiyar yarinya bari na kirata, sai kusan yanda zaku fanshe kuɗinku, dan ni maganin jin daɗinku nake bata, ashe bata baku kantama ba kuyi hkr"

Kiran layin shkurah tayi.

****
Kallon zuben tayi fuskanta ɗauke da mamaki, tsalle tayi ta rungume Manoor tana ihu, farin ciki, cikin dabara yake niman su haɗa baki sai ga kiran hajiya umaima ya shigo, ɗauka tayi tace.
"Mom, gani nan wayyo Allah," dasauri ta juya zata, fita, manoor na tambayarta, lafiya bata kula shi ba, tafi da mugun sauri.
Mashkur na ganin haka, ya rufa mata baya shima, wajen motarsa yaje dan baya sake, fita babu keyn motarsa a aljuhu,

Yanda tafigi motar, yasa shima bin bayanta yayi, bam bam ti bam bam, har unguwar sarki suka a tare suka isa.

ko parking batayi me kyau ba tashiga gidan, tsayawa yayi, daga waje yana jiran ganin fitowar wani.

......
Tana shiga tasame, umaima a zaune, dagudu ta karasa gabanta ta fashe da kuka, tace.
"Mom....."

Kauuu, ta ɗauketa da mari, ta hankaɗeta, da kafa, tace.
"Kuyi yanda, yadace da ita, sauran ku wullar da ita, waje dan bana, bukatarta, Karki ji zafi, zaki kawo min matsala a sana'ata ce, kuma kicire a ranki, ni ba Uwarki bace, dan nima tsitoki akayi daga gombe ne ko bauchi, aka kawo min ke ban taɓa haihuwa, ba dan kema kinyi abinkunya nake tunanin zaki, gudu hatsari ta afka miki, kika manta asalinki wayasani ko shegiyace ke ɗin, gata nan kuyi waje da ita."

Rike kumatunta tayi, wasu, hawaye masu zafi suna zarya a fuskanta ba marin bane yayi, mata ciwo sai maganar Umaima, duk wannan maganar a kunnen Mashkur wanda yaji shiru ya shigo dan ganin meke faruwa,

Jikinsane ya ɗauki rawa, hanun yasa aljuhu, ya ciro wayarsa, ya kira mommah yace.
"Mommah, N,,,,,a,,,,,,s,,,,a,,,,m,,,e ta again tasake shigowa rayuwata, akaro na biyu"

ihunta yaji, Darakta ya rike gashin kanta yana janta,
rike hanunsa mashkur yayi, sannan yace.
"Nawane kuɗinku, zan biya ni zan ɗauketa"

"Eyye har ka isa, ka biyani kuɗina.Kai ɗin ɗan gidan Uban waye, ni ba kuɗi nake bukata ba wannar suran me ɗauke da kayan morewa,"

ɗaga kafaɗa mashkur yayi, cikin ko in kula, yace.
"Tunda baku, bukatar kuɗi, toh bari na hauna muku, bullet ina ganin kowannenku zai same bibiyu, agoshinsa"

zaro yar bindigarsa, ya zare gidan harshashinsa ya hure,

Alh ɗalha, ya miki, ya ɗaga hanun sama, yace.
"Indai nine, na bari kuɗin akwai Allah"😟

saketa darakta yayi sannan ya fita, zuwa bakin kofa, yace.
"Allah ya isa min, kuma ban yafe ba, mugayen azalumai, wata kika ci ba kuɗi, wuta bal bal, kalidina fiya abadan." ya fita da mugun gudu, duk da halin da mashkur da itasuke ciki be hanasu kwashewa da dariya ba😹😝 mashkur harda rike ciki,

Alh A. maliki, da rarrafe yake tafiya, yaja hullarsa ya rufe, fuska, ga babbar rigarsa sai yawo yake, durkusawa mashkur yayi, ya taɓa shi, arazane, ya mike, yace.
"Yahayyun ya qayyun, ka rufa min asiri, yaro na tuba, bazan sake niman mata ba, kai na rantse da izufi 80, kai har da uwata, da ubana, idan nasake kallon mace, kazane ni"(😭)

Ya fashe da kuka, yana bawa mashkur hakuri, nuna masa hanya mashkur yayi,

yafita yana, ganinsa a waje, yace.
"Kuɗina da kika ci ban yafe ba, kuma idan na mutu fatalwa zan zama nazo miki, kai muka ɗan fashi sai na faɗawa yan sanda suzo, kama ka,"

lekowa mashkur yayi yace.
"Awo haka kace"

kafin mashkur ya rufe baki A,A maliki yayi, dungure da fitsari, a wandonsa karo, uku yayi kafin yafita daga gatee ɗin gidan😹


Jan kofar falorn yayi ya rufe yasaka key ɗin aljuhunsa sannan,
ya nuna mata kujera yace.
"Zauna kafin nafito, zanje wajen magajiyarku"

Ko kallon be isheta ba, tayi banza da shi, tana tsaye,

Shiga ɗakin yayi, yasameta, tana niman wajen ɓoya, "Ke zo nan, me kika sani akan wancar yarinyar,"

ya tambayeta fuska a haɗe jikinta na rawa ta buɗe wardrob ta ciro masa files har guda, biyu, sai sark'arta da zube, da kayanta da tayu hatsari dasu sannan ta masa bayanin a nutse, kallonta yayi ransa a ɓaci yace.
"Kinsan wacece ita, a madadin ki nima mata lafiya, sai kika ɓige da koya mata, karuwanci, toh ki kiyayye dawowana dan ba zai miki, kyau ba."

ya juya yafita.




Muraaaaaaaaaaaaaaaaaaaaaaa ya kamani.....😤😷
3/4/21, 9:46 AM - Ummi Tandama: *🙆QADDARAN RAYUWATA🙆*
_SHUKRAH_
Mai_Dambu


*Aunty Binta, Maman Sadeeq, Aunty Balkisu,Husna Kamshi, tare da Saheebata,😹 Ina godiya abisa yanda kuke karanta buk ɗin Qaddaran Rayuwata nagode sosai*

Masha karatu2 kuman ina godiya,sosai💕

Kundin Qaddaran Fans
Mamuh gee Novellah
Tare da

Real Mai Dambu Novel room
Aisha Novel Group💘

Musaman Deeja mashi thank you😇
   Sauran grps da ban ambace kuba, ina godiya tare da fatan Alkhairi

_Da kwarin gwiwarki nake tsaye da kafafuna,Indan banyi karya ba kece tauraruwar Littafina kuma ke haske ce, Ne bayyana kome,Ba zan gaji da jinjina miki ba, Hakazalika ba zai daina gode miki ba bakina ba zai gaji ba Inayinki Meelat ɗina😘_,

'''Kutt😂,Malamata dake da yan group ɗinki ina muku, fatan alkhairi Aisha sada micika😎'''



~Koda waye kike, zagin iyaye haramune, Idan bamuyi musu addu'a ba, toh karmu bisu da zagi, sannan ba mutunci bane, zagin mutun da baka san waye shi ba, haka ma kema bansan wacece ke ba, kinga babu adalci mu zagi juna, sannan duk wanda ya daraja iyayensa Toh har abada bazaiso a zagesu ba da wannan nake jan hankaliki baiwar Allah ki daina zagin babu kyau, abin kunya ce sannan don Allah ki bar zagin Jameela musa, Dan darajar iyayenki idan kina ganin girmansu toh ki daina don Allah,~👏 Allah kasa mudace duniya da lahira

*page 14*


B'ale botir ɗin rigarsa take, cikin nutsuwa, kamshin turarenta yake shaka, wanda daman tashafane dan shi,irin turaren haɗin nan ne, me birkita tunanin, a gefe guda kuwa gyaran aure yake, (Amma ku nemi oganniya ko husna sunsan sirrin gyaran aure)

             A hankali, kamshi yashiga lungu da sako na jikinshi lokaci guda yakai hanunshi k'ugunta sannan yakai kansa dai dai kunnenta muryanshi k'asa k'asa yace.

"My zuby, ina son turarenkin nan"

        murmushi tayi, hankalinta nakan gashin kirjinshi cikin wani irin salo me ɗaukar hankali,

       hanunshi yakara sakawa yajanyo dan wani irin,feeling yake jin akanta,  hmmm Allah sarki Zuby da zata gane da tanime soyayyar mashkur ba, sha'awarsa ba, dan ko kaɗan baya sonta yana tare da itace sabid, iyayen asalima zuciyarsa tana, tare da shkurah.

           Wasu abubuwa, sukewa, juna cike da muradin kasancewa tare, tsayiwane ta gagaresu harta kai suka zube, a kasar ɗakin, jikinsa na rawa, dan ya gama matsuwa ya akai gidan karshe,

     rike hanunshi tayi, ta buɗe idanunta da suka kaɗa sabida abubuwan da ta loda, shima zuba mata, ido yayi wanda suke cike da sha'awarta fal muryansa k'asar makoshi, yace.
"Me ye haka,?"
      ya jefa mata tambaya.
      Zanin gadon ta janyo, ta rufe jikinta muryarta na rawa tace.
"Jikina kake bukata, ni kuma sonka nake bukata, kasoni ya Mashkur koda kaɗan ne, wallahi zan kyautata maka fiye da yanzun, don Allah."

       Kare mata kallo yayi,yana tuna abinda Maina yayi masu, mikewa yayi ya nemi duk tulin bukatarta yarasa dan bakin ciki da kiyayyar Maina suka dawo masa sabo towel ɗinsa ya ɗauka yashiga banɗaki kuka tasake mara sauti, ga kayan matan da tasha ya fara jikata, wullar da zanin tayi,ta shige banɗaki,
               Yana shiga yasakewa kansa ruwa, aikuwa tana shiga banɗakin tarungume bayansa, tana zubda hawaye tare da bashi hakuri,

         tausayi tabashi aiko bakome uwar y'arsace juyawa yayi ya rungumeta dakyar suka, gama wanka,dan shafe-shafe, sumbace² sukayi, sannan suka fito, ba zai iya hakuri ba dan haka, gado suka dire nan aka shiga, kashe (arna😎)

      Bayan kura ya, lafa sai kace a filin yaki, suna makale da juna, yana shafa kanta yace.
"An turani kaduna, aiki kuma zanyi sati ɗaya, Insha Allah zan dawo ki haɗa min kayana dan gobene tafiyar."

        "Allah ya nuna mana, ya kaimu goben, amma Ya mashkur ina son kuɗi, zanje azare bikin." inji zuby.
       Matsalar zuby, kenan ita, bata da matsala kuɗi, kawai abata, kuma inda,zata same kuɗi toh bata da case kuma ba kananun kuɗi yake narka mata ba, yana tafiya zataje siyan magungunar mata, da mekyau da mara kyau ata cuse cuse, ita nam zata (bulge Angon matacciya😂)


       Wanka yashiga yayi ya ɗauro alola yafita masjid, tana kwance amai take ji, sosai dakyar ta mike tashiga tasake ruwa wanka tayi dan idan tace zata fara tsarkine amai zatayi, sabida karnin da take ji na, ruwan abinda take cusawa, shima mashkur ɓoye mata, ƴake amma tana matukar takura masa,
      bayan tagama wanka,ne tayi amai sosai, har sai da jikinta ya mutu, kallon kanta tayi a madubin dake banɗakin, kallon kirjinta tayi sun ɗan cika, sosai alamun shigar sabon ciki.
Ranta ne ya ɓaci, tana kallon kanta, a fili tace.
"Ina dakon banza, bayanshi bae san inayi ba, kaima flushen ɗinka zanyi, duk ranar da yafara sona zan sake haifa ɗa, ko cikin Shkurah abisa kuskure yashiga, balle wannan zubda shi zanyi."


Zubaida kenan bayan lil shkurah tasake samun ciki har sau biyu tana, zubdawa na shkurah ma babu yanda batayi ya zuɓe amma, cikin yaki sai ma azabar da tasha.

****
Zaune Alhaji Hammayo yake a wheel chair ɗinsa kallon Umma yayi cikin nutsuwa, duk da maganarsa bata fita, yace.
"Habiba kin hana kausar shaidawa y'an uwanki, inda kike sabidani ko, Habiba na amince miki kije kisada zumunta, kije kafin lokaci ya kore miki, kije kar laifina yayi yawa, nakasance mutum mara adalci, don Allah ki yafe min."

       Haɗiye kukanta tayi, sannan ta girgiza kai, tace.
"Zan tafi gida, amma nafison tafiya dakai, tuntuni nake binka muje germany ayi maka, aikin kashi amma kak'i toh taya nima zan iya tafiya nabarka idan ka amince sai muje ayi aikinki, shikenan tunda likitoti sun tabbatar zaka tashi, kashinka basu nakasa ba."

         Ta karshe maganar tana kallon,shi cikin nutsuwa, sake kallonta yayi, sannan ya gyaɗa mata kai alamun ya amince..

      Farin cikine ya lulluɓeta kaman t daka tsalle,yanda take ta zubawa ubangiji kirari shagala yayi, da kallonta dan wani zubin, komawa yarinya ɗanya shakaf take masa, idan tayi wani abu kuwa, sai takoma kamar shkurah, ɗago kai tayi suka haɗa idanun kashe mata ido ɗaya yayi , kunya yasa tarufe fuska,

      duk wannan abun da suke akan idon bilal, yana tsaye shima sun burgesu, shima yana ta dakon son amma yarasa yanda zayi dan be san yanda za'a karɓi alamarinsa ba dukda wacce yakeso, batasan yanayi ba,

  gyara murya yayi haɗi da sallama, zama yayi ya gaisu, kallonsa Alhaji hammayo yayi, sannan yace.
"Duk yan uwanka sunyi aure, dakace karatu, kayi ynz kana aiki, me ye matsalarka da aure"

           Itama umma zuba masa ido, tayi tana nazarinsa, shigowarsu mama da ummi yasa ta, maida hankalinta garesu.

           Sake mai-maita masa tambayar yayi, ɗagowa yayi, cikin nutsuwa.ya ɗan saci kallon Umma sannan ya maida hanklinsa kan Babansa yace.
"Ina da wacce nake, so amma bansan yanda zaku amshi alamarinta ba, dan...."

       Sai yayi shiru, ya sunkuyar dakansa kasa yana wasa da kafet ɗin falour ɗin.
"Humm, ina jinka akwai matsala kenan, a gun yarinyar"

"A'a babu matsala kawai, bazawara ce, kuma yar wajen Umma kausar ce."

     A tsorace ya kai ayar maganar dan gani yake Umma zata rufe shi da duka, sai yaga akasin haka, fuskarta ce ta yawalta da farin ciki, haka yanuna masa, tayi na'am da zabinsa, albarka tasaka masa, sannan tace zata kira kausar ta faɗa mata, inyaso idan suka dawo, sai aje niman auren.

  Zarro idanun yayi cikin jin kunya yace.
"Umma ban faɗa mata, ina s..."

       Dakuwa tai masa irin zagin nan, a ware hanun ta nuna maka✋😜
(_I'm real miss my grand Mah yaseen irin zaginta kenan aware hanun a nuna maka akan fuska😹_)Ubangiji ya gafarta musu, da rahama,



        Fita yayi yana dariya, tun lokacin da mommah tasan Umma tana nan bauchi, bayan mashkur ya sha dogon jinya yatashi a nan take faɗa musu,ai shkurah yar uwarsu ce, dan haka nan ma gidansune ko ba shkurah, toh ya ɗauki umma,  a matsayin uwa dan tare suka sha nono,

       A yanzun haka, ɗaukar lil shkurah yayi ya kawowa umma ta zauna a wajenta dan Mamanta bata wani kulawa da ita,

  ****
Washi gari...
Da safe wajen seven, mashkur yabar garin bauchi sai kaduna,

     ****
Garin kaduna,tsaye take rike da k'ugunta, tana kartawa wata yarinya rashin mutunci, akan ta kula mata saurayi cewa take.
"Yar iska, karuwa, banda rashin aji ina, zaki kula wanda yace baya sonki, ke wallahi nasake kamaki da abokina sai naci,"

       Janta yake yana rarrashinta cire hanunta tayi tace.
"Don Allah sake nk, Manoor zan ci kaniyarta jaka kawai, me bin namiji"

        Fincikota yayi da mugun karfi dake hill tasaka ai kuwa tayi tuntuɓe, ta faɗi, Ihuuuu tasaka tana yarfe hanunta, ita yarinyar kuwa da kawayenta suka kwashe da dariya,

      Dake a bakin wani hotel suke sunzo wani party kawarsu tana birthday shine yarinyar taje wajen abokin Shkurah wato preety.

       Shi kuma shigowarsa kenan hotel ɗin yazo kama masauki, yaga cincirindon matasa, maza da mata, gashi sai dariya suke ta kyalkyalewa.

     Faɗuwar be dameta ba, kaman dariyar da suke mata, manoor yayi-yayi ta tasha amma taki dan kafarta gocewa yayi, kuka take dan har muryarta na tashi, zuwa yayi ya wucce amma sautin kukan ya daki zuciyarsa, wani bak'on al'amari me ɗauke mamaki ya shige sa,

       Runtsa idanunsa yayi ya wucce,
     Cikin muryan

Please Login or Register in order to submit comment