Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abinda ya faru jikinshi har rawa yake idanunshi sunyi wani irin ja, kirane ya shigo wayarshi be duba ba ya ɗauka dariya maina yayi sosai sannan yace.
"Kazo da keke napep awala, yara zasuzo ɗaukarka, karka manta kai jami'in tsorone nima kuma haka, dan nayi aiki a inda sukafi naija kwarewa, ko yaya kayi motsi akan idanuna yake dan akewaye da kai yarana suna bibiyarka, kuskure daya zakayi tabbas zan kashe shkurah ta mutu kowa ya huta."

          Kashe kiran yayi cikin tashin hankali, ya juya zuba musu ido yayi sannan yace.
"Muna cikin tsaka me wuya, amma bari nagani Abubakar zan tafi inda suke kaikuma zaka jona wayarka akwai wani agogona, a cikin mota tana amfani da track devicene, duk inda muke zaku iya samun,code nomber tashine, (9yo8ea) kashigar cikin computer ɗinka zakuga inda muke koda a cikin karkashin ruwane,,,,,,,,," kallon umma yayi yanda take zuba kwalla ya je har kusa da ita, ya durkusa yace.
"Koda ni ban dawo ba shkurah zata dawo cikin koshin lafiya, umma na baki  shkurah karama."


Juyawa yayi, wajen Na'im yace.
"Ka kula min, da Shkurah idan ka aureta, dan sarauniyace"


      Daukar shkurah karama, yayi ya sumbaci goshinta sannan yafita dan........

😹😹😹 I like yanda Oga maina yake kafta rahin mutunci fa.
3/4/21, 9:47 AM - Ummi Tandama: *🙆QADDARAN RAYUWATA🙆*


MAI DAMBU CE

*Mashkur da Shkurah, bansan waye a cikinsu yafi shan wahala ba, amma kulara da yanda labarin yake tsakaninsu inda har mashkur zai iya hakuri ya sadaukar da farin cikinshi ga shkurah, toh a wannan zagayen me Shkurah zatayi dan mashkur*👌





*Page 21*

Kifa kanshi yayi akan sitiyerin motar cike da tashin hankali, dafa kirjinshi yayi wanda yake barazanar tarwatsewa,

     ɗago kanshi yayi idanunshi sunyi mugun ja, tada motar yayi, cikin azama, yabata wani mugun wuta cikin kwarewa yake gudu.

Yana wucce(G.g.bauchi) ya lura da motar da yake bin bayanshi kafin ya isa, Awala hotel son sha gabanshi taka birki yayi kaman antsila, da mugun sauri suka, fito basu bari ya buɗe motar ba, suka fasa glass kofar motar,
suka fito da shi suka jefashi a motarsu kiran sienna suka fice a guje.

*.......*
A police headquarter, haɗa track device ɗinsukayi cikin second sai ga, abin yana point ɗin inda suke duk inda suka bi yana nunawa musu,take aka cika mota da yan sanda da Na'im da Abubakar suka, tafi.

......
Ruwan sanyi kalau, ya watsa mata wani ajiyar zuciya tayi ta buɗe idanunta sai akan maina,
       hawaye masu zafi suka sauko mata daga idanunta, cikin rawan murya ta ɗago kai tace.
"Me kake bukata, kuma a rayuwata me yasa bazaka barni haka ba, me yasa bazaka barni na karasa sauran rayuwata a haka ba, Maina kabarni hakw don Allah."

       Wani kukane me cin raine ya kwace mata,

     Janyo kujeransa yayi, zuwa gabanta ya zauna dab da dab da ita, yatsar hanunsa yasaka akan lips ɗinshi, yace.
"Shhhhh, kiyi shiru ya isa haka, nima sonki nake shi yasa nazo a wargaza auren, ina son ki haifa min kyawawan yara masu kama, dake kinga ni bazan cutar dake ba, ga Yarana a nan idan wanca sha-sha-shan yazo sai yazama waliyina ke kuma wani daga cikin yarana yazama naki, idan kuma kika ce a'a" juyawa yayi
        yakalli wani kwai wuta, sannan ya maida kanshi gareta, tana kallonshi jikinta na rawa, cikin idanunta ya kalla sannan ya ɗaga hanunshi kafin ta kalle inda ya saita hanunshi sai karan harbi taji ba karamin razana tayi ba, rike kanta tayi cikin tashin hankali tana kuka,

"Idan kika kuskura kika ce bazaki aureni ba, haka zan fasa kan wanca banza i don't care, kin fahimceni ko"

        ɗago kai, tayi cikin rashin kunya tayi dariya, tace.
"Kayi kuskure Allah, daga kai har shi baku gabana, dan jirgin da ya kwasoku bansan shi ba, balle kuma wai,"

      dariya yayi sosai, kafin ya kalle ɗaya daga cikin yaranshi yace.
" ɗauko sillytap karufe mata baki, kince baki damu dashi bako, ok bari mugani idan da gaskene, kurefe mata baki sannan ku ɗaureta akan kujeran, mu zuba ido mugani."

  *.......*
Suna shigowa, gubi dam daman da jirgin ruwansu suna zuwa suka fito da shi, aka sakashi take suka tada inji,


Tafiya a cikin ruwa, cikin minti 30 suka iso wajen ingiza keyar shi har cikin wajen, daga nesa ya hangota, tana ganinshi ta fara girgiza kanta, cikin saurin tana nuna masa bayanshi dakanta, tana kuka har da bubuga, kujeran da take tana kuka.

       Kafin ya iso gurinta, duka aka sake masa akeyarshi wanda yaja, yayi mugun faɗuwa jini nafita ta bakinshi da hanci, rike kanshi yayi cikin azabar zafin da yake ji kaman kanshi zai cire,

         Sillytap ɗin maina yacire yana dariya, kuka take tare da ihu,

       "Maina wallahi wutarka, daban take kai devil ne, acikinsu kai ogan shaiɗanune Wallahi sai kayi mutuwar wulakqnci" take faɗa masa.

       Murmushi yayi, rike da karfe da yabugawa, Mashkur yana kallonta, ɗagawa yayi zai maka masa tace.
"Don girman ubangijin karka taɓashi ka barshi haka, maina kana tunanin mutuwa kuwa, Maina mashkur bai deserve kake mashi ba, Maina zokayi abinda zakayi min don Allah karka taɓashi."

       Cikin kuka take, maganar tana bubuga, kujeranta.

        Dakyar mashkur yake iya buɗe idanunshi, maina natsaye akanshi ɗaura masa kafa yayi akan kafaɗar mashkur,

          dariya maina yake yana kallon shkurah yace.
"Hhhhhh, kekika ce baki son mashkur yanzun kuma kice min, kar na dakeshi, toh faɗa min, kina sona,"

        saka kafarshi yayi ya duke fuskar mashkur.

      "Maina ban sani ba, nidai kabarshi kawai ko ina sonshi ko bana sonshi, ɗan uwanane kuma kaima ɗan uwankane maina kana da imani kuwa, da kana dashi ba zaka taɓa dukan mashkur ba na amince ina sonka kabarshi don Allah."

"Ina ai mutuwa itace, abinda yadace dashi,"

      ɗago kwalar rigar mashkur yayi, yace.
"Kalla akan idanunka, zan sake mai-maita abinda nayi mata shekara huɗu da suka wucce, sannan na harbeku baki ɗaya,"

      tunkuɗe mashkur yayi ya faɗi,

            Gurin shkurah yaje ya kifata da mari biyu sai da ta faɗi kasa sannan ya ɗagota, yashiga kunce mata ɗaurin da yasa aka mata,


    A gefen mashkur agogon hanunshi ya duba, sannan ya fara kokarin mikewa, dakyar ya durkusa akan gwiwarsa, sannan ya mike, haka yayi dai dai da kunce ɗaurin da maina yasa aka mata, tureshi tayi da gudu taje gurin mashkur,

             Cikin tsananin fusata, maina ya mike ya suri bindigar jikinsa yasaita da niyar harbin mashkur, sai a kafaɗar shkurah har sau biyu,

         Ajiyar zuciya tayi ta zube a jikin mashkur,

         Ganin yasaɓa saiti yasake ɗaukar karfen da ya bugawa, mashkur ya tunkaresu gadan-gadan yaɗaga, ashe akwai wayar wuta wacce ba'a rufe bakinta ba, aikuwa ya haɗu da karfen k'am ya k'ame, wuta tana wasan kura da shi.

(Yau kam naga masu farin ciki irinsu Aunty dada nasari Sadiya zabura, Mommy sayyed Asma'u da sauranku ni natafi zaman jinya maina)😹😹


       Allah sarki, ture kan shkurah mashkur yayi, ya shiga niman abinda zai taimakawa maina da gudu ya isa gurin kujeran da ya ɗaure shkurah, ya maka mashi ya faɗi can gefe guda yana, fizge fisgi,

        Karan harbi mashkur yayi ya kwanta sabida bullet yana shigowa har cikin wajen,  a waje kuwa, cikin sa'a yan sanda suka kashe yaran maina, dan sunki a kamasu saima buɗe musu wuta da sukayi dole yasa akayi musayan wuta, tsakaninsu.

Wasu yansanda suna waje,Na'im tare da Abubakar suka shiga, cikin da wasu yan sanda ganin mashkur sukayi ta ɗauko shkurah a hanunshi dan bata numfashi, haɗa hanya yake da sauri na'im ya isa zai karɓeta ɗago kai mashkur yayi ya kalleshi, ya kuma kalleta, sai ya mika masa ita,

           Na'im na amsarta shi kuma, ya nemi faɗuwa Abubakar da, wani ɗan sanda suka rikeshi aka fito dasu sai satar kallon na'im yake, sau biyu dai na'im yana kamashi, haka da ya gani yasa jikinshi yayi matukar sanyi,


        sakasu akayi a jirgi, sannan aka haɗa maina da yaranshi waje guda, har lokacin bai bar fizga ba.

          Dole aka bar wasu a gurin suka tawo dasu mashkur, ana tsallaka ruwa aka sakasu a mota, sai T.h,

      Sannan aka koma, kwaso su maina,

*.......*
Abubakarne yakira umma, ya faɗa musu kafin wani lokaci asibiti, ya cika da yan uwa, da abokan arziki, Allah sarki umma bata nemi shkurah ɗakin Mashkur taje ta zauna, inda kusan manyan likitotine aksnshi.

         Tabbas mashkur ya daku, dan tattaunawar da likitotin suketayi kenan akanshi, sun kwashi awa uku, kafin suka fito suna magana,

        Umma na ganinsu ta mike idanunta dab da kwalla tace.
"Zan iya ganin yarona kuwa"

      "Eh madam amma don Allah banda hayaniya dan ana son ya wuta," suka ce mata,


dasaurinta tashiga, tasame shi yana barci zama tayi a gurinshi,

Ayya maina, an kawo shi, nan dai sukayita kokarin ganin, ya dawo amma ina, saukin sai a hankali




😂😂😂😂😂😂😂😇 Allah idanuna yake hanani dogon typing, Amma insha Allah kome ya kusan kammala

Team ɗin Maina Shkurah ina gaisheku tare da
Team Mashkura ina muku fatan alkhairi ana tare.


_Wata tace Kamata yayi nasaka Love and touching heart story karkuyi tunanin karanbanine a'a gyara aka min shi yasa na antayo muku.💋_
3/4/21, 9:48 AM - Ummi Tandama: *🙆QADDARAN RAYUWATA🙆*


*LOVE AND TOUCHING HEART STORY*


MAI DAMBU CE*






*Page 22*

"Na'im zan baka shawara a matsayina na abokinka, idan zaka iya kahakura da shkurah Allah ba matarka bace, ka dubi ƴanda ya bada rayuwarshi dan nata, kai koni akace nayi wannan kasadar Allah ba zanyi ba, dan akwai mata da yawa a duniya karewa ma ba ahaifi uwar watq ba shawara kayi hkr ka bar mishi ita." inji faruq kenan abokin na'im,

      Shiru na'im yayi, yana nazarin maganar Faruq, ɗago kai yayi cikin karfin hali yace.
"A'a ni bazan barmashi ita ba har sai naji daga bakin shkurah shin meye ya shiga tsakaninsu haka da taki aurenshi."

       Dariya faruq yayi, kafin yace.
"My guy karka wahalar da kanka, ka janye kawai shine gaskiya, amma tunda kace haka ina jiranka, malam majun."

      Sun daɗe suna tattaunawa, akan abinda ya faru.

        Shkurah kan dakyar aka cire mata bullet ɗin, dan ji jiki sosai sai kusan asuba ta farka tana rarra raba idanunta, a ɗakin da take Aisha ce ta matso kusa da ita tace.
"Sannun ya jikin ina ke miki, ciwo."

"Adda ina mashkur yake?"

      tana kokarin mikewa daga kwanciyar datake, shiru Aisha tayi kafin tace.
"Meƴe matsalarki dashi, tunda hankalinki ya kwanta sabida ke, ya rasa..."

         "Isa!!! haka barni da ciwon dake damuna, karki kara min wani akai..." tana gama faɗan haka tajuyar da kanta gefe ta fashe da kuka, mara sauti ita kaɗai tasan halin da take ciki,
    har gari ya waye, bata daina kuka ba, shigowan Na'im ta haɗiye kukanta kallonta yayi cikin nutsuwa yace.

"Preety kukan me kike? ko kinji wani abu yasame mashkur ne, da kike kuka."

       D'ago idanunta tayi takalle shi, sannan ta aro dariyar dole akan fuskarta tace.
"Haba ina, ruwana da wani can, kawai hannuna ne ya dameni da zafi yasa nake kuka, amma babu kukan da nayiwa wani kato."

    Kallon cikin idanunta yayi, abinda bakinta yake faɗa daban, wanda idanunta suke faɗa dabam, murmushin yake yayi kafin yace.
"Ai kuwa, naji labari mara daɗi akan ciwon da yaji,dan likitoti sunce yasame matsala akanshi brain ɗinshi ya taɓu bazai wani jima zai mutu, kuma hankalina zai kwanta dan bani da wanda zai damar min mata a tunani."

A tsorace ta ɗago kanta, bakinta na rawa kansan wanda akace kuwa, mashkur ko maina, waye ya same matsala a brain ɗinshi."

        "Ooo maina nake nufi ba mashkur ba, kinsan sunan sune kusan iri ɗayane amma ya naga kin damu daga maganar mashkur, ko kina sonshine na janye."

        Tsareta yayi da idanun, ɓata rai tayi cike da borin kunya tace.
"Ban gane ba, mana zargina ne idan da ina sonshi da tuntuni ina gidanshi, bana son haka karka manta ɗan uwanane, da kake wannan maganar."

"Kenan kina sonshi? kike kokarin ɓoye emotion ɗinki akanshi Shkurah ki fada min me ya rabaki da shi, yanzun kuma NA hango sonshi a cikin idanunki ni mutum ne meson adalci idan kika min wallahi ashirye nake namiki, common fada min"

       D'ago kanta tayi duk kokarinta da taboye hawayenta amma ta gaza hanasu saukowa, a hankali tashiga bashi labarinsu.

         Har izuwa yanzun, jinjina kai yayi kafin yace.
"Hmm, Allah yasa mu dace zan tafi, kinsan gobe za'a ɗaura auren anso ɗagawa nace ayi haka muje ki karasa jinyarki agidana, da fatan banyi garaje ba."


     Girgiza masa kai tayi alamun a'a, yana fita ta fashe da kuka, tarasa meke damunta sai zuciyarta babu daɗi.

*........*
Ta bangaren Mashkur da jikinshi da sauki sosai dan har ya tashi kuma, umma ce a wajenshi ya ɗan sake kaɗan sunyi hira jefe jeje,

  Can umma ta kalle shi, cikin nutsuwa tace.
"Ka faɗawa Kausar kuwa, baka da lafiya, naga matarka ma batazo ba ko tana can azare ne,"

dariya yayi yace.
"Umma kina son mommah ta birkice kenan kawai a barta idan nasamd sauki, zan faɗa mata."

         "Toh shi kenan, Allah yabaka lafiya."

*.......*
Washi gari.......
A can gida shirin ɗaurin aure ake, amma asibiti ba haka abun yake ba dan daga shkurah har mashkur, babu wanda ya runtsa kowa da nashi fargaban.

        Abubakarne yazo ya canza umma, dan ta koma gida, yana zaune sai surutu yake, mashkur ya sunkuyar da kanshi baya uhh baya hmm,  karfe sha ɗaya dai rabi aka ɗaura auren, kiran Abubakar umma tayi ta faɗa mashi, ajiyar zuciya yasauke tare da cewa.
"Ubangiji ya basu zaman lafiya, da zuri'a ɗayyiba,Allah yasa karshen wahalarsu kenan"

      addu'a sosai yayi sannan ya katse kiran ya kalle mashkur, wanda ake wayar agabanshi, tsare abubakar yayi da idanun alamun tamvaya, dariya abubakar yayi, yace.
"An ɗaura aurensu shkurah ne"

          lumshe idanunshi yayi, kafin yace.
"Allah ya bada zaman lafiya," daga haka be sake magana ba, sai ma rufe idanunshi da yayi, dan zuciyarshi ta mashi nauyi, tankar a ɗaura masa dutsen warinji.


  *........*

Hankalin mommah a kashe har gida biu,ga jama'a da suka cika gidan, ga kuma rashin ganin mashkur, ɗaurewa take amma ta gama sarewa da zuwanshi..

      Mika mata waya, Zuhra tayi tace.
"Gashi Umman bauchi take kiranki,"

          Karɓa tayi cike da damuwa, tace.
"Habiba, ya naku jama'a da fatan an ɗaura cikin kwanciyar hankali,"

"Alhamadulillah, da fatan kuma haka, daman nakirakine na faɗa miki an ɗaura auren autarki da yarona, don Allag karki hanasu cikar muradin yaronane don Allah ki samusu albarka,"

dariya mommah tayi kafin tace.
"Allah yayi musu albarka amna idan yan kawo amarya sunzo ki haɗasu, akawo min ita bari na sanar da cikin gida."

     kashe wayar tayi, ta aika cikin gidan wato fada, nan akaje aka faɗawa sarki hussain yayi murna sosai, sannan ya tura cikin gida aka faɗa,

      Lokacin da zubaida taji maganar auren mashkur haukane batayi ba dan gigicewa tayi tana kuka da ihu.

*.......*
  A bauchi kuwa abinda, ya faru shine. Bayan na'im ya bar asibiti yaje yasame faruq ya faɗa masa yanda sukayi da Shkurah kwarin gwiwa faruq ya bashi da ya hakura da ita,

       Shine da akazo ɗaurin aure kawunshi da kanin babanshi, suka nimawa mashkur auren shkurah a madadin Na'im abin ya bawa kowa mamaki,  ansa aure da kai an ɗaura da wani mutane da yawa sun saka mashi albarka, da yashiga gurin umma kuwa gaza ɓoye kukanta tayi sai da hawayenta ya zuba, tayi masa godiya sosai.

Asibiti ya tawo, shi da faruq suka shiga gaisawa sukayi, sannan ya zauna a bakin gadon yana kallon mashkur, gani yayi ya ɓata rai yayi ciki-ciki da fuska, dariyar da na'im yake dannewa ne yafito,

        dafa kafaɗar mashkur yayi, yace.
"Kalmar ina sonki ko nace (I love you) word ne masu sauki faɗawa, amma ayukarsu ba kowa yake iyawa ba, sai zaɓaɓe, naga finafinai na karanta novel da hikayoyi akan So, amma banga wanda yayiwa so Bauta kaman kai, ka sadaukar da rayƴuwarka dan Soyayyarka, ko laila majnun, da romeo da julient kashe kansu sukayi, akan so kai kuma, soyayyar kabawa rayuwarka bazan ɓoye maka ba, ko a wasa bazanyi abinda kayi balle a zahirance, kai masoyine na haka kika, dan haka nabar maka lailarka majnun, dan dakai tadace ba dani ba, sai kasake fiskarka dan tunda nashigo kake, hararata, sai kayi hakuri da rayuwa nadai bar maka matarka, indan mutum baeyi dagaske ba, tabbas zaka iya kai mashi nauhi...."

        Dariya suka saka, dukkansu, ɗago kai mashkur yayi, ya ma rasa tacewa  sunkuyar da kanshi yayi.

💋💋💋💋 Nima narasa abin cewa dan wannan irin Sadaukarwa haka.....
3/4/21, 9:48 AM - Ummi Tandama: *🙆QADDARAN RAYUWATA🙆*

  '''LOVE AND TOUCHING HEART'''



MAI DAMBU CE

*Page 23*


A can azare kuwa, banda tashin hankali babu abinda Zubaida take, a ranar Abba ya korota,  tabiyo an kawo amarya taci, alwashin sai taga bayan amaryan da mashkur ya aura.
Da wannan tunanin take har suka iso bauchi abin dariya bata san nan gidan amaryarta ba ita ubaidatu tasani amma bata faɗa mata ba, a daren akaita gida a bakin yaranshi tasamu labarin abinda yasame, shi a ruɗe ta nufi asibiti.

*.......*
"Basan ta inda zanyi maka godiya ba, amma zan iya cewa ka ceto rayuwatane dan nasan idan narasata toh narasa farin cikina kenan dan zan rayune amma ruhina da zuciyana suna mace, itace masarafar rayuwata, Idan baxaka damu ba, nabaka kanwata zuhra, saura shekara ɗaya ta gama jami'a amma bazan maka dole ba, idan bata maka ba zaka iya faɗa min nagode." yace masa,

      "Wai waneni, ince bata min ba wallahi farkon ganina dakai ban zata kana jin hausa ba, sai da na lura har da zane kake dashi, a fuska da kuma yanda kake hausa yasa na yarda bahaushene kai, Ai a tunanina baindiye ne ko balarabe, Allah ina sonta koda bata kai kyau ba, balle nasan zata fika kyau."

      Zaro idanun Abubakar yayi, cikin mamaki irin na wasa, sannan ya ɓata fuskarshi yace.
"An fasa, dan nine yake sonta kawai ka sadaukar min da ita shi yafi, dan naga yanda kakewa sirikinka babu ɗa'a nikuwa zanyi ɗa'a da biyayya idan aka naɗaka sarkin katagum a bani sarautar, sirikin sarkin katagum,"

      Fillon dake kusa da mashkur ya ɗauka ya wurga, musu yayi fuskarshi ɗauke da kasaitacciyar murmushi,
            wacce ta karawa fuskarsa kyau duk da kasumbar da yatara, nurse ce tashigo duba, shi taga yanda yake murmushi, take love bird ya sureta😹

         gyara murya tayi, tashiga ciki nan ta shiga dubashi tana satar kallonshi, har ta gama tafito sai cizon yatsa take ina ma itace tasame Gentle guy irin wannan.

          Mikewa na'im yayi ya mika, masa hanun yace.
"Toh bako zaiyi halinsa, inaha Allah nan da wata me zuwa zanzo mu dai daita da ita, inyaso sai ku manya kushiga cikin zance na barku lafiya a kula da amarya dan akwai ciwo a jikinta, sai mun sake zuwa walimar sunan Insha Allah."





       Dariya sukayi, cike da farin ciki da annashuwa suka rabu,
           Sun dan taba,hira da abubakar sannan suka fita zuwa d'akin da maina yake,duk ya cika dakin da wari da d'auyi sai da suka rufe hancinsu wai ma, akwai masu kula dashi, kare masa kallo mashkur yayi cikin tashin hankali da tsoro, ganin yanda take finciko naman gabansa yana ci kuka mashkur yake wiwi cikin tashin hankali, nan ya shiga gyara masa kwanciya,  cikin muryan kuka mashkur yace.
“Kaga abinda kowa yake, nuna maka illar zina ga abinda yasameka, yanzun da wani idanun zan kalle Abba nace masa ga halin da kake ciki fisabilillahi kasan halin da kajefa kankuwa Maina yanzun duba idan Yar da kahaifa tasan abinda ya kashe mata, mahaifinta shine  wannan me make son race ko kataba tunanin xaka bar bayan tabbas kayi kuskure Dan kabar baya da kura.


     Maina kacucemu, ka zalumunce mu, kayi man's gibe, amma xanyi maka alfarma guda d'aya na rikeni yarka tsakanina da Allah zan mata tarbiya me kyau yanda koda taji labarin abinda ka aikata, addu'a kawai xata maka, bazata tsaneka ba, da wannan nake CE maka, Allah ya nufa shkurah ta zama matata, Kai kuma da mask irin halinka, ubangiji ya shiryeku."

      Yana gama fad'ar haka yajuya, ya bar masa d'akin dan matukar yana ganinsa wallahi zuciya zata iya janshi da yawa Dan yau jin kishin shkurah take sosai abinda be iyaba ma, yau gashi bar tsanar maina yake ji sosai ba nawasa ba.



           *........*
Large bakwai da rabi Zubaida ta iso, Asibitin tana wani cika Rana batsewa, kallo d'aya yayi mata tuni tanemi kome ta rasa, Dan wani kwarjini yayi mata, ganinta yasa ya sallame abubakar ya taxi gida Dan shine a gurinsa,

           Abubakar nafita ta mike, tsaye tashigo surfa masa bala'i kanshi yana kan wayarshi, har ta gama sauka yayi daga gadon ya rike hanunta suka fita, sai ward din da maina yake nan ya kaita, toshe hancinta tayi tana shirin amai.


Murmushi yayi cikin nutsuwa, sannan yace.
"Kardai baki game wanda take kwance ba ?, naga kina to she hanci wari ko, ya zakiyi Indan NA fada miki mains ne, akwance nan shi yasa ake son mutum yayi,me kyau  ko rayuwar zata masa kyau kinga dai karshen alawa kasa, karshen tika tiki tak kenan toh yarinya kibi duniya a sannun, wanda yake cikima tana jiranshi balle wanda yazo."

      Yana gama faɗar haka yayi, waje abinsa, ransa na mashi zafi ainun ji yake dama basu haɗa kome da maina ba, dan ya cutar dasu matuka gaya.

   Bayan tafiyar mashkur itama fitowa tayi takira wayan Nana tw faɗa mata, halin da maina yake ciki.




        Komawa ɗakin mashkur tayi, kujeran dake ɗakin taja ta zauna,kuka tasaka masa dan dole ya, tashi ya ɗagota daga kujeran ta dawo kusa dashi. Nan yashiga rarrashinta, tare da magana masu daɗi,



       ganin haka yasa ta narke a ɓ
jikinshi, tana zubda k'walla tace.
"Yaya me yasa, kayi aure baka faɗa min ba, Sannan wacce yarinya ka aura,..."

    "Duk wannan tambayar, ni zan amasa mikisu, kwantar da hankalinki Idan ta tare zaki ganta da idanunki"

         tunda ya faɗa mata haka bai sake magana ba,


*.......*
Tunda na'im yabar, asibinti take nimanshi a waya amma shiru kake ji, abin yayi matukar ɗaga mata hankali bashi babu alamanshi, tuntana boyewa har tayiwa Mama magana, nan ta rufe idanunta tacimata kaniya, sannan ta faɗa mata, yanzun ba da bane, dan da auren wani akanta.

       Haka tawuni sukusuku, har dare, ga faɗuwar gaba, da mugun tsoron dake addabarta.


*.......*
Washe gari...
Aka sallame, mashkur dan nashi da sauki, suna komawa gida yana wanka, ya ɗauki Zubaida zuwa gidanshi da yagina, a can new g.r.a, gidan ya haɗu ba karya kuma abin mamaki, part ukune sai Bq,

      Kome na gidan ashirye yake, daman shkurah yake jira shi yasa yayi gidan amma ba'a tare ba kallon Zubaida yayi, sannan yace.
"Kizaɓe ɗaya, daga zaɓi ɗaya daga cikinsu,"


        Kare musu, kallo tayi sannan tashiga ruwan idanun,dakyar tazaɓe wanda daman shine nata,

       mika mata, keys ɗin gidan yayi sannan ta buɗe suka shiga tana tabin ko ina da kallo, har ɗakunan da kicin.


        Mashkur ya zuba, kome a cikin gidan tun kafin dawowarsu daga chicago, yasa Abubakar yayi masa kome dan haka kallonta yayi sannan yace.
"Wancar kayan akwai abinda kike bukata, a ciki dan zan kyautar da kayan gidan ne baki ɗaya,"

        "Eh, akwai zanje na duba, " ok zamu iya komawa idan kika kwashi kayanki sai mudawo."


*.......*
Alhamdulillah, jikin shkurah yayi, sauki haɗa mata kayanta umma tayi sai azare,

        tunda ta isa ake hidima da ita,

        Ga dilke da halawa, sau biyu arana kullum.
Wasa wasa, sai da suks shafe wata biyu, har da rabi ciki da wajenta aka haɗata sannan Mommah ta dawo da ita,

   

Please Login or Register in order to submit comment