Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuma  nan da y'an kwanaki kanwarshi Ubaedatu xata shigo cikin kazamin,   rayuwar maina, tsaki yasake yana me hura iskan dake bakinshi waje abin ya karawa fuskanshi kyau kuma one eleven  dake kwance akan fuskar tayi, masifar mashi kyau take yafito bagudiren asali,

       Tunda yashiga sallah ne yafitar dashi dake akwai masalaci a cikin quarts ɗin tunda yayi sallar isha be sake fita.
        ***
Washi gari kowa yashirya cikin unifoam farin riga da bak'in wando sai  farin himar da bak'in takalmin haka duk suka saka amma banda Shkurah wacce tasaka siket iyakarshi k'wanji da sai farin riga me dogon hanun wanda kana hango farin vest da brz ɗinta sai karamin himar ɗinta wanda ta manna bajin ɗinta duk suna motar da yake kaisu wato sai horn ake mata amma tak'i fitowa tana zaune ita sai lokaci take karyawa kaman zasuyi kuka dan saura minti ashirin arufe gater ɗin schl ɗin

       Fitowa Aisha tai tasame tana wasa da abinci ɗaukar abincin tai takai mota sannan ta dawo tace
"zaki fitane ko sai nayi waje dake marar kunya kawai fita ki bani, guri kafin na k'waɗa miki mari"
     fita tai suka gamu da Ya bilal ya kuwa ya zuba mata rank'washi sai a kan idanun Abba dake akwai abu abakinta garin ihu tak'ware shiɗewa tai zata faɗi yayi maza ya riketa yana ce mata "sannun kinji bansan da abu a bakinki ba," bata iya magana ba sai hawayen da yake zuba mata,

      "saketa bilal wallahi shkurah idan na kamaki zan karyaki kiwuce mota kafin nazo wajen kai Alhamdulillah da samunki nazo wajen nasameki, Allah yashirya min ke tafarki madaidaicciya." inji umma kenan,
         tafiya take kaman wacce k'wai ya fashe mata a ciki sai zubda kwalla take tana sharewa da hanunta,

          shkurah kenan ita dai akan makarantar boko toh sai dai akasheta dan ta ranta baya kaunar karatun boko ba wai bata ganewa bane ita tashin safe ke damunta, zata raba dare tana shigar da hadda da duba wasu buks ɗin bokonta bazata kwanta ba sai karfe sha biu da rabi take kwanciya da asuba kuma tariga kowa tashi shi yasa bata da ishashen lokaci,

          Koda tashiga mota bata kula kowa ba sai Abdullahi sabida shi Aisha tabawa abincinta ya rike mata dan sunfi shiri sosai

         kallonta yayi cikin tsoron karta rufe shi da masifa yace

"Adda shkurah ga breakfast ɗinki kar yayi sanyi kinji"

      yana maganar amma fuskarshi cike da tsoronta dan har muryarshi rawa yake kallonshi tai da jajayen idanunta ta amshi tace
"Nagode Abdul zanci"

          ajiyar zuciya yan cikin motan har da sa'ointa suka sauke karɓa tai taci kaɗai ta juya ta ajiye sauran a bayan mota
    Suna isa cikin makarantar ana rufe gater kowa kama gabanshi yayi inda shukrah da rafi'a suka wucce ss³a salmah ta wucce ss³b,

        ***
Sauri yake dan har yaso makara agurguje yafito daga ɗakinshi dan yau suna da exercise  na Jirgin  kuma shine shugaba a wannan shashin kuma 8 yadace afara aikin ko karyawa beyi ba yabar gidan yaransa naganinsa duk suka k'ame suka sara masa da "good morning sir"

      ɗaga musu hanun yayi sannan ya shiga motar sai ofis,

                yana isa aka fara exercise ɗin basu suka bari ba sai wajen sha biyun rana yana sauka daga jirgi aka shaida masa ga Maina yazo yana jiranshi a ofis yana shiga ya mika masa hanun suka gaisa daga nan suka tsinke da hira kaman wasu kanari,

           sai one pm maina yabar ofis ɗin ya koma nashi ofis ɗin yana tsaka da aiki kira yashigo masa tun daga sauti ya soma murmushi yana kaɗa kai sai da kiran ya kusan tsinkewa ya ɗauka ya kara a kunne da cewa, "Assalamun Alaikumun momma na imiss you dole next week nashigo azare ma "

         dariya akai a ɗaya gefen sannan tace
"toh son Allah ya nuna mana, kuma kazo da shirin ganin dota in-law zubaida dan Abbanku ya faɗa min nan da sati biyu za'ayi bikinku amma son nasan, zubaida ba zaɓinka bane hakuri zan baka, kayi biyayya Allah zai baka wacce kakeso kaji,"

     murmushi yayi sannan yace
"momma karki damu insha Allah zanyi biyayya, anjima zan kiraki ina son nashiga da wasu document ne"

   Kashe wayar yayi sannan yacigaba da aikin gabanshi yana hararo auren Ubaida da Maina sam haɗin be masa ba ina laifin a haɗata da Baffa sai wannan tantirin,

            kauda tunanin maina yayi sannan ya shiga tunanin tasa matsalar shi, a fili yace
"ko sai yaushe nima zan same sarauniyarta" murmushi ya sake ciki da jin daɗi, ranshi yake ayana abubuwa da zayi idan yasame wacce ya faɗa sonta, toh tabbas zaiyiwa so bauta kuma zai rayasonta fiye dakanshi,

         lokacin salla nayi yafita ƴaje yayi sannan yafita break be dawo basai uku saura nan ya koma bakin aikinshi harsai wajen biyar ya gama la'asar yayi dan yau ya makara beyita akan lokaci ba yana idarwa ya nufi wajen motarshi sai gida

            ***
Karfe biyar da rabi suka fito daga schl dukkansu a gajiye daq'ar suke ɗaga kafa nan aka buɗe shafin hiran karatun da wasu na tambayar wasu me suka fahimta daga cikin waɗan da ake tambaya har da shkurah a ciki, duk da ta gaji amma amsa take basu dai dai yanda aka musu har da karin haske bayan sun gama ne aka shiga hiran jami'a dariya tai sannan tace
"tab wallahi ina son rayuwar bodin amma haka Umma ta hanani, kuma da alamun koda nagama ba zanyi  bodin ba sai day, haba ace mutum ya gama day ya cigaba aday da sake wallahi saura wata huɗu zuwa uku, fa zamu gama Insha Allah.

             Dariya Maryam Umar Jama'are tayi cike da zolaya sannan tace
" Kin haɗu mukuwa bodin zamu ke kam  sai dai zaman gida fa Allah sarki zamu ji daɗi kuma za'a kiramu da big girls, ko bebes" ta kalle ɗaya abokiyar tafiyarsu tana dariya,

      "Eh mana Muj mun girma ana ganin mu ansan ba yara bane mu sai dae akiramu da manya yara su oo sai dai gida karki damu idan muka waye zamu zo mu wayar dake fa dan babu mugunta" inji bebes,

        duk yan wajen maza da mata suka fashe da dariya abinda ya kular da shkurah kenan ta kaiwa bebes duka kauce ita kuma ta faɗa titi lokacin kuma mashkur yana sharan gudu ya kusan isa gida saura kiris badan ya taka burki ba ai kuwa runtse idanunta tai ta ɗaura hanunta akai ta ɗan d'uka kasa saura ɗaliban ihu suka saka tsoro da fargaba ne ya kama dukkanninsu ba yaran ba har shi kansa mashkur ɗin ai kuwa yaranshi suka sauko daga mota zasu rufeta da duka da bulalarsu wani mahaukacin horn yayi dan dole suka fasa fitowa yayi, daga motar ya karasa wajenta har wannan lokacin idanunta a rufe bata buɗe ba dan bata san,me zata gani ba ratsasu yayi ya harɗe hanunwanshi a kirji yana kallonta daga sama har ƙasa abinda yafi jan hankalinshi tulin gashinkanta wanda ya ɗaga daga baya zaka rantse acuci mazane gyaran murya yayi cikin sanyi rai, yace
"buɗe idanunki babu abinda ya faru dake kinji amma nan gaba don Allah kudaina wasan banza yanzun badon Allah ya takaita min ba wallahi bansan me zan cewa iyayenki, ba wucce kije suna jiranki"
A hankali ta buɗe idanunta ɗago kanta sai a fuskanshi kallonshi ta tsaya yi cike da tsoro raɓa gefenshi tai ta wucce bata iya magana ba sabida tsoranshi,

           Juyawa yayi yana kallon yanda take tafiya tsintar kanshi yayi da binta da kallo,
       itama tana tafiya amma  zuciyarta na uzura mata da ta juyo dan haka batai wani tunani ba ta juyo aikuwa suka haɗa ido tsorone yasake rufeta, tana ganin napep ta tsara musu suka shiga jikinta har rawa yake,

   yana ganin tafiyarsu ya sauke ajiyar zuciya shaf ya manta a tsakiyar hanya yake mutane sai raɓa gefenshi suke suna jin haushin yanda ya tsare musu hanya shiga mota yayi yabar titin tuki yake amma zuciyarshi yana shirin hanashi sakat fuskar shukrah ne yake masa yawo a cikin idanun dakyar ya isa gida kayanshi ma yaransa ne suka k'waso masa a gajiye yashige.

      

Inayinku💋
3/4/21, 9:44 AM - Ummi Tandama: *QADDARAN RAYUWATA*
_SHUKRAH_




    Huwallahu lazi Al'illa ha illahuwa
   AR-RAHAMAN AR-RAHIM AL-MALIK AL-QUDDUS👏👏👏

_Tsokaci akan wannan buk ɗin tun farko ya dace na faɗa amma ban faɗa ba labarin zai nuna mana karfin Addu'ar Iyaye akan Y'ay'ansu da kuma Addu'ar wannan aka zalumunta,Sai Addu'ar matafiyi, Wanda yazo a cikin hadisan manzon Allah (S.A.W) yace  Ubangiji yayi Alkawarin amsar Addu'ar mutane uku" cikin ɗauki sahabansa suka ce "Ya Annabin Allah suwaye mutanen ukun" yana kishingiɗe sai yatashi ya zauna yace " Addu'ar Iyaye, Addu'ar wanda aka zalunta sai Addu'ar matafiyi" yace kusani Allah baya taɓa juyawa Addu'arsu baya idan sukayi kafin rana tafaɗi yake amsarta idan kuma cikin dare ne kafin gari ya waye yake amsarta"_

        '''Allah ka kara masa son Annabi''' Amin Yarabb




_Fans ɗin wattpad kuna bani kala fa dan haka wannan shafin na kune ga voting jina nake kaman nafi kowa sa'a Ina godiya da fatan Alkhairi_💕💘

*page 4*

Koda me napep ya iso unguwarsu kafin wat ya sauka tarigasu sauka dake kuɗin ba'a hanunta yake ba yana hanun Rafi'a kusan a guje tashiga gidan  ko gabanta bata gani sabida tsabage tsoro da Mama suka haɗu ganin yanda ta barkice yasa mama tariko tace

"Ya naganki haka meke faru ? ina sauran abokan tafiyarkin suke,?"
     

ta jefa mata tambaya tana karantar cikin idanunta tabbas ak'wai abinda ya firgitata dan tasan shkurah ba kome ke bata tsoro ba amma, yau taga tsoro zalla a idanunta daga bakin gater ɗin gidan Salmah ta amsa da cewa,
"Ai mama yau ba dan Allah ya takaita ba da munzo muku da labarin," shiru tayi tana kallon yanda yan gidan kowa ya zuba mata idanun.

Umma ce tafito hanunta rike da casbi ta zubawa shkurah ido sannan tace,
"me yafaru ? a hanyar makarantar ba mamaki garin wasan banza ko ?"

       Rafi'a da tagama cire takalminta zata shiga part ɗinsu taɓe baki tai, sannan tace
"Idan suka haɗu su uku yanda kuka sannan dabobbi, haka suke wasan banza saura kaɗan da mota ta bita kanta, kuwa da kowa ya huta da haukarta da jin kai."

    Wannan maganar da rafi'a tayi ba karamin zafi yayiwa Umma ba amma dake tasan me take sai tayi murmushi kawai fuskarta cike da fara, aikuwa shkurah ta gaza hakuri da maganar ta nufeta dagan-dagan ta fisgota ta hankaɗa da jikin kofar part ɗinsu, tace
"Uwar me na tsare miki da kike min fatan mutuwa me bak'in zuciya wallahi idan baki fita idanun, ba zan miki shegen duka, wawiya kawai ina ruwana da rayuwarki."

     "Toh wucce muje ko bana son rashin hakuri kul kar nasake ganin haka, dan zan saɓa miki kina jina ko,"

               Ba musu ta ɗauki skull bag ɗinta tashige abinta amma ranta na zafi tana mamakin wannan al'amarin,

        Suna shiga palorn ta zube a kafet tana mai da numfashi lumshe idanunta tayi amma exactly fuskanshi take gani a cikin k'wayar idanunta buɗe ido da tayi da sauri tana zarresu, Aisha da tafito daga ɗinkisu ta kalleta, sai tayi tsaki ta wucce dan tasan wani, shirmenta ne ya zaunar  da ita a wajen,

        Tashi tayi tashiga ɗakin ta cire kayanta ta ninke sannan ta faɗa wanka ta jima sosai, aban ɗakin sannan tafito, kaya marasa nauyi tasaka sannan, ta gabatar da sallar magarib, buks ɗinta ta ɗauko ta fara dubawa.

          ***
Shima mashkur kusan shkurah yake gani abinda tayine ya bashi dariya sosai har hak'oranshi suka bayana, cikin nutsuwa ya shirya sannan yafita masjid,

      bai dawo gida basai bayan isha, abinda zai ci ya nima, yana gamawa yafita palo da laptop ɗinshi da wayarshi, momma ya kira zama yayi ya rufe idanunshi  bayan ya zuba kafafunshi a saman center table yana kaɗasu wani nishaɗi yake ji haɗi da nutsuwa bai san me ya janyo haka amma yana cikin nutsuwa , kiran ta yanke, ba a ɗauka ba ajiye wayar yayi yacigaba da aikinshi,

                 ***
Maina kenan duniya tazama sabuwa manne yake da wata yarinyar, kallo ɗaya zaka mata ka gane daga inda tafito,  sabida yanda gashin doki ya cika mata ga wani nail da tasaka a farcenta tana da kyau ba laifi, kallon shi tayi sannan tace
"Maina katagum me yasa baka sex dani skin to skin  wallahi bani da matsala, tun ɗazun nazo amma kak'inyi kome dani, sai shan win i swear bani da wata cuta, kuma kaine mutum na farko dana fara sani why not kacire shakku akaina."

       Wani shegen murmushin gefen baki yayi mata sannan ya ajiye kofin glass ɗin dake hanunshi ya juya ya kalleta kirjinta ya kalla yaji kome nashi ya ɗauki chaji yanda ya dace,

    dake a falo suke, kuma a kujera ɗaya suke me ɗaukar mutum biyu, janyota yayi a hankali yashiga sarrafata son ranshi, hmm shaiɗani dole mata su bishi dan ya iya sarrafa mace bana wasa ba,

            Duk iskanci Maina baya taɓa yarda yajewa mace babu condom ba yana tsoron ɗaukar ciwo, (Ashe iskancin karyane😂)

           Sai da ya kuna mata service sannan ya ɗauketa zuwa ɗakinshi anan yasaka condom ɗinshi amma ranta ya ɓaci da haka, kuma babu halin magana dan tasan halinshi sarai yanzun sai ya maketa, (Allah kashirya mana zuri'a al'umman muslumi baki ɗaya Allahumma Amin)

             ***
Washi gari  yau ba matsala dan harta manta Mashkur, kuma ba a same matsala, da ita ba tawajen shiryawa ba kusan ta rigasu, fitowa ba dan kome tai haka ba sai dan nasihar da Umma tayi mata kuma anyi dace, ta ɗauka sosai ya shiga jikinta,

           Suna gama shiryawa duk suka fito wajen mota suka tafi ke Rafi'a da niman faɗa tana zuwa ta bangajeta saura kaɗai ta faɗi,
      abin ya bawa kowa mamaki har shkurah juyawa tai ta kalli Umma murmushi tayi mata, alamun tai hakuri, shiga motar tai zuciyarta na mata zafi sosai,

     Sai da aka iso makarantar ai kuwa tana gaban shkurah abinda tai mata shi itama ta mata na hankaɗata sai da tafaɗi tana fitowa tai fuska sannan ta tsuguna gabanta, tace
"Ba gaba da gaba ko tabaya sai anshirya karki manta akwai watanin tsakaninmu, kuma har shida dan haka a kiyayye gaba dan idan haka yasake faruwa hmm, zan baki mamaki dan kinfi kowa sanin halina."

          Mikewa tayi zuciyarta yana tafasa sosai babu yanda ta iya da Shkurah amma da ta ɗauki mataki akanta.

     

           ***
Bayan sati guda yaso zuwa azare amma Allah be nufa ba, sabida tulin aikim da yake gabanshi dake yau da wuri ya dawo yana barandar gidan nasama yana wayane da momma sosai yake bata labarin wani karamin nasaran da yasamu kanshi a sunkuye, kaman ance ɗago kai sai akan fuskanta, ya zata a zuciyarshi ya faɗi haka yace
"I found my half"

      "Son me kace? you found your half wacece haka? son talk to me, " inji momma,

         gyara murya yayi ya shiga kame kame "a'a ni da maina nake kuma ai shi ɗin half ɗina ne, haba momma ba halin nai magana shikenan sai a min, fassara."

     Yanda yayi maganar cikin sigar shagwaɓa yasa tai murmushi irintasu ta manya tace
" Son just open your heart you  with feel happiness (Son ka buɗe zuciyarka, zakayi farin ciki),who are she (wacece ita) ?"
         "ayya momma na faɗa miki babu kowa fa da Maina nake fa" kaman yaron ɗan goye haka yake mata magana, jinshi take amma tafishi farin ciki, tace
"Ok tunda baka son nasanta, bawa maina mu gaisa."

        Katse kiran yayi yana lekasu Shkurah da suka wucce san yanxun ya rike bakinshi yana tuna irin katoɓaran da yayi, "Taɓ "  yace yana nazarin ya akayi ya iya rufta haka bayan shi be sani ba ɗaga kafaɗa yayi alamun ko a jikina
              ***
Duk da auren amsa shirin ko takwana amma, babu wanda yaji daɗin saka auren a kurarren lokaci, abinda basu sani ba shine dama can sarki ya gama shirinsa tsab kawai lokaci yake jira kuma Allah ya nufa,

Musaman iyaye mata dan sunso asaka kaman wata guda kafin nan anshirya amare sosai amma haka bai samu ba saɓida akurarran lokaci aka saka bikin dan ma amaren suna makaranta a kano, idan akayi biki aka gama zasu koma skul daga Ubaidatu har Zubaidatu suna karatune a B.u.k Ubaida a fannin Englishi itakuma Zubaida a
fannin Acc
        Maina yasame zuwa ganin Ubaidatu wacce aka ɗauki hoton da za'a asaka a kalanda da memo,da sauransu. Dakyar Mashkur yasame zuwa inda aka basu hutun kwanaki dan shagalin aurensu, wani abin mamaki dukda baifi sati guda da haɗuwa da Shkurah ba, wani lokacin yana ofis take wucewa ko idan ya dawo, haka kawai yake jinshi wani empty sai yake jin kaman ya shekara be ganta ba, ga uwa uba kewarta sau biyu suka haɗu tun bayan haɗuwarsu na farko, ranar alhamis da yamma sun taso shikuma yafi gidan mike kafa, gashi kusan duk abokan tafiyarta sun tafi, sunkki tsayawa suyi sallah sabida suna da hadda itakuma bazata ba sabida tana cikin yanayin lalura, shine tafito ita ɗaya abinka da unguwar manya kowa na gida ita ɗaya take sharan tafi gashi ko mashin babu balle, napep tana cikin tafiyane wasu matasa irin masu zuwa gidan y'an siyasa rok'o suka shiga binta suna mata magana bata kulasu ba, tacigaba da tafiya sai binta suke gashi wajen yayi shiru tana tsaka da addu'a sai ga mashkur yana tafiya hanunshi ɗaya na cikin aljuhun wandonshi  ɗaya rike da waya, ganin yanda suke mata rashin hankaline ya bashi haushi tsayawa yayi, yana jiran isowarsu, ai kuwa suna zuwa ya buga musu harara take suka kama gabansu dan yana da wani sirrin a tare da shi musaman magic eyes ɗinshi, wanda yake rikita mutane,

           Wucce shi tayi ya rufa mata baya har suka fita babban titi shi da kanshi ya tsara mata napep sannan ya zaro 1k yabawa me napep ɗin, a sanyaye yace
"kakaita gida karkayi gudu sosai fa, dan" kallon idanunta yayi sannan yacigaba da cewa"
naga kaman bata da lafiyane, kuma karka ɗauki wasu, dan kuɗinta na biya ita ɗaya"

        Ita dai burinta subar wajen ko hankalinta zai kwanta,  matsawa yayi daga jikin napep ɗin, suka tafi,

          toh basu sake haɗuwa ba sai a Arbian makert sunje siyayya da Aisha shima yaje sayan kayan abinci ya shiga gurin abin mamaki yaje zai ɗauki wani turaren uhdu wa kanwarshi zuhrah itama takai hanunta dukkansun basu lura ba sai suka ɗauki k'walin shi yarike gefe itama a masifance ta juya zata masa rashin mutunci karaf idanun,sun ya haɗe ja da baya tayi cikin tsoro, mika mata yayi tak'i karɓa Aisha ce ta iso wajen fuskanta ɗauke da mamakin ganin ƴanda ya tsareta da idanun sannan ya mika mata, amma dake kanta a sunkuye yake bata amsa ba, so take ta raɓa gefensh, gyara murya tai sannan tace
"Ayya kayi hakuri ai itama shine best turarenta, shi yasa aka same akasi kuka ɗauka tare, ba damuwa zata ɗauki wani, muje Shkurah"

         gyara tsayiwanshi yayi sannan yace
"Karku damu nima wa kanwata na ɗaukawa, amma tunda Shkurah tana so takarɓa zan nima mata wani,"

        Aisha taso kin karɓa amma jin yace
"ta ɗauke shi amatsayin yaya, shi yasa ta amsa tare da godiya, yaji daɗi duk da ba itace tai godiyar ba amma yaji abin har cikin ranshi."

         Abin dariya tare sukaita wayon tsince tsince kaya wasu abin wasu Zuhra yake ta ɗibawa, haka har suka gama, sunje biyan kuɗi yace a haɗa da nashi zarro idanun sukayi cike da mamaki hanunshi ya ɗaura akan bakinshi, alamun suyi mashi shiru,

      har wajen motarsu yasa aka kaimusu kayan sai godiya Aisha take amma shi duk hankalinshi yana kanta taki yarda su haɗa ido, dan wani nauyinshi take ji ga wani faɗuwar gaba da take ji,

         Yana wajen har motarsu tabar haraban wajen,

        Tun daga ranar basu sake haɗuwa ba,

           Zaune yake a ɗakin momma, yayi zurki cikin tunani ƴa marasa meke damunshi, kuma ba wani abu bane illa tunaninta shi bai san meke damunshi akanta ba amma idan da za'a ce ya zauna kusa da juna zaiyi fari ciki sosai, taɓa shi momma tayi hanunta rike da abinci zama tayi kusa da shi tana karantar fuskanshi, ɗiban abincin tai da spoon ta kai mashi baki, ba musu ya amsa amma baya jin daɗin abinci sake bashi tayi, ya amsa, sannan ta fara magana tace

" Son, kana try ɓoye wani a ranka, wanda nina rasa gane maka Son idan baka faɗa min ba wa zaka faɗawa, nifa mahaifiyarka ce kuma abokiyar shawaranka me ye matsalarka Son."

      Gyara zama yayi sannan yace
"Momma ban san meke damuna ba, ni dai kawai ina cikin damuwa, idan naganta sai naji ina tsoron mata magana, wallahi momma ban taɓa jin kome akan zubaida ba amma ita idan naganta ina samun nutsuwa sosai, nakan tsinci kaina cikin farin ciki fiye da tunanina momma ban taɓa jin kewar wani abu arayuwata kaman ita, ina matukar kewarta bazan iya ce miki ga yanda nake ji ba momma yau da nayi nisa da ita jinake kaman nayi shekara dubu, momma kawo hanunki kiji yanda heart ɗina yake buguwa, toh momma me haka yake nufi"

           Hawayene ya cika idanun ga koshi ga kwanan yunwa murmushi tayi wanda yasa hawayen ya zubo mata ta rasa kukan me take farin cikine ko bakin cikine,

          hanunta na kirjinshi, tana jin ynd zuciyarshi yake bugawa, idanunshi a rufe tausayin shine na ɗa da uwa ya kamata,



          Hmm Ayya


#Comments
#Share
&
#Voting
3/4/21, 9:44 AM - Ummi Tandama: *QADDARAN RAYUWATA*
_SHUKRAH_

Mai_Dambu

       Al-Salam Al-Muhmin Al-Muhaymin Al-Azeez 👏👏👏


       *Fatan Alkhair gareku Aunty Kyauta,Jelatyna,Aunty Dada Naseer,Aunty Fatima,Momina Zainaba Misau, ina jin daɗin kasancewa daku da fatan kuma haka*💕💞💋


_Bestie kina hanani magana dake nake alfahari bani mantawa dake kuma nayi hakuri_😍


 

       



*Page 5*



Cire hanunta tayi daga kirjinshi, sai lokacin ya buɗe idanu ya zuba akan, fuskanta yana kallon hawayen da yake zuba daga idanunta, gyara zaman yayi yace,
"Momma," shiru yayi be sake magana ba, kuma be fasa kallonta ba, damuwa ce ta bayyana karara a fuskanta share kwallarta tayi sannan tace,
"Son you too later,(Son kama kara) ni ina goyon bayanka amma, kasan halin da kake ciki kuwa ?, kasan meye yake damunka kuwa, ?"  tsare shi tayi da manyan idanunta, masu cike da kwarjini irin na jinin sarauta,
       gwauron numfashi ta sauke sannan tace,
" Son dagsk duk abin, ka faɗan kana jinsu akanta *?*"

  zuba mata ido yayi cikin nutsuwa, sannan ya langwaɓar da kanshi kaman ɗan karamin, yaro da yake son amashi wani abu,

             tsintar kanta tayi da farin ciki, mara misaltuwa tace,
"You are deep in love,(ka faɗa soyayyane) son yanzun har ka faɗa so, bakasani ba amma wata sarauniya ce haka da tayi nasaran sace, min zuciyar yaro, ok ko itace wacce ka taɓa ce min, you found your half, hmm ba half ɗinka bace kasamu, zuciyarkace tayi lucking sacewa,"

  matsanancin kunya ce takama shi har sai da yarufe idanunshi, yana sake murmushi a hankali, zuciyarshi tayi masa daɗi.

           Buɗe idanun yayi, sangarce yace,
"Momma toh, taya zan faɗa

Please Login or Register in order to submit comment