Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata bayan itama yarinyar bata wucce 17yrs ba, yanzun fa take shirin gama skull, ina tsoron kar nashiga hakkin  karatunta kuma, ina son nafaɗa mata kafin lokaci ya kure min,"
             shiru sukayi, dukkansu cike da damuwa can momma tace,
"Ina ganin kanuna mata, alamun kana sonta ai basai na faɗa maka  yanda zakayi ba, kafini sanin yanda zata faɗa sonka, dan haka kyaleni naje naji da bak'ina suna bukata sannan, ya kamata kashirya kashiga faɗa, dan kasan kaima ɗaya a cikin Emirate  councillors, dan Abbanku ya kawo min k'aranka baka son shiga fada, bansan me ye reason d'inka ba, but nabashi hakuri kuma, nace idan kazo zaka shigo har cikin gida wajensu Hajiya kilishi, zan fita amma ak'wai kaya a cikin wanca ak'watin, ka bud'u kayane daga Maiduguri yaya Zanna da Abbalawan, suka aiko maka suma ranar juma'a zasu iso, Dan haka kad'auki ak'watin ka kai d'akinka,"

        Tana gaba fad'an haka tafita daga d'akin, matukar tatsaya a ɗakin toh wallahi ba zaije fada ba, wai dogawara suna takura masa, da kirari shi yasa ya tsani zuwa fada,

              Babu yanda ya iya haka dole ya ɗauka yafita, da kayan.


             ***
Tafiya suke kuma, sauri take dan yau tana son taisa gidan, suna dai-dai quarts ɗin ta dago kozata hangoshi, tunda taga baya nan bata damu ba, daman addu'a take Allah yasa baya nan, dan idan yana nan tana jin yanda yake binta da idanu har susame napep,

          A gajiye suka isa, gida kwanciya tayi a falo dan kusan six da y'an mintoti suka shigo, tana wajen har aka kira sallah, sannan tashige ɗaki tayi wanka takwanta dan na up, buks ɗinta ta baza akan gado, tana dubawa sallamar Aisha yasa ta ɗago kai, tana kallonta bayan ta amsa, mata. 

     Zama Aisha tayi kusa da ita tace,
"Shkurah, nikuwa kinsake haɗuwa da wannan gayen da yayi mana siyayya, arbia market."

      Gabantane ya faɗi a razane ta ɗago tana kallon, Aisha yatsina fuska tayi tacigaba da aikinta tace,
"Kin bani ajiyar shine da zaki, tambayeni nasake haɗuwa, da shi zan haɗaku da umma tarabani dake, dan ni ba y'ar iska bace da zanta kula kowa,"

        tana gama faɗan tayi shiru tacigaba da duba buks ɗinta,
     mamakine ya rufe aisha tana kallonta, bakinta buɗe da mamaki daga tambaya, sai masifa haushine ya gama rufeta kaman ta tsinka mata mari, shareta tayi itama.

***
A azare kuwa maina ne tare da yarinyarshi Ruth, wacce maina yasa tazo dan biyan bukatar kanshi, giya yasha sosai dan duk lokacin da zai kwanta da mace ɗabi'arshi ce k'wank'waɗar giya, sai da yaga sannan ya kai hanun zai riketa ta fizge daga gareshi tace,
"Na gaji, bazan iya maka ba Maina katagum saura kwanaki ayi aurenka,amma ni baka tuna gobena sai naka kawai baka ɗauke ni abakin kome ba, sai dan biyan bukatarka na gaji, idan kuma zaka aureni fyn."

          Wata uwar ashariya ya maomalo mata, ranshi a ɓace ya fisgota yashiga kiciniyar rabata da kayanta, kai mashi duka take dan ya kyaleta amma ina, karshe ihu tasaka, wanda yayi da shigowar Mashkur kenan gidan dan anan matansu zasu zauna, da sauri ya shiga ɓamgaren Maina,yana kusa kai falorn idanunshi yayi masa tozali da abinda maina zai aikata,

           da sauri ya karasa ya ture shi, lokacin har yayi nasaran rabata da kayanta juya mata baya mashkur yayi sannan yace,
"maza kibar gidan nan, kafin na miki rashin mutunci."

          Meqewa maina yayi, cikin zafin nama mashkur yasaka kafa ta taɗe shi, ya faɗi k'asa rsnshi a ɓace ya sake yunkurin mikewa, mashkur yasake, mai maita masa, zuciyarshin zafi yace,
"Mashkur, zan maka abinda zai baka mamaki, matukar baka kyaleni ba"

        sam mashkur be wani damu, ba idan da sabo yasaba ganin haukar duk lokacin da yakora mashi kayan marmarinsa,

      jan center table ɗin da yake falon yayi ya zauna, a nutse yana kallon Maina,
        kauda kai yayi jin motsin yarinyar tafito zata bar gidan, maida hankalinshi yayi kan maina da yake bim ruth da ido ranshi yana kuna,

       gyaran murya mashkur yayi, sannan yace,
"Sai yaushe zaka daina bin matan layi, ina matukar jin zafin yanda kafito babban gida,amna sam bakasan ciwon kanka ba rayuwarka babu abinda kasani sak niman mata, maina Wallahi kaji tsoron Allah, katuba kafin lokaci ya kure maka, kukan kurciya....."

        "Ina ruwanka, eyye toh tsoron zanji Allah maina kafita harkata kayi hidimarka nima nayi nawa, bana son sa'ido ai kaima idan kasame mace ba kyaleta zakayi, ba gwara ni nawa yafito fili, irinku wayasan me kake aikatawa, Allah idan baka daina takurani ba zanje na faɗawa Momma, kana shiga rayuwata."

         Dariya ce takwace masa sosai sannan yace,
"Maina katagum, sarkin gobe ni kuma nayi maka alkawarin idan kaje, ka iya samun momma da wannan maganar, ita kuma ta tambayeni me yasa, nake shiga rayuwarka sai na faɗa mata gaskiya abinda kake na niman mata, muga kozata kara kallonka da mutunci, sannan da ake cewa wayasani ko nima inayi,hmmm ai wallahi idan nace zanyi matan da kansi zasu kawo min kansu, ni ina da mutunci kuma ina martaba mata, bazan iya cutar dasu, kuma bana son tarihin ya mai-maita kanshi akan yarana, Maina ina son kasani gyara kayanka baitaɓa zama sauke muraba ba, kacigaba maina."

     koda yabar gidan maina gidansu ya wucce ranshi yana jin ciwon abinda Maina yake aikatawa, koda yayi parking sai da yakifa kanshi a kan sitiyeri, can dai yafi daga motar yashiga cikin falon, shi da zai bita, kofar baya sai gashi ya biyo ta main falorn, ƴana shiga yasame Ubaida da sauran dangin momma, tunda yaƴi musu sallama yashiga ciki be ɗaga kai ya kalle kowa ba, ta kicin ya fita kofar baya dan yana shiga falon momma zai tarda mutane,



          


            Kwana yayi da damuwa aranshi har kusan asuba yasamu barci.


              Ranar asabar aka ɗaura auren Muh'd Hassan Muh'd(Mashkur) tare da Amaryar sa Zubaidatu Muh'd Hussain Muh'd.
          Sai  Muh'd Hussain Muh'd( Maina) tare da Amaryasa Ubaidatu Hassan Muh'd,

       biki yayi dan mashkur ba laife yayi wanka, sosai kowa ma haka, a wajen ɗaurin auren duk da fuskanshi a saketa amma kasan zuciyarshi cike take da marmarin Shkurah da muradinta. Baza gane haka dan fuskarshi bata nuna haka ba,


      Bayan ɗaurin auren ne aka tafi, Reception an goge wuya balaifi kan,

     A gida kuwa mata walima suka haɗa, bayan antashi aka kaisu wajen sarki hassan yayi musu nasiha akan zaman aure sosai ya tsoratar dasu,

          Bayan ya gama musune aka kai Zubaida cikin gida, ita kuma Ubaida gidansu daga can aka kaisu gidajensu bayan kowacce tasha faɗa, sosai.

           Bayan ankaisune suka sake shiryawa sai dinner, kome yayi kyau na wajen Ubaida, sanyeta da wani gown purple, Zubaida kuma,Peach colour sunyi kyau, sosai, Mashkur wani suite   yasaka me dark blue, Maina kuwa ashe colour,

        Anyi kome lafiya, a cikin kawayen  Zubaida  sai da maina ya jone da wata yarinya me suna Ma'amurah, ta haɗu iya haɗuwa,
    bayan antashi ne kowani ango ya ɗauki matarshi, ka idar kenan.

Wshi gari..
Akayi buɗan kai, inda Mashkur yafitar da Zubaida kunya haka ma maina ba laifi sunyi abinda ya dace,


             Haka kowa ya watse aka amare a gidajensu suna kuka,(😹)

           Bayan abokai sun rako angwaye dan kowa da abokanshi, idan kuka ga abokan Mashkur sun dace, da shi dan kamilalun mutane ne masu mutunci da daraja,

     tawajen maina ma haka, balaifi, mutanenshi suna da mutunci sai dai dake mutumin banzane dole aka samu yan bariki irinshi.

      Akowani ɓangare kome ya tafi dai-dai yanda ya dace.


             Bayan dawowar mashkur, leka ɗakin Zubaida yayi ya ajiye mata,laidarta sannan yayi mata sai da safe, abin ya bata mamaki ace ranar farkonshi amma yana gudun amaryarshi.

A ɓangaren Maina kuwa ɗokin wannan ranar yake, dan haka yana dawowa yashiga banɗakinsa yayi wanka sannan yasaka wasu riga da wando, yabi Ubaida ɗakinta yana shiga ita kuma lokacin tafito ban ɗaki daga ita sai towel,

       Wajenta yanufa ya amshi ɗayar towel ɗin da take goge gashinta yashiga goge mata duk kunyarshi ya rufe,

          bayan ya gama ne ya ɗauko, mai lotion ya shafe mata a jiki, wani rigar barci ya ɗauko zai saka mata takwace tashige banɗaki, taje tasaka yayi mata kyau kuwa, kallon kanta tayi taga ina zata iya fita, da wannan kayan,


    ganin tana, ɓata masa lokacine ya shiga banɗakin,kare mata kallo yayi sannan yace,

"My wify zakiyi citta fa, muje kici abinci sai mukwanta ko,"

         Jikinta asanyaye haka tabiyo shin dan ya riko hanunta wanda, jin laushin da yayi yasa ya fara sukurkucewa nama ya juye masu a wani tire da ya gani a ɗakin shi ya ciyar, da ita sannan tasha madara, bayan sun gama wanke bakinta tayi,


          Duk maina yagama k'waɗaituwa da son kasancewa da Ubaida tana hayewa gado, yabita, ko k'wanciyar arziki batayi ba ya birkitota jikinsh, abinda suka fi ɗaukar hankalinshi, boons ɗinta su yashiga, murzawa yana tsotsesu kaman wani karamin yaro, baki ɗaya sun tafi da hankalinshi, itakuwa zafi da bakon yanayi yake ratsata, mika take tana wani irin nishi, ɗagowa yayi yaga yanda take mika cikin yanayin da yafeta, ciki.


         Lashe koina najikinta yake kaman wani wanda yasame Lollipop, koda ya isa fadar karshe yashiga mata wasu abubuwa🙈😷

             Sai da yagama kashe mata jiki sannan yashiga kokarin karasa sauran aikin da ya faru, mmmmmm.

     Ya isa haka rawoton kar mu wucce gona da iri

*Inayinku*💋
3/4/21, 9:44 AM - Ummi Tandama: 🙆*QADDARAN RAYUWATA*🙆
_SHUKRAH_
Mai_Dambu

Al-Jabbar Al-Mutakabeer Al-Khaliq Al-Baariu👏👏👏


*Page 6*

Sai da ya shafe about awa ɗaya yana, abu ɗaya yana, abin tausayi duk tafita hayacinta dakyar take ajiyar zuciya, kifa kanshi yayi akan fuskanta yana lashe ruwan hawayen da yake zuba daga idanunta, tabbas yau yasame nutsuwa fiye da tunaninshi,
so yake yajanye daga jikinta, amma yanayinta ya hanashi, sabida itace mace ta farko da yayi mu'amala da ita babu condom, janyewa yana ya koma gefenta ya kwanta yana maida numfashi, a gajiye rufe idanunshi yayi yana tuna irin matan da yayi lalata dasu, so yake ya haɗasu da ita ko, zai gane akwai bambanci,."Hmm Ubaidata tafisu nesa bakusa ba,"yace.



Matsawa yayi, gurinta ya rungumeta,sosai yake jin tausayinta ya shiga zuba mata albarka dan yaji kome daga gareta, kaman yanda yace zatayi citta me yaji kuwa dan musaman aka sakata aɗaki na tsawon sati biyu ana mata dilke, tashi yayi ya sauka a gadon banɗakin yaje ya haɗa musu ruwa, zuwa yayi ya ɗauketa cak, ya kaita banɗaki ya taimaka mata ta gasa kanta yanda ya dace, sannan sukayi wankan tsarki suka fito,

wani rigar barci ƴa ɗauko mata, tasa sai binta da ido yake, dan ta shayar da shi mamaki sosai,
k'wanciya sukayi yana manne da ita,

***
A ɓangaren maahkur kuwa, tunda ya ajiye mata laida yashige ɗakinshi, cire kayan jikinshi yaƴi, sannan ya shiga bandaki ya watsa ruwa, da alawala yafito, sallar shafa'i da wutiri, yayi sannan yayi addu'a ya shafa ya kwanta,



Washi gari....
Tunda Mashkur ya dawo sallar asuba, be kwanta ba ya shiga banɗaki yayi wanka, ya shirya cikin ɗanyen boyal me masifar tsada, skyblue, takalminshi fari yasaka sai hularshi itakuma skya blue ce yayi kyau turare ya fesa , kallon kanshi yayi a mirro sannan yasaka, agogonshi silver, yayi kyau ba laifi.

Yana fita falo ya nufi ɗakin Zubaida, knocking yayi ba'a buɗe ba dan haka ya kama handle ɗin kofar ya murɗa yashiga dai-dai tafito kenan daga wanka, goge gashin kanta takeyi dan haka hankalinta yana kan abinda take,

Hankalin shi yana kan wani abu ya dauka yana, dubawa kuma y juya mata baya dan haka be san yadda take ba, gyara murya tayi sannan tace,
"Ina kwana Ya mashkur,"
juyowa yayi yana amsawa, ganin yanda take, daga ita sai towel, yayi saurin kauda kanshi yace,
"Lafiya lau, ya kika tashi ya bakunta, zanfita zuwa gida daga nan zan isa Fada, dan nasan yau gidan nan baza'a rasa masu zuwa ba, kin gane ko,"

gyaɗa masa kai tayi, cikin nutsuwa, be sake kallonta ba yafita sai da ya isa bakin kofa yace "sister sai anjima"

mamakine ya rufeta, shi kuma wani irin mutum ne, haka girgiza kai tayi sannan tacigaba da gyara jikinta,

.....
Ubaidatu tariga Maina farkawa wajen karfe shida da rabi, dakyar ta mike tashiga ban ɗaki, ta sakw haɗa ruwan zafi, tashiga a gurguje sannan tafita a rawan ta ɗauro alola, tafito sallah ta gabarta sannan ta koma inda Maina yake ta tasheshi, a sanyaye tace,
"Yaya maina katashi, munrasa sallar asuba, ynz kuma shida da arbain ne kar rana tafito bakayi sallah, ba babu kyau."

Ta karshe maganar tana kallon fuskanshi, buɗe ido yayi a hankali ya zubasu akanta, murmushi yayi mata sannan ya mike ya fita daga ɗakin. ya koma ɗakinshi.

A can yayi sallarshi, sannan ya shiga banɗaki yayi wanka, shima ya shirya cikin farin shadda, ya fito ɗakinta ya kome yasamu ta gyara ko ina tsab har tayi wanka, murmushi ya sakar mata sannan yaje har inda take shafa mai yakarɓi robon man ya latsa a hanunshi ya shiga goga mata, cikin wani irin yanayi a nan suka lalace,


Koda mashkur ya isa gidan Momma, yasamu yan maiduguri, wasu zasu je gidan shi dan sun kunsan tafiya gaishesu yayi sannan ya wucce ɗakin, Momma inda suke zaune da wasu daga cikin kannenta da matan Yayunta,
Hira suke irin na zumunci, da sallama ya shiga durkusawa yayi ya gaishesu, cike da jin kunya,

Zuciyar momma fari tass, haka take jinta ba kome ya kawo haka ba, sai dan samun nagartaccen ɗa, kuma me ladabi da biyayya, girgiza kai tayi a ranta tace,
"Ya Allah ka albarkaci rayuwar Mashkur da na yan uwanshi baki ɗaya,"

Zuba mata ido yayi cikin nutsuwa da shagwaɓa dan mashkur indai a gaban Momma ne kullum komawa yaro karame yake yace,
"Momma yunwa."
Duk mutane ɗakin suka zuba masa ido, yanda yayi maganar ko Zuhra bazatayi ba, kuma, koda ya faɗi haka tsuke fuska yayi yana kallon wayarshi,
"jeka zan sa Zuhra takawo maka, amma ai na aika muku da abinci, kashigo." tace mashi,

"Ok" yace sannan yafita daga ɗakin,

Abinci tayi mashi mara nauyi sannan ta haɗa mashi da farfesun kaza, tabawa zuhra takai mashi.

Satinsu biyu suka kai matansu makaranta,shi da Maina wanda ya ɗan same kintsi, a cikin sati buyi, dan tunda Ubaidatu ta gane irin mijinta ta cire raki da ta mike tsaye dan ta rikeshi da hanun bibiyu.


Suna kaisu suka juyo, zuwa bauchi, basu shigo ba sai kusan hudu na dare dan haka gidan maina da yake kusa nan suka yada zango,

Washi gari monday sukayi sallama kowa ya wucce wajen aikinshi.

Farin cikine fal zuciyar mashkur dan tunda a can zuciyarshi yake kaiwa da kawowa, dan cike yake da son yin tozali da ita, uwa uba kewarta da ya cika zuciyarshi,

Da wuri ya taso aiki a gurguje ya sake kayanshi, sannan yafito dai-dai hanyar wuccewarsu da motarshi ya pake a wajen ya hawu, samar motar ya xauna yana kallon hanyar da zata ɓulo,

dukda hira suke da zubaida a wasup amma be bata hankalinshi kaman yanda yazubawa hanyar da Shkurah zata fito,

Can yashiga jin muryan ɗalibai, kashe datar wayar yayi yana me raraba idanunshi.
Hangota yayi rataye da jaka,a kafaɗarta riga da sekit ɗin unifoam ɗin ya ɗauketa cak,
zuciyarshi ce tacigaba da bugawa a hankali har suka iso gurinshi, zasu wuce shima binsu yayi suna tafiyan dashi,

hiran da suke duk suka daina, yana tafiya amma yana satar kallonta, duk sai taji ta atakure dan haka tare napep suka shiga yi amma sukak'i sabida ɗaurowan hadiri lokaci guda, karshe shi ya tsida musu napep kuma yabiya kuɗin, kallonta yayi sannan yace,
"Shkurah, "

ɗagowa tayi suka haɗa ido,da saurin ta saukar da kanta tayi tana k'amk'ame jakarta. sai murza hanun jakar take, taki sake ɗago kai, ga ruwan da ya sauko kaman da bakin k'warya.

Me keken ne yace,
"Bawan Allah zamu tafi, kaga ruwan ya sauko da karfi"

gyara tsayiwarshi yayi sannan yace,
"Nima tsayi dani tayi, kace ta min magana sai na barku kutafi,"

mamakine ya rufe su maryam,
me nape da ya k'agu ya tafi yajuya, yace
"don Allah kisallame shi, mana mutafi,"

"Kyaleta malam kuje ga kuɗinkan" ya mika masa kuɗin, shi har ya juya,zai tafi ya tsinkayo muryarta tana cewa,
"malam maida mashi kuɗinshi, muma iyayenmu sun bamu kuɗin komawa gida, bana son haka, duk kabi ka uzura min"

murmushi yayi, sannan yabar wajen zuciyarshi cike da nisha, amma kuma ya yanke hukunci kauracewa hanyar har na tsawon kwanaki, yana cikin wannam tunanin ne, aka kirashi yashirya zasu wani aiki a lagos,


Bayan me napep yaja, sun fara tafiya, Salmah ce ta gaza hakuri tace,
"Wallahu baki da kirki, wannan mutumin yana da mutunci, tun daga ranar da ya kusan bugeki yake bibiyarki, zakiyi mamakin yanda muka saka miki ido dukkanmu nan muna musan dalilinki yasa yake zuwa nan ya tsaya kuma ke da kanki ranar kika ce badan shi ba da wasu yan iska sun miki rashin mutunci, masa kallon mutumin kirki beyi kama da na banza ba, kuma Allah kowa yaga yanda yake miki yasan sonki yake, dubeshi mana, kafin asame irinshi sai kin sha bakar wahala, my dear ki fahimce ni"

"Wallahi ni dai banga aibunshi, ba asalima, kun dace, a cikin kusan wata guda, ya faɗa kogin sonki don Allah karkiyi wasa da damarki" inji bebes,

Dariya maryam tayi, tace "yarinya kinyi, ba mamaki da zafinshi yake, kuma yanda nake ganinshi, kaman ma'aikacin tsorone, kawai baby, inda yazo da tayinshi karki mana bakin cikin shiga wancar motar"😜

Shiru tayi bata san me zata iƴa ce musu, ba amma kuma bazata iya son mutumin da suka haɗu a hanya ba, toh taya ma haka zai fari God forbid,


......
Bayan sun isa gida me napep ya ya basu canji taki karɓa tace,
" jeka kaima Allah yaci da rabonkane,"

godiya yayita zuba musu maryam da bebes suka nufi gidansu ita da salmah da rafi'a suka shiga gida, duk wannan hiran da akeyi tana ji kulle abin tayi a ranta,

Suna shiga cikin gida, kowa ya nufi wajensu ganin Babansu yasa rafi'a sake murmushi tace,
"Baba nikan makaranta katuramune ko tsayiwa da samaruka, amma ka tambayi sallama sune yan bada shawara."

Tana gama faɗan haka tashige part ɗinsu a guje, dan tasan shkurah bazata kyaleta ba,

tsaresu yayi yana kallonsu jikinsune ya ɗauki rawa,
"Bangane me take nufi, ba ku min bayani yanda zan gane inba haka ba zan zaneku,"

A nutse salmah tayi mashi bayani yanda ya fahimta, tana gama faɗa mashi Aisha da take kicin itama ta faɗa mashi yanda yayi musu hidima a haɗuwansu,

mai da kallonshi yayi kanta sunkuyar da kanta tayi kasa, murmushi, yayi sannan yace,
"Me yasa kike, masa haka kuma har hidima yake miki baki iya ce mashi kingode, me yasa"

Muryanta na rawa ta ɗago kai takalle Alhaji Hammayo, tace
"kai kace karatu, katuramu ba shashanci ba." shiru tayi idanunta na zubda kwalla ta cigaba da cewa.
"Baba ban wulakantashi ba amma kuma ai nimace ce, kuma na fito gidan mutunci da kima, akan hanya zan tsaya ina kulashi, nasan nayi kuskure rashin masa godiya, amma banyi haka da manufa ba,"

"Jeki ɗakinku" yace mata,

tana shiga falo, jikin Umma tazube tacigaba da kukanta,shafa mata kai umma tayi, hankali ta ɗago kai tace,
"Ummana laifene abinda nayi, kuskure na aikata, don Allah umma koda zanyi kuskure a rayuwata ki ɗauka Qaddaratace tasame ni, don Allah karki juya min baya"

rashe mata hawaye Umma tayi sannan tace,
"Wa yace miki, uwa tana iya juyawa y'ay'anta baya, koda sunayi ni bazan juya miki ba auta, dan nasan kowani bawa da yanda Allah yake jarabta shi, karki sake faɗan haka."



Tashi tayi tana dariya tashiga ɗakinsu,


Tun daga ranar bata sake ganinshi ba, tun abin be damunta har yakai idan suka biyo hanyar ta dunga raba idanunta kenansu Bebes suna lura da ita,


sannun a hankali tashiga musu maganarshi takance,
" Kunga wannan sarkin nacin yanzun ya daina zuwa, daman yan amore ne, hmm"

Idan sukaji haka shareta suke suyi banza da ita.

A cikin satin na biyu da ta ganshi Bebes da Maryam da Salmah suka haɗu a masalaci, salmah tace.
"Shkurah fa tadamu da, rashin ganin mutumin nan dan ko jiya da muka dawo , sai da tasake min maganarshi, ina ganin kaman sonshi take,"

"Kina ganin dagsk sonshi take, " inji maryam,

"Eh mana idan baso ba meye, zaisa takoma wata silent, kuma haka kawai zaki ga ta zauna tana rubutun abinda ya faru, na haɗuwansu am think that ta faɗane" inji Bebes.

"Toh idan muna tamtama, idan tazo mana da maganarshi mu dizgata mana muga yanda zatayi." inji salmah.



duk sai sukayi na'am da shawaranta, aikuwa ana tashi, sun zo inda yake zaman jiranta kallon wajen tayi fuskanta ɗauke da murmushi tace,
"Ai kunga inda yake tsayawa, yayita binmi Allah sarki"

"Mtsew ina ruwanmu, da inda yake tsayaewa ince damuka miki magana banza damu kikayi sai ynx da kika ga babu sarki sai Allah shine zaki addabemu, nan zayita binmu amma ko kallon arziki baya samu daga gareki sai ynxne zaki damemu da maganarshi dalla malama karki sake takura mana."


Allah sarki shkurah sarki faɗa yau itace ake muzanta mata akan abinda zuciyarta take azalzalarta da ta amayar dashi, kwalla ne masu zafi take zubdawa inda kuka yaci karfinta tsayawa sukayi suna kallon ikon Allah,

Durkusawa tayi a wajen tafashe da wani irin kuka me cin rai da taɓa zuciya suma sai suka biye mata suna kukan, sun zagayeta har da Rafi'a itama kuka take sosai.

Daga can ya hangosu dawowarshi kenan daga tafiya karkata kan motar yayi inda yayiwa yaranshi hanun da sutafi.

Wajensu yazo yayi parking sannan ya sauko, a hankali yake takawa dan ya gama gajiya ganin kaman itace a durkushe yasa ya kara saurin tafiyarshi, juyawa salmah tayi ta ganshi zatayi magana yasa hanunshi a bakinshi dan yaji tana magana ne,

haka ma sauran hanasu magana yayi ya durkusa, gabanta inda take cewa,
"Allah shine shaidana dan kaina bazan damu, da maganarshi ba zuciyata ke ingixani da nayi magana akanshi, toh meye laifina da zaku min masifa,"

duk cikin kuka take wannan maganar, tausayi da sontane suka cika zuciyarshi,
"lallai yau zaku sha, dukka shine kuka samin ita kuka, maza kubata hakuri." kaman daga sama take jin maganarshi dan haka da sauri ta ɗago kai shine kuwa,

Share hawayenta tayi ta mike ta ɓala mashi harara tare da murguɗa mashi baki, take kuka ya kare.

Murmushin nasara yayi dan haka tana gaba shi yana baya rike da jakarta da ya rigata ɗauka, su maryam kuwa suna bayanshi.
A gaban murmushi take, shima haka,



sun jima kafin dai daga karshe shi ya kaisu gida,


***
Har ynx ya gaza buɗe mata zuciyarshi, dan so yake, ta gama skull, tunda yasan gidansu jifa jifa yana zuwa,

Lokaci yatafi dan har sun kunsan fara jarabawa fita saura wata biyu.


*Muguwar Gamo*
Yau tun karfe uku ake sheka ruwa, har kusan sutashi sannan ruwan ya tsagaita, aikuwa tashesu da sauri suka fito abinda basu hawa mashin dan haka duk mutum biyu sukayi ta hawa, saura ita gashi ruwan ya dawo,

busu jakarta tayi suka tafi dashi.


Mashkur wanda be jima da dawowa ba ya tambayi wanda yasa tsaron shukrah ko suntashi yace mashi eh sauran sun tafi saura ita amma zaibi bayanta har tasame abin hawa.

Kashe kiran yayi ya ɗauki lema da rigar ruwa yafito kiran maina ne yashigo masa yace gashi a hanyar gidanshi nan zuwa,

be saurari me zaice ba ya kashe kiran,

tafito dai-dai jibrin Aminu model school shi kuma maina ya tawo kenan ya hangota, yanda kayanta ya kwanta a jikinta, riga da wandone a jikinta duk sun kwanta sabida ruwan da ya bugeta,

sai da yasame guri yayi parking yana kare mata kallo tsaye take a gurin tana jiran mashin ko nape ai wani mugun sha'awartane ya make shi, duk da yayi aure be fasa bin matan layi ba, shaiɗan ne yayi mashi huɗubar tsiya yafito daga motar ya tunkareta, kuwa da rigar ruwa yana zuwa wajenta ya warware zai kai hanunshi, wai zai saka mata ja da baya tayi tace,
"karka taɓa ni

Please Login or Register in order to submit comment