Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zubaida kukan take kaman me, mikewa Ubaida tayi ta goge fuskanta time table ta duba, ganin saura sati hudu sufara exam yasa tasaki murmushi, fita tayi daga ɗakin ta tafi, ɗakin kusa dasu akwai kawarta a cikin nan ta faɗa mata zata india duba yayanta da bashi da lafiya, kuma zata ɗauki kaman sati biu zuwa uku ko zata taimaka mata da test idan kuma an bada assgment ta turo mata ta email, idan tayi zata turo sai ta copy mata,"

      Amincewa kawar tayi, godiya tayi mata sannan tafito daga ɗakin, ɗakinsu ta koma ta haɗa kayanta cikin nutsuwa sannan tafita ɗakin kawarta taje tayi mata sallama, sannan taje ofishin jakadancin India dake nan kano taje, tacika foam ce mata sukayi taje ta dawo zuwa gobe.

     Dan dole ta dawo hostel nan ta cigaba da niman wani information, asibitin dasu Mommah suke, ta baki zuhra tasame sunan asibitin.

Washi gari.....
Tayi sallama da kowa, amma banda zubaida abin ya dame zubaida dan har kuka tayi, a ranar takira Nana mahaifiyarsu kenan ta faɗa mata, abinda maina yayi, jikin Nana har rawa yake nan tashiga shashin sarki ta faɗa mashi abinda maina ya aikata cike da bakin ciki da ɓacin rai yakira layinshi babu baya shiga duk wani inda sarki Husain yasan zai same maina babu,

            karshe kiran ogan maina yaya ya tambaye shi ko maina yana nan.
         Cike da mamaki ogan yace.
"Ai maina yabar kasan nan, ya koma amurka da aikin shekara biyar da sojojin Nato, ashe bai faɗa maka ba ayya kayi hakuri, maybe sun mashi kiran gaggawane."

"Ok nagode ba damuwa Allah yabashi sa'a." sarki hussain yace.

           Kallon Nana yayi ranshi na masa zafi, yace.
"Yanzun kinga illar abinda yasa nake, takura shi ko, ba iya wannan ba Maina shine shan giya, shine niman mata, duk inda kike kallon maina ya wucce haka"

        dariya yayi sannan yace.
"Ai ba damuwa, duniya ce tafi bagaruwa."

     yana gama faɗin haka ya wucce cikin turakanshi ita kuwa nana kuka tafashe da shi me cikin rai, tare da bakin cikin halin da maina yake ciki, can wani tunani yazo mata na ai ba mamaki asiri aka masa dan tasan kishiyoyintane dan suna gudun kar,  idan sarki ya mutu kar abawa maina sarauta idan aka san yana da mugun ɗabi'a(Wai da gaske asirine ɗaukar hakki😹,)


              ***
Ubaida ta isa india lafiya, daga airport aka wucce da ita, asibitin nan ta shiga niman indasu Mommah suke dakyar tasamesu da taimako wata nurse ita take lura da,  ganin yanda suke kama da mashkur yasa tayi mata magana cikin harshen turanci haɗi da india tace.
"Ke kanwar mashkur ne"

       jikinta na rawa tace, "Eh nice"

         "ok" tace mata tashiga gaba tana binta a baya har inda mashkur yake mommah ma tana zaune rike da hanunshi, godiya tayiwa nurse ɗin sannan tashiga ɗakin da sallama, ɗagowa mommah tayi tana kallonta, fuskanta ɗauke da mamaki, kukan da Ubaida ke haɗiyewa nr ya, kwace mata ajiye jakarta tayi, a kasa ta karasa wajen Momma ta, zuɓe a jikinta tana wani irin kuka me cin rai da ruhi.. hanunta na rike da mashkur ɗaya yana shafa kan Ubaidatu hawaye masu ɗumi na ɗiga daga idanunta.


         Sun ɗauki lokaci a haka, kafin ta haɗiye kukan ta ɗago da kanta tace.
"Mommah meke damunshi, suka ce."

Ajiyar zuciya mommah tayi sannan tace,
"Heart attack, lokaci guda abin ya bani mamaki da al'ajabi sosai dan kafin faruwan abin muyi waya da shi yake faɗa min, ana bikin saukar Shkurah, toh tundaga lokacin ban sake jinshi ba, sai da aka kirani wai bashi da lafiya."

    kallon mommah tayi cike da damuwa ganin yanda lokaci guda ta koma yasa ta ɓoye damuwarta bata faɗa mata ba ɗaura kanta tayi akan cinyar mommah.

      Can  ta kalleta da mamaki a fuskarta mommah tace.
"Ina mijinki yake? naga tunɗazun kika zo kuma ban ganshi ba.
     k'ak'aro murmushi tayi tace.
"Baya gari, amma shima zai zo."

         Haka suka cigaba da taɓa hira sama-sama
         satin ubaida biyu ta dawo, amma zuciyarta yana gurinsu dan a daddafe, suka fara karatu kafin exam ɗinsu.


          ***
A cikin wata biyu zuwa uku, shkurah, ɗan dawo hayacinta dan wannan lokacin yazo mata da hidima dayawa ga, gama skull ɗinsu ga bikin y'an gidansu wanda shine agabansu, hankali su ya tafi da tsara event da sauransu.


       Alhamdulillah yau Shkurah suka gama,paper karshe, gashi yau za'ayi kamun Aisha dan haka bata taɓa lokaci ba tafito daga class. A gajiye da kasala da yake sakata a gaba dan har barcu barci take ji, tana fita bakin gater ta faɗa mota, wani irin rana ake me ɗan karen zafi.

       Haka sauran yan uwant suka shiga mota, Kawarta Aisha Abbad ce ta leko ta motar tace.
"Dan girman Allah faɗa min sunan man da kike shafawa, babu kyau wulakanci fa"

      tsaki tayi sannan tace.
"Ke ni kirabu dani, wallahi bana shafa kome vase line nake shafa, muje don Allah."

       Dariya salmah tayi sannan tace.
"Dear wallahi kowa ya ganki dole yace kina shafa mai, kuma kin kara girma kinji kome hip hop ɗinki sunyi tam " duka takaiwa salmah ita kuma sai dariya har ɗa rafi'a tsokananta suke."


      Haka suka isa gida wanda ya cika makil da jama'a haka ta ratsasu tashige ɗakinsu kwanciya tayi ta zubda kome dake hanunta, ta hawu sauke ajiyar zuciya na gaji barcine yayi gaba da ita.

          Bata tashi ba sai, karfe biu da rabi ta farka wanka tayi tayi sallah azahar, siket fari da wani riga me ɗan guntu hanun tasaka, farin ɗan kune tasaka tufke gashinta tayi zuwa gefen kanta ta fito ɗakin Umma shiga tayi ta gaida yan uwan babanta sannan ta kalle Umma cikin shagwaɓa tace.
"Zanci ɗan wake umma, da kayan haɗi.."
     dan shi take bukata dan har wani haɗiye yawun daɗi take idan tatuna, yanda ɗan waken zai ji yaji....

          Hararanta umma tayi sannan tace.
"Ki wucce kicin akwai kayan ɗan wake kisa Sahura ta miki bana son, fitina ina da mutane a nan."

       "Toh umma" tafita, dariya yan uwan baban shkurah sukayi sannan ɗaya daga cikinsu tace.
"Habiba kin sakalta shkurah dayawa fa, shi yasa take rigama son ranta."

      Dukkansu dariya suka cigaba da yi.


          Karfe biyar aka tafi kamu, kome na wajen yayi kyau sosai.

Washi gari....
       Akayi waleema, da wasu.hidima dake ranae juma'a ne.
     Ranar asabar hidima ya karu, daga cikin bakin gidan har da kanwar maman Aunty amarya, duk suna tare a waje ana aiki, tana xaune shkurah tazo ta wucce, ta bita da idanun tasake dawowa haka tasake binta da shi mikewa tayi ta kira aunty amarya ɗaki,
       kallonta aunty amarya tayi sannan tace.
"Lafiya kika kirani,Inna."
       
Cike da tsoro tace.
"Yar mijinki tana da aurene,"
   "wacce kenan a cikinsu" inji Aunty Amarya.
             "Shrkul take ko shkulce ke ni ban iya sunanta ba wannan me kama da larabawan gidan naga alamun ɗanyen ciki a jikinta kuma wallahi baxan miki karya ba," inji Inna kenan.

        dariya tayi sannan tace.
"Tunda kika rantse nasan bazaki min karya ba, kuma nima na jima ina mata kallon haka, lokacin rugujewar fadarki yazo Habiba dan sai nasaki kuka a yau farin ciki haɗi da bakin ciki, abin zai bada ma'ana."


   Fita Aunty amarya tayi daga ɗakin tana jiran fitowar shkurah bata fito ba sai, da ta shirya cikin Atamfar super holland ɗinki riga da zani, wanda aka mata 6 pieces tayi kyau sosai, kamar itace amaryar,

       Dake a masalacin gida ake ɗaura auren Aisha, Abubakar kuma a masalacin gwallaga sai aka raba wasu suna gwallaga wasu nan, sanarwa akayi an ɗaura auren Aisha guɗa ake tayi, lokacin Aunty amarya, ta ɗaga murya da karfi dan lokacin Alhaji Hammayo ya shigo gidan kenan tace.
"Shkurah rabonki da al'adarki wata nawa kenan, kina min kama da masu juna biyu,gashi rabon Mashkur da zuwa kusan wata uku kenan, yaci moriya ya gudu, ko"

  
      Ba shkurah ba, harta Umma da ta mika mama wayarta sunyi waya da Ammar ɗan Mama da Alhaji Hammayo ya kora sabida yana shaye shaye da ɗauke ɗauke.
Sake wayar mama tayi cike da tsoro suma zubawa shkurah ido sukayi


_Nima zubawa Shkula ido nayi Aunty Ruky ayi min afuwa bansan yanda zan muku kuji daɗi ba wallahi da nayi kaddaranta ce tazo a haka, kunci da bakin ciki sunfi farin ciki da soyayyan cikin rayuwarta yawa_

              
*Ina yinku*💋
3/4/21, 9:45 AM - Ummi Tandama: *🙆QADDARAN RAYUWATA🙆*
_SHUKRAH_
Mai_Dambu

'''Watan azumin da ya wucce an tambayi Iman Zubairu Madaki, dangane da meye illar koran yaro daga gidan idan yayiwa iyayenshi kuskure, malam yace, illar koran yara daga gida shine, idan kakore shi zaifita yacigaba da abinda ka koreshi akanshi, zai ɓata maka suna, zai kasance yana jin zafinka zai aikata duk abinda yasan ranka zai ɓaci, Uwa uba ta sanadin shi zaka mutu, ko kashiga mugun hali, kuma zai zamewa al'umma fitina dan haka yake jan hankali ga iyayen da suyi hakuri da yaransu Allah yasa mudace'''

       next page zan kawo sauran bayanan.

Al-Muizzu Al-Sammeu Al-Baseer Al-Hakamu👏👏👏👏👏

*Sadeeya Zabura wannan shafin nakine*💋💜

*page 11*

Duk ilahin mutane,wajen shkurah, suka zubawa idanun dan son sanin sahihin gaskiyar abinda Aunty amarya ta faɗa.

         Jikinta rawa ya ɗauka tuni kofin glass ɗin hanunta ya faɗo kasa, sai ja da baya take,
         buga mata tsawa Alhaji Hammayo yayi cike da tashin hankali yace.
"Cikin waye a jikinki *?*"

Wani irin tsoro da firgici ne suka diro mata lokaci guda, durkusawa tayi ta kifa kanta a cinyarta, sannan ta ɗaga hanunwanta ta kare kanta, ciki da tashin hankali.

    Abinda ya farune da ita ya shiga dawo mata,sam bata zata rashin ganin period ɗinta zai yana nufin cikine da ita, fashewa da kuka tayi yana, zuwa ya rufeta da wani irin duka yana yi da hanun yana haɗawa da kafa, duka yake mata, irin wanda za'a yiwa Yaya sadeeq, yana tambayarta ciki waye a jikinta.

          Mama da Ummi ne suka kai mata, ya juya a fusace yace,
"Duk wacce tazo nan, a bakin aurenta." dan dole suka koma baya, umma tana tsaye kanta a sunkuye,  wani irin ciwo da zafin abinda ya faru da shkurah take ji,

      A hankali, tashiga nazarin ciwon da shkurah tayi a matsayinta na me ilimin halayar dan adam wato(Psychology) yaci ace ta karanci shkurah, taya haka ya faru.

Dukan da Alhj hammayo yakewa Shkurah wanda tun tana ihu har tayi shiru, shi ya dawo da Umma daga duniyar tunani cikin zafin, nama tashiga tsakaninsu, ɗaga shkurah tayi wacce hancinta da bakinta ke fida jini, ta rungumota zata shigar da ita cikin part ɗinta, a zafaffe yace.
"Wallahi karki sakata a cikin gidana, dan ba zan zauna da mazinaciya ba, indai karuwanci kika ce zaki jeki na sallamawa duniya ke, kuma kushaida nacire Zainab a cikin y'ayana, kaman yanda kika sani bakin ciki ba zaki ga me kyau ba, Allah ya wadaranki zainab haka zaki dawwama a cikin karuwanci."

Fisgota yayi ya hankadata zai fita da ita waje, duk cikin mutanen gidan aka rasa wanda zai ce masa yayi hakuri.

      rungume hanun umma tayi a kirji tana kallon shi yana hankaɗa Shkurah sai da ya tunkuɗata waje ta faɗi sannan Umma tace.

"Kaman yanda ka fitar da ita daga cikin gidan nan haka kaima, ka tsaya a waje sabida gidan da kake ihun bazata zauna ba a ciki mallakina ne,"

           A razane ya ɗago kanshi yana kallonta cike da mamaki, abinda tai masa, akan shkurah take sauran mutanen suka maida kallonsu kanta. murmushi tayi cike da izza da jin kai, ta karasa gaban Aunty Amarya tana kallonta.

      k'warjini Umma tayi mata, tsoro da shakkar umma suka bayyana a cikin idanunta, wani kasaitacciyar murmushi umma tayi, yanda kuka san jinin sarauta haka takoma tace.
"Mijinki bai taɓa faɗa miki, dukiyar da yake tak'ama da shi mallakina bane, ko ance miki dai dai da wanda yake baki ban sani bane, kin ɗauka na mallake kowa a gidan nan sabida, shine ko ance miki ni irinki ce wacce take zaune sabida abin duniya,"

        juyawa tayi cike da ɓacin rai tace.
"Na baka nan da awa uku, ka haɗa min kan dukiyata, itakuma zan kaita inda zata zauna,"

           ɗakinta ta koma ta ɗauki himar ɗinta da wani babban akwati ta shiga ɗakinsu shkurah ta haɗa kayan shkurah tsab tana kuka, sannan ta ɗauko atm da sabowar wayar da tasa bilal ya ɗauko mata a shagon da yake saida wayoyi idan yana gari.

       Jan jakar tayi tafita da shi, duk mutane kowa na tsaye kaman an shuka dusa, kiran bilal tayi tace.
"ɗauko motar can ka, kaimu Tashan yankari,"

      gefe ɗaya tana, kiran wani layi da wayarta kiran na shiga ta juya fulatanci,can ta maida shi da hausa tace.
" Ga me sunan, Ya goggo nan, zuwa next week idan nagama abinda ke gabana nima zan dawo, gida zan dawo cikinku koda kasheni zakuyi Zaituna, ga Shkurah nan zuwa."

           Bilal yana zuwa,da motar ya fito ya ɗauki a kwatin ya saka a motar, sannan umma ta shiga suka fita tana zaune a gefe yara sun cika inda take sai tattara rigarta take tana ɓoye fuskanta, kaman dai yanda tayi a baya faruwa, abin ciwon haukar ya dawo mata sabo fil, bilal ne yafi dan ya shigo da ita motar ta shiga ja da baya, tana gurnani, umma naganin haka ta kalle shi tace.
"koma mota zan shigo da ita, yanzun,"

     zuwa gurinta tayi cikin rarrashi take mata magana har ta amince tazo tashiga motar suka wucce tasha, inda suka nemi motar da zai tafi yola,  a lokaci nan aka biya kuɗin motar saura pasinja biyu a mota umma ta kalle cikin nutsu tace.
"Nasan duk da yanzun kina cikin wani, hali amma ai zaki iya faɗa min kome, tunda kina iya gane ni."

           Kallon Umma tayi cikin kuka ta rike kanta, tace.
"Shine"

"Mashkur" inji umma.

"A'a" tace,
"toh waye shi ɗin?" inji umma ta jefa mata tambaya,

Kwanciya tayi a jikin umma kin shashekar kuka, tace " umma Maina ne ranar saukarmu....."

       Ba umma kaɗai ba har bilal da yake gaban mota kuka yake, shafa kanta umma tayi sannan tace.
"Da yardan Ubangiji ba za'a sake keta miki haddi ba, babu wanda ya isa ya kusanceki da niyyar zina, zaki kasance cikin kariyar umma ubangiji,anyi na farko anyi na karshe, ba za'a sake ba kinji."

Rarrashinta take, har tayi shiru, sake kiran layi Zaituna tayi, sannan tace.
"Gamu a tasha insha Allah ynz zasu taso don Allah idan taxo ki kaimun ita asibiti, zaituna zan zo, akwai damu don Allah ki kai taga likitan k'wak'walawa don Allah sannan kisa min akanta karta taɓa lafiya cikin jikinta pls ."

        Kashe wayar tayi sannan suka fita sakamakon maganar da aka musu na ansami mutum biu duk matane uwa da y'a wajen matar taje suka gaisa sannan umma tace.
"Yola zaki ko, don Allah ga yarinyata bata da ishshiyar lafiya, ki luran min da ita don Allah na baki amanarta don Allah, ta karshe maganar idanunta cike da k'walla.

     "Insha Allah, zan rike miki ita, har ta isa inda kika turata." inji matar.

Umma tayi ɗan murmushi kafin tace.
"Kuna zuwa tasha, zaku same wacce zata ɗauketa, kanwata zatazo"

                  duk da halin da take ciki, bai hanata kallon Mahaifiyarta ba, cikin kuka tace.
"Umma haihuwa bata da amfani, umma ina jin idan na tafi, ba zan sake dawowa ba, umma ki yafe min saki kuka da nayi, kice baba ya yafe min, Don Allah Umma karki rabu da Baba sabida, ki min alkawarin a kullum zaki min addu'a dukda nasan kinayi," rungumeta umma tayi tana kuka tace.
Nayi miki alkawari, insha Allah zamu sake haɗuwa, kinji ko Shkurahta."

    Sai da aka musu magana sannan suka rabu tashiga mota kallon umma take sosai hawaye na zuba daga idanunta, har suka bar tashan mass.

         Komawa gida umma sukayi tayi parking kayanta baki ɗaya ta ɗauki mukulin ɗaya daga ciki gidajenta tasa bilal ya kwashe mata, zuwa gidanta dake makama new extension sai a lokacin mutane suka shiga bata hakuri koda albarkacin y'aya ta zauna, kuskure ne dai shkurah tayi, bau kyautu ace an rabu ba, ai haka ba daɗi, gashi ana cikin hidiman baki,  duk da me laifi amarya ce, amma tayi hakuri.

Dariya umma tayi sannan tace.
"Da yake dukanta wacece ta dakarta da shi da Mama da Ummi suka nemi dakarta da shi cewa yayi a bakin aurensu,"

      sake kallon matar da tayi maganar tayi tace.
"Shekaru talatin da uku zuwa da huɗu, baya ke kikace, hammayo ya auro me bakar kafa, lokacin da nake zuwa wajenki ki samin abinci sabida cikin jikina cewa kike ba zaki ba yar ba, dan baki sashi ya auro faran mace me farar kafa, ko ba haka ba, da Allah ya buɗa mashi kika ce ya kara aure, dan ba zaku so ya zauna da mace me fara kafa ba, ko ance miki ban san me nake ba yi bane, ki wuce kici arziki iya na yau gobe kuma a kama hanya,"

dakyar umma ta amince ta xauna sai da Hammayo yasa aka shigo da limamin dake sallah a masalacin gidan yayi mata nasiha, sannan ya koma kan Alhaji hammayo sosai yayi masa nasiha me shiga jiki, san yace ya yafewa shkurah wallahi ko shi ya shaida halinta kaddara ce ta faɗa mata, kuma babu wanda ya wucce haka,

             ***
Cikin awa huɗu suka isa, garin gombe, tafiya suke har suka wucce ako, sun nufi kaltingo nan suka samu ana ruwan sama kaman da bakin k'warya sabida karfin ruwan sauka sukayi akan hanya suka, tsaya kafin ruwan ya tsagaita.

         Suna gefen hanya ne wani wak'iya ta runtsa da motoccin wajen dan wata tankar mai ce tazo wuccewa tsawa ta faɗoasa, take tankar ta fashe man ya tarwatsu a ko ina dukda ana ruwa, tare ya kama motoccin da suke wajen, tashin hankalin, nan motar mutane sukai ta kamawa da wuta, har da motarsu shkurah ayya ganin haka driven ya ruɗe ya shiga rubass ya juya yayu karo da da wata mota nan yayi, nan motar ya fara dungure yana kamawa mutane ciki suna ihu, can cikin daji motar ta tsaya duk glass ɗin motar ta farfashe, sannan takama da wuta, dan ma anan ruwa,

                 A can titi ana tacire mutane a cikin mota, sai da sukq ci karfin na waje sannan suka faɗa dajin dan ceton na cikin wancar motar duk sun kone.

            haka aka janyo motar sai lokacin yan sanda suka iso wajen,

      suna bincike, suna gamawa, sukafito yaje da niyyar yin fitsari yaji nishin mutum yana lekawa yaga shkurah a kance tana fitar da numfashin wahala jini nafita ta hancinta murmushi yayi yace.
"Lady kinyi samuwa,"ciro wayarshi yayi daga aljuhun rigarshi ya latsa kiran,

     "Uban me zan maka corpru bala ince na biyaka kuɗin" inji lady kenan.

     murmushi yayi yace.
"Shegiya uwar karuwai samuwa na miki. wannan karon kuɗi nake so, kizo hanyar kaltigo ga kaya nan musu kyau amma zamanta a gurinki na da hatsari, zan bar miki alama, zan tsinki ganye na zuba a wajen da haka xaki gane."

     ***
Indian Hospital.....
Karan nauran da aka saka masa ne yayi kara alamun numfashinsa ya hawura sama da casa'in da tara. lokacin Momma tana rike da karamin alkur'ani tana karanta suratul yasin, da gudu, drs suka nufi ɗakin.

         Nan aka shiga bashi kulawa sujadan godiya Mommah,

  bakinshi ne yaketa motsi yana magana, dr Lakshman ne yakai kunnenshi jikin bakinshi, sai ji yayi yana faɗin " shkura"


***

       Daukar nombar motar sukayi sannan suka kai station nan aka kira tashan yankari aka faɗa musu motarsu tayi hatsari, kuma duk mutane ciki sun mutu.

       Umma tana zaune a ɗakinta, aka kira bilal dake nombar wayarshi ya bada nan aka faɗa masa muguwar sako.

            Falon Alhaji Hammayo yaje, duk da mutane, duk ya barki ce, sai zufa ne yake karyo masa kallon sadeeq yayi yace.
"Bros pls zo mana"

      tashi yayi yabi bayanshi, nan ya faɗa masa, salati ya tare da tashin hankali ya shiga falon duk da bilal yana ce masa karka ɗaga musu hankali, ina yana shiga falon yace.
"Baba shikenan, shkurah ta rasuuuuu"

             Cikin tashin hankali Alhaji Hammayo ya mike, sai kuma ya koma ya zauna ya rike kanshi ya fashe da kuka,

             mutane da suke falone suka fita waje nan suka fessa.

  Take  gidan biki ya koma gidan zaman makoki, a nutse mama tashiga ɗakin umma ta jima sosai sannan ta fara kawo mata, ayoyi da hadisai can tayi shahadar kuda ta faɗa mata, tunda ta sauke kanta, tare da ajiyar zuciya ta ɗago tayi kalle mama sannan tace,
"karki damu Allah da yabani ya amsheta toh me ye nakuka, wallahi bana jin kome, akan mutuwar sai ma shakkun da nake........





🙆 _Kowa shafi yana da nashi damuwar ina ganin zan hakura da buk ɗin baki ɗaya dan nasan yana saku kuka ni kuma bana son haka kuyi hkr sai naji daga gareku_
3/4/21, 9:46 AM - Ummi Tandama: *QADDARAR RAYUWATA*
_SHUKRAH_
Mai_Dambu
Litattafan da Na rubuta👇
*Yaro ma namijine*
*Kishiyata Jahadina*
*Wani  Al'amarin*
*Ni da Yaya Muh'd*
*Wani Jinkirin*
 


'''Kunsan kowa na da ra'ayinsa akan suna, ba wai bana son asalin sunana bane a'a Sunan Me Dambu sunane da yake da daraja a guna, kuma sunane da bazan taɓa mantawa da shi ba, Dan haka yau ɗaya nayi amfani da sunana, da kuma sunan Buks ɗin dan ku, ba dan kaina ba, Ina muku tafan alkhairi'''
*ILOVE YOU ALL*💋

'''Cigaban bayyanin Imam zubairu madaki, Tambaya ce guɗa ɗaya jal kafin na ɗaura sauran bayyanan.   malam yace idan kakori ɗa namiji ina da karfi zai iya fafutukar ya tsaya da kafarshi.
Idan kakori Y'a mace daga gidanka a matsayinka na Uba... Ya zatayi?
        da wannan tambayar ya rufe tafsirin yace yana jiran amsar a gun iyaye maza da suke cikin masjid Umar bini Khaɗab.'''

  
Shin kina karanta buk ɗin asa ke Ubace ga tambaya da malam ya jefa muku amsa na gareku, tunda ga Alhaji Hammayo ya kori Shkurah daga gidansa👌


*Page 12*
Sai gashi umma itake rarrashin y'an gidan lokaci guda kome ya k'wauɓe a cikin gidan biki, Alhaji Hammayo kuka, yake tsakaninshi da Allah inda yayita k'washewa Aunty Amarya albarka, har kofar ɗakinta yaje yana tsine mata, karshe dai ya haɗa mata har da saki,

            Karin tashin hankali, umma ta tubure masa da ya dawo da ita kan y'ay'anta ko tafita tabar masa, gidanshi.
Zubawa Umma idanun yayi yana rike da kirjinsa, dakyar yaje sauke numfashi durkusawa yayi cikin tashin hankali ya faɗi,kasa yana tari jini yana fita daga bakinsa, haɗi da yawun me yauki.

           Nan akayi kanshi cikin tashin hankali, akayi ni'ima dashi.
         _Saurin fushi yana kawo danasani,yanke hukunci cikin fushi, yana kawo nadama mara amfani._

        ***
Kaltingo,kaman yanda corpru bala yayi mata k'watance haka, kuwa tasame Shkurah. Cikin mawuyacin hali, cikin gaggawa aka ɗauketa zuwa, gidanta da yake cikin kaltingo, takira likitan da yake cirewa y'an matan da suke ɗauke da ciki, a cikin yaranta da suke harkan zaman kansu.

         Duba shkurah yayi sosai, sannan yace mata,
"A gaskiya lady wannan yarinyar, zamanta a cikinku akwai hatsari, dan ki dubi zanin jikinta da ɗan kunnen kunnenta, haɗi da, kidubeta da kyau y'ar manya ce, ba yar kananun mutane, bane kisan yanda zakiyi da ita."

          Murmushi tayi sosai, sannann ta gyara zamanta tace.
"Idan na turata kaduna gurin, kawata Umaima,

Please Login or Register in order to submit comment