Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

✨ *Noor-Al-Hayat*✨

_By Khaleesat Haiydar_📚✍🏻

*All thanks to Allah S.W.T for giving me the chance and privilege to start this book*

1.....

Muryar dattijuwar macen da baxata haura shekaru hamsin a duniya ba ne ya cika dakin, hankali tashe take jijjiga matashin saurayin da shekarunsa ashirin da takwas, kwance yake kan makeken gadon dakin, ta dinga cewa "Are you okay son, open ur eyes, Aliyuuuu ka bude idonka, What's ur problem..... Wani irin mafarki ne wannan ni fatima" sai a snn ya bude idanuwansa a firgice ya mike xaune yana bin dakin da kallo kirjinsa na heaving, lkci daya ya mayar da kallonsa kan mahaifiyarsa dake kallonsa ta ma kasa cewa komai, ya runtse ido cikin sanyin murya yace "Motherrr...." ta kamo hannunsa damuwa karara fuskarta tace "What's ur problem Aliyu? Meye matsalar ka ka gaya min, are you sick?" ya buda idanuwansa yana kallonta murya can kasa yace "Ki taya ni addu'a mum... I don't knw, I just can't have rest of mind, may be....." Sai kuma yyi shiru hawaye ya taru lumsassun idonsa, tace "Ni mahaifiyar ka ce Aliyu, kana da warce xaka fadi ma damuwar ka duk fadin duniyar nn banda ni, tell me where you've gone wrong, what wrong have u done, ka gaya min Aliyu" ya share xufar goshinsa ya daura kai bisa kafadunta a hankali yace "Ki taya ni da addu'a kawai ummata" dago Kansa tayi tace "Wato dai baxa ka fada min ba koh?" Shiru yyi yana kallonta da manyan idanuwansa, can ya lumshe su a hankali ya bude yace "I will continue praying mum, it's not even worth saying kema ki taya ni...." Sake sa tayi ta mike tsam ta nufi kofa ya bi ta da ido kafin ta fita a hankali yace "Ur prayers plss mum..." Bata tankasa ba ta yi ficewarta, ya kalli agogo karfe biyun dare ya mike jiki a sanyaye ya shiga bathroom.

*5years later*

A hanxarce ta karasa dauraye cup da spoon da ta wanke ta fito kitchen din ta kashe electronics dake a kunne parlor ta dau jakarta dake kan kujera ta sakale a kafada ta nufi kofar fita tana kallon agogon wrist dinta, doguwar riga ce yar kanti Sea green a jikinta sae karamin mayafi ja da flat shoe shi ma ja, don ita din ba gwanar sa hill bace tsabar tsayinta, jakar hannunta ma dai jan ne, bbu komai fuskarta banda powder da eye pencil sai chapette da ta goga a lips dinta, amma ba lallai ka yrda cewar bata shafa pink lipstick ba tsabar pinkness din lips din dake dauke da xagayen baki, ita kanta tasan her lips are Unique, but who cares?? D'an tsaki ta ja ta bude kofa ta fito rike da makullin da xata rufe kofar Apartment dinta, tsaye taga wani matashi bakin kofar dake kusa da apartment dinta shi ma fitowarsa kenan da alama xai kulle kofa, dogo ne sosai domin kuwa irinsu ake kira da gentlemen, kuma duk tsayinta sai ta ganta karama kusa da shi, ya fi kama da mutan Egypt ko Ethiopia duba da kalan haskensa da irin gashin kansa, bakar shade ce a idonsa da ya fito da ainahin tsayin hancinsa, fuskar nan tasa a tamke bbu annuri, a hankali ta sauka ta bar masa gun, yana gama rufe kofarsa ya juya ba tare da ya kalli inda take ba ya wuce parking space, bin sa tayi da kallo ta rasa gane ko mancewa yyi bai gyara belt dinsa ba, ko kuwa ass down yyi, sakin baki tayi ganin of course ass down din fa yyi, ta dauke kai cike da takaicin xama a compound daya da xa su yi da shi. Shine sabon tenant din apartment din dake kusa da nata bayan tashin makwabciyarta mai kirki Nancy, tun tashinta dama take ta addu'ar Allah yasa ba namiji bane xai kama flat din sai ga shi kuwa namijin ne, bata kuma sani ba sai a yanxu don tafi sati uku bata kasar tun bayan da suka yi hutu dawowarta kenan jiya da yamma, jiki ba kwari ta karasa rufe kofar ta fita don samun taxi da xai kai ta makaranta wato University of Cambridge dake kasar. Karfe biyu da 'yan mintuna suka fito school tare da kawarta Vanessa, tun shekararta ta farko suke tare gashi har sun doshi shekara ta uku kenan tunda saura masu yan watanni ne kawai, sai da vanessa ta jira kawartata ta hau taxi bayan ta sanar da shi Bridge street xai kai ta kafin ta daga mata hannu tace "See yah pretty" ta sakar mata murmushi tana daga mata hannu daga cikin taxi din tace "Alryt love" har suka isa gida hankalinta bai tare da ita tayi nisa cikin tunanin da take yi, har sai da muryar Ba'indiyen dake jan taxi din ya dawo da ita duniyar tunanin da ta shiga, ta fito ta mika masa kudinsa sannan ta shiga gida, da sauri ta shige apartment dinta bayan ta bude, duk da bata ga alamar yana gidan ba don babu motarsa a ma'ajiyar sa. Wanka ta fara yi tayi sllh snn ta shiga kitchen don girka abinda xata ci, Noodles kadai ya rage gidan, don haka ta daura ruwa ta shiga hada wa, kafin ya dahu ta kwashe dustbin dake kitchen ta bude kofa ta fita da tsintsiya, kasake tayi tana kallon uban kayan gym da ya jibge daga gefen flat dinsa, tun dawowarta sai a lkcn ta fito backyard din flat dinta, ta tabe baki ta dau tsintsiya ta hau share gun, har part dinsa sai da ta share tayi disposing bolar a basket ta koma ciki ta rufe kofarta, tana gama cin indomie ta wuce daki ta kwanta, ta jawo wayarta don duba agogo taga karfe uku saura minti biyar, ajiye wayar tayi don wa enda take da niyar kira tasan suna makaranta ynxu, ta lumshe ido. Ba ita ta tashi daga baccin da ya dauketa ba sai hudu da quarter, ta shiga bayi da sauri don dauro alwala tana idar da sllh kuma ta dau material din karatunta ta hau yi.

*Nigeria*

Zaune yake kan dining idanuwansa a kan system dinsa dake gabansa yana kallon kwallo, hango mahaifiyarsa da yyi tana sakkowa daga saman bene yasa shi saurin dauke plate din abincin dake gaban sa ya tura karkashin dinning din ya dau lemon dake cup ya sha kusan rabi sannan ya ajiye ya goge bakinsa da handkerchief ya ci gaba da kallonsa keenly, har ta karaso dining din idonta na gun da yake xaune, ta jingina da pillar din dake wajajen dining din tace "Ina abincin?" Dago kai yayi ya kalleta yace "Mum, ban ma yi noticing naki ba ae, na ci" tace "The plate?" Ya nuna mata hanyar kitchen yace "Har na wanke" girgixa kai tayi ta juya ta koma parlor, ya saci kallon abincin da ya ajiye kasar dining yyi saurin dauke ido ya ci gaba da kallonsa, lkci daya ya lumshe ido ya jinginar da kansa jikin kujerar dinning din, ya fi minti goma a haka yaji ance "Ya Aliyu...." Ya bude ido da sauri, kyakkyawar yarinyar dake tsaye gaban sa ta sakar masa murmushi tace "Ina yini" yace "Lafiya lau... Hanan" ta buda idanuwanta sosai tace "Kai ka ajiye abinci a kasan nan?" Ta fadi tana nuna masa inda ya tura abinci, ya kalli direction din parlor da sauri yaga mumy bata nan, dukawa yyi ya fiddo yace "Gashi ki ci na koshi" ta tabe baki tana kallon hadadden jollof rice din dake dauke da kayan yanke yanke a kai da kusan quarter din kaza a gefe da plantain, kallonta yake yaga tayi murmushi tace "Kai me yasa baka ci ba?" A kara jinginar da kansa da kujera a takaice yace "I am nt hungry, idan baxa ki ci ba kema ki kai ma masu gadi yanxu" dauka tayi ta nufi kofar fita parlorn, ya bita da ido kafin ya mike ya kashe system dinsa don bai son ta dawo ta samesa a gun ya haura sama da sauri.

Misalin Karfe tara na dare tana kitchen tana dafa ruwan Lipton kamar yanda ta saba kafin ta kwanta, sai a sannan ta dinga jin kewan Nancy, don da yanxu ta ganta a dai dai wannan lkcn tana xaune kan resting chair tana shan coffee tana chatting, duk da ita ba gwanar xama a waje bace amma so tari saboda Nancyn haka nan ita ma xata bude kofa ta fita ta sameta ta xauna, sun yi ta hira kenan har kusan sha daya kafin kowa ya shiga ciki sai kuma gobe, Kamar ance ta daga kai suka yi ido hudu da wannan mutumin na daxu da safe daga shi sai singlet da 3 qtr waya na kare kunnensa, daya hannunsa kuma na rike da kwalba, sosai gabanta ya fadi tayi saurin kallon kofar kitchen dinta don ta tabbatar a kulle yake, ta sake satan kallonsa taga ya dakatar da wayar da yake yana kallonta ta cikin window ita kanta ta kasa fassara irin kallon, a hankali ta kai hannu ta kashe gas dinta sannan ta kashe wutan kitchen din gaba daya ta fita parlor da sauri don ta hakura da ruwan Lipton din.

*Haske writers Association**💡

✨ *Noor-Al-Hayat*✨

_Khaleesat Haiydar_📚✍🏻

2......

Washegari tun da ta tashi sallahn asuba bata sake komawa ba, ta d'an yi aikace aikacen da xata yi, sannan ta shiga shirin makaranta, ta dau lkci xaune a parlor bayan ta gama shiryawa, can ta jawo wayarta dake gefenta tayi dialing number ta kai kunne a hankali, har ya gama ringing ba a daga ba ta ajiye wayar ta mike ta dau plate na cake da ta ci ta kai kitchen, karfe bakwai da rabi ta fito gidan domin wucewa makaranta, abaya ce ta Al-layl jikinta baki, sosai abayar ta haska ta kasancewar ta fara, tana kkrin rufe kofa da makulli ya bude kofar Apartment dinsa ya fito, bai ko kalli gefenta ganin xai kulle kofarsa yasa ta sauka a hankali ta basa waje tana kallonsa don ko considering dinta bai yi a tsaye wajen, yau ma kamar jiya kananun kaya ne jikinsa, yana sanye ne da deep Blue polo me wani rubutu da bata gani ba a gaban rigar da jean trouser baki, ya gama rufe kofar yyi wucewarsa ba tare da ya kalli inda take tsaye ba, kamar dai jiya ynxu ma sai ta ga kamar sagging trousers din yayi, yaushe rabon duniya da shigen haukan nan, ta bi sa da wani irin kallo, bata san lkcn da ta ja wani dogon tsakin takaici ba, lkci daya ya juyo yana kallonta kamar jiran tsakin yake, gabanta yayi mugun faduwa, ya xare glass dinsa wanda hakan ya bayyana manyan idanuwansa masu kamar brown, still tayi a inda take xuciyarta na bugawa tana kifta ido, sai a snn ta kare ma fuskarsa kallo ta kuma kara tabbatar da lallai shi din kilan balarabe ne, kafafuwarta suka kasa daukarta ganin ya nufo ta, ya iso dab da ita yana mata wani kallo kmr me counting words dinsa yace "Did.... You.... Just.... Hissed?" Ta wani hade rai har lkcn xuciyata bai daina bugawa ba ta dake tace "Did I Know you???" Daga sama har kasa ya kalleta yace "Did u skipped English Language in school?" Ta hadiye abu da kyar hakan kuma bai hanata harararsa ba tana juya ido tace "That's none of ur....." K'ara tayi a mugun tsorace jin yanda yyi gripping dinta da karfi yana mata wani kallo har tana iya jiyo numfashinsa, lkci daya jikinta ya dau rawa hawaye ya fara taruwa idonta tace "Let go of me right away...." sai da ya gama kare mata kallo daga sama har kasa snn ya tura ta yace "We stil remain in the same surrounding" yana fadin haka ya juya ya yi wucewar sa, ranta a dagule ta rufe kofarta da sauri ta fice gidan hawayen takaici cike idonta. Throughout a schl ranan bata da sukuni duk ta rasa me ke mata dadi, how on earth xata iya rayuwa da wannan mutumin a gida daya, Vanessa da ta lura da she wasn't her self tun shigowarta schl ta kalleta tace "Pretty what's ur problem, u look dull all day, mood swing?" Ta d'an yi murmushi ta ja lemonade din gabanta ta sha kadan ta ajiye don dama a cafeteria suke tace "You don't worry Friend, I will be okay, I will fix my problem...." Vanessa tace "Good" sai bayan la'asar ta koma gida daga school, tana shiga apartment dinta ta sa key duk da ta lura bai dawo ba don bbu motarsa a gidan, but it will be safe ta sa makullin, tana idar da sllh xata kwanta ta tuna xata yi shopping don bbu komai a gidan banda noodles, ko kadan bata ji dadin tuna hakan da tayi ba gashi bata son fita, ta kusa minti goma xaune tana contemplating ta je ko dai ta hakura sai gobe, ganin bata da option ta mike jiki ba kwari ta fiddo babban veil ta yafa kan doguwar rigar jikinta don mai karamin hannu ne ta dau yar Jakarta karama ta rataye a kafada ta fita, nearest shopping complex ta nufa a taxi, tayi duk shopping da zata yi sannan ta dawo gida, mai taxi din ya taimaka mata ya sauke siyayyar sannan ta basa kudinsa ta dau kadan daga kayan ta shiga gida, gabanta ya fadi sosai ganinsa tsaye a parking space dinsa yana waya, tunda ta kallesa sau daya bata sake kallonsa ba tana isa tsakiyar compound din ta aje kayan hannunta ta koma waje dauko wasu, har wani harhardewa take yi tsabar rudun da ta shiga na ganinsa, ta yi sahu uku a na karshe ta daga kai suka yi ido hudu don kallonta yake, tayi saurin dauke ido ba tare da ta lura da har ta iso gun da take ajiye kayan ba ta afka kai sai gata a kasa ledan hannunta ya fadi chocolates da biscuits dake ciki duk suka watse nan kasa, har lkcn bai daina kallonta ba kuma bai ce komai ba, ta mike tsaye da sauri tana karkade jikinta hawaye cike idonta ta ki yarda ta kalli inda yake, a sanyaye ta durkusa ta shiga hada chocolates din da biscuit waje daya, ta gama ta tashi ta dau kadan daga kayan ta kai cikin parlor bayan ta bude kofa da key, haka tayi sahu har hudu kafin ta gama kwashe duk kayan, ta saci kallonsa taga kallon direction dinta yake, wani matsiyacin kallo tayi masa hade da jan tsaki, gyada kai yayi a hankali yana kallonta da wani murmushi fuskarsa, ta banke kofar ta ta kulle da makulli. Daki ta shiga ta kwanta bayan ta kai kayan maxauninsu a kitchen, har lkcn ta kasa samun nutsuwa sai juye juye take, ita ce xata xauna gida daya da wannan mutumin, ta girgixa kai tace "Impossible" tana ta kwance har bakwai saura qtr daga karshe ta tashi xaune a hankali ta shiga toilet ta dauro alwala ta fito, tana idar da sllh ta dau wayarta tayi dialing number ta kai kunne, bayan wani lkci aka daga, bata ji mamakin muryar da taji ba aka ce "Anty we re missing you plsss" a hankali tace "Really?" Ya marairaice yace "Yes Anty, good evening...." Ta kwantar da kanta jikin gado tace "Evening How you, hw is school today?" Yace "fyn Aunt" tace "Ina Sudais?" Yace "He is praying" tace "And what about you?" Yace "I just performed ablution now" tace "Alryt, Ina Mummy?" Yace "She is at the parlor" tace "And Nanny?" Yace "She is washing our uniforms inside d bathroom" tace "Alryt dear, I will cal back later, go and pray" yace "OK byeeee" daga haka ta katse wayar ta ajiye ta tashi ta fita xuwa kitchen jin ta fara jin yunwa, irish ta shiga peeling don ganin shi xai fi mata sauki, a hnkli ta leka window din kitchen din jin muryar da tayi a waje, xaune ta gansa kan kujera a part dinsa waya kare kunnensa, fuskar nan tasa bbu yabo bbu fallasa ya shafa beard dinsa yace "I missed you more...." Sai can kuma ya wara idanuwansa da ko kadan bata son irin su yace "Ohk when will that be?" Mikewa yyi bayan wani lkci yayi pick din flower a jikin ganyen dake shuke gun yace "Sure! I will be looking forward baby, when coming just let me knw" yana fadin haka ya juyo suka yi ido hudu don haske ne sosai gun kamar rana snn wutan kitchen dinta ma a kunne yake, ta hade rai sosai tayi saurin dauke kai ta bar jikin window din, bbu wani walwala ta karasa abinda take tana yi kuma tana saton kallon window ga faduwa da gabanta yake taga ya bar wajen, har dai ta fice kitchen din bayan ta gama girkin ba don ta gyara ba. Yau alhamis throughout bata da lectures tana gida idan ta gaji da karatun ta kwanta, in lkcn sllh yyi ta tashi ta yi, tun takwas din safe ta lura ya fice gidan, hudu da kusan rabi aka danna bell dinta ta dago da sauri sanin bbu wanda take expecting a lkcn, Vanessa bata ce mata xata xo ba, ta fi minti daya rike da kirjinta da ya wani amsa kamar an soka mata abu mai tsini, duk da ba sabon abu bane hakan a gunta amma ta dade bata ji hakan ba sai xafin yyi mata yawa, jin an kuma dannawa ta dago a hankali bata dai ce komai ba, har dai taji xugin ya lafa sosai, ta mike da kyar ta isa gun kofar a hankali tace "Who's there?"

✨ *Noor Al-Hayat*✨






_By Khaleesat Haiydar_📚✍🏻






3.....

Muryar mace taji tace "Sorry for intruding Madam...." Jigum tayi na d'an lkci kafin ta bude kofar tana kallonta, baturiyar matar tace "Good evening...." Ta gyada mata kai tace "Same..." baturiyar tace "I am Clara Edward" a takaice ita ma tace "Khadijah Muhammad" Clara ta mika mata textbooks din hannunta tace "Can you please help keep this for you Neighbor? I mean Dr Ayman..." D'an buda ido Khadijah tayi ta girgixa kai da sauri tace "Of course noo, you just wait for him, I think that will be better" Clara tayi murmushi tace "But he said I can hand it over to you, I just gave him a call now..." kallon litattafen na tsaya yi gabana na faduwa, Clara tace "Yeah, i am travelling today, and i can't go with his material" Khadijah dai ba don ranta ya so ba ta karba, Clara ta mata godiya ta juya ta wuce, Khadijah ta rufe kofarta, nan kan kujera ta ajiye books din a parlor. Ta fito daga wanka misalin karfe takwas da wani abu aka danna bell, tsaye tayi da mamaki tana tunanin to waye kuma wannan, jin an sake dannawa ta xura Hijab ta fito parlor tace "Who?" Ba a ce komai ba hakan yasa taki karasawa, ga xuciyarta da ya fara bugawa, aka kuma danna bell din, dakewa tayi tace "Who's there?" A takaice taji muryarsa yace "Somebody, open right away" mamaki ya cika ta sosai har lkcn kuma xuciyarta bai daina bugawa ba, tayi karfin halin cewa "So? What did you want from me?" Yace "Open now" A fusace tace "Did you miss ur road!" Yace "Did you knw I can open the door my self?" hankalinta yyi mugun tashi, kamar xata yi kuka tace "And did you know I can also report you to the police right away" cikin tsigar rainin hankali yace "Ohh really? ohk then, let me get the door open for u so you can have ur way to d police" baya ta koma da sauri cikin rawar murya tace "Plss stay away from me, I don't knw you" hawaye cike idonta ta kare maganan, shiru bai ce komai ba, har ta fara tunanin ya wuce ne tana nan tsaye dai kamar an dasa ta don ta dade bata shiga tashin hankali irin na lkcn ba, can cikin husky voice taji yace "Then.... I want to get my reading materials from you" da sauri ta kalli textbooks dinsa da ta ajiye daxu, gaba daya ta mance da su, ta hade rai kamar yana ganinta tace "Sorry, i can't open my door now, you'll get it tomorrow at ur door step" yace "You must be joking, wil u get that door open and hand over my property to me" mamaki ya cikata tace "Sorry I can't" yace "This is serious" juyawa tayi ta koma kan kujera ta xauna, sai dai fa gabanta faduwa yake, bayan kusan second talatin yace "Look I am having exams, and I need those books" banxa tayi masa, a hankali taji yace "Alryt... Plss" shiru ta yi tana naxari d'an ita gaskiya tsoro take, can tayi tsaki ta kwashi books din ta nufi kofa, gabanta sae faduwa yake ta bude a hankali tana karanto addu'o'i a xuciyarta, tana bude kofar taji ya cafko ta, ta yi wani ihu ta saki books din hannunta jikinta na rawa, ya rungumota firmly har tana iya juyo numfashinsa, turasa ta shiga yi hankali tashe ta dinga cewa "Let go of me...." ya ki saketa yana kallon kwayar idonta fuskarsa daure yace "Isn't this what you're afraid of?" Yatsine fuska yyi ya turata yace "I am waiting for the police" daga haka ya duka ya kwashe books dinsa, tuni ta shige ciki dai dai lkcn da ya mike tayi banging kofarta ta sa lock, ya ja baya da sauri yace "Damn it.....

1 Comments On NOOR AL HAYAT
avatar
hauwau-8-3

1 year ago

Reply

Pls inason novel dinnan cplt

Please Login or Register in order to submit comment