Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bashi yake nuni da dole saitayiba Allah bb yanda bayayi hakan ya k'ara kwantarwa da Raihana hankali har take ta tuna baya tace to shiyasa batajin sha'awa har Allah ya kare mata ita da fad'awa tarkon samarin zamani take tatafi sujudush-shukri tayiwa Allah godiya, dan tasan ba mastala bace domin nassoshi da dama sunzo akan yuwuwar rashin fara al'adar mace akan gab'a, "Raihana ta tashi ka'in da na'in bata tab'a boye musu komai na harkar addini tayi yak'i dajin kunya a mastayinta na Uwa kuma Malama. Dan aganinta b'oyewa yaranka abubuwa musanman na harkar Addini Sam bata tasoba gara tin kafin abin yahau kansu kisanar dasu hakan zai basu damar da sunga alamar Balaga kezasu fara nema dak'arin bayani kuma kin d'auko hanyar da har'abada ba zasu tab'a b'oye miki sirrinsu ba ko wani abinda ya shige musu duhu Ke zasu fara tambaya kafin abokansu,kinga daga nan kin kulle k'ofar shawarar su da kowa saike Mahaifiya!!!, a wnn lokacin Raihana tasanar daTwins duk irin nauyin da hak'k'in Allah daya hau kansu. Snn hatta da yanda Ummul khair zata saka Pad(Always) ko(k'unzugu)saida Raihana ta nuna mata takuma gwada saka mata ta gaya mata duk bayan awa 3taje tacire hakan zai kareta daga kamuwa da Effection kuma karta sake ta dinga yarda ita ashara har sai tasaka aleda cikin leda snn ta yar Raihana tad'ora daka da da dinga starki da ruwan sanyi; ,a wnn lokacin Raihana shafi d'aya takeyi musu k'arin karatun Al'k'ur'ani Wanda yake zama daran kuma subiya mata roi-roi ga'iya k'ira'a ga iya futar da k'alk'ala da makharujul huruf gaskiya dai sai Sam barka wata rana Twins suka damu dasuje gurin Daddynsu a rana kun week end su dawo on Monday Raihana dakyar ta barsu, Abbas yy mamakin yadda yaga kooomai nasu yacanza dukda yana zuwa ganin su amma baya kaima 30min ya tafi sai gashi awuni d'aya sun mutuk'ar burgeshi sunk'ara shiga ransa suda Mmnsu hakan,yasashi yunk'urin komawa Islamiyya dan kar wata rana suk'ureshi. Sann kodan yak'ara kwarjini aidon Raihana idan taji yana d'an jefo Hadhisai da Ayoyi idan yafara zuwa zance dan yasan bb yadda za'ai tafara da mai ilimi snn ta k'are da jahili inaaaa aitun kafin wani mai ilimin ya kyallo ta tamak'ale masa kamar wancen k'aton gara nasan abinyi duk da ba duka ne masu ilimin ke'aiki dashi ba amma zaiyi wuya tana da iliminnan haka ta'auri jahili ko masu jigari-jigari irina saidai K'addara gaskiya "Raihana kuwa a yanzu bb maganar aure atare da'ita illadai taga burinta ya cika Twins sun zama Hafizai dukda irin mastin lambar da take samu a gun Mama da Dr Karima ammafa da suka lura munufarta da hujjojinta sunfi nasu yasa suka kyaleta suka kuma bita da addu'a dan cimma burin ta, dan sunyi tunani ko'Auren suka tilasta mata tayi da koma waye ba zata tab'a samun nustuwaba dan raba Abbashe ta zatayi balle su'ayanzu duk kaninsu basu da buri illa ta'auri Abbashe:::!!!!









AMSAR
MMN 3G





AMSAR💕
MMN 3G💕
[1/31, 9:26 AM] SARATU: ___*🍂BIYU BABU...!🍂*_
_SAMU DA RASHI..._
🍂🍂🍂
🍂🍂
🍂

_*AɭKAɭAMƖŊ✍:SARATU MUNZALI*_

_*(AMSAR💕)*_
_watpadd @ Ssaratu75..._

*dedicated to:AUNTY ZALY YOLA ( MMN AHMED)

Na sadaukar da wnn peg gareku y'an k'ungiyar AREWA WRITERS ASSOCIATION (Arewa ginshik'in Al'umma)Allah yaka'ara bunk'asa mana wnn k'ungiya ya k'ara had'a kammu, Allah kasa k'asar Arewa tayi alfhari damu aduniyar marubuta

*AREWA WRITES ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{arewa gin shiƙin al'ummah}💦*
_________________________________

https://www.facebook.com/104534761033461/posts/104535871033350/?substory_index=0&app=fbl

*BISMILLH RAHMANI RAHIM*
*P______26* 

____________📖Dr Karima tana nan tana fama da ciki Wanda yake haifar mata da mastaloli, akan dole tace sai sun dawo gida NIGERIA dukda irin kulawar datake samu wanda ba'irin nanan bane, amma ita tasan da alama akwai wasu sinadarai datake kwad'ayi wanda bbsu acan dan haka tata kura saida suka had'a kayansu dan tahowa, Dr Karima sauka tace dan Allah yawuce da'ita gidansu.amma Ahj Tijjani yak'i yace dole tafara zuwa gidanta tahuta snn tasauke masa gajiya idan yaso saiya kaita koda daddarene

Ab'angaran Ango Alh Saddam kuwa Mama tanan tana shan tarai-raya kala-kala

Haka shima Mama tana bashi kulawa sosai tana kima girmama shi da mutuntashi  sunadai kula da sauke hak'k'ok'in juna daidai gwargwado gakuma raya Luv dasuke agefe guda irinnasu na dattijai,

Abisa siyasa Mama ta bashi shawarar ya kamawa Hajja gida ya kuma samar mata y'an aiki suna kula da'ita zai samu lada karyayi duba da halayenta kuma yadena tuna baya akan abinda tayi masa tunyana k'arami yazamo mai yafiya dayin sakayyar alkhairi ga wanda yy maka sharri,

Alh Saddam yj dad'i shawarar warinda ta bashi kuma yad'auki d'amarar aikatawa,
. "Raihana murna da farincikin ganin Dr Karima abun baya musaltuwa " haka agun Mama da sukai waya akan za tazo gobe, Raihana sun tattaunawa sosai aranar kamar karsu rabu, Raihana tahad'o mata kayan kwari iri-iri harda yimata d'an malele "Dr Karima ta jidad'i sosai har mamakin yanda akai Raihana tasan abunda take muradi kenan, " ab'angaran Abbas ya jir jice a islamiyya baya fashi, dayaji hadith karaf zai haddace musanman wanda ke magana akan zaman takewar Aure "A washe gari Raihana da Dr Karima suka had'u agidan Mama sunsha hira sun more kayan da'd'i,wanda Alh Saddam yasa akai musu namu samman Mama ta k'ara taso da maganar Auren Raihana. tace tafi son ta staida wanda take so yadda dazarar anyi saukar Twins itama ad'aura mata Aure" Dr Karima tad'ora danata danuna gamsuwarta da'abinda Mama tace"Raihana kuwa ta cika tai bam, da Mama taga bata da niyyar basu amsa saitace ta yanke mata nanda wata2idan har bata staida mane miba to'ita zata stayar mata "Raihana tad'auka da wasa Mama take sai bata wani d'auki maganar da serious ba dan ganin ai Bazawara ita take zab'arwa kanta Miji kamar yadda Addini ya bata dama " haka suka gama shan hirarsu,Raihana ce itada suka fara tafiya gida inda Abul khair ke jansu. Anan Mama suka k'ara samun damar k'ara tattaunawa akan hanyar da zasu b'ullowa Raihana sunata Complaine akan yawan masu zuwa neman Aurenta kama daga kan mak'otansu zuwa wasu daga cikin abokanan Nazifi sai wad'anda suke gayawa Alh Saddam amma duk tak'i basu dama gashi sungame irin kora da halin da Twins suke musu muddin sukaji gunta akazo basa tab'a bari taji balle taje har maigadi suka korawa warning akan duk wanda yazo nemanta yace tabar garin,!!!"sai Mama tace zancen banza kenan basason tayi aure saidai tayita zama ds ai kuwa bazai yuwuba"Dr Karima tace waisu nan kishinta suke basa son kowa ya'aureta sai uy6y6u Abbas "Mama tace hmmm ainima bakiga irin naci da zaryar dayake miniba kullum tunda nazo gidannan ya bani hak'uri akan abinda yy yafi bb adadi,yanzu kuma yakoma magiyar dole saina saka baki acikin lamarin idan ba hakaba to wllh zamu rasashi ,Ahj Saddam yyta masa fada ranar yace ai dole sai tana sonka zaka Aureta ." Dr Karima tace ni wllh banga amfanin wnn delay d'inba aiyanzu yagane kurensa yy nadama ai itama Raihanan yin Auren shine mutuncinta da namu nawa take kwatan -kwatan ta kawai dan k'addara tagifta mata amma a'irin Auren wann zamanin ai baici tahaifi kamar wd'nn Twins ba, Amma gaskiya Mama keya kamata kifara shigo mata da maganar Abbas ahankali dukda nasan zaiyi wuya ta'amince amma Aurensa shine babban rufin sirinta da namu,"Mama tace kwarai kuwa inba shid'inba uban wad'annan y'ay'a wazai iya Aurarta taje masa dasu, idanma uban zata barwa tasan irin tarbiyyar matar? "Dr Karima race ai wllh Mama Raihana bama zata tab'a bari yaran nan suk'ara nisa da'ita ba saidai nisan Aure wanda daman tasan ya zama dole,ina zata iya barwa wata matar ubansu bayan irin wnn wahalar da tasha wajen gyaran rayuwarsu," Mama tace tohh Alhamdllh kinzo gab'a inda nake taso kizo shikkenan yanzu munsamu kwakwkwarar hujjar da zamu b'ullomata dashi danta yarda ta'auri Abbas d'in. Indai ta nuna batasan sa , sai Muce mata to tabashi Twins dan bazai tab'a yadda y'ay'ansa suyi Agolanci ba_,Dr Karima tace aikuwa Mama kinyi da bara wllh kina da fikra aike Raihanan tabiyo gashi suma Twins albarkar fresh brain tasa mesu. Suka saka dariya atare, Mama tace aiki kyaleta badai saura nanda wata uku saukar tasuba Allah dai yakaimu ai insha Allah tare da d'aurin auren za'ayi rana d'aya,Dr Karima tace Allah ys ainaga alama Alh Saddam ne yake k'ara tirata, Mama tace ehh mana aizanmasa maganar yabarta a hannun mu ,"wace maganar zan bari ahannun uwargidana kuma Amarya ta tahar abada,da Sauri suka rusuna suna dariya had'e da yimusu barka da zuwa,Ahj Tijjani yace hajiya da fatan kin lallab'amin tawa Amaryar? "Ahj Saddam yace dukkan su Amare waye zai lallab'a wani?kaima idan banda Abinka baka ganin ba'ita kad'aibace aidole,kowa yabi min ita a hankali, kunya duk tabi ta lullub'e Dr karima kawai tasun kuyar da kanta "Mama acikin hikima da dabara ta fara fahimtar ds duk irin shawarar da suka yanke da kwararan dalilansu" Ahj Saddam yaji mutuk'ar dad'in hakan kadan d'an nasa shima ya samu nustuwa amma sai bai bayyana ba ya nuna k'in a mince warsa saidai,lalle abar Raihana ta zab'i san zuciyarya, saida kyar Ahj Tijjani ya shawo kansa. Nan suka shafa dayin addu'ar Allah ya tabbatar ms da duk abinda yake shine mafi Alkhairi ,,"Raihana tunda suka iso agajiye take dan tabiyewa Twins lalle sai sun'biya gurin Training tayi sunata stokanarta wai ta fara zama Ajibo,,suna shiga get ita ta fara futowa tanufi cikin gida bata wani jira su sutafi tareba kawai sotake tajita akwance tana fad'awa falon Twins suka tafa harda shewa"Raihana gadan-gadan tanufi d'akinta bata an karaba saijinta tayi low www tamkar an shatalo k'afarta idanunta tuni ta damkesu jira kawai take tajita tananu a k'asa abin mama ki saijinta tayi a hannu tamkar jaririya. kuma tunta a saitin wata k'asumba bb shiri ta Ware idanuwanta tar-tar sai gasu akan!!!
AMSAR💕
MMN 3G💕
[1/31, 9:28 AM] SARATU: ___*🍂BIYU BABU...!🍂*_
_SAMU DA RASHI..._
🍂🍂🍂
🍂🍂
🍂

_*AɭKAɭAMƖŊ✍:SARATU MUNZALI*_

_*(AMSAR💕)*_
_watpadd @ Ssaratu75..._

*dedicated to:AUNTY ZALY YOLA ( MMN AHMED)

Na sadaukar da wnn peg a gareki a wnn karanma UMMIHAFSA
Kindace dazama Popular na Pan's din BIYU BABU💃💃

________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*BISMILLH RAHMANI RAHIM*

*P______27*

____________📖Raihana tarufe idonta tak'ara bud'ewa ta tabbatar ba gizo Abbas yake mataba da sauri cikin hasala dad'aga murya tace dallacen Mlm meye kuma haka ta dira daga jikinsa tana karkad'e nata jikin tacigaba dacewa da'izinin wama kashigo min gidan mijina!!!? Snn akanme zaka tallafoni haka tamkar wata y'arka ."Abbas dai yayi kasake tamkar wani soko dakyar ya'iya bud'e baki yace kiyi hakuri ganinai saura kad'an kifad'i snn kuma nasan nayi kuskuren shigowa batare da'izinin kiba kidai kara yin hakuri banga mai gadi a wageba shiyasa nashigo kaistaye Abbas yakuma rusunawa yace Allah yahuci zuciyar sarauniyar mata yamik'a hannunsa yajanyo mata rigarta tak'asa ganin tad'age a sanadin tallafota da yayi"Raihana tak'ara kufula takufce rigarta had'eda jada baya tace wai lafiyarka kalau kuwa!!!?kaga fice min daga gida karka kuma shigowa dagayau kastaya iya mastayinka fuww tawuce cikin d'aki" "Abbas ko'ajikinsa hasalima dramar tasu burgeshi take nan yy sauri yabita Raihana tanajin alamar ana biye da'ita saita juyo basai taga Abbas astugune ba yayi gurfane kamar wani bafade yace dan Allah badan niba kid'an saurareni koda 5minute ne pls Madam ya daga hannunsa alamar begging!, Raihana take taji yatab'o lagonta  dahar taji yad'an bata tausayi amma saita dake tace har'abada bazan tab'a baka wnn damarba taja staki tashige d'akinta ta saka key" Abbas ko'ajikinsa dan daman yasan dole hakan tafaru amma yace aransa insha Allah zanjuri zuwa rafi can kuma saiyace anya yarannan ba k'afar rago suka had'amin ba yaza'ai suce min tana tausayi da saurin yin afwa gawanda yanemi yafi yarta ta'irin wnn sigar!!! Dafa kafad'arsa da''akayi shiya d'ago dashi daga tunanin daya tafi "Twins yagani sai dariya suke" Abbas yasha kunu yace kuzo nan "Twins sukabi bayansa har bakin get " Abbas yadubesu yace anya Twins wnn shawarar zata b'ulle kuwa anya!!!? Kamar jira suke yarufe baki sai cewa sukai kaga Daddy dandai agajiye take yau munsa tayi Training tasha wahala amma wllh Dad batama son taga an durk'usa mata at all "Abbas yace ohhh kukuka jawo min ashe toma waya aikeku dakaita gun Training Kawai dan kusa min ita ciwon jiki!!!?" Twin's suka kwashe da dariya sukace Daddy bakaga yadda Mum takoma ba?Tab " Abbas yace to koyaya tazama ina ruwanku ni'ahaka nake son kayata nake kuma son naganta dan haka wnnne last warning yarik'e kunnu wansu "Ummul khair tasaki k'ara tace Daddy baka cika mana Alk'a warinmuba sai punishment " Abbas yacika musu kunnen yace ta'ina zan çika alk'awari bayan bansamu biyan buk'ataba aikujira kawai nima nasamu yadda nakeso. "Ummul khair ta shagwab'-gwab'e tace habba Dad to'aimu munfita tunda muka baka good Aidia " shidai Abul khair yana gefe sai kumbura yake"Abbas saida yagama zolayarsu staf snn yace ok to kustaya muyi masa laha kunaji zanbaku alk'awarinku amma ga sharad'ina "da sauri Twins suka amsa yafad'a zasuyi indai zai basu abinda yayi musu tanadi" Abbas yalura duk sunkai bango a k'aguwa da kuluwa saiya tunstire da dariya yace kowan nenku saiyaje yayi mata Massage "duk suka amsa snn Abbas yabasu abinda yy alk'awari nan suka saki ransu harda dariya suka k'ara gayawa Abbas duk irin abubuwanda Raihana tafiso ayimata da haka har sukayi sallama " koda suka isa gida suna zuwa suka tarar da Raihana akashin gid'e da'alama ta'idar da Sallahne suka shiga da sallama a tare bayan ta'amsa musu duk suka shige toilet saida sukayi wanka had'eda Al'wala snn suka zazzauna kusada Raihana tad'ago da kanta tace ke khairan kiyiwa Allah kid'agani kinji jikina kuwa Allah jina nake kamar wacca tayi surfe"Ummul khair tace Mum kenan dande baki saba bane bari yanzu nayi miki Massage zakiji dad'i "Raihana tace inafa zan gamsu da irin wnn Massage d'in naki kamar kina susa " Abul khair yace Mum nizan miki daman aibata iyaba nafita iyawa tin dacan "Da mamaki Raihana tace tohh kai wa kakewa dahar kafita iyawa!!!? kafin ya bata amsa Ummul khair tace aimuna yiwa Anti Safna" Abul khair yace Ai kinsan masu Sickler suna ciwon jiki so Massage yana taimaka musu kumafa har Mashing d'in Massaging tana dashi da Daddy yasiyo mata amma Allah Mum bata hawa saitace muzo muyita mata "Ummul khair tace Mum harfa Daddy shima duk ma yafimu iyawa" Raihana tasaki baki tace ohh a gabanku yake mata kenan?"Abul khair yad'an tab'e baki yace ehh mana some times " Raihana ta girgiza kai ta jinjinawa al'amarin snn ta gyara za manta tace kunajina koda mahaifiya ba haramun bane amma duba da yawan nassoshi dasuka zo akan nuna rashin halaccin hakan daga lokacin da d'anta ya Balaga bai halatta tabarshi yadinga kai hannunshi jikinta ko'ita takai nata jikinsa ko kuma yarinya ta Balaga Uba yadinka kai hannunsa jikinta ko nata jikinsa ko'irinsu runguma ko musabaha ko jingina da juna ko zama dab-da-dab "Ummul khair tace Mum ai a littafin kulasa da kikayi mana akwai inda Annabi (saw)idan zai tarbi Nana Fad'ima yana yimata kiss(Sumba), Raihana tayi murmushi tace Ummul khair ai Annabi (saw)na dabanne komai nasa bashida gami danamu ,kaidin shaid'an bai tab'a tasiri a kansaba , saidai muma acikin mutanen ana samun k'alilan masu starkin zuciya wad'an da zasu iya hugging d'in y'arsu batare da komai ya d'arsu a ransuba, dan shed'an shine mak'asudin jefa duk wani mugunyar k'azamin tunani da sharri a cikin zukata saidai fatan Ubangiji ya k'ara starkake zukatanmu " dukda cewa kiss (Sumba) ba k'aramin dankon k'auna yake k'arawaba a stakanin iyaye da y'ay'a , koyarwace ta'ddini kuna sunnah ce'ta fiyayyen halitta(saw)amma anwayi gari turawa sun kankane ta stabar lalacewa da sakaci irinnamu waimu Turawan suke koyawa samples na yadda zamuyi amma kuma muma dukda halinmu bazamu iya yiwa y'y'anmu baba, waimu kunya, wasu kuma gida dancine sai sud'auka miji kawai ya halatta ayiwa,amma da zamu'iya aduk lokutan da yaranmu zasu tafi makaranta bayan kindafa kansu kinyi musu Addu'a saiki kama fuskar yaronki ko yarin yarki kisakar matashi a kumatu namiji kuma 'agoshi  koda daga aike suka dawo ko sukayi wani abun nabur gewa har kikaji dad'i to kishi Albarka snn k'aton Kiss ya biyo baya dole saimun daure muncire kunya da shiri-rita, dan wllh ba k'aramin shak'uwa yake k'arawa astakanin iyaye da y"y'a ko stakinin Mata da Mijiba "sallamar da'akai ita takai hankalin su gaba d'aya zuwa bakin k'ofa dan ganin mai shigowa" mai aikice tashigo d'auke da Tray da Cooler ta rusuna tace Hjy ko'akai kan Dining?" Raihana tace aa barshi anan Haula yau bazan'iya d'anewa a saman nanba Ummul khair zuba mana kai kuma Abul khair jeka kawo mana ruwa muwanke hannu,"Haula tace yabarshi zankawo kafin tamik'e Abul khair harya tashi yanufi kitchen yana kawowa Raihana tasa hannu zata wanke nan suka fara rifima kowa yace shizai wanke Mata dakyar Raihana ta sasan tasu akan Abul khair yaci girma idan suka gamaci saiya wanke mata      *Akwana atashi yau saura sati Biyu saukar Twin's inda Raihana ta gayawa Alhj Tijjani yayi musu jagora zuwa makarantar Tahfeez d'in dasuka Fara zuwa akai musu Interview Wanda ya basu damar shigar dasu cikin sahun d'alibanda zasuyi sauka a sati2 masu zuwa "Raihana shiri take k'in-da na'in Mama da Dr Karima tare da Mazajensu kuwa shirin biki biyu suke dan tuni Mama takira Raihana dan suyi zaman sulhu nak'arshe," Raihana tanata sauri take kiran Mama Wanda batasan kona meyeba daganan tanason  tawuce gurin masu yimata kayan rabo ! Tana sako k'afarta bakin get sukayi ido hud'u da Abbas "Raihana takautar da kanta tashige mortar Dr,Karima wadda tabar mata saboda zirga-zirga, Abbas yanufi bakin Motar YY Kneel down yace Dan Allah Raihana kitaimaka mi kibani aron lokacinki dan Allah Maman Twins," Raihana tace nagaya maka bazan tab'a iya amincewa buk'atarkaba garama kasan Inda dare yy maka kajecan wad'anda suka had'ani dakai suntafi Tahfeez saika bisu can "Abbas yace niba gunsu nazoba gunki Nazo Raihana kinfa sani Allah dakansa yace ASSULHU KHAIR   ,  " Raihana gaba d'aya Abbas ya kashe mata jiki Dan babu abinda tastana aduniya kamar taga ana Begging d'inta wann Abu yana Sosa mata ranta take,takejin rauni da tausayi sun bujiro mata amma  dazarar ta kalli Abbas takejin bakin ciki ya ziyarci zuciyarta take tarufe motar, tabar shi'anan. "Mama tahad'a bataliya Dan zaman k'arshe dazasuyi da Raihana idan har a wann karan tak'i amincewaAuren Abbas to tabbas zasuce   tabashi Twins zasu nema masa mata tacigaba da zama dasu " Raihana tana hanya tana kukan bak'inciki,gashi yazo da k'ok'on bara gashi bazata tab'a iya taimaknsa akan wann buk'atarba Raihana  bata tab'a cinkaro da maineman taimako al'ahalin tana dashi batare data taimakaba koyaya  sau tari idan bata da'abin dazata IYA taimakawa takan dad'e abin yana damunta ,_Awan nan tunanin ta'isa tayi parking Motar a get snn,tashiga cikin gidan da sallama babban abinda yabawa Raihana mamaki,shine ganin yauma Mama takuma had'a mata jama'a kamar rannan dad'intama babu bare, da fara'a kowa ya'amsa mata tarusuna ta gaida kowa d'ago kan dazatayi saitaga Abbas, harta mik'e tags Mama nayi mata,nuni da shima ta gaisheshi " Raihana taji bbu dad'i amma tadubi umarnin Uwane snn kodan darajar mahaifinsa dake gurin aita mutun tashi sai ta kalleshi tace, Ina wuni,bata jira amsar saba tamik'e ,ba Abbas kad'aiba hatta da Ahj Saddam da Ahj Tijjani saidata burgesu "Mama tace inakuma zaki? aizama zakiyi dukkanmu ke muke jira" Raihana wadda daman akusa take nan tafashe da kuka mastananci ttunkafin taji maiza'ace "Mama haushi yakamata tace wnn wane sakarcine!!!?? Dan kinga muna lallab'aki ehh, to bari kiji wnn ne zama nak'arshe mekika yanke shawara!¡!? , " Raihana cikin kuka tataso tarik'e k'afar,Mama tace,Dan Allah Mama bana s.  ,"kafin tak'arasa Mama tace ya'isa nagane Inda kk dosa, to bari kiji munyarda bazakiAure shiba to lalene kidawo masa day'ay'ansa " ad'imauce Raihana tad'ago tace Mama a wnn karanma zaikuma sanadin rabani da y'ay'ana!!!? Mama tace y'ay'ansa dai!!! "Ahj Saddam yace kinga Hjy Abbas yayi saurin tarar numfashinsa bayan yamasta kusada Raihana,yayi gurfane mai had'eda goho cikin shek'ar kuka Wanda yakasa bashi dama yy magana duk mairauni zai tausayawa Abbas balle Ahj Saddam dayakejin zafin futar sautin kukan d'an nasa,it a kanta Raihana,b'arin zuciyarta tatausaya masa,amma idan tatuna itama haka yagwada rashin imani da rashin tausayawa akanta saitaji tak'ara stanarsa. cikin nata,sugar kukan dayafi na Abbas ban tausayi tad'ago ta kalleshi ido cikin ido Wanda yy sukayi jawur dukkansu ga hawaye dake tafaman zirara acikin na kowan nensu tace wllh ka cutar dani, ka zalunceni,tanason tak'ara wata maganar amma muryarta ta dashe dakyar take futa. Dan sautin kukan yafi k'arfi snn tacigaba dacewa kuma dukda haka alhakin bai'ishe kaba yan zuma kana ik'irarin kuma rabani dasu duk saboda biyan buk'atarka da sssankai ta k'ara fashewa da kuka itakanta Mama jarumta take amma kukan Raihana yana Sosa ranta kawai Dan tasan tana hango mata abinda zaifi zama mata alkhairi arayuwarta mai d'orewa,insha Allah" Abbas yy ta maza ya k'ara mastowa dabda Raihana ya jajirce zuciyarsa Dan,wani irin mugun bugawa take ya kamo hannuu wan Raihana ya damk'esu acikin nasa,dukda irin k'ok'arin datayi wajen kwacewa amma ina,ruk'onna Abbas babu sauki tinkafin yafara magana hawayen daketa kwaranya a fuskarsa tuni yajik'a hannayen Raihana yace nima gashinan haryau ina fuskantar sakayyar zaluntar danayi miki idan baki yafe minba me Uk'ubar Allah akaina zai k'areki dashi!!!?yasa hannunsa Yad'ago da fuskarta Wanda tinda ya fara maganar take a sunkuye hawayene kawai yaketa ambaliya "Raihana koda yad'ago fuskarta bata bari ta sake had'a ido dashiba" ganin hakan yasa Abbas Kiran sunanta awata irin siga mai tada stigar jiki Reaihaa naa ko kinason kiga mahaifin y'y'anki ya tagayyara ya tozarta ya wulak'nta a duniya saboda hak'k'inki!!!? Ya saki d'ayan hannunsa daga cikin nata ya durkusa gwiywo yinsa a dab da nata, ya d'aga hannu wansa ya had'esu wash sababbin hawayen masu d'umi suna k'ara sulalowa a kan fuskarsa yace Raihana dan darajar sonda kike yiwa Allah da Manzonsa da iyayenki da y'ay'anki Raihana kitai makeni ki yafemin kuka yaci k'arfinsa amma saida yak'arasa yace Rrrraiiihha kar kibari duniya ta shata min layi kamar yadda tasha tawa Hajja da Y'ay'anta Dan Girman Allah Raihana ya kwanto da kansa kan k'afafuntaina k'aunarki ina masifar sonki Raihana wllh tundaga ranar dana fara nadamar aikata lefina "Ahj Abbas tuni tausayin d'ansa ya sashi zubarda hawaye,Wanda hakan yasa yakasa jure gani ga haushin Raihana daya dinga bujuro masa kan tak' yafewa d'annasa bayan kowa yasan ba halinsa bane k'addara da rabon wad'annan y'ay'ane hankalinsa ya tashi ransa ya b'aci ainun,Dan baitab'a ganin kikan Abbas arayuwarsa irin na yauba jiyake sautin kukan tamkar ana babbaka zuciyarsa (Hmmmmm d'ad'a zuci kenan gobarar mahaifi) take ya mik'e ya funcuko hannun Abbas a zuciye jiyake tamkar ya rufe Raihana da duka ", haka itama Mama takeji a wnn karan,dan taga alamar Raihana tazama maras imani da tausayi ko'ina takoyi wnn kafiyarma oho mata" Ahj Saddam yace Daddy taso zo gaji " Abbas bashida zab'i haka ya mik'e jikinsa a sake duk ya jik'awa Raihana jikin siket d'inta da hijab d'inta da hawaye da Majina

AMSAR MMN 3G
[1/31, 10:13 AM] SARATU: ___*🍂BIYU BABU...!🍂*_
_SAMU DA RASHI..._
🍂🍂🍂
🍂🍂
🍂

_*AɭKAɭAMƖŊ✍:SARATU MUNZALI*_

_*(AMSAR💕)*_
_watpadd @ Ssaratu75..._

*dedicated to:AUNTY ZALY YOLA ( MMN AHMED)*

________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*BISMILLH RAHMANI RAHIM*

*P______28*

____________Raihana dakyar ta'iya
d'ago da kanta, ta wai-waya inda Alh Saddam yanufa da Abbas, tace Na yafe maka!!!, cak Alh Saddam da Abbas suka staya, wani irin mamaki da farin ciki ya mamaye zukatan su, "Mama ce tafara cewa Alhmdllh sai Alh Tijjani yace Masha Allah, " Dr Karima ta taso ta rungume,tace insha Allahu hakan zai zamo miki Alkairi a rayuwarki gaba d'aya kiyi hak'uri dan nasan ba'asan ranki ba , "Alh Saddam ya dawo da baya, rik'eda hannun Abbas yazo dab-da Raihana ya kamo hannunta ya had'a dana Abbas yace Allah ya shimiki Albarka,snn ya dubi Abbas yace Daddy ga'amanar Raihana nan Allah ya tayaka rik'o, " Raihana duk wnn budurin da'ake kanta yana sukuye kuma har yanzu hawaye bai daina zarya a fuskar taba,"Abbas yace insha Allah

Please Login or Register in order to submit comment