Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wanka ta shiryasu staf, ahaka tashin fidesu dan duk sunyi barci.


RANO

" inna nagama,cewar Karima!!!
"Toh ganinan nima, ina Raihana?
" KARIMA tace hmmm ai naga sai faman nawa take kamar bata son tafiyar.
"Inna tace hmmm, Allah ya kyauta,
" Raihana ta kammala tafito, tana ganin su astaye alamar ita kawai suke jira kawai saita fashe da kuka...
"A tare inna suka hada ido itada karima, lafiyarki kuwa? Inji inna,
" Raihana tace acikin kuka dan Allah kuje ku kadai, Wllh in dai na biku nagama yawo, babana yanajin abinda yafaru shi kenan na mutu,
"Karima tace to waishi ba musulmi bane da bazai d'auki k'addara ba? Aike dolen save ba yadda zaiyi, idan hannuka ya rub'e aiba zaka fire kayarba,
" inna tanisa can,sai tace kinga karima kyaleta ga duk kan alamu akwai abinda take gudu, wanda mu bamu saniba, kawai yanzu mutafi muje acan zamu fahimci komai, idan, takama mu fad'awa iyayenta idan kuma mukaga da mastala saimu dawo.
"Da gudu Raihana ta fad'a jikin inna,
Acikin shek'ar kuka tace Inna
Kawai kufadawa mamana tazo nangidan, daga nan sai afad'a mata komai, nasan wllh hakan zaifi.
" karima tace to gaya mana address din,
"Nan Raihana ta fada musu cikakken yanda zasuje garinsu.
" inna tace koda mun samu mastala ga wayata nan ki rik'eta a hannun ki saimu kira kik'ara yimana bayani,
"Raihana takarb'a, snn tayi musu Allah yakiye.



BICCI

" inna da karima sun sauka a k'auyen bicci lfy, kuma Sam basu wahala wajen samun gidansu Raihana ba, saboda sunan kakanta ta gaya musu dan tasan fitac cenea.
Har zasu shiga gidan Inna tatuna basu tambayi Raihana sunan maman taba, a take karima takira number Inna, tafada
musu.
"Suka shiga da sallama, gidan acike yake da yara, da matasa, da samari, ga iyayen su mata, Wanda da alama iyayen maza basanan, nan aka tarbesu hannu bibbiyu da kulawa, aka kawo musu ruwa, kunun zak'i harda fate, sukaita godiya.
" Inna saida suka d'an tab'a, snn sukai sallar azahar, daga nan inna tace dan Allah munzo gurin Rahmatuy,
"Nanfa suka d'au kuwa da sabuwar murna, dan suna tinanin marik'iyar Raihana ce daga birni,
" su kace wllh bata nan amma kujira dan tana kan hanya,
" inna tace aa zadai mubar sallahu, saboda, daga nesa muke, ba zamu iya jiraba.
" suka mik'e nan karima ta rarra bawa yaran kud'i , suna ta yiwa junansu godiya har suka futa.
"Suna futowa k'ofar gidan Inna tace karima yanxu haka zamu koma, gashi min manta bamu basu sallahu ba, koda number wayar Kice da sai mubasu su bata idan ta dawo.
" Karima tinda inna ta fara magana hankalin ta baya gun inna, tana can kallon wata mata dake tahowa, tana nufo inda suke, karima tai shiru snn tace, inna kinga...!!!
Kinga waccar matar , anya ba'ita bace mmn Raihana, dan gaskiya kamarsu tayi yawa.
"Inna tace kwarai kamar anstaga kara, sai dai tafi raihana haske sosai,
Tana isowa gunda suke, tai murmushi Wanda yak'ara bayyana furowa da kaman ninta da raihana, tace sannunku, bata jira amsar suba ta wuce,
" cikin sauri karima ta rik'o hannun ta, tace yawwa baiwar Allah, dan Allah ko kece RAHMATU?
"Cikin dariya tace ehh niçe, daga ina kuke?
Dan naga alama bak'ine Ku.
Inna tace kwarai kuwa, daman gurinki mukazo akace mana bakyanan, har munfito ma zamu tafi.
" Rahmatu tace Allah sarki sannunku toko zamu koma ciki?
"Cikin sauri karima tace aa ai munriga munyi sallama, da dai munyi magana anan ba komai,
" tace to shik kenan.
"Inna tace baiwai Allah daga Rano muke,
Ko kina da y'arda ta tab'a b'ata?
" Rahmatu tace ehh,amma mun fiddarai da'ita, mun k'addara tamutu, atake ta shiga cikin wani yanayi.
"Inna ta fahimci hakan ya bayyana akan fuskarta ,kawai sai tace, to kudai mun stinci wata yarinya, amma bamu da tabba cin ko y'arkice,
Idan babu matsala mai zai hana kizo kiganta?
" Rahmatu cikin zak'uwa tace ai saina biku koyanzu ma,
"Karima tayi murmushi tace aa mama baza'ai haka ba, kinga saboda iyalanki kar suga munzo ba shiri muntafi dake.
" Rahmatu tasan halin y'an gidansu, gashi kuma megidanta bayanan bare ta nemi izini, hakane yasa batai musu ba, sai tace to kubani kwatan cen gobe insha Allah zanzo, cikin sanyin jiki tafada,
"Inna tai mata cikakken kwatance, sannan karima tarubuta mata number wayarta, sukai sallama





" K'arar sauti wanda ya kauraye gidan,
Da farkon hajja bata zata acikin gidansu bane, saida yaji tabbas muryar Dr Hanna ce, snn ta mik'e cikin sauri, ta nufi d'akin ta,
Hajja tana shiga taga Dr Hanna acikin tashin hankali, kawai fad'i take hajja Raihana Raihana bata mutu ba look at her kinga.….!!!







AMSAR💕
[1/31, 8:54 AM] SARATU: ___*🍂BIYU BABU…!🍂*_
        _SAMU DA RASHI…_
               🍂🍂🍂
                 🍂🍂
                     🍂

      _*AɭKAɭAMƖŊ✍:SARATU MUNZALI*_

           _*(AMSAR💕)*_
        _watpadd @ Ssaratu75…_

*dedicated to:AUNTY ZALY YOLA ( MMN AHMED)

*AREWA WRITES ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{arewa gin shiƙin al'ummah}💦*
_________________________________

https://www.facebook.com/104534761033461/posts/104535871033350/?substory_index=0&app=fbl

*BISMILLH RAHMANI RAHIM*



P___9

____________📖Kee Hanna lfyrki k'alaw kuwa? Wace irin raihana...!!
Kinga tashi bud'e idonki, ba kowa anan, yarinyar data riga ta tamutu kuma,
Dr Hanna tayi firgigit....
Ta bude idon ta, tajanye k'aton bargon dake lullube a jikinta, tamike staye cak..
Gaba dayanta ta firgice, hajja dan Allah bakiganta taba? " hajja tace kai kai Hanna sai kace wata k'aramar yarinya, mafarki kikayi wanda har abada bazai tab'a zama gaskiya ba, dan Wanda ya mutu ya mutu, zauna nan bari nayi miki hayak'i, hajja tamik'e tajawo wata drower tad'auko cold ta kunna, bayan tad'orashi akan kasko, tajuya gun Hanna,wacca take ta zare ido, tace bari ina zuwa, zunbur hanna tamik'e tace to muje, hajja ta gane storon takeji har yanzu, kawai tace to muje, tadauko kaskon sukayo k'asa d'akin inna,
"Hanna tana biyeda hajja zunguy zunguy...
Har inna tad'auko wata Leda, tahada da wancen ta rage ta wancen, hardai ta gama, ta cewa hanna zauna, ba musu ta zauna, inna ta lulluba mata zani ,sannan ta shiga da kaskon, ta nata barba'da iccen, kafin second hayak'i yatir nik'e d'akin, banda tarinsu babu abinda kk jiyowa,
" Hanna da sauri ta yaye zanin, dataji numfashinta yana season, tafito parlour aguje, habba habba hajja, mene wann? Ta fad'a cikin shak'ewar murya...
"Hajja tace hmmm ai yanzu zakiji garau,
" Dr Hanna tace ni dama addu'a r nan ta storata amarki kk tina min nayi, amma wann hayak'i haka.. Tana fad'a tayi hanyar komawa samanta,
"Hajja tayi wata irin shaidaniyar dariya, tace ai kinji garau dole kinemi da addu'a na baki, kema da kikaje islamiyyar aka koya mk kin manta, balleni da ban tab'a had'a hanya da'itaba, tak'arasa maganar tana staki.
Dr Hanna tunda takoma d'akinta ta fad'a toilet,kawai mafar kin da tayine yake dawo mata, amma Sam babu storon yanzu , saidai razani acikin zuciyarta, wanda take ta maimaima inaa inaaa aiba tatafi kenan, she's gone forever.



RANO

" Yau take lahadi daidai da 18 Rabius sani shekara alif 1441/daidai da 15 December 2019.

"RAHMA ta sauka agarin rano, Wanda tad'ansha wahala kad'an kafin ta gane kwatan cen, duk da tahd'a da tambaya, amm kasan cewar bata tab'a zuwa ba yasa ta kasa ganewa da wuri,
Misalin karfe goma na safe, Rahmatu ta'iso unguqar, tambaya d'aya tayi, aka nuna mata hanyar gidan, ta'isa agajiye, tayi sallama shiru, ta kumayi, nanma shiru, saita k'arasa soro na biyu, anan taji ana hira sama_sama, tak'ara murya salamu alaikum...
Amsa sallamar da'akayi yasa Rahmatu saurin afkawa cikin gidan, saboda sautin muryar da tajiyo,   tana shiga sukai ido hudu da Raihana, ai kuwa ta daka wani uban stalle mai  had'e da ihu, maamaa...!!!
" tayi gunta da gudu ta k'an k'ameta,
"Inna da karima banda murmuahi babu abinda suke, daman basu gayawa raihana sunyi da mmnta zata zoba, sunce Mata dai basu same taba, amma sun bar sallahu.
" Rahmatu ta d'ago ta, cikin kuka tace Raihana daman zan kuma ganinki? Kullum addu'ata ubngj yahad'a nidake a daarussalam, idan kuma kina raye Allah ya baki kariyarsa, da kulawarsa agareki, lalle ubngj samiy'ud du'aa'u ne,
"Raihana tasa hannu tashare mata hawayen tace mama... Wllh ban tab'a minti 10 cikakke bantina kiba, nayi kewarki sosai mamata, takuma fadawa jikinta,
" Inna ta masto kusa dasu, tace Raihana zo kibari ta d'an zauna ta huta,
"Acikin murmushi mai had'eda kuka Rahmatu ta janyo Raihana ba tare data raba jikin suba, tazauna akan tabarma,
" karima tad'auko ruwa mai sanyi pure water ta kawo mata akan plet,
"Rahmatu a atake ta shanye guda biyu,
" inna talura da Hakan yasa ta cewa karima ta d'auko mata abinci a kula, da plet da spoon,
Ana kawo mata, da sauri Raihana tad'ago tace ahh...,
Inna kikace wnn bana manyan bak'inki bane? Ta fada cikin mmki,
"Inna tace kwarai, to ai itace babbar bak'uwar,ta k'arasa fad'a tana hararar Raihanan,
" Rahmatu ba tabi takan spoon d'in ba, ta wanko hannunta tafara cin abincin,
" Inna sai daga ta gamaci staff, sann suka gaisa, cikeda girmama juna, haka karima suka gaisa sosai,
"Raihana wanda tintana cin abincin ta dameta da tambaya, ina wane ina yasu wance, daga kan y'an uwanta zuwa kan k'awayenta, inna da karima dai har suka basu guri,
" Raihana tace mama ashe azzalumai Allah ya had'ani dasu, saita fad'a kan cinyarta takifa kanta ta nata faman kuka, mai stuma rai, Rahmatu har cikin k'ok'on ranta take jin zafin kukan y'artata, dukda batasan meya faruba,
Amma hakan bai hanata stiyayar hawaye ba.

"Sautin shash shek'ar kukan Raihana yasa inna da karima furowa dg d'aki,

"Kafin Ramatu tanemi sanin yadda akai sukaga Raihana, har inna tafara yimata bayani,
danta lura ta k'agu taji abinda ya faru da y'artata,

" Inna da karima suka fad'awa Rahmatu komai daya faru, 

"Idon Rahmatu yayi jaja wur, haka fuskarta duk lokon idonta ya kumbura,
Abunka da farar fata..
Taji ciwo sosai dajin abinda ya faru, hakan ys ta d'aga hannu wanta Sama tarok'i sarkin sarakuna mai k'arfin masu k'arfi daya sakawa y'arta,
" sann ta cewa Inna nagode sosai karima, lalle kin amsa sunanki mai karamchi, ubangiji yy muku sakayya da gidan Aljannah.
Atare inna da karima harda raihana suka amsa da AMEEN.

"Inna tace to yazu kya iya shawar tar mahaifinta, akan ku barta anan, saboda staron lafiyarta da tamu, dan gaskiya wann lamari yana buk'atar sirri ko yy kika gani?
" Rahmatu tace kwarai da gaske, amma gaskiya ya kamata nima nasar daku ko mud'in suwaye,
Saboda kun nemi da dole asanar da mahaifin Raiha, Wanda hak'k'ine shima akansa, dole yasan halin da akeciki,
To amma hakan bazai tab'a yuwu waba, mutuk'ar inason rayuwar y'ata , dan haka yazama dole saina gaya muku labarin RAIHANA da kuma suwaye iyenta.....!!!


KANO

"Abbas ya shiga yanayin damuwa mutuk'a, yagaji da yawo akan titina, kawai ya yanke shawarar zuwa wajen farin cikin rayuwarsa, wato tilon mahaifinsa, yana isa yatarar suna sallar azahar, nan yy alwala, yafara gabatar da nafila sann yad'ora da azahar,
Yana idarwa yy addu'o'insa snn yamik'e, ya iso gun Abba yasamu suna gaisawa da wani abokinsa wanda mak'ocinsa ne, akasarin lokuta suna haduwa, sud'an tat tauna masta lolin yau da gobe, Abbas ya rusuna ya gaida su, snn yasamu guri acan gefe yana jiran Abbansa,

"Ahj Saddam da abokinsa Ahj Tijjani, hirarsu tayi nisa wajen neman mafuta tintini, akan aurenda Abbas yakeso ya k'ara,
Hakan yasa Alhj Saddam yake k'ara jadda dawa abokinsa cewar da yayi aure da wuri da tini yanzu yanada y'ar budurwa da zasu hadasu Aure,
" Sai dai yace komai lokacine,
"Ahj tijjani yace dubi yanda duk yabi ya rame, da ganinsa kasan yana cikin damuwa, waima shin!!!
sun mayar masa da matarsa?Ahj Tijjani yy tambayar cikin haushi,
" Ahj Saddam yace ehh, amma aiga dukkan alamu jiya ne iyau,
Saidai fatan samun sauk'i daga Allah,
"Ahj Tijjani yace wai har yanzu yarinyar nan ba'asamu labarin taba?
" Ahj Saddam yaja numfashi yace tohh dakai dai muka ringa shiga da fita wajan nemanta, araye ko amace, amma Allah ya lullube saninsa,
Wllh Ahj haryau inajin yarin yarnan araina, kaga duk kwashe kwashen da hjy take na kawo y'an aiki, ban tab'a jin ko ganin mai d'a'ar taba.
"Ahj Tijjani yace hmmm shiyasa duk kaima gashi nan kabi ka damu, daman ka kwalla fawa ranka, kokai ko d'anka wani ya dace da Aureta,
Inajin kota gane alamar hakan yasa ta gudu, dan kar hjy ta gane ta kusan kashe ta,yak'ara maganar yana wata wawar dariya,
Suka cafke....
" Ahj Saddam yana dariya yace hmmm dan kuwa tasan hjy kaltum ba sauk'i, musam man akaina,
Kuma batasan aikin banza take ba, ina amfanin ana kishinka, har yasa a hanaka k'ara aure, alhalin da lafiyarka,
Kuma kasan abin mamaki....?
Ahj Tijjani ya gyad'a kai, alamar aa
"Ahj Saddam yaci gaba, kaga dukfa kishin nan da takeyi, stabar rashin adalci irinna wasu matan, itafa bata gamsar dani, kai hasalima, gabanta kusa yake da co....
" Abba ko naje nadawo? Abbas yak'aste masa magana, wanda sai a lokacin suka Tina da Abbas agefansu,
"Cikin kidima Ahj Saddam yace daddy ashe kana nan, aina dauka, ka koma mota kana jirana?
Yak'arasa maganar cikin inda inda.
" Abbas yace, cikin muryar tausa yawa, bari kawai naje Abba, zanzo gida anjima na sameka, sai ya mike,
"Ahj Tijjani yy saurin tare Ahj Saddam yace to shikkenan, ka ky'aleshi yaje, kasan shi akwai hankali, da sanin ya kamata,
Adole badan yaso hakanba ya bari Abbas yatafi, harga Allah kwata2 yamanta Abbas yana bayansu, ya saki layi , gashi yasan gurinsa yazo amma yak'i saura rarsa, kusan minti 20.

Jin antab'a kafad'arsa yasa ya dawo dg tunanin da take....








Allah ks yzm tsani na shiriya,
Allah ks min abinda aka amfana dashi acikin mizani


AMSAR💕
[1/31, 8:55 AM] SARATU: ___*🍂BIYU BABU…!🍂*_
        _SAMU DA RASHI…_
               🍂🍂🍂
                 🍂🍂
                     🍂

      _*AɭKAɭAMƖŊ✍:SARATU MUNZALI*_

           _*(AMSAR💕)*_
        _watpadd @ Ssaratu75…_

*dedicated to:AUNTY ZALY YOLA ( MMN AHMED)

*AREWA WRITES ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{arewa gin shiƙin al'ummah}💦*
_________________________________

https://www.facebook.com/104534761033461/posts/104535871033350/?substory_index=0&app=fbl

*BISMILLH RAHMANI RAHIM*

P______10

____________📖 Ahj Tijjani yace tinanin me kake haka?
"Ahj Saddam yace inajin tausayin yaran nan, Allah ys dai baiji hirar muba.
" Ahj Tijjani yace kai anya, banajin yaji saboda kamar hankalin sa yana kan waya,

Shidai Ahj Saddam jikinsa duk yy sanyi, haka sukayi sallama, suka rabu.

"Abbas tinda  ya tafi, yana gefen titi yy Perkin, saboda yanda yake jinjina abinda yaji,
Tausayin Abbansa ya dabai bayeshi, yana fad'i aransa, 
Ashe abinda ke damun Abba kenan, lalle dole yak'i gaya min abinda ya shafi matarsa, tabbas gara mastala ta da tashi,
Danni koba komai ina gamsuwa da safna, indai lafiyarta k'alaw, 
Saidai idan nata kura mata da yawane, yake kaita ga suma, amma  lalle nak'ara yankewa da soyayyar iyaye,
Allah sarki Abba ya ajiye damuwarsa agefe, yana ta tawa, burinsa ya nemo min mafuta,
Yaja numfashi, yak'ara jingina kansa a jikin kujera, ya dafe kansa,
Cikin rauni, ya cigaba da cewa,
Wayyo Abbana Ashe kaima ka kwad'aita da auren Raihana, na tabbata Abba yana nufin idan yace na auri Raihana na nuna masa bana sonta, shizai aure ta,

Wayyo Allahna ina kk Raihana!!!   

RANO

RAIHANA SANI.....

Rahmatu ta fara basu tarihin rayuwarsu,

MLM GARBA wani shaha rarrene ak'auyen BICCHI,
Kowa ya sanshi, a fannin samun al'barkar amfanin gona, matarsa day'a, uwar yaransa, bayan ta rasu yy aure aure, amma ba wacca ta haihu, har shima Allah ya karb'eshi.
Duk kanin y'ay'ansa mazane, su 5, tindaga kan babban, Mohd Auwal, har zuwa kan autansa, Mohd khamis.

Mahaifin Raihana shine d'ansa na biyu, wato MOHD SANI,

Gidan da suke cikinsa family house ne,
Wanda kowa da matansa da y'ay'ansa, biyu dg cikinsu matansu 3_3, d'aya kuma matansa 2,
Kowan nensu, yanada y'ay'a sama da goma,
d'an autansu khamis shi kadai ne yarasu yana matashi, bai aureba,

Mahaifin Raihana mlm Sani, shima matarsa day'a, Rahmatu,

" y'arsu d'aya Raihana, akasarin y'ay'an gidan auren zumunci suke had'asu,
Kad'an ne wad'anda suka auri bare,
Raihana kusan sa'anninta 3 akaiwa aure, wanda ba sufi 15 years ba, alokacin,
A dalilin auren da zasu kuma yiwa y'ay'ansu, wanda harda k'annen Raihana aciki, sai yakasance Raihana har zuwa lokacin bata samu mane miba, wanda badan tana da muni, ko wata mummunar d'abi'a ba, Allah dai bai kawo lokacin taba,
Hakan ya k'ara tinzira zuciyar mahaifin ta, harya yanke shawarar zaisa asauke mata Ash_Shafa, kota auru, kota mutu, hakan ba k'aramin d'agawa Rahmatu hankali yyba, tayi kuka, ta rok'eshi Allah da Annabi akan ya janye amma inaa,
Rahmatu kafin gari ya waye, ta hana idon ta barci, tana gayawa Allah, akan Allah ya d'orata akan mlm Sani, kan yajanye k'udirinsa, ya yarda zata kaita birni gurin K'anwar mahai fiyarta, bayan kuwa tasan bb wanda tasani acan, amma tak'udur ce dayin hakan zaifi, akan tabari yy abinda yy niyya akan Raihana, ta yanke shawarar ko aikatau ta kaita, wani gidan, ba tare da kowa ya saniba,

Hakan kuwa akai, Allah ya d'orata akansa, tun asuba suka bar gidan,

Wannan ne babban dalilin da yasa na taho da Raihana birni, ba tareda nasan inda zamu do saba,
Har Allah ys muka dace da gidan Ahj Saddam,
  saura wata 3 tacika shekara a gidan,
Wata rana naje ganinta, naji labarin ba'agan taba,
Tin ina boyewa mahaifin ta, atina nina za'aganta, har dai ya lura, ina yawan cemasa zani birni ,ga tashin hankalin da baya b'uya a fuskata,
Kawai saina gaya masa gaskiya,
Hakan yajawo harya sakeni, saki d'aya, banda gori, habaici, cin mutunci, bb wanda ban ganiba, agunsa har gurin y'angidan gaba day'a, 
Da shurun yy yawa akan sauraren ganinki, sai kowa ya fiddarai da kin mutu, amma bandani, dan jikina baitab'a bani kin mutuba,
Ko mafarki nayi dk, araye nake ganinki, sai dai naganki kinata kuka.....

Munsha wahala nida y'ata, agidan nan, stangwama, kyara, gori, duk dai,
Musam man ganin ni kad'aice banida kishiya,
Bayan sunsan halin mlm sani,
duk y'arda ya nema da aure, ba'abashi, saboda bak'in halinsa dayake nunawa akan y'arsa ta cikinsa, tintana k'arama, dan yafi kwallafa ransa akan nahaifa masa namiji,
Kowa yasan irin hakurin da nake dashi, sau dayawa abinci da kudina nake siya muci nida y'ata,  badan bashi da kudinba, sai dan tijara, da kuma haushin na haifa masa d'iya mace,
Ko ragon suna bai mataba, Nina saida akuyoyina nasai mata ragon suna,
Shiyasa da yawan mutane suke cewa butulcin da yywa Allah ys baik'ara bashi haihuwaba, daga baya kuma ya karb'e  guda d'ayar.

Mlm Auwalu, agunsa ne kad'ai nake samun sauki, kullum yana cikin bani hakuri, da yimin nasiha, shikad'ai yayo halin mahaifin su.
Allah kaji k'ansa da rahma....
Rahmatu tafashe da kuma,
"Raihana tace mama kawu babbane ya rasu? Innalillahi wayyo Allah sarki,
" inna da karima sukai mata ta'aziyya,
"Snn inna tace tabbas kinada kwara ran hujjoji, dan haka karki bari kowa yaji, duk sanda kk fahimci ya dawo kan hanyar daidai, to kya sanar dashi,
Lokacin bayan lokaci kyadinga zuwa ki ganta,

"Raihana tace cikin kuka, mama ina sadiya auta,?
" Rahmatu ta share kwalla tace, daman ita kad'ai ta rage acikin y'ay'ansa wanda baiwa aureba,
Dan harma ansaka ranar bikin tin kafin ya rasu,
Yanzu haka saura sati d'aya,
Shekaran jiya mahaifin ki yasani agaba, saina siyarda dabbo bina na bashi aron kudin,
Saboda yanzu nauyin gidan ya dawo kansa, dole shizai komai na auren,
Banyi masa musuba haka na tattarasu duka, garke guda ya siyar,

"Raihana tace habba mama kinfa sani, kud'a d'enda kk binsa basu da adadi, amma bai bakiba snn kika k'ara bashi, ta zinb'uro baki gaba.....

" Rahmatu tayi d'an yak'e tace, hmmm ba komai Raiha, sadiya ai  itama y'atace, ji nake kamar ke zan aurar, karki damu, wata rana zaibiyani,
"Inna da karima ba k'aramin jin_jinawa Rahmatu sukaiba, kan namijin k'ok'arin da takeyi, sun yaba da karam cinta sosai, ga hak'uri da maida lamuranta ga Allah.

" bayan sunyi sallar la'asar, Rahmatu tai himmar komawa,
"Inna ta d'auko kudin da Dr Hanna ta bawa karima, tace to gasu,....
" cikin kid'imewa Rahmatu tace niii..ta dafe k'irji
Na kaisu ina?!!!!

"Inna abin ya bata dariya, tace ai ya zama halak kici,

" Rahmatu tace, kurufa min asiri ai idan mlm Sani ya ganni da kud'a d'ennan, ta rik'e baki, wai_wai, to naashiga tara, bama 3ba, 3 sau 3.
"Aiba inna ba, hatta da karima da Raihana saida suka tinstira saboda dariya,

" Rahmatu ta cigaba, ko lokacin b'atanki, Ahj Saddam yanasa hjy kaltum ta kirani, ya bani abin arzik'i, kayan abinci harda kud'i,
Amma daga baya kwata _kwata, ya hanani zuwa bir nin, wayar ma kwace ta yy, ya b'alla layin,
To kinda da'ace haka bata faru ba, na'iya gaya masa Ahj Saddam ne ya bani, amma banda haka taya zan gaya masa inda n samu kud'i haka.......

"Inna tace tohh fahh...
Yanzu ina mafuta?

" Raihana tayi karaf...tace,
Mama, inna, kunsan yy za'ai ds?
Bata jira amsar suba, taci gaba da cewa,
Kawai asiyi gida, mu koma, Anti karima ta huta wahalar biyan haya,

Duk kanninsu mamaki sukai dajin maganar,
"Cikin sauri Rahmatu tace kwarai shikkenan, tunda yanzu Raihana ta zama taku,
" inna tayi kasak'e ...takasa magana, kawai mamakin kyawawan  d'abi'unsu take.
"Haka karima aranta tace,kaga yarinya mai zurfin tinani, da hankali, sai kace babba,

Mik'ewarda Rahmatu tayi yasa inna dawowa dg tunani, tace to da alkyri,
Ahakadai suka yanke shawarar, zasu sa anemo gida dai dai su,
Snn ragowar kud'i, zasu raba biyu, d'aya zasuyi d'awai niya Raihana ta koma makaranta dasu, kashi d'ayan kuma, zasu siyi dabbobi garke 2, sukaiwa Rahmatu k'auye taci gaba da kiwonta, natane halak malak, Inna tace karta damu, dakanta zata koma ka'uyen itada karima, harda Nazifi, sukai mata, azuwan nasune suka kawo tayi musu kiwo, bayan sun toshe musu, baki da kyautar kud'i, saboda Sufi yarda nasu ne, hakan zaisa ko mlm sani bazai kawo musu hariba.

" Rahmatu tayi murna sosai, har a fuskar ta , hakan ya bayyana, tayi tayi musu godiya da addu'a, bayan tayiwa Raihana nasiha sosai akan ta kula da kanta, a makaranta, snn halayenta data Santa ds na alkairi ta k'ara akai d'a'a da biyayya, da kyar ta rabu da jikinta, tarik'e hannun ta, tace to mama Allah y kiyaye, saura.... Saita durkusa kamar meyin ruko'u, ta tura mata kanta, daidai cikinta,
Rahmatu ta gane abinda take nufi, tunda d'abi'ar tace, ta saba tintana k'arama, duk abinda tayi na'aiki ko zata makaranta, dole saita dafa kanta , tashi mata albarka, yan Zuma hakan tayi,
Ta daga kanta tace Allahumma  barik feeki, wa hayaatuki, wa zurriy yatuki,
"Raihana ta d'ago cike da murna tace Ameen mama, tak'ara fad'awa jikinta,
Dakyar karima da inna suka janyeta, inna ta zirawa Rahmatu 5k ahannunta, tace kyahau mota kiyi staraba, sai Kice injini,
Takarb'a tana godiya harta fita, da Kuka fal a idonta,
Haka Raihana har kusan magrib tana Abu d'aya.



KANO

Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un
" Abbas ya fad'a, yayin da yashigo, yaga safna awani yanayi, dabai tab'a ganin ta acikin saba.... Safna safna ......!!!! 







Ya Allah k samin abinda al'umma suka amfana dashi a miza Nina.
 

Yaa Allah kai rik'o da hanna yena, kar kabani ikon rubuta basta......






AMSAR💕
[1/31, 8:56 AM] SARATU: ___*🍂BIYU BABU…!🍂*_
        _SAMU DA RASHI…_
               🍂🍂🍂
                 🍂🍂
                     🍂

      _*AɭKAɭAMƖŊ✍:SARATU MUNZALI*_

           _*(AMSAR💕)*_
        _watpadd @ Ssaratu75…_

*dedicated to:AUNTY ZALY YOLA ( MMN AHMED)

*AREWA WRITES ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{arewa gin shiƙin al'ummah}💦*
_________________________________

https://www.facebook.com/104534761033461/posts/104535871033350/?substory_index=0&app=fbl

*BISMILLH RAHMANI RAHIM*

P______11

____________📖safna...nan danan ya kid'ime, yakin kimeta, ya kwantar a kan gado,
Ya d'auk'o ruwan sanyi, yafara bin jikinta dashi, ahankali ahankali tafara saukar da numfashi, can saita d'an bude idon ta,
"Safna tana sane tayi haka, plan ta had'a duk dan ya kulata,
" Abbas Sam bai ganeba, k'ara lallab'ata yakema, sabo da larurarta,
"Safna tak'ara shagwame masa, sai narkewa take ajikinsa, " Abbas yad'a gota, ya cire mata singlet d'in jikinta, ya zame skin tiet din, ya mayar, da kanta kan flour, ya mik'e yacire jallabiyyar dk jikinsa, snn yasauko k'asa, saida ya lek'a d'akin safna ya tabbatar twins barcinsu suke lakadan snn yawuce kitchen yabud'e prige yad'auko drugs d'in safna, da fresh milk ya dawo sama,
Yana shigowa d'akin yasa meta a'yanda ya barta, yak'araso, yak'ara d'agota yasata ajikinsa, ya b'abbali drugs d'in yabata abaki, had'e da ruwa, yace oya swallow it....
Tana had'iyewa ta yastune fuska, tace acikin shagwab'a, dan Allah dear massage... Ta k'arasa

Please Login or Register in order to submit comment