Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hakan yasa muka rufa a bayanta dan mu dakatar da'ita gudun kartayi b'arna kota haddasa accident, to Allah yy hakan saiya faru, yanzu haka Ahj wad'anda ta huge suna can Hospital d'in Aminu Kano,

Ahj Saddam ya sauke  numfashi, ya waiga yace Hjy ina Hanna?
" Hjy Kaltum tace,ita kad'ai suka bawa izinin shiga danta duba lafiyarta,
"Abbas ya tari numfa shinta, yace Abba wai sunce taji rauni, snn ta karye a k'afa

" Ahj Saddam ya sauke salati, yana jijjiga kansa, saiga wani d'an matashi, ya shigo, bayan sun gaisa, sai yake gaya musu Dr Hanna ce tayi masa waya yanzu akan ya had had'o mata wad'annan drugs d'in da sauran kayan amfanin Doctors,

Ogan ya karb'a yy checking d'in komai sann ya sallami matashin,

Ya mik'e da niyar kaiwa Dr Hanna kayan, sai Ahj Saddam yace dan Allah d'ana ka bamu damar ganinta muga halin da take ciki, koda yaune kad'ai dan Allah

Oga da'ike musulmine yasan girman Allah, saiyaji nauyin Ahj Saddam,sai yace to kubiyoni, sai suka bi bayansa,


MALAM AMINU KANO TEACHING HOSPITAL

Tin akan hanya Nazifi yaketa kiran Dr Karima, harsuka  K'arasa, Dr Karima sun riga Nazifi isowa hospital d'in inda saka wuce direct zuwa Emergency,
Da sauri Dr tayi parking suka nufi ciki, koda suka shiga a take suka cicciro ID Card d'insu,suka nunawa Police Dr Karima tace ita suka kira d'azu, suka karb'a, suka duba snn suka gaya musu duk abinda ya haddasa faruwar accident d'in, kuma suka sanar dasu matar tana can Police Station , Dr karima taji dad'in yadda suke kula da aikinsu, hakan yasa basu b'ata lokacin ba aka basu izinin shiga, koda suka nufi ciki, sai suka tarar da wani bbn likita akan Inna, yana ganinsu ya nufo inda suke, bayan sun nuna masa ID Card d'insu sai Dr Karima ta sanar dashi mahifyar ta ce da matar K'aninta, dan haka yace yana duba Innane dan tana cikin Critical Condition, sud'an jirashi kad'an, Dr Karima kuka kawai take, shi kansa Dr ya lura tana cikin tashin hankali, dan ko da yaga ID Card d'insu, ya tabbatar Doctors ne, kuma sun samu kyaky-kyawan horo, sai yace da K'awar  Dr Karima, tad'anzo, bayan ta biyoshi, sai ya sanar da'ita Allah yywa Mmn cikawa, ita kuma d'ayar, sai yy mata nuni da inda Raihana take kwance, yaci gaba da cewa, ita kuma duk munyi mata gwaje -gwaje da'alama ta bugu sosai amma bata mutu ba, sai dai ta nata bleeding kasan cewar tana da juna biyu, dole sai anyi mata wankin ciki, da sauri tace dan Allah Dr kozan iya taimaka maka, na dubata,
Dr baiyi musuba yace alright go ahead, dan da yaga ID Card d'inta fannin da suka karanta kenan itada Dr Karima,  wato GYNECOLOGY

Tana zuwa kan Raihana nan danan ta bata taimakon gaggawa, snn ta umarci wasu Nurses dasu rufe mata jikinta sukaita Labour section, ga tanan zuwa,

Tana zuwa gun Dr taga shima har yasa an rufe Inna, za'a futa da'ita Envelope na waje...

Nazifi yana zuwa ya k'ara kiran no Dr Karima,da tafito gashi a waje, baisan inane Emergency ba,

Dr Karima da sauri ta mik'e ta futo waje, tana gaya masa daga get ya mik'o street zai hangota, da farar rigarsu irinta Doctors,
A cikin 4minute sai gashi, yy parking y futo da sauri, suka Shiga ciki, fad'i take yy jikin masu...!!!? Karima stabar kukan da take, bata bashi amsa ba, kawai tafiya take,
Suna Shiga sai sukaci karo da mutum biyu an rufesu duk akan gado, wasu Nurses suna turosu da niyyar futa ds, sai kuma Dr da k'awar Dr Karima suna biye dasu, sai suka staya cakk...
"Dr tana zuwa saita fad'a jikin Dr Karima tace Sorry Sis Allah yywa Inn rasuwa,tana maganar cikin dakewa da irin salansu na Doctor's, Raihana itama Allah ya..........
Aibata k'arasa fad'a ba sai sukaji yifff... Nazifi ya fad'i war-war ak'asa, ko mosti bayayi, Dr Karima kuwa tin kafin ta'ambaci sunan Raihana ta sume a jikin K'awarta Dr Hafsa......









Ya Allah kasa mucinye duk jarabawar da zaka jarrabemu da'ita,
Yaa Allah ka bamu ikon hakuri, juriya, da dangana,




AMSAR💕
MMN 3G💕
[1/31, 9:07 AM] SARATU: _*🍂BIYU BABU…!🍂*_
        _SAMU DA RASHI…_
               🍂🍂🍂
                 🍂🍂
                     🍂

      _*AɭKAɭAMƖŊ✍:Saɾatų mųŋχaɭɩ*_

           _*(AMSAR💕)*_
        _watpadd @ Ssaratu75…_

*ɖҽɖɩcatҽɖ tɷ:AUNTY ZALY YOLA MMN AHMAD*

    *🅿_____17*

  _*Sadaukarwar page d'in nan nakune Deejamah, Maryam Zazzafa, maryam Jos, Zainab Mohd, U/Salama, Mardiyya Shu'aibu, Maryam diyana,Mmn Usman,Mmn Humaira, Ummi Hafsa,  Ramla2 mmn 3B, and  u sis Farida, Nukhair, Kanziyya,Meenal, Mariya Mlm, masoyan BIYU BABU, madallah da Comments, dan da Comments d'in kune nake samun kwarin gwiwa sosai. MUNA KYAWUN TARE👍👍💖


________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________

https://www.facebook.com/104534761033461/posts/119016616251942/?app=fbl
   
*BISMILLAHR RAHMANI RAHIM*





____________📖Karb'i rabon dake jikin ta, wanda baifi....sai Dr Hafsa ta lura kamar Dr Karima bata mosti,nan Dr suka yo kansu, aka basu taimakon gaggawa, Dr Karima ta dawo hayyacinta, shi kuma Nazifi sunyi masa duk wani gwaje-gwaje amma shiru bai mostaba, sai Dr yace maza a kaishi MALE WORD ,
Dr Karima kuka take sosai jitake kamar itama ta mutu ta huta, rana d'aya, a lokaci d'aya, ta rasa rai har biyu, ga Nazifi shima bai farkaba, ta k'ara rirrik'e Dr Hafsa, suna kuka, da kyar ta lallab'ata ta d'anyi shiru, snn tace ai Raihana bata mutu ba, cikin jikinta ne kawai ya zube, kiyi hak'uri, Allah ys Aljannah ce makomar Inna, da kyar ta kama hannun ta suka nufi section d'in da'aka tafi da Nazifi,


Dr Hanna tayi nisa kwarai wajan bawa Safna kulawa wacca baccinta kawai take, batasan komai yake faruwaba, suna kanta dukkan su, k'arar ringing wayar Oga ce take ta ruri, d'agawarsa kenan, sukaji yace Allahu Akbar, Allah yj k'anta,
Gaba d'ayansu saida gabansu ya fad'i dararasssss....
Ogan ya kalli Ahj Saddam yace Kaji ko, tayi Sanadin rasa rai, ta kashe d'aya daga cikin wad'anda ta buge, y'ar stohur cikin su ta mutu, d'ayar dajji juwar kuma ta bugune sosai amma dai lfy, sai d'ayar kuma y'ar mata shiya, data rasa cikin dake jikinta, wanda baifi wata 3ba, itama har yanzu bata farka ba.

"Ahj Saddam stabar kid'ima saida ya cire hula, banda salati kala daban -daban dayake, ya kasa cewa komai

Haka Abbas, Hjy Kaltum da Dr Hanna banda gunjin kukan su, da fatar magina bb abinda ake jiyowa, kowa kansa ya kulle, duk sun kasa cewa komai,

Oga yy musu nuni da hannu alamar su fita,
Ahj Saddam ya jawo, Abbas su kayo waje, baijira yaga futo warsu, hjy kaltum ba kawai ya nufi waje, koda Ogan yaga haka, sai yace, suma su Hjyan suje,

Kafin su iso gun motar Ahj Saddam harya ta da'ita, yana ganin sun fito, saiya lek'o da kansa ta window yace kuje gida, nasan yanzu twins sun kusa dawowa, ni zamuje hospital muduba su, bai jira amsar suba yaja motar, har sun kusa, barin harabar station d'in sai Abbas yace Abba, da nabawa Hjy key d'in mota ta, sai ta wuce min'da'ita, dan naga atare sukazo da Mmn Safna....
Ahj Saddam yaja burki, yace kai musu, Abbas ya bud'e motar ya futa, suna staye a yanda suka barsu, har yanzu kukan suke, yana mik'a mata key d'in, tace jeka da abunka, ka gayawa twins su wuce gidan Hajja, dan Police zasu bimu dan yin bin cike, a gida, Abbas bai bata amsaba kawai ya jiyo, yana isowa cikin motar ya sanarwa da Abba, Abba yace bb yadda zamuyi, aikin sune, sai sun tabbatar da ta dad'e tana sha, ko kuma yaune ta fara. Abbas kuka kawai yake dan yasan shiya haddasa komai,
Da kyar ya'iya ciro wayarsa ya kira Twin ya sanar ds cewar su wuce gidan Dr Hanna, ba gida ba, sunso suji dalili, amma Abbas baya jira sunce komai y kashe wayar,


Bayan Dr Hafsa ta tai makawa Dr Karima sun'isa bakin gadon da aka kwantar da Nazifi, ta zaunar da'ita tace dan Allah ki k'ara hakuri, yanzu kinga yanda yake samun kulawa agun Consultant Dr's insha Allah zai dawo hayyacinsa, da alama zuciyar sace bata bugawa kamarda, amma da ransa, kiyi hak'uri, snn ki tayin addu'a ko arankine, kinji?
Dr Karima ta d'aga kai, tace to idonta hawaye yak'i stayawa,
Dr Hafsa tace bari naje Labour section naga halinda Raihana take ciki nasan yanzu sungama bata kulawa, bata jira amsar taba ta tafi,
Dr Karima da sauri ta riko hannun ta tace barina biki , inason naganta,
Dr Hafsa batai musuba ta kama hannun ta suka tafi,
Koda isarsu sai suka tarar bata nan, sai suka tambayi, wasu Nurses ina take, wacca aka kawo, sunyi accident, sai sukace ai Dr ya gama mata komai, yanzu haka, har ankaita d'akin hutu, sukaji dad'in hakan, direct suka nufi FEMALE WARD dan sufara duba Mama, suna shiga suka ganta a zaune,da'alama drip d'in da'aka sa mata ya k'are,sai ban deg da'aka sa mata a gefen goshinta da guiwar hannun ta, suka k'arasa Mama tana ganinsu ta tashi zaune sosai, Dr Karima ta fad'a jikinta tasa kuka na ban tausayi, kukanda duk wanda ya tab'a d'an d'ana d'acin rasa rai musamman na uwa ko uba, to idan har yaji kukan Dr Karima dole shima tasa rad'a d'in mutuwar ta dawo masa sabuwa, mur yatta, a sar k'ak'e tace Mama, Inna ta rasss....bata iya k'arasa fad'aba takuma fashewa da wani launin kukan mai bujiro da stanstar tausayin duk mai sauraro, Mama itama ta sau salati tana kuka, tan fad'in shikenan Allah y raba k'auna, Inna abinda kikai na alkyri Allah ys yabiki, Allah yy miki Rahma Inna, da kyar dai Dr Hafsa ta Ciro Dr Karima daga jikin Mama tana basu hak'uri, da cewa duk mai rai mamacine wataran, da sannu muma zamu bisu, dan Allah kuyi hak'uri Ku d'auki k'addara, kinsan Allah yana yiwa wanda ya mutu Azaba a sanadin kukan Rayayye, dan haka kudaina mata kuka irin haka, da jin haka sukai shiru, saidai hawaye da keta stiyaya,
Mama tace Raihana fa?
Nan Dr Karima taimata bayanin komai har abinda ya samu Nazifi,
Mama ta kifa kanta tana tayiwa Inna addu'a, da fatan su kuma Allah y tashi ka fad'unsu, nan sukai sallama da Mama, suka wuce, gun Raihana,
sun sameta sumul da'ita, fuskarta tayi haske tamkar kana tab'ata jini yy maka stattuwa, sai faman baccinta take, Dr Karima ta dudduba jikinta ta tabbatar bataji jiwon komai ba, tana juyowa, taga Dr Hafsa tana waya tana sanar da gidansu ayi maza akawo abinci kamar kula biyu da tea, da komai dai na buk'ata, tayi mata gdy, snn suka fita,

Sun dawo gurin Nazifi, sai sukaci karo da Ahj Saddam da Abbas, kasan cewar basu san junaba yasa basu kula suba kawai suka wuce zasu zauna,
Ahj Saddam yace snnku, suka d'ago a tare da cewa yawwa, cike da alamar tambayar waye shi?
Ahj Saddam yace ya masu miki? Ya kuma Karin hak'uri? Dr Hafsa tace Alhamdllh, dan Dr Karima har yanzu kuka take, Dr Hafsa tace bamu shaidaka ba Ahj
Ahj Saddam yace ehh wnn yy musu nuni da Abbas, dake zaune, Abbas ya gaji da tambaye 2, da Abba yake tin d'azu, akan nemansu, sai kawai ya samu guri ya kame, Ahj Saddam ya cigaba da cewa to shine mijin matar data haddasa Accident d'in,
Dr Karima ta d'aga a fusace ta dubi Abbas tace wllh ka shirya yin ban kwana da matarka, dan wllh yanda tayi sanadin rasa ran mahai fiyata, itama ya zama dole, ta rasa nata, ko zan rasa raina sai na d'auki fansan ran Inna....da kyar ta k'arasa fad'a kuka yaci k'arfinta
Dr Hafsa taja Ahj Saddam gefe, tace kayi hak'uri Ahj kasan yadda zafin rasa rai yake, musam man na uwa, kaimata uzuri, gashi yadda Police suka bamu bayanai ya nuna da ganganci acikin faruwar Accident d'in,
Ahj Saddam kamar ya fashe da kuka, yace hakane muma duk sunyi mana wnn bayanin kuma mungani mun tabbatar da hakan, amma dan Allah kuyi hak'uri, ni mahaifin mijintane,
Amma yadda za'ai yanzu ki kaimu muga marasa lafiyar daganan zan wuce, mubiya Bill, snn zan biya, amaidasu AMENITY,
Dr Hafsa tace to Anan suka gaisa da Abbas shima yy musu ta'aziyya, had'e da duba masu jikin, har sun d'auki hanya sai aka kira Ahj Saddam awaya, suna tafiya ya d'aga wayar, sai salati yake, harya daste wayar,
Daga Abbas har Dr Hafsa hankalin su nakan suji mai Ahj Saddam zaice,
Ahj Saddam ya staya da tafiyar yace dan Allah Dr kiyi hak'uri zamu dawo gobe gabad'a yammu mudu basu, yanzu kiran gaggawane Police sukaimin, ya zama dole naje yanzu, suna jirammu, kinsan mund'an jima munata neman gunda kuke,
Dr Hafsa tace bb komai Ahj, Allah y kaimu goben, aida sauk'i jikin nasu, anan Abbas ya masto yabata no wayarsa yace in case ko wani abun ya taso, ko suna buk'atar wani Abu dan Allah a kirashi, suna shirin tafiya sai sukaji Sallama a bayansu, a tare duk suka juya, Dr Hafsa tace yawwa Usman harka iso, to kaga d'akincen jeka kaiwa Dr Karima ganinan nima yanzu,
Ahj Saddam ya lura da abinci ne da ledoji, a hannun matashin, da alama abubuwan buk'atar marasa lafiyane aciki, a take ya staidashi shima harda ambar sunansa, Usman jimana, sai ya kalli Dr Hafsa yace yawwa kinyi saving no daddy, Dr Hafsa tace ehh nayi Ahj, "Ahj Saddam yace to dan Allah karb'i kayan hannunsa ki k'arasa ds, zai d'an bimu zanbashi sak'o, tace to, ta karb'i kayan hannun Usman tayi musu sallama,
Ahj Saddam saida suka fara zuwa suka biya Bill ta hanyar rubuta chalk, ya biya har kud'in d'akin da yakeso a maidasu, snn suka wuce Super Market, inda yasa Abbas ya tare d'an sahu, aka lode musu kaya sama da kasa harda seat d'in baya yy taf da katan - katan d'in faro, maltina, mineral, madara Milo, bread, tea flask har 3,
Food flask shima haka mai 2da mai3 , da bbr cooler d'aya, sai rapper tissues, bb wani abu na buk'atar zaman asibiti da basu siya musuba, snn Ahj Saddam ya bawa Usman kudi' masu yawa yace ya sallami d'an sahun sai yarik'e canjin,
Usman yy masa godiya sosai suka rabu,

" Ahj Saddam suna kan hanya yake tambayar Abbas waye wnn da suka gani a kwance? " Abbas yace bashi dai akai Accident d'in, amma yaji kamar wasu abayansa suna cewa, da'n wacca ta rasune, kuma mijin d'ayar data rasa cikin jikinta, "Ahj Saddam yace Allah sarki, ai dole ya shiga damuwa, lokaci d'aya Allah ya had'a masa jarraba 2, "Abbas yace wllh kuwa, a haka har suka k'araso gida, suna shiga suka tarar da motar Police a harabar gidan hakan yasa suka wuce part d'in Abbas kai staye, suna shiga gaba d'ayansu a tare suka k'ame a staye, dan ganin abinda ida nuwansu suka gane musu, ga Police zagaye da ko'ina a falon
Abbas ya zube k'asa ya fara buga kansa a k'asa da kyar aka rirri k'eshi, yana kuka yana fad'in ......









Yaa Allah kasa mufi k'arfin zukatanmu, Yaa Allah kasa muyi sab'ani da bak'ar k'addara, Yaa Allah kasa muyi hannun Riga da staustayi, Ameen Yaa mujeebad da'awaatiy







AMSAR💕
MMN 3G💕
[1/31, 9:13 AM] SARATU: _*🍂BIYU BABU…!🍂*_
        _SAMU DA RASHI…_
               🍂🍂🍂
                 🍂🍂
                     🍂

      _*AɭKAɭAMƖŊ✍:Saɾatų mųŋχaɭɩ*_

           _*(AMSAR💕)*_
        _watpadd @ Ssaratu75…_

*Dedicated to*AUTY ZALY YOLA MMN AHMAD



*Sadaukar war wannan Peg nakune Taurarin BIYU BABU
Deejamah da UmmiHafsa,
Godiya Maras Adadi agareku PAN'S, ina tutiya da tarin addu'o inku, Ubngj yy mk sakayya da mafificin Alkhairinsa,👍


________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________

https://www.facebook.com/104534761033461/posts/119016616251942/?app=fbl
   
*BISMILLAHR RAHMANI RAHIM*

    *🅿_____18*

____________📖WHISKEY...!!!? Safna takesha...!!!?
Yaa Salaaam...Abbas yana fad'a yana kuka, dakyar Ahj Saddam ya jawoshi kan kujera ya fara lalla shinsa, Hjy Kaltum banda uban tagumi bb abinda ta rafka,
Dr Hanna kuwa take sosai tana  hararar Abbas,
Police suka yiwa Ahj Saddam bayanin sun yanzu dai kowa ya tabbatar da ba yau ta fara wnn d'abi'arba, kuma abin mmkin ace daga mijinta har uwarta bb wanda ya sani? Ko ya gane?
Dan haka anyi babban sakaci, ya zama dole a kwatarwa baiwar Allah hak'k'inta, suka sa kai suka bar gidan,

Dr Hanna cikin k'unan rai tabi bayansu, tana fita ta tarar zasu tayarda mota, ta lek'a tace CP ina son magana da kai, "yace fad'i ina jinki"
"Dry Hanna tace ko zaka d'an fito gefe...?,
da'isa take maganar bada sigar lallamiba"
"Oga yace Impossible!! Saidai idan kindamu sosai toki fad'a ina jinki,"
"Dr Hanna ta d'an cije leb'e, da'alama maganarsa ta b'ata mata rai, sai tace zan biyaka ko nawa kace pls ka kashe case d'in nan, ya zama kamar ba'yiba pls"
"Oga ya kalleta a yankwane, yace look at u, dan Allah bakiji nauyin fad'ar wnn maganar ba? Scheme of u wllh, sbd selfish ai rai baifi raiba, Allahn daya haliccemu shiyace WANNAFSU BIN NAFSU,
Dan haka kisani niba ahalin y'an Corruption bane, kingane? kinga gaba saiki kula, baijira amsar taba yaja mota suka bar gidan,

" Dr Hanna takiici yaci k'arfinta, kanta ya kulle, ta rasa mafuta, kawai saita k'ara fasa wani kukan, ta zube agun, tana fad'in No Nooo, wllh bazai yuwuba, ko y'ar gidan uban wa Safna ta kashe wllh bb wanda ya'isa ya kashen y'ata Safna indai ina numfashi, ko dakuwa rayuka ta kashe, my Daughter is the best..is the best wllh... Gaba d'ayansu Ahj Saddam suka fito harda masu aiki, da mai gadi, kukan da rakin da takeyi yacika gidan ga dare sun tabbata har mak'ota suna jiyowa,
"Ahj Saddam ya k'arasa daf da'ita, yace habba Hanna sai kace ba musulmaba, ki yadda da k'addara, ba Allah ne ya baki itaba, to shiyaso ya hukunta hakan akanta, dan Allah kiyi hak'uri"

"A fusace ta d'ago tace ehh aidole kace nayi hak'uri da k'addara, wnnce k'addara!!? K'addara ko ganganci, Abbas d'anka shiya haddasa komai, shiyayiwa Safna rik'on ganganci harta fad'a cikin wnn masifar, kuma wllh Allah ya isa ban yafe maka ba,Abbas duniya da lahira....ta kifa kanta k'ara rusa wani uban kukan...
"Hjy Kaltum ta d'agota itama ida nuwanta sunk'ara jawur, tace 6ter ya'isa pls control your self, karki jawowa kanki wata cutar, insha Allah indai kud'i yana magani to kozamu sara pant na sawa, sai mun y'anto Safna, kinji? Pls sorry 6ter just control your anger..."

"Ahj Saddam yace kwarai kuwa Hjy gaya mata, ai duk wad'anda suke aikata irin wnn laifukan sunanan birjik ba'a wani yanke musu hukunci, sbd babun dokar musulunci ake a NIGERIA ba, dubu nawanw suka kashe rayuka, ansamu kwararan shaidu akan tabbatar da kisan, amma ba'a yanke musu hukunci saidai akaisu Prison, suyi zama shekaru aru-aru, wasu harsh stufa, wasuma file d'insu ya ba'ta, stabar rashin bin Roles & Regulations na Addinin Musulinci,
To ballantana muda muke da hannu da shuni, aituni maganar zamusa ta mutu, k'urmus, illadai mubiya Diyya, a zuwan da ganganci tayi kisan....dan haka ki kwantar da hankalinki ni nasan duk hanyar da zanbi, kisa a ranki kamar Safna ta dawo,
Ya mik'e da sauri yy part d'insa,
Abbas ya bishi da sauri har suka isa falon Ahj Saddam,
" Abbas yace Abba to yy zamuyi da hak'k'in Allah!!!?
"Ahj Saddam idonsa acikin na Abbas, sun kad'a sunyi wani irin Orange Color, stabar shiga Tension, yace duk sanda ta koma ga Allah, wato duk ranar da wa'adinta ya cika, to Allah zai mata da kansa, amma ba dai anan duniya ba, Not Now Abbas... Ya k'arasa fad'in maganar da stawa, snn yy gaba yabar,Abbas a wajen..

Abbas ya dafe kansa, yana fad'in Innalillah, yana mmkin yadda Abba zai biyewa y'an san zuciya, da san Duniya, ta yy Abba zai juyawa umarnin Allah baya?
Bayan duk cikin su, yafi kusanci da Safna, bayan shima yana bak'in cikin faruwar hakan, amma ya kamata abi lamarin cikin sauk'i da lislama, ba'a nuna k'arfin iko da isa da yalwar dukiya ba, ai Allah da kansa, shi daya haliccemu yana cewa, INNI HARRAMTU ZULMA ALAA NAFSIY, WA HARRAM TUHU BAINAKUM MUHARRA MAN, FALA TUZAA LIMUO
(NINA HARAMTA ZALUNCI AKAN KAINA, KUMA NA SANYASHI A KANKU ABIN HARAM TAWA, DAN HAKA KADA KUYI ZALUNCI,

Abbas da kyar jiri na ibarsa ya lalubo kujera ya kwanta, hawayene mai d'umi yake bin gefen fuskarsa zuwa kunne da wuyansa, anan bacci b'arawo yy awon gaba dashi....

Dr Hafsa tayi nisa gurin d'ebewa  Dr Karima kewa, mutuk'a, tunda Usman ya dawo ya sanar dasu yadda akai, har ya gama shigo da kayan Dr Karima bata ko d'aga kai ta kallesu ba, bare ta yaba, har suka gama rarraba kayan aduk inda ya kamata, kama daga d'akin Mama, na Raihana, dana Nazifi, bayan an canza musu d'akuna, a kur-kusa da juna, tin kafin Usman ya dawo,
A Safiyar yauma suna tare da Dr Hafsa, da kyar take rarra shinta hartayi breakfast,
Snn sukayi sallama da mutanan mak'otansu dake ta zuwa yimusu ta'aziyya da dubiya, dukda cewar tun a daran jiya k'annen Dr Karima sukazo daga garu ruwan da suke aure, dasu aka kai gawar Inna ayau, da k'arfe, 9:00na safe, snn suka biyo Dr Karima hospital dan ganin halin da d'an uwansu yake ciki, shida matarsa, da Mamanta, bayan sunsha koke-kokensu snn suka koma gida domin cigaba da karb'ar gaisuwa,

Ahj Saddam da Abbas dasune akakai gawar Inna, daga nan suka zarce, Station ganin Safna, danta farka, tin misalin 4:00na'asuba, anan suka taradda Dr Hanna da Hjy Kaltum, da'alama sun tattauna dan daganin idanunsu duk sun kumayin jawur, sun kun-kun bura, suna isa bayan sun gaisa ds sai suka wuce Office d'in CP, suka gaisa ya sanar dasu farkawar Safna, wadda ita kanta tayi surrender akan abinda ta aikata, tace sanadin b'acin raine ya haddassa hakan,
Ahj Saddam ya nemi dasu ganta suna shiga suka tarar kuka take sosai kamar ta zauce, Abbas ya rik'eta suka kuma bud'e sabon shafin wani kukan, maisa rud'ani, Abbas yana ta bata hak'uri, snn Abba ya masto ya sanar da'ita duk matakin daya q zai d'auka, dan hakfda ta kwantar da hankalinta,
Suna futowa Ogan ya sanar da Ahj Saddam sun shigar da maganar kotu, dan haka on sat saisu hallara,
Ahj Saddam yace kafin lokacin zaituro asawa Safna kafet, da AC, da Net, bayan tarin abubuwan da Dr Hanna ta taho dasu, duk dan gudun kar Safna ta d'auki Effection, amma fafur CP yak'i yarda, saida kyar daya tabbatar tana da larular Sickler, snn ya yarda,

Ahj Saddam yywa su Hjy Kaltum magana dasu biyoshi, zuwa Hospital dubiya, sun hanya yana da sak'a da warwara ta neman hanyar da zai b'ullo, gashi har sun shigar da maganar Kotu, da wnn tinanin har suka k'araso,
Direct suka wuce Amenity, bayan sun kira Dr Hafsa ta basu direction,

Dr Karima tana zaune a bakin gado bayan likita ya gama duba Mama yace Insha Allah yana tinanin ko gobe, za'a bata sallama, dg nan yy mata allurai snn ya futa,
Dr Hafsa tana tad'an jan Dr Karima da hira sama-sama, tace kinga yarin yarnan, tana war warewa ta nufi gun mijinta wllh tausayi take bani,
Dr Karima tace kedai bari, aida alma itama sun kusa bata sallama, dan tace ita ta war-ware yanzu takan mijinta take, bini-bini ta lek'a, jiyama Dr yana gama dubata tayi stalle ta fad'a d'akinsa,Mama tintana jinsu kad'an-kad'an har barci mai nauyi yy gaba da'ita, sbd alluranda Dr yy mata, da drugs data sha, suna ta hirar Raihana sai sukaji anturo k'ofar da Sallama, kafin su'amsa har Ahj Saddam ya sako kai, nan suka amsa snn, suka cikin gaisawa, sai Dr Hanna da Hjy Kaltum, suma suka shigo, ai gaba d'ayansu suka k'ame a staye, ganin Dr Karima, kowa ya shiga zulumin ta yaya...!!!?
Dr Hafsa ce ta kaste tunaninsu da cewa sannunku Hjy ya hanya?
Anan suka shiga gaisawa, Dr Karima ta mik'e tace Dr Hanna kaddai ganinku ya tabbatar minda cewar y'arkice tayi sanadin raauwar uwata...!!!?
Dr Hanna tayi shiru jikinta gaba d'aya yy sanyi, sai Hjy kaltum ce ta masto kusa da ita, tace dan Allah ki kwantar da hanlinki, itace wllh Safna ce stau stayin ya fad'a kanta, Afusace Dr Karima ta abura, cikin d'aga murya da sautin kula, tace tabd'ijan y'ar sangarta kenan, y'ar azzaluman bayi, to wllh kozan rasa raina saina nemi fansar ran uwata, dole itama a kasheta, daman irin wnn ranar nake jira, wacce zaku girbi abinda kk shuk....bata k'arasa fad'a ba Dr Hanna ta taso tarife mata baki ganin gaba d'aya hankalin Ahj Saddam da Abbas yana kan san sugane meke faruwane ,
Tace dan Allah kiyi hak'uri

Please Login or Register in order to submit comment