Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bari na fara kai maka abincin office da dare ko rana kazo kaci amma gaskiya karkace bazaka zo ba dan inka fadi ciwo bana kusa bansan ya zanyi ba" gyada mata kai yayi dan shima bayajin zai iya cewa adawo masa da ita hakanan dai zasuyi hakuri har iyayen suyi magana da kansu.

Yau jumua shiyasa yayi shirin zuwa tambuwal ya kwana biyu, kayan dayake ajiya na jarirai na Cikin Nafisa ya kwasa dan gudun kar Nabila tayi shirin dawowa kwatsam ya rasa mai zaice mata, ya isa lafiya lau ya kwashi kayan ya kai mata dakinta, tayi murna sosai ta zauna tana budewa yana kallon yadda ta bata rai sannan tace "haba don Allah wannan kayan duk babu na namiji a ciki gaskiya basuyi ba" Tabe baki yayi yace "Niba mahaukaci bane da zan fara siyan kayan maza bayan banga abinda aka haifa ba, sannan ki gode Allah a gaba na kikai wannan kauyancin, kayan nan duk unisex ne mace ko namiji na iya sawa su ake fara siya sai an haihu anga mace ce ko namiji ne sai a siya kayansu" sake bata rai tayi tace "nidai duk da haka in zaka sake zuwa muje tare zan zabo wanda nake so" tsaki yayi yace "ban iya abinda kika iyaba, ke komai bazaki ce kin gode ba in akai miki, Nabila bantaba zuwa da ita siyan abu ba amma ina kawowa zatayi ta godiya da addu'a ke kuwa daga zuwa kin kushe to in basu yimiki ba kisa su a wuta ki kona"  a hasale tace "dama ka kwaso uwar kilibibi da iyayi ai duk abinda nayi ni sai kace ba daidai bane, ita kakeso dole ka yabeta nikuma cusa maka ni Akayi ka wulakanta ni son ranka" shuru yayi ya kyaleta dan baizo da niyyar suyi wnnan rigimar ba, Allah sarki Nabila sai yanzu ya tuna ma ana zuwa da mace ta zabo abinda take so amma shi sai dai ya kira wata ta fada masa abubuwan da ake siyowa bai taba yiwa Nabila maganar siyan kayan jariri ba, idan taga ya shigo da kayan kuma indai bashi yace tazo ta gani ba bazata taba ba koda ita takai masa daki sai inshi yace tazo ta bude tagani kuma bata taba kushewa ba, haka kayanta daya saka mata a barka duk ganinsu kawai tayi sai yanzu hankalinsa ya kawo da matar abokinshi tana da ciki ya rakasu siyan kaya yakai sau biyar da nata dana babyn duk sai wanda take so, zama yaji gaba dayai yana kallon Nafisa duk ta hada rai idonta kamar har da hawaye, bai kyauta mata ba yabon wata mace kuma kishiyarta ita kuma yana zakulo laifinta, wayarshi ya dauka ya turawa Nabila massage "baby Allah yayi miki albarka, nagode da hakurin da kikayita yi dani Allah ya kara bamu hakuri da juna, ina sonki kuma zanyita sonki" koda ya duba Nafisa ta tashi daga wurin sai ya shiga tata numbern itama ya tura mata nata massage kamar haka "Matata ki koyi hakuri dani, Allah ya shiryeki kuma ya baki hakuri ban fadi maganar dan na bata miki rai ba, ina sonki kema" yana turawa ya gyara zaman hularshi yabar gidan.




*Dr A.S. Zaki*

EXQUISITE WRITERS FORUM 
*SAFIYYAH GALADANCHI*

_sadaukarwa ga yayata Billy galadanchi_

SHAFI NA ASHIRIN DA BAKWAI




Lokacin da massage din ya shigo tana rike Ramla dake ta sheka amai saboda ta lasa mata danyen mashanu Mura ta kama ta sai gurnani take da tari numfashi a baki, sai da ta goge jikinsu ta sauya mata kaya sannan ta duba sakon reply tayi masa "ameen sweety kaima Allah yayi maka albarka ya kara maka budi" ta tura masa.

Nafisa kuwa sai bayan isha'i ta dauki wayarta lokacin kuma taga massage din yaune karo na farko da yayi mata haka sai taji sanyi a ranta ajiye wayar tayi bata maida masa ba, yana jin karar shigowar massage ya duba yaga ni sai ya kirata, tana kokarin bawa Ramla Nono dake mata kuka ga tari datakeyi, yana jiyo kukanta ya gyara zamansa yana cewa "menene take kuka haka Nana"? Sai data sa mata Nonon tace "Mura fa inaga sai na kaita asibiti gobe, yau gaba daya kuka take yimin ga tari kirjinta yanata amsawa" cike da damuwa yace "to dan Allah kije da wuri a kula kuma kidaina kunna fanka a daki" tace "Ni dama mama bata bari na kunna fanka tunda na haihu, murar dai Allah ya kawo mata amma zan kara kiyayewa" sallama yayi mata dan baya gida kuma jin muryarta na kara sashi a yanayi.

Yaukam dayazo gida cin abinci saida ya matse yar mutane, har saura kadan ta jefar da Ramla dake hannunta "don girman Allah ajiyeta ki taimaka mini" Dariya tayi tace "taimako?hmm... hada kayanka kaje tambuwal" ya rike hannunta yace "bakiji mama na maganar komawarki ba"? Ta girgiza kai tana sake rike Ramla sannan ta dan matsa baya tace "yi kokari kaci abinci kaji nakusa dawowa" "wallahi na shiga matsi da takura, wata biyu fa" ruwa take zuba masa a kofi tace "haba Dr gafa abinci ina baka kullum sai in baka nan" tsaki yayi ya ture plate din "ni zoki dauke abincin nan kibini gida kafin goma na dawo dake, nafi bukatarki akan abincin nan ko dadinsa bana ji" ta daiga ana kawo mata yan kayan gyara kuma mama ta kawo mata pills na planning "ka dai kara hakuri inkuma in kira maka Mamane kuyi magana to" hararar ta yayi yace "kina ko da hankali" dariya kawai ta mike tsaye zata fita suka kusa karo da yaya, taja baya tana gaida shi ya amsa yana cewa "Ke ki shirya ki koma gidanki gobe, wane irin jego ne wata biyu ai abin yazo da shiga hakki kuma" kunya ta dabaibayeta dan tayi tunanin ko ya gansu ne ko yaji abinda Dr ke fada, bata san shi tun tana 40dys da haihuwa yaso ta koma ba mama ta hana last week yayi magana da baba yace zai fadawa mama takoma amma yaga shuru yanzu ya shigo yana motar Dr shiyasa duk ranshi ya baci baima fadawa mama ba direct wurinsu yayo ya shaida mata ta koma, tana fita ya nufi Dr tareda bashi hannu suka gaisa ya dauki Ramla yana cewa "Dr ina yini ya hakuri kuma" dariya ya danyi yana cewa "muna ta fama, hakuri ai ya zama dole, shekaranjiya wani abokina yana son sababbin tayoyin mota na bashi numbernka" Yaya yace "sosai ma ya kirani har ya sake dawowa ma tare da kaninshi lokacin ni ina wurin aiki saina hadasu da wani Lawal dake zama wurin" hirar su irin ta maza suka ci gaba dayi sun dade kafin Dr ya wuce kasan ranshi yana jin dadin yadda yayan nasu yayi.

Washe gari kayan da suka fi bukata kawai ta hada aka maida ita sauran sai mama ce ta hada su daga baya aka aika mata.

Washe garin ranar data koma ta shirya karfe goma ya wuce da ita zuwa Makaranta, tana sanye da doguwar riga ta atamfa maroon tasa gyale baki shikuma yasa yadi brown saida ya kaita har kusa da Hall din ya rike mata Ramla ta dauki Jakarta bakin Hall din ya mika mata Ramla ganin an zuba musu ido yana cewa "karki bari maza su dauketa dai" dariya ta shiga Hall din tanayi aka zuba mata ido tana jiyo wasu na cewa tayi kiba, kusa da Nana sule ta zauna tana cewa "hada min madara in bata kafin ta taramin jama'a dan bazan bude jikina a class ba wallahi" Nana sule tayi tsaki tana karbar feeder tace "kedai har abada bazaki daina iya shege ba, wa zaki boyewa Nonon to, kowa ya gama gani" hararar wasa tayi mata tace "inkin taba gani wane kala ne" tsaki ta sake yi ta karbi Ramla ta fara bata madarar ita kuwa dama neman abinda zata saka abakinta take bata saki ba saida ta shanye take ta koma bacci, lokacin da suka gama lectures kiranshi tayi a waya ta sanar dashi zata bi Nana ta sauketa gida "Babu matsala idan kin koma don Allah akwai wasu zasu zo karbar sako bansaniba ko kafin lokacin na dawo amma dai ki duba wardrobe din bango akwai wata jaka brown ki bude ki ciro dubu ashirin idan sunzo ki basu" ta amsa mata da to sannan ta zauna mota tana tada Ramla zaune tace "yar lukutar Anty Nana ina kika samo kiba" Nana tayi dariya tace "ina fa, kila wajen ubanta dan kekam kindai karu amma baki kibar da za ace keta biyo ba, Allah yagani randa kika kwana dakin miji na kwana da tausayinki se in ringa ganin kamar kakkarya ki zaiyi" dariya tayi sosai tace "hmmm...wallahi saima kingani nikaina na sadakar da mutuwa surutu ba kalar da banyi ba, amma dan karfin hali ana gamawa na mike zan gudu sai jiri ya debe ni" Nana sule ta saki wata babbar dariya har tana kokarin sauka daga titi tace "shegiya taji mazan" itama dariyar ta sake tace "to yanzu ba gashi har da ramlaty na ba, in goyeta in goye ubanta"  da irin wannan hirar Nana ta sauke ta gida amma tun daga nesa ta hango wasu yan mata biyu kofar gidanta sunata bubbugawa koda suka iso taga kanwar raliya ce da kanwar mijinta diyar gidan baba Hassan, sun sha tsayiwa ga hadari ta bude gidan suka shiga suna gaisawa nan take ta goya Ramla ta dafa musu indomie sannan ta zauna suna hira nan take jin ashe COE suke hostel suna karatu sai bayan la'asar sukace zasu wuce ta shiga daki ta bude Jakarta dubu biyar kadai gareta bata son zama zero ta basu hudu meyaci dayar itako zata zauna ba ko sisi, hakanan ta hada musu dubu biyar ta dauki rabin kwalin indomie ta zuba taliya aciki da maggi ta basu tace "kuyi hakuri sako za a zo karba dana maida ku tunda ga mota ina gudun in fita su zo" sukam wannan kyauta da suka ji dadinta basa bukatar ma ta kaisu ta dai rakasu bakin titi ta dawo.

Lokacin daya dawo yanaji tana waya da tela ya gama dinki tace yayi hakuri akwai kudin da take jira idan ta samu zata kirashi, shi kuw kudi yake so kwana uku yana kiranta tana cewa bata samu ba dan ihisanin baba take jira ko na yaya gashi duk basu kawo ba kudin da take da na babban target ne bata son tabawa, ta ajiye wayar tana cewa "bazan sake bawa mutumin nan dinki ba bana son takura" shiga dakin yayi ya sameta tana ninke kayan data wanke na Ramla yace "kice ya kawo miki kayan anjima kuma don Allah irin wannan lamarin kidaina kasa tambayata, nasan halinki karki kawo min wani uzuri" ta ji dadi har ranta dan ya kula itako ko a gida roko ba dabiarta bane shiysa batayi indai ba takai bango bane balle dakyar takai irin haka, godiya tayi masa da addua ya dauke ramla ya wuce da ita palo yana mata wasa.

Duk bayan sati biyu sai yaje tambuwal ya dauko Nafisa dan tace bazatayi awo a can ba sai dai sokoto yadda Nabila tayi yadai kyaleta tunda koba komai duk sati yana zuwa tambuwal din, wata rana yana jin babu dadi daga asibitin daya daukota sai ya shigo da ita gidan Nabila, tunda ta shigo take raba ido tana harare-harare palon tsaf kamar yau akai kaita sai kamshi yake, Nabila tana kitchen Ramla tana kwance a kasa ta shimfida mata zani ta ajiye ta tana bacci, lekowa tayi tana mamakin ganinshi tareda Nafisa amma saita wayance suka gaisa ta dauko abincin ta kawo palo ta ajiye musu Nafisa tace bata ci, shikam table yaja gabanshi yace "zuba min ki dauko min maganina bana jin dadi" sannu tayi masa ta zuba abincin sannan ta shiga daki ta dauko masa maganin, Nafisa sai binta da kallo take Nabila tayi murmushi tace "Nafisa ki shigo ki salla ko" dan tabe baki tayi sannan tamike tabi bayanta, jiki a sanyaye tayi sallar Nabila tace "ki kwanta mana kan gado mijin naki ma yaje ya kwanta dan baya jin dadi" Nafisa ta girgixa kai tana cewa "a'a nan ma ya isa na gode" Nabila ta juya ta bar mata dakin dan ta fara jiyo kukan Ramla.

Bayan ya dauketa sun koma tambuwal da yamma ranar saida ya kwana biyu can dan kwantawa yayi ciwo ranar da zai dawo Nafisa tasa shi a gaba ko irin gidan Nabila da kayan dakinta ko yamaida ita sokoto ya bude bakinsa yace "Innalillahiwa'inna'ilaihiraji'un Nafisa..."





*Dr A.S. Zaki*

EXQUISITE WRITERS FORUM 
*SAFIYYAH GALADANCHI*

sadaukarwa ga yayata Billy galadanchi

 

SHAFI NA ASHIRIN DA TAKWAS 

"Wai anya Nafisa kinada hankali"? Dauke kanta tayi daga kallonshi tace "ai dole kace banda hankali, waccen ita ake so ita ake Nunawa soyayya nikuma ana nunamin kiyayya kasan bazaka yi adalci ba ka hada mata biyu" dogon tsaki yaja yace "kayan dakin da kika gani na Nabila nan gidan da can sokoto ko kobo na babu a ciki iyayenta suka yi mata in kina bukatar canji ki canza dakanki ko kije gidanku ki fada musu kina son a canza miki ko labule ban siya mata ke ko cokali, sannan batun kice zaki koma sokoto bata ma taso ba dan wallahi keda zama sokoto har abada saidai kije ki dawo badai ni in daukeki in kaiki ba, banda wannan zarafin, karki sake tayar min da hankali kindai jini" tashi tsaye tayi ta fita daga dakin kai tsaye dakin mama ta shiga tana fada mata  Bata ma lura da Baba yana zaune a dakin ba shuru yayi yana kallonta Mama tace "har abada dai ke bazaki daina korafi ba, Allah yasa da aka ce ki bishi cewa kikayi ke baki iya zama sokoto a rayuwarki sai yanzu dan kinaso ayi fitina, don Allah ki rabu dani da fitinarki ban iyawa" juyawa tayi ta fita tana maganganu Baba yayi murmushi yace "ai duk ke kika koya mata, koda aka kawo yarinyar nan yadda batada wayo ko kadan da renon kwarai kikai mata da wani zancen ake ba wannan ba, amma kika hada kai da ita kuka sa yaro a tsakiya, yanzu ya samu inda ake lelenshi dole hankalinsa ya koma can" shuru tayi dan tasan batada gaskiya.
Ya shigo gidan ya samu Nabila Bata nan kwantawa yayi ya dauki waya ya kirata tana makota ta shiga su gaisa dan tunda ta dawo bata shiga ba kuma sunje mata suna "bari in tafi ya dawo yaga bana nan" ta fadawa matar tana mikewa tsaye ta dauki Ramla, rako ta tayi har gate tana cewa "idan dai matar ta shigo zan kiraki amma kayanta sunada kyau wallahi" dariya Nabila tayi tana cewa "to sai kin kira".

Shiga gidan tayi tana ta sauri, kai tsaye dakinshi ta wuce ta sameshi zaune gefen gado, zama tayi bayan ta sauke Ramla tace "ko dai jikin ne muje asibiti"? Ya girgiza kai yana daukar Ramla yace "kidai bani madara insha mai sanyi" tana kallonshi tace "Ni fa bana son haka da kakeyi bafa a wasa da ulcer kar ka janyo wani ciwon" murmushi yayi yace "hajjaju ga sunan magani a wayata idan munyi salla ki raka ni na siyo" juyawa tayi ta fita sai taga babu madara ta ruwa saida ta tsaya ta hada masa ta gari da ruwa masu dan zafi tasa zuma kadan sannan ta jefa kankara takai masa.

Tare suka fita shi yake dauke da Ramla da take ta mikewa tsaye a jikinshi Nabila tana driving, kalamu wahid pharmacy suka je, bayan magani yaron da suka sama a wurin yace "Ranka ya dade ka bari ayi maka allurar malaria tunda ga zafin jiki" Nabila ta karbe zancen da cewa "don Allah hada kayi masa kwana uku fa yana kwance amma sai maganin ulcer yake sha" Dr A.S yana zaune yana dan murmushi dan gaskiya yasan bai da lafiya, tun daga ranar ita take kaishi ayi masa allura har ya samu sauki.

Kwanansa biyu tambuwal wannan karon dan yana ganin Nafisa ta cimma EDD dinta ya kuwa yi sa'a ranar daya kwana na biyu ranar ta tashi da nakuda sai dai basu samu zuwa asibiti ba ta haihu a gida, dalilin daya saka sukaje nan asibitin aka duba su ita da abinda ta haifa, sai da suka dawo gida sannan ya dauki waya ya kira Nabila ya fada mata, a lokacin ita kuma tana kwance bata jin dadin jikinta Mura takeyi mai tsanani fuskarta duk tayi wani iri, "nace zan iya zuwa gobe tunda muna hutun mid semester"? Har zai hanata saboda yaji muryarta ta masu mura sai kuma yace "Ki bari to zan turo modi yazo dake amma ki shirya da wuri dan abu zai zo yi sai ki dauko min kudin dana ajiye gida ma kinsn inda suke ki saka mai a motar" ta gyada masa kai tana cewa "to shikenan anjima kuma zan dan fita shago in siyo abu" yace "duk babu damuwa ki debomin kayan sawa na nan duk sunyi datti" tayi murmushi ganin yadda yake ta amsa mata da sauri yana cikin farin ciki kenan tace "to baka fada min me aka samu ba" ya sosa kai "Mace aka samu" addua tayi masa sannan sukayi sallama, a ranta tace to naga magaji ya zama magajiya su Nafisa sai Yaya kuma, tashi tayi ta shirya ta fita kayan baby ta siyo ta dan debi wasu cikin na Ramla ta hada sannan ta hada kayansu na tafiya, saida ta cika akwati babba da karami dan yanzu Ramla rarrafe take ba wuya tayiwa kayan jikinta datti, lokacin da taje tayi mamakin ganin Nafisa a gidan wai mamarta tace ta zauna tunda ai duk gidane, iyayi kala-kala takeyi musamman Idan taga Nabila haka kawai idan yana dakin Nabila sai ta aika a kirashi ko kuma ta aika masa babynta wai tana ta kuka ta hanata ta huta, ko kuma idan Nabila ta shiga gaida ita sai ta ringa hira da masu zuwa barka tana cewa "ai yarinya kam duk wanda ya ga ubanta ya ganta musamman hancinsu" ranar da tace haka wasu yan uwanta suna zaune dayar tace "aikuwa ni wadda na gani a wurin Mama yanzu tafi kama da shi har jikinsu" Nafisa ta tura baki tareda fadin "aiko baki san kama ba"  Nabila tana ganin abin zai zama rigima sai tayi musu sallama ta koma dakinta, dama Dr jiranta yake dan babu inda ya fita ranar, tana shiga ta cire hijab tana sanye da straight skirt na roba da top yabi ta da kallo kafin ya kirata taje kusa da shi yace "kibar me kike shirgawa haka" ta dan bata rai tace "Nima inata mamakin kibar nan wallahi amma anty Maryam tace dama idan mace ta haihu tana budewa haka" ya girgiza kai yace "wallahi se kika yimin kamar farkon cikin Ramla" da sauri ta kalleshi tace "badai kamar ciki kake ganin nake da ba" ya gyada mata kai ta dafe kirji tace "da na shiga ukku watan Ramla nawa da zan dauki wani ciki, don Allah ka bar wannan maganar babu wani ciki" ganin yadda ta gigice ta bashi dariya yace "to ai da yanzu yarki ta fara ciwo kema bazakiyi ciki haka kawai baki gane ba kawai kiba dai kikayi" ta zauna tana cewa "yanzu naji batu" shuru yayi yana kallonta dan shi dai ba likitan masu ciki ba amma bazai raba daya biyu ba ciki take da shi.

Nafisa ko bata ki abinda ta haifa ba amma ta dade tana bugun kirji zata haifi namiji mafi yawan kayan data siya duk na maza ne yanzu bata san ya zata yi da su ba gashi ta gama yayatawa cewa namiji zata haifa, amma ta dauki alkawarin bazata sake dagawa haihuwa kafa ba dan wata bazata zo gida ta sameta ba kuma ta fita yaya agidan...






*Dr A.S. Zaki*

EXQUISITE WRITERS FORUM 
*SAFIYYAH GALADANCHI*

_sadaukarwa ga yayata Billy galadanchi_

SHAFI NA ASHIRIN DA TARA

Ranar suna kuwa dakin shi ta shige tasha kuka sai da ta gaji dan kanta, wai baiyiwa baby komai ba na rabawa yan biki, shikuma yaci mata mutunci ya hada da cewa "idan kinsan ko wane abu zai faru tsakanina dake sai kin tayar min da hankali gaskiya zan maidake gidanku, ke abin naki ya wuce kishi ya zama hassada da rashin sanin ciwon kai, karki sake ganin abu a wurin Nabila kice sai na miki dan ko daya bani nayi mata ba, ko ruwa na siya mata sai na siya na kawo miki kema akan me zaki tayar min da hankali, kayan biki su sukayi abinsu inba dana zo nan nagani ba ko ganinsu banyi wurinta ba, mota koda na fara ganinta da abarta naganta, karatu da kikace zaki koma bansan ya zaki iya karatu bama yanzu bayan kusan shekara goma da gama secondary school dinki ko rubutu baki iya ba bazanyi asarar kudina ba itama bokonta da abinta na ganta kuma har yanzu babanta yana kula da karatun ta, komai nata sai kinyi irinsa, ke baki san ilimin zama da mutane ba Nabila tanada saukin kai fiye da tunanin ki da zaki dawo kan hanya babu abu daya nata da zata miki shamaki dashi amma fitinarki ta hanaki ku zauna lafiya, bana son sake jin sunan Nabila daga bakinki inba alkhairi zakii fada akan matata ba, wayarki ko sati uku batayi ba dan canza miki ita kuwa tun kafin na aureta take rike da wayar har fashewa tayi amma bata taba yimin korafi ba saike, wayarki tana lafiya lau kinbi kin Addabeni seda na canza miki tata ko chaji bata rikewa dakyau, ki gyara halinki ko kuma wallahi na gaji" yana gama fadin haka ya fita dan dama abu yazo dauka tunda dangin ta sun cika gidan, yana fitowa ya hadu da Nabila ta riko kula da hannu daya hannu daya kuma tana dauke da Ramla data makale mata yau, sunyi wanka tasa mata kaya iri daya da ita atamfa da aka mata gown ya rage sai aka yiwa ramla kanta rufe da hula idonta sun kara girma da fitowa saboda kwalli tana ganinshi ta fara mika masa hannu, ya isa kusa dasu ya dauketa yana murmushi yace "fita fa zanyi Ramlaty" Nabila ta danyi tsaki tace "Don Allah ka kaimin ita gidan Raliya in karasa abincin can, yaran duk sun gudu sai Aisha kadai kuma aikin da saura" ya mika mata ita yana cewa "kema kinsan bazata zauna ba ki goya ta dai" ajiye kular tayi ta karbeta ranta duk a bace tace "wallahi Dr banida lafiya a tsaye kawai nake bansan me yake min dadi ba" fuskarta ya dan kurawa ido kafin ya karbi Ramla yace "ki samu pcm kisha kila stress ne bari na bada ita Dakin Mama" ta amsa da to ta shiga part din Nafisa bata ganta ba ta dawo, sai karfe daya ta gama hadawa ta dauki nata takai daki sannan ta aikawa mama nata shima ta aika masa nasa Aishan da ta tayata aiki ta gyara mata tsakar gidan tayi wanka ta shirya sannan ta fita, ita kuwa da tayi wani wanka kwantawa tayi dan wani zazzabi ya rufe ta hayaniyar mutane ta tasheta hakanan tayi kokari ta saka kaya ta fita akayi hidima da ita sai dare da aka gama watsewa Dr ya shigo ya sameta kwance, ya ajiye mata Ramla daya shigo da ita yana cewa "tun safe fa yarinya nacan na gararamba hannun mutane ance an kawo miki kin maida ita da kayan da za a sauya mata" bata yi masa magana ba saboda yawun da suka cika mata baki, tashi kawai tayi ta nufi daki ta zubar a toilet ta dawo ta zauna tana bugewa Ramla hannu da take kokarin tura mata cikin riga ta kalle shi tace "wallahi takura min take gashi yau sai a hankali na kasa cin komai" dan matsawa yayi kusa dasu ya rike mata hannu yana cewa "yakamata mu koma gobe jumu'a ban yadda da wannan ciwon naki ba" ta dan yamutsa fuska tace "wallahi nima yau gaba daya jikina a mace yake" a ranta ta karasa da cewa 'idan ma shine a markada shi' "da nayi murnar hakan gaskiya a shekara uku nayi yara uku ai kuwa ba abinda zanyi sai godiya ga Allah" dan hararar shi tayi tare da cewa "saboda bakai ke wahala da cikin ba ko" dariya yayi dan shikam da gaske yakeyi koda abubuwa na neman

Please Login or Register in order to submit comment