Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya danyi sannan yace "Baba don Allah kayi hakuri, tare suka zo da Baba na tambuwal gashi a palo" matsawa yayi ya bashi hanya dan yaga kamar shima shirin dukansa yake, dakin da baba ya nuna masa ya shiga da sallama ya isko Mama ta tsaya a kanta ta inda take shiga batanan take fita ba, sallama yayi ta juyo ta kalleshi sannan ta kama hanya ta fita tana amsa gaisuwar da yake mata, zuwa yayi kusa da ita yana kokarin dagata tace "karka taba ni, burinka ya cika ai" bai saurareta ba ya tada ita tsaye yace "Nabila pls menene haka wai, nifa kinsan Banida alaka da wannan yarinyar, da zan saurareta da yanzu bake nake aure ba, tun kafin ki shiga jami'a take yawo wurina ban taba kulata ba, haka kawai zaki bari wata banza ta hadamu irin haka" cire hannunsa tayi daga kafadarta tace "ko ba ita ba ai baka yin adalci tsakanina da matarka" iska ya fesar daga bakinsa yace "muje gida dai yanzu" gaba tayi yabi bayanta ko sallama bata yiwa Mama ba ko ta karbo Ramla, Muhammad ma shi ya dauko shi dan baro shi tayi, suka shiga mota suka wuce.

Mama tana kallonsu ranta a matukar bace, bata san dalilin wannan tashin hankali ba amma dole taje har gida ta samu Nabila, bata lamunci rayuwar aure irin wannan da matsalolin da zasufi karfin mata da miji ba har sai kowa yaji. Bayan sun isa gida palo ta zauna tana ci gaba da zubar da hawaye fuskarta duk ta kumbure ga shatin Bulala nan har kan idonta da bisa kumatu ga wuyanta ma duk sun kwanta mata a jiki, zama yayi gefenta ya ajiye Muhammad ya rike hannunta yace "Don Allah kiyi hakuri, banzaci abin zai kai haka ba, dama haka baba yake, da aurenki baki wuce duka ba Nabila, ji yadda jikinki yayi" shuru tayi masa saboda haushinsa da take ji, yama rasa ta inda zai kama sai hakuri yake ta bata ta kyale shi ya sake cewa "Nabila wallahi tunda nake a rayuwata ko matar dana so aure kafin Nafisa ban mata irin son da nake miki ba, mu bawa matsalolin nan baya kinsan wanene ni kuma na yaddq nayi laifi da zan miki fada har na canza salon zamanmu akan abinda kika yiwa nafisa amma zan kiyaye bazan sake ba, sannan karki sake cewa na sakeki kalmar tayi muni kinji, kiyi hakuri bazan sake ba don Allah mana ki dawo yadda kike da" sai lokacin taji ranta yayi sanyi harta kwatar da kanta jikinshi tana sauke ajiyar zuciya, ruwan wanka ya hada mata ya dauketa kamar jaririya ya kaita toilet din, Muhammad ya dauka ya shiga dashi dakinshi ya cire mai kaya ya masa wanka yana kallon yadda yake watsa mai ruwa masu dan zafi amma baccinsa yake da alama baida rigima, cikin towel ya dano shi ya dawo daki dashi ya shirya shi har lokacin bacci yake, dakinta ya koma ya sameta a zaune da towel, wani cream ya dauka ya shafa mata ajikinta duk inda bulalar ta kwanta yasa mata maganin ciwon ido sannan ya rurrufe gidan suka kwanta, cikin kunnenta ya rada mata magana da sauri ta tashi zaune tana cewa "zamuje asibiti gobe pls" ya maida ita ta kwanta yace "ba zaki samu wani cikin ba yanzu kinji kedai ki taimaka".

Da wani kalar ciwon jiki ta tashi ko breakfast bata iya hadawa ba sai masa yaje ya siyo musu suka ci shikam dayake yanada aji yayi wanka ya fita, palo ta dawo ta kwanta tana kallo har sha biyu tajiyo ana kwankwasa mata kofa, hijab dinta ta saka ta dauki Muhammad taje ta bude bayan ta tambaya waye taji muryar mace, sauke idonta tayi kasa ganin su Mama harda anty Maryam da anty nusaiba...




*Dr A.S. Zaki*

EXQUISITE WRITERS FORUM 
*SAFIYYAH GALADANCHI*

_sadaukarwa ga yayata Billy galadanchi_

SHAFI NA TALATIN DA BIYAR

Basu hanya tayi suka shigo anty Nusaiba nayi mata wani irin kallo, irin wanda yake nuna ni banma ga kin daku ba, Mama bata zauna palo ba saida ta isa dakin Nabila ta zauna gefen gado tare da ajiye Jakarta duk sai suka bi bayanta, Nabila tana shiga dakin ta shimfide Muhammad tareda zama tana gaida su sannan ta tashi da nufin kawo musu ruwa Mama tace "zo ki zauna ba dadewa zamuyi ba" dawowa tayi ta zauna kusa da Mama ta kalli fuskarta da har lokacin akwai shatin Bulala wanda har cikin idonta yayi ja ta daure fuska sosai tace "So nake ki fada min matsalarki da ta saka har kika bar gidan nan jiya da sunan yaji" ta sauke kanta kasa bata ce komai ba saida mama ta sake cewa "kina fa jina ko nima so kike in dake ki" hawayen dake kokarin zubowa daga idonta tayi kokarin maidawa amma saida suka fito, a hankali tace "Mama duk fa akan Nafisa ne, idan yaje ta bata masa rai sai yazo nan yana neman saukewa akaina nida banji ba bangani ba, bansan meya hadasu ba ranar yazo yanata cin rai babu walwala sai yaji ina rigima da Nana sule dan ban fada mata na haihu ba, kinga mijinta ya kwasota suka zo nan mukayi magana komai ya wuce amma shi bai wuce a wurinsa ba bayan kafin zuwansu babu irin cin mutuncin da baiyimin ba, Nafisa lokacin data haihu ko tsinke bata bani ba niko ban fada masa ba amma nace sai na rama shine fa dan ban bata kayan sunan Muhammad ba taje ta zugo shi yazo nan kamar ya dake ni daga karshe yabar min gidan babu sallama yayi sati daya tambuwal ko kirana bai taba yi ba Mama jego fa nake a lokacin ciwo nayi har asibiti zasu kwantar dani na Rokesu  suka bani magani na tsare sha har naji sauki bai sani ba, bayan ya dawo kuma yadda kika san baki muke nida shi iyakacin sa gaisawa dani shima dan nice nake kokarin gaidashi badan haka ba dani da banza duk daya, shekaranjiya nacemai zamuje karbo notification nida Nana yace idan naje in sameshi office, dama akwai wata yarinya dake sonshi can makaranta ta taba zuwa office din ina ciki naga bai kulata ba ashe nice mahaukaciya jiya ina shiga na samesu tare a office dinsa bance komai ba na fito muka je mu kayi abin da za muyi.

Na dawo gida na sameshi ya tsareni da maganar niko dama jira nake saboda haushinsa na kwanakin shine kawai na kwashi kayana zani gida saiya kira anty Nusaiba, wallahi mama ji nayi ko ganinsa bana sonyi a lokacin inna dawo gidan nan zan iya mutuwa kila" shuru Mama tayi kafin ta lalabo abin cewa sannan ta samu bayan dan lokaci tayi magana "Nabila bari in fada miki abinda baki sani ba, babu abinda yake saurin gurgunta Aure kamar yaji, karki sake barin gidan nan da sunan yaji har yafi ki shiga daki ki rufe kanki akan ki fita kije wani gidan ki kwana koda dakin uwarsa ne ba taki ba, ki ajiye zancen Nafisa gefe, sunanta ya daina shiga cikin matsalolinku ya rage garesa yayi adalci ko kar yayi tsakaninsa da Allah ne, sannan ban sanki da wannan Hali ba da zaki biye mata dan ta hanaki kema ki rama menene acikin kayan bikin da zaki hanata? yanzu ba gashi komai ya kare ba? Karki sake yin haka, idan mijinki yana fushi dake kokari za kiyi ko kinada gaskiya ki danne zuciyarki ki bashi hakuri idan kuka sabawa juna da fushi mai tsawo zata kai lokacinda koda daya yayi fushin daya bazai damu ba dan haka matsala bazata samu solution ba a tsakaninku saima tayita karuwa, haka yaji yake inyasan ya bata miki rai karshen abinda zakiyi ki kwashi kaya kibar gidan shi kuma yaje bikonki kindawo to hakan zai zamar muku dabi'a ko kin tafi bazai damu ba dan yasan zaki dawo, sannan maganar wannan budurwa tashi ki kauda kanki karki sake bari wata ta shiga tsakaninki da mijinki koda aurenta yace zaiyi  to barshi yayi wallahi mace bata isa ta hana namiji aure ba" Anty Nusaiba ta karbi zancen da cewa "to ba gani ba Mama? Kabiru bankosan ankai mai mata ba a boye yayi aurensa sai da ta hadasu dama yar gidan masu sara suka yaje ya dauko, bansan yayi aure ba sai da ya saketa ta dauko yar da suka haifa ta kawo min ta ajiye, yarinya jaririya sannan ya dawo yana yimin muzurai, wallahi Nabila kinsan Allah guda bantaba yi masa maganar ta ba kuma bai gani a fuskata ba, Allah kadai yasan darairan danayi ido biyu saboda damuwa na kasa bacci, dakyar ya samu ta karbi yarinyar nan tayi shekara daya ta maida min ita, kin ga kuma yarinya nan har ta girma, shi kuma har gaban abada bazai manta da halaccin danayi masa ba sau dayawa zai min kyauta da babu dalili sai daga baya yace min shi haka kawai yake jin bari yayi min kyauta saboda bai taba ganin mace irina ba, bana rigima dashi ko lokacin su mama basu san anyi ba sai daga baya bamu taba zaman sulhu dashi da iyayena ko nashi ba" Mama sunfi awa biyu gidan nan duk inda tasan matsala na iya bullowa sai da ta gyara ta, ta nuna mata kartayi sakaci da damar ta sannan ta tashi tace su wuce, Nabila ta rakasu tanajin kamar kar su wuce, sai da taga motar su ta bace sannan ta dawo cikin gidan ta dora abincin rana tayi wanka ta saka doguwar riga, ta kasa sabawa da skirt dinda yake so, duk da ta rame rigar tayi mata kyau saboda tana shayarwa kirjinta ya dan ciko sai dai fuskar da dole sai ta dau lokaci.

Tunda ya dawo yake mata wasu salo kala-kala ita mamaki ma yake bata, wato yasan abinda yayi bai kyauta ba kenan, yana cin abinci yake fada mata "naje can gida wurin Baba dan kinsan baba na tambuwal sau yau ya wuce" Ta dan kalle shi tace "tashin hankali ya hana ma na tuna shi ya kawoni" Dr yayi murmushi yace "ai gara da yazo saboda Baba bai huce ba cewa ma yake sai kin kawo key din motarki baza a sake baki mota ba sai kinyi hankali, shi kuma baba na tambuwal Maganar da yake duk nafiki laifi kuma na yarda da hakan, yanzu dai duk sun Hakura" ta sauke ajiyar zuciya bata ce komai ba, sai da ya gama cin abincin sannan yace "zaki rakani Abuja"? Ta girgiza kai alamar a'a "saboda me" tayi shuru dan tasan idan ta bishi boni zata ci ta kamar yasan mai take nufi sai ya kawar da zancen da cewa "idan munje wajen wata likita ta miki wannan Allura Babu matsala ko? Ina nufin ko sai wurin mama" ta girgiza kai tana cewa "ai duk daya ne idan dai akwai inda zamu ba matsala" "ok dan gidan Hajiya luba naje da safe tace na kawo ki wajen makociyarta likita ce harma sunyi magana" sai lokacin hankalinta ya kwanta, da dare ranar ya kaita matar tana ta tsokanar ta tana cewa "gaki yarinya dake bazaki bari kihi haihuwar lokaci daya ki gama ba sai ki huta duka" ta girgiza kanta tace "Mama nidai ina bukatar hutu koda na shekara hudu ne, ko yanzu ina wahala ga jariri ga yarinya bata wani girma ba" matar ta gyada kanta tace "gaskiya ne gara ko ba tazara mai nisa a samu shekara biyu zuwa uku a tsakani, sun dade tare ma tana bata shawara da bata misali da yayanta yadda sukayi tace dayar ma daga yin arbain ta samu wani ciki yaran sun tashi kamar twins.

Suna tafiya a mota yace "to yanzu fa zamuje"? Ta dan kalleshi kafin tayi magana yace "karki damu, gida ne zamuje gidan Ali harda Ramla zamu je kuma inada daki da palo a gidan tun ban gama karatu ba nayi zama can, kuma ina yin aure yasa akayi min gyaran part din karki damu ko kiyi tunanin hotel zamu zauna" tayi dariya mai dan sauti tace "ni tunani na baije can ba" shima dariyar yayi yace "to banda gobe zamuje tambuwal mu kwana biyu idan mun dawo sai mu wuce, goben sai kije ki dauko Ramla" ta gyada masa kai tana kallon Muhammad daya bude idonsa yasa hannu a baki yana tsotsa tace "baccin yaron nan fa yayi yawa yanzu ma saida na fadawa matar nan tace baida matsala ai har yanzu jariri ne" ya riko hannun yaron yana cewa "wata rana sai kinyi matsarsa yayi bacci yaki yi" cire masa hannun tayi tana bashi nono tace "ai Anty Maryam tace min inada aiki dan yaro namiji akwai kiriniya niko na saba da waccen yar sululu din sai naci amma batada kiriniya" fuskarta ya shafa yace "ke ta biyo ai".

Suna isa gida ta shiga dakinta shima yayi nasa dakin, drawer dinda take ajiye abubuwanta ta bude ta fito dasu duka duk wanda ta yadda dashi saita ajiye gefe wanda bata bukata ta maida shi, online class din Billy galadanchi data shiga ta nemo group din ta duba wani hadi da aka koyar waishi butar alfarma da wani da ake sha ta dudduba kayan taga na hadin duk tanada na dayanne dai sai ta nema ciro kayan tayi taje kitchen ta hada abubuwanta tasha ta boye sauren wannan hadin kuma tana cikin nikawa a blender ya shigo yana tambayarta menene wannan dakyar ta samo amsa tace "maganin basir ne" kofi ya ajiye gefenta yace "bani nima insha" ba yadda zatayi ta zuba masa tana cewa "da kankara yafi dadi" ya kuwa dauko ya fasa musu, ita data hada dan kanta kadan tasha duk ya shanye ya sake cewa "wannan ai furnace ko? Gaskiya maganin yanada dadi kiyimin list din kayan da ake hadawa insiyo" dariya ta hanata amsa masa sai daga baya tace "shikenan ka bari da safe" washe gari kuwa har ya fita ya kirata a waya yace "ki turomin mana" dole babu yadda ta iya ta tura masa, lokacin ta goya Muhammad ta fito dole napep zata hau dan ba mota tana tambuwal, ta fito tana takawa da kafa zuwa titi makociyarta ta fito da mijinta zasu fita su suka kaita har gida taji dadi dan tana gudun kwasarwa Muhammad iskan Napep.

Koda taje baba baya nan ta fadawa mama zancen tafiyar su taji dadi sosai tafito da kayan data siyawa su Ramla ta bata kaya ne da yawa dan tace ita yanzu ta daina tari ta wanke duk yaranta baffa ya rage kuma shima da rangadeden gidansa a kusa dasu.

Washe gari da azahar suka isa tambuwal yana sanye da yadi brown sai kamshi yake itama Nabila tasa leshi brown saidai yafi nashi haske ya karbar mata Muhammad itako ta dauki yar anacenta suna shiga gidan suka hadu da Nafisa ta ciyo gayu da leshi ja da bakin mayafi yarinyar ta na hannunta itama taci kwalliya wai biki ake gidansu shi yama manta, Nabila ta saki fuskarta tana gaisheta ta amsa mata can ciki ajiye ramla tayi ta karbi Babyn tana cewa "yar masu gida sai ina"? Nafisa ta kalli Dr tace "ashe kuna tafe" yace "eh kefa ina zaki da rana" tace "walima ake yau da karfe hudu kafin magrib ma na dawo" ya gyada kai kawai.

Tadan kara minti talatin kafin ta fita, ta kuma dawo da wuri nan take jin wai Abuja zasuje shida matarshi, a ranta tace "akwai babbar bala'i kenan".



*Dr A.S. Zaki*

EXQUISITE WRITERS FORUM 
*SAFIYYAH GALADANCHI*

_sadaukarwa ga yayata Billy galadanchi_

SHAFI NA TALATIN DA SHIDA

Tsugune tayi gaban murhu tana kokarin kunna gawayi tana ta jera tsaki ta juyo a dan hasale tana kallon Ramla tareda cewa "kije mana ki zauna ganinan zuwa, da wannan nacin naki zanji ko da haushin kunna gawayin nan dayaki kamawa" matsawa tayi kusa da ita ta rike mata kafafuwa ajiyar zuciya ta sauke tareda daukar ta tana cewa "in kika takuramin ruwan sanyi zan watsa miki kiyi bacci niko na hakura da wankan" Dr ya shigo yana cewa "wallahi kar ki mata wanka da ruwan sanyi" turo baki gaba tayi tana cewa "gawayin fa yaki ya kama ni nagaji" wayarsa ya ajiye kan tagar kitchen ya duruka ya gyara gawayin yadda iska zai shiga saiya kunna ashana da ledar data dora sama yace "muje ki sallameni kafin ki fito ya kama" Tabi bayansa tana cewa "kaifa ango ne yau yakamata kaje da wuri" bai tsaya palo ba ya wuce daki yana cewa "indai samu nima inyi wankan nan, inaga nine zan watsa ruwan sanyin nan" ta sauke Ramla tana cewa "kaga yadda mai idon nan kamar idanun mota ta makale ni yau, garama kayi ta kanka da wuri wallahi ko kadan bata jin zata sassauta min" ya taba kumatun Ramla yana mata wasa ta sake rike Nabila ya shiga toilet yana cewa "dama bance zan dauke ki ba" kusa da Muhammad Nabila ta ajiyeta tana cewa "zauna ki kula da kaninki yanzu zanje in dora mana ruwan wanka " ta kalli kofar toilet din tana cewa "kabari na dora ruwan mana karka watsa ruwan sanyi" ya fito yana gyara hannun rigarsa yace "ai nama fasa wankan bari kawai inje in kwanta" ya nufi kofar fita yana mata sallama binshi tayi ta rufe kofar ta bayan yafita tana dawowa tace "ai dole ka gudu kafin matarka ta yomin sallama" bata kwanta ba sai karfe goma sha daya, babu dadewa bacci ya dauke ta saboda gajiyar da tayi.

Zama yayi gefen gado ya kalli Nafisa yana cewa "ki samo min zanin gado sabo mana, wannan ya dade baki canza ba" ta gyara kwanciyarta tana cewa "aikam duk sunyi dauda sai dai gobe a wanke dan bansan da zuwanka ba" kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa, can tace "Nima fa Abuja nan binku zanyi" da mamaki ya kalleta yace "kamar yaya? Nace zanje dake ne"? Ta turo baki tace "sai yar gwal zakaje da ita ko? Baka son kwanciyar hankali kenan"? Kwantawa yayi ya ja bargo tareda kallonta dagaske yace "ke idan kika sake tada wannan maganar zan tabbatar na saba miki Nafisa"  turo baki tayi ba tareda tace komai ba, washe gari cike da haushinsa ya shareta Nabila ma da taga tayi mata magana bata kulata ba sai ta share ta, Ranar da zasu tafi kuwa da zungureren akwatinta ta fito ta cake bakin kofar gida.

sunyiwa mama sallama suka leka part dinta bata nan harda padlock ta saka ta rufe yana mamakin inda taje amma yasan ba nisa tayi ba, suna fitowa suka ci karo da ita Nabila ta dan kalleshi cike da haushinsa meyasa bazai fada mata da matarsa ya shirya tafiya ba, tayi kudurin idan suka isa skt bazata bishi ba yaje da Nafisa din, ta daidaita fuskarta tana karasawa kusa da Nafisa taji yana cewa "ke ki maida kayan nan gida na fada miki ban shirya zuwa dake ba idan zanje dake basai kin fada min ya kamata ba" ta dauke kai tana juya masa keya tace "billahillazi saidai a fasa tafiyar nan, munafurci kenan, ni za a nunawa iyayi da kilibibi duk inda zaka tana biye dakai diiiiii ni anbarni a kauye dan hadani da surfe da kauyanci, wallahi kafata kafarku inga karshen bariki da boko" cike da mamaki yace "ke matsa ki bani hanya kafin zuciyata ta rufe in dakeki" "duka na yaushe kuma"? Ta fada tana yi masa kallon ukku saura kwata, Nabila ta ja hannun Ramla ta dan raba gefensu zata fita ta jirasu a mota isan sun gama rigimar su same ta acan, tana tausayawa Nafisa da irin hukuncin da Dr zai yanke dan ita yanzu ta daina fada yana fada komai zaiyi ita nata ido ne sai kuma biyayya, tana cikin wannan tunanin taji an shakurota tareda wurgata baya, kafarta ta karkace dan batasan da zuwan lamarinba tayi baya zata fadi da sauri ta saka hannu daya ta dafe Muhammad dake kafadarta dayan hannun kuma tayi saurin dafa bayanta dan ta tare kanta amma sai ta fadi kan hannun, tana dagowa a zafafe ta juya ta kalli Nafisa tareda sauke mata maruka guda biyu a jere sai lokacin taji zafi a hannunta ta yarfa tana cewa "idan zakiyi irin wannan haukar ta tsaya iya kan mijinki wata kila shi zai iya dauka dan kin saba yi masa yana kyaleki, daga nesa ki tsaya ki duba dakyau tareda tabbatar da gonar wa zaki shiga, billahi banida kyau zan iya illataki, ke meyasa kanki baya dauka ne, naga alamar ko makarantar da kika je kina cikin yan cikon benchi ne kawai Jahila" wani irin zaburowa tayi Nabila taja baya tana cewa "ban iya hada jiki da kazama irinki wacce idan jikinta yaga ruwa wata kila wankan janaba ne tunda kin iya kwanciya da miji" tana kaiwa nan ta dago Ramla dake yashe a kasa tana kuka ta maida mata da takalminta ta nufi mota, Dr ya dankare tsaye yana kallonsu yana mamakin wai duk akanshi ake wannan, hannun Nafisa yaja ya shiga gida da ita ya kaita dakin mama sannan yace "Mama keda kika kawo yarinyar nan, ki maida ita gidansu wallahi tallahi indai na dawo na sameta gidan nan a bakin aurena da ita kenan, taje gida sai idan na nemeta" ya juyo ya fito ya baro mama cike da mamakin wannan lamarin dan ita bata san mai yake faruwa ba, a mota ya iske Nabila tana ta aikin rarrashin Ramla dataji ciwo a kafa harda jini ta saka tissue tana goge mata tana cewa "kiyi shuru kinji yanzu zan sa miki magani ya daina ciwo" shiga motar yayi ya dago kafar yana cije lip dinsa na kasa sannan yace "bari a siya plaster chemist a rufe mata wurin" ta sauke ajiyar zuciya tayi shuru tana jin har lokacin gabanta yana faduwa dan bata taba tunanin haukar Nafisa takai haka ba.

Sun kama hanya ya sa hannunsa daya ya riko nata, ta dago ta kalleshi yace "kiyi hakuri na rasa ya zanyi da ita" ta danyi murmushi tace "bakomai, watarana ko ance tayi bazata yi ba, kayi mata uzuri kishi take kuma akanka ne" ya girgiza kai yana cewa "Nayita yi mata uzuri Nana Aisha dole na nuna mata yanzu ta kaini bango, bata duba akwai yara ba ga jariri a hannunki take kokarin illata mini ku, ta taba Nana Aisha Nabila mace mafi soyuwa a wurina, wacce bata juri fushina data san daraja ta, Nafisa tayi karfin halin wurga min ke haka dan ta halaka mini ke, ba saboda ni take yi ba kuma saboda ke ne zan nuna mata kuma bazan bari tayi min haka ba" hannunsa ta sake rikewa ta kalleshi sosai tace "pls Dr think twice, gani take kamar kana fifitani akanta don Allah kafin ka yanke hukunci ka sassauta mata, kuma bana son kace komai yanzu ka bari ka huce" hannun yakai bakinsa hayi kissing yana cewa "that's the essence of marrying a wise woman, I love you my lady" tayi dariya tace "yeah I can see, i'm proud of you" ya rungumota daga gefe yana cewa "yau idan mun isa gida ki hada kayanmu da daren yau zamu wuce" taji wani dadi ya mamaye ranta suna isa gida ta hadawa Ramla friso shikuma ta hada masa cornflakes ta hadawa kanta suka sha tareda sake yin wanka ta hada musu kayansu sannan ta fara shiri, jallabiya ta dauko maroon tanada adon stones da igiya ta saka ta daure tareda sa hula baka ta shafa kwalli da hoda da janbaki kadan ta fesa turaruka, ta sawa Ramla jeans baki da riga maroon tayi mata parking gashinta tasa mata head band baki ta shafa mata kwalli Muhammad kuma overroll ta sa masa baki mai digon maroon ta kwantar masa da gashinsa dan ba ai masa aski ba, suka fita palo Dr ko bakin yadi ya saka da brown din hula da takalmi, sai lokacin taga yayi kiba tabishi da kallo tana cewa "wannan kyau haka sai kace mai shirin zuwa zance" yayi mata hararar wasa tareda fadin "ainine ma nake tunanin hanaki zuwa Airport a haka" tayi saurin fita tana cewa "nidai muje" Ramla ya dauka suka fita ya rufe gidan yana cewa "driver din gidan Hajiya luba zai kaimu na bashi key din motar ki yace zaije tambuwal ya dauko yakai can gidan" ta gyada masa kai kawai.

Motar

Please Login or Register in order to submit comment