Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi masa yawa amma ya tabbatar bazasu gagareshi ba.

Washe gari da Rana suka kama hanya tana ta mamakin Nafisa ko Cincin bata bata ba balle Naman suna ta dai ga Dr ya mika mata roba mai dan girma yace ta ajiye masa bayan mota taji zafi a robar da alamar Naman ne dan yanzu ake soyawa, shikuma yayi tunanin ta bata dan haka baiyi magana ba.

Suna isowa skt gida tace ya kaita zata ga mama amma ya dan jirata, tausayinta ya kama shi yabi bayanta da kallo danshi sarai wallahi yake hango ciki a jikinta, a zaune ta samu mama da takewa Maryam Fada akan yawan zuwa da take gida ka cikinta ya tsufa itama cikin yayi mata shigar ba zata dan yaronta bai shekara biyu ba tunda bayan auren Nabila ne ta haihu, Mama ta daga kai ta kalleta tace "yan biki kun dawo" tace  "Mama mun dawo, na dawo da rashin lafiya, jikina babu karfi ga zazzabi nake wuni dashi ko miyau ban iya hadiyewa" Mama ta rike baki tace "ohh ni wayannan yaran, haka kuka yo gado a tare, bari dai kiyi gwaji a gani" ta dan bata rai tace "Mama ni wallahi banson ciki idan ma shine zubar dashi zanyi" wani kallo mama tayi mata tace "haukar taki ta dawo ko? Zubar da ciki shege ne? Bazaki zubar ba kuma insha Allahu ciki ne dake" ta fada tana mikewa, hawaye suka zubowa Nabila tace "Anty Maryam yanzu ya zanyi da Ramla" tsaki tayi tace "ni mutuwa kika ga nayi, ki daiyi a hankali ni nace ina haihuwa roba za a samun dan wannan pills din basa yimin" komawa tayi ta kwanta kan kujera tana fashewa da kuka ta rufe fuskarta da mayafinta...




*Dr A.S. Zaki*

EXQUISITE WRITERS FORUM 
*SAFIYYAH GALADANCHI*

_sadaukarwa ga yayata Billy galadanchi_

SHAFI NA TALATIN




"Meya faru take kuka haka ko dukanta kuka yi"? Baba ya tambaya dan shigowarsa gidan kenan, Mama ta fito daga dakinta tana cewa "kukan iskanci mana" zama yayi gefenta yana kiran sunanta amma kunya ta hanata amsawa, ya kalli mama da alamar neman karin bayani dariya tayi tace "wai ciki nake ganin take da shi, to test zatayi da PT" sai lokacin yaji hankalinsa ya dan kwanta ya kalli Nabila yace "shine kikewa kuka haka kamar an dake ki? Baki san haihuwa baiwa ce da kyauta ba a wurin Allah, kinsan Hamdiyya dake zamfara shekara goma sha bakwai da aurenta ko bari bata taba yi ba, ga example a cikin gidanku ma hakan bazai sa ki godewa Allah ba? Kinga Maryam ma ai yaronta gashinan shekara daya da wata shida ne ko takwas za ai masa kani ko kanwa amma baki ga tayi wannan damuwar ba, Malama tashi kije ki gwada don Allah kuma banson inji kince zaki zubar" Mikewa tayi tana goge fuskarta ta shiga dakin Mama Baba kuwa daukar Ramla yayi ya wuce da ita palon shi daga nan ya sake fita waje inda yaga Dr zaune a mota, fitowa yayi daga motar ya nufi wajen Baba "Nabila na samu tana ta kuka a cikin gida" Dr yayi dan murmushi yace "ai tun kafin mu iso take hawaye" Baba yayi murmushi yace "to ka dai tsawatar mata dan mata duk hankalinsu zasu iya shuka maka hauka, kasa ido akanta kar taje ta zubar da shi" Dr ya dan sunkuyar da kai tareda Fadin "ai bazata iya zubarwa ba kawai dai damuwa ce tana sabawa shikenan" hira suka danyi sai gata ta fito fuska a daure, Baba ya sake ja mata kunne sannan suka wuce, suna zaune a mota ta kalli Dr tace "zan zubar da cikin nan" bata rai yayi ya kyaleta kamar ba dashi take magana ba, ta sake cewa "gobe zanje scanning, indai bai kai wata uku ba zubar da shi zanyi" kwafa yayi ya ce "Allah ya sa ki zubar dashi kiga kalar tawa haukar data fi taki" kallon fuskar shi tayi dan ta dauka zai goyi bayanta saboda labarin maza da take ji akan rashin son tara yaya tayi zaton yana cikinsu balle ma shi da yakeda mata har biyu "ko tausayi na baka ji? Wallahi yadda nake ji ko cikin Ramla banyiwa laulayi haka ba, kuma daga iya rarrafenta ko tafiya bata iya ba sai a yayeta kofa abinci yanzu ne ta fara ci" dan juyowa yayi ya kalleta "ko ina tausayinki bazan barki ki zubar da cikin halak ba, koda shegene bazan bari a zubar ba balle dan sunna, duk Jan kunnen da Baba ya miki baki ji ba, Ramla bazaki yayeta ba gobe idan kika je asibiti za a bata magani itama" shuru tayi ta kyaleshi dan bataji a ranta zata zauna da cikin ba, bata sake kula shi ba dan suna zuwa gida ko abinci bata nema ba ta kwanta Ramla na wurinsa shima ya share ta.
Washe gari da safe ta shirya sai ya kaita wata private akayi mata test na fitsari dana jini sannan ana ganin ciki suka tura ta scanning, sai ga ciki da wata hudu, kuka ta saka mishi duk ta janyo idanun mutanen wurin, jan hannunta yayi suka koma wajen likita ya rubuta mata magani harda Ramla sannan suka wuce, babu kalar lallashin da bai mata ba taki ji har dare ranar ko ruwa ta kasa sha dan ta sawa ranta damuwa, shikam dama fita yayi bai wuni gidan ba bayan ya dawo da ita, sai dare ya dawo ya sameta zaune a palo ta buga uban tagumi ya zauna da nufin sake lallashinta amma sai ta sake rokonshi idan da hali su samu likitan da zai iya zubar dashi, da zuciyarshi ta kawo sai ya daga hannu zai kwada mata mari sai kuma ya fasa, lokacin daya fara fada sai jikinta yayi sanyi yace "kina zubar da cikin nan ki tabbatar kina wasa da igiyar aurenki kenan, ashe bakida hankali ban sani ba, ana ga Annabi kina runtse ido, nace bazaki zubar ba kiyi kokari kuma kiga kin kaini bango kinji, yar rainin wayon banza kiyita kukan har hawayenki su kare" ya fada tareda bar mata palon, da sauri ta fada toilet din da ke palon saboda fitsarin daya matseta amma saida ta fara shi a tsaye kafin takai ga cire pant, tsoron daya bata daga hannu da niyyar dukanta da kuma sakin da yace zai yi mata inta zubar da cikin, wanke jikinta tayi ta fito ta dauke ramla datayi bacci a palon ta kaita daki kukan ma kin zuwa mata yayi, ta dauki wayarta ta hau online cikin sa'a kuwa taga kawarta online babbar mata ce yar bauchi a wani group na girki suka hadu matar tanada yarinya babba har ma ta aurar da ita, gaisawa sukayi cike da kwarin gwiwa da tunanin bazata samu mummunar shawara daga wurinta ba tace "momy akwai damuwa fa" Matar tace "ai shine nace kwana biyu ban ganki online ba ko lafiya" Nabila ta ce "Momy wallahi banda lafiya kuma kishiyata ta haihu naje can garinsu jiya muka dawo" 
"Subhuhanalillahi meyake damunki Nabila ko dai ciki ne dan tun wata biyu da suka wuce da kika sa hotonki status wallahi kinmin kamada masu ciki" dan murmushi Nabila tayi sannan tayi mata VN ta fada mata abinda ya faru har yanzu amma bata sanar da ita yace tana wasa da igiyar aurenta ba dan ko ita bata son tunowa da kalmar balle ta fadawa wani ita, matar ta tura mata VN itama tayi mata fada sosai sannan tace "kafin gari ya waye idan kinsan mijinki mai saukin kaine kije ki bashi hakuri, idan kinsan yanada wuyar saukowa kyaleshi harda safe amma lallai saikin bashi hakuri, yo ko ba dan tsoron mijin ba bazaki ji tsoron Allah ba idan kikaje wajen zubar da shi kika mutu fa? Kinga ki rufawa kanki asiri da iyayenki" hawaye data samu suka zubo mata ta share tace "Ni naji bazan zubar ba Amma momy ko tausaya mini bayayi fede ni fa akayi aka ciro Ramla ina jin tsoro idan ciwon bai gama warkewa ba kuma ace na sake yin wani ciki idan yayi girma ya zanyi kuma banson ace za a sake yanka ni" tunani tayi taga gaskiya akwai wannan amma ai babu tabbas sai ta fara kwantar mata da Hankali "ba lallai ya kasance haka ba indai kinji wata matsala da wuri kije asibiti kuma ba mamaki wannan ki haihu da kanki tunda dama wancen rashin wani a kusa ne ya janyo matsalar ki kwantar da hankalinki kinji, yanzu ki tashi kiyi abinda nace ni kwantawa zanyi dan gobe ina da tafiya zanje kano ne wajen wani aiki" Nabila ta ce "to Momy Allah yasa wata rana kizo sokoto" dariya matar tayi a fili tare da cewa "sokoto nisa sau biyu na taba zuwa kinsan baban su yar uwarki dan sokoto ne inya tashi zuwa sedai yazo da yaransa nikam ban jure wannan zaman mota amma ko dan saboda in ganki insha Allahu in zasu zo zan biyo su" sallama sukayiwa juna matar ta tafi off ita kam sai da ta sake dudduba wasu massage dan jikinta a mace yake kafin ta tashi tayi wanka tasa kayan bacci Ramla ta dauka ta Nufi dakinsa koda ta shiga yana kwance da waya a kunnensa da alama da Nafisa yake magana dan taji yana cewa "ina mai sunan goggo" ajiye Ramla tayi ta gyara mata katifarta a kasa sannan ta daukota zata shimfide ta sai ta tashi, kuka tafara dan yunwa ta tashe ta, Nabila ta dauketa tana bata Nono amma daga ta fara sha sai ta bari dan babu komai a nonon tunda uwar taki cin komai, data fahimci abinda yasa take kuka ga fuskar Dr dayake juyowa yana kallonsu babu alamar sauki gareta da alama kukan yana damunsa sai ta fita palo ta hada tea tana sha bawa Ramla bayan sun gama ta dawo dakin har lokacin waya yake cikin Ranta taji zafi dan kamar da gangan yake yi, hijab dinta data ajiye ta dauka tasa ta sake fita daga dakin kan doguwar kujera ta kwanta tana dan lallaba Ramla ta koma bacci kusan minti goma sha biyar ta sake nufar dake sai ta jiyo shi yana cewa "kifa kama yarinya karki koya mata fitina da kukan banza irin naki" dakinta ta nufa wannan karon ta dauko baro ta dawo ta shimfida kasa ta kwanta tareda kwantar da Ramla, rufe idonta kawai tayi amma baccin nan yaki zuwa, juyawa tayi tasa fuskarta karkashin kujera ta fara kuka har saida taji ta gaji tayi shuru, Ranar baccii rabi da rabi tayi shi dannko Ramla sau uku tana farkawa da kuka jikinta yayi zafi da alama zazzabi take, sai da ta bata magani kusan asuba sannan ta samu tayi bacci mai nauyi.

Dr kuwa da gangan yayi haka dan ya lura in baya haukace mata bane bazata taba fasawa ba, bai taba jin baya son cikin ba wallahi.

Da asuba daya fito bai lura dasu a palon ba ya wuce masallaci sai daya dawo yagansu suna bacci Ramla gaba daya ta hau jikin Nabila, ya dan kura mata ido kamar zai kyaleta sai kuma ya dawo ya dauke ramla daga jikin ta ya kaita dakinshi sannan  ya tasheta, yana ganin ta bude ido ya koma daki, a hankali ta tashi tanajin jikinta yayi ciwo saboda kwanciya a kasa tabi bayanshi da Kallo, dakinta ta wuce tayi salla ta shiga kitchen ta fara aikin breakfast bayan ta gama tayi shara duk bai fito ba. tana mopping sai gashi da shirin shi bata san inda zashi ba, kunyar hada ido taji dashi duk da wulakancin daya mata jiya ya bata mata rai "ina kwana" ta gaida shi kamar ba zai tsaya ba sai kuma ya juyo ya kalleta "lafiya lau, kin tashi lafiya" ta gyada masa kai kawai "akwai abinda kike bukata ne"? Ta sake girgiza masa kai "Nabila bana son ina magana kina amsa min da kai" muryarta na rawa ta ce "babu" ya gyara tsayuwarsa yace "yarinyar can bata da lafiya ne naji jikinta da zafi" Hawayen da take ta tarewa suka zubo tana son yin kuka tace "bata da lafiya jiya ma batayi bacci ba" jikinsa yaji yayi sanyi ganin tana hawaye amma sai yace "idan ta tashi ki bata maganin da aka siyo jiyan" yana gama fadin haka ya fita, ajiye mopping din tayi takoma bisa kujerar dining tana kuka a hankali, dama maza haka suke wulakanci yana ji yana gani yayi da gangan dan taji haushi, shikenan su zauna a haka tunda hakan yake so.

Har ya fita yana tafiya ya hau titi duk yaji hankalinsa bai kwanta a yadda ya baro ta ba, wani shago ya shiga ya siyo abubuwa daya lura sun kare ko sun kusa karewa a gidan a shagon yaga hulunan yara da takalmi ya siyawa Ramla daganan gida ya nufa dan gaskiya yaji bai kyauta ba abinda yayi.

kukan ya sa ta tashi daga wurin ta shiga dakin taganta a zaune, wanka kawai tayi mata itama tayi ta koma dakinta suna shiri taji karar bude gate dinshi, ta San bazai neme su ba shiyasa taci gaba da shirinta, ta saka bra da pant da under skirt saita ajiye towel dinsa data dauro daga can, gaban madubi ta tsaya tana kallon cikinta daya fara fitowa tayi murmushi tace "mace ko namiji ne bansani ba to kun kyauta da kuka boye sai bayan wata hudu kuka bayyana" ganinsa kawai tayi a bayanta ta cikin madubin, bata rai tayi amma suna hada ido sai ya kama kunnensa alamar ya tuba, dauke idonta tayi daga kallon shi shikuma ya matso kusa da ita tareda rungumeta yace "wanene Dr Abubakar Sadeeq Zaki idan Nana Aisha Nabila tana fushi dashi? Kiyi hakuri hukuncin dana dauka yayi tsauri" bata san lokacin da taketa sauke ajiyar zuciya ba kafin a hankali itama tace "kayi hakuri bazan zubar da cikin ba Na fasa, amma don Allah ka daina cewa zaka sake ni" rigar da zata saka ya dauko mata tareda taimaka mata ta saka yana cewa "fushin zuciya ne ya saka na furta amma zan kiyaye" sai lokacin taji ta dawo daidai a tare suka ci abinci ya bawa Ramla magani dakanshi sannan suka kwanta bacci dan asabar ce babu aiki, bacci sukayi sosai sannan tun daga lokacin ya samawa Ramla friso take sha ta rage tsotse uwarta, wani lokacin takanyi ciwo har a sa mata ruwa wata rana kuwa a ganta garau ga ciwo ga ciki ga goyo nata baiyi kamar na Maryam da bashida wata damuwa ba.

Tana zaune gida yau dan babu makaranta sai wayarta tayi kara tana dubawa taga Mama ce bayan sun gaisa take fada mata Maryam ta haihu ta samu mace, murna tayi sosai sannan ta kira Dr ta fada masa zata gidan Maryam dan cikin dare ta haihu da safe an sallameta.

Anty Nusaiba data ganta da ciki gata dauke da ramla sai tayi dariya cikin tsokana tace "kinganki kamar irin matan nan na kauye masu ciki da goyo" koda wasa ce amma taji zafin maganar sai dai tayi murmushi tace "to Anty ko in yaye Ramla in kawo miki ita" girgiza kai tayi da sauri tace "rabani da wahala ban iya raino yanzu shiyasa ina yin ta biyar nace na gama" Anty Maryam tace "to wallahi ni da masu ciki kike min kama" dakuwa tayi mata tace "kinci gidanku" Ramla ta mika hannu tana so ta dauketa Nabila ta mika mata ita suka zauna suna hira.

Bayan suna Ya shigo yana cewa "tashi muje yawo Tambuwal" murmushi tayi tace "so kake sai cikin nan kowa ya ganshi ko"? Yayi dariya yace "Eh dama ko Mama bata san dashi ba dan nidai ban fada mata ba gashi kin dade baki je ba" kaya kadan ta daukarwa Ramla itama ta shirya suka wuce sai da sukayi yawo a dangi kafin suka wuce gidan Mama na ganinta ta rike baki tace "to masha Allah Nabila ashe ashe" murmushin jin kunya tayi ta zauna tana gaisheta Mama ta amsa ta karbi Ramla tana cewa "Nabila kin yayeta ko"? Nabila tace "A'a Mama" mama ta zaro ido tace "yau kam bazaki koma da ita ba wallahi wahala ta miki yawa kawai a yayeta ki barta nan" sai da taji gabanta ya fadi amma sai tayi murmushi tace "to shikenan mama sai a aiko da kayanta kawai" Dr ya harareta tare da taka kafarta yi tayi kamar bata gane abinda yake nufi ba "Mama ana yaye haka babu shiri" irin kallon datai masa ya sa yayi shuru, suna zaune Nafisa ta shigo kamar ba ita ba suka gaisa Nabila ta mika hannun ta karbi babynta tana cewa "oyoyo kanwar Ramla a kokarin karbarta Nafisa ta hango ciki saura kadan ta saki babynta gabanta ya fadi amma ta danne tana cewa "masha Allahu ashe har kinyi nauyi" murmushi kawai tayi bata amsa mata ba, suna nan sai karfe shida bayan sunci abinci sannan yace su wuce kayan data debowa Ramla tabar mata tana cewa "Gobe sai a samu wanda zai shigo ya kawo mata kayanta" Ramla kuwa kamar ta sani saida aka mata wayo suka fita sai kuka take Ranar dakyar Mama taga safiya amma koda ta kwana biyu ta hakura da kukan sai dai ba mai daukartar inba Mama ba sai ko Nafisa da take gani kullum.

Baba kamar zai dauketa ya maida ita dan yaji haushin rabata da uwarta kai tsaye har yana cewa ai kauyanci ne wannan an daina yayin haka.

Nafisa ko ranar duk yadda taso daurewa ta kasa saida tayiwa Mama maganar cikin Nabila tace "mama ashe ciki ga Nabila har ya tsufa suka boye mana" mama ta harareta tace "yanzu daya kamata ki gani ba gashi kin gani ba" shuru tayi sanin yanzu Mama bata goyon bayanta hasalima kokari take taga ta tankwarata ta gyaru shiyasa ma matsalolinta da Dr suka ragu ganin baya yi mata kamar da yasa ta fahimci a da tana cikin duhun kai na zama da miji yanzu ko in tana so a zauna lafiya dole tayi yadda ake so.

Ranar Monday da kanshi ya kaita makaranta dan tace yanxu wahalar driving take ji sai ta ringa jin tana danne cikin da hannunta intana juya shi, lokacin daya isa venue din da zasuyi lecture din sai daya kaita kusan kofar ya zagayo ya bude mata tareda riko hannunta prof dinda zai musu lecture din yana ganinsa ya fito daga hall din, lokacin data fito daga motar cike da kunya ta gaida shi yayi murmushi yace "Dr bazaka fada min tana nan a yafe mata lecture ba" yayi murmushi shima tareda bashi hannu suka gaisa yace "to gani nayi tunda zata iya gara tazo din" ya sake cewa "to shikenan wani sati ma zamuyi test dannyau insha Allahu zamu yi covering" godiya Dr ya masa ya wuce dan ita kam tuni ta wuce aji.

hakanan take lallabawa tana zuwa jarabawar da suka fara akayi sati uku suka gama sai zaman gida, da yaga haka idan zashi tambuwal sai ta tafi gida idan ya dawo sai ya daukota, wannan zuwan sai da ya kwana hudu sannan ya dawo, shi yaje ya daukota yana kallon yadda take tafiya dakyar yace "Nabila sannu ya jikin ki, amma bakijin ciwon komai" ta sauke numfashi dakyar tace "ai mu wuce asibiti kawai ina shirin fadawa mama kace ka iso na fara jin ciwo" da sauri ya juya ya kalleta yaganta kamar lafiya lau "don Allah mu tafi na fara ganin wannan ruwan fa" tada motar yayi yanata jera mata sannu yana cewa "ko Akira Ummu, mun tafi asibiti mu kadai" kasa amsa masa tayi sai kada kafa take.

lokacin da suka isa kasa fitowa tayi sai daya dauko jakar kayansu dana Baby ya tallabota dakyar ya nufi ciki da ita wannan karon private hospital ya kaita, yayi zaune yana jiran sammako ya kasa kiran kowa sai addu'a yake, yana daga zaune bayan ya kusa awa guda babu wani labari aka turo masa nurse ta karbi kaya, mikawa yayi yana sauraren yaji mai zata ce amma bata ce komai ba sai daga baya ta dawo tace "sory An fa haihu ka samu soja..."




*Dr A.S. Zaki*

EXQUISITE WRITERS FORUM 
*SAFIYYAH GALADANCHI*

_sadaukarwa ga yayata Billy galadanchi_

SHAFI TALATIN DA DAYA

Wani irin murmushi yayi tareda sa hannunsa aljihu ya ciro kudin da baza su wuce dubu biyar ba ya mika mata, tayi dariya tare da kin karba tace "A'a Alhaji bazan karbar maka kudi ba" tana kokarin tafiya, saurin binta yayi yana cewa "don girman Allah ki karba ni na baki duk saboda in sake godewa Allah ki karba karki hanani samun lada" dama fuk fi'ili ne da iyayi tana so saita karba tana godiya, aiko acikin dakin haka tayi ta lallaba Nabila har aka gyara mata jikinta fes aka bata babynta, kallon Nurse din tayi tace "Sister amma sallamar mu za ayi ko" ta danyi shuru tace "to gaskiya ba yanzu ba amma bari Dr yazo" Nabila ta tashi tsaye tace "idan ba matsala zan fita waje inga mijina mu biyu kadai muka zo" nurse din tace "Ai indai lafiya lau kike bakya jin komai zaki iya zuwa" A hankali take tafiya saboda nauyin cikin kadai taji ya ragu amma jikinta har yanzu da saura, Dr yana ganinta sai yayi saurin tashi tsaye, ji yake kamar yayi ihu irin wanda zai nuna jin dadinsa fiye da yadda yake ji cikin ranshi, dan hararar wasa tayi masa lokacin daya iso kusa da ita Ta dafa shi tare da cewa "ina fushi dakai, baka zo ka taya ni nishi da gumurzun nakuda ba" Babyn ya karba daga hannunta yace "Na taya ki da addu'a Momy, sannu da kokari, babu abinda yake miki ciwo" ta lumshe masa idonta tana nufar kujerar daya taso ta ce "Na tsani asibiti, indama zasu bari mu wuce gida" gefenta ya tsaya yana kallon babyn kamar ranar ya fara ganin jariri, shi kanshi yasan suna kama har yatsun kafarsu iri daya, manyan idonsa da shi kansa yake shan surutu akansu gasu nan gulu-gulu a fuskar yaronshi, bakinsa ya dora kusa da kunnen yaron yayi masa addua da huduba da sunan dayake so, babyn ya tura hannunsa a baki yana tsotsa Dr yace "momy kalli yana tsotsar hannu yunwa yake ji" kallon shi tayi cike da tausayi tace "Allah sarki, kila da yana ciki bai koshi ba shinkafar da naci inda Mama, zo kaji dan Momy" Dariya Dr yayi yana mika mata shi A lokacin mama ta iso tareda Anty Nusaiba da matar Yaya harda Yayan, dukansu tsayawa sukayi aka gaisa Matar yaya tace "ke ashe kin fara nakuda kika ki fada muna zaune saiga kira wai kin haihu" saboda yaya yana wurin ta kasa sakewa iyakarta murmushi, suna wurin har aka sallamesu dan ta takura, dayake ba a shirya wanda zai zauna da ita ba a daren sai Dr yace tabi Mama, amma mama tace "da sassafe gobe Rabi zata zo, karka damu ku wuce kawai da ita can gidanta" da yake shima baya son su tafi sai hakan yayi masa Dadi ita kuwa mama badan ta so ba Baba dai ya ja musu kunne duk wacce tayi haihuwa ta biyu ta zauna gidanta indai ba wata matsala ce gagaruma ba" su anty Nusaiba basu bar gidan ba sai da tayi wanka ita da babyn sannan suka wuce, ai ko dama bacci ne a idonta dan haka bata dade ba tayi bacci, Dr kuwa aikin baza information na haihuwa ya same shi a daren ya kira mama ta tambuwal ya fada mata, taji dadi har cikin ranta har batasan lokacin da ta dauki Ramla ta Cillata sama ba tana cewa "yar yaye kinyi kani, sannu babbar yaya" Nafisa dake kokarin shiga part din ta jiyo ta, ko ba a fada ba ta fahimci nabila ta sauka kenan, sai ta kasa shiga takoma jikinta na rawa gabanta na faduwa, tana shiga dakin sai ta zauna gefen gado ta dafe kanta.

Group dinsu na Makaranta aka tura, wani arne da ake kira thankgod yace "ahhh Dr A.S no dey play ooo" abokinsa yace "TG watch your tongue oo before you say something that will put you in trouble" Hoton babyn aka tura sai nan Nana sule ta gani, hakan kuwa ya bata haushi har tayi kudurin bazata taba kiran Nabila ba indai ba ta kira ta ta sanar da ita akan haihuwar ba, a

Please Login or Register in order to submit comment