Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Anty nusaiba ta fito rike da makullin mota tana yiwa mama sallama ta kalli Nabila tayi dariya "naso ganinki da tsohon ciki kila a tukunya zakici abincin" bata saurareta ba saima wayarta da take dannawa replying massage dinsa take, daya turo yana bata hakuri akan yana so yazo amma abubuwa sunyi masa yawa zai samu lokaci yazo dan ta ganshi, hankalinta ya kwanta shi ba gurgu bane, tana masa replying tayi murmushi "Ko gurgu ma ai mutum ne, karka damu kayi aikinka hankali a kwance nima kaga exam nake a makaranta" yana kwance a dakinsa dan a daren bayan ya gama siyayya ya wuce tambuwal, "haka baba ya fadamin ki maida hankalinki kema kiyi jarabawar idan result dinki yayi kyau zan miki kyauta" ajiye wayar tayi ta dauki ruwa tasha sannan ta tura masa "Nagode" daga haka bai mata reply ba saboda matar shi data shigo dakin, ya daga kansa ya kalleta tana sanye da top ja sai zani da alama dashi ta wuni, farar fatar ta duk ta bushe tayi fururu, tunda ya shiga cikin gida ya gaisa da mutanen gidan yaganta a can ko shigowa bata yi ta masa ya hanya ba saboda tana fushi dashi zai yi aure, ita ba wasu shekaru ba duk ta tsofar da kanta ko haihuwa bata taba yi ba sai bari datayi so biyu amma ji yadda kazanta da rashin kula ya maida ita "ki koma inda kika fito tunda sai yanzu kika san da zuwana" zuba masa ido tayi tana sauraren fadan dayake mata "dubeki don Allah? Har ake ganin laifina dan zan kara aure? Bakiyi tunanin ma ko zan bukaci abinci ba ko ruwan wanka, se yanzu zaki zo ke ga mai miji zaki kwana dashi, aurenmu kawai saboda kwanciyar aure akayi shi kenan? Bazan koreki ba amma kije ki gyara jikinki bazan iya hada makwanci dake a haka ba Nafisa" shuru tayi dan tasan batada gaskiya ko a garin anata surutai da fadin gara yayi auren ya auro daidai dashi dan wannan kam basu dace ba, juyawa kawai tayi ta fita daga dakin kuma bata dawo ba wannan dalilin ya saka washe gari tun karfe shida ya dawo sokoto bai mata sallama ba.



*Dr A.S. Zaki*

EXQUISITE WRITERS FORUM 
*SAFIYYAH GALADANCHI*

_sadaukarwa ga yayata Billy galadanchi_

SHORT STORY 

SHAFI NA TAKWAS




Interval din kwana biyu suka samu babu exam sai yau zasuyi Na Dr A.S, haka kawai yake cikin nishadi, a cikin hall daya zasuyi exam din dan iya yan department din ne kuma Hall din yana da girma, role shida ne sai aka bawa yan ug3 role uku ug2 role uku

Kowane layi yana daukar mutum bakwai sai suka zazzauna hudu-hudu, ita dinma yau bai saka mata ido kamar ko yaushe ba.

Questions dinsa sunyi matukar sauki acikin 40 minutes aka fara submitting hankali a kwance, kafin lokaci yayi fiye da rabin aji sun gama Nabila kuwa tana cikin wayanda suka gama da wuri saboda tambayarsa bata bukatar dogon surutu its just straight forward.

Murmushi yayi yabi ta da kallo lokacin da take fita daga hall din tana fara'a a zuciyarshi yace "dukansu albarkacinki suka ci" ci gaba yayi da harhada booklet din yana tunanin tunda next week zasu gama exam ya kamata ya saka lokaci yaje wurinta yana son suyi magana irin ta masoya masu shirin aure ba maganar data zama dole saboda yana malaminta ba, yana son suyi magana batareda ya hango wannan tsoron nashi a idonta ba.




Ranar da zasuyi last paper dinsu a ranar za a kawo lefenta, ta leka dakin mama tayi mata sallama zata wuce mama tace "ke kifa dawo kina fitowa jarabawar nan" ta turo baki tana cewa "Nifa mama bana so su ganni wallahi" tsaki mama tayi tace "kindai ji na gaya miki" fitowa tayi tana magana kasa-kasa har ta shiga motar, yau black jallabiya ta saka da mayafi gold, har ta dan so tayi letti dan koda tazo har an gama jera wajen zama, ganinsa a gaban hall din ya saka ta jin tsoro, tafiya take a hankali tana raba ido wani daga cikin invigilators din ya daka mata tsawa "dalla malama kiyi sauri kinzo late kuma kina mana yanga, wa kike ganin nan yanada lokacin kallon yangar taki" daure fuska tayi kamar bata taba dariya ba ta nufi kusa dashi, a gaba ya sata ta zauna.

Dr A.S kallonsa yayi cike da jin haushi kamar ya fada masa cewar ya bata girmanta saboda matarshi ce amma kuma sai ya danne tareda dawowa kusa da ita ya tsaya, duk sai take jin kanta a takure haka ta dukufa da rubutu dama ita haka takeyi tana gama karanta question paper take ajiyeta gefe, ta soma rubutu bata dagoba sai da ta kammala, tana dagowa suka hada ido yana zaune yana facing dinta saurin dauke idonta tayi ta soma bubbuda pages din ta tana dubawa sannan daga baya ta rufe tareda mikewa ta nufi wurinsa zuciyarta na dan bubbugawa da sauri, karba yayi maimakon ya barta ta ajiye sannan ya bata attendance yace tayi signing out, seda ya duba yaga tayi filling duka information da ake bukata sannan ya ajiye tareda kallonta, itama shi take kallo alokacin, idonsu suka hadu har zata dauke nata taga yayi mata murmushi tareda cewa "you can go, all the best" sauke idonta tayi kasa tareda fitowa ta zauna jiran Nana sule dan tare zasu wuce.

Nana tana fitowa ta riko hannunta tareda cewa "muje mota in ajiye abubuwana ki rakani toilet fitsari nake ji" gun motar sukaje sun bata mintuna sha biyar suna magana saboda Nana sule dake mita akan rashin zuwan sa gashi har saura sati biyu bikin, daganan suka fara tafiya suna ci gaba da magana har suka shiga korido dinda zasu bi zuwa toilet din department din, Nabila ta ce "kinga ko kirana ma baiyi ba yau kuma ko massage ni wallahi ina son ganinshi amma kunya nake ji ince masa yazo" Nana sule ta tsaki ta ce "to sena gani idan ma boye miki yake in ankai ki ma karya fito" dariya sukayi a tare Nabila tace "yama isa ai da bazan yadda akaini ba seyazo ya durkusa a gabana ya bani hakuri akan rashin zuwansa, ko yayiwa kansa hasarar daren farkon ranar dan ko ankai ni yana tabani zan soma aljanun karya ina ihu tareda fadin kada ka taba mana mata, mu munsan darajarta" dariya sukayi mai karfi saboda yadda take dan tsalle tana nuna gabanta da hannu tareda zazzaro idanu irin na masu iskokai, yana tafe a bayansu a hankali cikin irin takon daya saba da assistant dinsa a bayansa dauke da booklet dinda aka gama yanzu zasu kai sama dariya ta kusa turnukeshi har taso tona masa asiri, ganin haka yasashi rabasu yana kara sauri ya wucesu, a tare suka matsa gefe suna zaro idanu, Nana sule tace "munshiga ukku duk yaji me muke fada" Nabila da taji fitsari na neman kufcemata ma ta kasa magana saboda tsoron da taji sam batayi tunanin akwai mutum a bayansu ba balle ma shi, har suka kama hanyar gida bata gama dawowa daidai ba.

Koda suka shiga gidan kamar ranar ake biki, wasu cousins dinta mata yayan wan mama tun a gate suka hadu Nan fa suka sata a gaba "Autar mata za a shiga sahun manya" dayar tace "na matsu inga Nabila da ciki ahhh! Inda ma zan zama kuda inshiga inga first night" kunya ta kamata tana murmushi kawai ta shige gaba tabarsu a baya palon ma duk mutane ne suka gaggaisa da mutanen sannan ta bude dakinta suka shige su biyu ne kawai sai anty Maryam data biyo bayansu tana kallon Nabila ta ce "wai bakiga wani ci gaba ba akan maganin hips din nan"? Ta tabe tana cewa "ko sun karu ya zan gane tunda ba skirt nake sawa ba, garama boobs naji bra dinda nasa jiya ta kama ni sosai" Anty maryam ta ce "to kici gaba dai banda skipping don Allah" ta amsa mata da to lokacin da take kokarin shiga toilet, wanka tayi ta sauya kaya zuwa gown din leshi maroon da adon baki suka zauna suna hira duk akan wannan mijin, suna cikin haka ne suka ga an turo kofar wasu manyan mata ne su biyu sai wasu matasa daga gani masu aurene sai yan mata su uku suna shigowa suka ganeta dan Nana sule cikin jikinta ya bayyana, kunya ta kama ta ganinsu haka bata shirya ba dan ita bata ma jiyo hayaniyar masu kawo kayan ba, gaidasu tayi suka amsa nan fa suka zauna bayan matan sun fita suna dan hira da ita duk da bata nuna musu sakewa ba sosai, yan matan duk suka karbi lambarta sannan suka yi mata salla dan akwai wayanda zasu koma tambuwal a ranar.

Massage ya shigo wayarta tana dubawa taga shine "zan shigo bayan magrib anjima idan Allah ya kaimu ina fatan ki soni kamar yadda nake sonki kuma kiyita sona" murmushi tayi sannan tayi masa reply "Duk abinda Babana yake so zan soshi fiyeda yadda yake tsammani, karkayi tunanin samun rashin karbuwa daga gareni da zan ki ka dana yi hakan tun randa aka baka ni, Allah ya kaimu lokacin lafiya ina tsumayen zuwanka" ba karamin dadi massage din yayi masa ba dan haka yake ta maimaita karanta shi tareda dariyar maganar da yaji tana yi dazu yan yara sai kagansu sun san abubuwa akan aure yanzu ita har tasan tayi karyar aljanu dan ta hana mijinta ya kusance ta, "gara dana ji dan kinayin aljanu a ranar zan dagargaje makaryaciya" har baisan lokacin daya furta hakan ba saboda jin dadi.

Yadi ya saka blue black yasha guga sosai sai kamshi yakeyi, tunda ya dawo daga makaranta yake jin baya jin dadi saboda yunwa rabonsa da abincin kwarai tunda aka fara exam komai sedai ya dan ci badai dan ya koshi ba.

Can kuwa tayi wanka tasa doguwar riga pink mai stones da mayafinta ta debi abincin da akayi na lefe tayi warming da naman kaji da drinks ta ajiye masa a palon Baba kan center table.

Mama sai nasiha take mata tana kara jaddada mata cewar ta natsu dukda tasan batada rawar kai, dama ta fadawa baba mai gadi bako zai zo ya kai shi palon Baba, dan haka tana zaune a palon cikin gidan massage ya shigo wayarta ya ce "kin saka an kawo ni palon Baba kuma kin barni a zaune, karkiyi kwalliya idan itace zata cinyemin lokaci kiyi hakuri ina sonki a haka" dariya tayi mai sauti sannan ta tashi ta nufi palon, yana zaune ya dan dafe kansa saboda kirjinsa dake masa zafi ya fara damunsa, ta daga labulen palon ta shigo tareda sallama, kamshin sa duk ya cika palon dagowa yayi ya amsa mata yana kallonta sosai,Rufe idonta tayi ta sake budewa dan ta tabbatar da anya kuwa kodai gizo ne yake mata.


*Dr A.S. Zaki*

EXQUISITE WRITERS FORUM 
*SAFIYYAH GALADANCHI*

_sadaukarwa ga yayata Billy galadanchi_

SHORT STORY 




SHAFI NA TARA




"Haka ake tarbon bako a garinku" ya fada tareda jinginar da bayansa jikin kujerar dayake zaune, gabanta ya fadi dakyar ta hadiye yawu amma duk da haka makogoronta a bushe yake bataji ya jika ba, har lokacin tana tsaye wasu tunani suka shiga yawo a kanta, dazu yaji suna maganar first nyt, shine mai turo mata massage har ta saki jiki suke musayar kalamai, yasha ganinta a mota tana ciye-ciye, ta runtse idonta tana hango su yana kissing dinta wai ita ce matarsa "Wayyo Allah na" ta furta a hankali tana yarfe hannunta, duk sai yaji ta kara burgeshi, saida ta juya kamar zata fita sai kuma ta tsaya tareda saita kanta ta juyo a hankali ta zauna gabanshi muryarta tana rawa ta gaida shi, ya amsa yana cewa "lafiya lau, kinga dodonki ko"? Tayi masa shuru " dan huci yayi sannan yace "idan ban takuraki ba ina bukatar ruwan zafi insha" kallonsa tayi irin ban fahimce ka ba, "tea haka wanda babu madara"  bata amsa Msa ba dan ji take kamar mafarki take yi, kitchen ta shiga ta hada masa ta kawo jikinta yana ta rawa ta mika masa karba yayi tareda bisimillah ya fara sipping amma rabi kadai yasha ya ajiye tareda da neman excuse a wurinta ya fita haka yaita jera gyatsa saida yaji ya dan lafa masa sannan ya koma, zama yayi ya fuskance ta ya fara magana "meyasa kike tsorona har haka? Ki daina tsoro na babu abinda zan miki sai alkhairi kinji, magana nake so muyi tunda kin ganni yanzu, saura sati biyu wane event zakiyi"? Ta kasa magana saboda yadda takejin jikinta yana rawa dakyar ta girgiza masa kai, ya kura mata ido yana kallonta, murmushi yayi sannan yace "Bani abincin can idan ni kika ajiyewa in kuma saboda ganin nine kin fasa bani bari na tashi na kara gaba kar yunwa ta illata ni" mikewa tayi a hankali jin abinda ya ce yasa ta zuba masa abincin badayawa ba ta ajiye gabanshi tare da bude ruwa ta zuba a cup, hanya ta kama zatayi waje ya ce "A'a zo ki zauna" dawowa tayi a ranta tana cewa 'na shiga ukku fitsari ya matseni' ta kasa koda sakewa kadan da kusancinsu, zama tayi a takuri ga sanyin Ac ga sanyin gari, shikam bisimillah yayi ya fara cin abincin shi yana dan danna wayarshi tareda kallonta ta gefen ido yana mamakin yadda take ta motse-motse, sai ganin yayi ta mike tsaye tana atishawa wacce daga jinta zaka fahimci karya ce, ta sake yin wata tana cewa "excuse me pls" ta fita da sauri tana kokarin kaiwa dakinta taji fitsarin ya fara zuba, tsaye tayi tana zare ido jin yaki tsayawa har ya soma bin tile, su Mama dake zaune a palon duk suka zuba mata ido, idon Anty maryam ya sauka kan tile din ta dafe kirji tana cewa "innalillahi Nabila duk tsoron Dr dinne ya saka ki fitsari a tsaye"? Tabe fuska tayi cike da muzanta ta ce "Anty ya matseni kuma ya hanani fitowa, kuma ai duk laifinku ne da baku fadamin shi bane, ni na rantse nama fasa wallahi tsoronshi nake" Mama taja dogon tsaki tace "zaki maza ki goge mini fitsarin a wurin ko sena gaura miki mari don ubanki" saboda tsananin takaicinta yasa tayi mata haka ta tabbatar da akusa da ita take mai hana ta kai mata duka sai Allah, Anty nusaiba tace "Mama don Allah kiyi hakuri" "inyi hakuri kamar yaya, aljani ta gani da zata ji tsoronshi har haka? Iskanci take yi kala-kala dan taga ana kyaleta na rantse da Allah in bata bi a hankali ba kafin ta bar gidan nan sena lakada mata duka akan wannan shashancin nata" duk shuru sukayi dansu abin dariya ma ya basu itako mama ta dauki abin da zafi.

Toilet ta wuce direct ta cire rigar da pant da under skirt ta wanke jikinta sannan ta daura towel taje ta goge wurin ta sauya wasu kaya sannan ta koma wurinshi tanata kumburi akan fadan da mama har yanzu bata kai karshen shi ba.

Koda ta shiga ya gama cin abincin kafin ta zauna ya ce "kiramin anty Maryam ko anty Nusaiba" juyawa tayi ta fita, dariya ya danyi saboda ganin ta sauya kaya, ya kalli kujerar data tashi yaga bata jike ba, a fili ya furta "yarinya tayi fitsari a wando" wayarshi tayi kara a lokacin kuma suka shigo su uku, wayar ya daga tareda cewa "Nafisa ya akayi"? Daga bangarenta ta ce "mama zata zo skt gobe kasuwa zata shiga ina so in biyota" ya dan kalli gefen Nabila sannan yace "ke akwai abinda zaki siya dinne"? Ta ce "A'a itadai zan raka" "kiyi zamanki gobe da safe zan shigo tunda bazaki siya komai ba" ya kashe wayr yana gaisawa dasu duka sannan yace "taki fadamin abinda zatayi lokacin biki gashi niko ina so in sallameta dan ayi shiri da wuri" Anty nusaiba tace "kyaleta kaji, dama babu abinda zatayi event daya ne dan haka duk abinda kaga dama ka bata" ya dan yi murmushi yana cewa "ko yar bidiar nan da yan mata ke yayi bazata yi ba" Anty maryam tace "to tsoho yai mana kane-kane yace mu zabi daya" ya gyada kai tareda dauko envelope guda biyu ya ajiye bisa table "gashinan to ranki ya dade idan bai isaba asanar dani" ya fada yana kallon Nabila data koma waje daya ta makure, bata kalle shi ba ta ce "Nagode Allah ya saka da alkhairi" ya amsa da ameen, mikewa yayi tareda cewa "biyoni ki karbi wani sako a mota" saida ta kalli su anty atare suka harareta dole ta wuce tabi bayanshi, material ne mai kyau sliver yabata takai a dinka mata lokacin biki wata yar uwarsu dake Abuja taje dubai ta siyo masa shi saboda tana kasuwanci can take zuwa dauko kaya, godiya tayi masa jikinta duk a mace sannan ta dawo cikin gida, tana zuwa ta shige daki ta fara kuka, daganan kosu anty bata san wucewarsu ba sai safe ta farka.

Tun daga ranar koya kira bata iya dauka sanan koya mata massage ba reply saima ya daina kira dan yace "kwana bakwai ya rage yarinya, bama zakiji tsorona ba sai kin ganmu nidake akan gado daya".

Ba wanda ya sake mata maganarshi sai shirinsu suke inda mama ta dage da gyaranta ciki da waje jama'a aka fara bikin inda akayi kamu da rana da dare akayi wankin amarya washe gari asabar akayi wuni da daurin aure, sai dare kuma ta rufe kanta a dakin baba wai wallahi bata zuwa, bugun duniya anyi taki budewa saida baba yazo dakanshi, tana bude mama ta sauke mata tagwayen maruka tareda janta sai gaban mota, sai tausayinta ake sun zata duk kukan da take kukan rabuwa da gida ne nan ko basu san maruka tasha ba, Nana sule ta shiga dayar motar dan tambuwal za a kaita a daren saboda ya gyara mata palonshi tareda gina daki da toilet sai kitchen ya hade mata sai idan sun koma makaranta zasu dawo sokoto

Karfe takwas da rabi acan tayi musu, Nana sule saboda ciki yasa bata kwana ba dan ta kusa haihuwa dan haka babu kowa a ka barota tunda akwai tafiya ta kusan awa daya bamai so dare yamasa.

Koda suka gama wucewa yana nan dakinsa dan abokanansa kowa yayi gaba bayan magrib ko dan rakiya bashida zuwa wurin amarya, sai karfe goma ya shiga part din Nafisa dan yi mata sallama amma ba abinda ya samu sai harara, dan wani takaicinsa take ji zaije ya kwana da wata mace ba ita ba, murmushi kawai yayi tareda durkusawa yayi mata kiss a kumatu ya juya.

 A tsaye ya sameta a palo tana kallon kujerun da aka siya Sharpsharp masu kyau yan kanana da suka saki fili sosai dan palon nada girma, sauke kanta kasa tayi tana jin yadda kanta ya sara tareda bugun zuciyarta.


*Dr A.S. Zaki*

EXQUISITE WRITERS FORUM 
*SAFIYYAH GALADANCHI*

_sadaukarwa ga yayata Billy galadanchi_

SHORT STORY 

SHAFI NA GOMA




Sosa wuyanta tayi ta rasa me zatayi, hankalinta ya dauku ko amsa masa sallama bata yi ba, ya karaso ciki yana sake maimaita sallamar, sauke kanta kasa tayi tareda amsawa sai da ya matso daf da ita sannan ya ce "me kike yi a tsaye" gabanta yana faduwa tana dan motsi da bakinta dakyar ta iya cewa "wayata nake nema" ya gyada kai yana cewa "kin ganta" ta girgiza kai ya sake cewa "samu wuri ki zauna na kira miki ita aji ko wani wurin ta fada" kujerar nesa dashi ta zauna tana gyara mayafinta ta sunkuyar da kanta, yana tsaye daga gefe ya kira layinta, a daki suka jiyo ringing dinta wanda dama ita tasan wayar tana daki, kai tsaye ciki ya nufa tabi bayanshi da kallo baki ta rike tana cewa "akwai kaniya yau senaga yadda za a kwana gidan nan" yadan jima a dakin kafin ya fito da alama alwala yayi, yace ta shigo ya koma dakin  saida ta gama dafe dafen kirji sannan tayi shahada ta shiga, ya nuna mata toilet "shiga kiyi alwala" shiga tayi batareda tayi musu ba tayo alwala tazo sukayi salla, ta koma can gefe ta makure, yana dan yi mata tambayoyi amma bata sake jiki ta bashi amsa ba idan ya matsa da sai yaji ma sai yaji tana magana muryarta na rawa alamar zatayi kuka, Naman ya tura mata gabanta da exotic yace "ga tsarabarki nan kici" ta girgiza masa kai kawai, dama yayi tunanin bazata ci ba sai ya kyaleta, sun dan jima a zaune idonta ko alamar bacci babu, tashi yayi shikam ya bude wardrobe inda ya jera kayansa ya ciro na bacci tana daga zaune yayi shirin kwanciya, sai rarraba ido take tana cewa aranta 'dani fa a dakin yake saka kaya, anya akwai lafiya nan kuwa'? Gefen nata kayan ya bude ya ciro mata doguwar riga mai kauri ya mika mata yana cewa "tashi ki rage kayan nauyin nan ki kwanta" a hankali tace "Ni nafison in kwanta da wannan ajikina ba sai na canza ba" gyara tsayuwarsa yayi ya ce "Nabila I insist you must wear this, tashi maza" ta sake girgiza kai "wallahi akwai sanyi wannan yafi kauri na jikina" a dan tsawace yace "common get up my friend" tun kafin ya rufe bakinsa ta mike tareda ajiye mayafinta gefen ta zuge zip din rigarta har kasa tsabar gidima a saman zanin datake daure dashi ta zura rigar, ya daure fuska kamar bai taba dariya ba, ta kwashe kayan data cire takai bisa laundry basket ta ajiye, kafin ta juyo yace "oya remove those underwears kizo ki kwanta" zanin ta kunce ta saka hannu ta balle bra tare da saka hijab sannan ta nufi kofar dakin tana cewa "Saida safe" ya zaro ido yana kallon yadda take sauri ya ce "ke zo ki kwanta" daga nesa ta hada gefe kanta da kafada kmar wata yarinya tace "palo zan kwanta" cije lip dinsa yayi na kasa ya ce "kizo ki hau gado ba abinda zan miki" ta juya da sauri tana hadawa da gudu ta ce "wallahi ban zuwa" baisan lokacin da dariya ta subuce masa ba yabi bayanta  da sauri bayan ya gama shan dariyar, tana ganinsa ta nufi kofa da gudu saidai kofar a rufe gam, tsayawa tayi tana zare ido shiko yayi kanta da saurinsa "wayyo uwata wayyo ubana, wayyo dangina kun kasheni, kun kashe Aishatu Nabila" bilhaqqi da gaske a tsorace take dashi ko muryar shi taji gabanta faduwa yake, durkusawa tayi saboda jin fitsarin daya zo mata lokaci daya ya fara zuba, ganin haka sai bai karasa isowa ba ya tsaya cike da tsoro shima, kodai aljanu gareta? Shi take tsoro ko kuma tsoro take ji kar ya kusance ta? Cike da tsoro ya kira sunanta, itako ga kunya ga tsoro sai ta kasa dagowa sai hawaye ke mata zuba, daga nesa bayan ya kara ja da baya ya ce "tashi ki wanke jikin ki bazan miki komai ba kinji, ni zan kwanta a palon" ta kasa dagowa saboda tsananin kunya, kujera ya samu ya zauna yana ta nazarin wannan wace irin yarinya ce, a zatonta baya wurin sai ta mike da sauri ta shige daki sai toilet ta wanke jikinta da rigar ta shanya ajikin karfe ta fito ta saka wata, ranta duk a bace yake ta samu wuri ta kwanta.

Yakai awa daya a zaune wurin sannan ya nufo dakin bayan ya kashe wutar palon, hawa gadon yayi dayake gauraye da kamshinta mai daukar hankali, saboda neman magana saida yakai kusa da ita sannan ya kwanta, dama baccin a tsorace take yinsa dan haka ta hanzarta mikewa, yasa hannu daya ya dawo da ita tareda danneta da hannun yace "ki kwanta bazan miki komai ba, na kasa bacci a kujerar palo ne, bazan miki komai ba" bayanta dake hade da kirjinsa yake jin yadda zuciyarta ge bugawa da karfi har bacci ya soma daukar shi amma ita ko gyangyadi batayi ba sai ma kanta da taji yana mata matukar ciwo gashi ya riketa da iya karfinsa, har asuba ko juyawa baiyiba, sai kiran salla ne ya tashe shi ya bude idonsa yana jin bugun zuciyarta har lokacin, ajiyar zuciya ya saki tareda mikewa zaune yayi addua sannan ya shiga toilet yayo alwala, anan dakin yayi salla tana bayanshi itama tayi tata sallar, bai ko kalleta ba ya nufi gado ya zauna yana karasa azkar dinshi, ta kalli gefensa

Please Login or Register in order to submit comment