Join Our WhatsApp Group

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

Login Register

ta amma shine ya korota, ta kai minti goma a zaune cikin mota ai lokacin ta fara neman key din motar dan bata ma lura dashi jikin kofar ba, ta fito zata duba kasa sai ta ganshi zarewa tayi ta koma motar a hankali take driving har ta fita daga faculty din, Dr ta ko satar kallon motar yake yana ci gaba da bayani a class duk dalibai sunsha jinin jikinsu. 
Maimakon ta wuce gida saita shiga gidan wata yar uwarshi daya taba kaita cousin dinsa ce yaya ummu, ta shiga da sallama suka gaisa tana ta murnar ganinta ta jata daki sunata hira kamar sun saba da dadewa har take tambayarta ta ga fuskarta a kumbure lafiya ko, dan yamutsa fuska tayi tace "wallahi bacci ne bansamu nayi dakyau ba kuma naje makaranta late lecturer ya hanani shiga" yaya Ummu ta ce "To amma kamar ba bacci ne kawai ba, bari in barki ki kwanta to" fita yaya tayi daga dakin ta barta amma duk yadda taso kasa komawa baccin tayi sai ta koma palo a can ta sameta tace mata zata wuce gida yaya ta ce "A'a kijira zuwa anjima mana kinga ga mai lalle nan zuwa zata yi miki, ko ba matar aure ba ai ana son ganin kafar mace da lalle da hannunta" gefen kujera ta zauna tana murmushi ta ce "Yaya zaman lallen ne jidali wallahi amma ina so" suna zaune mai lallan ta shigo a cikin minti talatin ta gama sawa Nabila, ta kwanta kan kujera daganan sai bacci ba ita ta tashi ba sai karfe daya lokacin lallen ya kai awa uku, wankewa tayi tareda yin salla dakyar saboda yunwa, Yaya ta shigo da kulolin abinci ta ajiye mata tace "to gashinan kici sai a zana miki baki a bayan hannu" tayi murmushi lokacin da take karbar plate ta ce "Yaya wannan bai isa ba"?ta girgiza mata kai sannan ta fita tana cewa "ina fa ai dole a karasa shi tunda aka fara" abincin ta ta zauna taci dakyau tasha ruwa sannan aka zana mata bai dade ba ya bushe ta wanke sannan ta tambayi kudin lallen yaya tace babu ruwanta, sai lokacin ta dauki wayarta daga jaka, missed calls sunfi guda ashirin harda baba hankalinta duk ya tashi mama ta fara kira tana dagawa ta kunduma mata zagi "ina kika je tundazu mijinki yazo nemanki anata kira kika ki dauka"? Ta girgiza kai kamar tana gabanta tace "Mama bacci nakeyi shiyasa ganinan gidan yaya ummu" mama ta daka mata tsawa ta ce "da izinin wa kika je can"? Mikewa tsaye tayi ta figi gyaleta da jaka tace "Mama bashine ya hanani shiga aji ba" "tunda shi ya hanaki shiga karki hanzarta ki koma gida kinaji" ta kashe wayar yaya ummu ta kalleta ta ce "kin shuka tsiyar ko"? Dariya tayi irinta yake tace "Ramawa nayi anty gashi zatayi ciki dani, bari in koma gida kar mama ta ci kaniyata" ana zana mata lalle a hannu ta ce "to leka kitchen jug yana nan kisha abinda ke ciki ko ki tafi dashi da bari nai se anjima idan abincin da kika ci ya dan fada amma yanzu sai kisha inbaki iya shanyewa kije dashi amma ki dawo min da jug dina"  ta rike baki tana cewa "wallahi yaya abubuwan nan tsoronsu nake yanzu duk inda naje sai anbani yau din nan saura kadan ayimin dinki aradu" fita tayi da sauri tana dariya ganin yadda yaya ummu ke hararta, Kadan ta sha ta wuce mota dan hankalinta duk ba a kwance yake ba.
Yana zaune a palo ya cika kamar zai fashe gabanshi robar coke ce da crackers yaci kadan yana jin karar bude gate da shigowarta, ya kurawa kofa ido, gabanta ya fadi lokacin da taga motar shi saida ta daidaita kanta sannan ta wuce cikin gidan ta tura kofar palon da sallama a bakinta, bai amsa ba ya daga ido yana kallonta ta gaida shi nan ma bai amsa ba ta wuce dakinta dama fuskar ta a daure take, ajiyar zuciya ya sauke ya tashi ya bi bayanta, tana shiga dakin ta cire rigar jikinta da under skirt ta dauko wata riga armless ta dauki wayarta zata fito suka kusa cin karo dashi, ja baya tayi tana sake daure fuska cike da jarumta ya dane hannu a kirji yana kallonta tare da fadin "Ina kika je"? Shuru tayi masa taki magana, saida ya daka mata tsawa taja baya tana zaro ido yace "raini ya shiga tsakanina dake ko? Ki kiyaye ni billahi banida kyau, dan kinga ina kyaleki shiyasa zaki fara raina min wayo, da aurena akanki kike yawo har kinsamu damar zuwa wani wurin bada izinina ba ko, kici gaba da gwadani ki gani zaki ga other side of me wanda baki sani ba" ya juya ya fita daga dakin  da niyyar shiga kitchen take amma saita fasa ta koma kan gado ta kwanta sai jera ajiyar zuciya take saboda bacin rai, bacci ya dauketa sai kusan magrib ta tashi, haka ta sake tashi da rai a dagule har tayi sallar isha'i ta sake wanka ta kwanta.
shuru-shuru yanata zuba ido bai ganta ba shi kanshi yunwar dake cinshi ta isheshi, kitchen ya wuce dakanshi ya dafa indomie yaci ya fita yabar gidan, bashi ya dawo ba sai karfe goma da rabi, duk yadda yaso ya share ta kasawa yayi after all ma shine ya bata mata rai dan haka ya nufi kofar dakin ta ya tura amma sai yajita a rufe ya kwankwasa sau uku bata bude ba, sai ya koma dakinshi ya dauko spare key yazo ya bude, a kwance ya sameta ta lafe jikin katifa ta ruhu da bargo, tana jin shigowarshi ta rufe idonta ya haura kan gadon tareda kwantawa kusa da ita ya shafa fuskarta shuru tayi ta kyaleshi saida taji hannunshi na kaiwa wani wuri a jikinta ta matsa da sauri tana cewa "bana so ka rabu dani don Allah, dama shi kadai ne amfanina a gidan nan dare yayi ka hanani bacci…"

*Dr A.S. Zaki*

EXQUISITE WRITERS FORUM 
*SAFIYYAH GALADANCHI*

_sadaukarwa ga yayata Billy galadanchi_

SHAFI NA GOMA SHA TAKWAS

*Yadda naso labarin nan bazai wuce 15 pages ba amma yanzu ya tashi daga short story, kuma naga kunata complain akan akara yawan pages saboda ban tsara labarin yayi tsayiba shiyasa nakeyi words dubu ko da dari daya a kowane shafi to yanzu ya tashi daga Short story duk da labarin yazo karshe, nagode**

Shuru yayi yana kallonta dan bai taba tunanin yadda take shakkarshi zata iya fadamai magana haka ba, "ni kike fadawa Magana Nana Aisha"? Bata juyo ta kalleshi ba dan Allah ya gani ma gabanta faduwa yake tace "ni ba magana nake fada maka ba amma ba a daki mutum a hana shi kuka ba, haba don Allah ga mari ga tsinka jaka da wanne zanji" juyo da ita yayi da karfi ya hada hannayenta duka biyu ya rike tareda tashi zaune ya zare mata idanuwansa suka kara girma yayi magana a dan tsawace "yaushe kalar wannan rainin ya shiga tsakanina dake? Nace yaushe kika rainani har haka" ta runtse idonta tana sauraren saukar mari ya ci gaba da cewa "ko gobe kikayi laifi dole ne a fada miki kinyi ba daidai ba saboda baki fi karfin haka ba, idan na sake tabaki kika gayamin maganar banza kamar wannan zakisan wanene ni da gaske, su sauran dana hana shiga fin su kikayi ko su ba daliban makaranta bane, ki sake yin letti ki gani idan zan barki ki shiga" ya yarfa hannayenta da karfi har saida daya hannunta ya daki bed side drawer sannan ya mike cike da fushi yabar dakin, mikewa tayi da sauri ta shiga toilet amma kafin takai ga tsugunawa tuni fitsarin ya soma zuba, daga tsaye ta karasa shi kawai saita fashe da kuka hannunta tun jiya da dare daya lankwasa mata shi takejin yana dan ciwo inta motsa shi sosai yanzu gashi ya sake ji mata ciwo dashi, tana toilet din tana wanke jikinta taji karar bude gate dinshi ya fita.

Tambuwal ya nufa a daren bashi ya isa ba sai sha biyu, Nafisa daya kira ta bude masa kofar tasha mamakin ganin shi, tare suka wuce dakinta amma ya debo takaici ya sake iske wani takaicin, dakinta kamar dakin gwanjo ko ina kaya ga plate din faten doya da wake anci an rage an dora bisa madubi, toilet dinta sai zarni yake yi, tsaki kawai yayi ya wuce dakinshi koda yayi kura amma yafi dakin waccen ballagazar. Nafisa kuwa bata san da zuwanshi ba data gyara yana wucewa ta shiga toilet tayi wanka tayi shaving ta shafa mai da humra masu kamshi sannan ta nufi dakinshi, har ya kwanta tabishi ta kwanta tareda rungumeshi dakyau, abin nema ya samu dama mai nema a duhu balle an haska mai, tare suka kwana rungume da juna cike da farin ciki.

Nabila ko a tsorace ta kwana a palo sai dai bacci Barawo ya sace ta, ko yunwa bata ji ba saboda bacinrai, dama haka auren yake? A dake ka a hana ka kuka, bata taba jin kishin Nafisa ba sai yau dan tasan a daren nan wurinta zashi dan haka da tsoro da kukan data sha suka hanata bacci, washe gari da zazzafan zazzabi ta tashi hakanan tayi wanka ta fita makaranta lecture din 12 to 1:30, Nana tana ganinta tasan akwai matsala amma data tambayeta sai tace "wallahi da zazzabi na kwana yanzu ma daurewa kawai nayi na shigo gashi malamin yaki zuwa" Nana sule ta ce "to ki koma gida amma da akwai hali da kinje asibiti dan matar aure mai expecting ciki ko wane time bata shan magani anyhow" ta jinjina kai tace "kila na wuce wurin Mama yanzu" nan sukayi sallama ta wuce saboda anzo daukarta Nabila ma lallabawa tayi ta shiga mota ta samu mama asibiti, wata mata kawar mama da suke aiki tare ita tace "Matron Bari a sayo ruwa asa mata kafin result din ya fito naga kamar ta galabaita" Mama tace "To ai babu gado ko ansa mata ruwa yanzu sedai ta zauna, ko kisa mata cannula idan munje gida insa mata ruwan da allura gaba daya" matar mai suna sister Maryam ta ce to shikenan, haka kuwa sukayi dama mama baba ke kaita aiki ya daukota sai ta kirashi a waya tace basai yazo ba, dakanta taja motar Nabila suka je gida saida sukayi salla tasa mata ruwan tana cewa "sai gobe result zai fito se ki shirya da wuri ki koma asibitin kila mijinki ma ya dawo yau" rufe idonta tayi saboda yadda kanta ke mata ciwo, daganan bacci ya dauketa koda ta farka ruwan ya kare har ancire mata, Alhmdllh taji sauki sai yunwa da take ji da jiri, ta samu mama har ta gama tuwo sai da ta ci tuwon sannan tayi laasar da magrib ta cewa mama zata wuce Mama ta ce "to ki fito da wuri goben ko kinada aji"? Ta girgiza kai tace "sai karfe hudu nakeda aji gobe.

Dr kuwa saida gari ya waye sannan ya fara tunanin abinda yayi bai kyauta ba kowa akayiwa abinda aka yi mata dole yaji haushi sannan bai kamata ya barta ita kadai ta kwana ba, yarinyar da bata wasa da cin abinci yau gashi yasa ta kwana da yunwa, Allah sarki bata ma sonshi aka aura mata shi duk biyayya tayi masa amma bai kamata ya juya mata baya ba, shikadai yake wannan tunanin lokacin dayake shafa mai, karfe goma sha biyu ya baro tambuwal karfe daya ya shigo sokoto makaranta ya fara shiga yayi lecture 2 to 4 sannan ya koma gida, yayi mamaki ganin bata nan yasan basuda lecture lokacin, tunanin daya zo masa kila tayi tafiyarta gida lallai kuwa da  yayi abin kunya, dakinshi ya shiga ya kwanta ya rasa abinda zaiyi, yana nan kwance har dare yaji karar shigowarta gidan, ya sauke ajiyar zuciya yana sauraren motsinta har ta shigo cikin palon, sai lokacin ya tashi ya fito ya tsaya bakin kofa yana kallonta.

Ganin motarsa a cikin gidan yasa taji shakkar haduwa dashi, ta shigo ciki a sanyaye ta nufi dakinta yana tsaye bakin kofa yana kallonta har ta shiga dalin ta rufe kofar, komawa dakinshi yayi ya zauna dan sai yaji kunyar haduwa da ita, bata zauna ba saida tayi wanka ta fito tana shafa mai ya turo kofar ya shigo, idonsa ya sauka kan hannunta na dama dake rufe da plaster, karbar mai yayi ya karasa shafa mata batareda yayi magana ba sannan ya dauko kayan data ajiye ya sa mata, ci gaba datayi da zama tana wasa da zobenta ya riko hannun nata yace "meya samekia hannu" a hankali tace "wani karfe ya yankeni shine na rufe" ya gyada kai kawai ya rasa mai zaice kuma, daukarta yayi ya tafi dakinsa da ita sannan ya rufe gidan ya koma dakin.

Tausayi ta bashi jin yadda gabanta ke faduwa zuciyarta na bugawa da sauri da sauri, bai mata komai ba illa rungumeta da yayi nan take bacci ya daukeshi itakam ta kasa bacci sai hawaye take, daga baya bacci ya dauketa haka ta sake tashi da zazzabi yana zaune kan sallaya dan sun makara bai fita masallaci ba, yana ganinta a zaune ya tashi daga inda yake ya koma kusa da ita "Nabila zazzabi ko? Jikinki zafi" batayi magana ba sai kanta data dafe dan ya mata nauyi, rike hannunta yayi ya mikar da ita tsaye ya ce "muje ki wanka da salla sai mu tafi asibiti" still binshi tayi har toilet din ya hada ruwan wanka wanda basu zafi kuma sanyinsu bai cutarwa, jallabiyar jikinshi ya cire tareda jefata daki kan gado ya dawo kusa da ita ta jingina bayanta da bangon toilet din dan matsawa baya tayi ta ce "a kashe wuta" ya harareta yana cewa "maganin me zai miki idan an kashe wutar? Kinga babu abinda zanmiki kuma jikinki ba bakona bane".

Hijab ya dauko mata bayan ta shirya gasunan a jere sunfi guda ashirin amma bata sawa saidai gyale kullum, saida suka shiga mota sannan tace "yau mama tace indawo inkarbi result din a koma wajen likita" cike da mamaki ya kalleta "yaushe kika je asibitin" ta ce "jiya naje dagacan ma na wuce gida aka samin ruwa bayan sun kare ne mama tacire sena dawo"  gyara zamansa yayi ya ce "saboda kina fushi dani shiyasa bazaki iya fadamin bakida lafiya ba? Nabila bana son fushi musamman a wurin karki sake bohemian ciwonki , shuru tayi bata ce masa komai ba, amma yaji haushi tunda har tambayarta saida yayi taki fada masa ruwa aka kara mata.

Yana rike da hannunta har suka karbi result din suka kaiwa mama ita tayi leading dinsu wajen likita, a tare suka shiga dakin har mama likitan ya duba result din yaga da akwai ciki 7wks bayan ya fada musu yayi mata tambayoyi tareda rubuta mata magani da shawarwari sannan ya dago yana dariya yace  "Na manta fa mamanki ma aikaciyar lafiya ce, zata baki shawarar data tace but pls you take care of your self and the baby" kunya ta kama ta sai ta sunkuyar da kanta kasa, bayan sun fita likitan ya tsaida Dr A.S suka sake gaisawa yace "kamar nasanka a dan fodio ko"? Dr ya ce "ba mamaki wane department kasan ni"? ya ce "nan wajen su Prof. Jabir" yayi murmushi yace "eh tabbas" likitan yayi kasa da murya yace "to a kula da yaron cikinnan dan baiyi kwari ba kar ya fita" murmushi kawai Dr yayi ya ce "nagode insha Allahu zan kiyaye" dan sosai ya fahimci abinda yake nufi. A zaune ya sameta wajen wani bench ya zauna yana cewa "tashi mu tafi sai a siya maganin kan hanya ko"? Ta ce "mama ta tafi ta siyo" ya ce "abin yayi yawa jiya tayi yau ma tayi bari ta dawo dai" suna nan zaune ta dawo ta mika mata ledar shikuma.ya ciro kudin aljihunsa da bashi da tabbacin ko nawa ne ya mika mata yana cewa "Mama ga kudinki don Allah ki karba" tayi murmushi tace "aikam ko zan karba sunyi yawa dan maganin dubu takwas ne da dari uku" nacewa yayi saita karba yasan kila bazasu wuce dubu sha uku ko sha biyu ba dan 20k ne yasa mai 5k ya siyo cream 1800 da sleepers din toilet guda biyu.

Chicken Republic ya tsaya ya siya musu abinci da kaza da sauran tarkace sannan ya wuce gida, suna shiga ya ajiye ledodin hannunsa ya rungumeta yana fadin "sannu Aisha Nabila sannu, nagode Allah ya biyaki ya miki albarka, kiyi hakuri Abubakar ya bata miki rai shekaranjiya kiyi hakuri yar kanwata kiyi hakuri matata, Allah ya sauke ki lafiya"....

*Dr A.S. Zaki*

EXQUISITE WRITERS FORUM 
*SAFIYYAH GALADANCHI*

_sadaukarwa ga yayata Billy galadanchi_

SHAFI NA GOMA SHA TAKWAS

*Yadda naso labarin nan bazai wuce 15 pages ba amma yanzu ya tashi daga short story, kuma naga kunata complain akan akara yawan pages saboda ban tsara labarin yayi tsayiba shiyasa nakeyi words dubu ko da dari daya a kowane shafi to yanzu ya tashi daga Short story duk da labarin yazo karshe, nagode**

Shuru yayi yana kallonta dan bai taba tunanin yadda take shakkarshi zata iya fadamai magana haka ba, "ni kike fadawa Magana Nana Aisha"? Bata juyo ta kalleshi ba dan Allah ya gani ma gabanta faduwa yake tace "ni ba magana nake fada maka ba amma ba a daki mutum a hana shi kuka ba, haba don Allah ga mari ga tsinka jaka da wanne zanji" juyo da ita yayi da karfi ya hada hannayenta duka biyu ya rike tareda tashi zaune ya zare mata idanuwansa suka kara girma yayi magana a dan tsawace "yaushe kalar wannan rainin ya shiga tsakanina dake? Nace yaushe kika rainani har haka" ta runtse idonta tana sauraren saukar mari ya ci gaba da cewa "ko gobe kikayi laifi dole ne a fada miki kinyi ba daidai ba saboda baki fi karfin haka ba, idan na sake tabaki kika gayamin maganar banza kamar wannan zakisan wanene ni da gaske, su sauran dana hana shiga fin su kikayi ko su ba daliban makaranta bane, ki sake yin letti ki gani idan zan barki ki shiga" ya yarfa hannayenta da karfi har saida daya hannunta ya daki bed side drawer sannan ya mike cike da fushi yabar dakin, mikewa tayi da sauri ta shiga toilet amma kafin takai ga tsugunawa tuni fitsarin ya soma zuba, daga tsaye ta karasa shi kawai saita fashe da kuka hannunta tun jiya da dare daya lankwasa mata shi takejin yana dan ciwo inta motsa shi sosai yanzu gashi ya sake ji mata ciwo dashi, tana toilet din tana wanke jikinta taji karar bude gate dinshi ya fita.

Tambuwal ya nufa a daren bashi ya isa ba sai sha biyu, Nafisa daya kira ta bude masa kofar tasha mamakin ganin shi, tare suka wuce dakinta amma ya debo takaici ya sake iske wani takaicin, dakinta kamar dakin gwanjo ko ina kaya ga plate din faten doya da wake anci an rage an dora bisa madubi, toilet dinta sai zarni yake yi, tsaki kawai yayi ya wuce dakinshi koda yayi kura amma yafi dakin waccen ballagazar. Nafisa kuwa bata san da zuwanshi ba data gyara yana wucewa ta shiga toilet tayi wanka tayi shaving ta shafa mai da humra masu kamshi sannan ta nufi dakinshi, har ya kwanta tabishi ta kwanta tareda rungumeshi dakyau, abin nema ya samu dama mai nema a duhu balle an haska mai, tare suka kwana rungume da juna cike da farin ciki.

Nabila ko a tsorace ta kwana a palo sai dai bacci Barawo ya sace ta, ko yunwa bata ji ba saboda bacinrai, dama haka auren yake? A dake ka a hana ka kuka, bata taba jin kishin Nafisa ba sai yau dan tasan a daren nan wurinta zashi dan haka da tsoro da kukan data sha suka hanata bacci, washe gari da zazzafan zazzabi ta tashi hakanan tayi wanka ta fita makaranta lecture din 12 to 1:30, Nana tana ganinta tasan akwai matsala amma data tambayeta sai tace "wallahi da zazzabi na kwana yanzu ma daurewa kawai nayi na shigo gashi malamin yaki zuwa" Nana sule ta ce "to ki koma gida amma da akwai hali da kinje asibiti dan matar aure mai expecting ciki ko wane time bata shan magani anyhow" ta jinjina kai tace "kila na wuce wurin Mama yanzu" nan sukayi sallama ta wuce saboda anzo daukarta Nabila ma lallabawa tayi ta shiga mota ta samu mama asibiti, wata mata kawar mama da suke aiki tare ita tace "Matron Bari a sayo ruwa asa mata kafin result din ya fito naga kamar ta galabaita" Mama tace "To ai babu gado ko ansa mata ruwa yanzu sedai ta zauna, ko kisa mata cannula idan munje gida insa mata ruwan da allura gaba daya" matar mai suna sister Maryam ta ce to shikenan, haka kuwa sukayi dama mama baba ke kaita aiki ya daukota sai ta kirashi a waya tace basai yazo ba, dakanta taja motar Nabila suka je gida saida sukayi salla tasa mata ruwan tana cewa "sai gobe result zai fito se ki shirya da wuri ki koma asibitin kila mijinki ma ya dawo yau" rufe idonta tayi saboda yadda kanta ke mata ciwo, daganan bacci ya dauketa koda ta farka ruwan ya kare har ancire mata, Alhmdllh taji sauki sai yunwa da take ji da jiri, ta samu mama har ta gama tuwo sai da ta ci tuwon sannan tayi laasar da magrib ta cewa mama zata wuce Mama ta ce "to ki fito da wuri goben ko kinada aji"? Ta girgiza kai tace "sai karfe hudu nakeda aji gobe.

Dr kuwa saida gari ya waye sannan ya fara tunanin abinda yayi bai kyauta ba kowa akayiwa abinda aka yi mata dole yaji haushi sannan bai kamata ya barta ita kadai ta kwana ba, yarinyar da bata wasa da cin abinci yau gashi yasa ta kwana da yunwa, Allah sarki bata ma sonshi aka aura mata shi duk biyayya tayi masa amma bai kamata ya juya mata baya ba, shikadai yake wannan tunanin lokacin dayake shafa mai, karfe goma sha biyu ya baro tambuwal karfe daya ya shigo sokoto makaranta ya fara shiga yayi lecture 2 to 4 sannan ya koma gida, yayi mamaki ganin bata nan yasan basuda lecture lokacin, tunanin daya zo masa kila tayi tafiyarta gida lallai kuwa da  yayi abin kunya, dakinshi ya shiga ya kwanta ya rasa abinda zaiyi, yana nan kwance har dare yaji karar shigowarta gidan, ya sauke ajiyar zuciya yana sauraren motsinta har ta shigo cikin palon, sai lokacin ya tashi ya fito ya tsaya bakin kofa yana kallonta.

Ganin motarsa a cikin gidan yasa taji shakkar haduwa dashi, ta shigo ciki a sanyaye ta nufi dakinta yana tsaye bakin kofa yana kallonta har ta shiga dalin ta rufe kofar, komawa dakinshi yayi ya zauna dan sai yaji kunyar haduwa da ita, bata zauna ba saida tayi wanka ta fito tana shafa mai ya turo kofar ya shigo, idonsa ya sauka kan hannunta na dama dake rufe da plaster, karbar mai yayi ya karasa shafa mata batareda yayi magana ba sannan ya dauko kayan data ajiye ya sa mata, ci gaba datayi da zama tana wasa da zobenta ya riko hannun nata yace "meya samekia hannu" a hankali tace "wani karfe ya yankeni shine na rufe" ya gyada kai kawai ya rasa mai zaice kuma, daukarta yayi ya tafi dakinsa da ita sannan ya rufe gidan ya koma dakin.

Tausayi ta bashi jin yadda gabanta ke faduwa zuciyarta na bugawa da sauri da sauri, bai mata komai ba illa rungumeta da yayi nan take bacci ya daukeshi itakam ta kasa bacci sai hawaye take, daga baya bacci ya dauketa haka ta sake tashi da zazzabi yana zaune kan sallaya dan sun makara bai fita masallaci ba, yana ganinta a zaune ya tashi daga inda yake ya koma kusa da ita "Nabila zazzabi ko? Jikinki zafi" batayi magana ba sai kanta data dafe dan ya mata nauyi, rike hannunta yayi ya mikar da ita tsaye ya ce "muje ki wanka da salla sai mu tafi asibiti" still binshi tayi har toilet din ya hada ruwan wanka wanda basu zafi kuma sanyinsu bai cutarwa, jallabiyar jikinshi ya cire

Please Login or Register in order to submit comment