Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da mutanenshi sukayi sallama sune na karshe da juyowa, hankalinshi duk yana kan gida da Nabila yasan ta shiga watan haihuwa duk da lafiya lau ya baro ta amma kasancewarta ita kadai ya saka yaji bai yadda da hakan ba akwai matsala, yana isa gida sai ya shiga ciki daga tsaye ya yi musu sallama ya kamo hanya yana tafiya yana kokarin kiranta lokacin kuma Mama ta kira baba ta fada mishi zataje gidan Nabila dan ga abinda ya faru bata daukar waya, yace ta jira shi amma ta kasa jira su hadu can dai ita da sister Maryam suka hau napep suka tafi gidan amma abin Haushi Dr da zai fita yasan tanada wani key sai ya rufe ta waje sunyi dukan kofar kamar ba gobe amma shuru.

Nabila tana kwance tana jin yadda ake buga kofar, Mama sai hawaye take tana fadin "fisabilillahi wane irin haukane kina ke kadai cikin gida ki rufe kofa haka" gidan dake kallon gidansu da wanda yake gefen su mazajen da matar daya daga ciki a tare suka fito daidai lokacin baba ya iso baiko daidaita aje motar ba ya fito yana cewa "maman baffa ya akayi" kofar a rufe bamu sani ba ko tana nan ko bata nan" daya daga cikin makotan nasu yace "tana nan dan naga fitar mijin shikadai" kafin ya rufe bakinsa sai ganin yayi Baba ya cire riga daga shi sai T-shirt ya fara hawa gate din a tare suka matsa suna cewa "Baba wayar nan fa karta yanke ka kabari a samo itace a daga ta" tab... Allah ya gani yana matukar son Nabila ko jinsu baya yi da hannu ya daga wayar ya sauka cikin gidan, yan mazan suka bishi bayan sun daga wayar amma kofar palonsu ta gaban gida security door ce sukayita zazzaga taki koda motsine Baba yace "akwai kofar baya"? Yama manta dasuwa yake tambaya zaga gidan yayi yaga kofar karfe ce duka uku yayi mata ta balle ya shiga sai ganin sa yayi a kofar kitchen dinta ta baya yana murdawa ta bude ya shiga cikin gidan kan center table ya hango key ya bude kofofin ya jefawa mazan key su bude masa gate, yana shiga dakinta ya ganta a kwance tana ta jera numfashi da karfi ga jini da ruwa a kasa kamar an zubar da Gangan, daukarta kawai yayi ya fita ita bata ma san yayi ba ta daiga haske har ta kulle idonta amma daga lokacin bata sake sanin abinda take ciki ba, hawayen Mama ya dauke lokacin data ganta a kid'ime ta kalli makociyarsu tace "baiwar Allah tunda kuna kusa don girman Allah ki rufe mata gidan ta bari mu koma asibiti muga abinda Allah zaiyi" jikinta yana rawa ta karba ta gyadawa mama kai, gabanta sai faduwa yake, gidan ta shiga ta rurrufe mata kofofin ta koma cikin gidan ta ita da mijinta sunata jajanta al'amarin,  sister Maryam ita tayi kokarin duba ta tagani har lokacin 4cm take, daganan tace "Maman Nabila ki kira Dr najib kawai a shirya CS babyn ma bai zauna daidai ba a cikin" tanayi tana sake dubata, hannun mama yana rawa ta kira Dr taci sa'a ko ya dauka bayani tayimai yadda lamarin yake nan take ya shirya emergency koda bai ganta ba suna zuwa akayi ciki da ita. Sai lokacin Hankalin Mama ya kawo babu kayan aiki dana Baby kiran waya takeyi ta yi na kawo mata nan take duk wanda ya Santa asibitin saida ya tsaya mata wasu nurses ma da suka tashi daga aikin safe sai suka kasa wucewa dan kana ganinta kasan akwai matsala ba kamar yadda suka saba ganin ta ba tanada fara'a da sakewa da mutane.

Wayar Nabila dayaketa kira ba a daga ba ya kara tayar mai da hankali, yana isowa ya bude gidan ya shiga bai lura da digon jini ba har ya zauna palo sanin bata nan, sai ya kira anty Maryam ta daga suka gaisa yace mata "Antynmu kanwarki tana kusa ne"? Tace "A'a bata zo ba nima yanzu nake kiranta bata dauka ba" ya tashi zaune daga gincirawar da yayi "gidanki nace taje zanje tambuwal bata zo ba, naga motarta na dauka ke kika zo kika dauketa" mikewa tsaye tayi itama tana cewa "Bari inkira mama inji ko gida taje" ta katse wayar sai ya ce "to ko bata fita ba tunda ko taje gida ga mota nan wazai kaita, kilama tana nan tana bacci as usual, yana fada ya shiga dakinta sai yaga wayar kan gado ga jini da ruwa kamar anyone rago, wayarta ya dauka ya shiga duddubawa hankali a tashe ya fito daga gidan ya rufe, har ya shiga mota ya fito ya kwankwasa kofar makotansu, mijin ya fito ganin shine ya rikw hannun sa bayan sun gaisa ya ce "Dr ya akayi matarka babu lafiya bakanan, bada dadewa ba yanzu iyayenta suka wuce da ita asibiti" wasu yawu ya hadiya dakyar tareda sakin hannunsa yace "Ibrahim akwai matsala, jini a dakinta kamar an yanka rago, bari inje" motar ya koma yajata da karfi.

Anty Maryam da taji meyake faruwa bata ma tuna da nemanta da Dr yake ba ta wuce asibitin.

Kusan a tare suka iso asibitin ita ta nuna masa inda su mama suke suna zuwa Mama ta rufe shi da fada "wane irin abune wannan Abubakar, ka bar yarinya ita kadai a cikin gida to ga abinda ya faru hankalinka ya kwanta" shuru yayi danshi ba fadanta ke daga hankalinsa ba yasan halin da matarshi take ciki Baba ne yace "Haba asma'u menene haka acikin asibiti" shuru tayi bata tanka shi ba sai komawa wani wuri tayi ta zauna, wurin Baba yaje ya gaida shi Nan baba ya fada masa abinda ya faru shima ya fada masa yadda sukayi kafin ya tafi.

"Baba yanzu ya ake ciki basu fito ba har yanzu"? Baba yace "to gamu nan dai ni wallahi duk jikina yayi sanyi muyita addua dai" Dr jiki a amace ya koma gefe ya kira yayanshi ya sanar dashi ya kira tambuwal, hankalin Mama ya tashi ta hijab kawai ta saka ta tafi tasha.

A can ciki ko lafiya lau suka ciro babyn data galabaita dakyar aka samu tayi kuka muryarta ko fita batayi sosai dan ta wahala, uwar ma haka aka dinketa da komai lafiya lau ita duk bata san anyi ba, sai da aka gama aka shirya baby lafiya lau sannan Dr yazo yana dudduba uwar sai yaga kamar bata numfashi, nan take suka fara kaiwa da komowa da gudu wata tsohuwar ward servant ta fita da sauri tana fadin "Innalillahiwa'inna'ilaihiraji'un meturon Allah ya baku hakuri ya zama gatan wannan jaririya da aka bari, innalillahi mutuwar kuruciya na roki ubangiji Allah ya karbi shahadar wannan yarinya, wannan ciki ashe batada rabon ganin abinda ta haifa" Dr yana jin labarin da take bayarwa ya kife, ana yayyafa masa ruwa ya farfado ya sake zubewa sumansa yakai biyar gaba daya kwakwalwarsa da zuciyarsa sun kasa dauka, mama da sauri ta tura kofar theater room din tana shiga ta hadu da Dr najib yana gaba ana turo gadon da Nabila take kai kurawa gadon ido tayi tana kallon ta gabanta na wani irin dokawa....






*Dr A.S. Zaki*

EXQUISITE WRITERS FORUM 
*SAFIYYAH GALADANCHI*

_sadaukarwa ga yayata Billy galadanchi_

SHAFI NA ASHIRIN DA BIYAR




banyi shafin nan acikin dadin rai ba, daya daga cikin fans dina Aisha usman ta rasa mahaifiyarta yau, don Allah ku sakata acikin addua Allah yasa mutuwa ta zama hutu a gareta

"Bisimillah matron an samu dakin da za'a kaita ko"?  Ya fada yana sa hannunsa a tura gadon "Mama tace Daki ko dai kabari Dr" cike da mamaki yace "kamar yaya? Ga yarinya idonta biyu, wayace miki ta mutu" dafe kanta tayi tana sauke ajiyar zuciya sannan tace "inna shatu, mijin Nabila suman sa Uku" a hasale Dr ya fita da kudurin dole sai tsohuwar nan tabar asibitin nan haka kwanaki ta jaza musu bala'i tayiwa wani bawan Allah albishir ya samu da namiji bayan shekara goma basu samu haihuwa ba sai gashi babyn ashe bata ma zo da rai ba kuma macece, mijin yaki yarda yace canza mai jariri akayi dakyar aka samu case din nan ya mutu, yanzu kuma gashi tayi ihun an mutu bayan ba uban daya fada mata cewar an mutu, Nabila da ake turawa kan gado ta bude idonta da take ganin ba daidia ba bata gane komai ba ta sake rufewa, sai lokacin mama ta fito ta hadu da sister Maryam ido sun mata jajir tasha kuka Mama ta kalleta tace "an gyara dakin"? Tace "eh" mama ta sake cewa "inna shatu da hauka ashe ba mutuwa akayi ba itace ta gigita mu, gata nan ana fitowa da ita" sister Maryam ko ta hau bakinta sai abinda ta mance wani data sani a ministry ta kira tana fada masa abinda yake faruwa.
Saida aka kaita dakin bacci ya dauketa sannan aka fara barinsu su ganta, Dr da kansa ke balain yi masa ciwo shi ya fara shiga, sai ajiyar zuciya yake saukewa kin fita yayi sai dai duk wanda ya shiga ya ganta ya fita jaririyar ko tana hannun Anty nusaiba sai ruwan zamzam aketa bata tana kananan kuka.
Sai lokacin mama ta samu ta koma gida ta harhado abubuwa ta dawo, mama ta tambuwal ma saboda wannan jidalin yasa dare yayi mata dole Anty Maryam da zata wuce ta kaita gida wurin Mama dan baba yace sai dai a samu wani ya kwana da Nabila sai aka tura wata Inna rabi dake hidima dasu idan lalura ta tashi a gidan, Dr kasa komawa gida yayi sai da yaga ta farka kan idon shi sannan hankalinshi ya kwanta, nurse dinda ke duty a daren aka kira sai akayi sa'a Dr najib yana yanan tare suka shigo dakin yana mata tambayoyi ko akwai inda yake mata ciwo, ta bude baki zatayi magana sai hawaye, dakyar tace "ciwo, cikina ciwo" ta fada tana jujjuya kanta nurse din ya matsa baya yacewa "bilkisu ku tada ita tsaye" bude baki Nabila tayi tace "Don Allah karku tadani wallahi ciwo nake ji" ta fada tana rike hannun Dr dake kusa da ita ya kalli Dr najib yace "likita ba matsala ai" ya gyada masa kai yana cewa "Eh ba matsala inbata motsa jikinta ba nan zata fi jin ciwo tunda allurar ta sake ta yanzu" zanin jikinta ya gyara mata suka tada ita zaune tana ta fadin "Innalillahiwa'inna'ilaihiraji'un Abubakar zafi ku barni na kwanta" kan kujerar roba suka zaunar da ita tana sauke ajiyar zuciya, Dr najib ya ce "bata babyn ta shayar da ita tunda ta farka" yaja hannun Dr suka fita, inna rabi da nurses din ba karamar darga sukayi da Nabila ba taki yarda su sake mata yarinyar wai karta danne mata ciwo.
"Abubakar nayi maka murna gaskiya, matarka tayi arziki irin haka ake yin sa'a da karar kwana amma ita dayake akwai sauran rayuwa a gaba ta tsira, babynku masha Allah gaskiya a shekarar nan babu babyn da tayi girmanta da kyau a dage da addu'a, yanzu abubuwan da zaka ajiye musu zan rubuta in baka dan wucewa zanyi akwai likitan da zai zo da dare yayi mata, na fadawa nurses din nan tunda matron ta wuce suyi mata dressing din ciwon" godiya Dr A.S yayi masa sannan ya karbi takardar yaje ya siyo kayan ya dawo, koda ya shiga har lokacin tana zaune gefenta babyn ce tana ta bacci zama yayi gefen gadon yace "kin gama ihun" kallon shi kawai tayi tace "a samomin kaya in saka" akwatin da mama ta kawo ya bude dan Inna Rabi ta fita rigar bacci sabuwa ya dauko mata ya saka mata tareda hula sannan ya sassauta mata zanin bai daureba dan zai taba ciwon, saida yaga ta kwanta tana cewa yunwa takeji nurses din nan sunce abata tea tasha ya gama hada mata ya bata tasha sannan yayi musu sallama ya wuce, daren nan saidai bacci barawo ya sace ta, washe gari tun karfe shida da rabi mama ta iso ita tayi mata wanka da towel ta goge ciwon tare da bata wasu kaya ta saka tana cewa "baku dinka zani kullum kece doguwar riga yanzu saida kika sa na yaga turmin atamfata na hada miki da top, tana sakawa tace "Mama ina da riga da zani bayan wanda na dinka lokacin aurena na sake yin wasu biyu suna nan gida" "sai ki kira mijinki yazo miki dasu yafi a ganki da wannan cas Kuregen" wayar ta ta tambaya aka bata ta kirashi lokacin har ya gama shirin fitowa komawa yayi ya dauko mata kayan yana jin wani irin sanyi har cikin ranshi saida ya sake hada musu kayan break fast harda iyayi ya dafa mata infomie ya soya kwai ya tafi asibitin, ganin mama ya saka ya kasa zama ya wuce kafin sha biyu duk su anty Maryam suna asibitin Maman Dr kuwa tana biyowa ta gaida Nabila da jiki Dr ya kaita tasha ya dawo.
Sai da mutane suka rage ta samu kanta sannan ta kira Nana sule, tana dagawa hakuri ta fara bata dan taga missed calls dinta amma bata kirata ba "malama Na sauka sai kizo kiga yarki in kinada lokacinta ita" Nabila ta fada tana turo baki, Nana tayi ihu kamar zata fasa gidan tace "kuna ina"? "Muna asibiti cs ne" kashe wayar tayi ta dauki goyonta ta rangada Abaya ta fito dan mai aikinta taje ganin gida, sai a hanya ta kira mijinta ta fada masa yace to Allah ya tsare.
Kwananta biyar a asibiti aka sallameta suka koma gida dole mama ta dauki hutu.

Suna zaune a daki tana kokarin canzawa babyn pampers Mama ta shigo tana cewa "Maryam tace min wai kince ayi suna jibi, anya kina iyawa" daukar ta tayi tana jijjigata tace "Mama ayi in huta gaba daya ko an kara sati daya mutane ba bari zasuyi a huta ba idan akayi sunan kowa sai ya kama kafarshi kinga ko su anty Maryam zasu samu su zauna gida su huta" Mama tace "to Allah yakaimu jibin lafiya sai ki kara magana da telanki kar yayi disappointing dinki" wayarta ta dauko sannan ta mikawa mama babyn tace "mama wuce da ita don Allah in samu inci abinci ta hana" Mama ta karbeta tana dungure mata kai da wasa tace "haba babyn nan kina wahalar mini da autar mata fa" itakam abin nema ta ya samu ta tuwon taci sosai ta dauki kofin fura ta shanye, tana kokarin tashi wayarta  tayi ringing ganin Dr ne tasan ya iso dan tun magrib yace gashinan zuwa, hijab dinta ta saka ta sameshi palon Baba riko hannunta yayi ta zauna yana cewa "ina babyn" tayi murmushi tace "za a kawota yanzu na leka ne naganta a hannun baba" ya gyara zamansa yana cewa "yajikin to"? "Naji sauki, matarka ta kirani dazu tace batajin dadi amma zata shigo gobe" ya gyada kai dan yaji dadi karo na farko yayiwa Nafisa Jan ido kuma ta rusuna saboda seda suka kai ruwa rana kafin ya samu ta kira ta din kuma yace bazai bata koda kudin motar zuwa bane tazo dan kanta, "Eh haka ta fadamin dazu a waya ciki gareta ashe" murmushi Nabila tayi tace "Lallai zaka sake zama daddy for the second time" hannayenta biyu ya hada tare da bata rai yace "ranar bana ce miki ki kira Maryam ko kije ba kika zauna ke kadai" gabanta ya fadi ganin kamar da gaske yake, sai ta dan saki fuskarta tace "Don Allah kayi hakuri, bacci ya daukeni inata sauri in fita sai ciwo ya kamani na kasa fita inata kiran waya duk basu dauka ba" ajiyar zuciya ya sauke yace "ai bance ki kwanta ba, har kinsa mama taga laifina ranar don Allah kiringa jin magana" ta gyada masa kai sannan ya sakar mata hannu suka ci gaba da hira, suna zaune suka jiyo kukan jaririyar duk ya karade gidan, saurin tashi tsaye tayi saiga anty Maryam ta shigo tana cewa "wannan yarinya bata aruwa sun hade kai itada Muhammad sun tayarmin da hankali" Nabila ta zauna tana dariya tace "inata so in fada miki jiya da dare bacci ta hanani yarinyar nan saida mama tazo ta dauketa, tana fita na rufe kofa da key sai gasu sun dawo naki budewa" ta ajiye mata ita tana cewa "yarinya yanzu ma kika fara karbe ta dan ta jima tanayi bata jin rarrashi ne" karbarta tayi ta samu wuri ta zauna tana cewa "sannu da zuwa yarinya mai kamada ni" dariya yayi yana cewa "Anty Maryam kinaji ko? Batada kunya" anty Maryam ta fita tana cewa "ai nagani ko kara batai mana".

Washe gari karfe biyu Nafisa ta iso bayan sun kwashi yan kallo da Dr wai batasan inda zata sauka ba, kashe wayarshi yayi ya kyaleta dole ta ajiye girman kai ta kira Nabila, wani bashar dake gidansu ta tura ya daukota ta shigo gidan tanata raba ido, Nabila da kanta ta shiga kitchen ta kawo mata kayan abinci da ruwa, tana zaunawa saiga kiran waya a wayar Nafisa ta daga tana fadin "anty saratu na iso" ta danyi shuru "wallahi ko kowa haka yake cewa ciki kamar ba wata biyu ba" tayi dariya sosai ta sake cewa "ancen cikin da namiji ke tsini, Allah dai ya raba lafiya" ta sake yin shuru daga baya tace "eh gatanan" ta fada tana mikawa Nabila waya, Nabila tana zaune tana kallonta tareda murmushi akan zancen da take kanar ita take fadawa wai cikin da namiji gareta karbar wayar tayi suka gaisa bayan ta ajiye wayar tace "Ashe ciki gareki, Allah ya raba lafiya ya inganta" Nafisa ta kalleta aranta tana cewa "magaji dai na nan zuwa bazaki sameni a gida ki haifa namiji ni ban haifa ba" a fili kuwa tace "ameen".




*Dr A.S. Zaki*

EXQUISITE WRITERS FORUM 
*SAFIYYAH GALADANCHI*

_sadaukarwa ga yayata Billy galadanchi_

SHAFI NA ASHIRIN DA SHIDA




Anty Maryam ta hadu da ita suka shiga wani daki daban tana nuna mata kayan data karbo mata tareda fadin "mijina yau sai da muka kai ruwa rana dan nace zan karbo miki dinki unguwar rogo, wai ya gaji da yawo" Nabila ta karbi kayan tana budewa tace "Ai da gaskiyarsa anty amma dai ya kara yi mana hakuri" tsaki Maryam tayi tace "yayi fushi yabarni da abinci na yau na safe, ana hidima gidanmu ya hanani yawo ai sai dai yayi hakuri" Nabila ta gwada kayan ajikin ta, daidai sukayi mata dan duk gowns ne ta cire tana cewa "Anty duba min dinkin nan kaikayi yakemin da zafi kadan" ta kwanta tana dage rigarta sama, dubawa tayi taga bakomai tace "kila warkewa zaiyi kije ki goge shi yanzu, ina kishiyarki da akace tazo" zaune ta tashi tana gyara rigarta tace "Tana dakina, bata dade da zuwa ba" Anty maryam ta dauki Jakarta ta kalli Nabila "Nan zata kwana"? Ta tambaya, Nabila ta danyi murmushi tace "Eh batada kowa nan inaga, anan dai zata kwana dan wallahi inya kaimin ita gidana sai munyi bala'i" maryam ta daki kafadarta tana yamutsa fuska tace "bama zai fara ba dan yana zuwa da ita wallahi mancewa zaiyi dake yayita murzarta" tsaki Nabila tayi ta fara tafiya tana cewa "bar fadamin karna kasa yi mata kirki yau" dariya maryam tayi suka fito daga dakin.

Washe gari tunda sassafe aka radawa baby Suna Ramla sunan yaiwa mutane Dadi, Dr kuwa alkawari yayi tuntuni saboda yana son sunan sai gashi yau Allah ya bashi ikon cikawa ya roki alfarma baya son lakani koda daga bakin Nabila ne su kirata da sunanta, Mai makeup har gida ta sameta tayi mata makeup da daurin dankwali, a sace Dr ya shiga gidan aka daukesu hoto ya wuce.

Sai shagali ake cikin gida kowa yazo saboda Nabila mutuniyar mutane ce, Nafisa kuwa bata sake ba sai da yan tambuwal suka zo jikinta duk a mace yake tana kallon yadda akai wasa da kudi wanda da gani tasan yafi karfin yin mijinta shikadai, abinci yakai kala biyar gashi batada ruwan leda na yawo ba sai na roba da drinks abinci babu kalar da akayi ba Nama, alala ma harda dafaffen kwai da Anta a ciki, manyan mata da yanmata suna shiga da fita, jikinta bai yi sanyi ba saida akazo walima shigar Nabila kadai ta girgiza gashi duk inda ta wurga kamshi take, filin gidansu yasha decoration kamar ranar aure.

Sai karfe shida Dr ya turo bus biyu a daukesu a maida su Tambuwal Nafisa ta nufi wurin Nabila tana murmushin yake, tace "Nabila zan bisu mu wuce har na dauko kayana" Nabila ta mike tsaye a gajiye tana dora Ramla a kafadarta tace "to muje kiji" suka dan matsa daga wurin mutane tace "Don Allah ki kirga min mutanen da suka zo ko a waya saiki fada min yanzu kinga na gaji Mama ma hankalinta ba a kwance ba, da safe zan aiko da sako sai ki basu, kuma na gode sosai naga abin arzki Allah ya nuna mana kema kin sauka lafiya" amsawa tayi da ameen sannan ta raka ta har gate sai da taga wucewarsu ta dawo gida.

a daren nan saida taje emergency saboda azabar ciwo da dinkin nan yake mata, data samu tayi bacci ranar Ramla ba wurinta ta kwana ba sai da asuba Mama ta kawo mata ita, Dr kuwa kamar zai Ari baki a waya data fadamai taje asbiti dan saida yaja mata kunne akan yawo yace kartayi tunda taga aikin kwananshi bakwai bai warke ba karta janyo wata matsa, sai da yayi shuru sanann tace "Don Allah kayi hakuri Naji sauki sosai ma banjin ciwon komai" ajiyar zuciya ya sauke saboda duk yadda ya dauko zafi bata katse shi sai ya sauke sannan saita dabaibaiyeshi da kalmar hakuri, shikam ya rasa wace irin yarinya ce aka haifa mai matukar saukin kai, ya tabbata da Nafisa zatayi masa koda rabin halin Nabila ne to zai sota koda rabin son da yakewa Nabila, ba wai baya sonta bane Halayenta ne suka sa ya kasa ganin farinta balle har ya fahimci yana sonta.

"Shikenan ya wuce, Ina Ramla" murmushi tayi jin ya sauka daga fushin tace "Gatanan duk ta tsotseni gashi ina jin zafi" yayi yar dariya "to kiyi hakuri idan tayi shekara biyu sai ki yayeta" a ranta tace, nabi shekara biyu da gudu, a fili kuma tace "Allah ya nunamin na yayeta din" ya amsa da ameen tareda cewa "ankoma makaranta" ta gyada kai "Eh amma nikam ai sai na kara hutu Nana sule ma ta fadamin jiya nace babu damar komawa da wuri, kila sai bayan sallar layya zan koma" hira suka ci gaba dayi yana bata labarin abokanansa yadda suke ta yabon abincin da abubuwan da aka raba musu.

yana yawan zuwa gidan ganin Ramla da uwarta tareda jin kewarsu kamar yayi hauka, a lokacin da Nabila ta dauka bata nan har ya fara ramewa dan baya iya cin abinci ko ina shi gashi bai iya yawon dangi neman abinci ba, gidan daya zauna kafin aurensu ma yakanje amma bai taba tsaywa yaci abinci ba, sai idan yaji ciwon shi na neman tashi sai ya tafi inda Nabila ta bashi abincin yaci, yauma kallonshi takeyi dan tun a makaranta ta fahimci baida lafiya, duk ya rame yayi duhu "yanzu fisabilillahi idan na mutu haka zaka koma duk kabi ka lalace? Ka ringa zuwa kana cin abinci to idan zan fita karfe takwas ko goma zan taho maka da abinci office" ya kalleta yana marairaice fuska yana cewa "kibar batun mutuwa, amma wallahi Nabila duk inda naje kasa ci nake musamman na siyarwa na gwada ranar nayita amai dan kyankyaso nagani a miyar, gidan Barrister kuwa wallahi ko sanda nake kwana gidan ban iya sakewa inci balle yanzu gashi ke kuma kince ba yanzu zaki dawo ba" tagumi tayi tana tunani ita dai bazata taba iya cewa a maida ita ba kuma koda wasa mama bata yi mata maganar komawarta ba, Mama kuwa ita a ganinta aiki akayiwa Nabila dan haka saitayi wata biyu sai ta koma dakinta yaran yanzu ba kunya garesu ba kar aje aiki ya samu matsala ko ta sake kwaso wani ciki abu ya lalace musu shiyasa ta kyaleta dan taga Nabila din ma kamar bata damu da komawar ba, "Dr ya zanyi to? Nidai bazan iya cewa amaidani ba ko anty Maryam bazan iya fadawa ba, ka dai

Please Login or Register in order to submit comment