Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da idonta suke a kumbure saboda wahala ta ce "ina kwana" ya daga kai tareda cewa "lafiya lau, ya bakon wuri" shuru tayi ta kasa bashi amsa, komawa yayi ya kwanta, ita ma saita lafe a kasa saboda yadda idonta ke rufewa dakansu dan bacci.

Sai karfe goma ya tashi, dama yana cike da haushin bacci yau ko ya samu ya rage, yana kallon yadda ta takure a kasa amma bai taba ta ba yashiga toilet yayi wanka ya fito sanye da kayan baccin ya dubeta tana zaune dan motsinsa ya tada ita ya ce "idan kin fita palo akwai kofa hannunki na dama da key a jiki, ki bude ki dauko min wata jaka kan gado zan dauki wani abu ne" wasu wahalallun yawu ta hadiye sannan ta fita ta bude kofar dakin tayi sallama dukda batayi tunanin akwai mutum ciki ba sai ji tayi ance "sannu uwar iya bariki da karuwanci...."


*Dr A.S. Zaki*

EXQUISITE WRITERS FORUM 
*SAFIYYAH GALADANCHI*

_sadaukarwa ga yayata Billy galadanchi_

SHORT STORY 

SHAFI NA GOMA SHA DAYA




Da mamaki take kallonta dan ita bata ma Santa ba ko jiya da aka kawota ba a wani kaita wurin wata ba bayan mahaifiyarshi, ko dai itace matar da ake cewa yanada? Kawar da tunanin tayi ta gaida ita "ina kwana" amma maimakon ta amsa mata sai tace "yana gidan ubanki, ina mijina? Karfe goma sha daya kin kulleshi a daki ko kunya babu" yadda take zazzare ido ya saka tayi azamar matsawa baya cikin tsoro tana mamakin to me tayi mata, sai ji tayi ta riko mata hannu, saurin Fizge hannun tayi ta fita tareda tura kofar tana cewa "ko dai mahaukaciya ce"? Shikam ya gaji da jiranta dan jakar sababbin Boxers da T-shirt dinsa ke ciki yana so ya sauya sai ya fito daga dakin yana kallonta taja ta tsaya "Ina jakar"? Ya tambayeta sai da ta hadiye miyau  tace "banganta ba" "ki shiga tana nan kan gado nace" ya sake tura ta dan haka kawai yake son kureta ko aikansa ne bata son zuwa, bude kofar tayi a hankali sai dai kafin ta karasa budewar sai ganin kanta tayi a kasa saboda yadda Nafisa ta turo kofar da karfi "subhuhanalillahi" ya fada tareda matsawa kusa da Nabila mikewa tayi da kanta tareda nufar cikin dakin tana shiga ta zauna tana kallon hannunta inda farcen Nafisa ya yage ta harda jini, tsaki tayi tareda cewa "an hada mutum da kauyawa, daga zuwa na har an fitar min da jini wato farautar rayuwata ake" dafe cikinta tayi daya koka saboda yunwa, durkusawa tayi gaban akwatin tarkacenta ta bude ta fito da brush da toothpaste ta shiga toilet.

"Kin fara shaye-shaye ne? Me tayi miki da zaki tunkudota haka har ta fadi, kin san me nafisa? Na rantse da Allah kibi a hankali nan da kike ganin Nabila bata iya fada ko neman magana ba, karki lalatamin ita da banzar rayuwarki daga zuwanta, idan kuma kika ji mata ciwo na miki rantsuwa sai na dauki mataki, bani key din daki na dake wajenki" ja tayi ta tsaya tana kallonshi gabanta sai faduwa yake "kibani nace" ya fada a tsawace dan yaga key din a hannunta, mika masa tayi sannan ta karewa palon kallo tareda fita, koda ya koma dakin ya samu tana toilet man ta ya dauka ya shafa tare da fesa turarukanta ya sa kayanshi ya fita zuwa sashen mama, bai dade da fita ba ta fito daga wanka saida ta leka taga baya dakin sannan ta fito da sauri ta shafa mai ta saka doguwar riga ta atamfa ta yafa gyalenta sannan ta nufi kitchen dinta dake waje ta bude fridge ta fito da kazar jiya da exotic, nan ta zauna kan kujera tayiwa naman kaca-kaca tasha exotic din sannan ta koma daki ta kwanta, ta rufe idonta da niyyar yin bacci sai gashi ya turo kofar dakin ya zauna gefenta yana cewa "muje ki gaida su Baba" tashi tayi da sauri tunowa da tayi suna nan ta janyo mayafinta ta yafa, ganin yadda tayi saurin tashi duk sai ya burgeshi da alama rigimar nan ta saka ta mance dasu shiyasa tayi saurin tashi, tana tsaye ya sameta a palo ya kalli hannunta inda taji ciwo harda sauran jini, yaji haushi dan ya san aikin Nafisa ne.

Har kasa ta durkusa tana gaidasu, fuskar mama dai baza a ga farin ciki ba amma kuma ba a daure take ba, Baba kuwa ya saki jiki har yana janta da hira tareda tambayarta kota ci abinci, murmushi tayi tace "naci Baba" ya gyada yan yaran gidan dana makota duk sun zagayeta suna kallonta sai duk taji idanu sun mata yawa, karfe daya ta koma dakinta bata dade ba su anty Maryam suka iso, dukansu sai kallon kurilla suke mata duk inda tayi suna kallonta ta ce "anty meramu kallon fa"? Anty Maryam tace "ganinki nayi kalau, duk gyaran da muka miki haka kika bari daren jiya ya tashi a banza" hararar ta tayi tace "gyaran na jiya ne kawai? Ni ki bar yimin maganar nan Anty nusaiba kice mata ta bari mana" Anty nusaiba tayi dariya tace "maryama kyaleta, ai duk wayon amarya sai ansha manta, muna gida Dr zai murkushe yar iska" anty Maryam ta tabe baki tace "oho dai gaya mata, ke Nabila dauko mana kazar amaryar dai muci muji ko ta gasu" dariya tayi ta shafa cikinta tace "kaza tana nan, yau da safe na shige kitchen nai mata cin huce haushi amma na dan rage" anty Maryam ta ce "wallahi sai kin biyashi kazarshi mara kunyar banza" zama tayi tana basu labarin Nafisa Anty Nusaiba tace "ke tsoron iskancin nan ya tsaya iya mijinki, kika nuna mata tsoro wahala zakiyi, ba cewa nayi ki biyeta kuyita hauka ba, amma dai banda nuna mata tsoro" sallama suka jiyo a palo Nabila ta amsa tareda fita, wasu tsofaffi ne suka shigo wai ganin daki, sakin fuskarta tayi ta kaisu har dakin suka gani suka fito sunata yi musu addua sai da ta raka su har tsakar gida bayan sun fada mata sunansu da matsayinsu a wurin Dr, wunin ranar haka tayi shi da baki har kusan magrib, gashi ba a kawo abinci ba, su anty Maryam sai mita suke mata ta gaji tace "to ni da akwai kayan abincin ai zan dafa da kaina, tun safe fa ya fita bai dawo ba sannan uwarsa ba sona take ba balle tasa adafa akawomin, kuyi hakuri ga biscuits can ajaka in kawo muku da exotic din daya rage guda daya kuci tunda kun kusa wucewa ma" Maryam dama bata hakurin yunwa saboda cikin da take da haka kuwa biscuits din suka ci har ita Nabila sannan ta rakasu mota suka wuce tana cewa sai tazo.

Koda akayi magrib babu wuta salla tayi ta zauna tana chtn a waya har akayi isha'i tayi sallar tareda shirin bacci ta kwanta, sai karfe tara ya dawo, gidan ya kuwa yi sa'a duka bakin basa nan dama du yake jira su waste, bangarenta shuru ga duhu kamar ba kowa, ya shiga dakin bayan yayi sallama, ta tashi zaune ta lalibo hijabinta ta saka tareda sauka kan gadon dan taga nan ya nufo ta gaidashi ya amsa tareda riko hannunta cike da son tsokanarta ya rungumota ta gefen kafada, ji tayi kamar tasha baking powder saboda yadda yawunta sukayi tsam, ta rike jikinta sosai "Babyna ya gida" ya tambaya tayi masa shuru, "bari ingani bakin nan yana aiki har yanzu ko ya mutu, bata fahimce shi ba sai ji tayi ya hade bakinsu "matse cinyoyinta tayi da karfi ta rikeshi tana kokarin raba kusancinsu, karfi ya saka mata dole ta hakura tana jin abinta yafi karfinta.

Duhu ta kurawa ido tana jiran taga yayi wani motsi ta bar masa gidan, har yanzu hannunsa take ji yana kaiwa wasu wurare a jikinta inda bai kamata ba, shikam sai murmushi yake yana shirin bacci har ya gama ya hawo gadon tare da cewa "haka ake tarbon ango Nabila? Baki bani abinci ba ko an cinye" daga nesan da take dashi ta ce "babu abincin" tashi zaune yayi ya ce "keda wa kuka ci" ta ce "ai ba a dafa bama" ya zaro ido yana cewa "ko mama ko Nafisa babu wanda ya kawo miki abinci? To me kika ci"? Muryarta na dan rawa dan dama tunda ya lagudeta take jin kuka tace "biscuits mukaci dasu anty Maryam kafin su wuce" bai yi magana ba ya tashi ya fita da wayarta yake haskawa ganin duhu yasa ta bi bayanshi ta tsaya kofar palo, ta dan jiyo muryarshi daga bangaren Nafisa yana balbaleta da fada sai Mama ta shigo part din ta kalleshi tace "daina daga mata murya kai, ita kayiwa amarya dan ta hanata abinci zaka sakata agaba kamar ubanta" ya dubi mama yayi kasa da murya "haba mama mutum fa aka ajiye ya wuni baici komai ba, nayi tunanin in batayi ba ke ki saka ta balle babu abinda ban ajiye ba na abinci saboda a dafa duka gida, gaskiya bakuyimin adalci ba" mama ta dubi Nafisa ta ce "ke wuce ki kwanta abinki kyaleshi, kai kuma inji saukar duka ko"? Baice komai ba ya juya ya koma part din Nabila, a bakin kofa ya hadu da ita jan hannunta kawai yayi ya koma daki da ita tareda cewa "dauki kayanki ki saka" tana kallonshi tace "ina zamu"? "Sokoto" ya bata amsa tana jin tsoro amma kuma sai taga in suka tafi akan yar wannan maganar zai iya kara ja mata bakin jini "bafa najin yunwa ka bari da safe zanyi girkin da kaina ba sai nsa wani ya dafa min ba" cikin tsawa ya ce "kisaka kayanki nace" bata ma san ta turo baki ba ta juya wurin wardrobe kayan ta saka ya fita tabishi suka rufe gidan yana rike da hannunta suka fito wajen gate Baba yana zaune yaga fitowarsu sai ya kirashi ya ce "ina zaku? Bai kamata kayi fushi ba tunda su duka kasan halinsu, ku koma ban yadda ku tafi ba" Ajiyar zuciya ya sauke baba ya kira Nabila ta dan matso ya mika mata leda tareda cewa "kije kici amma ki shirya gobe ki cirewa kanki takaici" karba tayi tana godiya taji dadi dan dama ita bata so su tafi, komawa sukayi dole itakam kitchen ta wuce ta juye indomie din a plate ta zauna palo taci tasha ruwa sannan ta koma dakin, ta maida kayan ta na bacci Dr kuwa yana nan kwance yana cin ransa, karshen gado ta hau ta kwanta ta rufe idonta da niyyar bacci amma sai taji ya janyota da karfi ta juyo tana fuskantar shi, hannunsa yake yawo dashi a jikinta ta rike hannun ya kwace hannunsa yana cewa "ba abinda zan miki hajiya ai first nyt dinda zakimin aljanu sai a sokoto ko"? Tayi masa shuru cike da kunya, kyaleta yayi ya rufe idonsa dan dama so yayi ya samu abinda ya samu a daren amma duk da karfin halin da takeyi wajen danne tsoron bai hanashi jiyo rawar da jikinta keyi ba shiyasa ya kyaleta randa zai zage a jikinta ranar zata fahimci bai san tsoronsa take ba.


*Dr A.S. Zaki*

EXQUISITE WRITERS FORUM 
*SAFIYYAH GALADANCHI*

_sadaukarwa ga yayata Billy galadanchi_

SHORT STORY 

SHAFI NA GOMA SHA BIYU




Washe garinko tunda sassafe aka kawo mata kayan aiki ta bude set din tukwanenta ta fere doya daya ta tafasa ta soya dakwai ajikin camp gas dinta da already Baba ya mata refilling dinsa tunda aka kawo kayan, debar musu tayi tasa saura a wata babbar kula tasa hijab dinta da kanta tayi sallama sashen Mama ta gaida ita ta amsa mata ba yabo ba fallasa sai ta ajiye kular tayi mata sallama, Mama ta ce "Ahhh Nabila wannan kokari haka tunda sassafe? Sannu Allah yayi albarka" ta karasa maganar bayan ta bude kular idan tace bata ji dadin wannan lamari ba tayi karya wallahi har kular ma gwanin sha'awa.

Tana komawa cikin gidan ta debarmasa ta kai masa har daki sannan ta dawo ta yanka kajin da aka kawo ta wanke ta dora tafasa sannan ta zauna anan kitchen din taci nata, dama ita muradi kawai ta ganta a zaune ba inda bata iya cin abinci indai zai shiga.

Bata fito ba sai karfe daya saboda gas din daya ne dan haka dole seta sauke wani take dora wani, ta wanke kayan duka ta koma cikin gidan tanajin matukar gajiya, a hankali ta shiga dakin ta ganshi a kwance yana bacci, komai a hankali takeyi har ta gama shirinta gudun kar ta Tadashi yauma atamfar ta saka riga da zaini ne, ta matukar iya daurin zane ta dauko mayafin da zai shiga da kayan ta dora ta fita a ranta tana cewa "se nagani idan kirki baya siye uwar miji kafin na karasa 5 days din da suka rage sena tabbatar sai taji dadin zama dani fiye da waccen mai hanci kamar yar china" shiga tayi ta samu tana salla ta zauna zaman jiranta, baki suka shigo gidan su da yawa ta dan saki fuskarta suka gaisa matar da yaranta su biyar biyu maza uku mata biyu ta ce "ko dai amaryar ce"? Nabila tayi murmushi kawai mama data Hattama salla ta juyo suka gaida dukansu ta kalli Nabila ta ce "matar yayanku ce dake Abuja yara ke jarabawa shiyasa sai jiya da dare suka iso" Nabila ta ce "hakane kuwa dan ina ganin su a status din Farida" abincin data kawo Mama ta ce suci Nabila ta rike hannun yan matan ta ce "kubarwa su mamanku wannan da yaya kuzo muje inbaku wani" ta rike hannun yaran kuwa suka bita a palonta ta zaunar dasu ta zuba musu a tare suka zauna suna ci, tana kwance tana hutawa dan cikinta ya dauka sosai karama acikin matan ta fara janta tana cewa ta rakata inda umma "mikewa tsaye tayi ta dauketa sannan taja hannun dayar suka fito, koda ta shiga part din ta samu Nafisa na can dan haka tana ajiyesu ta juyo, a hanya suka hadu ya fito daga cikin gidan dauke idonta tayi daga kallonsa, Dr yayi murmushi mai sauti ya rike hannunta ya koma cikin gidan da ita, "baby yunwa tun dazu nake bacci baki tashe ni ba" yadda yayi maganar wani iri taji kamar karamin yaro, cikin kokarin gwada nasihar da su Anty sukai mata ta ce "Eh kasan ba a son tashin mutum in yana bacci zai iya tashi da ciwon kai abincinka yana nan palo kan table" shiga sukayi ta zuba masa abincin yakici da kanshi wai sai ta bashi abaki, zaro ido tayi ta ce "Mama ta kirani najita kafin in shigo" ta mike tsaye zata gudu, hannu yasa ya dawo da ita gefenshi ya rungumeta ya ce "to zanci da kaina amma ki tsaya kusa dani ina kallonki ina jin sanyi a raina ke kuma kina samun lada" shuru tayi tana mamakin wannan lamari kan cinyarsa daya ya kwantar mata da kai tana fuskantar cikinshi, da sauri ta rufe idonta a ranta ta ce "ohh kamar ba malamin da nake gani a gaban aji yana hura hanci ba, yau nice kwance a cinyar shi yana min iya shege, gaskiya ban taba tunanin irin wannan zai shiga tsakaninmu ba" daga tunani bacci ya dauketa, bayan ya gama cin abincin ya janyo pillow dake kan kujera ya dora mata kanta sannan ya fita, part din Nafisa ya shiga Ya sameta zaune bakin kofa tana chtn wnda duk rabinsa voice note ne da Farida ta koya mata yadda ake dan ta gama secondary school amma bayan sunanta da kananan kalmomi ba abinda ta iya rubutawa a hausa, kallonta yayi gata da hasken fara kuma ba mummuna bace amma rashin kulawa ga jikinta na son dakusar da ita, hannu yasa ya mikar da ita sai toilet ya hada mata ruwan wanka ya barota toilet din dole tayi wanka dukda ko gaidashi batayiba, koda ta fito duk ya zubo da kayan wardrobe dinta da sukeda datti dakyar ya samo gown a kasansu ta dade a goge ya zarota, saida ya shiga dakin Nabila ya samo turare guda biyu ya dauki hotonsu sannan ya kai mata dakinta, Basilin kadai ya gani kan mirrow ya ajiye mata ta shafa yana tsaye saida yaga tayi yadda yakeso sannan ya ce "ki daure kayanki zan turo mai wanki ya dauka, sannan bari kiji bawai ina yin wannan kokarin bane dan ina son kiringa tsafta a'a Inayi ne dan karewa kaina mutunci da jin kunya a mutane a dubeki a lalace ace wai ni nake aurenki, inkinga dama ki gyara in baki ga dama ba kici gaba da kazanta Allah ko kwanciya dake zan ringa kyankyami" kuka ta fashe dashi dan taji zafin maganar shi ta karshe ta gabanshi tabi ta wuce part din mama.

Bi bayanta yayi dan ya shirya ayi wacce za ayi, yana kokarin shiga sai yaji mama na cewa "ke don Allah yimin shuru, kullum ke akewa laifi? Babu abinda kika iya, girki kikayi ko lasuwa bayayi, kiyimin shuru kina jina ko tun wuri kisan me yake miki ciwo, kalli Nabila ki gani ga kyau ga tsafta ga iya girki, karewarta ga ladabi, ki tashi tsaye ki kama mijinki kindai ga yaje birni ya dauko yar boko kamar shi kina nan zai mance da sunanki wallahi" maimakon tayi shuru sai hawaye suka kara zubowa amma saboda mama tana sonta yasa taji tausayinta tace "kiyi shuru zan masa magana kinji bazai sake cin zarafinki ba yi shuru mana" juyawa yayi yana murmushin jin dadi, bai dawo gidan ba sai dare, kitchen ya samu Nabila rike da wayarta tana haskawa sake gyara kitchen din take bayan kammala dafa shinkafa ta ajiye suci da sauran sauce dinda tayi da rana, rigar jikinta mai santsi ce dan tayi shirin baccinta rigar tanada wando iya cinya kalar purple mai haske tabi jikinta duk da ba wani kayan azo a gani gareta ba amma tayi kyau kitson kanta ya sauko har wuyanta anyi mata shuku, sai kamshi take, waya take da Nana Sule tana cewa "Wai yaya dai inace kinkai ga first EDD dinki" shuru tayi tana sauraronta kafin su gama suyi sallama, ta ajiye wayar tana cewa "chab...gaskiya sena hada da mai aiki inaga wannan gararamba har ina" turo kofar yayi ya shigo, gidan sannan ya tura kofar ya rufe ya karasa shigowa, ta window din kitchen ya fara hangota da dan saurinsa ya zaga ta kofa yana maimaita sallama, ta amsa tana dagowa daga duken da take, ji yayi kamar tace masa matso sai ganinsa tayi a kanta ya rungumeta gaba daya tare da daga ta sama ya nufi palo da ita yana cewa "Wanka yayi My love dole in baki tukwici.


*Dr A.S. Zaki*

EXQUISITE WRITERS FORUM 
*SAFIYYAH GALADANCHI*

_sadaukarwa ga yayata Billy galadanchi_

SHORT STORY 

SHAFI NA GOMA SHA UKU




Palo ya zauna kan kujera ya gyara mata zama a jikinshi, yana zama tana mikewa ya dawo da ita ya ce "in na sake taba ki kikayi kokarin gudu Allah ya na ganinki" yamutsa fuska tayi kamar zatayi kuka tace "to ai kace sai munje sokoto" share ta zancenta yayi yace "turarenki yamin dadi" ya fada yana saka kanshi side din wuyanta, ita dai ikon Allah ya mata yawa taga bilhakki har Allah ya isa akeso ai mata a Fakaice, acikin kunnenta ya fada mata yana jin yunwa, tayi kokarin tashi tsaye da Mataccen jikinta ta ce "shi nake kokarin daukowa daga kitchen" hijab dinta dake kan hannun kujera taja ta sanya ya kalleta yana murmushi wai jikin dayagama lugude ake boye masa, abincin ta kawo masa ita ta koma kitchen  dan lodin da tayi akwai kunya ya ganshi, yayi mamaki dayaga ta koma kitchen din har yagama cin abincin bata dawo ba, sai ya dauko kayan dayaci abincin dasu ya biyo bayanta, a zaune yaganta da plate kan cinyarta ta kusa cinyewa, ajiye plate din tayi katsa ta karbo kayan hannunsa ya kalleta tareda fadin "daga yau ki daina zuwa nan kina cin abinci idan ina nan ki zauna muci tare" ta gyada masa kai sannan ya karasa shiga ya wanke hannunsa yana kallon yadda suka kwaso kayan kitchen dinta kamar nan zata zauna zaman dindindin, yana kokarin fitowa aka dawo da wuta, yaji dadin hakan dan wayarshi ba chaji sosai, a tare suka shiga daki ta wuce kan gado ta kwanta saboda bacci take ji, Dr kuwa bai kwanta ba sai da yayi wanka, bai saka kayan baccin ba dan yau ji yake ba sani ba sabo balle dagin kafa.

Tana cikin bacci taji lamarinsa na neman zarmewa ta farka tareda cewa "sai fa a sokoto kayi alkawari" sai da yayi dariya kadan yace "na sauya alkawarin Nan sai yafi dadi" tayi shuru kusan minti goma ta bude baki da iya karfinta tace "Allahumma ajirniiiiii fimusibati, Na shiga ukku na shiga Hannu" ya kalleta acikin duhun ya ce "Karfa ki tara min mutane" ta rike hannunsa dake kusa da nata tace "ka manta tsoronka nake ji suma zanyi" ya shafa kanta "eh tsoron zan cire my love yana cin amanata wannan tsoron" kuka tasa masa irin na karya ta ce "Ba girmanka bane abinda kakeyi ba kyau, nifa yarinya ce wallahi kayimin girma" kyaleta yayi dan shi ya riga ya fara dialing jira kawai yake ayi picking ya fara making call din, lokacin da taji babu mafita ta shiga hnnun Dr ta fara lallashin kanta tana fadin "zan iya, Nabila zaki iya, kiyi hakuri, Allah ya baki hakuri haka kowace mace taji watarana sai labari daga yau zaki saba bazaki sake jin tsoro ko zafi ba, Allah na tuba Allah yasa bazanji zafi baaaaa" taja maganar tare da yin shuru shikenan kuma saida aka dauki lokacin ta bubbuga jikinshi "ko yanzu na daina tsoronka wallahi nagaji, bafa a dadewa irin haka, kai wai bakada tausayi ne" Dr kam abin nema ya samu yama mance da itace Nabila saida yaji ya tabbatar da ya fahimci bayanin da ake masa kan wayar sannan ya katse tareda sauke ajiyar zuciya.

Tsoro ma ta bashi jin yadda ta mike, take jiri ya kwasheta saida kanta ya bugi wardrobe yana matsowa kusa da ita yace "ke bakida hankali ne" ta hadiye yawu dakyar dan taji zafi akanta tace "Aure yafi karfina, na hakura yan kayana zan kulle azani ingudu wallahi in baka kaini gida sokoto ba gobe sena bar Nigeria" yana dariya ya daga ta ya ce "goben zan kaiki ba sai kin gudu ba, kefa naji kince haka kowace mace taji kema yanzu fa girma ya kama ki, hakuri akeyi dama kinji, sannu ina ne yake miki ciwo" jinsa kawai take amma gajiyar da takeji akanta kamar tayi dakon babbar mota akanta takeji, surutu ba kalar da batayi ba fitsarinta yafi biyar kafin safiya, dakyar yaga tayi wanka tayi salla har kansa ya soma ciwo har mamaki yake ashe tanada magana haka, saida yayi mata rantsuwa bazai sake yi mata komai ba sannan ta yadda ta sake kwantawa bayan tayi sallar, yana daga zaune yana huce gajiyar data dora masa, ya tashi ya koma kusa da ita, ya shafa kanta yana kallon fuskarta yace "Allah yayi miki albarka, Allah ya baki hakuri ya saka ki haifamin yara masu kama dake masu kyaun fuska da hali kamar ke, nagode sosai da kyautar da bazan iya biyanki ba, nagode sosai da samun natsuwa awurinki wadda na dade ina nema ban samu ba, nagode da aurena da kikayi koda bakya sona, Aisha Nabila zan soki inyita sonki" sake jan bargo yayi ya rufa musu tareda komawa bacci, sai karfe tara ya farka ya shirya ya fita, motsinsa ya tada ita amma ta kasa tashi saboda kunya tunowa take da irin surutun da tayita zubawa kamar radio mara saiti, shikam tunaninsa bacci take, tausayinta ya ringa ji da yabawa da kokarinta shiyasa bai tada ita ba ya fita dan ya nemo mata abinda zataci, yakai minti goma da fita sannan ta tashi bata nemi taimakon kowa ba ta shiga toilet tayi wanka, doguwar riga free ta saka sannan ta fita kitchen, saida ta fara dafa ruwan tea sannan ta shirya breakfast ta kai palo ta ajiye sannan tayi iya kokarinta wajen share gidan, wanda ta Debarwa su Mama ta saka hijab dinta ta kai mata amma bata zauna saboda ko tace tana jin dadin jikinta karya take, dawowa

Please Login or Register in order to submit comment