Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tayi ta zauna taci abincinta kan cikinta sannan ta hau kujera ta kwanta tareda daukar waya tayi kiran mama, tunda aka kawo ta sai yau zasuyi waya, gaida mama tayi ta amsa tana tambayarta ya mutanen gidan da mijinta ta amsa mata da duk suna lafiya sannan ta dora da cewa "Mama wane magani zan sha jikina ciwo yake min gaba daya" Mama ta danyi shuru ta ce "wane magani kuwa zakisha Nabila banda hakuri, kardai kisha wanda ya wuce pcm" ta girgiza kai ta ce "Mama pcm wallahi wani lokacin baya saurin aiki kidai turomin sunan wani" Mama ta ce "to shikenan zan turo miki Nabila amma bana son kisha wani magani yanzu dan bamu sani ba ko akwai ciki" kit ta kashe wayar a fili tace "ciki kuma mama, nikam ba yanzu ba" dariya mama tayi ganin ta kashe wayar ta fadawa Baba dake kusa da ita shima  dariyar yayi yace "yaran zamani kenan".

Dr sallama yayi ya shigo palon dauke da le

darshi, rufe idanta tayi kamar mai bacci. 




Kuyi hakuri yau yazo late, ba lallai kujini gobe ba har zuwa karshen wannan satin da zamu shiga inada hidima mai yawa.


*Dr A.S. Zaki*

EXQUISITE WRITERS FORUM 
*SAFIYYAH GALADANCHI*

_sadaukarwa ga yayata Billy galadanchi_

SHORT STORY 

SHAFI NA GOMA SHA HUDU

Kura mata ido yayi har ya iso kusa da ita ya zauna yana cewa "Washh Zuma dadiii Nabila" hararar kafafuwansa tayi dan ta kasa kallon fuskarshi, binta yayi ya kwanta gefenta ya matse ta da kujerar dan tayi musu kadan,ya dora hannunsa kugunta ya ce "inane yake miki ciwo"? Badan yana kusa da ita ba da bazaiji abinda take cewa ba, tashi yayi ya dauki ledar sannan ya dauketa ya ce "muje in shafa miki magani gashi na siyo" hannunta ta saka ta zagaye shi sannan tace "ga breakfast dinka can" ya sauketa gefen gadon yace "haba baby, ai ban isa jin yunwa ba yanzu, nakoshi da dadin da kika shayar dani jiya" juya masa baya tayi saboda kunyar maganar daya fada, Dr kuwa zip din rigarta ya zuge tareda sauketa kasa ta juyo tana kallonshi gabanta na faduwa, "karki damu honey magani kawai zan shafa miki in miki massaging jikinki" komawa tayi ta lafe tanajin yadda duk yabi jikinta da robe din batasan haka yake da zafi ba saida jikinta ya fara zafi ta rasa abinda yake mata dadi dakyar ta samu ya rage.

Ranar wuni sukayi a daki abinsu da rana ma batayi girki ba abincin daya fita ya samo suka ci, yaji dadi dan ta saki jiki dashi fiye da ko yaushe, Nabila kuwa a rnta cewa take tunda ankai final ai tsoro ya kare da fargaba, dama ita abu biyu yasa take tsoronshi, Na farko ganin malaminta ne kuma mutum mara daukar raini, abu kadan zai saka ka shiga matsala gashi a makaranta baisan abinda ake cewa murmushi ko dariya ba, Nabiyu ko girmansa take gani da tunanin yadda zasu kaya ranar daya nemi kusantarta to ashe abin ba haka yake ba in za a yarda ma kafin ta fara jin zafi duk abubuwan da yake mata dadi take ji har bisa harshenta.bayan la'asar tuwon semu tayi da miyar kubewa gaskiya dan ita tana girmama tuwo gashi ta kwana biyu bata ci ba dan haka yau ta shirya arangama dashi, Ashe Dr fitinanne ne bata tabbatar ba sai da dare duk jya kokarinta saida ta koka, shikenan kuma ya bude babin kwasar gara babu dagin kafa har suka cika kwana bakwai a tambuwal, dole kuma zai kara kwana biyu saboda ya kwana bangaren Nafisa kafin ya koma aiki, jarabawar da akayi duk bai samu yayi marking dinsu ba gashi tundaga aji daya har hudu yana dauka a semester din.

Daren ranar da zai koma dakin Nafisa sai dadi takeji da shirye-shiyen Tarbarshi bangaren Mama taje ta karbo mai tuwon da sukayi tazo ta share dakinta sama-sama tayi wanka ta daura zani da riga mara hannu, dakinsa ya shiga yayi wanka ya shirya tareda daukar wayarshi ya nufi dakinta, koda ya shiga tana tsaye tana taje gashinta dayake cunkushe, zama yayi gefen gadon yana cewa "gani nazo tunda ke baki je nema na ba" Murmushi yaga tayi masa ta ce "ai da nai niyyar inje in dauko ka daga dakin amaryar tunda ta hanani ganin ka yanzu" shuru yayi mata dan bayason yana sako maganar Nabila da ita yasanta sarai yar rainin wayo ce, kallon zanin gadon yayi yaga duk digon manja ne da alama akai take cin abinci, hakanan dole ya kwanta tunda waccen bata biyo shi ba wannan ma bazai ce ta bishi dakinshi ba yanzu, ta kashe wuta ta hawo gadon ta kwanta tareda shiga jikinshi, dan dauke kansa yayi daga kusa da nata bayan ya dora hannunsa bisa jikinta baya son warin man data shafawa gashinta.

A cikin bacci yajiyo sheshekar kukanta ya bude idonsa tareda kiran sunanta, bata amsa ba saima kara kukan da tayi, ya dago daga kwancen da take ya jata kusa dashi ya ce "haba Nafisa, kuka sai kace wata jaririya me akai miki"? "Kyankamina kakeyi? Bayan fiye da wata daya baka nemeni ba, kayimin kishiya sati daya kana dakinta duk dare ku hanamu bacci da surutunku amma yanzu kazo min nan ka kwanta kayi bacci kuma ko abinci baka tambaya ba, maganar daka fada kenan ta tabbata, tunda zakayi aure ka canza idan baka sona ka sakeni in koma gidanmu" cije lip dinsa na kasa yayi yana murmushi "shikenan zo ki gani, yau sai kin raina kanki" ya fada yana lalabar inda ta daure zanin jikinta.

Bangaren Nabila ko wani free take jin kanta a daren, gadon saida ta raba shi biyu tayi wata irin kwanciya sai bacci ko tunanin wani abu batayi ba wai shi kishi ita dai yau bata samu zatayi bacci ba.

Dakyar nafisa tayi sallar asuba saboda jigata har ya nufi toilet dinta da niyyar yin wanka ya fasa saboda har wani zarni yake yi, dakinsa kuwa kusan sati bai shiga ba yasan yayi dauda dan haka ya nufi Dakin Nabila ya samu tana bacci sharkaf da sanda ya shiga toilet din yayi wanka da alwala, ya turo kofar ya fito yana kawowa tsakiyar dakin daude da towel suka hana ido kurawa juna ido sukayi, shi yaji kunyar ganinsa da tayi yayo wankan tsarki, itako ta kura masa ido tana mamakin meya kawo shi wanka a dakinta, basarwa yayi ya nufi gaban madubi, itama ta dauke kanta tareda janyo hijab dinta dake gefe ta saka ta shiga toilet, alwala tayi ta fito har lokacin yana nan salla yake yi, bayanshi ta tsaya tayi tata sallar bayan ta idar ta gaidashi ya amsa yana cewa "ya kewata sweety"? Dauke kanta tayi daga kallonshi tana murmushi "gaskiya nayi matukar kewarki jiya, mafarkinki ne yajamini wanka yanzu, don Allah inzo zan samu wani abu" tashi tsaye tayi ta koma kan gado tareda jan bargo ta rufe har kanta, mikewa yayi ya fita daga dakin yana dariya, sai da gari yayi haske sannan ya dawo ya zauna kusa da ita, sunkuyawa yayi daidai bakinta yayi kissing dinta ta bude idonta tana kallonshi ya ce "tashi in saka ki aiki jaruma ta" duk da taji haushin tashinta da yayi amma bata nuna masa ba ta mike zaune, ya ce "dakina zaki gyaramin da toilet" sauka tayi daga kan gadon ta amsa masa da to, toilet ta shiga da sauri ta wanke bakinta sai gata ta fito dauke da kayan wanke toilet ta tambaye shi ko dakin a bude yake, ya amsa mata da eh, ta fita daga part dinta ta wuce nashi dakin ta fara shareware ta goge farin Mable dinda ke shimfide a kasan dakin, ta kwashe bedsheet din dan yayi dauda ta saka cikin laundry basket, toilet din ma ta wanke shi fes sannan ta dawo dakinta har lokacin yana kwance gefen gadon bayan yaje sun kwashi yan kallo da Nafisa, sabon zanin gadonta ta dauka ta shimfida masa, tana ajiye pillow sai gashi ya shigo, hijabinta take nema ta rufe jikinta dan yana can jikin kofar toilet din, dauke kansa yayi daga kallonta dan baya son ta saka hijab din ya ce "wai! Tsafta dadi" cike da rashin sakin jiki ta karasa jikin kofar ta janyo hijab dinta tareda fita daga dakin, shikenan bata sake ganinshi ba sai dare acikin bacci ma sukayi sallama dn babu wuta wayarta ma ta mutu dan ita ta wuni tana dannawa.

Da safe ya shigo ya fada mata ta shirya zasu koma sokoto, dan haka ta shiga wanka dama ta gajj da zaman kadaicin nan, tana cikin matan nan da basa ciwon mara sai dai ciwon kai ko kafafafu, tasan dai jiya da dare taji kanta yana dan ciwo ashe period dinta ne yazo, tayi wanka ta fito amma ta manta bata dauko pad ba gashi tana rushing sosai, tana tsaye ya dawo dakin tana jin motsinsa tayi tsaki tareda fadin "mutum sai shegen yawo" "kin shirya"? Ta girgiza masa kai tana matse kafafuwanta ya kalleta yana mamaki "sweetheart lafiya"? Ta dan yamutsa fuska ta ce "jini ke zuba babu..." kafin ta karasa ya hango shi yana bin kafarta cikeda tashin hankali ya furta innalillahi wa'inna'ilaihiraji'un tareda fita daga dakin, shi duk a zatonsa cikine zai zuba kamar yadda Nafisa tayi shiyasa ya tafi ya kirawo mama yabar Nabila a tsaye cike da mamakin tsoron data gani a idonsa.



*Dr A.S. Zaki*

EXQUISITE WRITERS FORUM 
*SAFIYYAH GALADANCHI*

_sadaukarwa ga yayata Billy galadanchi_

SHORT STORY 

SHAFI NA GOMA SHA BIYAR

*Salamualaikum fans don Allah kuyi hakuri na dauki hoto sai wani sati saboda hidima tayimin yawa yanzu bana samun lokacin typing*




"Bana son hauka kai, wane irin cikine daga zuwan yarinya kwana takwas yau" hannunta ya janyo "muje ki ganewa idonki wallahi jini ke mata zuba" wuce shi tayi duk da bata yadda ciki bane indai ba zuwa yayi yasaka yarinyar mutane ta samu matsala ba, side dinda babu carpet taje ta dan tsuguna a haka Mama ta sameta ta ganta kalau amma ga digon jini a kasa kusa da ita ta matsa tare da fadin "tashi ki saka pad ku wuce asibiti" wata kalar kunya taji sauke kanta kasa tayi ta ce "Mama haka nakeyi fa idan zanyi Al'adata ba wata matsala bace" bata yadda ba ta matsa kusa da ita tace "jini har haka Nabila? Tashi to kiyi wanka" mikewa tayi tana cewa "pad ne banida ai mama yanzu na fito daga wankan" "bari a aika a siyo miki" mama tace bayan ta fito daga dakin ta kalli Dr yana zaune kan kujera hankali duk a tashe "ka ringa kwantar da hankalinka in zakayi abu wallahi harkasa kaina ya fara ciwo, jinin alada ne fa yake mata zuba haka kuma bama sosai bane yana kwana biyu zai rage" ajiyar zuciya ya sauke ya ce "to ai mama ni bantaba ganin jinin alada haka ba kuma kinsan Nafisa daga tunanin period ne aka rasa cikin jikinta shiyasa akace tsaro da kaya yafi ban cigiya" Mama ta amsa da "lallai kam kanada abin mamaki abubakar yaushe ma akayi daren da har gari zai waye, bari inbayar asiyo mata pad" yana tsaye har ta fita sannan ya koma dakin direct toilet ya wuce, ta zabura daga zaunen da take kan toilet sit dan tunda suke bai taba samunta a toilet ba sai yau, sauke towel din tayi ta rufe jikinta tana kallonshi, bai damu da ganin ta firgita ba ya matsa kusa da ita "ya rage zuba? Amma kin tabbatar hakan ba matsala bane"? Ta gyada masa kai tana cewa "ka fita wanka zanyi, ba matsala kawai ma dan bansan zaizo yau bane da bazaka gane inayi ba" bucket ya matsa kusa da famfo ya tara ruwa "ai gaskiya bakida lafiya ki bari inmiki wankan" saurin kashe ruwan tayi "ba wanka nakeson cewa ba tsarki kawai zanyi yanzu nayi wanka" ya sake kunnawa ya ce "Nima tsarkin zan miki ba wanka nake son cewa ba" sake kashewa tayi ta raba gefenshi zata wuce "na gama tsarkin pant zan dauko" dawo da ita yayi gabanshi "dawo bari na dauko miki" da gudu ta nufi kofa tace "muryar mama nakeji a waje kamar" ya rike hannunta ya langabar dakai gefe kamar yaro "bari na karbo miki, har yanzu yana zuba" tsayawa tayi tana kallonshi har ya fita babu dadewa sai gashi ya dawo harda pant din rike a hannunsa, saboda jaraba nacewa yayi saida ya tsaya har ta saka suka dawo dakin tare, yana dakin har ta gama shiri sannan ya daukar mata dan karamin akwatin data hada kayanta ciki suka fito.

Sallama suka yiwa mama har zasu fita ta mikawa mama key tace "gashi mama ko zaki nemi wani abu aciki idan ma babu ki ajiyemin a wurinki" dadi mama taji ta karba "ba abinda zan nema sai dai in ajiye miki, kuyi ta hakuri Allah yayi muku albarka don Allah ina gaida hajiya da Alhaji saina samu lokaci zamu shigo" ta amsa da zasu ji, har sun nufi babban gate saita juyo ta shiga part din nafisa tayi mata sallama amma a dakile ta amsa mata da Allah ya tsare, bata damu ba ta fito suka wuce dama ita dadi takeji zata koma gida.

A tunaninta gidansu zai kaita se taga sun wuce gidansa, tana so tayi magana amma taga ya daure fuska kamar bashi ba, maida kallonta tayi gefe ta buga tagumi tana tunanin gida.

Yana sane yayi mata haka dan shikam bazai kaita gida a haka ba, "ko in kaiki kiga mama"? Ya tsokaneta, ta juyo ta da sauri tace "eh ingaidasu ba" dariya yayi mai dan sauti "bazan maidake yadda suka bani ke ba, karewarta ma jini na miki zuba, ki bari sai kinyi ciki yauwa nan kam nasan sungane ba wasa muka sa nida ke ba" maganarshi ta saka taji kunya bata kula shi ba tayi masa shuru.

Daren ranar ta fahimci abinda ake cewa jaraba, tunda take jin labarin aure bata taba zaton yakai haka ba, bacci rabi da rabi haka tayishi dakyar taga wayewar gari, namiji da shegen son jiki kamar yaro na goye.

yan islamiyar su ta unguwa kamar jira suke ta dawo suka aiko mata massage zasu zo, snacks kawai tasa aka yi mata dama akwai drinks a gidan, bai fita ba ya tsaya marking jarabawa anan gida, sai wani dadi yakeji yau shine a gida da matarshi yayi wanka yana hutawa a dakinshi akan sabon gado da haske ko ina jikinsa da dakinsa sai wani sabon kamshi mai kamada juna yake yi toilet dinsa kamar ya kwanta ya kwana aciki, matarshi fes ta saka doguwar riga tana gift awa yana kallonta kamar wata tauraruwa, idan ya tuna haka sai ya sake wata fankama a fili ya furta "wani abinma sai jibi idan ankoma makaranta in sauke daure fuska ina hura hanci na sakota a gaban mota ina bata umurni tana gama lecture ta same ni office dina" murmushi ya sake yi tunowa da yanada damar latseta a office din.

Har rana yana gidan, lokacin bakinta sun cika gida sau surutu ke tashi, bayan ta ajiye musu kayan data sa akayi dan su ta debar masa nasa ta kai mai daki, tace bazatayi girki ba, kallo yake a jikin system dinsa ya dago yana kallonta ta ajiye masa kan bed side tace "sai dai abincin dare kaci wannan bazan iya wani girki ba yanzu rana tayi" tashi zaune yayi ya dauki meatpie ya ce "to yana iya ai ba yadda zanyi tunda kece mai gidan sai yadda kikayi dani" murmushi kawai tayi ya sake cewa "kin iya wannan"? Ta girgiza kai tace "a kayan fukawa bayan wainar fulawa da dan wake da fanke ba abinda na iya" Maltina yadan kurba ya ce "don Allah ki koya ina so" ta amsa da "insha Allahu bari na koma wajensu" fitowa tayi lokacin har sun cinye wasu sun dauka zasu tafi dashi, raka su tayi har gate suka fita suna mata mitar ta musu rowar ango bayan yana gidan.

Yau dai sai shiri take tun safe yace zai kaita gida saidai abinda bata sani ba yana nufin ta gaidasu su dawo amma zai biya da ita barkar matar wani abokinsa data haihu.


*Dr A.S. Zaki*

EXQUISITE WRITERS FORUM 
*SAFIYYAH GALADANCHI*

_sadaukarwa ga yayata Billy galadanchi_

SHORT STORY 

SHAFI NA GOMA SHA SHIDA




Kallonta yake tundaga sama har kasa bayan ta gama shiri, yau dinma doguwar riga ce a jikinta A line babu ta inda ta kamata sai kyalli take saboda adon stones data sha "wai nikam ba a canza wannan doguwar rigar ne kisa wani abu wanda ba ita ba mana kullum cikin abu daya" kallon rigar tayi sannan ta amsa mishi "ni bana saka wani abu idan ba doguwar riga ba gaba daya kayana doguwar riga ce" ya jinjina kai ya ce "jeki sa riga da zani aina ganki da su ko" zama tayi kan kujera ta ce "nikam suna tambuwal acan ba baro su dama guda biyu ne anty Maryam tasa aka dinka min" tashi tsaye yayi ya dauki makullin motar shi ya ce "tashi mu tafi" mikewa tayi tabi bayanshi ta rufe gidan sannan ta  fita wajen gate saida ya fito da mota suka rufe gate din a tare.

Lokacin da suka isa gidan duk yadda take jin dadi da murna kasa nunawa tayi ta jera dashi dole suka shiga gidan a tare, Mama da Baffa da Baba duk suna gidan sai yarinyar Anty Nusaiba ta biyu da tazo kwana biyu zara, a palon suka zauna tana tayi kasa dakai kamar wata bakuwa, mama kuwa ba karamin farinciki tayi ba ganin yadda yarinyar ta ta koma, ta kara nutsuwa kuma ta danyi kiba anan palo ta barshi da Baba suka wuce Daki ita da mama, wasu abubuwa da duk bata samu ta bata ba lolacin hidimar ta harhada mata harda wasu kayan sawa da abubuwan ci dan tasan halin Nabila da kwalama, acikin kwali ta jera mata su ta rufe sannan ta samu jaka tasaka mata kayan "idan Ibrahim ya shigo yau ko gobe sai ya kai miki makullin motarki, Baban ki yaso a canza miki wata kamar yadda akayiwa sauran yan uwanki, to abubuwa sun musu yawa dan kinsan goggonki jikinta ya tashi suna Abuja ma dawainiyar duk tana kansu, idan hankali ya kwanta sai a karbi wannan a canzo miki" ta amsa da to tana cewa "babu komai mama ai na kira Anty hajara ance tare sukaje tace jikin da sauki dai za'a ce wannan dinma ba matsala tunda batafi shekara  biyu ba kuma ba taba gyaranta ba" mama taji dadin maganarta ta ce "to Allah yayi albarka, ayita hakuri naji yace zakuje wurin barka da akwai abinda zaki kai ko" ta gyada kai "eh matsalar dai bansan me aka samu ba ko macece ko namiji inaga kuma duk kayan da suka rage na mace ne" mama ta ce "to jeki ki tambayo shi bari in duba inga ko akwai wanda na siya kwanaki wajen barka Maryam tace sunyi yawa na rage" fita tayi daga dakin ta sameshi da cup a hannunshi yana shan fura ta dan durkusa gabanshi tace "dama ina so ne inji mace ko namiji aka haifa" ya kalleta tareda cewa "karfa ki karbarwa mama kaya zamu tsaya mu siya yanzu kafin muje" tsugunawa tayi ta dafa carpet din tsakiyar palon da hannunta ta ce "No ba abinta zan karba ba, dama ina ajiye kayan babies incase koda wata ta haihu to nasan kafin nabar gida inada na mace shine nakeso inji idan mace aka haifa sai in dauko kayan" ya jinjina kai ya ce "mace ce harya sa mata suna ma" mikewa tsaye tayi  tace "bari in dauko to" cup din hannunsa ya ajiye saboda baba daya shigo, kamar karta tafi haka taji Mama ta kalleta yadda fuskarta tayi wani iri Mama ta riko hannunta suka dan matsa ta ce "Nana kinada matsala ne" ta girgiza kai amma idonta sun cika da hawaye "kowa haka yake hakuri zaki saba, ince dai ba haka kike nunawa mijinki haka"?ta sake girgiza kai ta ce "Mama ban saba dashi ba" murmushi Mama tayi ta ce "banson iya shege, zaki saba dashi ki saki jikinki kibar tsoronshi idan akwai abinda yake damunki ki kirani ki sanar dani kinji, wuce ku tafi kinga shi har ya fita" godiya tayiwa mama ta dauki kayanta ta wuce, Baba har takai kofa ya mika mata envelope karba tai tana godiya yace mata zai kirata, kayan Dr ya kama mata ta saka booth suka wuce suna tafe bisa hanya wayarta tayi ringing ganin Nana sule ce yasa tayi saurin dauka dan azatonta ko ta haihu ne "Amarya ga dinkin ki Ubale ya kawomin dazu" a hankali tace "to wa zaki bawa ya kawo min nasan ke ba fita zaki iyayi ba yanzu" Nana sule ta ce "to gaskiya dai yanzu kam banda shi ke bazaki zo ki karba ba" ta danyi murmushi tana satar kallonshi tace "to ki ajiye idan mun koma makaranta saiki fito min dasu idan kuma kin haihu nazo sai na karba" karbar wayar yayi ya dora kunnensa tareda yin sallama ya ce "yimin kwatancen gidanki sai muzo mu karba yanzu" cike da kunya tayi masa kwatancen gidan sannan tayi masa sallama ya juyo yana kallon ta ya ce "Baby meyasa zaki ringa yimin haka? Idan bakice inkaiki wuri ki karbo sako ba wa zai kaiki"? Shuru tayi masa tana wasa da yatsunta, juyawa yayi ya koma inda suka fito babu dadewa suka isa ya ce "to kiyi sauri" fita tayi daga motar ta shiga gidan suka rungume juna ita da Nana ta kalleta daga sama har kasa ta ce "kambuuuu...kiba kika soma yi shegiya? Ahh yarinya taji dadin dakin miji" tsaki tayi ta ce "mika mini kayana na wuce na baroshi a waje" dauko mata kayan tayi tana mata tsiya tace "akwai wani sako aciki in kin bude muyi magana a waya" sallama tayi mata ta fito suka wuce ya kalli ledar yana cewa "menene a ciki" ta ce "dinkine telanta yamin" ya jinjina kai yana cewa "to idan munje gida zan gani idan yayi kyau sena biya, murmushi kawai tayi masa.

Koda sukaje barka anan ya barta sai bayan la'asar, abokin nashi ya jashi sukaje siyan dabbobin da za'a yanka na suna koda ya dawo ta galabaita da yunwa dan an kawo mata abinci kadan a plate kamar ta roka basusan ita baifi Loma takwas zatayi dashi ya kare ba, sallama tayiwa matar mai suna Fatima suka wuce.

Jira kawai yake su isa gidan ya baje a palo ya bude kayan dinkin anan yaga wata leda saida ya bude ya karanta sunan abubuwan yayi murmushi a ranshi yace duk yanzu zata shasu kafin dare, ya bude dinkin yaji dadi sosai ganin harda fitted gown da straight gown da skirt sunyi masa kyau sosai ya ninke su ya ajiye itako tana kitchen saida ta rage yunwa da bread da tea sannan ta dora abincin dare.

Bayan wani dan lokaci kadan aka koma makaranta ita saida ta kara sati daya ta koma dan saida ta jira Nana ta dawo daga kebbi dan ta haihu, ranar da zata koma ranar bai bari tayi baccin kirki ba shiyasa ta makara tashi, har yayi wanka yazo yana tashinta amma ta kasa mikewa ya ce "kinsan Allah idan na riga ki shiga aji bazaki shiga ba ki tashi ko nai tafiyata" dakyar ta mike ta shiga toilet tayi wanka koda ta fito baya nan, da sauri ta shirya ta dauki key din motar ta tabi bayanshi, gudu take ta tsalawa ko karyawa batayi ba amma kash koda ta isa yana kusa da hall din, parking tayi da sauri ta fito har saida ta manta da key din motar ajikin kofa ta nufi hall  din, kafin ta shiga hall din yayi shuru saboda yadda ya daure fuska yana kallonsu, cike da natsuwa ta taka kafarta ta shiga maganar da yayi ta katse mata tafiya cike da mamaki ta juya tana kallonshi har saida ya sake maimaitawa...



*Dr A.S. Zaki*

EXQUISITE WRITERS FORUM 
*SAFIYYAH GALADANCHI*

_sadaukarwa ga yayata Billy galadanchi_

SHORT STORY 

SHAFI NA GOMA SHA BAKWAI 




Kallonsa ta sake yi tana jin yadda duk idanu suka dawo kanta, ta cije lip dinta na kasa sannan ta nufi kofar ta fita, jiki a mace ta shiga mota tana jin yadda ko ina na jikinta ke ciwo har can inda ba a fada ta tabbata jiya da dare wani abu yaje yasha dan ta dandani kudar

Please Login or Register in order to submit comment