Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aure ta kwanta da irinsa" ta nufi madubi tana cire ribbon din kanta ta ajiye tace "Rawahu Dr A.S Zaki ko"? Yayi dariya sosai harda rike ciki sannan ya dago yana cewa "ya miki kyau, wai meyasa bakida kunya wannan rigar da kin sani ma baki saka ba" ta kalli jikinta tace "Kunyar Mara kunya asara" kusa da ita ya tsaya yace "bari ingani to ko sauyamin ke akayi yau".

Marukan da Nafisa tasha a daren sunkai biyar musamman wajen uwarta tace "kin kunyata mu yar iskar yarinya, ke dan bakida hankali ayo miki kishiya wannan yar duniya bazaki kama kanki ba, gata da fara'a da son mutane ga jiki mai kyau kullum kayanta kamar an dinka su bisa jikinta, diyanta kamar diyan turawa ke Kin zauna kamar jaka cikin gida, ba wanka ba wanki ba shara balle shi turare kila baki ko da shi, kwanaki gidan dan sarki ji nayi ana gardama anji kamshin turaren wuta aka ce daga gidanku ne nan take Inna kande tace amaryar Abubakar ce, har ansan kamshin turaren gidanta cikin unguwa keko gakinan kullum jiya Iyau in anga kinyi wanka sai salla ko biki, wallahi keji kunya kuma indai ba son kikai ya sakoki ba to ki gyara dan koni Nabila na burgeni balle shi miji, Allah kadai yasan gatan da yake sha in sun sauke labule" Nafisa dai babu baki sai hawaye harda kannenta suka sa baki dayar tace "kuma wallahi mama gashi da kokarin siya mata kayan kwarai, manyan lesuka da tamfofi amma bata sawa ko atamfar roba baki ganin ya kawo mata sai dai in anko ce" Nafisa ta dauki takalmi ta jefa mata tareda fadin "sena ci ubanki in kina samin baki cikin magana" Mama tace "kar insake ganin kin jefeta wallahi bayan salla zan wanketa inkai dakin miji" tashi kawai tayi ta shige daki tana goge hawaye, komai ya gama lalace mata.

Mama tabi bayanta da kallo tana cewa "ga mace har mace amma ba gyara, wannan kishiya taki in baki tashi tsaye ba mamaki kike shirin sha ballagazar banza".




*Dr A.S. Zaki*

EXQUISITE WRITERS FORUM 
*SAFIYYAH GALADANCHI*

_sadaukarwa ga yayata Billy galadanchi_

SHAFI NA ARBA'IN 

LAST PAGE

Abinda bai taba yi ba yayi sati uku ta dauka har yana neman zarcewa a na hudu a sokoto ba tareda yaje tambuwal ba, satin daya wuce da wannan da aka shiga Nabila tana lura da yawan sakonnin ban hakuri da Nafisa ke tura masa, sau daya tagani yana wajen wanka duk da bata yi masa bincike a waya amma sai kawai zuciyarta ta bata ta duba message din budewa tayi ta karanta tagansu sunkai guda biyar, sai ta ajiye wayar ta zauna zaman jiransa har ya fito ta mika masa wayar tare da Fadin "kayi hakuri wayarka na hannuna sako ya shigo na shiga by mistake" yana goge jikinsa ya karbi wayar ya duba kafeta yayi da ido yana daure fuska yace "bincike kike yimin? Yaushe muka fara haka" ta dan zaro ido gabanta yana faduwa tace "muntaba yin haka ne? Don Allah kayi hakuri ba bincike nake yi ba" karamin tsaki yayi yana cewa "kedai kika sani" tabi bayansa da kallo cike da rashin jin dadi, bude kofar dakin tayi ta fita, shima kallonta yayi yana hango irin kibar da tayi yasan bata taba daukar masa waya tayi bincike ba ko yanzu taka mata birki yake kar wata rana shaidan ya ingizata duk da babu wani abu da yake boye mata amma dole yanada sirri tsakaninsa da iyalinsa, duba da irin massage dinda Nafisa take turowa tana shaida masa kalar missing dinsa da tayi da kuma yadda zata tarairayeshi idan ya dawo, murmushi yayi tunowa da lallaifa wani tabawa ya rubuta massage din dama kuma yau yake shirin zuwa Tambuwal din dan Baba ya kirashi ya kuma fada masa abinda yayi bai kyauta ba.

Fitowa yayi da shirinsa yaga yaran su kadai a palo Ramla tana wasa Muhammad yana bacci kan kujera, daukarsa yayi yashiga dakinta tana zaune tayi shuru ta daga ido ta kalleshi ya shimfide Muhammad gefenta yana cewa "ya fara juyi ki daina ajiye shi kam kujera yana bacci kar ya fado" ta gyada kai tana sake jan shi tsakiyar gadon, "Ni zan wuce tambuwal idan babu damuwa zaki iya zuwa gida ki kwana inkina so, bansan yaushe zan dawo ba kuma" A hankali tace "to Allah ya tsare ina gaida su Mama" ya amsa tareda juyawa ya fita, shareware tayi da zancen shi dan tana ganin kawai shedan ne yake son kawo musu matsala.

Bayan ya isa bai shiga gidan ba sai da ya kirata a waya ta daga tana yi masa ya hanya yace "na sauka lafiya yanzu, meyasa da zan taho naga kinyi wani iri dake ba kamar yadda muka saba ba"? Ta kakaro murmushi tace "Anya idonka ya ganni da kyau kuwa" kissing dinta yayi ta wayar tareda fadin "bakomai dama kiranki nayi in fada miki nayi missing dinki kuma ina sonki" dadi taji har cikin ranta a hankali tace "i miss you more and I love you more" dafe kirjinsa yayi yace "la'ilaha illallahu nayi bakin ciki da bana kusa kika fadi kalmar nan da nake ta jiran ki fada amma kinsan me? Jibi zan dawo" dariya tayi a fili tace "to Allah ya kaimu, anjima zamuyi magana yanzu Muhammad ya tashi zanji dashi" sallama ya mata yana jin kamar ya koma skt, fitowa yayi daga motar bayan ya dauko tsarabar daya zo da ita ya shiga gidan, ko ina shuru kamar ba kowa a gidan yayi sallama, Nafisa tana zaune kan kujera a palonta ta jiyo sallamar shi mikewa tayi ta amsa tana fitowa ya dan zuba mata ido tana sanye da leshi pink riga da zani hardasu Jan baki murmushi yayi duk da yaji nauyin ganinta amma sai ya fuske ya mika mata ledar yana karewa tsakar gidan kallo ko ina fess binta yayi cikin palon yana cewa "Mun same ku lafiya"? Ta zauna tana cewa "Lafiya lau ya ka baro su Ramla" yayi murmushin jin dadi yace "tana skt lafiya lau ai da nasan zaki tambayeta dana zo miki da ita" mikewa tayi tana cewa "baka kira zaka zo ba gashi abincin da mukayi da rana shi zamuci har dare" "ki bani ruwa kawai kuma ba sai anyi girkin dare ba, ina Nana"? Ta nuna daki tana cewa "bacci take yi" ya gyada kai kawai yana kwantar da kansa jikin kujerar sai lokacin ya lura da gyaran datayi ta canja kujeru, mikewa yayi ya shiga daki yaga sabon gado mai kyau kalar milk da brown ba laifi dakin yana kamshi sai dai bai kai na Nabila ba dan ita kam tundaga gate yaje shakar kamshin gidanta, rage kayan jikinshi yayi ya kwanta kusa da Nana yana dan kada kafarshi, har dakin ta biyo shi da ruwan yana sha yana kallonta da alama yanzu tana wanka danyaga tayi haske farar fatarta ta sake fitowa tas, yana lura da yadda ta kasa sakewa dashi sai ya tambayeta ina mama "sun tafi sokoto wajen gaisuwa" ya gyada kai dan bai san waya rasu ba sai yace "tun yaushe Nana take bacci" tace "bata dade da yin baccin ba ka shigo" ya mike tsaye yana cewa "ok muje dakina kiji" binshi tayi baya, nidai ban bisu ba iya nan palon na tsaya.




A haka rayuwarsu ta ci gaba da tafiya duk da Nafisa ta sauya amma saboda halinta ne wani lokacin sai ta bada kanta, shekara biyar Kenan yanzu tunda tayi haihuwa daya bata sake yi ba Nabila ko bayan Muhammad ta haifi Aliyu yanzu ga wani cikin na hudu data kwallafawa rai da son haihuwar mace, Tambuwal suka zo suna Farida ta haihu Tana kokarin shiga dakin Nafisa ta kai mata abincin data dafa ita da mutanenta tayi sallama basu ji ba sunyi nisa wajen tsegumi ana cewa wai kodai Nabila ta jefe ta shiyasa har yanzu bata sake haihuwa ba ita kuwa ta dage da neman cika gida da yara, har ta juya dan zancen ba dadin sauraro gareshi ba amma wannan cikin ya sakata saurin hasala da kasa controlling temper dinta komawa tayi dakin batareda tayi sallama ba ta ajiye kular abincin sanann ta dago ta kalli Nafisa tace "Nabarku da Allah, Nafisa banta mummunan zato akanki ba babu abinda kika tare min amma ni koda yaushe baki taba fadar alkhairi akaina, tunda uwata ta haifeni bantaba koda ganin boka a hanya balle naje wajen shi saboda in cutar da wani ba, babu mutumin dayayi matsayin insiyar da lahirata akanshi haka kawai saboda ni inji dadin duniya, kuna cewa na cika gida da yaya nasan saboda gado ne ko, to me mijin naki ya ajiye da zan tara yaya saboda su gada? Ku kuke wannan tunanin kuda kuka girma cikin babu da talauci ni tunda na taso alhamdulillahi abin duniya baya dada ni da kasa kuma nasan na Gina kaina zan kuma ci gaba insha Allahu bada abin uba kadai zasuyi gadara ba" Dr daya shigo dakin duk bata sani ba ya kalleta yaga yadda ta hakikance su kuma yan gulmar duk sun yi shuru kamar ruwa ya cisu, kallon Nafisa yayi yace "nidai karki illatamin mata don Allah" yaja hannun Nabila yana cewa "Zo muje kisha ruwan sanyi kyalesu banson kina hasala irin haka" duk suka bisu da kallo jiki a sanyaye, suna isa dakinta ta samu wuri kan kujera ta zauna tana cewa "halayen matarka zasu saka in tsaneta a rayuwata wani lokacin inaji kamar ace kanwatace insameta inyi mata duka" zama yayi kusa da ita yakira sunanta "Nana Aisha Nabila" ta dade bata ji sunan daga bakinshi ba ta dago ta kalle shi yace "akwai abubuwan da basai na fito fili na fada miki ba wanda suke bambanta ki da Nafisa, ya kamata ki gane da kanki abubuwan ta su daina damunki ji yadda kike gumi akan ta don Allah" hannunta ta dora kan nashi dayake goge mata zufan dashi sannan ta dan karkatar da kanta gefe ta murmushi yace "yauwa ko ke fa, ga Ramlar kinta zama budurwa harfa ta shiga primary 1 Muhammad yana nursery 3 hydar kuma kinga yanzu zai shiga makaranta wannan kadai zaisa ki daina damuwa da wata can" ta dora hannunta kan cikinta tana cewa "wata Nana Aisha Nabila itama nanda shekara uku tana nursery 1 din" ya dungure mata kai yana cewa "kodai Wani Abubakar Sadeeq ba" ta matse masa baki tana tana cewa "inga yawun nan naka marasa kyau zubo da su karka hadiye" cire hannun yayi yana dariya ya tashi tsaye yace "zanje indawo ki shirya karfe shida zamu juya gobe Monday ina fita aiki tunda ke kin fara hutu" Allah ya tsare tayi masa, wuri ta samu ta zauna tana danna wayarta da anty Maryam ke mata magana akan cewa ya kamata ta zauna wuri daya tunda ta shiga watan haihuwarta.

Sallama akayi daga waje ta amsa tana gyara zamanta, Nafisa ce ta shigo fuskarta cike da damuwa ta kasa samun sukuni tunda Nabila tace ta barta da Allah ta samu wuri ta zauna tana jin yadda  Nabila ta kureta da ido a hankali tace "Don Allah Nabila kiyi hakuri, Nagane kuskurena insha Allah bazan sake kwatanta hakan a gareki ba" Nabila ta danyi shuru tanajin kamar ba komai a ranta sannan tace "Nafisa nidai ina baki shawara in zaki zauna da mutum ki zauna dashi tsakani da Allah ki yarda babu abinda zai iya yi miki sai da yardar Allah, daga karshe kuma ba komai ya riga ya wuce Allah ya yafe mana" Nafisa ta sauke ajiyar zuciya tareda cewa "Nagode Nabila, Nana tace min Babansu yace yau zaku wuce gashi ban gama hada kayanta ba" Nafisa ta danyi murmushi tace "ki bada wanda yake kusa kawai kayanta acan ai basuda adadi" sallama tayi mata ta fita tanajin kamar ta sauke wasu kaya masu nauyi.

Saida Ramla ta shiga Jss1 sannan Nafisa ta samu ciki ta Haifi Namiji a lokacin yaran Nabila shida hudu maza biyu mata sai a ta shidan ta samu mace daganan tace to ita ta daina Haihuwa, aikinta take zuwa sannan kuma ta koma masters, Dr ko ya kara zama wani babban mutum har office dinsu Nabila ansan Dr sau dayawa take complain ya daina makale mata amma ko wani gari tafiya ta kamasu daga office sai ya bita Nana da Ramla suna Abuja yanzu ma Muhammad ya tada kayar baya sai ya koma can ita ba ruwanta indai autarta na kusa da ita, Dr ya kara samun dama ba yara gidan sosai Duk inda Nabila tasa kafa yana biye da ita cikin gidan ta juyo tana kallonshi dan aiki take a kitchen ya kawo nama da dare kuma ya hanata dafawa sai binta yake yana lalaba ta juyo tana cewa "don girman Allah ka fita haba dakai zanji koda auta" daure fuska yayi sosai saita ganshi kamar lokacin dayake lecturer din su yayi magana cikin tsawa yace "yimin shuru" ganin yadda ta zaro ido tareda dauke numfashinta ya masifar bashi dariya har ya kasa rikewa ya durkusa a wurin da sauri ta fita yana kiranta taki tsaywa saida ta isa toilet kafin ta cire pant sai ga fitsari na zuba ya bata tsoro sosai, turo kafar yayi yana ci gaba da dariya yana nunata haushinsa yasa tayi kansa ya dauketa yana cewa "laah na manta kinyi fitsari a wando" ta rike masa wuya itama batasan lokacin da dariyar ta kwace mata ba.







ALHAMDULILLAHI.

Anan na kawo karshen wannan littafin sai mun hadu a labari na nagaba.





An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment