Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yaga bata wurin da alama ta shiga gida, shigewa motar yayi ya tafi bayan baba ma ya wuce.




A lokacin data shiga gida fridge ta bude ta saka kayan data shigo dasu sannan ta nemi wuri ta kwanta a palo, Mama bata nan a lokacin tana wurin aiki, baffa yana makaranta sai ya kasance babu kowa a gidan sai ita kadai.




Yana driving yana nazarin abinda zuciyarshi take ganin ya dace wanda zuciyarshi take kulla mishi, tabbas hakan shine kadai sauki a gareshi indai zai samu abinda yake hasashe to kaso casa'in da tara na daga damuwarshi ta yaye.

Makaranta ya koma saboda yanada lecture da yan ug4, yana nufo office dinshi ya hango matar nan a tsaye yau ta zuba kyau na musamman ta saka fara atamfa mai zanen baki tayi lalle ja, dauke idonsa yayi daga kanta ya bude kofar ya shiga yadan zauna sai yaji an kwankwasa, daga zaunen dayake ya bada damar ashigo, saida yaji karar rufe kofar sannan ya dago idonsa yana kare mata kallo, gaida shi tayi ya amsa yana ci gaba da kallonta da mamakin yadda take wani kallonsa tana yinkamar tanaso ya yaba surar jikinta tareda samun kujer ta zauna, "malam nidai na gani ina so, duk yawon da nake yi a makarntar nan ina yinsa ne domin kai, ka yarda dani ka aureni zan shayar dakai zuma ta sanann na kula dakai har karshen rayuwata" sake daga idonsa yayi ya kalleta sannan yace "idan babu damuwa ki fita mana" sake gyara zama tayi ta fuskanceshi da dan karamin bakinta daya sha jan baki yanata kyalli ta ce "don Allah ka duba maganar nan, har gaban gobe masoyi shine abin alfahari, ina sonka zan share maka hawayenka zakayi alfahari dani, dube ni mena rasa? Ga sura mai kyau ga farar fata, ga kyaun fuska, inada gashi menene na rasa da zaka ki sona"? Ba tare da ya daga idonsa ya dubeta ba ya ce "idan bakya so kiyi nadamar shigowa makarantar nan a yau ki gaggauta fitar min daga office" tana bude bakinta zata yi magana yace "get out malama" fita tayi da sauri amma kafin ta rufe kofar ta ce "tunda na saka rai dakai to ka zuba ido ka gani sai ka durkusa kana rokona in aure ka wannan kuma shine lokacina" dogon tsaki yaja yana cewa acikin ransa "jahila mara aji kawai" mikewa yayi ya nufi aji dan lokaci yayi har ya makara ma. Da misalin karfe 4:30 yana zaune a wani babban palo yana binsa da kallo a bansa kuma ruwa ne da lemu sai cake amma ko daya bai taba ba, Baba ne ya bude wata kofa ya shigo tareda cewa "Abubakar kayi hakuri na barka ko, kasan issues basa karewa yanzu" murmushi kawai Dr A.S yayi Baba ya zauan yana fuskantar shi, cike da natsuwa Dr A.S ya soma yiwa baba bayani "sunana Abubakar Sadeeq Zaki, ni dan tambuwal ne iyayena da sauran yan uwana suna can, acan suke zama, inada mata guda daya, ni lecturer ne a nan jami'ar usman dan Fodio a department din Sociology faculty of social science, senior lecturer kuma exam officer, Naga Nana Aisha inasonta da aure amma wannan maganar bata taba hadamu ba nida ita kuma idan babu damuwa bana so ta sani a yanzu idan har Allah yasa kun bani ita bayan kunyi bincike a kaina saboda zai iya affecting karatun ta".


Baba ya danyi shuru sannan ya ce "Bazan so gaskiya 8nyi mata dole ba amma kafin akai ga yin auren kayi kokari taji tana raayinka, saboda ni a zahiri banga abinda zata ki ka saboda shi ba, idan har na gama binci ke na akanka zaka jini" godiya  sosai Dr A.S yayiwa baba sannan ya fita.

Washe gari baba bai tsaya wani nazari ba dan yayi magana da Mama ya sanar da ita komai dan haka sai suka saka bincike akanshi.

Mama maaikaciyar asibiti ce matsayin matron a asibitin specialist ta saba da mutane sosai itama a nata bangaren tayi tambaya akansa ta gefen kawarta da sukayi karatu a tare, matar tayi farin ciki sosai saboda dan uwan mijinta ne, anan ne take bawa mama labarin asalin auren sa da matarsa ta farko auren hadi ne ta gefen uwarshi itako yar jega ce, sannan baya jin dadin yarinyar ko kadan saboda tanada rawar kai gashi ta samu daurin gindi a wajen uwarshi da danginsa, anan jikin mama yaso yayi sanyi amma bata nunawa matar ba, saida ta koma gida ta fadawa baba shima hakan da taji duk an fada masa dan shima yasan mutane sosai a garin amma kuma yaron ya samu yabo fiye da tunaninsa.

Sai da taji sauki ta koma makaranta sannan Baba ya hada meeting da sauran yayansa da kaninsa saboda shine babba agidansu sai mata biyu da maza biyu, yayansa kuwa daga babban yayansu Nabila sai yayyenta mata biyu nusaiba da Maryam sai baffa su biyar kenan.

Dukansu sunyi na'am da maganar sai mama ce take ganin kamar zata iya samun matsala da uwarsa da danginsa amma Baba yace shi ba ruwansa da wannan kowa da halinsa ake zama dashi.

sati daya baba ya bayar tazara sannan ya kira Dr A.S ya fada masa ya bashi dama ya turo magabatanshi, wannan maganar yajita kamar anyi masa bushara da aljanna, sanadin haka saida yayi nafila ta godiya ga Allah saboda Allah ya saka masa son Nana Aisha.

Shiri yayi takanas yaje tambuwal da maganar uwarsa ta kawo matsala saboda masifar ta ringayi amma ko dar bai ji ba tunda mahaifinshi ya amince, ganin baiyi kamar ya damu da fitinarta ba ya saka ta kirashi a daki tana tambayarshi wacece yarinyar bai boye mata ba ya bata duka labarin yarinyar sannan ya hada da rokon addua a wajenta, duk da har ranta bata so amma sai ta yi musu addua a zahiri.

Washe garin ranar ya koma karfe goma yake da lecture dasu koda ya shiga ajin tana tsaye tareda class rep dinsu a tsaye suna magana, irin kallon dayayi mata ya saka ta neman wuri ta zauna, saida aji yayi shuru ana saurarenshi ya kalle ta tana zaune kusa da class rep din Nana sule na bayanta ya ce "Aisha nabila tashi daga wurin nan" zaro ido tayi tana kallonshi har saida ya sake maimaitawa sannan ta mike cike da mamaki ta zauna kusa da Nana sule.



*Dr A.S. Zaki*

EXQUISITE WRITERS FORUM 
*SAFIYYAH GALADANCHI*

_sadaukarwa ga yayata Billy galadanchi_

SHORT STORY 

SHAFI NA BIYAR




Tunda tayi noticing changes daga wurinshi ta kara tsorata dashi saboda duk tambayar da zaiyi sai ya fara nunata sai dai idan batada abin cewa tayi shuru tana kallon kasa cike da tsoro.

Tambaya yake yi yana so ya musu fixing lecture saboda an kusa exam gashi basuyi nisa sosai ba, "Nana Aisha Nabila what time are you having lectures in your department tomorrow" a tsorace ta sake dagowa kafin ta mike tsaye tace "sir we don't have any lecture tomorrow" dagowa yayi ya kalleta kmar mai nazari sannan yace "ok class let's meet tomorrow by 8 to 10 at this venue" dayawa sunji haushi harda ita kuma ya lura da hakan su ko sun saba da free day ne ranar dan haka sukaji haushi ya fito dasu kuma tun 8, kwashe takardunsa yayi ya sake cewa "Aisha Nabila where is my attendance"? da hannu ta nuna masa gaban class rep, ya sauko daga kan stage din tare da karba sannan ya fita, Nana sule ta kalleta tare da cewa "kin shiga uku da wannan mutumin yau ji dakanshi a kanki ya sauke" tsaki tayi ganin yadda aka zuba mata ido ana kallonta tareda jiyo wasu maganganu suna tashi na tsegumi "Nana wallahi ya samin ido daga sau daya daya min mutunci shikenan ya kara samun damar samin ido, bazan zo goben ba sai na gani" dariya Nana tayi ta mike tana cewa "to nidai tashi muje ko na barki wallahi yau mijina baya jin dadi ko fita aiki beyi ba" mikewa tayi tana cewa "kin kawo mini naman? Mijinki Allah ya bashi lafiya" Nana tace "yana mota muje ki dauka, ameen Allah ya nuna min aurenki" Dariya tayi da kunyar karya tace "Ameen, mijin da zai aureni gskiya yayi sa'a" Nana ta kalleta tace "hmmm senaga kunfi dacewa da Dr A.S" tarar numfashinta tayi tana zare ido "maza tofar da yawun nan, Allah ya tsare in aureshi wallahi, dubeni fa ai zuwa daya zai karya ni sannan ga shegen ji dakai, ai tamu ma bazata zo daya ba" tabe baki Nana sule tayi ta ce "to goggo maida wukar bance shi zaki aura ba amma bakisan waye mijinki ba in Allah ya ce shine sekin aure shi ko zaki mutu" sai ta ware hannayenta tana cewa "Nidai mu bar wannan maganar kinji har naji gabana ya fara faduwa" "wai wai wai....Alamar soyayya kenan indai faduwar gaba kika ji" tsaki kawai tayi taki amsa mata, daidai motar ta suka tsaya ta dauko mata wata roba mai murfi ta bata godiya tayi ta nufi tata motar sai Nana tace "to matar Dr sai mun hadu gobe" cije lip dinta na kasa tayi tana hararar ta amma bata ce komai ba, tana zama cikin mota ta bude robar, murmushi tayi ganin harda kaza a ciki ta dauki daya tasa a bakinta, bata nufi gida ba saida ta tsaya ta siya coke sannan koda ta isa gida ta kusa cinyeshi, tsaki tayi lolacin data tuno da wayarta da bata gani ba, ta rasa inda ta bar wayar sati daya kenan rabonta da ita.




Office ya shiga bayan yabar class dinsu ya duba karamar wayarta data bari a motar sa wanda rashin chaji yasa ta mutu shikuwa se yau ya nemo irin charger din wayar dan haka kawai yakeso yayi mata bincike, ta cika full kuwa yana kunna ta massages suka shigo guda uku biyu da wata number daya MTN ne, massages din ya bude ya karanta na farkon kamar namijinne ya turo ya ce (salam Nana aisha nayita kiranki wayar a kashe konkinyi blocking dina ne? Nana ya kamata ki gane Mubarak yana sonki akwai abinda ya hanashi turowa yafi so sai yadawo don Allah ki saurare shi kuyi magana dan yace koya kira ki voice call ko ta wechat bakya dagawa) shuru yayi yana nanata sunan Mubarak, inda ba dan yasan class rep na nan ba daya ce shine dan sunan shi Mubarak kuma dazu yaga tana masa wani murmushi, a fili ya ce "zasu gane su duka koma bashi bane nasan shima sonta yake" sannan ya shiga na biyun, yayi shuru yana kallon massage din daya matukar bata masa rai, kawai sai ya shiga replying ya ce "Naga ni da shi wanda zai taimaki wani, nayi dana sanin soyayya da takkwallai irinku da basu san darajar dan Adam ba, kasa a ranka  baka taba sanin wata Nana Aisha Nabila ba shika ka fada masa yasan da hakan na shafe babinsa a littafin rayuwata" ya tura sai yaga kuma ba kati, tashi yayi yaje refreshment centre ya siyo shi yasaka sannan ya sake resending tare da kashe wayar ya saka ta a drawer din table dinshi.

Washe gari kuwa kin zuwa lectures din tayi yanata baza ido bai ganta ba ita da kawarta, sai yayi tunanin a kwai dalili, ta wani gefen kuma murna ce cike da zuciyarshi saboda yau za'a je nema masa aurenta, duka ajin sai da ya basu kyautar 10 marks suka fita cike da farin ciki da murna wanann karon ya karya record dinda ya kafa na rowar maki da mugunta saboda kaf rabin ajin yan carryover ne.

Tunda ta tashi take jin jikinta a mace haka dai tayita zama a daki saida Maryam tazo suka kule a daki sannan ta kalli Maryam din ta ce "Meramu wannan kibar fa ta macece" Maryam ta kwanta kusa da ita taca "Nabila aure dadi... musamman in kika yi dace" kallonta tayi tace "Nifa ba labarin aure na tambayeki ba kina naga kinyi" dariya tayi tareda mikewa zaune tace "shine sirrin kibar yarinya kema ai kin kusa auren zaki fahimci me nake nufi, ga abinci me dadi se wanda ranki yake so ga soyayya karshe ga barin madara kullum" Nabila ta shafi cikinta dake kukan yunwa tace "bar wannan magana Anty Maryama, amma kinsan Baba so yake ya aurar dani" Maryam ta ce "kedai kiyita addua tashi ki dafa mana Indomie ita babynki yake so" tashi tayi tana murna tace "don Allah ciki gareki" Maryam tace "sa wasa yarinya wallahi cikina wata uku" juyawa tayi tana murmushi ta fita.




Shabiyu na ranar aka bada aurenta amma saidai maganar ta juye dan atake aka saka rana wadda bata kai wata uku ba, wannan aikin baban Dr ne saboda sunyi magana ya fahimci halin da Dr din yake ciki, sun biya sadaki a take wurin sannan da saka ranar da za'a kawo lefe.

Suna zaune da mama a palo ta dawo daga aiki kenan sai gashi ana ta shigo da kayan nagani inaso, Nabila ta bude ido tana cewa "Laahh mama na waye"? Mama ta kalleta da irin ko in kula da baki sani ba din nan tace "Naki ne Aisha babanki ya miki miji ya kirani yace har sadaki sun kawo" wani irin shuru taji akanta tana kallin mama Amma bata ce komai ba dan ta rasa wane irin yanayi ne take ciki.


*Dr A.S. Zaki*

EXQUISITE WRITERS FORUM 
*SAFIYYAH GALADANCHI*

_sadaukarwa ga yayata Billy galadanchi_

SHORT STORY 

SHAFI NA SHIDA




Bayan mintuna kadan sai ta tashi ta shiga daki tareda saka kuka saboda tunawa da tayi da irin soyayyar da sukayi da Mubarak tun tana ss3 ashe ba shine mijinta ba wannan kuma bata san ma ya yake ba, gashi bata taba iya yiwa iyayenta musu akan abinda suka zaba mata koda takalmi ne, turo kofar akayi ta daga kanta tana kallon anty Maryam, ita ko ta shigo da murmushi tana cewa "Amarya kukan dadi ne zaki fara shan barin madara"? Nabila ta dan kalleta tare da cewa "hardake za a hada baki aki fadamin anyi min miji? Shakuwar mu bai kamata ace kema kin min shuru ba dan kinsan ni bazanki mijin da kuka kawo mini ba" tausayinta Anty maryam taji da haka ta zauna kusa da ita tareda riko hannunta ta ce "kiyi hakuri Baba  ne yace kar a fada miki Anty nusaiba ma taso sanar dake amma yace baya so ki sani, kiyi hakuri Nabila mijinki kyakkyawa ne ga kyan hali kuma dan gaye ne insha Allahu kinyi dace" murmushi tayi ta ce "koma dai wanene ba kun bada ni ba" Maryam ta shafa kanta tace "eh na miki murna zakiyi kina nan kusa" dariya tayi sannan tace "to ya sunansa"? Anty nusaiba da shigowarta kenan ta ranga musu guda tareda fadin "sunansa Abubakar Sadeeq  suna mai dadi amarya" hararan wasa tayi mata tace "nayi fushi Anty ko a waya kimin ya jiki sannan kuma kika min miji bayan bance ina so ba" Anty nusaiba ta yi fuskar serious tareda zama kusa da ita su ka sata a tsakiya tace "baba ne ya hana Nabila kinga karki damu nasan halinki shiyasa nima ban damuba daya hana insha Allahu sanadin biyayya zakiyi alfahari" ta gyada kai tana cewa "dan sammini biscuit din to" Anty tace "Naki ne kije gasu can kiyi ta ci da sha" mikewa tayi ta fita palon mama ta gani da wasu yan uwansu har an raba kayan an cire mata nata, ta gaidasu mama ta nuna mata tace "kirawo baffa ya kama miki kikai dakinki ki aje keda kawayenki" taji dadi dan ba rabawa zatayi ba kawai yan makarantar su zata cirewa da yan islamiya sauran kuwa zata ajiye a mota tayi ta sha, ita da kanta ta kwashe su duka takai dakin ta ajiye drinks da ruwa dole takai wasu store dan zasu tare mata space a dakin dayawa.

Duk da bata ji dadi ba amma kuma tayi kokarin dannewa sanadin hakan kuma ya faranta ran iyayenta da yayyenta ya kuma basu karfin gwiwar aurar da ita din.

Ranar Monday da safe kuwa ta kaiwa Nana kayan ta rabawa yan class dinsu kowa sai mamaki yake wasu suna cewa ashe idan Dr yaji an mata miji seya ji haushi dan sun gano sonta yake.

Zama sukayi Nana sule ta ce "wallahi Nabila abin kamar a mafarki kuma kince  bakisan shi ba" Nabila ta tabe baki tana cewa "kinga massage din daya turomin a ranar" ta fada tana nuna mata massage din ya ce 'Alhmdllh. Soyayyar da nake miki ta saka na nemi aurenki wajen iyayenki, kiyi hakuri ban nemi izininki ba, ki kwantar da hankalinki ganinki nayi naji ina sonki ba tallarki aka kawomin ba ba kuma sadakarki aka bani ba, kiyi mana addua da fata na alkhairi insha Allahu zamuyi alfahari da juna, Yau jumu'a Na biya sadakin ki Aisha zan soki kuma inyita sonki' Nana sule tayi murmushi tareda fadin "kalamansa akwai dadi da wayewa a ciki Allah yasa fuskarsa ma ta kasance a haka da kuma rayuwarsa" Ameen ta amsa sannan suka maida hankali ga malamin daya shiga a lokacin.

Baba da yaya suka tafi da ita shagon furnitures mafi tsada a garin sokoto kayansu masu kyau ne da suke kawowa daga waje duk da basusan yaya gidan Dr yake ba haka suka siya mata kujeru set biyu da gado biyu, center carpet na duka daki da palo dana dinning area, dinning table da wasu coffee table mai kujeru guda biyu, da sauran kawata gida.

Da murnarta suka dawo gida inda take shirin fara exam da kuma shirin aurenta, da  wannan mijin nata daya zabi ya boye kansa a gareta sai dai koda yaushe yakan tura mata sako dan yaji lafiyarta, bata taba yi masa replying ba.

Yau zasuyi exam ta uku ya shigo dauke da booklets da question papers yanata hura hanci da hararar student, duk wanda ya tara ya samu, saida ya daka musu tsawa suka nutsu, ya daki table din da ke gaba tareda cewa "tashi koma baya, ke dawo nan ki zauna" ya fada yana nuna Nabila, jikinta na rawa ta kwaso exam card dinta ta dawo gaban ta zauna yana  lura da duk yadda ta gigice, sannan ya nuna hular kansa tareda cewa "which color is this"? Duka hall din suka ce "Red" ya gyada kai ya sake cewa "when you see this color what comes up to your mind first" wasu na dariya suka ce "Danger sir" yayi murmushin mugunta "so be careful" duk sukayi shuru dan sun san halinshi kenan yau yazo da rashin mutunci kenan.

Nabila tana zaune kawai tana mamakin yadda ya zuba mata ido yana kallonta sannan ya matsa mata da zuwa kanta ya tsaya duk ta daburce dakyar taga sun gama  exam din sun fita. Bayan ta koma gida tana kwance a daki tana hutawa sai ga kira da wannan numbern, saida ta katse saiya turo sako 'sweetheart pls pick the call mana abu zan tambayeki' yadan bada tazarar minti biyar seta sake kira, dagawa tayi tareda yin sallama ya amsa cikin wata murya daya soma amfani da ita a yau sannan ya ce "menene size dinki na bra"? Shuru tayi kamar bata ji shi ba har ya sake maimaitawa, murmushi yayi yace "gani a shago Aishatu kiyi magana" dan lumshe idonta tayi saboda kunyar abinda zata fada din data ce "32" a hankali ya ce "are you sure karfa ya miki yawa" shuru tayi masa, murmushi yayi yace "ok to shikenan pant fa"? Kit yaji ta kashe , gabanta na faduwa ga kunya sai taji kamar tasan muryar wallahi, amma gaskiya muryarsa nada matukar dadi, sai tayi girma kuma gata hade da kamar mura tana bada wani sauti mai shiga zuciya, kwantawa tayi tana ta murmushi tare da tunanin ya suffar wannan bawan Allah, Baba ya turo kofar dakin da sallama, sai ta tashi da sauri tana gyara zamanta.


*Dr A.S. Zaki*

EXQUISITE WRITERS FORUM 
*SAFIYYAH GALADANCHI*

_sadaukarwa ga yayata Billy galadanchi_

SHORT STORY 

SHAFI NA BAKWAI 

*salam. Pls duk wanda keson novel din nan daga farko suyi following wannan link din sai in tura musu nagaji da badashi individually*

https://chat.whatsapp.com/D1UejYMEqMtH9aENSROJYn

7

Kujerar madubi ya janyo tareda zama yana fuskantar ta, yaji dadin ganin batada damuwa yanzu ma kamar tana cikin farin ciki, gaida shi tayi ya amsa yana cewa "har yanzu akwai sauran kayan can" ta kalli gefen daya nuna cike da kunya tace "Eh Baba akwai, kasan tunda ba garin nan nayi secondary school ba duk banida wasu kawaye da yawa" yana murmushi yace "ke kuwa dama haka kike so kiyita hadiya ko"? Tayi dariya kawai gyara zamansa yayi ya fuskance ta dakyau sannan ya ce "Aisha kina da labarin an rage sati biyu acikin date dinda aka sa na aurenki"? Ta girgiza masa kai alamar bata sani ba "ganin hutun naku bashida tsayi kuma shi mijin naki dole zai tafi dake garinsu dake nan sokoto bana so a taba miki lokacin shiga ajinki shiyasa nayi amfani da lokacin hutun ku sai ayi a gama har ku huta sannan a koma, hakan yayi miki" dariyar karfin hali tayi da kunya a tare ta ce "Haba Baba, nikam duk yadda kukayi banida matsala insha Allahu" hannu ya saka a cikin aljihun shi ya dauko zobuna guda biyu daya na azurfa daya na zinari, ya mika mata ya ce "saka in gani ko kin kara kiba bazasu miki ba" saboda tsananin son zobe da take sai taji dadi ta karba ta saka tana nuna masa "ai Baba kasan yatsuna kaga sunmin daidai ko"? Ya gyada kai ya ce "to nagode yar autata Allah ya miki albarka yasa muce gara da mukayi" sai da taga fitar shi sannan a hankali tace Ameen, tashi tayi ta shiga toilet ta dan watsa ruwa, tana fitowa mama ta leko tace "ke zo ki same ni daki" hijab ta dora kan towel din da ke jikinta ta bi bayan Mama, kaya ta gani sun zagaye mama da anty nusaiba da bata san ma tazo ba, zama tayi gabansu tana kallon kayan, Mama ta fara dauka da guda-guda tana mata bayaninsu, daga karshe ta mika mata wasu ruwa a gora guda biyu tace "tafi da wannan tun yanzu ki fara tsarki dashi a ruwan dumi kawai zaki dan zuba kina tsarki har idan ankaiki fa karki fasa dan yana maganin infection da Kariya sannan yanada kamshi, musamman bayan kin gama hada shimfida da mijinki kafin komai kiyi tsarki dashi" fuska ta yamutsa ga kunya ga haushi tace "Maaamaaa ni menene hadina da wannan kayan kuma" Mama ta saki baki tana kallonta Anty Nusaiba ta ce "ke bari infito miki a mutum, a shekarunki dole kisan wannan lamari koda bakiyi aure ba kinada labarinshi kuma idan aka kaiki dole shi zaki yi da mijinki, bakida wanda suka wuce mu wannan da kika gani ma inkinsan abinda ake cewa bugun lamba to shine bayanin ma ba akai ciki ba, akwai randa xakiji abinda zakiga kamar yafi karfin kunnen ki kuma dole ki dauka, duk haka mama tai mana bata wasa da rayuwar aure kiyi yadda tace kawai, komai kyaun mutum ya kara da wanka balle ke da duk mun fiki auki dole a tashi tsaye da gyaranki, dauki dai abinda ta baki kije ki fara anfani dashi, dauki kuma ga wata leda chan kiringa shan garin a fura ko kunu ko nono na hips ne da boobs ko kadan kika kara yafi ace baki ba" tana turo baki ta dauka ta nufi dakinta dasu saida ta shiga toilet tayi tsarkin tana jin dadin kamshin abin ta fito ta shafa mai na gyaran jiki data karba yanzu shima sai kamshi yake yi.

A fili ta ce "Shi wannan mutumin sai gata ake masa bayan ko saninsa banyi ba" rigar bacci ta saka tareda saka hijab ta fita kitchen dan yunwa take ji, sai da ta duba kullin tuwon dayafi kowanne girma sai ta hado da madaidaici ta debo miya a karamin bowl ta kwaso fiye da rabin naman dake cikin miyar ta dawo palo ta baje ta fara ci bayan tayi bisimillah, Mama taja ta tsaya kanta tana mamakin wannan lamari ta kwaso nama sannan ga wannan mugun ci da take kokarin hanata amma abin ya faskara, dagowa tayi tana kallon mama tareda yin fuskar tausayi "a'a menene na kallona nikam, kisa himma kiyita ci watarana zakiji kunya awurin miji gashi dai kuma zakiyi aure" ta girgiza kai tana cewa "ai bazanci a gabanshi ba mama"

Please Login or Register in order to submit comment