Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Yazeed kaki kaje ka ganni Sanan yanxu Ina maka magana kayi Shiru. Sorry Sister kece daga Xuwa Kika nufi wannan tshowuwar. Ayeririri inno tayi guda yau nagane kishi irin na yazeedu dama Nadade danasanin kishina kake Cikin gidan nan Shiyasa kake Alfarma,Aurene dai kayimun tsufa Akai kasuwa.dariya duk Sukayi, banda yazeed da yaja tsaki Mtsww kinada matsala wannan tsohuwar Wlh. Tashi yake kokarin yi mai ya tuna yadawo ya Xauna.Abba jibi ne tafiyata Xamuje tare da Nazir da yusuf! Allah ya kaimu my Son. Amin Abbana,mamy bakice Komai ba. Allah yamuku Albarka Son Allah ya tsareku gaba daya.Amin Mamy ta. bro yazeed Ina Xaka ne wai??Sister Saudiya Xani Nayi muku addu'a. gyaran murya Inno tayi tana kyafta ma leemah ido. itama leemah kashema inno ido tayi Alamar ta gane. Laaaa Abba Ai muma jibi Sukace Zamu tafi. Kallonta yazeed yayi kinga idan kinje Saikiyi addu'Anki ma kawai. dariya Leemah tayi kaima ka karamun da taka ba. Tunda tafiyarku taxo daya ai saiku hada tafiyar gaba daya ko? Mamy ke tambayar Yazeed. Haka kuwa ya dace inno ta fada. Hararar inno yayi,ya kalli mamy. Kai Aa mamy tunda itama da kawayenta Zata Gara Suyi tafiyarsu ni banason Shirmen Su. da Sauri Inno tace Amadi kanajinshi fa. Murmushi Abba yayi kyaleshi tashi kaje yazeed Kowa yayi tafiyarshi daban yama fi. Tashi yazeed yayi yana fadin yawwa Abbana yasan Halin yara. Inno data Saki baki yana fita tace Amadi Bazaka daina biye yaron nan ba kenan? Inno Rabu dashi dakaina Xanje Nahada musu tafiyar. Murna Leemah tayi tace yawwa Abbana.

Kausar na karasawa gida gaisawa kawai tayi da Hajiya sai yar firar dasukai.Hajiya bari Nayi wanka yunwa nakeji Wlh.maxa yar Albarka Kiyi kixo kici Abinci.Toh mamah. Yawwa Kausar Kafin kitafi nikuwa maganin dakike Amfani dasu kinajin chanji Ajikin ki? "Sosai ma Hajiya" kinga maganin infection din nan ma Saura Kadan,Sati biyu kawai nayi Amfani dashi Naji Alamar Sauki,har Asibiti naje Sun tabbatar Mun dacewa banida Wani Ciwo Yanzu Ajikina.kai Alhmdllh Nayi matukar farin ciki Hajiya ta fada tana daga hannu Sama. Amma mamah ni haryanzu ina fargabar tarewata gidan Yusuf! Kallonta Hajiya tayi kina nufin duk Rawar kafa din nan da Yusuf keyi Akanki haryanzu babu Abinda ya shiga tsakaninku? Kausar taji nauyin maganar Amma ya zatayi mahaifiyarta ce itace wadda yazama dole tasan matsalar ta,domin daga Ubangijin daya Halliceta Sai Mazon Sa babu wani wanda yachanchanta ta girmama bayan Su Sai mahaifiyarta da Mahaifinta daga bisani Sauran mutane. Dan haka babu wani Amfani danta boye mata Sirrinta. Eh mamah babu Abinda ya shiga tsakanina dashi ina tsoron kada yakasance Nidin ba budurwa bace karashe maganar tayi da kuka. Jawota Hajiya tayi kan jikinta tana Shafa bayanta,ya'isa yata na fada miki babu Abinda Xai faru tsakaninki dashi Sai Alkairi ki kwantar da hankalinki. Inason yanxu kisanar dani gaskiya kin taba Aikata wani da Da Namiji ne? Da sauri Kausar tace Wlh Allah mamah bantaba Aikata Wani Abu dana miji ba. Indai hakane kuwa Kausar ki daina daga hankalinki Akan Wani Abu na daban. Shikenan Mamah insha Allah Na daina.Allah miki Albarka ya kareki daga Sharrin mutum da Aljani da dukkan Abu Mai cutarwa.Allah Amin Hajiyata Kausar ta fada tana kissing Hajiya A kumatu.maxa tashi kiyi Wanka.Tom Hajiya.....Namance ban fada miki ba mamah! Meke nan yata?? Jibi Xamu tafi Saudiyya. Kai masha Allah Naji dadi Allah ya tsareku.Amn Kausar ta fada tayi Ciki. Tana Shiga kiran Yusuf na Shigowa wayarta. Da murmushi ta daga.my wife I miss you Abinda Yusuf yafara fadi kenan. Miss you more Kausar ta fada kasa kasa. Meke damunki Sweetheart kaman kinyi kuka. Zaro ido tayi Kaman yana ganinta banyi ba Sweety Kawai gajiya ne. Sorry kinji.Uhum kawai Kausar tace. Albishirinki! "Goro my Honey" jibi ne tafiyarmu Saudiyya nida Yazeed da Nazeer. Wow what a Wonderful Story lyk Sweet. Ajiyar Xuciya yusuf yayi dan nace Zanyi tafiya kike murna Haka? Waye ya fada maka kawai dan inaganin Xamu tafi tare gani ga mijina Shiyasa na fada haka. Me kike fada haka? ina fada maka jibi muma Xamu tafi. Wow yusuf ya fada are you Sure? Yeah Kausar tace! Naji dadi matuka dole tafiyata ta dawo nida ke. No Honey mu hada gaba dayan mu dai. yes Yusuf yafada da karfi hakan ma yafi. Wayyo Xaka fasamun kunne. Am Sorry my.dariya Kausar tayi kama kunenka. Shima dariya yayi kin mance wa'azin jiya dakikai ko? Au na mance.kin kyauta Ai. Uhum Uhum Kausar tace kaman irin Xatai kuka din nan. Menene Kuma Sweetheart? Ni Wanka fa Xanyi ka hanani. Sorry kice dai kinason nazo namiji oya Shirya ina Xuwa.Rufe ido tayi ni banaso. Zakiyi bayani idan kikaxo hannu ba wanka bama har.......kashe wayan Kausar tayi jin duk Zai kashe Mata jiki.Hanyar toilet tayi face dinta dauke da murmushi.

πŸ’–πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’–πŸ’‹πŸ’‹πŸ’–
YAR LESBIAN CE
πŸ’–πŸ’‹πŸ’‹πŸ’–πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’–
By
Nadeeya mohd Ahmad
(πŸ’–NADSEERπŸ’‹)

dedicated to
Xaynab Ummu mahbub

Page..45/46

Zaune Suke babban parlon Abba mamy inno and Leemah. Inno naji tana magana idan ni baka yarda da Zancena ba Ai Ga Halimatu nan Ka tambaya Amadi. Kafin ma Abba yakai ga tambayar Leemah tayi Sauri tace Abba Wlh da gaskene bro Yazeed da feenah Suna Soyayya.Kasan dai yanda bro yake da yaya yusuf baya boye mishi komai,kuma Kasan yanda nake da feenah idan ma baka yarda ba Abba Bari ka gani.wayarta taciro ta Shiga Nuna ma Abba pic din feenah da yazeed har wanda take bacci kan jikinshi a mota. Girgiza Kai Abba yayi yanxu dai na Shirya muku tafiya Anjuma da Karfe 8 Zaku tafi. Haba Amadi inno ta fada ya muna magana mai Muhimanci kana wani xance. Sallamar Kausar ya hana Abba cewa komai. Da gudu Leemah ta tashi tayi kanta.my kausar harkun karaso. Kardai ki ballamun yarinya mamy ta fada daga Nesa.dariya Sukayi suka karasa. har Kasa Kausar ta tsugunna tana gaida Mamy da Abba.Amsawa Sukai Cikin kulawa.Mamy tashiga tambayar ya Hajiya.Mamy lafiyansu qalau tace Agaidaku.muna amsawa. Juyawa Kausar tayi ta gaida Inno.Cikin Kulawa inno ta Amsa ma Kausar. Mamy ce tace Ai ba karamin birgeni kukai Ranar walimanku ba. Yarana Akwai hazaka.Allah yamuku Albarka. Amn Sukace Gaba daya. Abba yace Ai Wajen Aiki daya ma Zan Sama musu.yeee Leemah ta fada.Abba dama bro yazeed ya daukemu a Asibitin Shi. Nima haka nake gani mamy ta fada.Shikenan idan kun dawo Saiku Kai mishi takkadunku ya duba Ai. Thanks Abba Kausar ta fada Kai adurkushe. Kausar waye ya kawoki ne?Leemah ta fada? Yusuf ne ya Shiga wajen yazeed yanzu. Waini ina Nafeesatu Abba ya tambaya.da Sauri Leemah tace Abba Ai tace Xatazo yanzu duk ta nan Xamu wuce. Inno ganin Xa'a Shiririntar da wanchan magana yasa ta kalli Kausar.kafso Dan Allah Nafeesatu ba budurwar tsaka bace?? Gaba daya parlon Sukasa dariya. Kausar tace eh Suna Soyayya Amma babu wanda Sukeso yasani. kallon Abba mamy tayi kajifa mutane duk Hakan Suke fada,Anya Abban Leemah ba Gaskiya bane kuwa? Koma dai menene bari Nakira yazeed din Suzo Shida yusuf. Kafin ya daga wayar ya kira Su feenah Sukashigo tare da yaya Nazir,mum,dad Sai Twins. Ai gaba daya parlon yakara hargetsewa Leemah da Kausar Sukai Kan feenah. Twins Sukai wajen inno,Mamy ta tashi tana taren Aminiyarta mum yayin da Abba ke fadin Aminina Umar Faruk bako waya. duk lokaci daya kuma suka koma Suka Xauna Aka Shiga gaisawa. Dad yace Alhaji Ahmad katara mutane A parlon naka. Inno najin haka tace Umaru Gara ma dakazo ai domin magana mai Muhimanci Akeyi. toh Toh Alhmdllh Dad ya fada,Ai Saimu cigaba. Abbane ya kalli feenah yace Yata Angama karatu lafiya? Alhmdllh Abba feenah ta fada Cikin Sanyin muryarta. Masha Allah Abba ya fada. Yanxu Sai maganar Aure ko kuma neman Aiki? durkusar da Kai kasa feenah tayi tace Aiki Abba. Ahhh ban yarda ba yata nafison kufara Aiki kuna dakunan maxajenku. Feenah batace komai ba.Abba yace yanzu wa kika tsayar Amatsayin mijin Aure? Saida tayi Shiru nadan lokaci daga bisani tace Abba yaya Kabeer! Toh Shikenan Kinga dama gobe mukeson Xuwa Yola din Xamusan Abinyi Allah yamuku Albarka.Amin duk yan wajen Suka fadi.Inno kallon feenah tayi Nafisatu kifadi tsakaninki da Allah kada Ki cutar da kanki. Kallon Inno feenah tafarayi dan bata gane me take fadi ba.harara ta Sauke mata takara daure fuska. Haushi inno taji tace kin harara kanki ni Gata nakeson nayi miki.ganin inno Xata fadi wata magana yasa Abba cewa kutashi kushiga ciki feenah.tashi tayi Leemah da Kausar na binta a baya. Waikai Amadi meyasa kakemun Hakane yakamata fa muba yaran nan Abinda Zukatansu Suke so ba san Ranmu ba. Haba inno bakiga yanxu Agabanki na tambayeta ba tace Kabeer ne Xabinta. Dad ne yace wai meke faruwa ne? Da Sauri Inno ta kwashe komai wanda yusuf ya fada mata game da feenah da yazeed harma da karinta ta kara ta fadama dad.kallon kallo Aka shigayi tsakanin dad da mum. Inno ce ta katsesu idan ban fada daidai ba Ai ga Nazeer Nan Shima ya Sani. Kallon tambaya Daddy yayima Nazeer. Eh daddy Akwai Soyayya atsakaninsu tun Kafin nafara Son Leemah! Toh gashinan kunji ni nasani andade Ana Boye Abu Anan gidan Amma ku kunki yarda,Wata kila saikun gani da idonku Xaku yarda. Aa inno bawai munki yarda bane yanzu Agaban idonki Mukai ma yarinya magana ta fadi wanda takeso kuma.Amma bari mukira yazeed muji ta bakinshi. Itama Feenah adawo da ita Suyi magana tare dad ya fada. Mubeen jeka kira bro yazeed mumy ta fada yayin datace Mubeena ta kira su feenah.

Kusan Atare Su feenah Suka Shigo parlon tare dasu yazeed. Xama Sukai gaba dayansu.dad ya kalli feenah Ummina kin tabbatar Kabeer Shine wanda kike So? Eh dad ba tuntuni kuka tsayar da maganar ba! Kuna waya dashi ne? Aa dad inaganin ko yanada aiki Sosai yasa baya kirana. Amma kun taba Xama kunyi magana ta fahimta dashi? Sunkuyar da kai tayi kasa Aa dad. Wannan ya Nuna cewa dan kibi umarninmu yasa Zaki Auri Kabeer. da Sauri feenat ta dago kai Aa dad inason Shi ma.kinasonshi Kuma Akace kuna Soyayya da dan'wankin yazeed. Wani bugun Zuciya taji lokaci daya Hawaye yashiga Xubo mata. Tambayarki Nayi ummina ba kuka nace kimun ba. dad Wlh kudaina kama maganar Inno daga ta ganni naje gyaramai daki Shikenan take fada ma mutane wai Soyayya muke. dariya Abun yaso ba Leemah,Kausar,Nazeer da yusuf ganin yanda inno ta bude baki gaba daya. Nice namiki Karya munafuka sau nawa Ina kamaku Kuna Zance?Rannan harcemun kukai nabar wajen ina takura muku. Amadi Shiyasa nace maka kasaka Abun hangen Nesa kaki yau gashi Ana karyatani Akan gaskiya ta. feenah jitake Kamar ta shake Inno domin Arayuwarta babu Abinda ta tsana irin batai Abu ba Ace tayi. Dad Ni Wlh karya.....da Sauri mum ta bige mata baki. Abba ne ya kalli yazeed wanda yayi mutuwar Xaune Sabida bakin cikin Abinda inno tamishi. Yazeed banason Karya Menene gaskiyar Wannan maganar? Kuna Soyayya da feenah ko Aa? da Ker yazeed ya dago kanshi Abba ni ban san komai game da maganar nan ba,ina ganin feenah dince take Sona har ta fada ma inno. da Sauri Inno tace kwarai haka Akayi domin......wani kuka da feenah ta fashe dashi yasa inno yin Shiru. Dad kaji wannan tsohuwar ko Wlh Sharri takemun ni banason yazeed bana kaunarshi Na tsaneshi.Yazeed maganganun feenah ba karamin haushi Suka bashi ba.Kamar ni take fadama irin kalmomin nan.nan da nan idonshi Suka Kada. Dad ni Asalima banida makiyin daya wuce yazeed. Ya'isheni dad yafada da karfi Xan Saba miki mara mutumci kawai.dad Wlh da gaske nake maka bana kaunarshi...mari mum ta kai kan face din feenah da Sauri mamy dake kusa ta tare.daga feenah tayi takaita dakin Leemah Xauna daughter Kada ma kikara fitowa Nasan Wasa inno take ke ba'ajin yazeed bace ma. daga Haka mamy takoma parlon.Abba! Yazeed ka tabbata bakason feenah? Eh Abba Ni bana sonta. Ina yarinyar danace kanemo Nan da month? Abba bansamu ba. da Kyau kashirya Nasamo maka mata A Katsina Xamuyi Komai kafin Ka dawo daga Saudiya daka dawo Xan hada Aurenka Dana yusuf. Wani miyau Yazeed ya hadiye da ker be iya amsama Abba ba. Kan Nazeer Abba ya juyo.yarona matar danace kasamo ka Samo? durkusar dakai kasa yayi yace Nasamo Abba. toh Alhmdllh Ka tsallake Auren yar kauye. Yarinyar gidan waye? Abba Leemah ce. Murmushi Abba yayi ya kalli Leemah.Halimat Wai Hakane kin Amince mawa Dana?Rufe face tayi eh Abba.duka wajen dariya Sukayi,banda yazeed dake jin kanshi Kamar Zai fado. Abba ya kalli dad.Alhaji Umar Faruk ina nema ma dana Auren yarka Haleemah! Murmushin manya dad yayi ya kalli Leemah, my daughter kin tabbatar Nazeer shine Zabin ki? Eh dad na tabbata.toh Masha Allah. Alhaji Ahmad na ba yata Auren danka.gaba daya wajen Suke fadin Masha Allah. Abba yace ko Xaka iya Sanar damu yaushe Xamu turo Asaka Rana? Xanyi Shawara dad yafada.haka Sukayita Raharsu.yazeed dayaji Zaman duk ya isheshi ya tashi yanufi part dinshi.

Kan bed ya Kwanta Rike da kanshi.Ni yarinyar nan take fada ma bata kauna?Tambaya yashiga yima kanshi. Waini take cema bata da makiyi irina,Wlh Saitayi dana Sanin fadamun wannan maganar. Ni basa'anta bane Ni dama Ko tana Sona me Xanyi da ita,yarinya ce fa Sai iskanci cike da Ciki tazo yau saita fadamun Abinda Naji tanayi kwanaki menene Shi. Kokuma namata dukan tsiya kafin nabar gidan nan yau.Wayyo Allah yazeed yafada tunowa da Abba yace Xaimai Aure Nan da Sati biyu. Innalillah Ni yanxu wace yar bolan Abba zai Aura mun?Nasan mafita idan naje Saudiyya gaba Xanyi ba sainaga wanda Xa"ama Auren dole ba. Yusuf ne yashigo dakin yana kunshe dariya ganin yanda yazeed ya kwanta Kamar Wanda yayi Shaye Shaye. dafashi yayi Dr yazeed tunanin mai kake haka? Mtsww yazeed yaja tsaki Wlh sainayi maganin inno Agidan nan,tunda tazo take wargazamun Abubuwan dana shiryama Rayuwata,idan banda wulakanci tarasa wanda Xata hadani da ita sai waccen fitsa rararriyar yarinyar,kuma Wlh Xanga Wanda Xa'ama Auren dole Agidan nan. Sorry my friend yusuf Ya fada yana kama Hanun yazeed ganin yanayinshi yasan ba karamin baci Ranshi yayi ba. Ka kwantar da Hankalinka Yazeed pls. Babu wani Aure daxa'a Maka,matsala daya! daka sani Ka Amince dacewa kanason feenah da Komai yazo da Sauki. Fixge hanunshi yazeed yayi daga Hanun yusuf. Ya isheka yusuf tunda kai kasamu matar da kakeso Shikenan,ni ko Oho! Matsalarka kawai naso Son ranka kake nufi,idan son feenah din kake kaje kafada mana a daura maka Auren mata biyu lokaci daya.gara ma Na Auri yar kauyen Akan yarinyar Nan Wlh.kallonshi yusuf yayi haka kace ko yazeed? Eh haka Nace. Alright tashi kashirya Nan da Anjuma kasan Xamu tafi. Ni babu ma inda Zani yazeed ya fada Rai Abace. Kudin jirgin fa? Ayi Asara yazeed ya fada ataikaice. Shikenan tunda Kace Haka kayita Xama kaga Anjuma bakasan me Xa'a kara bullo maka dashi ba. Da Sauri yazeed yace Waite bari na Shirya.dariya Yusuf yayi ya ware hannunwa Alamar ko Ajikinshi.

Da ker Leemah da Kausar Suka shawo Kan feenah ta tsayar da kukan ta. Haba kausar yazakice Kada nadamu bayan kinsan Inno ba gaskiya ta fada ba.dan Allah kujifa harcewa yake wai nice Nace inasonshi haba Dan Allah mai Zanso jikin yazeed.Ni Wlh Inno din Nan gara ta Koma kauyensu yafi. Ya isa my Feenah ki natsu. Ke kin tabbatar kinason Kabeer? Koma banasonshi Kausar ina ruwan inno dan Allah. Naji Nima lokacin da'aka fadamun ban yarda ba.Amma kifadamun kinason Kabeer ko Aa,Nima Zan fada Miki mafita daya yanxu. Shiru feenah tayi daga bisani ta tashi daga kan Leemah ta kamo hanun kausar.bazan'iya boye muku komai ba,Banason Kabeer Xan Aureshi Sabida banason ko Wani namiji Ayanzu,Amma ina da bukatar yin Aure kodan Na kiyaye Mutumci n.a.,kunfi Kowa Sanin matsalar dake damuna.Nisawa Sukai Leemah tace Amma me yasa bakyason bro Yazeed? Banasonshi Sabida dalilai da dama.Xan iya fada muku daya banasonshi dan bemun ba. Inno dake labe bakin kofa tashiga.Nafeesatu Kiyi hakuri jikata dazun bakina ne ya Subuce,Sabida yazeed ya dade yana Sonki daxun haushin Abinda kika cemai yasa Shima yace baya Sonki. Kinsan mene??kallonta kawai feenah keyi batace komai ba. yazeed girman kai gareshi inno tacigaba Shiyasa kullum Sai yazo yacemun kece ke Sonshi.nikuma ina biye maine kawai,Amma nariga Nasan Shine ke Sonki. magana feenah Zatai.....inno tai Saurin Cewa Abu daya Xakiyi Nafisatu kafin kutafi Yau Kiyi yanda Zakiyi kinunama su Amadi Yazeed ne kesonki bake ke Sonshi ba ta hakane Xa'a rabaku domin Naji yana kara fadi waike kesonshi Kuma iyayenku sun yarda da Hakan. Tunda Inno tafara magana Kausar da Leemah Suka gano Wani Shirin inno takara Shiryawa.Dan haka Sukayi dariya Aboye Afili Sukace tabbas maganar inno gaskiya ce kinemi Mafita kafin mutafi yau. Shiru Feenah tayi tanason tuna Mafita.kallonta inno tayi tace ko mafitar ma Saina nema maki? Shiru Feenah tayi. Magana inno Zatai Mamy tashigo kutashi kushirya yanxu Xaku tafi. tashi inno tayi itama tafita tana fadin kidai San Abinyi. Cikin kankanin lokaci Suka Shirya inda feenah tana Shirin tana nema ma kanta Mafita ne.Murmushi Naga tayi yes yaune Ranar daxan Rama Abinda Yamun.fita Sukai gaba dayansu babban parlon inda Suka tarar dasu Yusuf suma Sun Shirya.yazeed ne kawai babu Awajen. Abba ne yace wai Ina yazeed Ko mutafi mubarshi ne. Mamy ce tace Mubeen kira bro dinku. yana fita ba dadewa yadawo yace gashinan Xuwa. feenah najin haka ta tashi tayi waje.kusan karo takusa yi da yazeed.hanunshi taja Suka koma baya. Suna Xuwa tsakar gidan ta kalleshi Ido Cikin ido. Dr yazeed Kayi kuskure dakace Nice Nake Sonka,kasan Nasha fada maka banga Abun so Ajikinka ba. So bama Wannan ba Anfadamun Komai Nasani kuma Kasani bana sonka bazan Aure kaba Kuma Ka janye da maganar wai wani kana Sona. Yazeed tunda feenah tafara magana yake kare mata kallo, yanda dan Karamin bakinta ke motsawa Ahankali da yanda take juya idano ba karamin burgeshi yayi ba,Haushin dayakeji gaba daya yaji yafita mai.Cikin Wani irin voice yace.yanxu me kikazo kimun? Nazo nayi maka gargadi Sannan Ancemun Nasamu Mafita Ayau so baruwana da wannan Xancen,Amma yau dinnan Xan Rama Abinda ka taba mun. Hannu takai kan wuyanshi take yazeed yaji Wani irin yarrrrrrr. Saitin bakinshi takai nata, Nasan haka kayimun da ina bacci.kallonta kawai yake domin Shi kadai yasan Yanda yakeji. Lips dinta ta daura kan nashi ta kama tafara tsotsa. Inno naji tana fadin Bari nakirasu da kaina.tashi tayi tafito Abinda data gani yasata komawa Ciki.ina masu Cewa tsaka da Nafisatu basa Soyayya duk kufito kugani. feenah taji Sanda inno ta fada haka...Shiko gogan har yafara Son ya Xarce. Lokacin da yan parlon Suka fito yayi daidai da lokacin da feenah ta cire bakinta tana Nuna yazeed Haba Dr yazeed Nace bana sonka ko dole ne, tayaya Zan Aureka bayan Kana kokarin Aikata Son Ranka. Kajiko Amadi Sumbatar juna fa Sukeyi Kuma Sanan kace ba Soyayya Anan?Lallai kuduba Al'amarin Nan. Daga Haka inno tashiga Ciki kamar ta taka Rawa dan dadi.

[12/26/2017, 17:44] 80k: πŸ’–πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’–πŸ’‹πŸ’‹πŸ’–
YAR LESBIAN CE
πŸ’–πŸ’‹πŸ’‹πŸ’–πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’–
By
Nadeeya mohd Ahmad
(πŸ’–NadseerπŸ’‹)

dedicated to
Xaynab Ummu mahbub

Page...47/48

Documents By AIHAUSANOVELS

Always visit Aihausanovels.com.ng For downloading free hausa novels

Like our Facebook page Fb.me/aihausanovels


Mutuwar tsaye Su Abba Sukai A wajen.Sundai Ga bakin feenah na motse Amma babu wanda yasan me take fada. da Ker Abba yasamu yace mukoma Ciki,dukkansu Sukai Ciki banda Leemah daketa faman daukan Su feenah pic,ganin feenah ta tawo yasa itama tayi Ciki. Yazeed da idonshi ya kada yakoma jaaaa kasa motsa kafarshi yayi,gaba daya feenah ta kashe mai jiki,bangare daya yana jin Nauyin Hada ido da iyayenshi,yarinyar nan ta kasheni,ta Aikata laifi ganinsu Inno gaba daya tamaida laifin Kaina.da ker yasamu yaja kafarshi yayi parlon Cikin fargaba.Shiga yayi ya Zauna kamar yanda yaga kowa A Xaune. Saida Shiru ya biyo baya nadan lokaci daga bisani Abba ya kalli Mamy kutashi mukaisu Airport din ko. tashi Sukai gaba daya inno ba karamin Haushi tajiba ganin Ba'Ayi maganar data so ba. ita tafara yin gaba tana fadin Oh ni Inno yaran Zamani Saidai Abarsu Idan Sunason junansu da Aure iyayensu Suka kasa fahimta Sai lalata ta biyo baya. Sumbatar juna ikon Allah. Gaba daya wajen kunyar maganar da inno take Sukeyi,Amma ba wanda ya'isa ya tanka dan Sungane Su take Azauna Ayi maganar. Dan haka Suka Nufi harabar gidan tana fadin Anan fa Suka tsaya Ana Sumba Ni inno kada dai Suje Suyi Aika Aika. Yazeed da gaba daya inno ta gama Kular dashi kusan Atare Sukaja tsaki tare da feenah. Aikuwa kamar jira inno take kunma iyayenku tsaki tun farko Saida nafada muku Ku fadi Gaskiya Baku fadi ba.yanzu kuna Sumbatar juna Ai Abinda Zakuyi Nan gaba Saiya fi haka. durkusar da kai kasa feenah tayi tana data Sanin Abinda ta Aikata,Sai yanzu ta gano Cewa inno wani Shirin ta mata yasa daxun tazo tana lallabata. babu wanda yakula inno haka tarinka Sababinta. Mota biyu Sukai Zuwa Airport. Motar Abba ne Agaba inda ya dauki Mamy Agaba baya kuma feenah,Kausar,Leemah Sai Twins. Motar Dad dake baya kuma inno ce Agaba Sai Mum,Nazeer,yazeed Sai yusuf Ahaka Suka karasa babban airport dake garin kaduna. Suna karasawa baifi da minti30 ba Akafara kiran Suna. yusuf dariyar mugunta yake domin yasan yanda ya hada Zaman Cikin jirgin. Kausar Akafara kira tashiga bayanta Yusuf ne. Inda Suka Zauna Awata kujera ita tana Ciki wajen window yayin da Yusuf ke gefenta. Kallonshi tayi My Yusuf Kaine kashirya Hakan ko? Murmushi ya mata ya lakaci hancinta yes my wife Sabida muyi fira Sosai nayi Hakan.ba'a wani juma ba Leemah da Nazir Suka Shigo.dayan bangaren Suka Zauna inda Suke seat daya dasu yusuf.Murmushi duk Suka sakar ma junansu. Akasa Najiyo inno nafadin Amma yan Company din nan Basuyi hadin nan daidai ba Amadi,! Karfa tsaka ya matse Nafeesatu a lungu Gara kusan Abunyi.tsaki Yazeed yaja yayi Shigewarshi Cikin jirgin.yayin da feenah tabi bayanshi. Chan karshe ta wuce kowa taje ta Xauna. Saida Akai wasu mintuna wata mata tazo kusa da feenah,Sister idan bazaki damu ba Zance miki wanann wajen Zamana ne. Kallonta feenah tayi tace Ok tashi tayi tana neman Wajen Xama Amma duk da mutane.gashi lokaci daya Aka fara Sanar da jirgi xai tashi. Ba yanda Xatai takoma kusa da yazeed ta Xauna. Tabe baki yayi lokaci daya Kuma ya tashi tsaye ban hanya ya fada rai Abace.matsawa tayi da Sauri Amma duk da haka Saida ya taka mata kafa da karfi.Runtse ido tayi tanajin Xafin wajen,dallah malama Shiga Ciki kiban Nan. Matsawa tayi Ciki hawaye Na Xuba kan face dinta. Ahaka duk Suka Saka belt jirgi yatashi. Allah ya tsare duk yan wajen Suka fada banda inno dake daga ma jirgin Hannu tana fadin tsaka yatafi. Da Haka Suka koma Cikin motoci Sukabar airport din. Su Abba na karasawa duk Suka Zube a parlo.dama Alhaji Umar Faruk Abinda yasa nace kada kuhuce Ku biyo ta nan inason Nace maka kashirya gobe Muje Yola Kan maganar feenah da Kabeer. Kwarai Nima nayi tunanin Haka dad ya fada. Da Sauri inno tace Ku kuwa kunada Hankali? Bakuga Abinda yaranku Suka Aikata daxu bane da bazaku basu Abinda Suke So ba.ko Kuma haka Akai muku? Toh indai n.a. isa daku kubi Xabin yaranku ba Son Ranku ba.daga Haka tayi gaba tabar parlon. Kallon dad Abba yayi Kada kadamu Alhaji Faruk Kasan girma yazo mata.murmushi dad yayi yace Allah dai yakaro musu tsawon Kwana mai Albarka.Amin duk Sukace daga bisani Su mum Suka tashi.Toh Fatima Zamu tafi.Kai Hafsat kibar Twins mana Su Kwana biyu. Kuma Ai ban kawo musu kaya ba.kada kidamu yanzu Xan fita Nasiya musu.

2 Comments On YAR LESBIAN CE Book 2
avatar
umar-6-7

1 year ago

Reply

Nice book

avatar
abubakar-ibrahim-7

7 months ago

Reply

Yes

Please Login or Register in order to submit comment