Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya Azurtasu da haihuwar Yara 3 Nazir Shine babba Sai Aishatu Sai Sukai Auta Umar daga nan haihuwar ta tsaya musu, kusan kansu duk daya dan ita Nafisa Akai Akai take haihuwar ta, duk da cewa Fulanine Iyayen su basuyi kasa a quiwa wajen ganin yaran nasu Sunyi Karatun Islam dana Zamani ba, Sun taso da hazaka Nazir da Aishatu Aji daya Suke Inda suka wuce Umar da Aji daya,,,,,,, bayan Su Aishatu Sun Kammala Secondary dinsune Tasamu miji tayi Aure Anan yola inda yarage Nazir da umar wanda tun tasowarsu suke Son junansu Ahaka Nazir yaki ci gaba da karatunshi cewa Sai Umar ya Zana jarabawarshi ta Secondary Sucigaba tare,,,,,,,,,Masha Allah bayan lokuta Sun Samu addimetion Suka tafi makaranta a .A. B .U . Zariya,,,,, Hutu ke kaisu garin yola Suna matukar temakon iyayensu duk dacewa babu Abinda Suka nema Suka Rasa hutun Karshe dasukai Suka koma yola Anan ne Nazir yasamu mata yayi Aure yacigama da business Alokacin Aishatu tana da yara 4 duk Maza Anso Umar yafito da mata Ahadashi da Dan uwanshi yace Shifa Ina karatu mai Zurfi yake So yayi inda yasha banban da Sauran yan uwanshi kenan,,,,,,,Alhji Ibrahim bai cika takuraba indai wajen karatune Shiyasama ya Amince da Hakan, Umar kaduna yakoma don cigaba da karatunshi wanda da ker Nafisa ta Amince da Hakan yakanje ya dubasu Akai Akai, karatu yake Sosai wanda yasamu degree har biyu Anan ne ma ya yake Shawaran yafara business gun Wani Mahaifin Abokin Shi Alhji Aminu,,,,,,,,Suna gudanar da komai cikin Amana da gsky lura da Hakan ne watarana Alhji Aminu ya kirashi...... Umar badon komai na kiraka ba Nalurada irin Amanarka da Iliminka Da nagartarka Sannan Kwanakin baya dakuje yola da Sulaiman yabani labarin irin mutumcin iyayenka,,,,,,,,Don Haka na yake Shawaran Zan baka Auren Yata "Hafsat" Sai Asan nan Umar yadago Kai yace duk Abinda Ka yanke daidaine Baba Nasan bazaka taba cutar daniba Nayi matukar farin ciki duk dai Nasan cewa daman bazanji Kunya ba. Kaje Zanje yola muyi magana da Mahafinka Kafin nan Zaka fara Zance da Hafsa dan kufahimci Juna Yace toh Baba Alhji Aminu yaje yola Mahaifan Umar Sunyi farin ciki matuka Duk dacewa Sunso dan nasu yayi Aure a yola cikin yan uwanshi, Amma basu nunaba Sabida Alhji Aminu dattijon kwaraine bayan wata biyu Umar da Hafsa An fahimci juna inda Suke gudanar da Soyayya mai tsafta abinka da masu ilimi Acikin watan kuma Aka Saka Aurensu Ranar Wata juma'a misalin Karfe 10:00 dunbin mutane Suka Sheda Auren Umar Ibrahim da Amaryarshi Hafsat Aminu, Su Aishatu dasu Nazir duksunzo kaduna Kasancewar Agidan Alhji Aminu Ake gabatar da komai Hatta Su Hajiya Nafisa da Matar Nazir data haifa yara biyu mace da na miji duka suka dungumo Anci Ansha Anyi komai cikin Mutumci. Wani katafaren gida da Umar yagina A Unguwar Dosa Nan Aka kai Hafsa Gidane kato nagani nafada komai yayiπŸ‘Œ


Bayan Shekara daya
Hafsace Zaune da katon Cikinta Tana duba wasu takaddu Sai rintse ido take tana cije baki daga dukkan Alamu batajin dadi Abun taga Saici gaba yake tayanke Shawaran kiran Mijinta Awaya. tana Sanar dashi yatawo Dan dama banisa yake da gidaba Sabi da ita kasancewar Soyayya Suke Sosai danko Sharokan Sai Haka lol Hafsa machace yar boko Ga Kyau Kota'ina ta hadu Ga iya Zama da miji Shiyasa Suke cin karansu ba babbaka. Yana ganin Halin da take Ciki ya temaka mata Suka Shiga mota Sai Asibti Cikin mintuna da bazasu wuce5 ba Aka fito da jariri Kato farisol kyakyawa dashi. Wayyo zokaga murna wajen masoyan nan biyu dama duk Wasu masoya nasu. Ahaka Aka Sallmesu Suka wuce gida cikin farin ciki Aishatu Ita tazo ta Zauna da Hafsa har'akai Suna Ranar Suna yaro yaci Suna NAZIR Sunan yayan dadyn shi kenan. Bayan watsewar taron Suna da dare yana Zaune Suna fira Ga yaronsu sun rungume daga yau dai Hafsa kin koma "Mumy" murmushi tayi tace kai kuma "daddy" ba Ahaka Zamansu yacigaba da tafiya... yaron yanada wayo Sosai Dan haka yana Cika 3years Suka Sashi makaranta dama gaba dayansu Burinsu Kenan yana kokari kuwa matuka Bayan yacika Shekaru biyar ne Mumy ta tashi da wani Zazzabi mai tsanani Ai ba bata lokaci Suka wuce Asibiti gwajin farko ya nuna tana dauke da Ciki Wata 4 Murna Sukai Sosai dawowarsu kenan daga Asibiti Aka kirashi daddy A waya cewa Allah yama maihafinshi Rasuwa gaba daya Nima danake Typing Saida naji Ajikina Kasancewar tsowo mai Mutumci yarigamu gidan gsky😡 Tuni Suka Shirya Suka dunguma yola Harda iyayen Hafsa watoh Alhji Aminu da Hajiya Amina mahaifiya gun Mumy Kenan. Sunje inda Achan wasu Sukayi dan koke kokensu bayan Kwana bakwai Kowa yadawo Akabar Inna Nafisa Achan Haka Suke kiranta. Sundawo gida lafiya inda mumy tacigaba da Rainon Cikinta daddy yana kula da ita.
[12/11, 14:42] Hassan Atk:
[12/11, 14:42] Hassan Atk: πŸ’–πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’–πŸ’‹πŸ’‹πŸ’–
YAR LESBIAN CE
πŸ’–πŸ’‹πŸ’‹πŸ’–πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’–
By
Nadeeya Muhammad Ahmad

In dedicated to
Xaynab Ummu mahbub

*page dina na farkon Wan nan Novle Nayi korafi Kan cewa yakamata mai karatu ya tsaya ya natsu kan karatu kamin yayi bakaar magana, Amma jiya Nasamu masu mgn kan cewa Zan bata tarbiyyar wasu, Amma Naji dadi danasama wanda Suka fahimceni fiye da masu Zagin😑 Sannan Zan kara dacewa duk wanda yaga bazai juri karanta book din nan ba Can leave it. Danni da Masoya littafin nan yanzu muka fara*πŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ

Wannan page Nakune Masoya littafin "yar lesbian ce" love you allπŸ’–

Page......5

Bayan Rasuwar Alhji Ibrahim Kamin su daddy Sutawo bayanda basuyi da Inna Nafisa kan ta biyosu ba Amma firrrr taki, Acewarta inda Kasar mijinta take itama Nan Za'a Saka ta idan tasu tazo. bayan Wata Tara da Wani yamanci Mumy Suna Zaune Suna fira da Matar Sulaiman Aminin daddy kenan, Dan Su daddy Tare Suka taso Sunayin komai da Sulaiman da Wani Abokinsu Ahmad duk dacewa Ahmad ya Rigasu Aure Dan Saida yayi Aure ya haihu ďa Namiji Sannan daddy yayi nashi Auren Saikuma Sulaiman yaya Awajen Mumy kuma Aboki Awajen daddy Shima yayi Nashi Auren. Mumy Takasance irin matan nan ne masu tattalin miji wanda Ko Zumunci basucika yiba Sabida kula da mazan su dan Haka bata zuwa ko'ina daga gidansu Sai wajen Aikinta dan Cikakkiyar barrister ce, Tana dan Zuwa YOLA wani lokacin idan daddy Zaije, ba kasafe tacika Ziyartar Maryam Matar Sulaiman ba Saidai Ita maryam din ke yawan Zuwa mata, ko Sau daya Kuma bata taba tunanin Zuwa gidan Fatima matar Ahmad ba itama Kuwa fatiman tace bazatazoba harsai mumy taje mata,,,,,kullum cikin Sa Rana take Amma ina,,,,,,,,hakan ce takasance Ayau ma tare Suke da Maryam Wacce Nazir yarada ma UMMA Tana ma mumy korafi Wlh kedai Hafsa bazaki chanza haliba kullum kina gida Kamar daddawa da Anyi magana kice daddyn Nazir na Gari Kamar dan ke kadai Akai miji, Kai Maryam kedai kullum maganar ki kenan idan ban Kula da Shiba waye Zai kula dashi beda kowa Anan garin wanda ya wuce ni da Nazir Sai wannan Cikin Nawa Uhum Toh dan Allah badole na Zamemai gata gaba da baya ba? Kizama Shi yazama ke Kawai karshen magana kenan Maryam tafada tana gyara Zamanta,,,,,,,,, Bari Nakawo miki Abinci kici Amma maganar nazama Shi yazama ni na nawa kuma Ai munzama tsoka daya mumy tafada tana bin Hanyar kitchen,,,,,,,Kayattacen Abincin da ta dafa ma daddy Aciki ta iba ma Maryam, tanaci Suna fira, Umma ce tace wai kuwa kinsan Fatima ta Haihu yau kwana hudu kenan, Kai Haba mai Aka Samu? Tahaifi diya mace, kai tubarakallah Allah ya Raya.Amin Umma tace Sannan Takara dacewa Saiki kishirya Kije Barka, Kai Maryam bakida tausayi wan nan Cikin Nawa Haihuwa ko yau ko gobe Zakice naje barka, Uhum haka kawai ma Anki Ziyara bare yanzu da Akeda Hujja mai Karfi. Kyadai ji dashi Ai Zan kirata namata barka. Allah yasa. Ni Zan tafi, haba Maryam tun Yanzu? Eh Ai nafi Mara Zumunci, ki kwantar da Hankalinki nima Zanzo. Muna jiran Ranar da babu. dahaka ta tashi Mumy taimata Rakiya.

Cikin daran Ranar Nakuda tazo ma mumy, tun tana daurewa Har takasa ta tashi daddy dake bacci cikin Rudu ya dau key din mota ya temaka mata Suka fita yasata Amota yadawo ya dau Nazir dake bacci Sai SULTANA HOSPITAL dake nan Unguwar Dosa KADUNA Mumy tasha wuya A wannan haihuwan dan saida Aka kwashi Awanni tana Abu daya daddy Zufa kawai yake yana kaiwa da komowa, daker ya'iya daukan waya ya kira Sulaiman ya Sheda mishi daga bisani ya kira Ahmad, Kusan atare Suka karaso Sulaiman da Maryam, Sai Ahmad wanda matarshi ta Haihu badaman tazo, Zuwan Su Kuma yayi daidai da fitowar wata nurses tasheda musu Anhaihu diya Mace, Atare Suka Shiga dakin Suna ma mumy Sannu yayin da daddy ya dau yarinyar, SUBHANALLAH tsarki ya tabbata ga Allah wanda da ikonshi yake Samar da Abu mai Kyau da Mara Kyau, daddy ne yafada yana nunama Ahmad (Abba) dake kusa dashi babyn, Sunyaba da kyan babyn Dan Ajin farkoce wajen Kyau. Ahakadai washe gari Aka Sallamesu Sukayi gida, Kai Alhmdullah duk dacewa Mumy bamai Son Zumunci bace mutane Sai zuwa barka Ake, Sabida kyan jariryar ke rudan wasu yarinyar tun tana jaririya da farin jininta. RANAR SUNA yan YOLA duk Sun Hallara Mutane kota'Ina kowa farin ciki yake Anci Ansha taron Suna yatshi lfy inda Yarinya taci Sunan Kakarta mahaifiyar babanta wato NAFISA Zasuna cemataa (Feenat) Haka Rayuwa tacigaba Mumy na kokari wajen faranta Ran mijinta yara kuwa Tasamu wata dattijuwa Ladi ita ke kula dasu.

Lokacin da Feenat tacika Shekaru Uku Alokacin Aka Sata makaranta nursery "iman Academy" dake Unguwar Dosa, makarntar hade take da Islamiyya, Idan Sun tashi 12am Sai suke Shiga Islamiyya 5pm driver ke daukosu lokacin Nazir yana primary6 Mamah LADI itaa ke kula da komai nasu, Feenat tana Maida Hankali yarinayace mai hazaka aduka bangare biyu, Bawanda feenah ke Kulawa Dan ita din yarinyace marason Hayaniya, Kawarta daya Halima Itama Sabida kokarinta Yasa Abotarsu tazo daya da Feenat, BAYAN WANI LOKACI Abubuwa da dama Sun faru, Feenat Sun Zana jarabawar fita daga Secondary. Ayayin da Suka kara Shakuwa da Kawarta leemah Sosai, daddy ya tura Nazir Kasar Turkey Achan yake cigaba da Karatun inda yake Karatun Soja, Alokacin Feenat ta damu kan rabuwarsu da yayanta Sabida Shakuwar dake tsakaninsu, Leemah Itama tasanar da feenat cewa brother dinta yaje karatu America yana karatu Doctor, Mumy takara Haihuwa inda ta Haifa Twins, Mace da namiji namijin yaci Sunan kakanshi daya Rasu Ibrahim Suna kiranshi (Mubeen) inda macen taci Sunan Mahaifiyar Mumy Aminatu Suna kiranta (mubeena) Anyi Shagali Sosai. Haryanzu mumy batasamu taje gidan Fatima matar Ahmad ba............Feenat basu hada iyayensu Kawanceba ita da Leemah Acewarsu Koda Zasuyi Karyar fita yawo sarinka karya dazuwa dagidajen juna tunda kowacce Agidansu Ansan irin Shakuwar da kawayen biyu Sukayi

BAYAN SHEKARU.

Wata tsaleliyar budurwace wadda Aqallah Zatai Shekaru 18 duguwace ba irin Sosai ba,farace mai matsakaitan idanu Samanshi dauke yake da dogayen gashin idanu, girarta Aciki take ta kwanta lufff, Tana da diri batada kiba Kuma ba Arame Take ba, kirjinta cike yake idan baka Zata ba Zaka Iya Cewa Wata mai yawan Shekaruce. fuskarta dauke take da dogon Hanci yayin da pink din bakinta y kasance karami, kwance take kan makeken gadon dake manne jikin ginin dakin tana danne dannen waya da Alama Chat take Ringing..... dayar wayar dake kusa da ita tafara. Hello besty daga dayan bangaren Aka amsa Hy feenat ina hanya zan zo gidanku fa, dagaske? Allah da gaske,Saikin karaso ok. Ba'afi Minti20 tsakaniba Saiga ta tashigo, turo Kofar tayi, dasauri Feenat ta Sakko Suka Rungume Juna, leemah Shine Baki gayamun Zakizoba, Sorry Kawata magana Zamuyi, Inajinki besty, Hawaye tafara Feenat yanzu Rabuwa Zamuyi, Zaro ido feenat tayi tace Akan me?muda muka Shirya yanda Rayuwarmu Zata kasance,kokinmance cewa komai namu iri dayane kinsan matsalata nasan taki,ke kikace Hatta Ranar aurenmu Rana daya zekasance, Leemah kin mance Ranar da kikacemun Mu Auri miji daya kokuma Mu Auri wa' da kani duk Dan mukasance Tare. Leemah duk kinmance yau kikemana Zancen Rabuwa. dan Allah Feenah ki kwantar da Hankalinki Ki Saurareni. INAJINKI besty Abba nane yasmamin Wata School Of Nursing A Abuja Shine yace Zai turani, Sabuwar Makarantace yanzu take tashe Akace. Hmmm Ajiyar Zuciya Feenat tayi tace Dan wan nan besty Shine kika dagamun hankli indan Wannan Zanmawa daddy magana Nima yasani Skul din Ai dani dake mai Rabamu Sai Allah.
πŸ’–πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’–πŸ’‹πŸ’‹πŸ’–
YAR LESBIAN CE
πŸ’–πŸ’‹πŸ’‹πŸ’–πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’–
By
Nadeeya Muhammad Ahmad

In dedicated to
Xaynab Ummu mahbub

Page....6

bayan tafiyar Leemah. fitowa tayi da niyar Samun daddy tafada mishi, mumy tasamu Zaune a parlor ga Twins gefenta bangare guda wasu takaddune birjik da Alama Akwai Abinda take nima cikinsu. tawowa tayi ta Zauna ta jingina da jikin Mumy, Mumy Sannu, yawwa my daughter Ai najiki da Halima Shine bata Shigo yau ta gaidaniba, mumy Tana cikin damuwa ne wai Acewarta yau Zamu Rabu, kinsan ma wai menene dalili?? "Aa"mumy tafada tana girgiza Kai, Mumy wai Akan Abbanta ya Sama mata Skul a Abuja,,,,,,, 😊Murmushi Mumy tayi tace Ai dole tace Za'a Rabaku tunda ganin Juna Zemuku wuya, da Sauri Feenat ta dago kanta, Mumy Zuwa nayi Nagayama daddy nima yakaini Skul din Ai, Ke dai kincika Son Rigima. daga.....koda yake aima kunfi kusa da dadyn naki mumy tafada tana daga kafadaπŸ™… Yayin da tacigaba da dube dubenta. Feenat Maida kanta tayi kan tv dake manne jikin bango, wani American film Akeyi a Mbc Action, lokaci daya ta rintse idonta ganin Abinda turawan ke Aikatawa, mace ce Rungume jikin Wani Saurayi Sanye da wata yar riga wanda komai na jikin ta Abayyane yake, shafa jikinta yake Very Slowly, Yayin da bakinshi yake cikin nata yana tshotsa Kamar yasamu Sweet, itakuma Hannu daya tasakalo ta bayanshi tana Shafawa tanayi tana lumshe ido,,,,,,,,, take wani Abu ya Ziyarci Feenat wanda takan Dan jishi lokaci Zuwa lokaci, Kafafunta tahada ta matsesu waje daya Dan wani Abu takeji kamar yana yawo jikinta, Remote tajawo ta chanza tasha Zuwa Zee Aflam, Cikin Kasan Zuciyar ta kuwa cewa take Aure Zanyi Gaskiya tunda malan musa yagaya mana idan Kaji makamancin Haka Sha'awa ce kuma wajibine kanimi mijin Aure idan Kaji Zaka Cutu.

Sallamr dady ce ta dawo da Feenat daga tunanin da takeyi, Amsawa Sukai Yayin da mumy ta tashi tayi hugging dinshi barka da dawowa, ga bashi ba nima da Aure nayi duk lokacin da mijina yadawo Haka Zanmai maiyuwa bazanji Abun da naji dazun ba, Feenat ke fira da Zuciyar ta, Ummina yau ba magana, cikin inda inda tace Sannu da zuwa daddy, yawwa Ummina ko bakijin dadine? Jiranka take Shiyasa tayi wani kamar Mara gaskiya mumy ta fada tana ciremai takalamin kafarshi, my Kinji mai mamynki ta fada ko fira Zamuyi, daddy kaci Abinci ka huta Saina fada maka, wayaki ya Saurari Zancen Umminshi cikin Zumudi? fadamun kamin naci Abincin, Sunkuyar da Kai kasa tayi daddy dama Akwai Wata Skul Of nursing da Aka bude a Abuja Abban Su Leemah Chan Ze kaita pls daddy inason Skul din nima. Shiru nadan lokaci daga bisani daddy yace ban Amince ba, nace ban Amince ba Ita Leemah din dako iyayenta bamu Saniba Zakice komai Sai kinyi irin nata, indai nine na haifeki ban yarda ba inada burin nayimuku komai dakuke bukata Amma banda wannan, daga haka yatashi ya Haura Sama, tashi mumy tayi Zata Bishi Feenat ta Rukota mumy pls kisa baki yabarni kinfi kowa Sanin irin Shakuwata da Leemah, Mumy tun muna yara fa muke......kuka ne ya kwace mata, dafa kanta mumy tayi tace my daughter am sorry to said you kibi Umarnin mahafinki, Sabida kinfi kowa Sanin dadynki yafi kowa Son yaga kunyi karatu kunzama wani Abu, tunda kikaga bai Amince ba kiyi hakuri Kawai, daga Haka mumy ta tashi. da gudu itama feenat ta tashi ta Haura Saman daret dakinta tayi tafada kan bed tana kuka mai tsuma Zuciya, Saida taci kukanta Mai isarta tukun ta jawo phone dinta tafara dealing number Leemah, HELLO.... my besty dafatan daddy ya Amince Kinga harna Suyomana wasu kayayyakin Amfani kinsan Anko Zamu rinkayi yanda Zamu birge duk wata maijin kanta Askul din nan, Ke Kinga wani takalmi duk yanda Akai kwanan nan yafito yayi Kyau, Ke mayyar Abaya nasiyo Miki Su birjik, idan Kinga Akwai Abunda kikeso ki hanzarta gobe Kije kasuwa, Dan Wlh harna hangomu A Skul din nan, Skul dinfa ance sai Dan wane da wane Kinga yanzu Za'a kara Sanin muba yaran Kananan mutane bane. besty kinbarni inata Mgn kice wani Abu mana.
Ajiyar Zurciya feenat tayi yayinda taji Son Kawarta ta yakara dira mata A'zuciya, Cikin dashashiyar murya tace leemah daddy.......aitun kamin takarasa Leemah tace kada kice mun be Amince ba Yanayin muryanki ya nuna Hakan. Wlh Leemah yace "Aa" Itama mumy namata magana wai nabi umarnin Shi hakan Shine daidai. Innalillahi ni Yanzu Zan iya cigaba da Rayuwa batare dake bane, Ina nima Nahakura da tafiyan nan duk Skul din dazakishiga nima ita nakeso. Karki haka Leemah kamata yayi kisa Abba yazo yasamu daddy ya fahimtar tashi. Wow inasonki Feenat kin Iya hango Abu mai Kyau, Bari Anjuma Zan Samu Abba na da maganar Allah yasa idan yazo daddy ya Amince, Amin dai my Leemah Nima inasonki. Nariga na dade dasani ai kawata, besty bari nacigaba da hada mana kayanmu, kincika Zumudi. Keko Ai dole Muma Zamu Zama manyan yara, Atare Suka kwashe da dariya. Jeki karasa saimunyi waya Anjuma. ok.bye.

Tunani Kawai take Azuciyarta barkatai Shin Anya daddy ze'amince kuwa? Kodai nakira Leemah Nace tabari, Maiyuwuwa Karatuna A kaduna Shine yafi Alkairi Shiyasa daddy yaki Amincewa, Toh Amma ai karatun zaifi dadi Idan kana Tare da kawarka wacce kuke Shawara da ita tunda Ita mumy bata fiye Zama Ai fira da Itaba. Kai kada na takurama Zuciyata kan tunani bari nabari Leemah ta turo Abbanta Kawai. remote tajawo ta kunna t.v. take Abinda tagani dazun a Mbc Action ya fado mata Arai, Haka kurum taji tana Sha'awar cigaba da kallon film din, bari nagani ko basu gamaba tafada cikin Ranta tana chanza Tashar, Oh Wow basu gamaba, 😨Kai basu gama irin wannan wajenba kenan film din duk haka yake, dukufa tayi tana kallo Sosai har'inda wasu turawa Su biyu Suke fira da Harshen turanci, dukansu mata ne, dayar ke fada ma yar'uwarta irin Son da take mata, Kallmar So karara take Zayyanemata kamar irin Saurayi da budurwa din Nan, take kuma tajawo ta Suka koma Suna fuskantar juna tana cigaba da gaya mata tana Shafa fuskarta, dayar ce takara matsowa Sosai ta hade bakinsu waje daya tafara kissing dinta Sosai, Feenat lisp dinta ta kamo tafara lasa jitake kamar itace Akema hakan, turawan Nan Sun lula har takai ga Sun cirema juna kaya, Shafeshafe Kawai Suke Suna nishi, Wayyo Allah feenat tafada tana kankame jikinta, dama Ana irin haka mace da mace Toh koshine lesbian din da naji Ana fada Kai Subhanallah Ance ubangijimu Allahu yana fishi mai tsanani damasuyi irin Wannan harkan. Kashen TV tayi gaba daya tafara istigifari na kallon da tayi, bangare guda jikinta Sai Rawa yake Wani Abu takeji yana yawo A jikinta, kawai itama Sha'awan take takasance jikin namiji. turo kofar Akayi cikin Sallama, Kasa amsawa tayi Saidai yunkurin tashi da takeyi takasa, my feenah fushi kike haryanzu jifa idonki Yanda Suka kumbura Alamar kuka kikai Sosai, Mumy banjin dadi ne, Sannu daughter na kada kisa Abun Aranki Kinji,

2 Comments On YAR LESBIAN CE Book 2
avatar
umar-6-7

1 year ago

Reply

Nice book

avatar
abubakar-ibrahim-7

4 months ago

Reply

Yes

Please Login or Register in order to submit comment